Kenza eBookz

Taimiyah book complete document by ayshat dansabo lemu txt by hausanovels com - Chapter 35

Taimiyah book complete document by ayshat dansabo lemu txt by hausanovels com - Chapter 35

Taimiyah book complete document by ayshat dansabo lemu txt by hausanovels com Chapter 35: Taimiyah book complete document by ayshat dansabo lemu txt by…

4,471 words

Basmah tayi maganar tana miƙawa Zuhurah kuɗin,Zuhurah ta amsa Basmah ta fice don tafiya inda za ta.

Daga can ɓangaren sasan Iyah kuwa,lokacin da ta isa cikin falonta sai ta wuce zuwa ɗakin TAIMIYYAH direct. Ta samu TAIMIYYAH a kwance ta yi zurfi cikin tunani,sai ta zauna daga gefen gadon tana cewa, "Zainab tashi mu yi magana."

TAIMIYYAH ta yinƙura ta tashi zaune, tana duban Iyah fuskarta a narke,Iyah ta dubi TAIMIYYAH tana cewa, "Zainabu kin ji dai da maganar da Hajiya ta zo mana da shi ko? Bana so ki zafafa ko ki hana kanki sukuni da yawan tunani,ki fawwala Allah lamarin mu kuma yi addu'a, don bamu san abinda Allah ke nufi da haɗamu da waɗannan bayin Allah a rana tsaka ba,jikina ya yi sanyi da bayanin da Hajiyar ta yi akan mafarkin da ya ke yi da me irin idanunki,kar ki damu kanki da yawan tunani kamar yadda Hajiyar ta ce, ki saurare shi mu kuma yi addu'a, Allah ya zaɓa mana mafi alkhairy,idan mijinki ne za ki aure shi ko muna so ko bama so,don haka tun daga yau ki dage da addu'a, mun rabu da ita akan cewa zan saka Babanki Sani yayi bincike akan su,duk abinda muka ji zan sanar da ita sai a turo manyansa,don nema masa izinin fara zuwa zance wajenki sabida ku fahimci juna,ina fata ko don ƙaunar da ta nuna akan ki,ba za ki guji jininta tilo ɗaya da ta mallaka ba,matuƙar mun same sa da kyawawan halayya,Allah ya duba maraicinki ya yi miki zaɓi mafi alkhairy."

TAIMIYYAH da duk jikinta yake a sanyaye ta amsa da cewa, "Ameen Iyah amma ni tsoro nake ji, ina ganin kamar sun fi ƙarfinmu, kuma kar ki manta yana da mata ,kuma jininsa ce matar Iyah,ni dai gaskiya tsoro nak....."

"Zainabu kar kice za ki ja da yin Allah,ki yi addu'a ne kamar yadda na faɗi,kasancewarsa me mata ba abin damuwa bane, don Allah ya fiki sanin komi amma kuma ya kawo shi cikin rayuwarki,Allah ya fi mu sanin abinda yasa ya ƙaddari silar haɗuwarki da mahaifiyarsa,har sanadi yasa ya gane cewa ke ce yarinyar da ake nuna masa cikin baccinsa,wannan kaɗai ya isa yasa ki nutsu ki barwa Allah ikon sa,mu jira mu ga abinda Allah zai hukunta kinji ko?"

TAIMIYYAH ta dubi Iyah a sanyaye tana me gyaɗa kai, ba tare da tace komi ba. Iyah ta cigaba da yi wa TAIMIYYAH ƙarin bayani, akan labarin Maleek ɗin da Hajjah ta dinga bata, da irin yadda tun ganinsa da TAIMIYYAH ya kasa nutsuwa.Ita dai TAIMIYYAH jin Iyah kawai ta ke yi ,tana kallon komi kamar mafarki ko almara,tunaninta ya hasko mata yadda suka kwashe da shi ɗazu a waya,da yadda har ya fara kiranta da wife ɗinsa, kamar wanda akai wa albishir da cewa an basa ita,wani baƙon yanayi ya doka acikin zuciyarta,idanunta na hasko mata kyakykyawar miskilalliyar fuskar Maleek Ado ɗin,da yadda yake furta kalamansa cike da ƙasaita. Har Iyah ta gama bayananta ta tashi ta fice daga ɗakin,zuciyar TAIMIYYAH bata huta daga tunanin Maleek Ado ba..........✍🏻

#Ɗansabo ce# [12/14, 10:13 PM] +234 703 769 7050: Littafin TAIMIYYAH paid book ne,ga duk wanda ta tsincesa a kowani irin group ne,kiji tsoran Allah karki karanta sai kin biya 500 naira only.

Za ku iya min magana ta wannan number ɗin 08167768704, ko kuma ku turo kuɗin ku kai tsaye ta wannan account ɗin 0504192664 aisha ibrahim dansabo GTbank.*

*Sai ku tura shaidan biyanku ta wannan line ɗin 08167768704.*

Masu turo credit za ku turo katin MTN na 500 ta wannan line ɗin 08167768704.

_Ina ƴan kasuwa masu buƙatar a tallata muku hajar ku? Maza ku garzayo da kuɗi ƙalilan a tallata muku kayan siyarwanku sai dai kawai ku ji ana kiran waya don buƙatan sayan kayan ku,ku tuntuɓeni ta layina kamar haka 08167768704._

*59*

Washegari TAIMIYYAH ta dawo daga skull ne kawai,ta tadda danƙareriyar motar Hajiya Aysha fake a cikin compound ɗin gidansu. A hankali take takowa daga bakin gate ɗin zuwa ciki,sabida gajiyan da tayi a skull ɗin yau,har za ta wuce motar sai ta hangi Shehu daga ciki yana zaune,hakan yasa ta nufi wajen motar suka gaisa,sannan ta wuce zuwa sasan Iyah .

Da sallama ta isa bakin ƙofar shiga falon Iyah,Iyah daga ciki ta amsa sallamar da TAIMIYYAH tayi,hakan yasa TAIMIYYAH kutsa kanta ciki,idanunta suka sauka akan Hajiya Aysha da ke zaune cikin falon,an cika gabanta da kayan cima,don tun jiya da TAIMIYYAH ta sanar da Iyah cewa Hajiyan za ta zo,Iyah ta tashi yau da shirin tarbanta ita da Babah Ladi.

TAIMIYYAH ta isa cikin falon fuskarta na blushing, ta ƙarisa kusa da kujeran da Hajjah ke zaune,ta durƙusa ta kwashi gaisuwa.Hajjah ta amsa gaisuwar cike da kulawa idanunta akan TAIMIYYAH da tayi mata kyau sosai, cikin hijab ɗin jikinta kalar maroon,TAIMIYYAH ta dubi Iyah tana cewa, "IYah ina yini,na dawo".

Iyah ta amsa da cewa, "Lafiya lau, barka da dawowa Zaynab,ai tun ɗazu Hajiya ke tamabayar yaushe za ki dawo,don tace zuwar naki ne sai ki maza ki shiga ciki, ki kintsa ki fito ki ci abinci."

TAIMIYYAH sai ta dubi Iyah da sauri tana cewa, "Tuh Iyah bari in shiga daga ciki, sallah zan yi sai in fito."

Daga haka TAIMIYYAH ta miƙe tana dafa ƙafarta, ta fara takawa don isa zuwa ɗakinta,zuciyarta na cike da mamakin kalaman Iyah na cewa wai Hajiya wajenta ta zo. Har ta cire hijab ɗin jikinta ta nufi toilet, tunani abinda zai sa Hajiya ta yo takakki zuwa wajenta take yi,haka nan dai ta yi uzurinta ta ɗauro alwala ta fito ta tada sallah.

*20 Minutes Later.*

Hajiya Aysha ce ta fara da baiwa su Iyah labarin cikakken asalinta in da da soma cewa,

" Sunana Ayshatu Aliyu,haifaffiyar jihar Katsina,mahaifina Alhaji Aliyu shine Magajin Garin Katsina a wancan lokacin,mahaifiyar mu Hauwa ita kaɗai ce matar mahaifin mu har suka bar gidan duniya, bai sake wani aure ba kuma mu uku kaɗai suka haifa a duniya,Hadeeza itace Babba,sai ni Ayshatu sai Autar mu Hauwa'u. Na yi karatuna tun daga kan primary har ya zuwa jami'a,na kuma yi aure ina da shekaru sha tara a duniya, lokacin ina shekarar ƙarshe a jami'ar Ahmadu Bello da kenan Zaria,na karanci course ɗin Libarary Science ne. Mijina marigayi Alhaji Ibrahim Ado haifaffen garin Zaria ne, a wata Unguwa da ake kira Lowcos cikin lardin birnin Zazzau. Mun haɗu da shi ne a cikin jami'ar Ahmadu Bello, watarana ya kawo ziyara cikin makarantar, a matsayinsa na tsohon ɗalibin jami'ar. Ba mu jima da haɗuwa ba soyayyah me ƙarfi ya ƙullo tsakaninmu, har ta kai ga manya sun shiga ciki an sanya mana ranar aure." Hajjah ta cigaba da cewa, " A lokacin Ibrahim Ado yana aiki ne da hukumar Custum, inda har ya fara taka matsayi me girma a lokacin,don irin mazannan ne da ke tsayawa su samu ilimi me zurfi kafin su yi aure.Mun haɗu da watanni uku aka yi bikin mu ni da shi,aka ɗakkoni daga Katsina aka kawo ni Zaria,cikin sabon gidan da ya gina a cikin Unguwar Tukur-Tukur. Cikin shekaru goma da aurenmu na haifi adadin ƴaƴa biyar,amma duk suna mutuwa sai daga ƙarshe Ubangiji ya raya min Abdul-maleek, wanda na haife shi muna da shekaru sha biyu da aure. Hakan yasa ni da mahaifinsa muka ɗauki son duniya muka ɗaura akansa,sai dai hakan bai hana mu ba shi ingantacciyar tarbiya ba. Gata da kulawar da yake samu hatta daga wajen kakarsa wacce ta haifi Ubansa, bai sa ya taso a sangarce ba,sabida jajircewata wajen ganin ya samu tarbiya me kyau. Sam bana nuna masa so a zahiri yadda zai sangarce,yana da shekaru goma muka tattara muka koma Lagos da zama,sabida lokacin mahaifinsa ya kusa zama Asistant Controler na ƙasa. A can Lagos Maleek kamar yadda muke kiransa,ya kammala karatunsa na primary,daga nan ya wuce secondary skull, lokacin ne kuma Autar mu Hauwa ita ma aure ya kawo ta garin Lagos,na yi farin ciki da hakan a lokacin, domin dama ban san kowa a Lagos ba lokacin da muka koma. Cikin ƙanƙanin lokaci Maleek ya yi wani irin sabo da Antynsa Hausa,shaƙuwa ya shiga tsakaninsu sosai,duk idan ya dawo skull zai matsa sai driver ya kaisa gidanta.yana SS 2 ma ya iya driving sosai abinsa, uban kuma ya ɗaure masa gindi ya siya masa sabuwar mota,sai ya zamana da ya dawo skull zai ɗauki mota ya wuce gidan Anty Hauwa. Kominsa ita ce hatta abu idan yana so, sai ya fara sanar mata kafin ni in sani.Bayan ya kammala karatun Secondary ne mahaifinsa ya fita da shi England, a can ya haɗo deegree ɗinsa na farko da na biyu, duk a fannin da ya shafi siyasa wato 'Political Science'

Hajjah ta sake ɗan numfasawa sannan ta cigaba da cewa, "Ya dawo ƙasar Nigeria ya cidda an baiwa mahaifinsa, muƙamin Assistant Controler na ƙasa baki ɗaya,wanda wannan babban muƙami ya janyowa mahaifinsa tsana a wajen ƴan adawa sosai. Maleek ya dawo ƙasar bai fi da shekara ɗaya ba,ya fara aiki da Port ɓangaren Shiffing Board aka aje sa, sabida ƙafa da ubansa ke da shi a gwamnati, tunda aiki a manyan gurare irin wannan sai ƴaƴan masu faɗa aji a ƙasar,da waɗanda suke da babban matsayi a siyasar ƙasar, ko suke kusa gwamnati sosai. Ya fara aiki cikin sa a kuma yana taɓa Businees tun yana England,ya kan turo kayayyakin gina-gine ana sayar masa,lokacin da ya fara aiki bai daina ba, sai ma abin ya ƙara haɓaka ya fara ordern manyan kaya ana shigo masa dasu ta jiragen ruwa, shi kuma yana sararwa ƴan kasuwa masu harkan sayar da kayan gina-gine na zamani. Maleek miskiline sosai da sam ba yi da son hayaniya,ba yi da yawan magana sosai, sannan yana da isa da ƙasaita tamkar shine jinin sarautar, ba ni mahaifiyarsa da nake matsayin ƴar Magajin garin Katsina ba. Duk da miskilancinsa mutum ne me tsananin tausayin na ƙasa da shi,me yawan kyauta da alkhairy ga mabuƙata, kamar yadda ya ta so ya ga mahaifinsa na yi.Yana da son aba shi girma kuma baya ɗaukar raini tun yana da ƙarancin shekarunsa, tun da ya dawo ya fara aiki burina ya tafi akan son ya yi aure,amma shi sam ba ya ma so na ɗakko zancen,sai ya ce shi aure lokaci ne idan lokacinsa yayi zai yi. Shekaru biyu da bai wa mahaifinsa muƙamin Assistant Controler,Anty Hauwa ta haifi ƴarta ta farko wacce aka sanyawa suna Suhailah,daga kanta kuma ba ta kuma haihuwa ba sai dai ɓari da tai ta yi akai-akai. Suhailah na da shekaru biyu,ranar wata juma'ar da ba za mu taɓa mantawa ba, aka kashe mahaifin Maleek,wato Alhaji Ibrahim Ado a garin Lagos da daddare, akan hanyarsa ta dawowa gida,lokacin ya dawo daga duba wani abokin aikinsu da bashi da lafiya,a she makasan na biye da motarsa ba tare da shi ya sani ba,har ya kusa isowa gida suka buɗe masa wuta tare da harbesa har lahira."

Hajjah ta kai hannu ta share hawayen da ya zubo mata,na tuna da mummunan ranar da ba za ta taɓa mantawa da shi, a tarihin rayuwarta ba,ta cigaba da cewa, "Faɗin irin tashin hankali da giginta da muka shiga ma ɓata baki ne.Mun ɗauki tsayin lokaci kafin mu dangana,har mu cigaba da rayuw ba don zuciyoyinmu, sun daina jin zafi da raɗaɗin rashin mutum irin Alhaji Ibrahim Ado ba. Kuma wannan shine silar tsanata da garin Lagos,ta yadda ko sunan garin aka kira sai na ji zuciyata ta motsa da ɓacin rai me tsanani.Maleek shi ne ya gina min Sabon gida bayan fitana takaba,na tare a cikinsa a Gonar Ganye,a lokacin ne kuma aka kammala tattara dukiyar da Ibrahim ya bari aka raba mana gado,in da ni da tilon ɗana muka lashe kaf dukiya da kadarorin da marigayin ya tara,sabida lokacin iyayensa sun ɗan jima da rasuwa, a dalilin mummunar gobara da ya tashi a sabon gidan da Ibrahim ɗin ya gina musu, suka bar cikin Family House ɗinsu.Wannan rabon gado shi ya janyo mana wata irin tsana daga danginsa,da ƙanninsa maza biyu da suka ci burin ina ma mace Ibrahim ya haifa,sabida su ma su samu shiga cikin magada,amma sai Allah ya ƙaddara cewa namiji ya bari. Har a yau da na ke muku wannan maganar, dangin uban Maleek basa ƙaunarsa,suna matuƙar nuna adawa da irin arziƙin da ya gada,ga kuma na shi ɗaukakan da kullum cigaba ya ke. Arziƙi sai dai muce Alhamdulillah! Don ba mu san rashi ba indai na kuɗi ne.Shekaran Ibrahim uku da rasuwa aka sake rafka min wani rashin me asalin ɗaga hankali, Anty Hauwa ƙanwata da muka baro a Lagos itace ta rasu,sanadiyar haɗarin mota za su zo wani biki da za mu yi a Katsina a wancan lokacin, tana cikin mutum na farko da ta fara amsa kiran Ubangiji a cikin motar, ƴar ta Suhailah kaɗai ta rayu a cikin motar, lokacin ta fara tasawa tana da shekaru biyar a duniya.

Mutuwar Hauwa ya gigitamu ni da Maleek fiye da yadda zan misalta.Don shi Maleek sun yi waya da ita a lokacin da motarsu ta taso,take sanar da shi gasu cikin mota sun ma taso,don shi mijinta yace ta bari sai ana gobe bikin su biyo jirgi, amma sai ta nuna tafi son zuwa tun wednesday. Ta matsa masa sai ta taho,sai yayi mata irin gatsennan yace sai dai ta biyo mota,to da yake ajali na kira sai ta amince, shi kuma ganin ta nace ya biya mata kuɗin motar suka kamo hanya. Mu dai sai gawarta aka isa da shi can Katsina,ƴan uwa da dangi suka shiga cikin mummunan yanayi.Maleek lokacin da muka bar Zaria muka isa Katsina ko magana ba ya yi sai kuka.Don mutuwar ya gigita shi matuƙa barin ma da muka isa, ya tadda yadda Suhailah ke faman kuka kamar tasan uwar ta tafi kenan har abada. Bayan anyi kwana bakwai da rasuwar Hauwa, aka yi bikin da aka ɗaga sabida rasuwartata. An yi bikin da kwana biyu na haɗo kan mu har Suhailah muka ta ho Zaria, bayan na roƙi mahaifinta akan ya bani riƙonta,yace in ɗauka amma idan ya yi magana uwarsa bata amince ba, to zai biyoni har Zaria ya amshi abarsa. Cikin ikon Allah ma sai uwar tasa bata hana ba,hakan shine silar da riƙon Suhailah ya dawo hannuna tana da shekaru biyar a duniya. Hajjah ta cigaba da cewa, "Maleek shi ba mazauni bane, don yana can Lagos ɗinsa sai duk ƙarshen wata ko bayan sati uku yake zuwa Zaria, ya yi kwanaki biyar ko sati ɗaya ya juya inda ya fito, har kuma lokacin bai taɓa cemin yana da budurwa ba bare ayi maganar aure. Shekarunsa kuma kullum ƙaruwa suke yi don har ya shiga shakaru 26 a lokacin,ni kuma bani da burin da ya wuce ya yi auren ,amma shi ko a jikinsa,tun ina magana har na gaji na koma yi masa addu'a. Suhailah ta taho cikin gata da kulawa a hannuna, babu me cewa bani na kawo ta duniya ba,gaba ɗaya ta manta da uwarta sai dai idan ta ganta a hoto.Na sanya ta makaranta mafi tsada na boko da islamiya, babu abinda ta nema ta rasa,maraicin uwa ma bata san shi ba don yadda na ke ji da ita ko Hauwa na raye iyakar gatan da za ta bata kenan. Lokacin da ta girma ta zama budurwa ne na fara lura da zuciyarta ya fara karkata akan Maleek,sabida yadda take gaza nutsuwa idan ya zo gari.Na cigaba da sanya mata ido har na tabbatar da hasashena gaskiya ne, soyayyar ɗan uwanta me zafi ne ya kama zuciyarta,shi kuma wanda ake yi dominsa bai ma san tana yi ba,sabida sam ba yi shiga harkarta sabida ita akwai surutu da rawar kai, shi kuma miskili ne mara son hayaniya,tana shekaran farko a jami'a na tirketa akan ta gayamin gaskiya, idan son Maleek ɗin take yi da gaske kuma za ta iya aurensa,aiko Suhailah babu kunya ta sanar min shi take so,amma sai ta roƙeni akan kada in faɗi masa, sabida tsoransa take ji sosai,don ba ya sakar mata fuska ko kaɗan. Ni na san yadda nayi da rarrashi da ban baki har na ciyo kan Maleek ya amince zai aure ƴar uwarsa, kuma ƙanwarsa Suhailah,ba don yana jin sonta a zuciyarsa ba ,sai don kawai yayi min biyayya a matsayina na mahaifiyarsa, da ba ya iya saɓa abinda na ke so. Ba a ja lokaci ba manya suka shigo cikin maganar,mahaifin Suhailah ya fi kowa murna da wannan haɗin,yayin da su ku ma dangin Maleek suka sake ɗaukar zafi damu.Sabida sun so su yi masa tallan yaransu ƴan mata ya aura ,sabida kwaɗayin dukiya sai dai basu ga fuska a wajen Maleek ɗin ba, bare kuma ni da sam na daina shiga sabgar su sai abinda ba a rasa ba. Haka akai bikin Maleek da Suhailah suka tare a danƙareran gidan da Maleek ɗin ya gina a GRA. Duk wanda ya je ya ga irin daular da ke cikin gidan Suhailah sai yayi mata murna,dangin ubanta su kai ta santin gida da murnan cewa ƴar su ta samu gidan daula,masu hassada kuma su kai tayi mu dai bamu san ma suna yi ba. Suhailah ta cigaba da karatunta a ɗakin mijinta,amma ma fi zamanta yafi ga gida na,sabida Maleek baya zuwa sai duk bayan sati uku. Ita kuma Suhailah bata son zaman kaɗaici, hakan yasa yana tafiya za ta tattaro ta dawo min gidana,sai da nayi da gaske na samar mata ƴan aiki, da kuma ma'aikatan da Maleek ya zuba maza a gidan,da mai gadi,sannan ne Suhailah ta haƙura ta fara zama ita da ƴan aiki a gidanta. Anyi auren da shekara ɗaya mahaifin Suhailah ya rasu shi ma,ta zama cikakkiyar marainiyar da babu uwa ba uba. Shekararsu biyar kenan zasu shiga da aure,amma Allah bai bada haihuwa ba,wannan shine taƙaitaccen tarihina dana iyali na Hajiya Fatima."

Hajjah ta kai ƙarshen labarinta tana duban TAIMIYYAH da Iyah da ke saurararta,Iyah ta numfasa ta ce, "Allah sarki,Allah Ubangiji ya yi musu rahama tare da na mu iyayen da ƴan uwa musulmi baki ɗaya."

Hajjah ta amsa da cewa, "Ameen." Kafin ta sake amsa gaisuwar da TAIMIYYAH tayi mata, na rashin mijinta da ƴar uwarta,ta dubi TAIMIYYAH cikin ido wacce ta fara gano in da Hajiya Aysha ta dosa,don sunan Maleek da ya shigo cikin labarinta ya bata tabbacin cewa ba kowa bane ya zo wajenta sai ɗan Hajiya Ayshan.

Hajjah ta cigaba da duban TAIMIYYAH tana zayyane musu, yadda suka yi da Maleek akanta,tun daga maganar da tayi masa akan cewa ya zo ya ga TAIMIYYAR,har kawo yadda suka yi da shi a jiya kafin ya bar gari,ta ƙare maganar da cewa, "Zainab Maleek ɗa na ne, wanda shi kaɗai na mallaka a duniya, na so ace ina da wani ɗan wanda bai taɓa aure ba, sabida in saka shi ya zo ya nemi aurenki,amma ba ni da kowa sai Maleek. Shiyasa shi ɗin dai na ke da burin ya sake samun nagartacciyar mace me tarbiya a karo na biyu,ina fata za ki amshe sa a matsayin miji,ba tare da kin yi la'akari da aurensa ko dangantakar da ke tsakaninsa da matarsa ba,Maleek ya kamu da ƙaunarki ne tun lokacin da yake mafarki da me irin siffar idanunki,bai gane hakan bane sai a shekaranjiya da ku kai ido huɗu da shi,daga yana yin da ya dawo min a gigice, da irin kamalaman da yake yi akanki,na gano tarin ƙaunarki da ya taso daga can ƙasar zuciyarsa ya bayyana kansa. Zaynab ina fata za ki amince mu haɗa jini da ke,domin ɗorewar zumunci da samun iri me kyau daga gare ki.Ina miki albishir da cewa Maleek zai riƙe ki da amana,zai kuma zame miki mijin marainiya kamar yadda ya ke shi ma maraya.Sai dai banzo nan don na tirsasa zuciyarki ta amince da abinda baki da ra'ayi akai ba,idan har kin ji baki son Maleek, ba za a yi miki dole ba,Hajiya ina fata ke ma za ki amince ɗan ki ya zama surukinki idan Allah ya yi nufin kasancewar hakan?"

Hajjah ta ƙare maganar tana duban Iyah,wacce tayi sakato tana duban Hajjahn,ta rasa ma me zata ce sai da ƙyar tayi ƙarfin halin faɗin, "Hajiya na rasa da wani baki zan bayyana irin ƙauna da alkhairin da kike nufin wannan yarinya da shi,tabbas idan har Zainab ta amince da ɗan mu zan yi farin ciki mara misaltuwa,babu abinda zan ce dangane da wannan lamari, duba da irin mafarkin da yaron ya fara yi tun farko,don Allah kaɗai ya san me ya ke nufi da hakan,sannan haɗuwar mu da ke da bayyanar TAIMIYYAH, a matsayin wacce yaron ki ke mafarki da wani ɓangare na siffarta, shima babban lamari ne da sai dai mu bi da addu'a,kar ki damu Hajiya idan har yaran suka fahimci juna, ina baki tabbacin zan shige gaba wajen ganin an ƙulla alkhairy ,in dai har zai riƙe min jika da amana ya kare mata martabarta,su kuma zauna lafiya da matarsa,to ni bani da haufi domin me sonka da gaskiya ne zai so ɗansa ya haɗa zuriya da naka,babu abinda zance miki sai godia akan ƙauna da tausayin da kike nunawa Zaynab."

Iyah tayi maganar har muryarta na ɗan rawa,TAIMIYYAH kuwa ƙasa ta yi da kanta, ƙirjinta na wani dokawa da yanayin da ba za ta iya fassarawa ba.Hajjah ta dubi TAIMIYYAH cike da ƙauna ta ke cewa, "Ƴa ta tashi ki je daga ciki na ga alamun kin shiga ruɗani,za mu gama magana da Iyah amma ina roƙarwa Maleek alfarma, a riƙa ɗaga wayarsa idan ya kira,sabida shi mutum ne da bai iya saka abu ransa da sauƙi ba,ina fata tsoro ya kau tunda kinji waye shi, daga ina kuma ya ke,so please ki ɗauki wayarsa ki sauraresa, ta hakane za ki gane idan za ki iya amincewa da shi,Allah ya yi miki albarka ya kuma haɗa zuciyoyinku ke da shi Zainab."

Hajjah ta ƙare maganar tana bin bayan TAIMIYYAH da kallo,wacce ta ke takawa a hankali tamkar wacce ƙwai ya fashemawa a ciki,sabida yadda zuciyarta ke cikin wani irin ruɗani da kullewar kai..........✍🏻

#Ɗansabo ce# [12/14, 10:13 PM] +234 703 769 7050: Littafin TAIMIYYAH paid book ne,ga duk wanda ta tsincesa a kowani irin group ne,kiji tsoran Allah karki karanta sai kin biya 500 naira only.

Za ku iya min magana ta wannan number ɗin 08167768704, ko kuma ku turo kuɗin ku kai tsaye ta wannan account ɗin 0504192664 aisha ibrahim dansabo GTbank.*

*Sai ku tura shaidan biyanku ta wannan line ɗin 08167768704.*

Masu turo credit za ku turo katin MTN na 500 ta wannan line ɗin 08167768704.

_Ina ƴan kasuwa masu buƙatar a tallata muku hajar ku? Maza ku garzayo da kuɗi ƙalilan a tallata muku kayan siyarwanku sai dai kawai ku ji ana kiran waya don buƙatan sayan kayan ku,ku tuntuɓeni ta layina kamar haka 08167768704._

*61*

Kwanakin Hajjah biyar da xuwa gidansu TAIMIYYAH,ya kama ranar Friday. Misalin ƙarfe takwas na dare, Baba Sani ya shigo sasan Iyah don gaisheta, kamar yadda ya saba duk sanda ya dawo weekend.

Bayan sun gama gaisawa da Iyah,ita ma TAIMIYYAH ta fito suka gaisa sai ta koma ɗakinta,kamar yadda ta saba don basu waje shi da Iyah su zanta,Iyah ta ɗaga manyan idanunta ta sauke akan Baba Sani, kafin ta fara da cewa, "Sani za ka iya tuna labarin Hajiyar nan me kirki dana baka,wacce suka kaɗe Zainab wata ɗaya da ya wuce?"

Baba Sani ya gyaɗa kai yana cewa Iyah, "Eh Iyah na gane ta, wacce ki ka ce har ta zo nan gidan ranar walima,har ta baiwa TAIMIYYAH ɗankunnin gwal ko?"

Iyah ta yi saurin faɗin, "Eh tabbas kuwa ita nake nufi Sani,to ita ce ta sake dawowa yau kwanaki biyar kenan,sai dai wannan karon ta zo da wani lamari me girma ne......"

A hankali Iyah ta zayyanewa Baba Sani yadda suka yi da Hajjah,da kuma wayar da Maleek ɗin suke yi da TAIMIYYAH,don tun daga ran da Hajjah ta zo ta tafi ,ya maida kiran TAIMIYYAH a waya tamkar ibada,tun tana wa Iyah ƙorafin ya faye naci da miskilanci,har Iyah ta gaji da jin ƙorafin ma ita,Iyah ta kai ƙarshe tana cewa maganar da cewa, "To ka ji yadda muka rabu da ita, don haka ina so daga yau zuwa jibi ka bincika can Family House ɗin nasu, don a ji ya ya mu'amalarsa da danginsa ya ke? Sannan kuma ka binciki abokanan Sameer na kusa,waɗanda da ke can Lagos don a binciki halayyar Maleek ɗin da abokanan aikinsa,tunda shi ma duk wajen da marigayi yayi aiki yake,sai dai shi Hajiya tace a ɓangaren shiffin board yake,wanda a yanzu haka ma shi ke riƙe da kujeran chairman na shiffing board gaba ɗaya."

Baba Sani ya jinjina kai cike da mamakin wannan lamari ya dubi Iyah ya ce, "Ai Iyah wannan abu ya kwana gidan sauƙi ,in dai ɗan magariya former Assitant Controler ne da na sani, Yaron Alhaji Ado Ibrahim da family House ɗinsu ke lowcost, ai maƙotan abokina Alhaji Buhary ne,zai san komi akan duk wani labari da ya shafesu,zan kira shi mu yi magana anjima nan,sannan kina nufin shi Chairman ɗin da kansa ma ya tako har nan ya ga Zainab,lallai wannan lamari me girma ne da Allah kaɗai yasan abinda ya shirya.Sai mu cigaba da addu'a Allah tabbatar mana alkhairy,amma fa ba ƙananun mutane bane waɗannan."

Iyah ta jinjina kai tana cewa, "Hakane Sani addu'ar mu ke kan yi, sai ka taya mu kaima,amma ina so wannan maganar ya zama tsakanina da kai ne, ban amince Zuwairah ta ji komi ba har sai lamarin ya tabbata, sabida bana son surutu da sanya ido."

Baba Sani da tun fil-azal ya san Iyah bata son Umma sabida halayyarta,sai ya jinjina kai yana cewa, "In sha Allah Iyah babu wanda zai ji daga gareni,Allah ya shige mana gaba ya tabbatar mana da alkhairy,amma ita Zainab ta amince za ta iya aurensa?"

Iyah ta murmusa ta bai wa Baba Sani amsa da cewa, "To tunda take sauraransa a waya,su shafe mintuna masu yawa ka ga kenan akwai alamun zai samu kanta,tana dai yawan complain cewa ya cika miskilanci, ga shi yana da mata ita tana jin tsoro kaza da kaza,amma tunda a hakan dai basu fasa waya ba, kuma bana ganinta cikin wani damuwa, ka ga akwai alamun ta fara ba shi zuciyarta kenan."

Baba Sani ya jinjina kai ya ce, "Hakane, to Allah yayi mana jagora ya tabbatar da alkhairy."

Iyah ta amsa da cewa, "Ameen." Daga haka Baba Sanin ya yi mata sallama,ya baro sasan zuciyarsa na cigaba da al'ajabin wannan labari,sosai ya dinga addu'ar Allah ya ƙulla alkhairy,don zai fi kowa murna ace Zainab ɗin ta samu gidan hutu da za a kula da ita."

TAIMIYYAH da ke cikin ɗakinta tana operating system ɗinta,ta jiyo muryar Iyah na ƙwallo mata kira,ta amsa tana tsaida aikin da take yi, ta miƙe ta fice daga ɗakin zuwa falon Iyah.

Iyah da idanunta ke kan TAIMIYYAH har ta ƙariso wajen da ta ke zaune ta furta, "Zainabu zauna mu yi magana."

Readers Also Read