Kenza eBookz

Triplets book 1 complete by star lady - Chapter 12

Triplets book 1 complete by star lady - Chapter 12

Triplets book 1 complete by star lady Chapter 12: Triplets book 1 complete by star lady Chapter 12. dawo da kallon sa daddy yayi kan su Irfan kafin yace…

4,466 words

dawo da kallon sa daddy yayi kan su Irfan kafin yace "Ku tashi kuje ɗaki kuyi wanka kuzo kuci abinci" ya kai karshen maganar tare da kiran Zuwaira da Nana a kan su zo su kai su masaukin su miƙewa Akil yayi, yayi gaba yana faɗin "Ni banga abincin ci a gidan nan ba haka kuma ban ga wajen kwana ba dan haka hotel zan tafi na kama" yayi maganar cikin harshen turanci murmushi daddy yayi yana mamaki Akil, Abban su Imran yana da kuɗi na fitar hankali haka ita ma Ammie su dan tafi Abban su ma kuɗi nesa ba kusa ba, to amma shi ma daddy Jelly bazaa kirashi talaka ba koda kuwa a gaban su Ammie ne ya wuci su kirasa da talaka kuma wan nan gidan nashi yafi karfin a ce ba'a ga wajen kwana ba, kawai dai Ammie su ta ɓata su da kuɗi ne suna abun da suke so shi dai Imran yana da kyakkyawar zuciya ne kawai shi yasa baya biyewa abun da Ammie ke yi musu baya damuwa da kuɗin da suke da shi

shi dai Irfan gaba ɗaya sai yaji babu daɗi sai ma yaji da bai sa Imran ya tawo da su Akil ba gashi sunzo suna yiwa bappa rashin kunya, jiki ba kwari shima Imran ya miƙe Zuwaira ta musu jagora zuwa boys quarters su Aafia kuma Nana ta kai su ɗakin kusa da na daddy Aafia Umaisha Akila, ita kuma Jelly daman gadon ta na bedroom ɗin daddy

Share fisabilillah 👏

To masu karatu sai mun haɗu gobe idan mai dukka ya kai

💞Star Lady💞

*💞TRIPLET'💞11

*💞The beginning💞*

*Episode 11*

*🛫WASHINGTON DC🛬*

*LOT 33.*

*07:30*

Iskan sanyin safiya na kaɗawa yanayin weather garin gwanin ban sha'awa, iskan na kaɗawa a hankali hankali, duk da cewa a koi sanyi hunturu amma hakan bai hana kaji daɗin iskan dake kaɗawa ba, a hankali Michael ke tattako staircase yana saukowa jikin sa sanye yake da wando 3 cutar blue da t-shirt mai laushi mara nauyi fari kal kamar yanzu ya fito da ita daga kwalin ta saboda haske ta ya ɗaura jacket blue color mai ɗan girma a saman kayan nasa, hannun sa na ɗaure da dankareriyar gold watch mai bala'i kyau da tsada sai kyalli yake yana ɗaukan ido, ya tara kyakyawan dogon gashin can nan nashi daya sha gyara ya ɗaure a bayan wuya ya zubo kaɗan ta gaban goshin sa kamar mace, fuskar nan a ɗaure tam kai da ganin sa kaga Tiger ne da gaske,

katafaren palon su a gyare tsab sai daddaɗar kamshin air freshener da sanyin Ac ke tashi, kai kace yanzu a ka zuba komai na palon saboda yadda suke tsab kamar hannu bai taɓa taɓasu ba,

kai tsaye wajen table ɗin cin abinci Michael ya nufa, wasu jigba jibgan Bodyguard ne tsaye a wajen table ɗin sanye suke cikin suit baki da glass baki a face nasu fuskar nan tasu kamar hadari a ɗaure tamau babu alama imani ko ɗigo a ransu, sun jeru yali gefe da gefe sun sanya table ɗin a tsakiyar su, bodyguard 12 ta gefen nan 12 ta gefen nan,

tun Michael bai iso wajen ba suka fara sara masa, ko kallon in da suke bai yi ba ya nufi saman kujerar table ɗin, a sukwane ɗaya daga cikin bodyguard ɗin ya ja masa kujerar baya, ya zauna, cikin sauri ɗaya daga cikin su yace cikin harshen turanci "Sir me za'a zuba maka?" Da hannu ya musu nuni da wata dan kareriyar warmer mai ɗauke da Nasville hot chicken, nan take suka fara serving na shi, nan daddy da Uncle Herry suka isko sa, da sauri bodyguard suka ja musu kujera suma suka zauna, suna zama sai ga John da Jay suka iso wajen, suma haka bodyguard suka ja musu kujera suka zauna

Cike da so da kauna daddy yace "My Tiger where is James?" ba tare da ya kalli in da daddyn yake ba yace "I don't know" cikin sauri John yace "he had gone out" shiru daddy ya ɗan yi kafin yace "Why two days ɗin nan James ke fita since morning kuma baya dawowa sai can dare" shi dai Michael bai tanka daddy ba abincin sa kawai yake ci hankalin sa kwance

waya daddy ya ɗauko ya shiga contact ya fara kiran number da a kayi saving da my lion, sai ringing wayar take amma ba'a ɗaga ba, har wayar ta katse ba'a ɗaga ba, sake kira daddy yayi, a karo na biyu ma ba'a ɗaga ba, sai a karo na uku shima sai da wayar ta kusa katsewa san nan a ka ɗaga, kara wayar a kunne daddy yayi ya tattara nitsuwar sa cike da so da kauna yace "Hello my lion" shiru a ka ɗan yi na 40 second kafin wata zazzakar voice mai tashin kai mai bala'i daɗi yace "Good morning dad" nauyayyar ajiyar zuciya dad ya sauke kafin yace "my lion how are you doing this morning?" Shiru ya ɗan yi, su Michael duk sun nitsu, shi Michael ma har abincin ya dai na ci yayi shiru ya nitsu dan yaji ko karar sa daddy zai kai, shi kam John har kerma jikin sa keyi Uncle Herry sai zazzare ido yake, Jay kam ba'a magana, ba su kaɗai ba har ta jibga jibgan Bodyguard dake tsaitsaye a kan su dan basu kulawa sai da suka kara shiga hankalin su kowannen su sai zazzare ido yake sun kasa kunne suna sauraron daddy, kowa sai addu'a yake Allah yasa ba wani abu a kan sa daddy zai faɗa ba

"What's going on daddy you called me this early morning hope there is no problem?" Lion yayi maganar cikin sanyin muryan ga sexy voice nashi mai bala'i daɗin sauraro ciki ciki yake magana kamar bai son buɗe bakin sa,

cikin sauri dad yace "I want you to investigate for me where James is out every early in the morning and coming back home in the evening" shiru lion yayi kamar bai ji me dad yace ba, bin wayar da kallo daddy yayi dan yaga ko lion ya katse kiran, bai kuma katse kiran ba ganin haka yasa daddy ya gane lion na nufin ko a koi wata matsala bayan wan nan, hakan yasa cikin sauri dad ɗin yace "There's no other problem" dad na kai karshen maganar ɗif lion ya kashe wayar sa, dogon numfashi daddy yaja tare da sauke nauyayyar ajiyar zuciya ya ɗago ya kalli su Michael da suka zuba masa ido suna jiran suji ko lion ya bashi wani sako a kansu, su kuwa bodyguard sai sauke ajiyar zuciya suke tun da sunji ba karan su dad ya kai ba

Kallon Uncle Herry daddy yayi cikin harshen turanci suke magana "Herry ina mamakin Romeo sosai yanzu, ba ma shi kaɗai ba dukkan su suna bani mamaki over" cikin sauri Uncle Herry yace "Nima dai gaskiya ina mamakin Romeo da James how comes yanzu yake ɗan respecting naka how? why?" Shiru daddy ya ɗan yi kafin yace "Tun last 5 Month ago Romeo ya fara ɗaukan kirana in yayi tafiya har ma ya min magana cikin girmamawa har ma ya tambaye ni ko a koi wani problem abun da a baya ko zan shekara ina kiran sa sai ya ga damar ɗauka kuma ban isshe shi kallo ba to why? Why suka canza haka? Ina son sanin dalili" guntun tsaki Michael yaja tare da cire hannun sa daga cikin abincin ya ajiye spoon da yar karamar wukar hannun nasa, da sauri ɗaya daga cikin bodyguard ɗin ya ciro masa tissue paper ya goge masa bakin sa, sai kwaɓe fuska Michael ɗin yake ya miƙe ya nufi hanyar fita daga palon

"My tiger what about church?" Daddy ya tambaya, ba tare da Michael ya juyo ba yace "I can't go" cikin sauri daddy ya miƙe tsaye yana faɗin "Are you mad? Are you heard what you said?" A fusace Michael ya juyo a ƙule yace "I'm not mad, I knew what I said, let me repeat it again maybe you will understand what I mean, I said i can't go anywhere, in fact as from today i can't go to the church again" tashin sense cikin sauri Uncle Herry ya miƙe yana faɗin "William ina ganin mu kira Pasto yazo yayiwa Michael addu'a dan ina ga ya samu matsala a brain nashi" Johnson ne ya cabki zancen da cewa "Yes daddy saboda ya faɗa a School wai ya dai na shan wine" jiki na rawa daddy ya ɗauko wayar sa ya shiga contact tsabar ɓacin rai har idon sa baya gani sosai,

ganin daddy zai yi kirane kuma yasan mutun ɗaya zai kira yasa Michael saurin cewa "Sorry dad rai na ne ya ɓaci amma I'm sorry today i have an exam so ba zan samu damar zuwa church ba amma gobe zanje" ya kai karshen maganar tare da ficewa daga palon yana mai jin haushi, shi ba wani abu yasa bai son zuwa church ɗin ba pace Pasto su daya tsani gani, bai son pasto ko kaɗan tun yana yaro sai an sha fama da shi yake zuwa church ɗin,

Jin abun da Michael yace yasa daddy sauke nauyayyar ajiyar zuciya tare da komawa ya zauna sai ajiyar zuciya yake ta faman sauƙewa a ran sa yana faɗin "Thank you Jesus"

*Michael*

Kai tsaye School ya nufa, sai sharara gudu yake a kan shinfiɗaɗiyar titin mai laushi wadda babu kwarzane ko kaɗan, da motar sa kirar *Aston Martin*.

Yana shiga school ya kashe Motar sa a parking space na *Harvard Square Parking Garage*, ya fito tare da Lucky Copper Winston, kai tsaye office na dr tyrian ya wuce, babu ko excuse bare jiran umarnin haka ya faɗa cikin office ɗin fuska a ɗaure, tsabar tsorata Dr har yana kokarin guduwa dan banyi expecting ganin kowa a lokacin ba,

kai tsaye wajen sa Michael ya nufa fuskar nan tasa a ɗaure tam kamar hadari dan dad ya ɓata masa rai over,

Yana zuwa ya damko wuyar rigar Dr cike da bada umarni ya fara magana cikin harshen turanci "Idan har this time ma ka faɗar dani baka bani Mark ba kasa na kara samun carry over kasa Romeo ya bani punishment idan... Michael bai kai karshen maganar ba Dr yace "A'a ni na isa ai kana rubuta Exam nan dole na baka mark" kallon banza Michael ya masa kafin yace "Chemaka a kayi zan rubuta Exam ɗin? Ni ba wani Exam da zan rubuta kai zaka rubuta min da kan ka, kuma kayi marking ka bani mark full" ya kai karshen maganar tare da sakin wuyar rigar dr ya juya ya fice daga office ɗin yana wani kwaɓe fuska, nauyayyar ajiyar zuciya Dr ya sauƙe kafin yace "Oh wan nan bala'i da me tayi kama dole muyi meeting na malamai mu san yadda zamuyi mu bawa Michael result mai kyau dan ya bar School nan mu huta" haka dai Dr ya rinƙa surutan sa shi kaɗai,

Shi kuwa Michael yana fita kai tsaye gore place ya wuce yaje ya zauna su lucky suka zauna kusa da shi.

💞💞💞💞💞💞💞💞

*KANO*

Bayan sallar issha zaune suke gaba ɗayan su a palon daddy amma ban da Akil, sai Jelly da Akila da basa wajen suna cikin ɗaki suna can Akila tasawa Jelly wan nan ta canza mata wan nan sai shiri suke kamar wayan da zasu je party

Daddy na zaune kusa da Imran da Irfan suna hira, wayar sa tayi kara alamar shigowar kira, cikin sauri ya duba wayar dan daman yana expecting na kira, Engineer Muhammad Imam shine sunan da ya bayyana a kan screen ɗin wayar jikin daddy har kerma yake wajen picking na call ɗin ya manna wayar a kunnen sa yana faɗin "Engr ya ake ciki" tsabar zumuɗi ya manta da sallama ma, daga ɗayan ɓangaren Engr yace "Congratulation sir company mu gomnati ta bawa contract na aikin nan" miƙewa tsaye daddy yayi tare da dukawa ya ajiye wayar yayiwa Allah sujudur shukur yana zubawa Allah kirari da godiya mai tarin yawa, ganin daddy yayi sujudur shukur yasa Irfan da Imran suma suka sauko suka taya sa yiwa Allah godiya ta hanyar yin sujudur shukur ɗin suma duk da basu san me ya faru ba me daddy ke wa sujudur shukur ɗin,

Daddy ya ɗan jima yana yiwa Allah godiya kafin ya ɗago ya ɗauki wayar sa yayi ta zubawa Engr Muhammad Imam godiya da fatan alkhari, san nan sukayi sallama ya katse kiran,

cike da murna ya sanar da su Imran abun da ya faru, sosai suka taya shi murna da yi masa fatan alkhari, sosai suka ji daɗi su Aafia duk sun masa addu'ar fatan alkhari yaji daɗi sosai,

Cikin wan nan farincikin Jelly da Akila suka fito daga bedroom suka same su, jelly tasha make up mai bala'i kyau Akila ta sanya mata wandon jeans blue mai stone a jiki sai yar karamar riga mai karamin hannu pink color tayi kyau sosai da sosai,

wow shi ne abun da Imran ya iya furtawa kenan, kyau iya kyau Jelly tayi Akila ta tsantsara mata kwalliya, sosai Aafia da Umaisha suka zuba mata ido dan Jelly ba baya ba wajen kyau bare kuma kyan ya haɗu da make up kai Masha Allah, kasa jurewa Imran yayi yana bala'i son Jelly tun tana yar jaririya, miƙewa yayi ya riƙo hannun ta yana jin kamar yace daddy ya ɗaura musu Aure yanzu sai a barta sai ta girma sai yazo ya ɗauki matar sa dan gani yake kamar za'a kwace masa ita tun da shi ba'a kano yake ba, shi ma daddy ya lura da halin da Imran ɗin ke ciki da kuma abun da yake so sai dai ba zai iya yiwa Jelly aure a haka ba har sai ta mallaki hankalin kan ta ta girma ta faɗa da bakin ta a lokacin tana son Imran ɗin, dan tayu yanzu soyayyar yarinta ne kar ta girma tazo ta canza raayi,

shi dai Irfan sai murmushi yake yi abun sa yana yiwa Imran fatan alkhari shi da Jelly a zuciyar sa, sai shagwaɓa Jelly ke zuba musu Imran na biye mata ita kuwa Akila na musu video, sai murmushi dad yake yana addu'ar Allah ya cika masa burin sa ya aurar da Jelly ga Imran, Aafia tayi nadamar cewa Jelly mummuna da tayi ashe kwalliyar da daddy ya matane yasa tayi muni ashe kyakyawace ajin farko,

Akila na tsaka da yi wa su Imran video wayar ta ta fara kara alamar kira ya shigo, Yaya Akil shi ne sunan da ya bayyana a kan screen ɗin wayar, cikin sauri ta ɗauki call ɗin tare da kara wayar a kunnen ta tana faɗin "Hello yaya Akil" a ta kai ce yace "Bawa yarinyar nan wayar" shiru ta ɗan yi kafin tace "Wace yarinya kuma yaya Akil?" Dogon tsaki yaja kafin yace "Wan nan mai kama da Abba mana" ɗago ido Akila tayi ta kalli Aafia da Umaisha dan ta ga waye kuma mai kama da Abban su a cikin su, sai taga ashe Umaisha ce mamaki ne ya kamata ko yaushe yaya Akil ya ga Umaisha har yasan tana kama da Abba kuma ohon masa mutun kaman wani mai juju a kai, tayi nisa cikin tunani sai jin muryan Akil tayi yana faɗin "Ba da ke nake bane?" Yar firgigit tayi tare da miƙawa Umaisha wayar, ba musu Umaisha ta ansa tare da mannawa a kunnen ta tana faɗin "Waye ne?" Cikin tsawa Akil yace "Ni kike tambaya waye Ni?" Kallon Akila Umaisha tayi dan ita har lokacin bata san da wa take magana ba bata ɗauki muryan sa ba tun da yau suka taɓa haɗuwa kuma yau ɗin ma ba wani magana sosai yayi da su ba,

Kasa tayi ta murya cikin girmamawa tace "Kayi hakuri ni ban san waye kai ba ne shiyasa nake tambaya" a ta kaice cikin faɗa yace "Mijin kine to, idan kin koma ki sanar da mahaifin ki idan na samu time zan zo a ɗaura aure!!" tashin sense shi kuma Akil kalar nashi soyayyar kenan, waro ido waje Umaisha tayi muryan ta na sarkewa tace "Akila amma wan nan mahaukaci ne kika haɗani da shi ko?" Waro ido waje Akila tayi su daddy kuma sun zubawa Umaisha ɗin ido

hannu Irfan yasa ya amsa wayar, yana bin screen ɗin wayar da kallo, ganin an rubuta Yaya Akil ne yasa Irfan ya sanya wayar a hand-free, cikin tsawa Akil yace "Ke ni kike cewa mahaukaci dan zan rufa miki asiri to wallahi ko kina so ko baki so sai kin aure ni gwara ma ki sani tun wuri idan kin koma ki sanar da mahaifin ki idan na samu time zanzo na kawo sadaki na ɗauke ki, amma kafin nan dole kullun sai munyi waya kuma idan na kira baki ɗaga ba wallahi zakiyi dana sani, gobe kafin na tafi zan sayo waya na kawo miki dan naga kamar baku da karfin sayan waya kina jina ko? Idan kika kuskura kika min taurin kai Allah zan sa a ɗauko ki a kawo min ke a daren nan na kira limamin masallacin mu a waya ya fita ya tara jama'a ya daura mana aure kuma zama dani ya zama maki dole!!" Tashin sense shi dai daddy abun ma dariya ya bashi yau ga ikon Allah soyayya dole aure dole, yau Aafia taji abun da yafi karfin ta shi kan Irfan ya rasa bakin magana dan Akil yafi karfin sa, Imran ne yayi ta maza ya amsa wayar yana faɗin "Sannu Akil idan ma son ta kake ta haka ake ansar soyayya?" cikin masifa Akil yace "Yaya Imran babu ruwanka dani ni ba son ta nake ba Auren ta zan yi kuma dole a aura min ita dole kuma ta zauna dani tana min aiki da biyayya dan daman da yar aiki take kama yar datti ma irin ta!!" ita dai Umaisha yau taga tashin hankali shiru tayi ta sunkuyar da kan ta kasa,

a kule Imran yace "Okey yar datti ko to ka bar mana yar dattin mu idan ka sake kiran ta a waya Allah sai na ɓallaka zan ga wanda zai nema kama auren nata wallahi ko bappa ya baka ita sai na hana" cikin fushi Akil yace "Kai yaya Imran waye yace maka ni ina neman izin daga wani wai bappa ya bani Auren ta? Kai ka san wani abu wai izini ni ban san shi ba, ni abun da na sani shine dole a bani ita ko anki ko anso idan ba haka ba kuma muzuba mu gani kasan sauran" ya kai karshen maganar tare da katse kiran salati dad yasa yana faɗin "Anya Akil baya shan wani abu kuwa?" Girgiza kai Imran yayi yana faɗin "Wallahi daddy baya shan komai shi dai haka yake komai da karfi da izza yake cewa zai ansa shi bai san wani abu wai bada hakuri ko lallaɓa mutun ya baka abu ba, a'a shi yana ganin kamar komai kuɗi na iya saya shi yasa sai yace komai da izza da kuɗi zai ansa" jinjina kai daddy yayi kafin yace "Yarantace zai daina idan yayi hankali" shiru Imran yayi yana tunani,

dafa kafadar Imran ɗin Irfan yayi yana faɗin "Karka damu my bro ni nasan yarinta ke damun Akil" kallon su Umaisha da sukayi mutuwar zaune Imran yayi kafin yace "Sister kuje daki ku kwanta ko tun da already kun ci abinci" ba musu suka miƙe suka wuce bedroom nasu palon ya rage daga daddy Irfan sai Imran ita ma Jelly ta wuce bedroom na daddy

dawo da kallon sa kan Irfan Imran yayi cikin nitsuwa ya fara magana "Irfan tun da kaji Akil yace zai auri Umaisha to tabbas da gaske yana son tane kuma in har ya kai wa Ammie da Abba maganar nan tofa mai iya hana wan nan auren sai dai Allah, dan ko bappa yace ba zai bawa Akil Umaisha ba Abba yana iya sawa a ɗauko ta kuma a aure mata Akil a gaban bappa ba yadda ya iya, ni duk wan nan bashi ne damuwa ta ba Akil yaro ne bai wani mallaki hankalin kan sa sosai ba 22 years yake da shi san nan bai san yin abu a hankali ba shi komai da izza da karfi yake kwata bai san girman nagaba da shi ba baya girmama mutane ba zai taɓa ganin darajar sister ba a wulakance zai riƙe ta na san halin sa sosai tabbas yana son ta tun da har ya iya cewa zai aureta amma duk da wan nan son da yake mata ba zai taɓa riƙe ta da daraja ba dan bai san darajar ɗan adam ba kullun cikin faɗa muke da shi a kan hakan, nike gaba da shi amma saboda wan nan banzan hali na sa yasa na sallama masa girman yana da jiji da kai ga izza da masifar faɗa ga ɗaukan zafi zuciya da rashin kunya duk ya haɗe komai, zan yi iya kan bakin kokari na wajen naga na gyarashi ya zama mutun, nasan zai sai wa Umaisha waya kamar yadda ya faɗa to dan Allah Irfan ina neman alfarman da ku kyaleta ta rinƙa magana da shi a hankali hankali har mu samu ya sauya tun da yana son ta In Sha Allah idan suna waya zamu iya samun wani sauyi" jinjina kai Irfan yayi yana faɗin "Karka damu ɗan uwana" sai murmushi daddy ke yi yana yabawa Imran a ransa, daga haka suka miƙe suka nufi table ɗin cin abinci daman already su Aafia sun ci nasu abincin tun kafin su daddy su dawo sallar issha.

💞💞💞💞💞💞💞💞

*KADUNA*

Wata hajiya ce zaune cikin wani katafaren palo na alfarma mai ɗauke da manya manyan sofa set, set 2 launin Ash da baki ga Makekiyar Tv plasma manne a bango, daga ɗan gefe hadaɗiyar table ɗin cin abinci ne mai matikar kyau mai ɗauke da kujeru 6, daga kusa da table ɗin staircase ne mai kyau a wajen ɗan gaba da staircase ɗin kofar kitchen mai girma gaske ne a wajen, gaba ɗaya curtains na palon launin Ash da ratsin baki ne kalar sofa ɗin, daga tsakiyar sofa set ɗin wata kyakkyawar Chinese carpet baki ne sai sofa table saman carpet ɗin, duk wan nan haɗuwar palon babu gyara dan ko ina a watse yake kaca kaca duk datti ga kwanikan abinci saman table ɗin duk anci an bar ragowa shi kan shi kitchen ɗin a watse yake sai warin ruɓaɓen abinci ke tashi ta ko ina a cikin kitchen ɗin gaba ɗaya ya buɗe palon da wari, ta ko ina a cikin palon ledojin takeaway da su kan su takeaway ɗin ne, palon dai ba kyan gani, zaune hajiyar nan take saman sofa mai zaman mutun 2, ba karya kyakkyawace ajin farko fara ce tas har hasken nata ma yayi wani iri kamar bata da jini a jikin ta saboda hasken da tayi, sanye take cikin wata mahaukaciyar bubu irin na larabawa masu manya manyan mayafan nan, gaba ɗaya rigar duk datti ita kan ta hajiyar warin datti take, babbar mace ce wadda a kalla zata kai 45 years sai dai tana da ɗan ƙaramin jiki wadda idan ka ganta zaka yi tunanin 25 years ko 30 years take da shi duk da bata gyara jikin nata amma yana da kyau sosai, ta ɗaura kafa ɗaya kan ɗaya tana latsawa wayar ta kirar Samsung A72, da sallama wata hajiya ta shigo palon tare da wani Alhaji na biye da ita a baya, tun daga bakin kofar shigo hajiyar ta toshe hanci tana faɗin "Subhanallah me haka kuma Hajiya yana ji wari palon" ko kallon in da suke Hajiya bata yi ba ta ci-gaba da latsar wayar ta, karisowa cikin palon suka yi suka zauna saman sofa shi kan shi Alhajin sai kwaɓe fuska yake ya tara yawu a baki ya kasa haɗiyewa "Hajiya dan Allah me ya mutu a palon nan?" Cewar hajiyar da ta shigo yanzu cikin faɗa Hajiya tace "Ke Zainab ban san iskanci fa waye ma ya gayye ku gidan nan?" Kallon Alhajin Zainab tayi kafin tace "Baban Farooq kaji ko? Sai da nace maka ba zan zo gidan nan ba ka dage sai munzo mun duba abokin ka to ga irin ta nan" ta kai karshen maganar tare da miƙewa ta fara tattara palon tana faɗin "Ni ba zan iya zama a kazantar nan ba" shi dai Alhaji ya kasa magana sai mamaki kazantar Hajiya yake ita warin ma baya damun ta tab lallai abokina na kokari wai irin wan nan abu haka, ita dai Hajiya ko kallon in da suke baya yi ba kan ta na kan wayar ta, ita kuma Zainab ta ci-gaba da da tattara palon har ta kai kitchen, wani warine ya bugo mata hanci wadda yasa ta yin baya ba shiri, cikin masifa tace "Ke dai Hajiya wallahi kinji kunya, ga yaranki nan tsab tsab da su basa son kazan ta amma ke sai uban kazan ta kamar zai kashe ki thank God ma da Allah yasa Part na yaran daban ai da kunyar da zakiji sai tafi haka" ita dai Hajiya bata tanka ba, da dai taga surutun Zainab ya ishe ta sai ta miƙe ta haura sama abun ta, dogon tsaki Zainab taja tare da wucewa ta koma cikin kitchen ɗin ta ci-gaba da aikin tana toshe hanci, girgiza kai kawai Alhaji yayi tare da ciro wayar sa ya fara latsawa ga uban yawu da ya tara a baki,

Ihu mai gigita kwakwalwa Zainab ta saki daga cikin Kitchen ɗin, a guje Alhaji ya miƙe ya nufi Kitchen ɗin, kwance ragajab ya iskota a kasa ga jini na zuba daga gakin ta idon ta sun ɗagu sama bakin ciki gaba ɗaya ya bace idon nata ya zama fari zalla, zaro ido waje Alhaji yayi tare da karisawa wajen ta yana ihu yana kiran sunan ta amma ina bata ko motsi, duƙawa yayi yasa hannu yana kokarin ɗaga ta nan take idon ta ya sauya launi zuwa Pink color san man ya sake komawa purple kafin ya koma maroon kamar jini, ihu Alhajin ya fasa sai da Hajiya ta sauko kasa da gudun gaske tana faɗin "Lafiya nake jin Ihu?" A guje Alhaji ya fice daga cikin Kitchen ɗin ya bar gidan ma gaba ɗaya, kamar wani mahaukaci haka ya dawo sai baza babban riga yake a kan titi yana gudu, daga karshe ma cire babban rigar yayi yayi wurgi da ita a kan hanya ya ci gaba da guduwa

Share fisabilillah 👏

To masu karatu sai mun haɗu gobe idan mai dukka ya kai

💞Star Lady💞

*💞TRIPLET'💞

*💞The beginning💞*

*Episode 12*

Ganin abun dake faruwa da Zainab yasa Hajiya ta fasa ihu tayi waje tana kiran mai gadi, da gudu mai gadi ya fito da toilet ba tare da ya ɗaure wandon sa ba saboda yasan halin Hajiya da bala'i masifa karta masa wani hukuncin,

Readers Also Read