Tarko complete novel - Chapter 101
Tarko complete novel Chapter 101: Tarko complete novel Chapter 101. ****** ********** ****** A gajiye ya shigo gidan don har ya manta da zancen dawowan…
2,602 words
****** ********** ****** A gajiye ya shigo gidan don har ya manta da zancen dawowan Fatima da akace tayi saboda aikin dake a gaban shi lokacin, Yana shiga gida su Aina da yar uwar tane su kai mai Oyoyo Uncle, cikin jin dadi da farin ciki, Rugumay yaran yayi zuwa jikin shi cikin so da kauna tare da dan sauke numfashin sa, a hankali, Ya dan dago yaran daga jikin shi yana cewa har kun dawo ashe suka ce eh, Daddy Ba maman mu ta dauke mu takai mu can gurin kaka ba muna cewwa ta dawo damu amma sai taki ko school bama zuwa acan din, Wani irin tausayin yan marayun yaran ne ya kamashi yaji yaran sun bala,in ba shi tausayi sosai a ran shi, Dan kara rugumay su yayi yana cewa kubari yanzu zaku dinga zuwa school insha Allahu, Daga inda take tsaye ta sake ajitan zuciya mai karfi don duk abinda ke faruwa tsakanin shi da yaran tana gani daga inda take labe, Salawatu wace take zaune zaman jiran azo aiwa Fatima rashin mutunci sai gashi taga, an rungumay yaran Fatima, har ana firan arziki da su, Ido qaje acikin mamaki taje kallon shi don har ta kasa bude baki tai mai sannu da zuwa, Sam Salawatu bataso haka ba don ita so tayi da ya shigo yai wa Fatima rashin mutuncin sai ta wulakanta sosai,, Paet din shi ya nufa da dan sarsarfa har ya ahiga dakin shi inda sai a lokacin ta kawar da idon ra daga gare shi a cikin kutawa, Fatima ta sake labule tana cewa yar iskan mata ai kadan kika gani wallahi don yadda na bar gidan nan sai kubar shi kuma,
Wanka yashiga inda ya fito yana tsane ruwan jikin shi da da dan karamin towel din shi, A sanyaye tai sallama a dakin inda ya dago kai ya dan dube ta kallo daya ya kawar da kanshi daga kallon ta, Har gaban shi ta karaso inda takai gwiwar ta har kasa a gaban shi, acikin ladabi tace, Ina wuni Yaya Bukar ? Abinda ya tuna mai da baya ke nan , Kalman da take kiran shi a zamanin da suke soyayyan saurayi da budurwa, a tsakanin su, Wata ajiyar zuciya ya sauke gami da fesar da iska irin ta relief din nan, Bakin gado ya koma ya zauna yadan daga kai ya kalleta tana inda ya barta a tsugune, Hawaye sai sintiri suke a fuskan ta yayin da ya kara kallon ta yaga cikin jikin ta har ya dan turo daga jikin ta, Ta ramay tayi baki duk ta fita daga hayacin ta da gani nadama duk ya baiyyana a tare da ita, Hawaye sai har yanzu sintiri yake a fuskanta, tana dan kokarin gogewa, da habar hannun ta, Wani bala,in tausayin tane ya lulube shi yasan cewa yanzu tai nadama daga irin halaiyar ta ,, Muryan shi taji yana kiran sunan ta yayin da kanta yake sade a kasa tana sharban kuka, Yace Fatima ki bar wanan kuka ki dakata muyi magana dake please, Kala batace mai ba sai dan kaiwa zaune da tayi daga inda take a tsugune da farko, Kafin ya kai ga yin magana saiga Salawatu ta fado dakin cikin wani irn tako tana taunan chew gun kas kas, da ita, Sweet Oga abinci fa yana a table tun dazun nan gashi naga baka sauko ba, Zan sauko yanzu insha Allahu, idan na gama abinda nakeyi, Maimakon ta fita sai ta dan tsaya rai a bace ya juyo gurin da take tsaye yace, bakiji bane Naji tace a sanyayye ta wuce buguzun buguzun da ita rai a bace,, Gaba dayan su binta da kallo su kayi don kowa ya fahinci may take nufi da hakan da tayi, Ya juya inda Fatima take a zaune agurin mirror din dakin nashi, yace mata yanzu dai ishara ta saura a gare ki don ko haka dakike gani ya isheki ishara, Ki godewa Allah, ki kuma godewa yar uwaki meenatu Don Meenatu ce wace tun kan nashigo gidan nan ta taushi zuciyata akan zancen ki, Don tun ina asibiti gurin ta labarin dawowar ki garin nan ya samay ni, Irin yadda ta ga na dauki zafi ya sata kwantar min da zuciya da kalamai masu fahintar da mutum, Wani irin kallon mamaki take mai ashe ma watace har ta tausasa mai zuciyar shi a kan ta abin da take tunane ke nan a zuciyar ta ,,, Tace cikin dan dago kai da wani irin murya, mai rauni ita Meenatu dai ta bada hakkuri akaina cikin daga kai yace kwarai da gaske,, Wani irin murmushi yayi mai sauti yace kinga Allah ya warware maki, idan har kina da fasaha, Mikewa yayi yana cewa ni zan sauka kasa zamu karasa maganan zuwa gobe insha Allah, Ya fara tafiya tace Yaya Aliyu bai san cewa mundawo ba yau din nan don bamu fadawa kowa zancen dawowan mu ba, Cikin mamaki ya juyo yana kallon ta a cikin wani irin kallo yace k ko yaza,ayi kizo bada sani yan gidan ku ba, Idan su kaji cewa kina anan zargin wani abu fa daga baya idan sunji cewa kina nan, A hankali ta dago kai tana mai fuskantar shi Acikin muryan kuka tace saboda bamu san irin karban da zakai muna bane a lokacin, Idan har zaka karbe mu duk abinda zasu fada ba zai damay ni muddin ina dakina zaune, Tausayi ne takara bashi watau so ne ya rufe mata ido har ta iya barin yan uwan ta duk da dinbin wullakancin da yai mata na,rashin zuwa duban ta tunbayan zuwan ta gida gashi harda cikin shi ke tare da ita a jikin ta, Amma, duk bai sa ya tafi, gurin ta ya duba lafiyan taba gashi yanzu ta kwaso jiki kuma again ta dawo gare shi, Wanan ma kawai ya isa yai hakkuri ya mayar da ita dakinta, suci gàba da zaman hakkuri, atsakanin su, A hankali ta mike jiki ba kwari tabi bayan, maigidan suka sauko tare, daga sama, Wanda a lokacin duk Salawatu ta riga ta cika fam kamar zata fashe don takaici, Fatima dakin ta tanufa inda tasamu har yaran ta sunci abincin da nasaka Ramatu ta kawo masu daga part dina, Takara jin wani irin nauyi da tasamu yaran sunci abinci har suyi barci a cikin dadin rai,
****** ********** ****** Ina kwance a saman gadon sabon dakina watau dakin asibiti wanda ya koma tankar dakina na gida, yanzu don a ciki nake komai, Inda nake under control din likita shi da nurse's ke ta kokari akan mu ni da sauran yan uwa masu irin matsalata, Ya Abubakar ne ya shigo dakin yana dauke da Amir a kafadan shi sai Dije wace daga bayan shi take tafe da Aisha da Ramatu, Yaron yana hangoni yafara wagale baki yana mika hannu yana son indauke shi, Tausayi sosai yaron ya bani don nasan cewa yana a cikin kewar uwa a lokacin, A hankali na mike ina kokarin kaiwa daga zaune, duk kan su idanuwan su yana a kaina, har na kai zaune sai faman yi min sanu kawai su keyi, Idanuwan Yayana duk suna a kaina kamar ace ya kama min ciwon na mike ni, Sai da yaga na kai zaune sanan ya gyara farar kujerar roban da aka bashi dan ya zauna, Gwago Habbi ce ta shigo tana kokarin mika mai takardan da likita ya bayar a bashi idan yazo, A hankali yake bin takardan da karatu har ya kai karshen ta ida ya dago kai yana ce min takarda scanning ce ta karshen wata da ake maki duk karshen wata, Sam bani kaunar wanan scanning din don idan akai min na kan koma tankar an doke ni ne sosai, Nace ni gaskiya normal nake ba,sai nayi wanan awon nasu ba, Murmushi kawai Yaya yayi tare da cewa daurewa zakiyi ai maki kamar yadda suka bukata daga gare ki, Kaina na kawar gefe cike da jin haushin wanan bukatar ta likita a gare ni, Muryan Yaya Abubakar naji ya na cewa wanan abin yana da sanyi kuwa, Yana nufin drink's din da Ramatu ta hado min don in sha, Kamar may rada yace cikin dan gyara zaman shi azubo min kadan nasha please, don duk a gajiye nake, Dije tace ita amaryan taka da ta dawo bata hado maka bane kasha,? Yace cikin murmushi kina kishi ke nan ko don banga abinda ya kawo zancen taba a nan a daidai lokacin da ake mika mai kofin drinks din Ayya da ta hado min yaji kayan yaji, sai kamshi ya ke tashi daga ciki, Amfanin shi shine yana taimakawa Baby dake aciki da abubuwa da dama kamar su, wanke kwakwalwa, wanke idonuwa sukara hasken gani da karfi, Yana kuma gyara mahaifan mace maiciki don ta fitar da zaki da kazantar dake a jikin ta, A hankali yake dan kurba ruwan kunun ayyan yayin da Dije ke ci gaba da mashi sheri akan cewa shi ai angone, Sai da ya kusa shanyewa yake cewa Dije kema dai na gane kina kishin Fatima sosai, Tace matar da ta tsufa da ita da wanan ai ina ganin ba wani tseraiya a tsakanin haihuwan su, Tankar baiji ta ba sai saidai satar kallon reaction din da zan nuna don jin cewa cikine wai a jiikin Fatima, Azaton shi yadda su kai ta hauka a lokacin da na samu ciki nima a yanzu irin shi zan yi da naji zancen a yanzu, Amma sabanin hakan sai ya gani kawai ina dan murmushi ina cewa Dije ai idan mun haihu a lokaci guda kinga sai a hade sunan a cashe kawai,, Bai juyo ya kalleni ba amma hankalin shi yana a gareni yace wa Dije kinga babu zancen komawan ki gurin malam ke nan sai ki zauna anan mu ci gaba da, zama dake kina tsare mu na yaro, Dariya akasa adakin inda suke cewa cafdi yaya akasamu ma har tazo saida Baba musa yasaka baki, Ya lura cewa ba abinda ya damau nida zancen wai ina kishi ko bakin ciki akan zancen cikin jikin Fatima, Sun dauki lokaci a dakin suna tayani hira har zuwa wani lokaci sukai min sallama auka tafi, Wani irin sanyi Yaya Abubakar yaji a zuciyar shi fuskan shi ta baiyyana farinciki, Don a zaton shi zanyi zanyi ta fitina har na tayar da hankalina gani da ciki a jikina Kuma ba lafiya a tare dabi, Shine dayake boye min zance yanzu haka baiso Dije ta kawo cen ba agabana, Mun rabu dashi inda sheda min cewa zai dawo da dare mu je gurin scanning din, Na ansa mai da cewa Alkah yadawo dashi lafiya Abinda bai sani ba shine nima daurewa nake don nima mace ce tankar kowace irin mace mai kishi,,,,
ZEEE MAKAWA YELWA
🕸🕸🕸TARKO🕸🕸🕸 🕸🕸🕸🕸🕸🕸 1⃣0⃣1⃣
ZAINAB IDRIS MAKAWA
ALLAH AL GHANI
MUNA GODIYA GA ALLAH UBANGIJI SUBBAHANAHU, WATA,ALA DA YA BADA KON YIN TARON WA,AZIN KASA LAFIYA AKA KUMA WATSE LAFIYA A GARIN MU YELWA YAURI KEBBI STATE, ALLA YAMAI DA KOWA GIDA LAFIYA ALLAHUMA AMEEN SUNNAH SAK INSHA ALLAH, 👏👏👏👏👏👏
Abubuwa nata faruwa a cikin yan watani daga ciki harda, samun canjin gurin aikin da Yaya Abubakar yasamu Yanzu an mai da shi branch din su dake garin photercouht ya samu General Manager na maikatar gaba daya,, Wanda hakan ne ya sa shi barin gari badon ran shi yaso ba duk da ci gaban da ya samu, Wanan mu,kamin yasamay shi ne da ga Allah sai kuma, chief din maaikatar nasu wanda yai sanadin zaman shi hakan Don sani halin kwazon aikin da yake dashi tun zaman da sukayi a garin Lagos dashi, Yaso ace a lokacin mun haihu saboda ya,samu kwanciyan hankali , Dole hakace ta saka shi yawan zuwa gida akai akai don ya duba lafiyan mu musan man ni da na,ke kwance asibiti da, dadewa, Kamar kullun yau ma da ya shigo garin weekend ya samu iyalin shi lafiya inda ya gudanar da abubuwan da suka kama ga ko wani daga cikin iyalin nashi, Sai da har yanzu baida kwanciyan hankali saboda, irin yadda yaga doctor's din asibitin suna faman bani special kulawa, Wanan ne ke tayar mai da hankalin shi don sai yake ganin cewa akwai fa matsala ne atare dani, a hakan, Bayan yazo ya idar da duk wani abinda ya dace yaiwa iyalinshi, ana gobe zai koma ne fitina ya taso a tsakanin matan shi na gida, Salawatu da Sadiya inda Salawatu tace, sai Sadiya ta sakar mata duty ta wai saboda gobe maigida zai koma gurin aikin shi, A take fitina ya tashi inda Sadiya tace mata ina tafito mai ma take nufi da hakan don bata fahince ta ba, Fada da rikici ne sosai ya wanzu a tsakanin su, inda suka rikice da yaya acikin gidan, Maigidan yana ciki yana jin su haka yafito yadan gega ta gefen su ya dauki keys din shi zuwa waje,,batare da yace masu uffan, ba, Ya samay ni kwance ina karanta novel din Ànty Rufaida, Umar sallaman shi ce ya sani dakatar da karatun da nakeyi a lokacin, Fuskana dauke da murmushi nake mai sannu da zuwa don tun jiya da ya iso yazo gaida ni bai samu dawowa guri na ba sai yanzu da ya shigo, din nan , Ganin yanayin fuskan shi kawai ya sa ni gane cewa yana acikin yar damuwa, Da wasa nake ce mai, nidai gaskiya a maidani gida nagaji da wanan zaman ace sai mutum ya wani haihu zaibar wanan gurin, Da kyat, na samu nadan dago daga kwancen da nake ina kokari gyara daurin zanina da ya sance a lokacin, Kallon tsab yabini dashi yana cewa amma dai wanan cikin yafi na Amir girma nake gani, Nace cikin dan cije baki wata kila mace ce zan samu yayana, Yace yana mai kallon cikin nawa Allah dai ya saukeki lafiya koma wani iri ne , Nace yayin da na dan mike da kyau ina cewa, to Yaya ba ance cikin diya mace yafi girma ba sosai , Haka kuma haihuwan diya mace yafi fitina da wahala, sosai, Murmushi yayi batare da yace komai ba naji ya sauke ajiyqn zuciya, Abinda yasani maida hankalina ke nan don nasan wanan irin nishin magana ce kumshe a cikin shi, Yace Meenatu naso ace zuwa yanzu ban daga zuwa ko ina ba ina zaune a tare da ku, don naga lafiyan ku, Murmushi nayi na kai zaune ina cewa, haba yaya ai adduan ka yafi komai a gare mu, Don ko kana nan shine kawai zamu bukata a gare ka, Sai naji ya sauke ajiyan zuciya yana dan girgiza kan shi a hankali, yayin da idanuwan shi suke a lumshe yana dan buga kafan shi a hankali saman ties, din dakin, Meenatu haihuwan ki yana bukatana a kusa don hankali baya a kwance can inda nake don zama kawai na keyi a gurin, Nace haba yayana ai insha Allahu lafiya zan sauka yan kuda na kwana, Magana ta dariya ta saka shi don sai yake ganin ni babu abinda ya damay ni, ko kadan Shi duk hankalin shi a tashe yake don zamana asibiti yafi komai daga mai hankali duk abinda yakeyi hankalin shi yana guri na kamar yai tsutsuwa ya dawo, Yace yanzu transfer nake kokarin nema don na dawo nan kowa ma ya huta don, hakan banda kwanciyan hakali wallahi, Haba Yayana don Allah kabar zancen neman transfer din nan don gaskiya, zaman ka a can aiwani karuwane agare mu baki daya, Idanuwan shi naga ya lumshe a hankali tare da, dan gyara zaman shi a saman kujera, Ina daga kwance nake ta yi mai magana a cikin kwanciyan hankali, batare da yace min komai ba yake saurare na,