Kenza eBookz

Tarko complete novel - Chapter 93

Tarko complete novel - Chapter 93

Tarko complete novel Chapter 93: Tarko complete novel Chapter 93. ****** ********** ****** A haka rayuwa ta ke ci gaba a gidan mu yau dadi gobe wuya har…

2,243 words

****** ********** ****** A haka rayuwa ta ke ci gaba a gidan mu yau dadi gobe wuya har zuwa lokacin da ya shirya sallaman Su Dije da Mama Sa,a wa yanda ya barsu don su dan huta duk da yawan aiken da malam ke yi mashi, Amma yace ba zata dawo ba sai yaro yai kwari sosai, Duk abubuwan da Yaya ya sayo muna a tafiyan da yayi sun iso lafiya, har ya tafi Lagos yai clearing an sako a mota zuwa gida, Sam dukkan mu ba mu da labarin hakan saboda, sai da kayan suka iso gare mu, Ina wankin kayan yarana a laundry tare da dan gyara gura rai da safe lokacin ne kiran wayan shi ya shigo min, Nai mamaki da wanan kiran don nasan cewa yana a cikin gida a lokacin ga kuma kiran wayan shi yashigo min, Ina goye da Amir a baya na na bar Aisha a gurin Baba Ramatu suna hira tana aiki, A falon mu na samay shi shida Anty sadiya sai Fatima wace a kusan tare muka shigo da ita, Salawatu ce tai karshen fitowa da alaman daga barci take a lokacin,, Gaba dayan mu mun samu guri kamar yadda ya umurce da yi saidai nice dake da goyo nake daga tsaye ta bayan kushin ina dan jijiga yaron a hankali, Yai dan gyaran muryan shi a hankali abinda ya kara samu natsuwa ke nan don jin may zaice, Daya bayan daya yakalle mu yafara da Sadiya yace, Da mukai waya dake ina kasar Hong Kong watackalar mota kikace na zaba, Sai a lokacin ne zancen ya fara dawo muna a zuciyar mu cewa mun taba irin wana zancen ai, A hankali Sadiya tace mai fara nace maka kazabo, yace good, Ya juyo gurin da nake tsaye yace wace kalla kikace na zaba nace a takaice baka, Inda Salawatu take zaune ya duba ta dan bata rai yace wani kala tace Assh, sai ya juya gurin Fatima yace, kefa fuskan ta tankar zatai kuka saboda bacin rai don tana ganin ai tozarci ne ace har da Meenatu tana gaban ta ga komai yanzu a gidan nan, saida yakara tambayan ta da cewa Ehhey ? Saida ta hade wasu yawu tace, da kyat, Ja nace ma yace good masha Allahu Yace anjima zuwa rana zaku ga motocin ku sun iso kowa kalan nata zata dauka, don ita ta zabi abinta da kanta,, A take fuskan kowar mu ya washe don murna, sai muka fara godiya muna cewa mun, gode mai cewa Allah ya saka da alheri Allah ya kara sabon budi,ta hanyar alheri,, Nan aka shiga buga waya ana fadawa yan uwa da abokan arziki abin arziki ya samay mu, Mutum na farko da na fara kira shine mahaifina tare da mahaifiya na, Sai uncle dina da Ànty Amarya, tunda nasan cewa yau weekend ne kowan su na gida, lokacin, Murna nake tasha inda na kira Yayana Ibrahim na sheda mai ya taya ni murna tare da godewa Allah ubangiji wata,ala, Motaci sun iso lafiya inda kowacen mu tafita waje don taga zabinta, Motace ta gani tafada, ta yayin irin ta zamani na mata aka sayo muna Duk wanda yaga wanan motocin sai yai mamaki yadda akayi ya iya saya muna mu dukka,, Sai ranan ya bawa kowa, sarkan gold daya saya muna, haba wata sabuwar murna takara tashi, ga kuma wasu kayan amfani foreign once da ya sayo muna, masu kyau, Kowa sai mamakin irin yadda Allah ya daukaka Yaya Abubakar a lokaci guda saboda kwazon shi, A folona mun saka kayan a gaba muna kallo nida Ramatu da Aisha su Baba Wadda suka shigo folon sundawo daga gurin dana motoci, Baba Hamza wanda ya zube a saman kujera a folo na yana cewa wallahi Diyata kin iya zabe duk wanda yazo yaga motocin nan naki kwai ake zance, Ina kokarin aje kayan da na kwaso agurin shanya nake cewa kai Baba na kodai kana yabon na diyar kane,, Yace No wallahi ba hakana bane duk wanda yazo sai kiji yana yaba kyaun motar taki wallahi, Nace to Allah ya sa mu more ma abin mu shi kuma Allah ya kara mai budi ta hanyotin Alheri suka karba min da cewa Ameen, Nan mu ka zauna da su suna cin abinci muna hira dasu acikin farin ciki, Baba Wadda yake kara, fada min irin na,sarorin da wannan tafiyan ya jawo wa Yayan Abubakar, Shiru nayi a zahiri ina sauraren shi amma a can cikin zuciya na sai tunane nakeyi yadda zan shawo kan Yaya Abubakar ya taimakawa yan uwan mu a gida, Dabara tafado min don haka sai na bar zance har in ina da duty sai na gabatar mai da ita, Sai har koki aketayi acikin gidan kowana abinda ke a gaban sa duk kwanakin nan,

****** ********** ****** Bayan nagama aiyukana na kammala komai na koma part dina nakara gyarawa, Don ni abadan bana son ganin kazata a gidan mace ko kadan saboda na tashi ina ganin irin yadda, mamana take da mugun tsabta duk da ban kaita ba,, Kamar kullun suna folo zaune ana zaman saka ido da kyashin juna wai zaman hada kai, Salawatu wace dawowanta kenan daga yawon zuwa gwada wa yan uwa mota tana bashi labarin abinda aka fada, agurin nuna motan,, Na fito dauke da, kayan da zan tafi da su danki Yayana inda na gan su zaune a falo nai tankar bangan su ba, Don ni izuwa yanzu ban son wanan zaman saboda na fahinci zamane na sake magana, Idan ance ba,a ganni ba nakan ce saboda Amir baya son sanyi da yawa yana mura, yasa na daina fitowa akai,akai, Ina tako guda guda inda duk idanuwan su yadawo zuwa gareni ina saye da dogon rigan larabawan Egypt, Daga gurin da suke ina iya gane irin kallon da Yayana yai min, Ashe idon Fatima wace tankar tana magana da diyarta idon ta na akan mu, kishi sosai ya baiyyana saidai a zaton ta ba,a fahince ta ba, Murmushi mai alamar signal na sake mai tare da ci gaba da tafiyana, Na dauko Amir na kwanta ban wani dade ba sosai sai gashi ya shigi dakin, Ya samay ni ina waya da wata course mate dina tana fada min cewa, result ya fito, Har ya shiga wanka ban gama wayan ba saidai kafin yafito mun kashe wayan, Tea na dan hada mai duk da tea din ba wani mai yawa bane acan kasan cup ne sai dai yana kara mai lafiya irin ta maza, Ta bayana najishi ya rungumoni sanyi da jikin shi ke dashi gami da reaction din da naji yasani sauke ajiyan zuciya,, a hankali, Nace mai kafito yace eh Sweet sister may ki ke yine nace a hankali, shayin ka nake hada ma,, Ok kawai yace Yasakeni ya nufi gaban mirror din shi yana goga roll,on a jikin shi, Yace ban san ya zamuyi ba zancen tafiyanki saudiya ga Amir bai kai lokacin yayye ba Najuyo nai har da idona cikin sigar jan hankali, nace ai idan Allah ya bashi kafa zuwa lokacin sai kawai in yayye shi in tafi,, Yadan yi jim kamar yana tunane sai can yake cewa amma kina ganin hakan bazai zama mai matsala ba ko ? Na ce insha Allahu babu abinda zai samay shi a lokacin ai mutane da yawa suna barin yara su tafi, su sauke farali, Yace Good Allah ya gwada muna lokaci dake da Fatima zaku tafi. Allah ya kaimu kawai na iya furtawa, Sai da na kai bakin gado na juyo ina cewa amma akwai masu zuwa acan gida ko ? Ya zubo min ido kamar mai nazari can yace dafa cikin su Baba musa nake son wasu su tafi harda, Mama Sa,a saboda Baba ya rokeni hakan, Saidai ban son Mama ta san zanen don gudun fitina, Nace Yaya dama ina son in maka tuni akan zancen su babadin nace amma yakama su a aika masu da wani abin alheri don su shedacewa kasamu wanan cigaban haka, Murmushi yasake min yana cewa dama nasan da wanan zancen ban tsan manin har akai war haka baki min zancen ba, Yace na san cewa duk zancen ki ke akan mutanen gidane yake,,,

ZEEE MAKAWA YELWA

🕸🕸🕸TARKO🕸🕸🕸 🕸🕸🕸🕸🕸🕸 9⃣5⃣

ZAINAB IDRIS MAKAWA

ALLAH AL A'FUW

Zaune yarinyar take tayi tagumi da hannu biyun ta, ita ka dai a makaranta babu kowa sai maigadin makaran ta Tayi kuka har tagaji dan abincin ta ya kare, ba ruwa, a goran ruwan ta, saima maigadine ya dan saya mata ruwan leda, tasha, Daga gurin kitso duk da nasan cewa Aisha ta dawo amma hankalina yana gurinta don ban taba fita nabar ta ba ita kadai duk inda zamu tafi tare muke, da ita, Duk da na dawo ina jin yunwa amma da ihun kiran sunan Aisha nakeyi, Yaya Abubakar yana zaune yana waya nai sallama na wuce part dina cikin kiran yarinyar, Ramatu tafito hankali a tashe tana cewa Hajiya ai Aisha, bata dawo ina ce ko, kuna tare ne, Gabana ya ba da dam dam yar mutane tun safe bata dawo ba har zuwa yanzu karfe shidda da rabi na yamma, Yaron na mika mata da sauri na juya ina cewa na shiga uku ni Meenatu, ina yar mutane ta shiga yau, A folo na samu Fatima da Salawatu, suna tare da Yaya a zaune suna magana akan wani program da akeyi,, Ido a rufe nace Maman Aina, yaran basu dawo daga, school bane har yanzu, abinda duk ya dawo da hankalin su a gareni ke nan,lokaci guda, Kafin taba ni amsa yarta karama ta fito tana magana da uwar, ido a waje na kara cewa cikin wani murya na tashin hankali, Fatima acan ki bar min yar mutane yau ko na shiga uku a garin mutane, daga haka na juya zuwa hanyan, waje Muryan shi naji cikin tsawa yana cewa, Ke Meenatu ya akayi ne wai cak na tsaya hankali a tashe nake cewa da zan tafi kitso ne na tafi har dakin ta nace yau Mijin Fattu baya gari don Allah idan zata dauko yara ta hada da Aisha ta sauko min don zan tafi gidan Anty saloon yini, ni da Fattu,, Juyawa yayi inda Fatima taje zaune tana gyarawa yar ta igiyar riga yace ina yarinyar da tace ki dauko mata, Batace komai ba sai dan jawo yarta zuwa jikin ta da tayi wani irin murya mai daka tsawa yace wai ba dake nake bane ina kikabar min yarinyar mutans nace, Ganin yanayin shi ya canza a lokaci guda yasa ta dago kai tana kallon shi ido a cikin ido tace aini bance mata dama zan dauko yarinyar ba koda ta fadamin, Ita may zai hana ta, tafi tadauko ta daga inda take saini zata aika take nufi ko may, Mikewa yayi da karfi yana fadin innalillahi wa,ina alaihin rajju,un, Daga haka ya mike nabi bayan shi inda a tare muka kai waje nan muka fada mota a tare a lokacin Baba Wadda suka shigo gidan a cikin hilux, Bayan mun fita suke tambayan Ramatu da su Sadiya da suka fito a cikin tashin hankali, Suna bin mu da kallon tashin hankalin yaya za ayi idan yarinya ta bace a cikin garin Abuja, Ai suma bayan mu suka bi zuwa school din hankali a tashe Gudu sosai Yaya Abubakar ke ta kwasa har Allah ya kaimu lafiya makarantan, Tun daga nesa muka hango get din makarantan a rufe, hakan ya kara tayar muna da hankali, Bayan mun samu guri mun Parker motar ne, sai, ya fita zuwa, duba get din dake da kwado daga waje ashema a bude gurin yake, Mun samay ta kwance tana barci a dan gefen dakalin zaman maigadin, Yana ganin mu ya fara fada yana cewa gaskiya baku kyautawa yarinyar nan ba sam ace tun karfe daya ba ,a zo daukan yarinya ba sai yanzu, Hakkuri Yaya Abubakar yabawa maigadin yace ai matsala aka samu don bai gari shi wanda kuma yake dauko mu yai tafiya ne, Bayan mu kama hanya gaba dayan mu har su Baba Wadda sai ajiyan zuciya yarinyar ke ta saukewa alaman tayi kuka harta gaji, Sai lalashinta nakeyi inadan shashafata ina cewa Aisha yi hakkuri kin ji don Allah ki yi hakkuri ban san cewa ba a dauko ki ba, Tace cikin murya mai rauni naga maman Aina zata dauke su nazo sai tace min wai najira za,a zo a daukeni ,wai su wani guri zasu, tafi, Baice komai ba sai tukin motan yakeyi kawai batare da ya tanka muna ba sai dai duk abinda mukeyi yana kallon mu tankar baya ganin mu, Ashe duk a hasale yake don dai ni ban fahinci yana acikin fushi bane a lokacin, Mun kusa shiga uguwar mu yake ce min daga gobe Hamza ya fara koya maki mota, Tau kawai na iya cewa batare da na kara furta wani abuba akai, Mun iso mun samu su Ramatu a wajen gida har da Fattu da akafada masu, cewa ga abinda ke faruwa, A folo muka samu su Sadiya sai dai Fatima ita bata gurin kowa sai, tambayan yadda akayi yakeyi, Sama Yaya ya haye batare da ya kara tankawa kowa ba nima jan hannun yarinyar nayi na shiga da ita bathroom nai mata wanka, Sai na hada mata tea maizafi nace tasha don zaifi warware mata hanjin ta saboda ta dade bata ci komai ba, alokacin, Ina zaune a gefen ta Baba Ramatu tana goye da Amir yai barci a bayanta don har tai mai wanka ta shirya shi ko,

Readers Also Read

More by Bilyn Abdull