Tarko complete novel - Chapter 50
Tarko complete novel Chapter 50: Tarko complete novel Chapter 50. ****** ********** ****** Zaune take a falo tun lokacin da taji fitan maigidan Idan ba…
3,309 words
****** ********** ****** Zaune take a falo tun lokacin da taji fitan maigidan Idan ba karya zuciyar ta ke mata ba tana iya cewa yau tun safe ban fito daga part din Yaya Abubakar ba, Hakan ne ya bata daman ya kewa a zuciyan ta cewa ta tashi ta leka dakin Yaya Abubakar tagani, A kwance ta hangoni nadunkule guri guda ina barci, abina hankali kwance, Ta dade tana kallon zuciyar ta na kiyas ta mata abubuwa da dama akaina, Gyara kwanciyar da nayi yasa ta saurin ja da baya da sauri tasake labulen kofan tabar gurin, Tun kagin ta karasa saukowa daga stairs din ta hango Ramatu tafito daga dakin Anty Sadiya, Tana saye acikin hijab din ta har kasa tana dauke da flask din ruwan zafi a hannunta, Ganin ta doshi hanyar kitchen yasa Salawatu wani irin daka mata tsawa,, Ke dakata lafiya ina zaki shiga wa mutane haka ? Daga ina kike ne ma wai ? Ramatu wacce tsawan Salawatu yadan sata yar kaduwa tajuyo tana kare tamata kallo, Akaron farko da tafara ganin ta ke nan a gidan tun shigowanta jiya, Cikin dan rusunnawa tace, hajiya ina kwana ? Ya aiyuka, Kalafiya ta karba da cewa tare da watsa mata wani irin kallon rainin hankali na ke wacece, Daga ina kike na haka ? Cikin wani irin kallon tun daga sama har kasan ta, Ramatu tace daga sashen wacan Hajiya da bata da lafiya nice wace aka kawo don in dinga taimaka mata, Sai da tai mata wani kallon rainin wayo har zuwa kasa tace, Uummww kece dai mai kwadai da bata san ciwon kanta ba ko yan uwanta suna gudun ta ke don kwaidai kin zo kin tara ko ? Murmushi Ramatu tayi tace, ai taimako ne hajiya babu abinda zai faru insha Allah, Daga haka Salawatu ta,watso mata harara cikin kallon ke kika sani tajuya fuuu ta shige part din ta, Ramatu tabi ta da kallon mamaki har shigewan ta cikki ta kada kai tana cewa akwai magana ke nan a gidan nan suna da tantiriya, ashe, agidan haka ?
****** ********** ****** Hasken rana ne ya hasko min fuska na daga window dakin ta baya, Abinda ya sani bude idona kenan nauyi naji jikina yayi sosai , Sai daga baya nagane cewa ina dakin Yaya Abubakar ne har wanan lokacin, A hankali na yunkura na mike zaune nadan dade a zaune bakin gado kafin na yunkura namike tare da tattara duk kayayakina zuwa kasa part dina, A hankali na tako zuwa kasa inda na hadu da Ramatu ta dauko ruwan zafin da ta dafa , Tana ganina ta tsaya tana cewa sannu uwar daki na ashe yau kuma jikin ya tabu ne haka, Alhaji ne ke fada muna dazun da zai fita yace baki barci da dadi ba daren jiya, Nadam lumshe ido alamar ciwo nace ai naji sauki sosai, jikin dai ne ba karfi, Ta dan kauce min kadan duk da ba ko a kusa muke ba amma saboda girmamawa ta dan kauce gefe, guda, Ina shiga daki na fada saman gadona tare da lumshe idanuwa na Zuwa can na sauke ajiyan zuciya tare da bude idona, Sallaman Ramatu naji adakin nawa tana cewz ko akwai abinda zan taimaka maki dashine Hajiya, Cikin dan lumshe ido nace yuwan nake ji sosai wallahi, Tace ko may zaki ci yanzu nace ko tea ne ki hada min don Allah, Fitan ta don zuwa hado min tea din yai daidai da kiran wayan yaya Abubakar, Nadauka a hankali da cewa Sallamu Alaikum cikin yar siriri yan murya,, Muryan shi yana cewa Meenat kin tashi yaya jikin naki ne ? Na lumshe ido na tankar yana kusa dani don jin muryan shi da ya daji kunnuwa na, Nace eh yaya naji sauki ai, Kin sauko ne ko kina kwance har yanzu sama, nace ina daki na kwance ne zan sha tea ina jin yunwa ne sosai, Yace A,a wanan jin yuwa fa Meenat kamar mai Ulcer ? Murmushi nayi batare da na bashi ansa ba, nace hmmm kawai cikin lumshe ido, Bayan nasha tea din da Ramatu ta hado min nasha, Sai wani irin zufa ya fara karyo min duk jikina ta ko ina inajin wani irin zafi, Don haka na fada bathroom na watsa ruwan don inji dama ajikina, Bayan fitowan na ne na dan ji karfin jikina ba kamar yadda na tashi ba don haka na dan jawo wani dogon riga jallabiya na saka ajikina. Cikin daurewa na nufi dakin Anty Sadiya, don in duba lafiyan ta, Nasamu Ramatu tana hada mata abinci zata ci, da kuma dan gyara mata filo, Mungaisa da ita ina mai kallon hannuwa ta yau gaskiya babu laifi don hannu ya tsane sosai ba kamar baya ba, Nace cikin murya ta kasala anty ya jikin ta amsa cikin wani kushe fusaka da cewa, Da sauki yaya naki jikin dazu yake fadamin cewa wai daren jiya bakuyi barci ba, Nace cikin murmushin karfin hali wallahi fever ne ya kamani acikin dare mai karfi amma naji sauki ai yanzu sosai, Jikin nawane kawai nake jin shi wani iri kamar ba nawa ba, Tace Allah ya sauwaka na ansa da fadar amin tare da kurawa hannuwanta ido ina kallon su, Munyi shiru can take cewa wai ko matar gidan nan tana nan kuwa, Ban yi saurin kawo watake nufi ba don sai ina kallon ta ina mamaren kowa cece bayan ita, Sai Ramatuce ke cewa Hajiya aini dazun tabani tsoro sosai don yadda muka kwasa da ita da safe, Sai nagane cewa Salawatu take nufi nace tana nan mana , Anty Sadiya tace wai ciki gare ta maigidan ke fada jiya yana cewa wai kwanan duk bata jin dadi saboda duk abinda taci sai ta dinga jin tashin zuciya, Gabana ya fadi inda na tuna cewa cikin da ya zube min fa hakana nadinga amai alokacin shigar shi, Kardai ace jiya jiya da fara karban girkina har na dauki wani cikin nafara laulayi haka da sauri, Muryan Sadiya ce ke cewa, ai ni wanan matar ban dauke ta acikin masu hankali ba sam, Murmushi nayi ina mamaki araina irin mugu kishin dake a tsakanin anty da Salawatu, A raina nace aiko ni ban tsiraba kenan don nima aikishiyace, Namike batare da nakara cewa kallaba adakin ina cewa zandan tafi in kwanta, kadan, Daga haka nasa kai nabar dakin na nufi part dina, Nasamu misscalled din yaya Abubakar har biyu ban bata lokaci ba gurin kiran shi, Najiya nacewa ina kika shigane tun dazun baki dauki waya ba haka, Nace natafi gaida Anty Sadiya ce nabae wayan adaki , Yace alright, Yajikin naki yanzu I hope baki kara aman ba dai ko zuwa yanzu ? Nace bankara ba yaya naji sauki ai sosai don banajin komai yanzu, Amsa da cewa masha Allah may kikeso azo maku dashi, nace a hankali babu komai yaya, Hmmm kawai yace baikara cewa komai ba naji ya kashe wayan nashi, Nima nasaka tawa wayan a caji na dan saya kofar dakina na kwanta atake barci yai gaba dani,,,,
ZEEE MAKAWA YELWA 🕸🕸🕸TARKO🕸🕸🕸 🕸🕸🕸🕸🕸🕸 6⃣4⃣
ZAINAB IDRIS MAKAWA
ALLAH- AL-WAKEEL,,,
Don Allah ina neman addu,an ku gareni nafatan alheri ga abinda nasa gabana, Ya Allah kataimaki boyar ka Zainab kaba ta miji nagari mai mutun ci da sanin ya kamata,,,, Allahuma Ameeen Allah
Tun ranan da nai wanan ciwon sai na samu sauki sai abinda na lura dashi yanzu ina yawan yin zazabin dare, Sai dai kusan asuba sai kuma Allah ya kawo min sauki,, Don haka sai ban wani yawan damuwa da hakan sai ina ganin ai fever ne kawai,, Sai kuma nadawo da shan ruwan Lipton dina kamar farko, Anty Amarya nakira ina sheda mata irin halin yanayin da nake ciki yanzu, Cikin tausa murya tankar wani yana kusa da ita, tace, Shin Meenat ko dai cikin ki dama bai zube ba na ? Nace nima a hankali walle ban sani ba Anty ko bai zube ba , Tace kai duk yadda akanyi cikin nan yana nan jikin ki ki la dai bleeding na kawai kin kayi kwana ki, Tace shin ke san wani abu yanzu nace a,a anty ta ja bakin ki dai kiyi shiru don kesan halin bakar mugunyar kishiyar ki, bata da kyaun hali, Don haka kiyi shiru dai kar ki bari har shi maigidan yasan da zancen ki, Na amsa da fadar cewa to anty , Anty Amarya tace Allah dai yasa cikin nan baizube ba ma muga tsiya gurin munafukar kishiyar ki, Nace, Anty ai itama ciki ne da ita a yanzu haka sai fama shagwaba takeyi wa mijin ta, Tsuki mai kara sosai Anty tayi don jin haushin zancen, Tace wanan makira kilama karya takeyi wallahi yanzu haka kira ma makirci ne irin na tsufin mata, Mun dan dauki lokaci muna hiran da ita tana fada min yadda zanyi, Don tana bukatar in jagulawa Salawatu rayuwa ta yadda batai tsan mani ba daga gare ni,,,, ****** ********** ****** Kamar yadda Anty Amarya tace min in kauda komai a zuciya na in yi haka din nayi kuwa,, Don gaba daya ,nima yanzu na sake ma Salawatu , don ina gwada mata cewa nima fa A, ce, A kwance nake kasa dakina saman ties saboda inajin dadin irin sanyin dake fitowa daga kasan ties din, Ban san shigowan Yaya Abubakar a dakin nawa ba sai dai ganin shi nayi a gabana, Yadan dauki lokaci a tsaye gabana yana kare min kallo, cikin wani irin yanayi, Ganin shi tsaye a kaina yasani kokarin mikewa zaune daga kwancen da nake, Muryan shi naji yana cewa No kwanta abinki kawai, Sai ya duko ya tsugun na agaba da fuska na har muna iya jin numfashin junan mu, Cikin wani irin kallon sha,awa yake ce wa may yasa may ki kika kwanta haka a kasa, Duk da ba dadi nake ji a jikin na wa ba sai nayi kokarin kirikiro murmushin dole nace, Kawai dai na kwantane in dan huta don zaman haka ya ishe ni, Yaya Abubakar yace amma jikin ki kamar mara lafiya tare da kai hannun shi ajikina yana dan tabawa, Nace lafiya na kalau Yaya bandai gama walwarewa banre kawai, daga rashin lafiyan da nayi, Yai dan shiru can yana kokarin mikewa daga tsaye yake cewa,munyi waya da malam tsoho dazun yake tambayana ke, Murmushi na sake tare da kokarin mikewa daga zaune nace,, Allah sarki suna lafiya ko ? A gaban mirror dina ya tsaya ya dan jingina jikin shi da katakon mirror, yace, Autan shi wai yake tambaya yaushe ne zai dawo nake ce mai aikece kika tsaida shi, anan, Na dan langabe kaina nace cikin shagwaba yaya kada kasa malam ya rikeni fa, Duk wanda ya tambaya ina Wadsa sai yace ai yana wurin Meenatu Abuja, Lokacin da yaya yadago a mirror ya ke cewa kinga sai mutane suce ai yar tashi ta kosa, Kaina na kara langabewa cikin tausa murya kamar wata karamar yarinya nace hai ,Yaya , Zai fita daga dakin yake cewa zan shiga wanka yau a fito falo please ?
Salawatu wace ke labe daga kofan daki tana sauraren mu da leke, saboda wai bata san may yasa yake yawan dadewa a dakina ba, Tai sauri tabar gurin zuwa can kasa stairs din part din shi tankar mai neman wani abu a gurin, Shiko yana fitowa ya na fitowa bai tsaya bata lokaci ba kawai ya haura sama abin shi,
****** ********* ****** Abin duniya ya taru yaiwa Hajja katutu azuciyar ta da fili saboda yadda Dodo yanzu al,amarin nashi duk ya riki ce mata, Ko ita kadai ce a zaune sai ta fara surutu kamar ta baba, Sai tai ta faman diban ruwa zuwa, cikin dakin da ta aje Dodon nata, Gashi yanzu sai take gani ai duk abin duniyar da ta tara kamar a ana zuke su ne, Ita dai ba tabasu takeyi ba don bata yarda tayi asaran kwandala daga kudin ta,, Bata sadaka bata kyauta bata hasara balle don Allah yi hakkuri, indan an mata barna, Don haka ta dauki alwashin sai ta ga bayan duk wani wanda ya ke kokarin kashe mata Dodon ta, Yanzu abubuwa take yankawa agidan ta tana ba mutane sadakar nama amma babu masu karban sadakan a shiyan nasu, Sai tai dabaran kawai wani uguwa don ita kawai, bukatan ta shine tayi yankan dabba da sunan zata bawa Dodon ta jini Da ta nasa hakan duk gurin da tai yankan daniyar haka jinin zai samay shi, yasha don samun waraka,,, Daga haka tasamu har ya dan samu sauki daga saluntar da jikin shi keyi don tabashin da akayi, Gashi kuma bokanta yai mata nisa yanzu ba kamar da farko a lokacin da yake a gari ba,,
****** ********** ****** Kaina da yasha gyara gurin Antyn Saloon na daura mai ribbon har gida uku, Wando tree quarter nasa tare da wani dan farin riga iya kuguna ,sai kamshi da na shafa ta ko ina ajikina, Yanzu na tabbatar da cewa, Baba Wadda ya bar falon namu saboda bai faye dadewa ba a gida da dare yana zuwa gurin fira tare da,su Baba Hamza,, don yace yafi son ya sauka a gidan su maman Biu,, Yaya Abubakar yana zaune a falon fuskan shi da hankalin shi yana saman system din shi, Takalmin da ke a kafa na suke kara kwas, kwas kwas, Anty Saloon ce ta sayar min dasu da naje gun wanki kai, Abinda yasa Yaya,Abubakar dago kai daga abinda yake yi a cikin system din shi, Salawatu wace ke daga kwance saman kujera two seaters, ta dago kai da sauri don ganin ko wacece, shigowa a lokacin saboda sam batai zaton haka ba Daga inda nake ina kallon yadda take taunar chewing gun kamar a solow, Ga duk rabin yan shamukkakun nonon ta a waje, Wai ita adole tasa rigan daukan hankalin maigida a dole,,, Ido Yaya Abubakar ya sako min tare da dan susucewa,, ga mi da barin abinda ya keyi, A hankali na karasa isowa gurin shi ina dan tsotson lollipop din dake a hannu na hankali, kamar wata Baby Gefen kujerar shi na zauna daidai saitin kafan shi, tare da cewa acikin wata zakkakan murya nace Yaya ina wuni ? Ina jin lokacin da, yai firgigit, tare, da wani irin ajiyan zuciya a hankali, Yace Meena yaya gajiya ? Ido na lumshe tare da yin wani har dasu nace akwai shi gaskiya yaya, Salawatu daga gurin da take a kwance cikin wani irin murya mai kama da mara lafiya,tace, dear yau ina son shan shawarma, Yaya Abubakar ya dubi time yace may yasa baki fada ba tun dazu sai yanzu, Tace yanzun ne ai shan shi yazo min a rai duk wani iri nake ji kamar zanyi amai, takara fadi a cikin shagwaba, A hankali na yunkura daniyar mikewa saboda bani bukatar yafita yabar ni da ita a falon mu biyu, Nace Yaya, don Allah idan ka fita ka taimakamin da Ice cream da fresh fruits please,,, Daga haka kawai na mike zuwa part dina cikin tako irin na jan aji,,, Daga gurin da Salawatu take a kwance tace zakici uban ki yar iskan yarinya, kawai, Sai nayi magani wanan shegeyar yarinyar mara kunya kawai, Unlucky Yaya Abubakar bai samu sakon Salawatu ba amma sai gashi da sakona niki niki a leda, Ina zaune bakin gado dagani sai daurin zani a gaba ina kokarin saka rigar barcina ajikina, Yashigo dakin bakin shi dauke da sallama yana mai kura min ido, Yace adaidai lokacin da yake aje ledan hannun shi a gefen gadona, Har zaki kwanta ke nan yanzu ? Nace, Yaya na gajine ina son indan kwanta in huta ne, wallahi, Yace Oya tashi kisha Ice cream, din kafin ya narke, uana kokarin bude ledan da ya shigo dashi dakin a lokacin, Roban Ice cream din ya dauko min yana kokarin budewa, ina kallon shi har sai da ya bude, yamiko min nakarba tare da fadar nagode yaya, Godiyan yai masa dadi sosai irin yadda naga ya lumshe idanuwan shi, yana murmushi, Abinda rai ke so a take na fara shan Ice, cream din kamar mayunwaciya, Irin yadda nake sha babu kakautawa yasa shi kura min ido acikin mamaki, Muryan Yaya Abubakar da samun Ice cream yasa na manta cewa yana dakin tsaye ya harde hannayen shi, guri guda ya kuramin ido yana gani irin yadda nake haukan sha, Yace haba Meenat yanzu kina son wanan abin haka kika kasa fada min, indinga sayo maki, Ya kamata ace kin saki jiki dani zuwa yanzu ace nasan bukatar ki, Don kada ki dinga sa ina zaluntar ki haka dubi yadda kike shan abu tankar mayunwaciya, Cikin shagwaba nace ni yaya ban san yadda zance a dinga sayo min abuba haka ni kadai, Sai inga cewa baka sayo wa sauran yan uwa na ba ai, gara sai a,sayo muna gaba dayan mu, Yai murmushi yace aikuwa kowace da abinda takance azo mata dashi, wanan ai abin ra,ayi ne , Don kinga ita Salawa ai abinda tace tana bukatar a sayo mata ko ? Yafara tafiya yake cewa ashe shiyasa kika kasa tuna min da zancen lefen ki da na manta banyi maki ba ko ? Murmushi nayi tare da dukar da kaina ina man cigaba da shan Ice cream dina sai dai wanan karon a hankali na fara sha, Yana mai dafa kofan gita dakina yake cewa kiyi hakkuri please wallah mantawa na shap da zance, Amma yanzu na bada sako a kasar Dubai za a hado maki duk abinda ya kamata, Kuma nasan cewa Anty Amarya zasu ga cewa kawai dai banda niyar maki ne shiyasa na share zancen,, Nace cikin kada kai gaskiya wallahi Yaya banta ba jin wanda yai wanan zancen ba, Yace ok hakan yayi yanzu dai ai zasu ga kayan ya riske su girshi ko ? Bugon kofan da Salawa takeyi tare da kwada Sallama da karfi yasa shi yin shiru, A zuciye yace, wai waye wai ta karba daga kofa da cewa Nice, Bai fita daga dakin ba sai daga labulr da yayi ta yadda zata iya hangoni, daga inda nake zaune, ina shan Ice cream di na, Yana bude labulen na hango Salawatu a tsaye cikin masifa, Ta zuba mai wani irin uban harara, tare da jefan sa da wani irin mugun kallo Mai cike da zargi akan yadda ta han goni daga bakin gado a zaune , Yaya Abubakar ya hade, ran shi yana mata wani irin duba yace Lafiya haka,? Ta wani ya mutsa fuska tace naga dawo wanka tun dazu kuma banga sakon nawa har yanzu,, Ya kara daure fuska yace tun da ni yaron aiken ki ne shine kika kasa hakkuri har izo in samay ki, Salawatu ta fahinci yanayin da Yaya Abubakar ya nuna mata na bacin ran shi, Watau ma yana nufin cewa tazo tana damuwar shi ke nan ko ? Saboda iya mu,amulan salawatu da maza zata iya gane k irin halin da namiji ke ciki tundai mashi da take mutuwar so, Wani irin kishine da bakin ciki suka ziyarci zuciyan ta Idanun ta suka canza launi a lokaci guda tare jin wani irin haushi da takaici, Ta tabe baki tace, duk dai abinda, mutum yayi ai Allah yana ganin sa, Yaya Abubakar, yasaki wani murmushin takaici yace, Idan zaki iya jiran inzo sai ki jirani idan bazaki iyaba kuma sai ki shigo ko ? Ta tabaki ta juya acikin bacin rai zuwa tsakiyan falo zuciyan ta tankar ya buga, saboda wani irin bakin kishi da ke cin ta,, Bayan ta ya bi da kallo a hasale yana maigirgiza kan sa a cikin takaici tare da yin tsuki, Ya juyo yana fuskanta ta na dukar da kaina da sauri naci gaba da shan Ice dina, Sai da ya dan dauki dan lokaci kadan a dakin nawa duk da ba komai yake yi ba inba wayan shi da yake ta faman dakila ba, sanan ya fito, yana mai min sai da safe,