Kenza eBookz

Triplets book 1 complete by star lady - Chapter 18

Triplets book 1 complete by star lady - Chapter 18

Triplets book 1 complete by star lady Chapter 18: Triplets book 1 complete by star lady Chapter 18. Rimsha na tsaka da zanen ta bata san lokacin da hawaye…

4,376 words

Rimsha na tsaka da zanen ta bata san lokacin da hawaye suka fara gangaro mata a idon ta ba, sai dai kawai taga hawayen a kan cardboard paper ɗin suna zuba, cikin sauri ta sanya hannu a firskar ta dan taji da gasken kuka take, jin da gaske hawaye ne yasa tayi saurin gogewa ta ci-gaba da design nata, nan take taji kan ta na sara mata kamar zai fashe, idan ta tuna daddy yace kar a sake kallon GAR sai taji kan ta ya kara sara mata da karfi kamar zai fashe, a haka ta jure ta ci-gaba da zanen yayin da ita kuma Gwaggo ta kafe Tv da idon ta, tana kallon Arewa 24,

Sosai Rimsha ta kawata kyan GAR a ranta kuma haka ta fito da shi fili ta zana a cardboard paper ta, wow gashi daman ta kware a fannin zanen, abun ba'a cewa komai, zanen yayi kyau over ta tsara kyan sa iya son ranta har da sanya masa pink lips, da pink color na zane ta zana shi ya fita kamar ki kirashi ya amsa, nan take murmushi ya kubce mata ta kura masa ido cikin ranta tana kawata kayan sa yafi haka

Babu ko sallama Jehan ta shigo palon ta fito daga wajen motsa jiki, sanye take cikin wando skin tight baki da riga irin na yan kwallo shi ma baki, sai zufa take haɗawa da alama ta motsa jiki sosai, ko kallon in da su gwaggo suke ba tayi ba ta wuce zata haura sama, cikin sauri gwaggo tace

"Jehan ke dai ba zaki dai na wan nan abin ba ko? Wai ma da kika dage kike wan nan shirmen waye ya faɗa miki a gidan nan a koi wan da zai kyaleki kiyi aikin ɗan sandan?" Guntun tsaki Jehan taja kafin tace "Wai ke gwaggo ina ruwan ki da ni? To sai ki hanani yin abun da nake so ɗin mu gani, aikin ɗan sanda nake so ko kuma aikin jarida, kai ni nafi son aikin ɗan sandan ma kuma zanga wanda zai hana ni, Kinga gwaggo wlh ki fita sabgata idan ba haka ba ina fara aiki kece mutun na farko da zan fara sanyawa a cell in ce kina dillancin kwayoyin maye kuma ba wanda ya isa ya fitar da ke dan har kwayar sai na nemo na sanya miki cikin jaka dan a ji daɗin kama ki" waro ido waje gwaggo tayi tana faɗin "Sabon topic yau kuma, tohh a ina kuma kika koyo wan nan sabon topic ɗin kuma yau? A ba shakka dole ne kiyi aikin ɗan sanda, tun yanzu kin iya shirya sharri kiri kiri a'a Allah ya bada Sa'a Allah baki hakuri ni Aishatu jeki yi wanka da yamma ma ki kara motsa jiki abun ki daga nan sai koyan harɓi, daga nan sai kaki dan duk wani muna furci na yan sanda kam kin iya shi ba sai kin koya ba kai tsaye kawai zaki shiga aiki" sai murmushin dole Rimsha ke musu dan gwaggo da Jehan basu rabuwa kuma basu haɗuwa

Tsaki Jehan taja ta nufi sama tana faɗin "Ai na zaci zaki yi wata magana ne da kin ga yadda ake tsiya kuwa" shiru gwaggo tayi dan tasan halin Jehan ba sauki yanzu sai ta sa hawan jinin ta ya tashi, miƙewa Rimsha tayi tana faɗin "Gwaggo let me go and sleep I'm feeling headache" zaro ido waje Gwaggo tayi tare da jawo ta jikin ta tana faɗin "Sorry Allah ya baki lafiya" ta kai karshen maganar tare da manna mata kiss a goshi, kakalo murmushi Rimsha tayi kafin ta miƙe daga jikin gwaggo ta haura sama ta nufi bedroom nasu

Ko da ta shiga bedroom ɗin nasu Jehan na toilet tana wanka, hayewa saman gadon ta tayi ta kwanta ta shige lallausan bargon ta ta rufe jikin ta dukka har kan ta, san nan ta rungumi zanen GAR da tayi ta fara ruwan hawaye kasa kasa tana faɗin "Me yasa daddy zaka hana ni kallon sa?" Sosai take hawaye wani na bin wani, nan take zazzaɓi mai zafi ya rufe ta ga bala'i ciwon kai mai tsanani, a haka barcin wahala ya ɗauke ta,

koda Jehan ta fito daga toilet, bata ma lura sa Rimsha ɗin ba, ta wuce taje ta shirya cikin jallabiya irin na shan iska nan Black colar, ta saki gashi har baya san nan ya haye saman gadon ta, tajawo wayar ta ta shiga latsawa tana murmushi tana addu'ar Allah ya cika mata burin ta na zama yar sanda.

_______________________________

*KADUNA*

03:00 pm

Gaba ɗaya su Abbi suna zaune a Palo Irfan ya gama shirye shiryen tafiya Uk on Monday zai wuce, sai murna yake while su Aafia na taya sa, sai hira suke cike da kaunar juna, kowan nan su fuskar sa ɗauke da murmushi.

Da sallama mai gadi ya shigo palon, Abbi da Irfan har suna haɗa baki wajen amsa masa sallamar tasa "Lafiya mai gadi" cewar Irfan, cikin girmamawa mai gadi yace "Wani bako ne yazo yace na kira masa matar sa, shine na tambaye sa waye yace bai sani ba idan naje kawai nace a na kiran matar Akil tasan kan ta" tashin sense kallon su Aafia Abbi yayi kafin yace "Yau she ku kayi aure ban sani ba? Dan ku kaɗai ne mata a gidan nan" Jinjina kai Irfan yayi kafin yace da mai gadi "Je kace ya shigo" da sauri mai gadi ya wuce ya koma bakin gate, shi kuma Akil ya dawo da kallon sa kan Abbi cikin nitsuwa ta fara yiwa Abbi bayanin abun da ke faruwa ta sigar da zai fahimter, shiru Abbi ya ɗan yi kafin ya ɗago yana kokarin yin magana mai gadi ya dawo bakin sa ɗauke da sallama.

"Ina yake?" Irfan ya tambayi mai gadi, Mai gadi yace "Oga yace wai in ce muku idan shiga gidan yake son yi ai ba sai an masa iso ba, ba sai an bashi izini ba yasan hanyar shigowar dan haka bai da niya kawai in ce matar sa tazo yanzun nan ya bata 2mins" shiru Irfan ya ɗan yi na yan seconni kafin yace "Shike nan jeka abun ka, ke kuma Umaisha ta shi kije" Abbi zai yi magana Irfan yayi saurin cewa "Dan Allah Abbi kayi hakuri na yau kawai zan ga gudun ruwan sane" shiru Abbi yayi bai yi magana ba, miƙewa Umaisha tayi jiki a mace cike da jin kunya ta haye sama.

Jim kaɗan ta fito sanye da yar karamar gyale a jikin ta tazo ta wuce su Abbi kunya kamar ta shige cikin kasa haka ta nufi waje, ba karya da Abbi yaji Akil na son Umaisha yaji daɗi sosai ko ba komai zasu kara dankon zumunci, amma sai dai yana tausayawa Umaisha ɗin dan yasan zama surukar hajiya Umaiya ba karamin abu bane sai wanda ya shirya dan masifaffiyar mace ce lamba ɗaya, sai dai duk masifar ta sai ka taɓo ta san nan kuma idan tana son ka zaka ji daɗi dan tana da kyau ta over ga wadda tayi niya, kuma tana da kirki ga wadda take so.

Baki ɗauke da sallama Umaisha ta isa wajen sa, yana tsaye jikin motar sa ya bawa gidan nasu baya ya Kifa kan sa a jikin motar kamar mai tunanin wani abu, yau sanye yake cikin dakakkiyar shadda milk color mai bala'i tsada ɗinkin ta zauna a jikin sa sosai, half jomfa a ka masa yasha hula kamar ustaz,

jin sallamar ta yasa ya juyo cikin nitsuwa, kallo ɗaya ya mata ya ɗaure fuska sosai kamar bai san Menene dariya ba, a kule yace cikin tsawa "Ki koma kije ki sanya hijabi!! Kuma idan kika kuskura na sake ganin ki ba hijabi sai ranki ya ɓaci!!" Ya karisa maganar kamar zai wanka mata mari saboda haushi, murya na rawa tace "Kayi hakuri yaya Akil bani da hijabi ne shi yasa, duk wanda yaya Irfan ya saya mana na kyautar da yaya Irfan ya koma Zaria lokacin" a fusace ya ɗaga hannu har zai mareta sai kuma ya fasa cikin fushi yace "Shiga mota muje" cike da tsoro tace "Ina zamuje?" Shiru ya mata kamar bai ji me tace ba, ganin haka yasa tace "To bari na faɗa wa su Abbi sai nazo mu tafi...bata kai karshen maganar ba taji saukan mari a kumatun ta, rai a matukar ɓace yace "A matsayin kanwa na mareki ba mata ba, ke har kin isa nace muje kice min ina zamuje, san nan kuma daga yau idan nace kiyi abu kika ce min bari ki tambayo wani Allah sai ran ki ta ɓaci, dan ba wanda zaki tambaya ida zakiyi abu sai nine, nine mijin ki ke mallaki nane, ni kaɗai nake da iko da ke, ba wanda ya isa ya nuna min abun da zan yi a kan ki, dan ke ɗin mata tace!!" Ya kai karshen maganar tare da ciro handkerchief daga aljihun sa ya miƙa mata a kan ta goge hawaye, a hankali ta sanya hannu tana hawaye zata ansa handkerchief ɗin, ganin tana abu a hankali zata ɓata masa lokaci ne yasa, ya sanya hannun sa da kan sa ya goge mata hawayen yana faɗin "A matsayin kan wa nake miki hakan" bayan ya goge mata hawayen da kan sa ya buɗe mata motar ta shiga gidan gaba san nan shima ya zagaya ta ɗayan gefen ya shiga ya tada motar suka bar wajen.

Kai tsaye *ABC supermarket* suka nufa, yana tuki yana zuba mata kashe di da dokokin irin kayan da zata rinƙa sawa, gaba ɗaya yayin cancel ɗin gyale a cikin kayan ta, haka riga da wando yace kar ta sake sawa sai tazo gidan sa, san nan attachment da eyelashes duk ya hana yayi cancel, hijabi har kasa ya yarje mata tarinƙan sawa idan zata je school, dokoki kala kala iri iri ya kafa mata, tare da kashe din idan ta karya masa doka ɗaya zatayi bayani sai ranta ya ɓaci, ita kuwa cikin ranta cewa take "zan dai na duk abun da ka hana amma wlh ban da sa gyale, sai na sa in dai gyale ne sai dai ka kashe ni" shiru yayi bai sake magana ba har suka isa super market ɗin

cike da bada umarni yace "Ki zauna a nan karki yarda ki leka waje" ya kai karshen maganar tare da ficewa daga Motar ya nufi cikin super market ɗin, sai tsaki take ja, a kule tace "Sai an sa gyale mugu kawai"

Haka tayi ta surutan ta ita kaɗai, har ya dawo hannun sa rike da ledoji manya manya guda biyu, ba tare da ya mata magana ba ya ajiye a gidan bayan motar san nan ya shiga gidan gaba, ya tada motar kai tsaye suka wuce *kasuwar barci* a nan yaje da kan sa ya zaɓa mata manya manyan hijabai wadda yana da tabbacin zasu kai mata har kasa, dan a wan nan karon ma a mota ya barta ya hana ta fita, hijabi 12 ya saya mata manya manya har kasa san nan ya sayawa Aafia ma 12 ya wuce ya dawo mota, yana zama wayar sa ta fara kara, guntun tsaki yaja tare da ɗauko wayar ya duba, a nutse yayi picking call ɗin yana faɗin "Sorry Abla na manta ne amma bari na sa miki yanzu, sai yaushe zaki zo ne?" Daga ɗayan ɓangaren Abla tace "Yaya Akil wai ina yaya Imran ne? Sai kiran sa nake amma baya ɗagawa" kallon face ɗin Umaisha yayi ta cikin mirror motar kafin yace "Abla ni bana gida na fita da Auntyn ku amma idan na dawo zan duba miki me yasa baya ɗaukan kiran, amma dai koma me kin dai san ba da gan gan yaki ɗauka bako?" Da sauri Abla tace "Yaya Akil Auntyn mu kuma? Jinjina kai yayi yana faɗin "Eh Auntyn ku" cikin zumuɗi tace "Dan Allah yaya Akil ka bata waya mu gaisa" "Me zaki faɗa mata?" Shagwaɓa murya tayi kafin tace "Kai yaya Akil gaisawa kawai zamuyi" girgiza kai yayi yana faɗin "A'a ai na sanki ne da iya yi" "Kai yaya ba wani iyayi Allah" sanya wayar yayi a hand-free san nan ya miƙa wa Umaisha, jikin ta har kerma yake wajen ansar wayar tana faɗin "Assalamu alaikum" da murna Abla tace "Waalaikumussalam Auntyn mu ina wuni?" Kallon sa ta kasan ido Umaisha tayi kafin tace "Lafiya lou Aunty Abla yasu mama?" kunna motar sa yayi ya ɗauki hanya yana sauraron hirar tasu

Sai murmushi Umaisha ke yi, Abla tace "Auntyn mu waye baban ki? Yar gidan sarki ne ke ko yar governor? Dan nasan yaya Akil ba zai zaɓo mana yar gidan kananan mutane ba" nan take face ɗin Umaisha ta sauya ta dai na murmushi jiki a mace tace "Ni ba...bata karisa ba ya ansa wayar cikin faɗa yace "Abla abun da zaki tambaye ta kenan? Wan nan tambayar ni zaki yiwa ai ba ita ba" murya na rawa Abla tace "Kayi hakuri yaya Akil" tsawa ya daka mata "Abla kullun ina faɗa miki ki ɗauki duniya da sauki ki dai na jin zancen Ammie a kunnan ki baki ji ko? Kullun sai na faɗa miki ki dai na cewa kina kyamar talakawa amma baki ji ko kaɗan ko? Ya miki kyau to ba yar kowa bace yar talakawa ce, kuma a haka nace nake so ko akoi wadda ya isa ya hanani auren zaɓin rai na ne?" Murya har sarkewa yake tace "Kayi hakuri yaya Akil tuba nake" dogon tsaki yaja tare da katse kiran, shiru Umaisha tayi tana tunani "Ashe daman yaya Akil yana da hankali, ashe kawai zafin rai gare sa ba wai rashin hankali ba Allah sarki, Allah ya sassauta masa zafin kan nan da zuciyar nan tasa"

shiru sukayi dukkan su, ba wanda ya sake magana har suka isa kofar gida, ya kashe motar sa ya fito ya ɗauka mata ledojin dan yasan ba zata iya ɗauka ba

suna shiga harabar gida a nan suka isko Abbi da Irfan da Aafia, suna tsaye cirko cirko saboda da sukaji Umaisha shiru bata dawo ba shi sukazo su leka ko tana wajen ganin bata nan shine suka tsaya suna tattaunawa ta ina Irfan zai je neman ta

ganin su yasa Umaisha ta tafi da sauri ta faɗa jikin yaya Irfan tana ɓoye fuska dan ita a koi ta da kunya sosai, har gaban su Abbi yazo ya ajiye mata ledojin cikin girmamawa yace "Sannu ku ina wuni uncle" da fara'a Abbi yace "Lafiya lou Alhadulillah ina kuka je ne na fito ban same ku ba?" Juyawa Akil yayi ya bawa Irfan hannu yana faɗin "Yanzu dan na fita da matata sai na faɗa wa wani in da na kai ta, wan nan sirrin mune ai" tashin sense kallon Irfan Abbi yayi kafin yace "Ni kam Irfan ko dai ka aurar da Umaisha ban sani bane?" Wuce Akil yayi abun sa ya nufi gate yana faɗin "My wife sai mun yi waya" kallon sa Irfan yayi har sai da ya fice san nan yace "Umaisha ku kwashe kayan kuje ciki" cikin sauri suka kwashe kayan da sauri suka wuce ciki Aafia tana ta kallon Umaisha tana jiran suje ɗaki ta tambaye ta ina Akil ya kai ta

Gyara tsayuwa Irfan yayi cikin nitsuwa ta fara magana "Abbi kayi hakuri haka halin Akil yake muna masa fatan yayi hankali ta dalilin Umaisha mun yi magana da Imran a kan hakan san nan kuma Abbi idan ka lura yaro ne fa 22 years yake da shi" cikin fushi Abbi yace "A'a wlh bai isa ba wan nan iskanci ba zan ɗauka ba, bai isa yazo ya min wan nan iskanci a gida ba ya ɗauki yata lokacin da yake so ya fita da ita san nan ya dawo da ita lokacin da yake so in masa magana yace min shi da matar sa to a yau she ta zama matar sa? Wlh idan yamin tsiya sai na haramta masa auren Umaisha in ga wanda ya isa ya sa na bashi ita, ya koma ya tambayi yaya cikin kannen sa waye mai zafi ma faɗa ci zai faɗa masa, daga yau ka sanar ma sa idan ba zai shigo cikin Palo yayi hira da Umaisha ba to ya bari bana bukata daman bance masa tana neman mijiba kwata kwata ma nawa tace 15 years fa gare ta zai fara koya mata wasu ɗabiun ya sauke min ya daga tarbiyar dana ɗorata to bai isa ba yaya ma yayi kaɗan a kan wan nan zance bare shi, kuma nayi cancelled fita da Umaisha suje wani wajen, idan wani abun yake son nuna mata ko ya saya mata to sai dai yaje shi kaɗai ya dawo ya kawo mata nan!!!" Shiru Irfan yayi dan yasan halin Abbi yana da saukin kai da fara'a amma idan a ka taɓosa yana da zafi sosai, yana da faɗa kuma wan nan karon a kan gaskiya yake faɗar sa dole su nunawa Akil Umaisha na da daraja dole su saya mata kima

Wucewa Abbi yayi ya shige cikin palo ransa a matukar ɓace, jiki ba kwari Irfan yabi bayan sa, ko da ya shiga palon Abbi ya wuce bedroom na shi, shi ma sai ya wuce bedroom na shi jiki a mace.

A ɓangaren su Aafia kuwa, suna shiga bedroom na su da murna Aafia ta fara watsa kayan tana fitarwa, ganin manya manyan hijabai ne yasa taja dogon tsaki ta ture ledojin, ta jawo wan da ya sawo daga super market tana faɗin "Lallai Umaisha kina da babban aiki a gaban ki wan nan hijabai dukka lallai kina ruwa" da sauri Umaisha tace "A'a Aunty Afi muna dai ruwa, dan hijabai ɗin ba nawa ni kaɗai bane, nawa 12 naki 12 ne ai" zaro ido waje Aafia tayi kafin tace "Sannu Uban na wlh bai isa yace zai sani sanya hijabi ba, ina ruwan sa ma dani tab aiko gyalen ma sai na ga daman sawa in ga uban da ya isa ya sani sawa, shegen idon sa kamar na duji" dariya Umaisha tayi tana faɗin "Ni fa da yace naje na sanya hijabi har karya na masa nace bani da su, na ɗauka zai kyaleni yace na ci-gaba da sa gyalen, amma sai na ga akasin haka ya tasani a gaba mukaje kasuwa ya kwaso min wan nan abubuwan dukka dan iskanci" ta kai karshen maganar tare da kwanciya saman gadon, tsaki Aafia taja tana fitar da abubuwan cikin ledojin super market ɗin, chocolate ne kala kala dasu hollandia milk su biscuits sweet da sauran kayan kwalama, nan Aafia ta ware wanda zata ci lokacin ta tattara sauran ta zuba su cikin bedside drawer, ta tasa wadda ta ware a gefe kuma tana ci suna yar hiran duniya.

__________________________________

*WASHINGTON DC*

Jay

Yana komawa ya zauna saman kujerar table ɗin yana sauke ajiyar zuciya ba tare da yayi magana ba, tun da daddy yaga haka sai bai tambaye sa ina Romeo ɗin ba, yayi shiru suka ci-gaba da cin abincin su.

Kallon Micheal James yayi cikin kulawa yace "My bro bana son ka rinƙa yin irin abubuwan nan da kake yana da kyau kayiwa sauran mata adalci, mum daban suma sauran mata daban, ba dukka suka taru suka zama ɗaya ba, ba wai ina faɗa maka haka bane dan ka kula mata ko wani abu no nima bani da lokacin kula mace kwata kwata a rayuwa ta, ba kuma ina faɗa maka hakan bane ko dan ka yarda da mace ko kuma mum batayi laifi ba, no mum tayi babban laifi, wadda ta cancanci mu tsaneta kuma dole mu kasa yarda da mata saboda abun da mun tayi ta cutar da zuciyar mu ta sa mana tabon da ba zai goge ba, amma yana da kyau ka cire tsanar su a ranka, dan wani lokaci suna da amfani, kuma ina son kayi hakuri ka shirya muje New York mu gaida mum gobe, please na san bata da burin da ya wuce ta gan mu, ba wai dan wani abu zamu je gaishe ta ba sai dan sada zumunci, ba wai dan muna son ta ko zamu yafe mata ba a'a kawai yana da kyau ne muje ɗin, shekara 18 kenan rabon mu da mugan ta fa tun da tazo sau ɗaya daddy ya koreta bata sake zuwa ba why mu ba zamu je ba?" Miƙewa Michael yayi tare da buga table ɗin cikin fushi yace "I told you to stop talking about that human for me!! I said I don't like, wai a na dole ne? Nace bana son jin zancen wata mata ni bani da uwa daddy shi ne kawai duniya ta, karka sake cewa muje wajen wata mummy idan kuma ka sake wlh barin muku gidan zanyi!!!" a fusace Shima daddy ya miƙe rai a matukar ɓace ya fara magana "be careful James, idan ka sake mana maganar wata shashashar mata a nan sai ranka ya ɓaci, bamu son ta kuma babu in da zaku je, idan ma ka sake maganar ta to sai dai ka nemi wani uban ba ni ba" ya kai karshen maganar tare da rungume Micheal yana rarrashin sa yana ɗan bubbuga masa baya

Share fisabilillah 👏

To masu karatu sai mun haɗu gobe idan mai dukka ya kai

💞Star Lady💞

💞 TRIPLET'S💞 18

https://chat.whatsapp.com/Fv91yECNmlW3W0mQG2hGSo

*THE BEGINNING*

💞*STAR LADY*💞

EPISODE 18

*Washington DC*

a fusace Shima daddy ya miƙe rai a matukar ɓace ya fara magana "be careful James, idan ka sake mana maganar wata shashashar mata a nan sai ranka ya ɓaci, bamu son ta kuma babu in da zaku je, idan ma ka sake maganar ta to sai dai ka nemi wani uban ba ni ba" ya kai karshen maganar tare da rungume Micheal yana rarrashin sa yana ɗan bubbuga masa baya, girgizar kai James yayi kafin ya miƙe tsaye cikin fushi ya bar palon, yana jin haushin abun da mum ta musu da kuma irin tsanar da Romeo, daddy, Michael, Tga, uncle herry, suka mata.

A gefen su Michael kuwa komawa daddy yayi ya zauna shi ma Michael ya koma ya zauna,

"Micheal where is your exam card?" cewar Jay yayi maganar yana tsare Michael da ido, a kule Michael yace "Wai Jay meye ruwan ka da ni ne? A koi wani business ne tsakanin mu?" Dariya Jay yayi yana faɗin "Michael baka da gaskiya" a fusace Michael ya buga table ɗin ya fara sunfa uwar masifa ta in da yake shiga ba ta nan yake fita ba sai dannan sa su daddy suke, cikin wasa John yace "Kai Micheal is it not our brother? kake masa tsawa haka" cikin fushi Micheal ya danko wuyar rigar John yana kokarin yin magana sukaji takun tafi daga bayan su, wadda ko basu juya ba sun san mai wan nan takun, a sukwane Michael ya saki wuyar rigar John ɗin tare da tattara nitsuwar sa waje guda, gaba ɗaya palon yayi tsit, duk wani halitta mai rai a palon sai da ta nitsu tsit kamar ba kowa.

A hankali yake sako kafar sa yana taka staircase ɗin kamar bai san taka kasa matashi ne mai jini a jiki farine tas farin Bature dogo ne sosai mai faffaɗar kirjin kamar wani zaki yana da murɗadɗen jiki wadda kallo ɗaya zaka masa kasan yasamu training mai kyau ya koshi da training, ɗamtsen hannun san nan kamar zasu fashe saboda horon da ya ke bawa kan sa, sanye yake da wando guntu 3 cutar hakan ne ya bawa kyawawan kafofin sa bayyana ga wasu gashi dark black mai tsantsi da laushi kwance a kyawawan fararen kafofin nasa har izuwa idon sahu na kafar sa hakan ba karamin kyau ya kara masa ba, yana sanye da riga mai ƙaramin hannu hakan ya bawa tuma tuman ɗamtsen hannun sa damar bayya kamar zasu fashe saboda horo, ga wasu kyawawan gashi dark black sai sheki suke kwance a hannun na sa har izuwa idon sahu na hannun sa, kasan cewar a komai face mask a face nashi baka ganin face na shin sai dai dara daran light blue eyes na shi masu bala'i kyau da ɗaukan hankali gwanin burgewa, yana da dogayen gashin ido kamar ya sa eyelashes, gashin geran sa kuwa a cike suke kamar zasu haɗe saboda cika gasu a kwance luf kamar an zana masa sai sheki da kyalli suke, sai faman lumshe dara daran light blue eyes na shi yake kamar mai jin barci, lallausan dark black curly hair sa da ya sha gyaran nan kuwa ya ɗaure a bayan sa, kaɗan ya zubo masa ta gaban goshin sa, hakan ba karamin kyau ya kara wa face nasa ba, ya kara kawata kyan sa sosai ya fito da face ɗin gwanin ban sha'awa da burgewa, soft skin nasa nan kamar ka taɓa jini ta fito saboda kwanciya da laushin da yayi yaji hutu kamar bai taɓa fita waje ba, kyawawan fararen kafofin sa na sanye cikin wani haɗaɗiyar bedroom slippers mai bala'i kyau da laushi jikin takalman duk gashi kamar gashin jikin mage, san nan yana da dogayen yatsun kafa da na hannu farare tas mai ɗauke da kumba (farce) farare tas kamar audiga yatsun nashi a koi lallausan bakin gashi mai tsantsi kwance a kan su haka zalika yatsun hannun sa dogaye ne sosai suna da ɗan kauri kaɗan masu ɗauke da kumba (farce) farare tas kamar audiga, yana da kwantatciyar lallausan bakin saje a gefen kumatun sa har izuwa gemun, sai dai bai bar gemu ba, a hankali yake takowa kan sa na duƙe kan wayar sa kirar *falcon Supernova IPhone 6 pink diamond* wadda a kalla kuɗin ta ya kai ($48.5 million) a hankali yake latsa wayar kamar baya son taɓa screen ɗin wayar, hannun sa na ɗaure da dangareriyar gold watch irin na hannun su Michael sak. Duk in da ya sanya kafar sa, sai wani kyakkyawan ƙaton karen sa dake gefen sa mai suna Brady ya sa na shi kafar. Brady irin manya manyan karen nan ne masu gashi ajiki sosai wadda yake har kasa duk in da Romeo yayi taku ɗaya sai Brady ma yayi taku ɗaya, tun bai karisa shigowa palon ba wan nan daddaɗar fitinanniyar kamshin perfume na shin ta kauraye ko wani lungu da sako na cikin palon, sai shakan kamshin bodyguard nasu ke yi suna lumshe ido, dan kamshin perfume na shi number ɗaya ne a duniya wajen daɗi

Readers Also Read