Kenza eBookz

Tarko complete novel - Chapter 10

Tarko complete novel - Chapter 10

Tarko complete novel Chapter 10: Tarko complete novel Chapter 10. Ya kai wani lokaci zaune a falon batare da sanin su ba, Duk zancen da sukeyi a lokacin…

3,277 words

Ya kai wani lokaci zaune a falon batare da sanin su ba, Duk zancen da sukeyi a lokacin yayan nasu Abubakar yana sauraron ,su, Bawani zance bane sai zancen wa yan nan bakin matan da suka kawo wa sadiya ziyaran dubiya a asibiti dazun da yamma, A daidai lokacin da yake shirin magana ne yaji muryan da tun fara zancen bata ce komai ba tana cewa, To ke anty Samira may ye abin kushewa a wanan zancen ? Ina dai wa yan nan matan da kike zance akai da sanin yayan mu sukazo, gurin ko Kuma ai yayan mu idan kin kula yai farin cikin zuwan nasu, Don haka kama yayi mu ma muyi farin ciki ga duk wani abinda da dan uwan mu ke son don taya shi, jin dadin abin, Amma ni sai banga wani abin kushewa ba sam ga re su, tunda don dan uwan mu suka zo gurin, Bafa ke ce zaki zauna mai da su ba shike ra,ayin abin shi don haka namu addu,a kawai idan da alheri a ciki, Allah ya,,,,,, Da sauri Aisha ta dakawa Meena tsawa tace Alheri a cikin may fa ? Amma ko dai ke Meena ke bani mamaki kwarai da gaske, Wa yan,ga yan barikin zakiwa yaya Abubakar kwadayin su, Kallon mamaki Meena taiwa yar uwar nata kamar za tai magana sai kuma Mike don kokarin barin dakin don zuwa bayi, ta watsa ruwa har takai kofa sai ta dan juyo tace Ai da ku san cewa ba,kwa son su sai ku,ki karban kudin su da su ka baku, Daga haka tabar dakin zuwa abinda take kokarin yi kai tsaye, Daga gurin da Abubakar yake zaune yana jiyo hiran yan uwan nashi cikin fahintar ko wacen su,,, Huci yayi tare da furzar da iskan dake a bakin shi zuciyar shi na mai suya, tankar ya fada dakin da yaran suke a ciki,

***** ****** ***** Bayan kwana biyu an sallamo matar yayan nasu daga asibiti bayan dan jiyan da tayi saboda ciwon maran dake yawan damun ta akai, akai, idan tana period, Sai dai wanan karon ya fi na kullun matsala shine dalilin kwanciyar ta asibitin, Sosai yaiwa malam tsoho tsaraba don jin dadin wanan tsohon, Wanda ya sha wahala dashi alokacin da yake yaro da kuma lokacin da yake bukatan taimako, Motar ma,aikatar su ce ya dauko don ta mayar mai da yaran da suka zo mai hutu daga gida, Inda yaiwa kowacen su tsaraba daidai gwargwado, Ranan Jumma, da safe sukai shirin tafiya komawa birnin kebbi, da lodin kayan su, Yaso samira ta tsaya da su har zuwa wani lokaci amma fafir tace ita bazata kara zama ba inda tasa mai kuka da tashin hankali, Yana tsaye yana kallon su har suka shiga mota inda Meena ce can baya zaune, Driver ya ja mota suna dagawa yayan nasu hannu cikin bankwana, Bacewar motar su yasa shi sauke ajiyan zuciya cikin sanyi, Ya juya zuwa cikin gidan shi don shirin fita gurin aiki,,,

***** ******* ***** A sai musalin magriba suka isa saboda lalacewan da motar su ta dan yi a hanya, Duk wanda ke gida ko haraban wajen gidan yasan da isowan yan matan gidan, Don hayaniyar yan kannen su tare da sauran yan uwa da ya kaure shiyan, Malam tsoho daga cikin massalacin shi inda ya ke zaune yana jiran lokacin sallah yai murmushi kawai, Don jin dadin Allah ya kawo mai yan jikokin shi gida lafiya, daga sada zumuncin da suka tafi yi gurin dan uwan shi, Duk wani tsaraban da suka iso da shi tun daga kayan su har na sako duk a sashen mama Ladi a ka jibge su, Hand bags din sune kawai kowa ta samu karasawa dashi sashen su, Meena dai sallah ta ga,batar a lokacin, don gudun kada lokaci ya kure mata, Sai da ta tabbatar da cewa, i,zuwa yanzu mutane sun dan rarage a gurin, Sannan ta nufi sashen mama Ladi don ta gaida ita ta dauko kayan ta,,, Hannu Meena rike da yar uwan ta tare da kanin su guda wanda ke binta a bayan ta, Tun dan kwanar da zai sadaka da sashen na mama Ladi zaka iya jiyo muryan ta kamar fada, Sannu a hankali Meena ta karasa gurin inda ta samu anyi dai, dai da kayan cikin da trolley din ta, Ga kuma mahaifiyar murja ita ma a tsaye cikin tujara da nuna masifa a idon ta, A hankali, Meena tace mama sannu da gida mun samay ku, lafiya ? Mama Ladi wace bataji Meena ba alokacin saboda masifan da maman murja ke yi da ita cewa don may zata budewa yara kayan su ta kamar wa yanda sukayo sata, a can, ? Idon Meena ne ya ciciko da hawaye don takaici da bakin ciki a hankali ta duka gurin tana dan tattara kayan ta cikin kunan rai, Duk wani abinda ya danganci abinda aka saya masu a Abuja gefe guda Meena ta ahe wanan abin Inda ta tattara yan kayan ta dama ba wasu shirgi ta tafidasu masu yawa ba don haka tamike tabar gurin Meena na shiga sashen mahaifin ta wanda aka kewaye da dan guntun katangar jan laka, Sai yar rufa ta kara wanda akayi tankar barandan kwano inda suke shan iska, Dakin da take zama da yan uwanta can ta nufa a cikin bacin rai, Kan,nen ta da sukaje tare sune ke fadawa mahaifiyar su cewa mama ladi ta budewa Meena kaya tana bincike ga maman Murja can ta na fada akai, Duk da rayuwan mama Saratu ya baci amma sai ta kan,ne a cikin zuciyar ta kawai, Daga gurin da take tsaye ne take wa yar nata fada akan to may zai bata mata rai har ta,shiga damuwa kamar wace bata san may ake a ciki ba,, Mama ni ba fushi nake akan kayan ba yadda dai mama ta watsar muna da kaya a tsakar gida tana tone tone tankar munyi sata acan, Baba Samaila ne ya shigo gida da murnan shi don ganin yarsa da yake ji da ita ta dawo, gida lafiya, Bakin Baba Samaila har kunne don murna sai,dai kuma a irin halin da ya samu yar nashi a ciki sai murnan ya koma mai ciki, Ladi ladi ladi Allah dai ya shirye ki abinda Baba ya iya furtawa ke nan a lokacin, Ina kike Amina, ? Gani Baba ko Ladi takawo maki kayan nan kada ki fara ki karbe su kin ji ko, To Baba inji Meena cikin sanyin murya ta ansa wa mahaifin nata,,,

***** ****** ***** Mama Ladi bayan ta gama fada da mahaifiyar murja wace tai ma mama Ladi tas, kuma ta dauki kayan yaran ta tafi da shi cikin gori, Sai a lokacin ne idon ta ya bude inda take neman jakar kayan Meena don ta mai da kayan nata ciki, Samira ce ke fada mata cewa ai Meena tazo ta dauki kayan ta ta tafi tun dazun, Idon ya kai gurin kayan da ta,zube kasa wanda dan ta Abubakar ya,sayawa su Meena din, a matsayin tsaraba, Cikin tsawa tace wa Samira ta kwashi English wear takaiwa Meena ta bar mata turamen zannun , Center carpet da sautan kayan da ya aiko wa malam tsoho tana so , asa mata su a cikin daki, Samira tace amma mama yaya fa cewa yayi akawo wa malam tsoho su yasa guda dakin shi guda kuma ya aje a waje gurin da yake bada karatu, Shin wai Samira ke ta kin ka haihwa min mai sunan malam ko niya,? Kayan Meena Samira ta kwasa don ta kaiwa yar uwan nata, Sai dai tana shiga Baba Samaila yace Samira ta koma da kayan tace wa mama a bar su kawai, Meena ta gode don bata cikin ragga,, Samira tana fada,wa mama sakon Baba samaila sai cewa mama tayi mahaukaci kawai, Alluran sojan na ya motsa mai hita batune don rigima shika so, Kaya dai na amshe su bashi kuma da wadda zai yi da ni don dana yai gaba ko , Shehu ya roka muna Allah ya amsa muna, Abinda dawiwa shikai ya kwasa tunda ba shi iya sai mata irin su,

Washe gari tun da safe aka tashi da gyaran dakin mama Ladi inda aka shimfida mata carpet din da ta mamaye,,, Sauran sakon mutane kuma sai wanda ta ba don son ran ta, Meenat ko tun daren jiya tasawa kan ta hakkuri akan kayan nata badon komai sai don irin wanan cin fuskan, da mama Ladi tai masu ita da mahaifanta, Don haka ranan shirin komawa sokoto ta yi ni dashi don duk wani abin da za,a bukata na tafiyan ta baba ya shirya mata su tsab, Washegari tun da Safe tabat garin birnin kebbi zuwa Sokoto, A cikin shirin ta ta tafi sallaman malam tsoho wanda a lokacin har yafito majalisar shi ko yana dan kishi gide yana lazimi a hankali Inda yaji sallamar jikan nashi da sauri yadago kai yana kallon ta cikin mamaki, ya ce, Amina badai tahiya zaki yi yau ba da dawowan ki baki ko huta ba, ? Dauri ki bari wani sati ke ga sai ki shi makarantan ko ? Meena wace take kokarin gyara jakar hannun ta don ta durkusa ta gaida tsohon tace, Malam walleh ban tsayi kaga an, wuce ni ga karatu kusan sati biyu ke nan, Me nika tsayawa yi gida in tai in isko notes da yawa, Malam tsoho yadan kada kai cikin jimamyn zancen jikan nashi ya na kokarin tura hannu shi cikin aljihun wando shi Yace to baku kun,katai birnin taraiyya kun kai ,zaman ku ba, ? Hmm inji Meena wace ke duke a gaban tsohon kakan nasu mai farin gemu, Ta,ce malam ko ni an bazama munkayi ba mata tai ta a bata da lahiya shina mun ka tsaya har taji sauki, Subbahanallah halan missa may ta inji malam tsoho ya na tambayan jikan nashi cikin son jin karin bayani, Walleh malam ban sani ba yadda dai niji suna hwadi shi na wai duk wata haka takai, Mika mata kudin da ya ciro daga aljihun shi yakeyi ya fadin i maza ki boye tun yan sa idon ga ba su tai ciki hwada ma uwayen su ba,,, Meena takarba tana cewa ta gode inda tabi umurnin malam tai sauri ta tura kudin cikin jakar hannun ta, Tambayan ta yayi da cewa to Amina an, nan da sokoto shina ki kai wanga sakko haka? Kafin taba da ansa daya daga cikin yan rakiyan ta yaba da ansa da cewa, Don tana son kafin ta shiga makaranta ta dan tsaya gidan uncle din ta, ta, huta,,,,, Tsohuwar motar akori,kura na Baban ta shine za,a kaita tasha daahi suna tafe hayaki na tashi motar na wani kara, booooooooooo,,,,,

***** ****** ***** Lokacin da duk ake wanan zancen Baba Buhari baya gari sai da ya dawo ne ya samu labari gurin kishiyar mama Ladi din, A cikin bacin rai ya nufi gurin da mama Ladi take a bakin murhu tana tankaden garin dawa na tuwo ga karkashi a gefe guda wanda ta gama gyarawa zatai miya dashi,,,,, Ladi, ke wace irin mahaukaciyan mata ce wai, Shin ko kauyan cina har yanzu ka cin ki na ladi ko rashin mutunci irin naku Ginbanawa ka da mun ki, Sai a lokacin mama Ladi ta dago kai ita ma a cikin masifa take don ta riga ta shirya akan wanan zancen , Don bazata dauki wanan rainin ba a dinga zuwa cin arzikin Dan ta kai tsaye, Ita kan sam ba zata yarda da hakan ba sai dai duk wani sako ko aike yazo ta gurin ta direct ki kuma taba wanda ranta ke so,,, Malam shin sau nawa kake son in fada maka cewa Dan ga dai dana ne ba wani na ya haifa min shi ba,, Sakona ina so don haka sai a jira wani ko ? Takare she zancen cikin muguda baki irin na mata kauye, Tare da dukawa gurin murhun ta don ci gaba da aikin girkin da takeyi, Tsaye Baba Buhari ya yi cike da mamakin irin wanan karfin halin na mama Ladi da kuma rashin kunya, Ya san cewa idan ya tanka a lokacin za, ayi batatta don haka ya juya direct zuwa gurin mahaifin shi, Don ya sanar dashi saboda malam tsoho yai ma duk diyan shi shamaki akan saurin daukan mataki ga iyalin su,,,,

****** ******* ****** Anty Meena oyoyo Anty Meena oyoyo yaran gidan uncle ke wanan ihun lokacin da mai yar besfa ya aje Meena da kayan ta a kofan gidan su dake a cikin Sama,Road, Ihun yaran ne yasa iyayen su gane cewa Meena tadawo Meena sarkin aiki ga tsabta da iya girki, Haka matan gidan na uncle din ta ke ce mata, a duk lokacin da ta tsiri yin wani aiki,,, Anty Amarya wace itace tafi bawa Meena fuska agidan ta kwaso da saurin ta daga dakin ta cikin farin cikj da ganin Meena din, Ja tayi ta tsaya a daidai lokacin da sukai kicibis da Meenatun a kofan shigowa falon su, Meena wace ta duka tana daukan dan karamin dan Anty amarya wanda yaga meena yake murmushin nuna yasan ta fa, Shin Meenatu ba dai mai kin kafara shafawa ba ko ? Meena wace ta ji maganar uwar dakin ta kamar a mafarki tai saurin dagowa cikin dariya tana cewa, A, a,a wallah anty mikaini ? Ke koga yadda kin ka koma Meenatu an ? Dariya Meena tayi don jin zolayan da amaryan uncle din nata ke mata, Sai a lokacin uwar gidan wace ke zaune tun shigowan Meena din saman dining table tana shan abu a cup tai magana, Walleh Meeana an duk ke canza kamar ba ke ta ba, ? Ko mummy ? Inji Meena din wace ke ta faman murmushi saboda jin dadin ganin yan uwan ta, Gaskiya inba, don gida gida bane da sai tace nan gidan uncle din ta yafi mata dadin zama don ba wani sa ido ko tsangwama a gidan Ba kamar gidan su ba da duk abinda mutum keyi idon mutane na gare shi,,,,,,,

ZEEE MAKAWA YELWA 🕸🕸🕸TARKO🕸🕸🕸 🕸🕸🕸🕸🕸 1⃣6⃣

ZAINAB IDRIS MAKAWA

ALLAH- AS-SALAAM,,,,,,

Baba Buhari ne zaune a gaban mahaifin shi malam tsoho, inda yake koro mai duk yadda al,amuran da suka faru, akayi, Malam tsoho sai faman kada kai ya ke yi don mamaki koda yake bai dauki sarakuwan nashi cikin mutanen kirki ba dama, Tun farko bai ra,ayin ta sam da dan nashi abudai ne in yaro yace yana ra,ayi sai a kyaleshi yayi, Ina kake malami Naam Baba ya ansa wa mahaifin nashi a cikin ladabi, Katai kayi hakkuri kajiya ? Halin Ladi sai ita,, To amma Baba , Hannu malam tsoho ya daga mai alaman ya isa haka nan, Shiru Baba buhari yayi a vikin biyayya yanà mai dukar da kan shi a lokacin, Magana gudane shine kayan yatinyar ga Aminatu wanda an,kan ansa, Hakan baiyi dadi ba sam wallahi sai dai kawai ayi hakkuri abar zancen, Shi kuma Samaila zan ganshi in mai magana don kada ya dauki abin da zafi a ran shi, To amma yarinyar ga Aminatu yau ta koma makaranta sam banga wani bacin rai a tare da ita ba, Baba ai kasan yarinyar yarinyar kirki ce ba zata taba nunawa ba,, Amma zanga sauran abokan tafiyan nata don inji ko may yafaru acan gidan dan naka, Saboda naji cewa wai matar, mai suna batada lafiya, Baba shima cikin mamaki ya tambaya, ya ce, may ke damun ta, Bari dai mu bincika a hankali, Kasan matar taka bata da kwanciyar hankali balle a ce, ayi zancen kai tsaye, Hakane Baba inji Baba buhari ya ba mahaifin shi ansa atakaice, Cikin kwantar da harshe Baba buhari ya ce, to baba Su wa yan nan kayan na wurin ka fada ta mamaye yaya za,ayi da su? Cikin sauri malam tsoho ya ce, kai, kai dama ai wanan kayan yara ne kabar mata kawai Allah sa albarka kaji, To ,Baba inji Baba buhari ya ansa acikin ladabi,

****** ****** ****** Wanan labarin da yazo ma Abubakar yai matukar bata mashi rayuwa, sosai Ya dade yana tambayar Baba Wadda wanda ya bugo mai waya yana sheda mai abinda ke faruwa, Sam baji dadin jin wai mama ta karbe kayan yar gurin kanin mahaifin shi, Yariyar da duk kusan zaman su a gurin shi ya na hankalce da cewa ita ce mafi wahala agidan, nashi, Amma sai gashi wai ita ce kuma mama ta karbewa kayan, Ba komai kamar yadda yai wa Baba wadda alkawarin zai aikowa Baba samaila da wani abu don ya dan rage zafi,,,, Kiran Salawatu ce ya,shigo a wayan shi abinda ya dan washe mai zuciya ke nan, Daukar wayan yayi a cikin jin dadi yana mai cewa ya akayi ne Salawa, kamar yadda yakan kirata Cikin lumshe ido don jin dadin sautin muryan dan matashin da tayi tace, Babu komai Sir na dai kiraka ne kawai don inji muryan ka, Tooooo, fa inji Abubakar din wanda ya fadi haka acikin yar dariya da nuna mamaki, Cikin lumshe ido yace ni har na isa babban yarinya kamar ki, ki ce kina son jin murya na, Sir ai har ka wuce hakan a gurina, Tau na gode inji Abubakar ya fadi haka a cikin jin dadi da nuna kulawa,

****** ******* ****** Aisha wace ke zaune kusa da kakan ta wace ya turawa kwalban zuma da tazo roko gurin shi wai zataci masa dashi, Malam tsoho yace wai ke Aisha, may matar yayan naku ta bakune haka kowan ku yai kiba da haske haka,? Da sauri Aisha ta dago kai cikin jin mamakin maganar kakanta, Ta ce malam muka dai bawa kan mu ko ? Matar da bata iya ko da kula da kanta ba balle wani, Ai in fada maka malam wanan matar sam wallahi bata dace da yaya Abubakar ba, Malam ya dauko mata wani guntun kilishi a leda wanda yaji kuli kuli, da yaji yace karbi wanan, Karki tashi ki zauna sai kin cinye don kar ki fita dashi wani yagani gashi iyakar shi ke nan, Nan Aisha ta samu guri tafara yagan kilishi a hankali, Malam tsoho yace to shi yayan na ku may yake ci da bata girki, Samira tace wai sayowa yakeyi ko kuma ita samiran ta dafa amma yace wai ba dadi girkin Samira, Shine da muka tafi kasan halin Meena da son aiki itace ta kirkiro muna girki da sauran aiyuka har mukeyi, Malam yace toshi yayan naku yana ci ko ? Ta ce malam cikindago kai tare da tsaida cin kilishin ta tace sosai ma har fa da cefanai yake yo,wa daga baya, sai mu girka, Kai malam tsoho ya kada, don al,ajabi ace wai mace bata girki a gidan ta, Bai kai ga karasa tunanen shi ba sai yaji muryan Aisha tana cewa, Wallahi, malam yaya Abubakar sam bai yi sa,an mata ba, Ga mace wata iri ba fasali ba zuben suffan mata ko kadan,, Wai ma malam baka san wani abuba yanzun haka wata tsohuwar yar bariki tana nan ta lakewa yaya Abubakar gam, kamar chewing gun, Gaban malam ne ya fadi don jin sabon masifan da ke shirin kara bullowa jikan nashi, Ya na tunanen yadda zai bullowa zancen Sadiya sai kuma ga wani sabon zance anzo mai da shi, Gaskiya dole ne yasan abin yi akai, Bazai hana shi aure ba amma yar kirki yar asali wace ta fito daga zuria mai mutunci, To amma shi Abubakar din yana ra,ayin ita matar da ki kace yanzu din ? Daidai lokacin da Aisha ke kokarin tura kilishin karshe abaki tace, Malam matar fa mai kudi ce, don ko da zamu dawo dubu ashirin taba mu sabbi fill da su, Wani iri malam ya ji amma afili sai cewa yayi Allah ya kyauta kawai,,,

Readers Also Read

More by Bilyn Abdull