Kenza eBookz

Taimiyah book complete document by ayshat dansabo lemu txt by hausanovels com - Chapter 33

Taimiyah book complete document by ayshat dansabo lemu txt by hausanovels com - Chapter 33

Taimiyah book complete document by ayshat dansabo lemu txt by hausanovels com Chapter 33: Taimiyah book complete document by ayshat dansabo lemu txt by…

4,466 words

Yayi maganar yana jin yadda zuciyarsa ke cigaba da dokawa akan TAIMIYYAH,shi karan kansa ba zai iya fassara yanayin da yake ciki,akan ganin TAIMIYYAH da yayi yau ɗaya ba.Yana jin lokacin da Hajjah ta kai hannunta tana shafa sumar kansa,amma ya kasa ko da motsi kamar yadda itama Hajjah ba ta ce komi ba,suka ɗauki tsawon lokaci a haka,kafin Hajjah ta fara da cewa, "Abdulmaleek idan har TAIMIYYAH ta kasance,ita ce ake nuna maka wani ɓangaren na siffarta a cikin baccinka,to tabbas akwai wani ɓoyayyen al'amari da Ubangiji ya barwa kansa sani,jikina yayi matuƙar yin sanyi da jin hakan, kamar yadda wani sashi na zuciyata ke farin ciki da jin hakan,ka duƙufa da addu'a sannan kuma mu yi istikhara, mu nemi zaɓin Allah akan wannan lamari,duk abinda Ubangiji ya hukunta sai mu amsa a matsayin zaɓinsa ba na mu ba."

Maleek ya ɗago kansa daga jikin Hajjah,yana me zuba mata manyan idanunsa,kafin ya jinjina kai yana cewa, "Hakane Hajjah,amma baki ji yadda nake ji a cikin zuciyata ba,ba kiji yadda ƙirjina ke bugawa da wani yanayi da baki ba zai iya miki bayani ba Hajjah,koma miye zai faru na rigama na sallama, ina kuma ji ajikina da wuya ƙaddaran aure bai haɗani da Zaynab ba,don yadda zuciyata ke doka mata ban taɓa jin irin hakan akan kowace mace ba,zan aure ta, zan kuma zauna da ita har ƙarshen numfashi na Hajjah."

Maleek ya yi maganar yana duban yadda wani irin abu ya haska a idanun Hajjah,kafin fuskarta ya washe da wani irin faffaɗan murmushi,wanda ya jima bai ga irinsa akan fuskar Hajjar ba.Ta cigaba da kallonsa da tsananin mamaki da murnan jin kalaman da suka fito daga bakinsa,ta kamo hannunsa ta riƙe tana cewa, "Maleek daga gani ɗaya da ka yi wa TAIMIYYAH har ka yanke cewa zaka iya aurenta,da gaske ka ke yi za ka iya aurenta ka zauna da ita a yadda take babu cutarwa? Bana so ka yi gaggawa har sai ka tabbatar da irin ƙaunar da kake mata a zuciyarka,bana so ka ji tausayin nakasanta ka ce za ka aureta don hakan,ina so ka aureta da zuciya ɗaya ne,kuma kana me jin so da ƙaunarta, ba wai don tana gurguwaba sai don ɗabi'u da kyawun tarbiyyyah da nagartarta.Don haka kamar yadda na faɗi ne ka je kayi istikhara ka nemi zaɓin Allah, duk abinda ka cigaba da ji akanta ka sanar dani,ni kuma na yi alqawarin nema maka aurenta da gaugawa,Allah shi kaɗai yasan abinda yake nufi da haɗuwata da wannan Yarinyar,don ina jinta a zuciyata fiye da yadda zan iya misalta maka Maleek."

Hajjah tayi maganar cike da nuna irin ƙarfin ƙaunar da take ji akan TAIMIYYAH,ta cigaba da cewa, "Ina fata baka sanar da ita wanda ya tura ka xuwa gareta ba,don bana so su san cewa kai ɗana ne,har sai ka ji da gaske kana ƙaunarta, za ka kuma iya zama da ita tsakaninka da Mahaliccin sammai da ƙassai,sannan idan har Zaynab ba ta aminta da kai ba, to zamu haƙura da ƙudirinmu don ba zan so ai mata dole ba."

Kalaman Hajjah na ƙarshe ne suka girgiza zuciyar Maleek Ado,har yayi saurin ɗagowa ya dubi Hajjah, da wani yanayi akan fuskarsa ya ce, "A'a Hajjah ki daina faɗin hakan don Allah,ban fara jin irin wannan yanayin da nake ji akanta don in daina ba,tun kafin na yi tozali da ita a zahiri in ga irin idanun da nake gani a cikin baccina,na ke shiga wani yanayi kafin in koma da walwalata,a yau dana gansu a zahiri saman kyakykyawar wannan halittar, ba na ji zan sake samun sukunin zuciya da cikakkiyar nutsuwa,ba tare da na mallaketa gaba ɗayanta ta dawo a ƙarƙashin ikona ba,don haka don Allah ki daina fatan ba za ta so tilon ɗanki ba please!"

Yadda Maleek ya ƙare maganar cike da magiya,abin har al'ajabi ya bai wa Hajjah.Ta jinjina kai tana sake sallamawa ƙudiran Ubangiji,don bata taɓa tunanin ganin irin abinda take gani a yanzu akan fuskar Maleek ba.

Hajjah ta dafa kansa tana faɗin, "Shikenan Maleek ka kwantar da hankalinka, In sha Allah alkhairi zai biyo bayan wannan lamarin."

Maleek sai ya tashi daga ƙasan carfet,ya nufi kan doguwar kujeran Hajjah ya zauna,yana me zamewa kaɗan bayansa ya ginjina da jikin kujeran sosai,sannan ya lumshe idanunsa. Hajjah ta nufi ɓangaren dining,inda aka aje wani ƙaramin fridge,ta ciro goran ruwa me matsakaicin sanyi,ta nufo wajen da Maleek ke zaune idanunsa a lumshe.Ta ɓalle murfin goran ruwan tana miƙa masa ta ke cewa, "Maleek karɓi ka sha ruwan sanyi,ko ka dawo cikin nutsuwarka sosai."

Maleek sai ya buɗe idanunsa yana kallon goran ruwan da Hajjah ke miƙo masa,kafin ya kai hannu ya amsa goran yana cewa, "Thank u Hajjah." Daga haka ya kai goran ruwan kan bakinsa,ya fara sha sanyin ruwan na ratsa maƙoshinsa,ya sha fiye da rabin ruwan sannan ya aje goran daga ƙasa yana sauke numfashi. Ya dubi direction ɗin da Hajjah ke zaune ta tsura masa ido,ya jefeta da murmushi me sanyi.Hajjah ta maida masa da martanin murmushin,sannan ta yi magana cike da tsokana ta ce, "Maleek ashe dai karon ka da gurguwar Hajjah me zafi ne,tunda gashi haɗuwa ɗaya duk ka fita hayyacinka,da kai ka ɗauka aljanace kake gani da idanun bil'adama a cikin baccin naka?"

Maleek ya jinjina kai yana cewa, "Seriously Hajjah ba za ki gane me nake ji akan wannan yarinyar ba yanzu, ki taimaka ki bani numbarta zan yi magana da ita zuwa anjima."

Hajjah ta saki murmushi me faɗi,kafin ta tashi ta ɗakko wayarta ta miƙawa Maleek.Ya amsa yana dubanta da fuskar shagwaɓa yace, "Hajjah to wani suna ki kai saving numbar da shi?"

Hajjah ta aika masa harara tana cewa, "TAIMIYYAH." Daga haka ta koma ta zauna murmushi na blushing saman fuskarta.Maleek ya shiga contact ɗin wayar Hajjah, ya lalubo sunan TAIMIYYAH,yana lode lambobin cikin wayarsa wani irin yanayi na kewaye zuciyarsa.

Ya tashi ya isa inda Hajjah ke zaune, ya aje mata wayar a kusa da ita ya ce, "Hajjah Allah ƙara girma zan fita yanzu,amma zuwa anjima zan dawo kafin in wuce GRA,ina fata zuwa lokacin an yi min soup ɗin dana ce."

Daga haka sukai sallama da Hajjah,ya taka yana barin cikin falon,gabaki ɗaya yana ji tamkar ana ingiza zuciyarsa,akan son sake ganin waɗannan idanun a saman fuskar TAIMIYYAH.

Da ƙyar ya iya controllling zuciyarsa, har ta iya haƙura da kiran TAIMIYYAH vid call,ya haƙura sai zuwa dare idan ya koma can gidansa,ya nutsuwa akan gadon baccinsa sannan sai ya kira ta.

Ya karya kan motarsa da ya ɗauka a gidan Hajjah, ya kamo hanyar shiga cikin City,don zuwa wajen wani old friend ɗinsa da ke Unguwar Alƙali cikin Zaria City........✍🏻

#Ɗansabo ce# [12/14, 10:12 PM] +234 703 769 7050: Littafin TAIMIYYAH paid book ne,ga duk wanda ta tsincesa a kowani irin group ne,kiji tsoran Allah karki karanta sai kin biya 500 naira only.

Za ku iya min magana ta wannan number ɗin 08167768704, ko kuma ku turo kuɗin ku kai tsaye ta wannan account ɗin 0504192664 aisha ibrahim dansabo GTbank.*

*Sai ku tura shaidan biyanku ta wannan line ɗin 08167768704.*

Masu turo credit za ku turo katin MTN na 500 ta wannan line ɗin 08167768704.

_Ina ƴan kasuwa masu buƙatar a tallata muku hajar ku? Maza ku garzayo da kuɗi ƙalilan a tallata muku kayan siyarwanku sai dai kawai ku ji ana kiran waya don buƙatan sayan kayan ku,ku tuntuɓeni ta layina kamar haka 08167768704._

*57*

Basmah da qawayenta,Amna da Sharifa ne zaune cikin ɗakin baccin su Basman.Sharifa ta dubi Basmah tana cewa, "Besty ni fa wallahi na yi matuƙar mamakin jin cewa, wai an sanya miki ranar aure kamar daga sama,shi ko wannan wani guy ne ya zo da zafinsa haka,a ina kuka haɗu?"

Basmah ta saki ƙayataccen murmushi tana duban cikin idanun Sharifa ta ce, "Ke dai bari kawai ƙawata,da zafinsa ya zo kam amma maganan long story ne,bari in baku labarin yadda muka haɗu...."

Basmah ta zayyane ma su Sharifa labarin tun farkon ganinta da Nass tare da TAIMIYYAH,har kawo yau da ake zancen aurensu,nan da watanni uku masu zuwa.Ta kare maganan tana cewa, "Friends wallahi ni kaina ganin abin na ke kamar a dream da,amma tunda Umma ta je Yobe ta kai sunansa wajen oga teacher,shikenan komi ya tafi yadda muke so,kar ku so ku ga yadda Nass ke nuna min so a yanzu,kamar dama can ni zuciyarsa ta fara so ba wata gurguwaba."

Ta kai ƙarshen maganar tana kwashewa da dariya, su Amna na taya ta.Kafin su tsaida dariyan Sharifa na faɗin, "Ke bamu mu ga pics ɗinsa inga kalarsa ,da har kika iya rufe ido ki kai wa ƴar uwarki ta jini ƙwacensa,gaskiya Basmah ba ku da kyau. Ni har tausayin baiwar Allah ya kamani,da ace uwarsa bata raba alaƙar dake tsakaninsu ba, ahakan zaku farraqa tsakaninsu ki auresa babu tsoran Allah?"

Sharifa ta ƙare maganar da tambayar Basmah, tana tsare ta da ido.Basmah tayi saurin haɗe fuska tana dannawa Sharifa harara ta ce, "Eh...! Lallai Sharifa Salis, yaushe kika fara wa'azi bani da labari? Ke idan ana maganar wanɗanda suka san kan snatching har kya yi motsi ma,kar ki ɓata min rai please! Bari dai in nuna miki kalar haɗuwarsa,sannan sai ki san cewa ko ke ce, za ki iya yin komi don ya zama mallakinki."

Basmah tayi maganar tana danno pic ɗin Nass,wanda ya yi azabar kyau.Ya ɗauki pic ɗin ne sanye da ƙananun kaya,a wani haɗaɗɗen wajen cin abinci a garin Abuja.Ta miƙawa Sharifa wayar tana cewa, "Amshi ki gani ƙawata."

Sharifa ta miƙa hannu ta amsa wayar Basmah,tana ɗaura idanunta akan screen ɗin wayar,idanunta suka sauka akan kyakykyawar fuskar Nass Aliyu.Take ta ji wani dumm..! Cikin kanta,ta sake tsurawa hoton idanu tana sake hango tsantsar kyawunsa da haɗuwarsa,tabbas bata ga laifin Basmah da ta ruɗe akansa, har suka shiga suka fita za ta mallakesa ya zama nata ba.

Ta ɗauke idanunta daga duban hoton, ta mayar kan Basmah dake ta faman blushing,idanunta akan Sharifan. Sharifa ta miƙawa Amna wayar tana cewa, "Ungo Amna ki gani,gaskiya guy ɗin ya haɗu ba karya wallahi."

Amna ta amsa wayar ta kalli pic ɗin per seconds,sannan ta miƙawa Basmah wayarta tana cewa, "Gaskiya ya haɗu ba karya Basmah,banga laifinki ba don ko ni na samu dama zan iya yin wuff da shi."

Basmah ta warce wayarta daga hannun Amna, ta tsuke face ta ce, "Ban son iskanci ƙawata, a gabana ki ke faɗin hakan?"

Sharifa ta amshe da faɗin, "To miye aciki ke ma ai ƙwacensa ki ka yi ƙawata,bare ma wasa Amna take yi miki,Allah ya sanya alkhairy ya kaimu lokaci,mu ci uwar sabada a ranar."

Suka sheƙe da dariyar shaƙiyanci,Basmah na cigaba da basu labarin yadda tsare-tsaren bikin zai kasance.Sai can yamma shaƙiƙan ƙawayen Basmah na tun secondary skull,wato Sharifa Salis da Amna Muktar suka bar gidansu Basmahn,bayan ta yo musu rakiya har bakin gate.

__________

TAIMIYYAH da tunda ta shige ɗaki bayan tafiyar Maleek Ado,ba ta fito ba sai bayan sallan isha'i.Direct kuma wajen cin abinci ta nufa don yin dinner,ta zauna bada jimawa ba Iyah ta iso wajen,tana ɗaura idanunta akan TAIMIYYAH ta ke cewa, "Au ashe kin fito,da yanzu ai nake shirin zuwa ɗakin naki inga ko lafiya,daga tafiyan mutum sai ki ƙule a ɗaki kina faman tunane-tunane,to ni dai babu ruwana bana son kina sanyawa kanki damuwa akan abinda bai kai ya kawo ba.Ki yi addu'a a duk abinda kika ga ya shigo cikin rayuwarki,Allah baya taɓa jarabtar bawa sai akan abinda zai iya ɗauka,don haka ki dinga sanyawa kanki salama don Allah Zainabu."

TAIMIYYAH ta ɗaga kai ta dubi Iyah da manyan idanunta kafin ta ce, "Hakane Iyah nima ba tunani nake yi ba,kawai na ɗanyi karatu ne sai na tsaya duba wasu littafai,ganin lokacin sallah yayi yasa na tsaya na gabatar da sallar magriba, na jira akai isha'i sannan na fito cin abinci."

Iyah ta zauna tana faɗin, "To da dai yafi miki Zainabu kar kiji tsoran komi, In sha Allah koma waye alkhairy ne ya kawo sa ba sharri ba."

Daga haka suka zuzzuba abincin suka fara ci,suna hira kaɗan-kaɗan har suka kammala cin abincin.TAIMIYYAH ta koma daga cikin falon Iyah ta zauna,tana ɗaukar remote ta sauya tasha zuwa Bollywood.So take yi ta hana zuciyarta yawan tunanin mutumin ɗazu,ta ƙura ido akan TVn ba don tana da tabbacin zata fahimci komi ba.Ta rasa meyasa tunaninsa yaƙi fita daga zuciyarta,ya yi mata tsaye a rai, da ta rufe ido hannuwansa take ji a fuskarta,ta yi saurin sake manna idanunta akan screen ɗin TV, tana kallon fuskar fararen fatar dake gilmawa a ciki,ba tare da ta san kan film ɗin ba, bare ta fara fahimtan ina aka dosa ma.

Ƙaran shigowar saƙo cikin wayarta,yasa ta ɗaga ido ta kalli agogon dake manne jikin bango,inda ya nuna ƙarfe 8:49pm (Takwas da mintuna arba'in da tara na dare).

Sai ta maido dubanta kan wayarta,tana me kai hannu ta yi swiping screen lock ɗin wayar.Idanunta ya sauka akan baƙin lambobin da aka turo saƙon,sai ta samu kanta da buɗe saƙon don ganin daga waye?

_"Salam Zaynabbb! Hope u are fine,please zan kira vid call in the next some minutes,ki yi picking call ɗin please!_ "

Waɗannan sune kalaman dake rubuce cikin saƙon.TAIMIYYAH ta karanta saƙon a ƙallah kusan sau uku, amma brain ɗinta bai kawo koda wasa cewa daga Maleek bane,don ta san har suka rabu bata bashi numbarta ba, 'To ko dai Yah Emran ne?', Tunaninta ya haska mata hakan, tana jin wani abu na taɓa ranta.Sai dai kafin ta sake wani dogon tunani, kira ta vid call ɗin ya shigo wayarta,ta tsurawa wayar ido tana ji haka kawai zuciyarta na fara dokawa da ƙarfi. Sai ta miƙe tsam! Tana duban Iyah da ke zaune cikin falon,ta nufi hanyar zuwa ɗakinta tana cewa, "Iyah bari in amsa call, idan na gama bacci bai zo ba,zan dawo na ƙarisa kallon."

Ta cigaba da dafe ƙafarta tana takawa ta nufi hanyar ɗakinta,Iyah tabi bayanta da kallon tana ɗan taɓe baki, ta miƙa hannu ta ɗakko remote,ta canza tasha daga Bollywood zuwa Sunnah TV.

TAIMIYYAH na shiga ɗakinta zama tayi daga bakin bed, lokacin da wani kiran ke shigowa,ganin wannan karon ba vid call bane,sai zuciyarta ta ingizata akan ta ɗaga wayar ta ji ko waye?

Ta yi receving call ɗin tana kai wayan kunni ba tare da tace komi ba,sai ƙirjinta da ke faman doka mata da wani irin yanayi da bata san dalilin hakan ba.

Ƙasaitacciyar muryar Maleek Ado ne ya shiga kunnuwan TAIMIYYAH, in da ya ke cewa, "Hello! Zaynabb!"

Take wani abu ya doka cikin tsakiyar kan TAIMIYYAH. Ta yi saurin dafe wayar da ke neman suɓucewa a hannunta, tana cigaba da yin shiru ba tare da tayi magana ba,har sai da muryar Maleek ya sake kiran sunanta, cikin wani irin salo da bata taɓa jin mahalukin daya iya sarrafa harshensa, wajen iya kiran asalin sunanta kamar haka ba.

Ta saki numfashin da bata san ta riƙe ba kafin ta furta, "Na'am wa ke magana please?"

Tayi tambayar cikin sanyin murya sosai,tana jiyo yadda shi ma ya sauke numfashi daga ɓangarensa, kafin ya furta, "Maleek Ibrahim ne Zaunabb! Meyasa ba ki yi picking vid call ba,ko ba ki ga message ɗin dana turo miki before in kira ba ne ?"

Ya yi maganar cikin muryarsa me cike da izza,yana sauraran jin me TAIMIYYAH za ta ce? Ta buɗe baki murya can ƙasa take cewa, "Ban san lambar waye ba ne,sabida ban baka lambata ba,don Allah ya aka yi ka samu lambata?"

TAIMIYYAH ta jefa masa tambayar cikin wani irin sanyin muryar ta.

"Ki yi picking vid call da zan kira yanzu Zaynabb please!"

Maleek ya furta hakan yana cuting call ɗin,ya kira ta vid call ɗin.

TAIMIYYAH sai ta janyo Hijab ɗinta da ke saman gado ta sanya, kalar Hijab ɗin blue black ne,sai da ta gyara zaman wuyan Hijab ɗin sosai sannan tayi receiving vid call ɗin,tana jin yadda bugun zuciyarta ke ƙaruwa.

Kyakykyawar miskilalliyar fuskar Maleek Ado ne,ya bayyana akan allon screen ɗin wayarta,yana kwance daga kan makeken bed ɗinsa,yana sanye cikin milk ɗin pajamas da suka haske fatarsa. TAIMIYYAH tayi saurin ɗauke face ɗinta daga dubansa.Maleek Ado da idanunsa ke kan screen ɗin wayarsa, lokacin da kyakykyawar fuskar TAIMIYYAH ta bayyana masa,sai ya samu kansa da lumshe idanunsa, wani abu na sake dokawa cikin kansa.Ya buɗe idanun ya sauke a side face ɗinta,sabida yadda ta ƙi yadda ta sake kallonsa ta cikin wayartata.Sai yayi magana very low yana cewa, "Zaynabb ki kalleni don Allah ko zan samu cikakkiyar nutsuwa,idan na sanya idanuna cikin kwayar idanunki,waɗanda suka jima suna gilmayya cikin barcina."

Waɗannan furucin da Maleek ya furtasu,su suka sanya TAIMIYYAH saurin duban fuskar wayarta.Manyan idanunta suka sake sauka akan fuskar Maleek,wanda idanunsa ke kafe akan allon screen ɗin wayarsa,ya sauke ajiyar zuciya yana kallon cikin idanun TAIMIYYAH,wani baƙon yanayi na sake lulluɓe ruhinsa,tare da aika wani irin zazzafan saƙo,cikin kowacce kafa ta sadarwa da ke jikinsa.TAIMIYYAH ta sake ƙasa da murya tana cewa, "Don Allah ka daina jefa zuciyata cikin ruɗani,tun ɗazu ka ke furta wasu kalamai da ke nuna kaman ka taɓa sanina awani waje,please! waya turo ka zuwa gareni,ko ince a ina ka taɓa ganina da har kake ganin idanuna acikin baccinka?"

TAIMIYYAH ta kai ƙarshen maganar tana duban fuskar Maleek Ado,cike da son ya fayyace mata yadda aka yi ya santa, har ya kawo kansa gareta.Sam ita ba ta san irin illar da salon maganarta ya yiwa zuciyar Maleek Ado ba,wanda tunda ta fara magana yake duban fuskarta da manyan idanunta,waɗanda suka ƙara girma bisa screen ɗin wayarsa.

Ya wani cije lips ɗinsa, yana ji tamkar ya tsinci TAIMIYYAH a kusa da shi,don kawai ya tasata a gaba ya yi ta kallon kwayar idanunta,waɗanda suka jima suna ruɗa tunaninsa a cikin mafarki.Idanun da ya gama sallamawa cewa ,na wata aljanace can daban wacce ke son kawo ruɗani cikin duniyarsa, a wancan lokacin,amma sai gashi yau Allah ya bayyana masa cikakkiyar surar mamallakiyarsu a zahiri,cikin lokacin da bai taɓa tunani ko hasashe ba, 'ta ya shi ko zai yi sakacin da wannan halittar za ta kubce masa?' Tunanin ya haska cikin kansa da wani irin tasirin da bai taɓa tunani ba.Ya sake duban fuskarta wacce ta sunkuyar da shi ƙasa,da alamu tafin hannunta take kallo,sai ya sake kiran sunanta 'Zaynabb!' TAIMIYYAH tayi firgigit! Ta ɗago manyan idanunta da suka sake girma ta sauke akan fuskarsa,tana me shagwaɓe fuskarta da muryarta duka a lokaci guda,sannan ta furta, "Na'am! Don Allah ka sanar da ni waye kai? A ina ka sanni please!?"

Maleek ya ɗan taɓe baki yana sake miskile fuskarsa ya ce, "Zaynabb meyasa na ke baki tsoro ne wai? Sunana Maleek Ado na sanar miki tun ɗazu,maganar ki san ko ni waye za ki sani amma ba yanzu ba,in da na sanki kuwa da kike magana akai,to a cikin mafarkina na fara sanin idanunki ba fuskarki ba,a cikin mafarki na fara jin wannan muryar taki me kama da magic,a cikin mafarki na san wani ɓangare naki Zaynab,shiyasa yau da idanuna suka sauka akanki,gaba ɗaya na rasa dukkanin nutsuwata.Oya tell me wacece Zainab TAIMIYYAH please?"

Maleek ya yi maganar yana duban yadda TAIMIYYAH ta zaro idanunta, cike da zallar mamakin kalamansa take dubansa,don baƙarmin tsoratata kalamansa na cewa a cikin mafarki ya fara saninta su kai ba.Ta buɗe baki muryarta na shaking take cewa, "Na ji zan sanar da kai komi game da ni, amma sai ka fara bani labarin yadda aka yi, ka ke mafarki da irin idanuna."

Karon farko da Maleek Ado ya saki murmushin da bai shirya yinsa ba,idanunsa na zube fes akan fuskar TAIMIYYAH.Kafin ya maida face ɗinsa ya miskileta kamar yadda take ada, yana farawa da faɗin. "Zaynab zai kai kaman watanni shida zuwa takwas baya, da na fara mafarki da me siffar idanunki a cikin baccina,ya zamana kusan kullum ne sai nayi mafarki da Yarinyar me irin idanunki, amma ba'a taɓa nuna min zahirin fuskar ko wace ce ba,sai dai a nuna min waɗannan idanun masu haske,suna kuka tana miƙo min hannu kamar tana buƙatan taimako daga gare ni,da zaran na miƙa hannu zan kama hannun da ta ke miƙomin, sai na mafarka daga baccin ina jin wani irin yanayi da bana iya fassara shi...."

Ya ɗan numfasa kaɗan kafin ya cigaba da cewa, "Tun ina yin mafarkin jefi-jefi har mafarkin ya zame min jiki,kuma duk sanda na farka na kan yini cikin tunanin, wace ce wacce ake nuna min idanunta amma bana ganin zahirin surar fuskarta? Amma har in ƙaraci tunanina bana gano komi,daga ƙarshema sai na sanyawa zuciyata cewa aljana ce kawai,don inba aljana ba babu yadda za a yi mutum ya dinga ganin siffar idanu babu fuska,ban kuma taɓa gayawa kowa ina mafarkin ba sai sau ɗaya dana faɗiwa Mahaifiyata,tun kuma bayan dana sanar da ita bada daɗewa ba sai na daina mafarkin baki ɗaya,ban kuma ƙara tuhuman kaina ko meyasa na daina yawan mafarkinba,illa daɗi da naji a lokacin ina cewa addu'ata ne ya amsu, Allah ne ya rabani da ganin idanun aljanar mafarkina.Kwatsam! Sai gashi yau na ga irin idanun akan fuskarki a zahiri Zaynab,ta ya bazan ruɗe har in kasa controlling kaina ba?"

Ya kai karshen maganarsa yana duban yadda TAIMIYYAH ta nutsu tana saurarensa.....✍🏻

#Ɗansabo ce# [12/14, 10:12 PM] +234 703 769 7050: Littafin TAIMIYYAH paid book ne,ga duk wanda ta tsincesa a kowani irin group ne,kiji tsoran Allah karki karanta sai kin biya 500 naira only.

Za ku iya min magana ta wannan number ɗin 08167768704, ko kuma ku turo kuɗin ku kai tsaye ta wannan account ɗin 0504192664 aisha ibrahim dansabo GTbank.*

*Sai ku tura shaidan biyanku ta wannan line ɗin 08167768704.*

Masu turo credit za ku turo katin MTN na 500 ta wannan line ɗin 08167768704.

_Ina ƴan kasuwa masu buƙatar a tallata muku hajar ku? Maza ku garzayo da kuɗi ƙalilan a tallata muku kayan siyarwanku sai dai kawai ku ji ana kiran waya don buƙatan sayan kayan ku,ku tuntuɓeni ta layina kamar haka 08167768704._

*58*

TAIMIYYAH gaba ɗaya kanta kullewa yayi da jin labarin mafarkin da Maleek Ado ya yi tayi a baya,kuma wai me irin idanunta Maleek ɗin ya ke gani a cikin mafarkin nasa. Memakon ta tsaya ta cigaba da sauraransa, sai kawai ta kashe wayarta,tana me jingina jikinta da jikin gadon, ta lumshe idanunta.

Bakomi ke yawo a kanta ba, sai moment ɗin ɗazu da yamma zuwa yanzu,gaba ki ɗaya sai ta ji tana tsoran Maleek ɗin ma baki ɗaya.Tana ji yana sake kiranta amma tayi biris da wayar,har ta gama ɓurarinta ta tsinke,zuwa can sai ta ji ƙaran shigowar saƙo cikin wayartata.

Ta miƙa hannu a hankali kamar me tsoron taɓa wayar,ta janyota ta yi swiping tare da buɗo saƙon kai tsaye,don ganin me ke rubuce a ciki,idanunta suka sauka akan kalaman daya aiko kamar haka, " _Zaynabb meyasa zaki kashe min waya?Zan barki ki nutsu da kyau, amma kada ki ce za ki damu kanki da yawan tunanin,cewa sai kin san ko waye ni cikin gaggawa,soon za ki sani Zaynabb.Gud night wife to be._ "

TAIMIYYAH ta dinga karanta saƙon yafi sau goma,kanta na sake ɗaurewa tare da jin matsanancin fargaba, da tsoron wannan mutumi.Kalamansa na ƙarshe ke sake gigita tunaninta inda yace "Wife to be." Tunanin ya haska da wasu irin tarin tambayoyi da suka cika kwanyarta, 'A ina ya san ni,kuma waye ya bashi numberta har ya kirani,ba tare da na bashi ni a karan kaina ba?"

Waɗannan tambayoyin suka cika zuciyar TAIMIYYAH, tare da sake kulle mata kai,ta ƙurawa saƙon idanu tana sake karantawa a karo na goma sha ɗaya.Ta ɗauke dubanta daga karanta saƙon, tana nanata sunansa akan harshenta a bayyane, "Maleek Ado." Kamar yadda ya rubuta daga ƙasan saƙon,ta maida idanunta ta lumshe abinda ya faru ɗazu a falon Abie na dawowa kwanyarta, 'Kenan da gaske mafarkin ya ke yi da irin idanunta,shiyasa ya shiga shock lokacin da ya ganta a zahiri,har yana kasa riƙe kansa sai da ya taɓa fuskarta?" Wannan tunanin ya haska cikin kanta,tana jin wani irin abu na shiga jikinta yana ratsa ɓargonta.Ta sake rintse idanunta zuciyarta na wani irin bugu,ta buɗe idanun tana kai hannu ta shafa fuskarta,ji take yi kamar har lokacin lallausar hannunsa na kan fuskarta ne.

Da ƙyar TAIMIYYAH ta iya yakice tunanin komi, ta sakko daga kan bed ɗin ta nufi toilet,alwala ta ɗauro ta fito ta nufi kan sallaya don gabatar da shafa'i da wuturi, wanda bata yi sai za ta kwanta bacci.

Lokacin da ta idar light off kawai ta yi ta bi lafiyar gado,bayan ta canza kayan jikinta zuwa na bacci,ta jima sosai tana faman tunane-tunane duk akan Maleek Ado.Wanda ya yi mata tsaye a cikin rai, ta ke kuma da buƙatan sanin cikakken waye shi,ya akayi kuma har ya kawo kansa gidansu alhali yace mafarki ya ke kawai da me irin idanunta? Sai da TAIMIYYAH ta ga cewa tunani zai iya halaka kwanyarta, sannan ta lumshe idanunta tana fara karonto azkar na kwanciya bacci.

_____________

A ɓangaren Maleek Ado kuwa,lokacin da ya turawa TAIMIYYAH saƙon,sai ya maida kansa ya kwantar akan pillow yana me lumshe idanunsa.

Muryar TAIMIYYAH da salon maganarta ke dawo masa,yana jin wani irin feeling na dabaibaiye zuciyarsa.Idanunta yake haskowa a lokacin da take waro masa su,bayan ya gama bata labarin mafarkin da ya dinga yi da mai irin idanunta.Kyakykyawar murmushi ya bayyana a saman miskilalliyar fuskarsa,ya kai hannu zuwa kansa yana yamutsa sassalkan gashin kansa me matuƙar ɗaukar ido,sabida kuɗin da suman ke ci ba kaɗan bane.

Kiran Suhailah ne ya shigo cikin wayarsa,hakan ya dawo da shi cikin hayyacinsa,daga duniyar tunanin TAIMIYYAH da ya lula.

Ya miƙa hannu ya janyo wayar, yana receiving call ɗin tare da gyara kwanciyarsa sosai.Muryar Suhailah cikin shagwaɓa ya shiga kunnuwansa lokacin da ta ke cewa, "Hello! my Maleek kana jina?"

Maleek ya buɗe idanunsa yana cuting call ɗin,ya kirata vid call kawai don yana buƙatar ganin yanayin da take ciki.

Fuskar Suhailah zuwa gangar jikinta ne ya bayyana a allon screen ɗinsa,lokacin da Suhailah tayi receiving vid call ɗin.Maleek Ado ya sauke ganinsa a kan rigar baccin da ke jikinta kalar pink me santsi,rigar me faɗin wuya ce hakan yasa ƙirjinta ya fito sosai ta sama.Ya ɗauke idanunsa daga kallon ƙirjinta ya mayar zuwa kan fuskarta,idanunsu suka gauraya dana Suhailah, wacce ita ma nata idanun ke kan kallon face ɗinsa.Ta sakar mata kyakykyawar murmushi tana faɗin,

"My Maleek i miss u,tun ɗazu nake kiran line ɗinnan naka ina jin busy,na kira Hajjah ma bata ɗaga ba,har yanzu fa bana jin daɗin jikina Baby."

Tayi maganar cike da shagwaɓa ganin yadda Maleek ɗin ya tsura mata ido,kafin ya buɗe baki kamar mara son magana ya ce, "Sorry wife,sauƙi ai a hankali yake samuwa, hope dai kina shan magungunan yadda ya dace?" Suhailah ta gyaɗa kai cike da tabbatar masa da cewar tana sha,sai Maleek ya cigaba da cewa,

"Alright! Karki damu zazzaɓin zai tafi soon wife,but i miss u wife so much,oya kiss me wife."

Readers Also Read