Tarko complete novel - Chapter 6
Tarko complete novel Chapter 6: Tarko complete novel Chapter 6. *** *** *** *** Wanan ne karon ne farkon shigowar ta garin sokoto, iyakarta birnin kebbi…
3,334 words
*** *** *** *** Wanan ne karon ne farkon shigowar ta garin sokoto, iyakarta birnin kebbi sai ko gwandu ko kalgo gurin gwagon ta, Hakan yasa tun shigowar ta take raraba ido gurin kallon yanayin garin, Gidan dan uwar mahaiyarta Baba ya fara kai ta don ta san guri, Malam Nafi,u malamin asibiti a cikin garin sokoto, yake aiki, Yana da mata guda biyu da yara biyar, yana da dan rufin asirin shi, gwargwadon kima, A gidan Baba zaibar Meenat yadda su ka yanke shawara cewa shi uncle Nafi,u ne zai kai ta idan weekend ya kare,,, Ameenat tana tsaye kofan gidan uncle dauke da dan karamin yaron amaryan shi na goye, Ida tayo wa mahaifinta rakiya don ya ce bazai kwana ba ranan zai koma gida, Baba ya,ce tau, Amina ki kasance da halinki nagari da nasan ki dashi, Nakawo nan karatune don ci gaban ki duk da dai kin ga malam ba wai yaso hakan bane, Don Allah ki rike mutuncin ki, Ki rike ibada ki tuna da irin gidan da ki kafito kada ki sawa, zuciyan ki kwadan duniya ko kadan, Ki jira rabon ki don rabon mutum bai taba wuce shi, inji Allah, Nan da nan idon Meena ya kawo hawaye amma sai ta wayan,ce da sherewa da bayan hannun ta,, Ga wanan mahaifiyar ki nan duk abinda ya shige maki duhu ki sanar dashi don zai aiko min insha Allah, Nabar ku lafiya Allah ya bada sa,a yasa a dace duniya da lahira , Wani irin kuka ne yazowa Meenat duk yadda take son zuwa boarding da kuma sokoto sai taji yau bata so kwata,kwata, Kasan cewar yaune rana na farko da ta taba barin iyayyen ta zuwa wani gurin,, Tayi da ta sani da ma ba,ta,zo ba ta,zauna gida tare da mahaifanta da yan uwan ta,, Cikin gida takoma inda ta zauna folo don babu dakin wace zatace zata nufa daga cikin matan uncle din nata,, Har kayan ta duk a nan suka bar mata su afolon gidan nasu, Wanan bai hana Meenat mikewa don zuwa tattara kwanon da akaci abinci ta fara wankewa,,, Tare da ita ranan uwargidan tai girki don kusan aikin Meenat ce tayi shi don ta iya,,, Dan kwana biyun da Meenat tayi a gidan uncle din ta yasa amaryan shi Sakinat ta ja Meena ajiki don ta fahinci yarinyace wace bata son jikin ta, Ranan da za,a kai Meenat makaranta uncle Shafi,u ya dan kara mata sayayyan provision masu dan yawa da dai yan sauran abinda zata bukata wanda Baba bai sayo mata ba,
*** *** ***
Tun tafiyan Meenat sokoto Baba suke wasan boya da malam mahaifin shi, Da zaran anyi sallah asuba Baba ya fita bai,dawo,wa gida sai dare lokacin malam ya shige gida, Saboda tsoron haduwar su da malam din,wanda bai so tafiyan maryam karatu har wani gari ba, Sati guda cif da tafiyan Meenat ranan Baba yadawo daga gurin neman kudin shi da yake yar buga bugan shi, Baba Buhari ya tsayar dashi a kofan gida yana mai nasihan cewa ya tafi ya gaida malam don kwana biyu ke nan yana jin yana tambayar shi, Jikin Baba samaila yai sanyi don haka ya yanke shawaran shiga gurin malam din yau, Baba samaila bai yi sanyi a gwiwa ba yana gama gyara jikin shi ko abinci bai tsaya ci ba ya nufi sashen mahaifin shi, Bayan sun gaisa sai yar shiru ya biyo baya kadan, Muryan malam ce ta ratsa shirun da cewa Samaila guduna kakeyi kwanan nan ko don nace kada ka kai yar karatu wani gari, Baba samaila yadan gyara zaman shi cikin ladabi yace ba hakana bane malam aiyukane sukai min yawa shinassa, Murmushi malam ya yi tare da girgiza kan shi, yace, Duk da na san cewa yanzu zamani yana tafiya,ne da ilimin zamanin, To amma ita diya mace tarbiyan ta sai iyayen ta sune zasu tarbiyar da abin,su yadda ya kamata, To amma naso ace ka kalli lamarin ta fuska biyu, addini da kuma zamani, Don haka na kyale kane kawai don da gida biyu aka sanshi dama , Saboda kace gurin wan mahaifiyar ta zata zauna don yana garin, Don haka na kyale ka ka tafi da ita amma nan gaba ban son gardama akan diyan ku,, Baba Samaila yace a yi hakkuri malam baza,a sake ba insha Allah,,, Bakomai inji malam ai Ameena yarinya ce mai natsuwa da hakkuri Allah ya bada sa,a ,,,,,
*** *** ***
Yau Monday, ma,aikatar su Abubakar sun bude Monday su da, transfer a hannayen su, Wada daga ciki su har da Abubakar wanda ya samu karin girman bazata, saboda kwazon shi ga aiki, Gashi kuma an turo shi Abuja , babban headquarter su da ke can, da zama,,, Sosai sauran abokan aikin shi musaman hausawa suka fara farin ciki wani hanya kuma suna bakin ciki rabuwa da mutum kamili irin Abubakar din, Inda ba bata lokaci suka yai haraman zuwa yin reporting,
*** *** *** Mama Ladi ne zaune daki da yaranta mata biyu da ke aure a cikin gari, Bukin suna akeyi a gidan can sashen baba su, guda, Mama Ladi ce ke magana, da yaran nata alokacin, Inda babban yar ta ta kawo zancen, dan uwan su Abubakar da cewa, Mama yanzu shi mai sunan malam haka zai zauna da mace bata haihuwa kuma bai damu ba, ? Cikin Fushi mama Ladi tace wa yar nata, shi da ke zama da ita ya ce maki yagaji da hakan ne, Binta wace itace ke bi wa Abubakar gurin haihuwa tace, Cikin murmushi, haba mama ke dai baki son sam ayi zancen wanan matar ta mai sunan malam, Mace sai dan banzan tsiwa, taurin kai da nakasa ga kekessasshiyar zuciya da rashin sanin ciwon kai, Idan Baba Wada yana bada labarin ta wallahi mama kare bai ja, Mama kin san fa shi ba wai zai taba zuwa gida ya fadi irin halin rayuwan da yake ciki da ita bane, Tafarkon mai suna maryam tace, nidai wallahi mama ke ce mai son wanan hadin tun farko, Don dai wallahi Abubakar bai dace da wanan matar ba sam,, Shin wai ina ruwanku da wanan zance ita naga ta dace da shi shiya sa na hada su, Shikuma Wada dama munafunci ya tafi yi shi yasa bai fadawa kowa ba lokacin da zai tafi, don da ban yarda ba, Gaba dayan su suka yi shiru da bakin su, don sun san cewa Sadiya bata taba baki a gurin maman su,,, Maryam ce tace ai Samira tana can zamu ji komai abakinta idan ta dawo,,,
*** *** ***
Saye yake cikin bakaken suit, kai tsaye ya ke tafiyan shi mai kama da ta kasaita da isa, Yana rike da wayar shi a hannun shi na dama sai briefcase din da ya rika a hannu guda, Idon shi ya na manne da farin glass mai kama da medicated, Tun daga nesa mutanen da ke zirga,zirga a maikatar suke satan kallon shi,, Kallo guda za kai mashi ka gano cewa namiji ne jan gwarzo don a cikin azama yake tafiyan shi,,, Office din shugaban su ya nufa kai tsaye tare da taimakon wani lebura, Abdullahi wanda suka hadu tun a bakin get, Abubakar ya yaba kwarai da kyawon gurin inda, girman gurin da kuma yawan ma,aikata yasashi gane cewa ba karamin guri yazo ba yanzu, Office din shi babban fiye da tsan manin shi don kusan ya kai wani taki mai tsawo, Bai wani tsaya bata lokaci ba don dama shi mutum ne mai kwazo ga aiki, Farin jinin jama,a ke gareshi duk inda yake to amma kuma gashi shi mutum ne wanda baida surutu,,
Meenat yarinya mai hazaka inda ta hadu da wata Yarinya, Aisha,yar kauyen, sokoto Bodinga,, Meenat da Aisha sunyi mugun shakuwa a tare su ke komai nasu, kasancewan a rana guda aka kawosu makarantan, A haka rayuwan su yaci gaba da kasancewa a tare da junan su, Kokarin Meenat yasa aka santa cikin dan lokaci don duk wani abinda za,ayi a makarantar na kokarin, da ita a ciki, Wanan ne yasa mata farin jini gurin yan uwanta dalibai da malaman su, Baba yana yawan ziyaranta inda in yazo Meenat, zata dinga jawo mutane azo aga mahaifin ta, Shiko Baba samaila yanajin dadin hakan da yar na shi take yi mai a cikin yan uwanta, Saboda gudun surutu yasa idan an samu hutu mai gajeren zango Meenat bata zuwa birnin kebbi, Saidai idan dogon zango ne takan je tayi hutu a cikin yan uwanta,,,,
*** *** *** Mama Ladi wace tun ganin yadda Meena ta koma da tazo hutu sai hankalinta ya tashi, Amma a fili sai cewa take yi sokoto fa kawai mutum ya tafi amma daga uwa har uba duk sun rude sunawa mutane wani zance wai diyar su na karatu sokoto, Wanan irin abin da, mama ke yi duk wanda yasan yadda matan wanan shiyan suke, ba wani bakon alamari ba ne wanan, Don haka abinta sam bai damu Zurian Baba Samaila, Ita mama Ladi bawai Baba samaila take wa wanan kyashin ba kowa ne na gidan idan taga mai da alamar dan haskawa, To fa da ita da mai shi kwana biyu sai anji su don sai sanadin da tai fada da mutum tai mai gori,,
*** *** *** Salawatu wata matashiya ce ma aikaciya a ma,aikatan su Abubakar, Fittaciya ce agurin aman tana yawan ji da kan,ta gata yar gaye irin na karshen nan, Tana duke saman computer dake a gaban ta tana aiki, Muryan aminiyar ta kuma babban kawar ta, lubana, taji tana cewa kai, Amma wanan gayen karshe ke nan bai da inda yake da makusa, Ji tafiyan shima kawai don Allah, A hankali Salawatu ta dago kan ta daga abinda takeyi, Gaban ta ne ya ba da ras don ganin irin haduwar da guy din yayi,, Amma dai wanan bako ne ko ? Salawatu ce ke tambayar, Lubana ta bata ansa da cewa shine mana aka cenza mai,makon Emos,, Da mamaki suke kallon Abubakar har ya karaso inda suke ya wuce, Bayan shi suka bi gaba daya da kallo a lokaci guda, suna, mamakin halittan shi, Don dai su ya yi masu a rayuwan su sai dai matsala guda shine da alama baida sakin fuska, Salawatu tace Lubuna ki sa aranki daga yau cewa kamar na samo kan shi na gama, ko, Amma fa ni abinda na hango Salawatu kamar wanan bazai wani girmay ki sosai ba, And so what ? Ta fada cikin wani irin yin har da idon ta, Shine ma ai daidai move, di na, idan baki sani ba, A cikin hausan na yan yaren garin Abuja suke magana,
*** *** *** Tun daga wanan ranan Salawatu ta fara shi,shigewa Abubakar, da gaisuwa ta fara mashi a cikin ladabi, Sai kuma ta fara dan canza shigar ta irin na yaran hausawa ainihi,,, Duk yadda tasan za tayi su hadu a rana sai Salawatu tayi don su hadu, da Abubakar , Sadiya da Samira duk sun dawo nan Abuja yanzu tare da shi, Inda ma,aikatar su, ta bashi gida maikyau ga kuma girma sai dai ba,a cikin kwatas din su bane, Sadiya yanzu da yake andawo arewa tana dan ganin yadda mata ke gyara , Hakan yasa ta itama tadan fara gyaran jikin ta amma sama,sama,,,,,, Yanayi yanzu ya canza sosai don cigaba ya samu sosai gurin Abubakar, Bin kwakwafi irin na Salawatu har saida ta gane gidan Abubakar, Da sannu har ta dan fara kaiwa matar shi sadiya ziyara agida,,,,,
ZEEE MAKAWA YELWA 🕸🕸🕸TARKO🕸🕸🕸 🕸🕸🕸🕸🕸🕸 1⃣0⃣
ZAINAB IDRIS MAKAWA
SIRAATAL- LAZEENA AN'AMTA `ALAIHIM,GHAYRIL-MAGHDOOBI `ALAIHIM WALAD-DA,AALLEEN (AMEEN)
AFUWAN YAN UWA A POST DIN JIYA PLS GYARAN KU A GARENI YA NA KARA MIN KARFI DA KWAZO A KO DA YAU,SHE NAGODE KWARAI DA KULAWAN KU,,,,,,,
A, zaune yake cikin office din shi wanda yasha kayan electronic din ma,aikata, Kan shi a duke yana faman aikin tun safe baida lokacin kan shi idan har yana office, din, Hakan ya sa ba kowa ne yasan da shi ba a ma,aikatan, nasu saboda girman gurin,, Abubakar yana hankalce da irin harin da matan ma,aikatan ke kawo mashi, Sai dai yakan gwada masu tankar bai fahinci manufar su ba,,, Don shi ko a gida bai faye son hulda da yan uwan shi mata ba, Don a ganin Abubakar sakewa mace fuska raini ne hakan ke jawo wa mutum so,sai,,, Hakan ya sa duk wata mace wace ta san ko waye Abubakar za ta shede shi da cewa mutum ne mai wulakanci sosai, Don abin ya zama mai jiki irin tsare gidan shi ba mata ba kawai har ma mazan,
Tafiya, yake kamar mai hanzari, hannun shi guda saye a cikin Aljihun shi, hanyar zuwa, gurin saida abincin ma,aikatar nasu ya nufa, Ba kasafai zaka ga Abubakar a wanan gurin ba, Iya karshi, indan harka ganshi drink ne kawai zai sha sai snacks wani lokaci Sauri ya ke yi don ya karasa gurin saboda yunwa yakeji gashi kuma da aiki a office da yawa, Tun daga nesa,suka hango shi, a lokacin ita salawatu ta juya bayan ta tana waya, Ta,bota Lubuna tayi da dan yatsunta ta na gwada mata shi, Cikin sauri Salawatu ta juyo don idon ta ya gane mata shi , Shigan shi cikin restaurant din masu aikin gurin ya samay shi don jin ko may zai kawo mai, A daidai wanan lokacin Salawatu suka karasa karasowa gurin ita da Lubuna, Cikin wani, ladabi, na kissa suke gaishe shi harda dan rusun nawa, Sir inji Salawatu, ya mutanen gida ? Cikin mamaki yadan dago kai don jin abinda ta fada , Sai,dai yana mamaki wasu mutanen gida ne ta sani har take tambayar shi, Mamaki a fuskan shi karara yadago kai da niyar tambayar ta, A lokacin ne kuma drinks din da yai oda ya iso gare shi, Ganin su gurin ya sa ma,aikacin ya tambaye shi a cikin ladabi da cewa, Ko za,a kawo masu nasu abin shan ne, su ma, ? Sai ya dago don jin may za su ce, Lubuna tace kwarai kuwa mungode kwarai Sir, Bayan wucewan ma,aikacin ne Lubuna tace, Wanan sunan, ta Salawatu , nikuma Lubuna nake, Mun yaba kwarai da mutuncin ka a wanan ma,aikatan , Muna ganin ka shine yau nace bari muzo don mu gaida kai, Sai da ya kurba drinks din dake a cikin cup din dake hannun shi tukun tare da lumshe idon shi , Saboda mamakin irin karfin halin da su kayi na taron shi haka kai tsaye, Dama yana da labarin yan matan Abuja tun lokacin da akai mai transfer ake bashi labarin su, A takaice ya bata ansa da cewa nagode, Lubuna da mutuntawan ku, Daga haka mai,kawo masu drinks, din ya iso dauke, da tiren drinks din su,,, Daidai lokacin da zasu fara sha ne shikuma Abubakar ya mike da niyar barin gurin,,, Cikin wani irin muryan kissa suke cewa mungode Sir, Hannu ya daga masu alamar, is,ok, daga haka kawai ya sa kai abinshi ya bar gurin,,
*** *** ***
Dawowan Abubakar Abuja yasa izuwa yanzu mutanen gidan su suna samun labarisa akai,akai, Bakamar lokacin da yake zaune a Lagos ba da mai jin duriyan su, Hakan yaza yanzu labaran ci gaban da Abubakar ke yawan samu yake isowa garin birnin kebbi, Sai dai wanan labarin a gurin mutane har da kari sikeyi a kai, Sadiya tafi Abubakar, rashin kula da,gida don ita indon ta na,ta ne ma suyi zaman su a can ba,tare da sun shigo kebbi ba, Abu guda ne shi duk wanda yasan Abubakar idan har yai sa,an ganin shi zai dan iya wa mutum alheri kadan, Sai dai kuma idan har sako zai yi zuwa gida, to fa mama Ladi, ita ce za tai kato,kato da sakon sai wanda ranta yaso abawa, Duk da ko malam tsoho sai taga dama bashi abinda taga dama, Hakan da takeyi shi ya kara tayarwa da malam tsoho hankali don yasan cewa nan gaba gaba,daya kan zurian nashi zai kasu ne daban,daban,,, Yanzu kwata,kwata ta daina, bawa yan gidan alheri sai dai takai waje don bidan suna,
***** ***** ***** Zaune yau yake a office din shi aiki yai mai yawa kamar kullun, Don yanzu komai kara bunkasa gaba gaba yake mai, Dawowan shi daga gurin meeting ke nan yana kokarin ganin, ya shigar da abinda sukai meeting akai cikin net, Sakatariyar office din su, ce ta turo kofa, ta shigo tana saye da wando da riga bakake, Batare da ya dago kai ba, ya ke ce mata, yadai Ruth ? Tace Sir cikin harshen turanci kana da bako kusan kwana biyu ke nan yana zuwa wai yana son ganin ka ne, Cikin sauri ya dago kan shi yana mai kallonta, Inda ya kara maimaitawa da cewa kwana biyu shine baki fada min ba Ruth sai yau, Ruth ta dan sosa kai tace cikin rusunnawa, Gani nayi miutumin bai cancanci ya ganka bane don baiyi kama da abokin hurda ba, Ya fi yi kama da Beggars, Cikin dan daka tsawa ya katse ta da cewa, ki ce ya shigo pls, Umurni na baki daga yau kada ki kara hana bako na gani na kowani iri ne, Umurni na baki kada ki kara kawo min naki uzurin, Irin yadda yai magana yaba Ruth tsoro don haka jiki na rawa tafita da sauri don yiwa bakon iso, Don tunda sabon boss din na su yazo bata taba ganin bacin ranshi ba irin yau, Karan bude kofan tayi don shigowa da bakon da tace din yana ta ziyaran su,, Ba, wani bane bakon illa Baba masijan su na Lagos watau, malam mudi,, A cikin mamaki yace malam Mudi kaine a nan kuma ? Barka da zuwa, Kasa malam Muddi din yazube yana cewa Rankaidade barka da warhaka,? Yau she kazo garin nan tashi mana Bissimilla ga guri kazauna yana mai nuna mai gurin zama, A dan ta kure malam mudi ya zauna saboda yana ganin bai dace ya zaune kusa da shugaban shi ba, Bayan ya sha rruwan da Ruth takawo maine dan kadan Sai kuma yadago kai yana mai kallon Abubakar din, Hawaye suka zubo mai inda yake cewa don Allah gurinka, nazo rankai dade ka tausaya min , Kai min hanyar da zandawo nan Arewa a cikin yan uwa na in har da halin yin hakan, ? Dama sana,a nakeyi acan bayan yar kariyar arzikin da na samu shine wani yai mun hanyar wanan aikin, Sai kuma ya kara sa yar sheshejan kuka, alokaci guda, Subbahanallah haba malam ai zancen bai kai na kuka ba, Ka tsaya muyi maganar fahinta kawai ina ga zaifi,,,,
***** ***** ***** So,sai duk wani girma na diya mace ya baiyyanawa Meenat, Da ka ganta kasan cewa daga zurian gidan malam Manya take sabode ta debo irin jikin iyayyen ta maza, a gurin tsayi, Sai dai ita abin nata ya raba gida biyu ne don duk fuskan ta da launin jikin ta na fulanin gwandu, ne,,, Wanda yasan Meenat a baya yanzu idan ya ganta yasan cewa a kwai canji sosai ga lamarinta, Ta waye ta zama yar birni sosai, ga turanci a bakin ta, kamar wace ta taso gidan da ake turanci tun tana karama, Wayen Meenat ya karawa mama Ladi hassadan ta sosai a ranta don tasan cewa ko yar ta Samira wace ke can Abuja gidan yayan ta batai wanan kyaun ba, Gashi duk Meenat zata zo gida sai Uncle Shafi,u yaba da motar shi ankawo ta cikin mutunci, tare da dan tsaraban ta duk da ba yawa amma sai ankasa an,bawa kowa tsaraban, a gidan,, Ita ko mama wanan abin ke kara sa ta yanzu jin haushin Samaila da iyalan shi,, Don duk wani motsi na, su da wani tako na,su duk idon mama Ladi yana kan su, Babu karin haushi sai yadda Malam ke alfahari da yar jikar nashi, Tundai da aka nuna su suna wani gasan karatu a NTA sokoto, Wanda kowa ke murnan ganin ta cikin TV tana wasa kwakwalwa da sauran dalibai, yan uwan ta,, Don haka ta raya arayuwan ta cewa bazata taba barin Samaila har yai nisa akan harkokin ci gaban shi ba,