Kenza eBookz

Taimiyah book complete document by ayshat dansabo lemu txt by hausanovels com - Chapter 37

Taimiyah book complete document by ayshat dansabo lemu txt by hausanovels com - Chapter 37

Taimiyah book complete document by ayshat dansabo lemu txt by hausanovels com Chapter 37: Taimiyah book complete document by ayshat dansabo lemu txt by…

4,363 words

TAIMIYYAH ta miƙe tare da dafa guiwar ƙafarta ta fara takawa don isa wajen table ɗin,in da aka jere komi a kai ta ɗakko goran table water da glass cup, ta juyo don kai wa Maleek Ado wanda idanunsa ke kanta, tunda ta tashi ya ke faman ƙarewa yanayin tafiyarta kallo,wani irin abu ya ke ji na danne zuciyarsa, yana sake haifar da zazzafar ƙaunarta a duk ilahirin jinin jikinsa.

TAIMIYYAH ta aje masa goran ruwan da cup ɗin,daga saman hannun kujeran da ya ke zaune,tana faman mita cikin zuciyarta na yadda ya ke bin ta da mayen kallo, kamar zai cinye ta. Ta zumɓure baki cike da shagwaɓa ta ce, "Ga ruwan ko na zuba maka ne?"

Ta ƙare maganar tana ɗaga manyan idanunta ta dubi fuskarsa,ganin ita ya ke kallo yasa ta ɗauke kai tana sake narke fuska, Maleek murya can ƙasa ya furta, "Da ni ki ke so na zuba da kaina wife?"

TAIMIYYAH ta kuma dubansa jin yadda ya yi maganar a dake,sai dai yadda fuskarsa ta ke a miskile, ba za ka taɓa cewa kaf maganganun da yayi daga bakinsa suka fito ba,ta ɗan taɓe baki kaɗan lokacin da ta ke kai kyakykyawar hunnunta, mai ɗauke da zara-zaran yatsu ta ɗauki goran ruwan ta buɗe, tare da zuba masa cikin cup ta miƙa masa. Maleek Ado ya zubawa kyawawan yatsunta ido, yana sake jin tsoran mafarkin da ya yi ta yi da irin waɗannan yatsun, a lokacin da takan miƙo masa su a cikin bacci tana neman ɗauki daga garesa,sai dai a wancan lokacin da ya miƙa hannunsa don kamata,ya ke farkawa daga baccinsa a firgice,yau ga hannun a gabansa tana miƙo masa cup ɗin ruwa a zahiri ba a cikin mafarki ba. Ya sauke zazzafar numfashi yana miƙa hannunsa, ya amshi cup ɗin ruwan ya kai bakinsa, ita kuma TAIMIYYAH ta yi saurin komawa mazauninta, tana sake yin ƙasa da kanta don haka kawai ƙamshinsa da ta sake shaƙowa da kyau, lokacin da suke daf da juna ya dinga kashe jikinta, yana haifar da wani yanayi a cikin zuciyarta.

Maleek ya shanye ruwan tas! Ya dire cup ɗin daga saman kujerar ya dubi TAIMIYYAH,ganin yadda ta sauke kanta ƙasa ya sa shi furta, "Zaynab yaushe za ku kammala Computer traning ɗin da kike zuwa?"

TAIMIYYAH ta dube sa ta ce, "Saura one week mu amsa certificate na kammalawa."

"Very good! Zan yi magana da Hajjah, bari na xo na wuce don idan ina cigaba da ganin waɗannan idanun,ina kuma jin wannan muryar a kusa da ni, to za ki cigaba da illata zuciyata ne kawai,da ƙaunarki da ke neman ƙure duk wata jarumtar Maleek."

Maleek ya yi maganar idanunsa akan TAIMIYYAH, wacce ta waro masa nata idanun cike da mamakin kalamansa,ganin sun haɗa ido yasa ta saurin maida kanta ƙasa kunya na lulluɓeta. Maleek ya saki murmushi kaɗan kafin ya ce , "Zaynabb kin cika kunya da yawa ,anya ko zan samu irin kulawar da nake buƙata daga mace a gunki?"

TAIMIYYAH ta yi saurin dubansa kamalaman da bata shirya furtasu ba,suka suɓuce akan harshenta suka yo waje inda ta ce, "Ai ita na san tana baka."

Maleek da idanunsa ke kan bakin TAIMIYYAH, bai san lokacin da murmushi ya haska a samar fuskarsa ba, yayi saurin cewa, "Ita wa ce Zaynabb?"

TAIMIYYAH da wani kishi da haushin kanta ya gama cika ta,sabida yadda tayi suɓul kalam ta furta kalaman a fili har ya ji,sai sake narke face ta ce, "Ita matarka mana."

Maleek sai ya miskile face cike da don tsokanarta ya furta, "Oh! Tana bani mana sosai ma,kin san ta iya luv shiyasa na ke so ke ma ki rage wannan kunyar,sabida ku dinga gasa da juna wajen nuna min luv ɗin, ko ba haka ba wife?"

TAIMIYYAH tayi kicin-kicin da face tare zumɓuro ɗan ƙaramin bakinta,cike da shagwaɓa ta ke duban Maleek ta ce, "Ni ban iya ba tunda ita ta iya shikenan sai ta dinga nuna maka luv ɗin."

"No Babe! It's not okey for me, cox ke ma soon za ki zama mallakina, kuma dole ina buƙatar ki dinga nuna min luv a zahiri."

Maleek ya yi maganar yana sake miskile face, amma can ƙasan zuciyarsa dariyane fal cikinsa,sabida yadda TAIMIYYAH ke yi da fuska cike da nuna kishi a zahiri,hakan ba ƙaramin sake kimsa soyayyarta ya yi a zuciyarsa ba.

TAIMIYYAH bata kuma magana ba sai tashi da ta yi,ta isa wajen da aka shirya coolers ɗin abincin da ta ɓata lokaci ta yi masa. Ta fara da buɗe cooler ɗin farko tana tambayar Maleek me za ta zuba masa? Ya ɗago manyan idanunsa ya kai kanta yana cewa, "No wife am full ,Hajjah ta cika min ciki da abincinta."

TAIMIYYAH ta tsuke fuska cike da rashin jin daɗi ta furta, "Please! A zuba maka dai ko kaɗan ne, ka ga na ɓata lokaci me yawa wajen yin girkin,in zuba please?"

Yadda ta marairaice masa cike da shagwaɓa, yasa Maleek kasa sake gwaleta a karo na biyu,sai ya ɗaga mata kai yana furta, "Amma ɗan kaɗan Zaynabb."

TAIMIYYAH ta zuba masa shinkafar ɗan kaɗan, ta zuba haɗin Salad ɗin daga gefe guda,sanna ta taso ta kawo masa tana me aje plate ɗin daga saman kujera.

Maleek kaɗan ya ci abincin amma ya ji daɗinsa ƙwarai,tare da jin mamakin cewa Zaynab ɗin ce da kanta tayi wannan haɗaɗɗan abincin.

Lokacin da ya tashi tafiya TAIMIYYAH ta shiga da shi wajen Ummie suka gaisa,ya aje mata kuɗaɗe masu yawa,Ummie ta yi masa godia bayan ta yi iya yinta ya ɗauki kuɗinsa ya ƙi, daga wajen Ummie TAIMIYYAH ta yi masa jagora zuwa wajen Hajjaju Iyah. Maleek ya zube ya kwashi gaisuwa tare ajewa Iyah kuɗaɗe ita ma masu yawa, Iyah ta yi maza ta ce TAIMIYYAH ta kwashe kuɗin ta mayar masa. Maleek ya nunawa Iyah cewa ba zai ji daɗi ba, idan har bata amshi kuɗin ba,hakan yasa Iyah haƙura ta bar kuɗin suka fito daga falon shi da TAIMIYYAH, wacce za ta yi masa rakiya zuwa bakin ƙofar fita daga Part ɗin nasu.

Maleek ya dakata daga tafiyar da ya ke yi, lokacin da ya fahimci cewa iya bakin ƙofar fitowa kawai TAIMIYYAH za ta yi masa rakiyar,ya buɗe baki cike da ƙasaita ya ke furta, "Zaynabb iya nan kawai za ki yi rakiyar?"

Ta gyaɗa masa kai tana magana cike da shagwaɓa ta ke cewa, "Sorry na gaji ne shiyasa, ka gaida Hajjah da kyau Allah ya tsare hanya."

Maleek ya ji daɗin kalamanta ƙwarai, shiyasa ya sakar mata ƙaramin smile ya ce, "Ameen wife thank u, Hajjah za ta ji sosai but ba ki ce in gaida Anty ɗinki ba, tare muka taho fa tana wajen Hajjah."

TAIMIYYAH sai ta kwaɓe face tace , "Ka gaishe ta tuh."

Maleek ya sake sakin murmushi yana yin gaba,TAIMIYYAH ta bi bayansa da kallo tana jin wani irin zazzafan feeling na kwaranya a zuciyarta,ta juya cikin slowly zuwa cikin falon Iyah.

Zamanta bada jimawa ba Tukur ya fara shigowa da manyan ledoji masu ɗauke da tambarin SAHAD STORE, daga ita har Iyah suka zubawa manyan ledojin har huɗu da Tukur ya aje a falon ido. Tukur ya juya ya fice bayan sun gaisa da Iyah, ya sanar da ita cewa Maleek da ya fita yanzu ne yasa shi shigowa da kayan.

Iyah ta jinjina kai kawai tana rasa bakin magana,don ita sam bata son irin waɗannan ɗawainiyar. TAIMIYYAH sai ta tashi tsam! Ta nufi ɗakinta ba tare da ta bi ta kan sababin da Iyah ta fara yi akan yawan kayan ba.....✍🏻

#Ɗansabo ce# [12/14, 10:13 PM] +234 703 769 7050: Littafin TAIMIYYAH paid book ne,ga duk wanda ta tsincesa a kowani irin group ne,kiji tsoran Allah karki karanta sai kin biya 500 naira only.

Za ku iya min magana ta wannan number ɗin 08167768704, ko kuma ku turo kuɗin ku kai tsaye ta wannan account ɗin 0504192664 aisha ibrahim dansabo GTbank.*

*Sai ku tura shaidan biyanku ta wannan line ɗin 08167768704.*

Masu turo credit za ku turo katin MTN na 500 ta wannan line ɗin 08167768704.

_Ina ƴan kasuwa masu buƙatar a tallata muku hajar ku? Maza ku garzayo da kuɗi ƙalilan a tallata muku kayan siyarwanku sai dai kawai ku ji ana kiran waya don buƙatan sayan kayan ku,ku tuntuɓeni ta layina kamar haka 08167768704._

*63*

*Gonar Ganye.* *09:40pm*

Baka jin sautin komi cikin falon Hajjah sai na kukan da Suhailah ke yi, me taɓa zuciyar duk wani me saurarenta. Daga Maleek har Hajjah kallonta suke yi cike da tausayi me tarin yawa, Hajjah ta tashi ta isa wajen da Suhailah ke zaune, ta haɗe kanta da guiwa tana razgar kuka. Ta zauna kusa da ita tana me ɗago fuskarta ta fara faɗin, "Suhailah haƙury za ki yi, na san akwai ciwo amma bamu isa mu ja da hukuncin Ubangijiba,Maleek zai sake aure ne ba don ya daina sonki ko ya daina ƙaunarki ba,haka ba don ba ki haihu zai sake aure ba, zai sake aure ne sabida haka Allah ya rubuta masa cikin littafin ƙaddaransa, za ki fahimci hakan ne daga labarin da muka baki, tun daga kan mafarkin da yake yi da Yarinyar, har kawo haɗuwata da ita da sanadin da ya zama silar kulluwar zumunci a tsakaninmu da su.Suhailah bana so ki ga cewa ba a yi miki adalci ba, shiyasa na zaɓi ku taho nan don a buɗe miki komi, ba wai ki ji magana daga sama ba,ina baki haƙury tare da tausar zuciyarki,akan ki ɗauki ƙarin auren da Maleek zai yi a matsayin rubutacciyar ƙaddaranku ke da shi,wanda mu da ku duka bamu isa ja da hukuncin Ubangiji akan hakan ba,don haka ki nutsu ki rungumi ƙaddara tare da baiwa mijinki goyan baya, ki yi addu'a Allah ya haɗa kan ku ya ba ku dauwamammiyar zaman lafiya."

Hajjah ta ƙare maganar tana me rungumo Suhailah zuwa jikinta, ta cigaba da rarrashinta da kalamai na kwantar da hankali.

Suhailah ta ɗago kanta daga jikin Hajjah, tana kallon direction ɗin da A.Maleek ke zaune, sai kawai ta sake barkewa da kuka,babu abinda ke amsa kuwwa cikin kanta da kunnuwarta ,sai maganar ƙarin auren da zai yi nan da lokaci kaɗan, kamar yadda ya sanar mata da bakinsa.

Maleek ya ɗago manyan idanunsa ya sauke akan fuskar Suhailah, yana jin tausayinta me girma na kassara zuciyarsa. Memakon ya yi magana sai kawai ya miƙe yana barin musu falon ,ya fice baki ɗaya don ba zai iya zama yana cigaba da sauraren sautin kukan Suhailah ba.

Daga Hajjah har Suhailah suka bi bayansa da kallo, Suhailah ta sake fashewa da kuka tana ji tamkar zuciyarta za ta fashe,wani mahaukacin kishin Maleek ke sake danne zuciyarta. Duk iya yadda Hajjah ta kai da son ta ga cewa Suhailah ta fahimce ta abin ya ci tura,sai ma tashi da Suhailar ta yi ta nufi ɗakinta na tun asali a gidan, ta kulle kanta a ciki don bata son sake jin kowani irin rarrashi daga wajen Hajjah, ta kuma gama ƙudurcewa a zuciyarta ba za ta bi Maleek zuwa GRA gidansu su kwana tare ba,don haushinsa take ji daga shi har Hajjan.

Gaba ɗaya daren idan Suhailah ta ce ta rintsa to ta yi ƙarya,tsanar Hajjah da Maleek take ji me zafi a ranta, tana ganin cewa sun daina ƙaunarta ne kawai,sabida Allah ya jarabceta da rashin haihuwa.

Ko da gari ya waye duk iya bugun ƙofar da Hajjah ta dinga yi, akan Suhailah ta buɗe ta saurareta abin ya ci tura,sai ma cewa ta yi da Hajjah ta tafi abin ta don ba za ta taɓa buɗe ƙofar ba,gara su barta ta mutu su ɗauki gawarta tunda sun daina ƙaunarta, don an ga ba idon iyayenta a raye.

Waɗannan kalamai na Suhailah su suka dugunzuma zuciyar Hajjah,ta juya cikin tsananin fushi ta nufi ɗakinta don kiran Maleek,ta sanar da shi halin da take ciki da Suhailah. Lokacin da Maleek ya iso gidan Hajjah da ƙyar Suhailah ta yadda ta buɗe ƙofar ɗakin, kallo ɗaya ya yi wa idanunta ya san ko kaɗan bata samu bacci ba. Sai tausayinta ya kama zuciyarsa,ya isa gareta yana ƙoƙarin sanyata a jikinsa ya rungumeta, amma sai Suhailah ta yi gaggawar hankaɗe hannunwansa daga taɓa jikinta,ta fara gaya masa zafafan kalaman da suka hasala zuciyar Maleek. Ya ɗaga hannu zai ɗauke ta da mari sakamakon zafafan kalaman da ta faɗi na ƙarshe tana cewa, "Kar ka kuskura ka ce za ka sake taɓani,ka je can wajen gurguwar na sallama mata kai Yaya Maleek, tunda ka tsaneni ka ci amanata, ka zaɓi auren nakasasshiya sabida ban haihu ba,meyasa idan auren za ka ƙara ba za a sanyaka ka auro me lafiya ba sai gurguwa, nakasasshiya sabida ku tozarta ni...."

Hannun da ya ɗaga zai zabga mata mari ne ,ya sanya Suhailah gintse kalamanta,Maleek da idanunsa suka fara sauya launi ko me ya tuna? Sai ya sauke hannunsa ba tare da ya kai mata marin ba kamar yadda ya yi niyya. Ya juya cikin tsananin fishi ya fito daga ɗakin ya nufi ɗakin Hajjah. A zaune ya samu Hajjah ranta a matuƙar ɓace ita ma, don kalaman Suhailah sam basu yi mata daɗi ba ko kaɗan. Ya isa kusa da ita ya zauna yana buɗe baki ya ce, "Hajjah haƙury za ki yi da Suhailah, ni da ke duka mun riga mun san sai hakan ya faru,idan har ta ji maganar aurennan,don haka ki yi biris da ita da duk wani haukar kishin da za ta nuna,ni zan wuce Lagos zuwa anjima,amma ita zan barta anan ta samu kaman 2 weeks kafin ta koma Abuja,watakila zuwa lokacin ta saduda ta haƙurewa zuciyarta, don duk wani haukanta ba su isa su hana komi ba,sannan ki gargaɗeta akan aibanta halittar Zaynab a gaban idanuna,idan har ta cigaba da hakan zan mugun saɓa mata,don ko a yanzu ma na kai zuciyata nesa ne da sai na kwaɗa mata mari."

Maleek ya yi maganar cikin fishi me tsanani, don a yanzu idan akwai abinda ya tsani ji bai wuce a kira TAIMIYYAH da suna gurguwaba,hakan na masa ciwo ko da a ce daga bakin ita TAIMIYYAR kalmar ya fita. Hajjah ta jinjina kanta kafin ta dubi cikin idanunsa tana faɗin, "Allah ya tsare hanya Maleek, tabbas barin Suhailah a nan ɗin shi zai fi,don tana buƙatar a bata space ta huce,zan kuma san ta inda zan ɓullo mata,ai kishi ba hauka bane."

Daga haka Maleek ya yi sallama da Hajjah ya fito daga gidan, ba tare da ya sake bi ta kan Suhailah ba. Yusuf Driver shi ne zai kai shi Kaduna, ya bi flight ɗin 2 zuwa Lagos.Suna kan hanya ne ya kira TAIMIYYAH a waya su kai sallama da juna,akan cewa nan da sati biyu masu zuwa zai sake dawowa,wanda ya ke fata idan ya dawo ɗin kafin ya bar gari an kai kuɗi da kayan sanya ranar aurensu,don ba ya ji zai iya ƙara watanni biyu ba tare da ya mallaki TAIMIYYAH a matsayin halaliyarsa ba.

__________

*Bayan Sati Uku*

*Saturday, 05:56pm.*

Umma ta dubi Baba Sani hankalinta a matuƙar tashe ta ce, "Yanzu Baban Basmah kana nufin duk waɗannan uban kwalayen, kamar za a buɗe shago kayan sanya ranar auran TAIMIYYAH ne? Wai shin ma da yaushe ta samu mijin har magana yayi ƙarfi,ba tare da ko sau ɗaya bakinka ya furta hakan ba?"

Umma ta kai ƙarshen maganar da jefa masa tambaya, tana jin yadda zuciyarta ke sake rufewa da wani irin duhun ɓacin rai,idanunta na cigaba da kallon uban kwalaye zuwa katan-katan nasu ruwa da juice, da suka cinye rabin bango guda na falon daga sama har ƙasa. Bata taɓama ganin kayan sanya ranar auren da aka haɗo kayayyaki irin wannan ba, ta sake ɗaga idanunta ta dubi Baba Sani wanda ya tamke fuska tamau, ba shi kuma da niyyar bata amsar tambayarta. hakan yasa ta sake gyara zama tana fuskantarsa sosai ta ce, "Kana jina fa Baban Sadeeq,na ce da yaushe ta samu mijin har aka sanya rana da gaggawa haka,mu da muke gida ɗaya bamu taɓa ganin ko ƙyallinsa ba?sai kawai rana tsaka mu ga waɗannan uban kaya kamar za a buɗe shagon provition,ina jiye muku tsoron kar ku ɗauki nakasasshiyar marainiyar Allah ku baiwa ɗan yankan kai, bayan biki ya miƙawa ƙungiya jininta su shanye,don dai daga ganin waɗannan kaya an san dukiya ne ya ruɗeku, har kuka amsa da gaggawa za ku sallamata,wai shin ma a ina ta samo mijin ne?"

Umma ta sake jefawa Baba Sani tambayar tana kafeshi da idanunta,sam bata damu da irin mugun kallon da yake bin ta da shi ba. Ya buɗe baki ya yi magana cikin ɓacin rai yana cewa, "A gabana Zuwairah, a gabana zaki buɗe baki kina furta irin waɗannan mugayen kalaman akan jinin Sameer? To kar ki kuskura ki ƙure haƙurina don zan mugun baki mamaki, da ki ke maganar ba ku san da samun mijinba, dole ne idan Zaynab ta samu miji sai an yi shela duniya ta sani,ko kuma dole sai kin sani kafin ayi komi sabida ke ce waliyiyarta ko? To bari ki ji ba zan ɗauki duk wani shirme ba,don ina sane da irin ƙiyayyar da ki ke nuna mata tun asali,kuma maganar kada mu baiwa ɗan shan jini,idan mun ba shi ki je ki ƙwatota daga hannunsa idan ya tabbata ɗan shan jinin ne,kar ki kuskura ki sake min magana makamancin wannan Zuwairah kinji na faɗa miki."

Baba Sani ya tashi fuu..! Ya bar mata falon ya shige ɗakin baccinsa, ransa a matuƙar ɓace da kalaman da Umman ta gaggaya masa. Umma ta bi bayansa da kallo tana jin wani tashin hankali na sake rufto mata,ga takaicin rashin samun cikakken amsar tambayarta, na son sanin cikakken waye wanda za su ɗauki auren gurguwar da ta tsana su ba shi? Tana shirin tashi ta bi Baba Sani Sadeeq ya yi sallama yana shigowa cikin falon, sai ta yi saurin dubansa lokacin da yake takowa zuwa cikin falon Baba Sanin, idanunsa akan uban kayan sanya ranar auren TAIMIYYAH da su ke tsibe. Ya samu waje ya zauna yana gaida Umma, wacce gaba ɗaya take jin tamkar ta ari hauka, sabida baƙin cikin da ke damun zuciyarta. Ta amsa gaisuwar Sadeeq a lalace kafin ta dubi cikin idanunsa tana jefa masa tambayar da ke cin ranta, "Kai Sadeeq wai wa ye mutumin da waccar gurguwar za ta aura? Da har ake ɓoye mana maganar tun farko,sai kawai muka ji labarin an sanya ranar aurensu, kuma don wulaƙanci wai duk gaba ɗaya za a yi bikin da na su Basmah,sabida a tozartamu a nuna ta samo me arziƙin da ya kere mazajen da ƴaƴana za su aura,don daga ganin wannan uban kayan an san cewa ba daga ƙaramin gida suka fito ba,sanar dani ɗan gidan uban waye za ta aura a garinnan?"

Sadeeq ya yi saurin duban Umma yana mamakin yadda ta fusata, tana ɗaga murya cike da zallar tashin hankalin da ke haskawa akan fuskarta,ya ɗan cije bakinsa yana jin tsanar halayyar mahaifiyar tasa na ƙona ransa, ya buɗe baki a hankali ya ce, "Umma ni ma ban san shi ba,amma Baba ya ce ɗan gidan tsohon Asistant Controller ne da ya rasu, Marigayi Alhaji Ibrahim Ado,sunan guy ɗin Alhaji Abdulmaleek Ado, ana kiran da Maleek Ado kaɗai,gaskiya a yadda Baba ke bani labari ba ƙananun mutane ba ne, don sun tara arziƙi me ɗinbin yawa,gashi guy ɗin a yanzu haka shike riƙe da muƙamin Chairman na Shiffing Board na baki ɗaya. Kin ga ko baƙaramin mutum ba ne ,duk da cewa yaro ne ba wai Babba ba don duka bai ma kai 40yrs ba thirty something ya ke."

Sadeeq ya gama ratafawa Umma jawabin cike da basarwa, idanunsa akan uban kayan da ke tsibe cikin falon Baban nasu. Umma da tuni zufa ya gama jiƙe wani ɓangare na jikinta, sai ta dubi Sadeeq cike da ɓacin rai ta ce, "Eh lallai dole a ɓoye mana ayi komi a munafurce,sabida ni ce da ƴaƴana ba a so da alkhairy sai musaka gurguwa. Duk kuma ba kowa ke da alhakin hakan ba sai waccar tsohuwar makiran kakar ta ku Iyah. Sabida na ji ana ƙishin-ƙishin cewa wai ai uwar Mutumin ce, suka kaɗe TAIMIYYAH ɗin watannin baya,ka ga kenan Iyah ita ce ta kitsawa uwar tasa wannan munufurcin, akan su haɗa aure tsakanin gurguwarta da ɗan matar,to Allah yasa ba ɗan ƙungiya bane ya je ya sai da ita bayan auren."

Sadeeq ya yi hanzarin duban Umma yana faɗin, "Subhanallah! Umma wani irin kalami ki ke yi haka marar daɗin ji? Don Allah ki sanyawa zuciyarki salama, ki yi wa Zaynab fatan alkhairy ne ba sharri ba,ni dai ina ji a jikina cewa alkhairy ke bibiye da rayuwarta In sha Allah. Kuma ina farin ciki da wannan auren da za ta yi , Allah ya bashi ikon riƙe ta da amana ita da abokiyar zamanta."

"Au yana ma da aure shi ne za a ɗauki gurguwa a cinna masa? Eh! lallai wannan ya nuna cewa tsabagen kwaɗayi da son a nuna mana iyakarmu ace ta auri me arziƙi ne,shiyasa makirar ta ƙulla abin."

Umma ta sake kwaɓowa Sadeeq waɗannan banzayan kalaman,hakan yasa Sadeeq tashi ya baro falon Baba Sanin, ba tare da ya tsaya tambayar Umman akan cewa ko Baba Sanin na nan ba?

____________

Daga can Part ɗin Ummie kuwa TAIMIYYAH ce zaune ita da Ummie, suna magana akan Doughnut da TAIMIYYAH za ta yi a raba sadaka, ranar da Ummien za ta fita takaba nan da sati me zuwa. TAIMIYYAH ta dubi Ummie tana cewa, "Amma dai Ummie za ki zauna anan tare da mu, ba gida Kd za ki koma ba ko?"

Ummie da gaba ɗaya a ƴan kwanakinnan ta ke sake jin kewar mijinta da yaranta me tsanani na damun zuciyarta,ta yi murmushin ƙarfin hali tare da cewa, "To ganinan dai Zaynab,zan cigaba da zama dai har zuwa ayi bikinku sannan sai na tattara na koma gida,sai dai na dinga kowawa Iyah ziyara time to time,ni duk na ƙosa ma time ya zo mu sha biki in ga cewa na aurar da ɗiyata, ko kya haifomin jikokin da zan yi alfahari dasu."

TAIMIYYAH ta yi saurin kai bakin gyalenta ta rufe fuskarta, cike da tsananin jin kunyar kalaman Ummien. Ummie ta saki dariya kunyar TAIMIYYAH na sake birgeta, tare da haifar da tarin ƙaunarta me tsanani a cikin zuciyarta. Ta buɗe baki cike da son sake tsokanar TAIMIYYAH ta ce, "Haba daughter ko ke baki son ki haifo little Nahar ne ,wacce za ta dinga ɗebe mana kewar wacce muka rasa?"

TAIMIYYAH da kalaman Ummie suka motsa zuciyarta,sai ta yi saurin duban fuskar Ummie da ke faman murmushi ta ce, "Ina so Ummie in dai Allah zai bani ina so,kuma In sha Allah zan roƙa a maida min sunan Nahar ɗita da na rasa."

Yadda TAIMIYYAH ta yi maganar fuskarta na haskawa da tarin kewar ƴar uwarta,ya sanya Ummie jin zuciyarta ta taɓu,ta yi saurin kauda zancen ta hanyar faɗin, "In sha Allah Zaynab za ki haifa,Allah zai ba ki rabo da gaugawa kamar yadda auren ya zo cikin gaugawa."

Daga haka Ummie ta mai da hiran ya koma tattaunawa akan yadda za su shirya shagalin bikin, idan lokaci ya yi, ita dai TAIMIYYAH kunya ya hanata biyewa Ummien su yi maganar yadda ya dace.

Kiran Maleek da ya shigo cikin vid call ne ya sanya TAIMIYYAH tashi ta nufi bedroom ɗin Ummie don amsa wayar.

A kan Sofa da ke cikin ɗakin ta yi masauki lokacin da take receiving call ɗin, tare da gyara zaman gyalen da ta yafa ajikinta.

Ta saki kyakykyawar murmushi lokacin da face ɗin Maleek ya bayyana a allon screen ɗin sabuwar wayar da ya siya mata,wani irin soyayyarsa ta ke ji a ƴan kwanakinnan na ƙaruwa a cikin zuciyarta.

A.Maleek Ado wanda ke kwance akan doguwar kujerar 3 seater,wanda ke cikin haɗaɗɗen falon gidansa da ke can Lagos,ya sauke idanunsa akan face ɗin TAIMIYYAH, yana jin wani irin sabon feeling akanta na kewaye jinin jikinsa.

"Yaya Maleek ina yini ya aiki?"

TAIMIYYAH ta furta da muryarta me cike da shagwaɓar da ke motsa zuciyar Maleek Ado. Ya kafeta da ido yana taɓe baki kaɗan ya ke faɗin, "Wife ni fa ban san wannan sunan wai Yaya, ta ina na zama Yayanki in banda son kalar dangi, cewa za ki yi ina yini Darling."

Yadda ya yi maganar a miskile ya sanya TAIMIYYAH zunɓure baki tana sakin murmushi,cike da shagwaɓa ta narke murya ta ce, "Ni dai Yayana ne kai, tunda ni ƴar Hajjah ce ka ga kenan kai Yayana ne."

"No wife ni ban yarda ba,tunda soon za a ganki da ƙaton cikin da za ki haifo min twins, don da nayi mafarki kin yi ciki an ce twins za mu samu. Kin ga kenan ni ba Yayanki bane, ko Yayanki zai iya yi wa ƙanwarsa ciki ne ta haihu?"

Maleek Ado ya yi maganar cike da basarwa, tamkar ba sakin layi ya yi ba ko a jikinsa. TAIMIYYAH da tsananin kunya ya lulluɓeta sai ta yi saurin jan gyalenta, ta rufe face ɗinta da hannu ɗaya,cikin murya me cike da shagwaɓa ta ce, "Don Allah Yah Maleek ka bari, ni wallahi kunya na ke ji zaka sa in kashe wayata Allah kuwa."

Maleek ya saki ƙaramin smile yana saurin faɗin, "No wife wallahi kar ki fara kashe min waya,kuma a buɗe min fuskata ni banson wani gulma, wai a dole ana jin kunya ta."

TAIMIYYAH ta buɗe fuskarta har lokacin kunyar kalamansa ta ke ji, shi ko ya basar ko ajikinsa sai ma cigaba da zaro mata zance ya ke yi. Sun ɗauki lokaci suna waya,kafin Maleek ya yadda su yi sallama,ganin lokacin kiran sallar magrib ya kusa.

Lokacin da TAIMIYYAH ta koma Sasan Iyah, ta same su ne zaune ita da Baba Sani,da alamu suna tattauna magana ne me muhimmanci, hakan yasa TAIMIYYAH na gaida Baba Sani ta shige ɗaki.

Sai da daddare ne bayan sun kammmala yin dinner, Iyah ke sanar da TAIMIYYAH maganar da suka yi da Baba Sani,akan son ya nemi auren Ummie da zaran ta fita takaba nan da sati ɗaya me zuwa. TAIMIYYAH ta dubi Iyah da wani irin tarin farin ciki daya haska cikin idanunta,bakinta har rawa yake wajen faɗin, "Wow! Iyah aiko kin yi tunani me kyau, to me Baba Sanin ya ce?"

Readers Also Read