Tarko complete novel - Chapter 21
Tarko complete novel Chapter 21: Tarko complete novel Chapter 21. A gidan mu nasamu kofan gidan a sake kamar yadda na jawo shi da zan fita, Hakan ne ya…
3,436 words
A gidan mu nasamu kofan gidan a sake kamar yadda na jawo shi da zan fita, Hakan ne ya sani gane cewa tun fitana Anty Sadiya bata fito ba ke nan balle ta rufe gida, Dakin ta na nufa don in sheda mata cewa na dawo daga gurin kitson da na tafi, Na samay ta a kwance tana ta sharar barcin ta hankali kwance, Najawo baya cikin mamakin ta na juya zuwa sashe na, A falo na hadu da Hamza dan gidan da na fito kitso dauke da kula a hannun shi, Sallama ya kara yi na ansa mai cikin mamaki daga gurin da yake tsaye ta kofa yake cewa , Mama tace wai in kawo maki Biski ne wai idan tai maki tayi acan ba,aki ci ba, Banda yadda zan yi dole na karba na,dauko wani kula daga kitchen na juye aciki, Daki na shiga na debo sabulu da omo nasa aleda nace ya kaiwa Fattu, yace na gode Shi kuma na bashi dari biyu saboda dauko abincin da yai min,, Saman dinning table na aje abincin na wuce zuwa daki, Har na zauna sai na tuna da maganar Anty Amarya da tace duk lokacin da nake da girki in tabbatar da cewa na gyarawa maigida dakin shi tsab, Don haka namike da sauri don zuwa na fara gyarawa kafin lokacin sallah ya karaso, Kofan shigowa gidan mu na jawo,na rufe da key don kada wani ya shigo muna, A hankali nake hawa saman benen da nake zaton dakin maigidan ne a can, Kasan,cewar yace rana na farko da zan fara shiga dakin nashi, Nayi zaton cewa zan samu dakin a rufe amma kuma sai na samu abude yake, Abin yabani mamaki don azatona rufewa ya ke yi , Gashi matar gidan na ta sharan barci abin ta batare da ta damu ko wani zai iya shigo masu ba, Kayane birjit ko ina acikin dakin babu gyara ko kadan Zanin gadon yai wani motsu, mutsu saboda rashin gyara, Dole na cire hijab dina na shiga aiki ba shiri, na kai wani lokaci acikin dakin, Don har sallah aciki na gabatar na tara kayan wankin da suke gefen tarshe a kasa guri guda, na daure cikin zanin gadon da na kwashe, Kafin wani lokaci dakin ya koma kamar ba shi ba don nan take yafara kamshi, Sai karfe uku na sauko saboda unders din dana tsaya wankewa,, A hankali nake tafiya zuwa kasa, don duk jikina yana ciwo saboda gajiyan aikin da na sha, Don ina zaton tun tarewan su gidan ba,a taba gyaran dakin ba, Tun saura steps biyu in sauko na hango Anty Sadiya a zaune saman kujeran dining tana cin Biskin da Maman Bi,u ta aiko min da shi, Tafiya na da taji yasa ta dago kai don taga kowaye, Wani kallo mai kama da harara tai min tare da dauke kai, taci gaba da cin abincin ta,, Acikin sakin fuska nace har kin tashi,? Acikin wani irin murya dasasshe tace eh, Kanta a duke tace, A,she har kin dawo har kin girka muna abinci, yanzu da na farka na,fitone nagani, Amsa na bata da cewa ba,nice na girka ba , Gidan da na tafi kitso ne suka aiko min dashi, dazun, Nazaci cewa bazata ci gaba da cin abincin ba amma sai naga kawai tana ci gaba da ci,abin ta, Ban zauna ba sai da na gama hada muna abincin dare, Nai sallah sanan nazo na zauna don inci abinci, tare, dan hutawa, Ba laifi don girkin tsohuwar yai dadi sosai, ashe abin da ya sa Anty Sadiya ta ci fiye da rabin kulan, abincin ke nan,
****** ********* ****** Malam tsoho zaune tare da yaran shi da suke shawaran don zuwa Abuja su taya dan su murnan samun karin girma, Sai da tsohon ya gama sauraren shawaran da baba Samaila suka kawo mashi shi da sauran yan uwan shi, Sanan ya dan nisa a cikin jin dadi ya ce gaskiya yaji dadin wanan shawaran badon komai ba,sai don a nuwa jikan nashi irin kaunar da suke mai, Amma kuma ga shawara guda ya kamata a fadawa mahaifiyar shi ko akwai daga cikin yan uwan ta da zasu, Haka kuma can 2urin ita matar tashi don kada sai mun tafi su zo suce basu da labari, Kowa yaji dadin wanan shawaran da malam tsoho ya kara kawo wa,
Baba Buhari yagama zaiyanawa Mama Ladi sakon malam amma sai cewa tayi ita gaskiya babu wani dan uwanta dazata fadawa cewa ya zo a tafi, Baba Buhari yace har yayan ki bazaki fadawa ba ko zai samu zuwa, Amma sai mama Ladi tace ita fa kada aiwa yara gaiyya zuwa gida yana fama da kan shi, Baba Buhari yace wai ke Ladi, shin yaron ga ke kadai kika haife shi ne da kike nuna min haka, To bari kiji yadda kike ganin cewa zaki yi iko da shi haka nan nake iya iko dashi ina dai kyaleki ne kawai don ba hankali gare ki ba, Ai baka sanin banda hankali sai na sa yaturo maku da yar ku gida tukun, Yanzu haka ma ina tsan manin ya a ko ta dai can gidan da take zaune ne a sokoto, Nunata Baba Buhari yayi da hannu yana fadin ji mahaukaciya, Ai in,kinga auren yaran nan ya mutu to babu gudan su ne, Daga haka Baba ya wuce abinshi dama malam tsoho ne ya matsa akan wai yazo dai ya shawarce ta don a fitar mata da hakkin ta,
****** ********* ****** Wanka nayi inda na tsala kwalliya kamar yadda Anty ta fada mun in dinga yi,, da zaran mun raba girki, Tun daga haraban gidan falon, gidan har zuwa kitchen da kuma,sauran sassan gidan yau fes,suke, sun sha gyara, Uwa uba kuma dakin maigidan da bai taba ganin an mai hakaba, Kafin shigowan shi gidan su Hamza ne suka kamo mai TV daga cikin kwalin shi sabo fil, Anty Sadiya wace ke zaune a falon tana kallo season film kamar kullun a wanan lokacin, Ta dan dago kan ta, tana gani tai saurin kau da kai gefe don takaici, Da Sallama yaya Abubakar ya shigo gidan yana sagale da corth din shi ga kafadar shi, Gaba daya yau sai ya ga gidan duk ya canza ma a lokaci guda, Kitchen na fito dauke da jug, din ruwan sanyi hade da cup,a hannu na, Daidai lokavin da ya ke zama saman kujera a falon, Idon shi kyam a kaina baya ko kyaftawa, Anty Sadiya wace ke kallon shi ta wutsiyan ido taja dogon tsuki, Murmushi yaya ya sake saboda ya fahinci abinda takewa tsakin, Sai alokacin yadan kau da kan shi gareni cikin zuciyar shi fadi yakeyi ita dai wanan yarinyar komai nata daban , Har tafiyan ta da kuma iya ladabin ta nadaban ne, Sai da nakai kasa na nafara tsiyaya mashi ruwa a,cikin cup nace mai sannu da dawowa yaya, Shiru ba ansa yasani saurin daga kai yana rike sa goshin shi tankar yana masa ciwo, Hakan ya tabbatar min da cewa yana dan cikin damuwa ne kila alokacin, Ga ruwan nace masa abinda ya sa shin firgigi ya dan dago kai, tare da yin dan takai,taccen murmushi a lokaci guda, Sosai naga yasha ruwan tare da sauke ajiyan ziciya yayin da uake aje cup din saman table, Dago kai yayi ya dubeni sosai sai yace a kasalance, Kedawa kukai wanan aikin haka ? Kaina na dan dukar a kasa ina wasa da hannun jug din dake gaba na nace ni kadai, tare da kara sunkuyar da kai na akasa, A hankali yace ki daina wanan wahalan idan ina gida zanyi da kaina. Don Bake kadai bace ke batawa don haka kinfa wahalan zai maki yawa, Daga haka ya mike zuwa sama inda dakin shi yake, Gaba daya sai yaga dakin ya canza mashi, don bai taba zaton abinda ke ciki suna da haske haka ba, Da mamaki a fuskan shi ya tsaya yana karewa dakin kallon cikin sha,awa,
Wanka yayi yafito cikin kananin kaya ajikkn shi sai kamshi ke tashi, Tv da ya shigo dashine yakira mai hakawa don a haka a daki na,,,,,
ZEEE MAKAWA YELWA [7/30, 07:13] Anty Lantana: 🕸🕸🕸TARKO🕸🕸🕸 🕸🕸🕸🕸🕸🕸 3⃣8⃣
ZAINAB IDRIS MAKAWA
ALLAH-AS-SAMI,
Tv plasma, yar madaidai ciya ta bango yaya Abubakar yasa a ka hada min a daki na, Naji dadin wanan abin da, yaya yai min Ko banza zan samu abokin hira a daki na, A yan kwanakin da na yi a gidan yayan mu na fahinci cewa yanzu komai ya canza agidan nashi bakamar wancan zuwan da mukayi da yan uwa na ba, Ba sai an fadawa mutun cewa yanzu yaya Abubakar yana cikin walwala ba da falala da nasarorin rayuwa, Hakan kan sa in,zauna ina tunanen shi yaya Abubakar wani irin mutum ne wai ? Ace duk wanan tatin dukiyan da Allah ya bashi tun yana cikin kurciyan shi amma bai damu da iyayyen mu na gida ba, sam, Irin halin rayuwan da nasan su na fama da shi kamar may ? Amma shi kuma gashi cikin jin, dadin rayuwa, ya tara wasu irin motoci har guda uku a farfajiyan gidan shi, Sai kyali da daukan ido sukeyi da ka tunkari gidan, Yanzu falon gidan da ke samun gyara ko da yaushe, shima abin sha,awa ne, Amma kuma fa, iyayyen na can a cikin wahala sai sun samo abinda za,aci agida,ko wace rana, Girgiza kaina nayi saboda takaici, da bakin ciki, Wasu siraran hawaye suka zubo daga idona saboda bacin rai, Gefen bayan hannu na sa, na,shafe dan guntun hawaye, Aiki nake a kitchen amma ina tunanen yadda zan fadakar da yaya mun cewa mutanen gidan mu suna bukatan taimakon shi, Babu fuska agurin yaya Abubakar dan iya fada mashi wanan maganan, Haka naci gaba da aikina batare da na samu wani mafita ba daga zancen,
Yanzu duk wani girkin gidan da gyaran gida ni ke yin don Anty Sadiya tace wa maigidan bazata iya ba ita, Don duk tayi sai ace ba a iya ci, Ya yace ai ba, ance bane don har da ke baki iya ci idan kinyi, Tun da naga sun fara wanan gardaman na mike tsam nabar gurin don bazan tsaya agabana yana wa mace kamar Anty Sadiya fadan girki ba, Wani lokaci kuma yaya zai ce kada na girka komai zai bada take away akawo muna,
Yau ma kamar kullun kasan cewa ranan jumma ,a ce, tun safe na tashi na gyara ko ina na gidan nai muna breakfast lafiyayye, Kafin duk su fito har na gama hada komai, na gyara muna ko ina gidan sai faman kamshi turaren da Maman Bi,u tabani nasa ga yar boner, Cikin wasu fararen material nake masu dan adon silver flowers a jikin su, dinkin dogon rigane har kasa da dogon hannu, sai dan kwalin su dana daura duk da yana sulbewa, Abin da nafara kula dashi, shine yaya Abubakar yajin dadin irin yanayi da yanzu gidan shi yake ciki, Saboda bai iya boye murnan shi da farincikin shi a duk lokacin da yaga ko yaji gidan ya dauki kamshi, Ada na zaci daga shi gar matar duk kaza mai ne tundai irin yadda naga dakin kwanan shi kacakaca, Sai yanzu nagane cewa gyaran guri bana namiji bane aikin mace ce, cikin ma yana kokarin gyarawa ke nan shi, Tun fitowa daga daki na hango, yaya Abubakar acikin annuri , Ga kwar jini kalar nashi da ya kara hasaka shi, yafitar mai da surar shi sosai, Voil ce mai kyau da tsada fara a jikin shi sai kyalli yakeyi, Kokarin zuba kunun kokon da kosai da na dama muna yake yi a cup duk kamshin kosai ya kama dining area din, Fitowa na ke nan daga dakin ina cikin kwalliya bazaka ce nice nai wanan aiyukan ba, Jin karan rufe kofa na yasa shi saurin dago kai yana kallon inda nake tafen, Kunya ne ya kamani saboda irin kallon da yayan nawa ke min don ya ki ko kifta idon shi a kaina, Da sauri na dukar da kaina kasa don kunyar kamani da yai ina mai kallon tantancewa, Anty Sadiya wace take zaune tana dan juya kokon ta a hankali da spoon ta dago ido ta dube shi, Wani irin mamaki da haushin shi ne ya rufe ta wai a ce Abubakar sadaukin da ta sani ne ke irin wanan abin agaban yar karamar yarinya, irina, A gefen shi kadan na dan rusun na ina cewa yaya ina kwana,? Ajiyan zuciya ya sauke tare da cewa lafiya kalau Meenatu, Juyawa nayi da niyar in gaida Anty Sadiya, sai naji muryan yayana yana cewa, Ke yaushe har kika tashi kikayi wanan ai,yukan haka, ne ? Murmushi kawai nai masa ba tare da na bashi ansa ba, Na juya gurin ta na ce ina kwana Anty ? Nasan cewa tun da yaya yana zaune zan samu ta karba min , Inda dai daga ni sai ita ne to ba lalai,ne ta ansa min ba, Yaya Abubakar ya dan motsa kadan daga inda yake zaune, Zauna ki karya ka da, kuma ki tsaya wani aiki har yai sanyi, Da kan shi ya jawo jug din kokon zuwa gabana yana kokarin dauko cup Anty Sadiya ta buga wani tsaki tare da,buga mai harara, Kosai kwara uku ta dauka tare da cup din kokon ta zuwa dakin ta, Batare da kowan mu ya kulata ba mukaci gaba da kwasan breakfast dinmu sai dai gaskiya bazan iya sake jiki na ba, Yaya Abubakar wanda ya tsura min ido yana kallon yadda nake wasa da bakin cup din dake gabana A hankali naji yace, Meenatu , A bazata naji kiran nashi don haka sai na kasa dago kai na in kalle shi, Kaina a kasa na dan ansa cikii,ciki da Na,am,, May yasa baki son cin abinci ne, wai ? Sai a lokacin na dan dago kaina, na kalle shi, Gira ya daga min tare da daure fuskan shi yana cewa, Ko kin fi son idan mutanen gida sun gan ki suce kin ramay sosai, Ga yunwa ga aiki, ? Dagowa nayi da sauri na dube shi don mamaki sai kuma, na dan yi Murmushi tare da girgiza kai na kawai, alaman a,a, Kafin wanin mu yayi magana sai sallama mukaji daga kofan falo, Gaba dayan mu ka juya muna kallon kofan don muga mai muna sallama , Don babu masu shigowa gidan mu saboda masu gidan basu hurda da kowa nake gani, Mace tafara shigowa dauke da yar,ta a hannu ga kuma wani dan namiji yana bin ta, Da mamaki muke kallon ta inda namike tsaye daga inda nakr zaune, Ina cewa Sannun ku da zuwa cikin yar sake fuska, Ganin nayi fara,a yasa matar yin fara,a itama tana cewa ina kwana na ansa cikin harshen mu na sakkwatawa da lahiya lau, Gurin da yaya Abubakar yake zaune ta ke kallo tana ce mai ina kwana,? Ya amsa mata sama,sama da lafiya, Cikin nuna jin kunya da nauyi kanta a kasa take cewa, Ya,ce nace ma wai yana waje, A cikin yar mamaki yaya Abubakar ke cewa wake nan? Batai magana ba sai yar murmushin da tayo kawai, Mikewa yaya yayi zuwa waje don yaga ko waye ke mai sallama, Malam Mudi ne ashe yaron wajen aikin su yaya , Shine yazo da maidakin shi don ta gaida mu, Sun taba zuwa alokacin suna tsohon gida sai Anty Sadiya ta bar su a falo zaune ta shige daki abin ta, A cikin yar fara,a nace mata, ga kujera ku zauna don ban san ko daga ina take ba, A tare da malam Mudi, yaya yashigo gidan, Yana cewa shigo mana ai ban san cewa kasan anguwar ba, Yace ai kwatance malam Abdullahi yai masa, da haka yagane gurin, Shi ne su kazo yi muna barka da jumma,a gurin da nake kokarin fitowa daga daki bayan na saka hijjabi, Suke kallo na a cikin mutumci na gaida shi tare da girmamawa, Zai dan girmay ma yaya Abubakar kadan ga shekaru, Addu,a ya dinga yi yana mai rokan muna zama lafiya tare fatan samun zuri,a masu albarka, Yaya Abubakar ne kawai ke cewa Ameen Ameen, cikon jin dadin addu,an, Anty Sadiya ta fito dakin ta dauke da cup din da tasha kunun a ciki, daga dakin ta Ganin bakin mu yasa ta kallon su a cikin mamaki, tana kokarin tuna kamar ta san su Shiga kitchen, take kokarin yi don aje kayan dake hannun ta, Yar rigar barci ne ajikin ta mai guntun hannu sai zani da ta daura saman rigan, A take naga annurin fuskan yaya Abubakar ya gushe saboda ganin yadda Sadiya ta fito waje ga bako hakans, Ta gane abinda yake nufi don haka naga ta shige kitchen da sauri, Yaya ne ke cewa zasu zauna anan zasu yi ni damu har su dawo gurin aiki, Sosai naji dadin jin yau muna da abokan fira a gidan babu zaman kadai ci yau, Suna fita Anty Sadiya wace ta boye a kitchen don hararan da tasha tai saurin fitowa, Ina kwana matar ke mata amma bata tsaya amsawa ba tashige dakin ta, Kallon matar nayi tàre da kokarin daukan yarinyar ta ina cewa zo mu shiga ciki, Dakina muka shiga ida matar ta fara kallon yadda na dan gyara dakin nawa, Dakin yaba sha,awa sosai don yadda ko ina yake tsab ga kamshi na tashi Kitchen na koma na dauko sauran kosai da kokon na kawo wa yaran tare da sugar, Ina gyara yarinya, na ke cewa ya sunan ki yan mata,? Uwar ce tace min Hanifa don sunan mahaifiyar shi ce, Nace tau na gyarawa yarinyan, rigan ta tare da mika mata kosai guda daga, Tv na kunna masu inda muka kai mbc 3, don yaran su kalli cartoon, Anan gari kuke ne ? Tambayan da nai mata ke nan don mu kauda shirun , Tace eh aida tare muke can Lagos da su sai daga baya, baban su ya dawo nan garin saboda maigidan ga. Amma kinga matan nan kamar bata san mu ba ina gashe ta tana shigewa, Yar dariya nayi ina kokarin zama a bakin gadona, Nace ko dai bata gane ku bane ? Hmm ke ce dai bakuwan ta don bata da hali wanan matar, Murmushi kawai na yi, don ban son muyi zancen ta sam, Don mu kau da maganan sai cewa nayi, kin san kowa da irin halinsa Ita Anty ba mai yawan son hayaniya bace, Kafin tace wani abu sai cewa nayi, Wa yaron ta ya ko in dauko maka ruwa ne kasha, Kun san uwa da dan ta sai murmushin jin dadi, matar ta ke yi, Bayan na gama zance da yaranta ne nadan dago ina dariya Matar tadan dube ni cikin nuna sakewan ta, dani tana cewa, May ye sunan ki ne nace mata Amina, amma Meena ake ce min, A a,a ashe sunan mutanen da ke gare ki ? Nace sunan kwarai mai asali ba, Sunan mahaifiyar Manzo Allah ne fa kin ko ga ba karamin suna bane, Matar tace min nikin ga sunana Hajjara, ke ashe duk mune nace acikin wasa, Nan muka shiga hiran suna yen zamani da kuma irin yadda malamai ke fadakar da mu Musanman mata akan sa sunan da baida ma,ana wa yaran su, Daga mace taji suna tana sha,awan shi kawai sai ta sawa yaron ta batare da sanin ma,anar shi ba, Kosan da na ajewa yaran ta takai guda abaki tace amma kuna da masu kosan kwairai a unguwar nan, Ai bana sayarwa bane nafada mata cikin murmushi, Da sauri ta dago kai tana min kallon mamaki jin cewa wai nice nayi, Nake fada mata cewa ai da blender nai amfani na markaden tankwa shi yasa yai lau,shi da kyau, Gaskiya kin yi kokari, don kin ga zaman birni irin Abuja ba wani abincin irin na gida mutum ke samun yi ba, Nace mata, amma ai sai in mace bataso sarrafa abincin ba ko Kinga ai shinkafa zaki iya, sarrafata kamar yin dambu, fate, tuwo dafaduka shinkafa da wake, waina, sai da miya kamar yadda akasarin mata sukagi yi, Wake kuma zaki iya yin faten wake, alale, dan wake da maida yaji, tubani, da sauran su, Ka,fin,in ce wani abu maman Hanifa tace min wai amma gurin tsohuwa kika tashi ko, Dariya tabani sosai nace acikin dariya maman Hanifa sai ka tashi gurin tsofi zaka iya girkin gargajiya, ? Yar ta da ke kuka tana son shan mama ta dan jawo zuwa jikin ta tana kokarin bude riga ta, Tacewa kin san ko wasu uwayen namu ba damuwa sukayi da su koyar da girkin ba, Nai dariya nace mata zama a cikin babban gida yasani iya girkin gargajiya, Girkin zamani kuma a wajen anty amarya na koyi yin su,,,