Kenza eBookz

Triplets book 1 complete by star lady - Chapter 10

Triplets book 1 complete by star lady - Chapter 10

Triplets book 1 complete by star lady Chapter 10: Triplets book 1 complete by star lady Chapter 10. Shi kuwa uncle gudu yake kamar zai tashi sama yana ihu…

4,385 words

Shi kuwa uncle gudu yake kamar zai tashi sama yana ihu a kawo masa ɗauki amma ina duk in da yazo wucewa sai student sun tashi sun gudu dan sun san halin lucky duk wan da ya kwana ya tashi a Harvard University to yasan da zaman Lucky da Winston Copper karnukan nan bala'i ne basu da mutunci gashi sun samu horo da kyau wajen Michel, duk abun da Michel ɗin yace suyi shi suke idan yace su rikita mutun zasu bi mutun amma ba da gudu sosai yadda zasu kama mutumin ba sai su bishi da gudu kaɗan kaɗan dan su galabaitar da mutun san nan duk in da ka shiga sai sun bika ba wanda ya isa ya raba ka da su sai shi Michel ɗin da ya haɗa ka da su,

Tsabar gudun da uncle yake har sai da wandon sa ta cire ya rage daga shi sai Short sai uban zufa yake yana ihu yana neman tai mako,

a guje ya shiga Harvard Community garden wajen cike yake da student, ganin uncle da gudu yana ihu ga kuma lucky na bin sa a baya ne yasa gaba ɗaya student ɗin suka fara gudun cetan kan su suma,

uncle dai yanzu karfin sa ta fara karewa ya rage gudu daker yake nishi girgiza jiki Lucky yayi tare da yin haushi mai firgita kwakwalwa nan take uncle ya ji sabon karfi yazo masa ya kara kwasawa a guje ya nufi wajen garden ɗin yana ihu kamar mahaukaci,

a guje ya shiga wajen Harvard swimming pool dake kusa da goro place watermelon, manya manyan swimming pools ne a wajen wadda a kalla zasu kai 20 an kawata wajen sosai da sosai,

a sukwane uncle ya faɗa cikin pool ɗaya, a tunanin sa ya tsira sai nishi yake sama sama kamar zai mutu, lucky na shigowa wajen shi ma ya faɗa cikin ruwa ihu uncle ya fasa tare da fita a sukwane jikin sa duk ruwa tsantsin tiles ya kwashe shi ya faɗin ƙasa ya buga kai a tiles, rage gudu lucky yayi har sai da uncle ya miƙe ya ci gaba da gudu san nan shi ma lucky ya rufa masa baya.

Share fisabilillah 👏

To masu karatu sai mun haɗu gobe idan mai dukka ya kai mu shin ya uncle zai ƙare da *Lucky* wayyo ni *Princess Teema* Michel na sha'anin sa 🤣🤣🤣🤣🤣

💞Star Lady💞

*💞TRIPLET'💞

*💞The beginning💞*

*Episode 9*

.....Idan uncle yayi kamar zai tsaya sai Lucky ya girgiza jikin sa yayi haushi mai rikita ƙwaƙwalwa, uncle kuma da yaji haka sai yayi tsammanin lucky ya kusa kama shi ne sai ya daure ya kara karfin gudun nasa, gaba ɗaya student da ke ganin halin da uncle ke ciki sun tausaya masa ba kaɗan ba dan ya fara manya ta a kalla zai kai 45 years ba yaro bane, ga abun dariya ga kuma abun tausayi,

Shi kuwa Michel yana zaune hankalin sa kwance, kallon sa test yayi cikin muryan neman alfarma yace "Please Michel ku ɗauke ni aiki mana a gidan ku koda goge muku takalma ne idan zaku fita ina son in ganni dai na zauna a cikin gidan ku" shiru Michel ya ɗan yi kafin yace "Babu wan da ya isa ya kawo wani Mai aiki gidan mu idan ba Romeo ba shi kaɗai yake iya ɗaukan masu aikin da yake so, ko daddy bai isa yace ya ɗauko mai aiki ba kuma shi Romeo kafin ya ɗauki mai aiki yana da doka, dokar kuwa itace idan har yaga ka dace ya ɗauke ka aiki tofa zaku yi agreement da shi ne zai rubuta maka takarda kasa hannu misali idan zai ɗauke ka aiki zai faɗa maka aikin wata kaza ko Shekara kaza zaka masa idan ka amin ce to zai rubuta maka takarda kasa hannu, idan kuma kasa hannu tofa ka sani komai zai faru sai ka cika adadin shekarun da kukayi da shi ko da baban kane ya mutu a ranar sai kazo aiki baka da wani iko da kan ka sai abun da yace kayi kuma shi aikin sa bata da time ko wani lokaci yana iya saka aiki koda cikin dare ne, babu wan da ya isa ya tinkari Romeo yace ya ɗaga maka kafa, ko daddy ka sani tsoron sa yake, kuma mu ai kasani dukka gidan mu sojoji ne masu aiki har abinci sojoji su ke girkawa wan nan tsarin Romeo ne" "please Michel ka ɗan roƙe sa mana ya ɗauke ni ko da mai goge muku takalma ne" kallon sama da kasa Michel ya masa kafin yace "Ko daddy bai isa ya ce da Romeo ga abun da zai yi ba shifa abun da ya ga dama yake, kai mutun ma ya isa ya tinkare sa yace masa yayi wani abun hmmm ka tambayi Johnson ya faɗa maka, kai bama sai an faɗa maka ba ni zan baka 1 million $ idan ka iya tinkarar Romeo ka gaida shi ma kawai" ya kai karshen maganar tare da miƙa wa ya bar wajen cikin sauri dest da test da John ɗin suka rufa masa baya, da sauri karnukan sa biyu Winston da Copper suka diro kasa tare da girgiza jikin su wasu jibga jibga da su cikin takun ƙasaita suka rufa masa baya,

A ɓangaren uncle kuwa kasa cigaba da guduwa yayi ya zube kasa a dai dai Allston dake kusa da hanyar tafiya community garden, ya kasa ci gaba da numfashi, numfashi ta masa wahalar jawuwa hakan yasa numfashin sa ta ɗauke ya sume, da guduwa Lucky ya kariso kansa yana kokarin kai masa cizo a kafa Michel da ya iso wajen yanzu yace "Wait Lucky" ba musu lucky ya tsaya tare da juyawa da gudu ya koma wajen Michel ɗin shafa kan sa Michel yayi kafin ya juya ya bar wajen Lucky Winston Copper suka sufa masa baya san nan su dest suka rufawa su lucky baya,

Su Michel na tafiya sauran uncle's ɗin suka zo suka ɗauki uncle dake sume suna ta masifa "da ma ai mun faɗa maka karka shiga sabgar wayan nan kaƙi yanzu gashi kaji a jikin ka ai" haka sukayi ta surfa masifa har suka wuce da shi cikin *(HUHS) Harvard University Health Services*

Shi kuwa Michel kai tsaye ya wuce *Harvard Square Parking Garage* yaje ya shiga dankareriyar motar sa kirar *Aston Martin* a guje Winston Copper suka shiga gidan baya shi kuma Lucky ya shiga gidan gaba, Johnson ma wucewa yayi ya shiga motar sa, kuɗi Michel ya ɗebo dollars ya miƙawa su dest yana faɗin "Kai test zaka iya zuwa ka gaida Romeo ne gobe na zo maka da kuɗin ka cash 1 million dollars zan baka idan ma sun maka kaɗan zan karama" cikin sauri test yace "A'a ni nama fasa batun aikin ai" turɓune fuska Michel yayi kafin ya miƙa musu kuɗin hannun sa yana faɗin "See you next time guy's" ba musu dest da test suka ansa kuɗi, Michel ya kunna motar sa da gudun gaske ya figeta ya bar School ɗin dama shi Johnson tun isowar su parking space ɗin yaja motar sa bai tsaya wani magana ba, su ma dest da test kowa ya shiga motar sa ya wuce gida dan yau ba zama a School sun san sunyi tsiya kar aje a faɗa wa daddyn su gwara shi Machel shi da Johnson ba mai karfin gwiwar iya nufan hanyar gidan su ma bare ya kai karan su.

John wadda kuka fi sani da Johnson ɗane ga uncle ɗin su Romeo, mai suna uncle herry a gidan su Michel ɗin yake da zama da shi da ɗan uwan sa jay.

Gudu sosai Machel ke shararawa a kan makekiyar titin *beach drive* duk motar da tazo sai dai ta kauce ta bashi hanya ba dai shi ya kauce ba, mutane na girmama shi saboda tambarin dake gaban bambam motar sa wadda a ka rubuta *William jacop Family* saboda wan nan suna yasa suke kaucewa su bashi hanya,

*Washington DC*

Birni ne mai matukar kyau da ɗaukan hankali kuma shi ne babban birnin Usa gaba ɗaya garine na manya manyan masu kuɗi ta duniya, garine mai cike da dogayen gine gine na alfarma ga wurare daban daban na wasanni da kayatar da ɗan adam, duk ta in da ka juya irin wayen nan kyawawan jirgin kasa na masu shiga har cikin anguwa nan ne (Portland train) ma su kama da luckgerious bus, ko wani bakin titi zaka samu kyawawan kujerun zama wadda passenger zai zauna ya jira jirgin kasa ko Asalin Bus, kowani wajen da kujera yake an sanya masa runfa mai matukar kyau saboda ruwan sama kowa harkan gaban sa kawai yake ba ruwan wani da wani, *Washington DC* garin ya haɗu ta ko ina ya kayatar matuka, kawatuwar sa ba zai faɗu a baki ba,

Sosai Michael ya kunna kiɗar sa ya kure volume yana sharara gudu yana kaɗa kai su lucky na tayasa, cikin kankanin lokaci ya iso katafaren unguwar su mai suna *lot 33*, anguwa ce ta manya manyan masu kuɗi da masu mulki ma'ana yan siyasa da sarakuna, ko ta ina a anguwar the most billion dollars gidaje ne a wajen wata gidan ma idan ka ganta kace da gold a kayi ta, anguwar tsab tsab take babu alamar datti ko kaɗan kamar mutane basa rayuwa a waje saboda hasken da tsabtar unguwar tayi, har kan titi babu alamar datti ko kaɗan duk wani lungu da sako na anguwar titi ne mai matukar kyau shifiɗe har bakin kofar gidaje, gaba ɗaya gidajen dake wajen babu hawa 2 daga uku yayi sama dogayen gini ne sosai a unguwar kai dagani ba tambaya kasan anguwar na masu shi ne. Wata dankareriyar hanya Michel ya miƙa kai da ganin hanyar kasan ta musamman ce, kai tsaye wata aljannar duniya ya tinkara, dan wan nan gida itace aljannar duniya, tun daga nesa ya fara danna horn na motar sa,

a guje wasu jibga jibgan sojoji masu jini a jika lafiyayyu masu razana mai rai suka wangale masa tampatsetsen gate ɗin wadda da ganin gate ɗin kai kasan ba gidan wasa bane a wajen, dan haɗuwar gate ɗin gidan kawai ma abun lallo ne,

yana kari sowa wajen ya danna hancin motar sa cikin gidan ya nufi second gate sai sara masa jibga jibgan sojojin suke, in da second gate ɗin yake, kafin ka karisa wajen sai ka shiga ta wani waje kamar ɗaki wadda a ka rubuta scanning a wajen, cikin wajen yana bada wuta launin purple, wajen bai da nisa da gate 2, wajen cike yake da na'urorin da a ka haɗa su da jikin bangon wajen, san nan wajen babu kofa zaka shiga ta nan idan wajen ya gama scanning naka sai ka fita ta can haka wajen yake

ko da Michel ya isa wajen, dai dai wajen da a ka rubuta scanning place ya tsaya, yana jira, sai da na'uran dake wajen tayi scanning na motar sa tsab dan tabbatar da ba wani mugun abu a motar tasa, bayan na'uran ta gama scanning sai da ta ɗauki 2mins san nan gate 2 yayi kara kiii kafin ya buɗe kansa da kan sa alamar motar Michel babu komai dan gate ɗin an haɗata da nauran ne idan a koi wani mugun abu a tattare da kai to gate ɗin bazata buɗe ba zatayi kara kamar jiniyar motar yan sanda su kuma jibga jibgan sojojin dake bakin gate na farko suzo su kamaka su binciki me kazo da shi yasa nauran ke kara shiyasa a gate ɗin farko a kasa sojoji na biyu kuma gate mai aiki da na'ura mai buɗe kan ta kuma ta rufe kanta.

Da gudun gaske Michel ya figi motar sa zuwa cikin gida

````Wow````

Gida ne mai girman Hectare 4 wato plot 24 kenan, gida ne gari guda, gaba ɗaya gidan har jikin bango da kasa, tiles da glass ne kai kace ginin tiles da glass ne kawai, hawa huɗu ne gidan, ginin ya tsaru iya tsaruwa ya fita iya fita ko gidan shugaban kasa albarka parking space na gidan kawai taci 3 palo san nan shi kan shi parking space ɗin a keɓe yake waje guda an sa masa katafaren gate da na'urorin da zasu wanke motar da a ka fita da ita idan an dawo, kamar ɗaki a ka gina parking space ɗin motocin ne kala kala jere a wajen,

a tsakiyar harabar gidan wani gini a kayi kamar rijiya a ka kewaye wajen san nan a kayi wanin gini a tsakiya kamar fai fai ruwa na zuba a wajen,

garden na gidan ya kai girman plot 2 cike yake da kana kanan flowers masu kamshi launin je da kore a dai dai kofar shiga garden ɗin daga ɗan gefe an rubuta *Romeo da flowers*, ga manya manyan kujeru masu numfashi na hutawa shirye a wajen, ga fitillu masu hasken gaske sun haske ko ina, gaba ɗaya garɗen ɗin kewaye yake da glass ƙasan sa kuma tiles ne wani gefen kuma grass carpet, tsayawa zayyana muku haɗuwar garden ɗin nan zai cimana lokacin sosai, wajen lambun daddy kawai yaci 2 plot, dan daddy mutun ne mai son lambu sosai, kowani ɗaki a gidan yana da balcony ta gaban sa an kawata wajen da furanni masu ɗaukan hankali, gaba ɗaya gidan kewaye yake da jibga jibgan sojojin masu jini a jika suna tsaye rike da manya manyan bindigu fuskar nan tasu kamar an aiko musu da sakon mutuwa, idan ba kana da dakakkiyar zuciya ba ka kalli face ɗin sojojin nan to zaka iya sumewa dan babu alamar annuri a face nasu ko kaɗan, kowani lungu da sako na gidan jibga jibgan sojoji ne riƙe da manya manyan bindigu kai kace wajen yaki zasu tafi, kai daganin hakan kasan ba gidan wasa kazo ba, manya manyan swimming pools uku ne a gidan ɗaya na Romeo ne shi kaɗai ba mai zuwa wajen sai shi, biyun kuma na sauran yan gida, haɗuwar wan nan gida ba zai faɗu a baki ba dan gidan nan gari ne guda,

Kai tsaye parking space Michael ya nufa yana zuwa wajen, daga saman gate ɗin wata yar na'ura kamar yar baby ta fara karanto number motar sa daga farko har karshe san nan ta kira sunan wadda ya fita da motar, nan take gate ɗin ta buɗe kan ta, Michael ya shige, duk wani kofa na gidan sai da Romeo ya sai tata da nauran sa dan ya rinƙa samun information a kan waye ya fita waye ya shigo, ko mota zasu ɗauka sai yasan da wani mota suka fita kuma waye ya fita da motar, ko wani kofa a koi matakan tsaro a jikin ta, idan ba gate ɗin farko na shigowa gidan ba bawani waje dake da mai gadi shi ma gate ɗin farko ya bar shi ne dan criminal ya samu ya wuce gate ɗin farko ya shiga gidan, gate na biyu ya tonasa asiri, kuma ba halin guduwa sojojin dake gate na farko zasu yi ram sa shi wan nan shi ne dalilin da yasa ya bar jibga jibgan sojoji a wajen,

Michel na shigar da motar sa ya kashe ta ya fito tare da su lucky, ya danna wani waje kamar remote san nan ya fice daga wajen su lucky na biye da shi, nan take ruwa ya fara sauƙowa yana wanke masa motar tasa, a she ruwa ya danna dan ta wanke masa motar.

Yana fita ya wuce wajen ɗakin su lucky dake kusa da garɗen, ɗakin karnukan ma duniya guda ne har da katon gado a ka sanya musu kai kace ba kuɗi a ke sawa ake sayen abubuwan nan ba, yana kai su ɗakin su ya rufe su ya fito

Kai tsaye katafaren kofar da zata sada shi da cikin gida ya nufa shi kan shi kofar ma abun kallo ne, yana zuwa wajen ya buɗe yatsun sa ya ɗaura saman finger scanner yana kwaɓe fuska yana jin haushin wan nan matakan tsaro irin na gidan, ba karamin fama ya shaba kafin Romeo ya yarda ya dai na haɗa shi da bodyguard suna raka shi School har rashin lafiyar karya yayi dan a barshi ya rinƙa fita shi kaɗai yana shanawar sa, bayan finger scanner ta gama scanning na hannun sa ne katafaren kofar mai girman ta wangale kan ta, guntun tsaki yaja tare da kutsa kan sa cikin,

wani aljannar duniya ne a wajen palone mai girman plot 1 da rabi shi kansa palon yayi girman gidan wani, palon ɗauke yake da tampatsa tampatsan kujeru na alfarma masu numfashi set huɗu ko wani set kuma yana da nisa da ɗan uwan sa kai kace ma kujerun ba a palo ɗaya suke ba saboda ratan dake tsakanin su zaka ce palo huɗu ne kusa da juna amma kuma ba haka bane dukka palo ɗaya ne girman palon ne yasa a kai wa kowani set da mazaunin sa, kowani set da kalar sa sky blue fari milk golden color shine colors ɗin kujerun, wajen table ɗin cin abincin su ma duniya ne guda, table ɗin yana da tsawon 2meter ga haɗanɗun kujerun sa launin golden color masu ɗaukan hankali da ɗaukan ido guda 24, gaba ɗaya curtains na falon farare ne kal kamar yanzu a ka fito da su daga kwalin su saboda haske, Makekiyar Tv ɗaya ne a palon mai bala'i girma wadda idan kana kallon mutun sai kaga kamar ka kira shi ya amsa saboda girman Tv, fentin palon gaba ɗaya golden color ne sai ɗaukan ido yake kamar gidan gold, daga kusa da sofa set milk color nan wata iriyar tampatsetsiyar staircase ne mai kamar indomie raun haka kamar maganain sauro haka staircase ɗin yake, daga farkon staircase ɗin a miƙe yake straight daya ɗan yi nisa kamar nisan tsawon mutun daga nan sai ya tafi sama a nannaɗe kamar maganin sauro, shi kan shi staircase ɗin abun kallon ne duniya ne guda fentin jikin sa golden color ne kamar gold san nan ga wasu kwayaye fitillilu a jikin sa dake haske stair ɗin da kyau sai walwali yake yana kwalli kamar gold, staircase ɗin nan ya haɗu iya haɗawa sosai, gashi tsab da shi kamar kafa bai taɓa taka kan shi ba,

a kasan iya palo da katafaren kitchen ne kawai a wajen sai wajen dining table wadda shima duniya guda ne wajen, kitchen ɗin kawai kusan 1 plot ne a wajen babu abun buƙata da babu a kitchen ɗin jibga jibgan sojoji ne ke musu girki da duk wani aiki na gidan gaba ɗaya gidan daga farkon ta har karshen ta babu alamar mace a cikin ta

gaba ɗaya palon kasan kewaye yake da tsadaddun curtains masu bala'i kyau da ɗaukan hankali farare tas ko ta ina hasken gaske ne a palon saboda kyawawan fitullin dake bada haske daga sama POP, palon nan a gyare yake tsab kai kace ba a taɓa taɓa komai na palon nan ba saboda tsab ɗin da yake, sai wani fitinan ne kamshi ke tashi a palon kamar an yi ɓarim turare, Wan nan gida dai sai dai muce Masha Allah dan ta ko ina yayi ne

Kai tsaye staircase ɗin Michel ya nufa sai kwaɓe fuska yaƙe, yana hawa wani kyakkyawan Bature ya sauko wadda kallo ɗaya zaka masa kasan daddyn su ne dan kammanin sa ɗaya da Michel sai dai shi kwayar idon sa blue ne, ko kallon in da yake Michel bai yi ba ya wuce, cikin sauri daddy yace "Welcome My tiger" da yake haka daddy ke kiran sa a cewar daddyn wai idon Michel ɗin na shining like Tiger eyes shi yasa yake ce masa tiger "Thank you dad" ya faɗa tare da wucewa ya karisa hawa saman, a mai makon ya shiga palon saman sai ya kauce hanya ya shari kwana ya nufi wajen wata kofa wadda daga bakin kofar kana iya leko palon kasa, kofar ya sanyawa fingerprint na shi na tsakiya, nan take kofar ta buɗe ya shige abun sa, shi kuma daddy ya wuce ya sauƙa palon kasa ya nufi wajen sofa sky blue ya zauna tare da kunna News a makeken Tv plasma su.

💞💞💞💞💞💞💞💞

*KANO*

Sai 04:00 pm su jelly suka dawo gida a motar Imran, sauri sauri Imran ya sauƙe su a gida tare da yin sallama da daddy dan lokacin jelly tayi barci a jikin daddy sauri sauri ya juya kan motar sa ya bar gidan dan tsoron kar dare ta masa a hanya ba shi da amsan da zai bawa Ammie sa idan ta tuhume sa a kan ina yaje, wucewa cikin gida daddy yayi kai tsaye bedroom na shi ya wuce su Zuwaira na gaida shi amma bai kula su ba saboda bai son amsa magana jelly ta tashi daga barcin da take, saman gadon ta dake bedroom na shi ya kwantar da ita a hankali dan karta tashi, sai bayan ya kwatar da ita ya tuna sun manta basket na ta a motar Imran, wucewa yayi ya ajiye jakar computer sa ya nufi toilet dan yin wanka.

💞💞💞💞💞💞💞💞

*👹 DAULAR MUTUWA 👹*

Yan sanda mota biyu ne suka shiga wajen wan nan dajin dan sun samu labarin akoi gidan magicians a wajen, tun daga ɗan nesa suka kashe motocin su, suka sauka suna tafiya da kafa a hankali hankali kamar wasu ɓarayi sai sanɗa suke suna tafiya, suna addu'ar Allah yasa nan shine address ɗin da a ka basu kuma Allah ya basu Sa'a su samu su tarwatsa wan nan gidan dan an sanar da su waje ne mai haɗari ga kuma a saran rayuka da basu ji ba basu gani ba da ake a wajen, a na zaluntar bayin Allah a wajen,

Sunyi tafiya mai nisan gaske sunayi suna duba map har sun gaji wasu daga cikin su suka cire takalmin kafarsu suka ci-gaba da takawa da tafin kafar su,

Dai dai wasu bishiyoyin masu tsawo ga wajen da ɗan duhu saboda cikan ganyen bishiyoyin, suna shiga wajen sun ɗan fara tafiya kenan suka fara jin wata iriyar gigitatchiyar takun sahu dan duk in da a ka taka sai kasa ta bada dum dum, a guje suka nemi wajen ɓuya kowa yayi ta kansa suka laɓe suna ɗan leƙowa wasu sun laɓe wajen bayan bishiya wasu kuma sun shige cikin ciyayi, suna tsaye sunyi tsurutasu suna jiran su ga wanene zai bayyana,

ba karamin girgiza sukayi ba ganin barbushi basu taɓa ganin irin wan nan halitta mai girma da muni har haka ba nan take tsoro ya bayyana a face nasu wasu daga cikin su fitsarin tsoro suka saki a wandon su, wasu kuma sumewa sukayi a wajen dan halittar Barbushi sai mai karfin imani zai iya kallon sa kuma yasha lafiya, wani ɗan sandan ma har da kashi yayi a wando saboda tsoro, jikin su sai kerma yake ido ya rena fata sai zufa suke sun kasa riƙe bingun hannun su wasu daga cikin su sai kalmar shahada kawai suke furtawa a ran su, shima kalmar shahadar basu iya furtashi dai dai ba dan akoi masu ɗauko farkon kalmar shahada su karasa da wata sura ko nasi ko falaki saboda tsoro,

ɗaya daga cikin sune yayi ta maza ya saita Barbushi da bindiga, hannun sa sai rawa yake haka ya daure ya danna kunamar bindigar ya harbi Barbushi a sai tin hannun sa, abun da ya kara rikita ƙwaƙwalwa su shine da bullet ɗin yaje sai ya daki hannun Barbushi ya faɗi kasa kamar wadda ya daki karfe, ihu ɗan sandan da yayi harbin ya saki saboda tsorata dan bai taɓa ganin in da aka harɓi mutun kuma bullet ɗin taje ta daki jikin sa kuma ta dawo kasa ta faɗi kamar ta daki karfe ba, jin ihun ɗan sandan yasa Barbushi juyo da idon sa masu kama da wuta dai dai sai tin in da yaji ihun, kasan cewar wajen da ɗan duhu baka gani sosai yasa nan taƙe idon Barbushi ta rikiɗe ta zama kamar torchlight mai hasken gaske kai tsaye sai kan ɗan sandan da ya harbe sa hasken idon nasa yaje, a guje ɗan sandan ya fita daga maɓoyar sa yana kokarin guduwa

Girgiza jiki barbushi yayi ya fasa ihu mai rikita ƙwaƙwalwa da wan nan katuwar muryan tasa san nan ya zuro harshen sa waje wata iriyar doguwa harshen nasa tayi kamar igiya, yana tsaye a wajen ya aika harshen nasa ta capko masa ɗan sandan nan, ya kawosa gaban sa ɗago katuwar mummunar hannayen sa yayi ya damki ɗan sandan nan ya murɗe masa wuya ya ji kake kakas kas wuyar ta karye nan take rai tayi halinta ɗan sandan ya mutu, buɗe mummunar bakin sa duk wari kamar shadda yayi ya jefa ɗan sandan a cikin ta ga hakoran san nan zabga zabga kamar block a ka jera masa gasu da tsini kaifi kamar wuƙa nan take ya fara tauna ɗan sandan da gabza ganzan hakoran sa, kan kace me jinin ɗan sandan ya fara gangarowa daga bakin Barbushi hancin sa har ta ido

ihu sauran yan sandan da suka rage suka fasa tare da fita a guje suka bazama, suna neman cetar ransu, girgiza jikin sa Barbushi yayi kafin ya durkusa a wajen nan take ya rikiɗe ya zama katuwar maciji mai katon kai kamar faranti, ihu yan sandan nan suke basu san in da suke takawa ba guduwa kawai suke masu kashi a wando suna yi masu fitsari suna yi, kwanciya Barbushi da ya rinkiɗe ya zama katuwar maciji yayi ya kutsa ta cikin grass dake wajen yabi bayan yan sandan, duk wanda ya kama haɗiye su yake kamar paracetamol, yan sanda Shabiyar ne suka shigo cikin dajin Barbushi ya cinye uku yanzu biyar sun sume a wajen da suka fara ganin barbushi bakwai kuma suna gudun cetar rai sai kalmar shahada suke shima kalmar shahadar ba dai dai suke faɗe ba saboda tsoro da suke ciki

Sai da Barbushi ya cinye yan sanda biyar daga cikin su san nan yaji ya ɗan koshi sai ya fara kamasu yana murɗe musu wuya idan sun mutu sai ya goya su a bayan sa,

har ya gama kashe su dukka ba tare da ya lura da biyar ɗin da suka sume a wajen bishiyoyin ba ya ɗauki gawar wayan da ya kashe san nan ya rikiɗe ya koma asalin mummmunar halittar sa ya wuce ya koma in da ya fito

Su kuma biyar ɗin suna sume a in da suke.

💞💞💞💞💞💞💞💞

*WASHINGTON DC*

*Harvard University*

Readers Also Read