Triplets book 1 complete by star lady - Chapter 26
Triplets book 1 complete by star lady Chapter 26: Triplets book 1 complete by star lady Chapter 26. a fusace ɗaya daga cikin su yace "Tafiya dake mukazo yi…
4,437 words
a fusace ɗaya daga cikin su yace "Tafiya dake mukazo yi ma'ana kidnaping naki mukazo yi" kwashewa da dariya gwaggo tayi kafin tace "Amma dai ku mahaukatane ko? Jehan ɗin kukazo kamawa to gata ku ɗauke ta" miƙewa tsaye Jehan tayi tana faɗin "Haba dai dirty Boyz ni zaku yi kidnaping? To muje mana gani nan ai" ta kai karshen maganar tare da dirowa kasa daga saman gadon, sosai Nasir ya kara tsorata, yanzu ya kara tabbatar wa kan sa akoi abun da Jehan ta taka, dan haka kawai ba zata ce su kama ta ba, in kaji makaho yace muyi wasan jifa to dutse ya taka, hakan yasa ya fara ja da baya da baya, yayin da Jehan ke tin karosa tana faɗin "Muje ko" ba shiri suma abokan Nasir ɗin suka fara ja baya baya suna bin Nasir "Gwaggo ɗauko waya kicewa DPO su kariso yanzu" cewar Jehan ɗin
jin haka yasa Nasir ya kwasa a kuje yayi waje, wandon sa na faɗuwa ya haye saman katanga kamar biri ya dira waje, yayin da suma abokan nasa suka rufa masa baya
Fadil na ganin su Nasir sun yi waje shima ya fito a guje dan kar DPO yazo ya kama shi, a ɗari suma suka haye katanga suka dira waje.
Suna fita Jehan ta kwaso a guje ta haye saman gadon ta rungume gwaggo tana faɗin "wayyo na shiga uku ni Jehan" ita kan ta gwaggo kirjin ta sai dukan uku uku yake, yau taga abun da yafi karfin ta, ashe duk wannan cika baki da suke kirjin su sai dukan uku uku yake a tsorace suke, kawai karfin haline ,irin na Jehan da gwaggo kamar wasu wayan da suka taki wata tsiya ashe duk bogene tsoro cike fal ransu
Kuka Jehan tasa tana faɗin "gwaggo dan Allah mu bar gidan nan kar su sake dawowa wlh tsoro nake ji" rungume ta gwaggo tayi tana faɗin "Ni kai na saura kaɗan nayi fitsari a wando saboda tsoro kawai karfin haline innalillahi wa inna ilaihir rajiun Allah mun gode maka da ka kuɓutar damu daga wannan masifa" jin gwaggo tayi zancen fitsari yasa Jehan ta taɓa jikin ta da sauri dan lokaci da su Nasir ke magana ita ma ji tayi kamar zatayi fitsari a wando saboda tsoro, ashe ta yi fitsarin ma bata sani ba ga kayan barcin ta a jike, kara rungume gwaggo tayi jikin ta sai kerma yake tana haɗa zufan wahala, while ita ma gwaggo sai zufan take haɗawa gashi tana jin fitsari amma tsoron fita take, an kasa samun wanda zai iya miƙewa cikin su ya rufe musu kofar ɗakin saboda tsoro, ga mum kuma kwance a bakin kofa a sume basu sani ba.
Haka a zaune rungume da juna suka kwana, sun kasa rintsawa saboda tsoro gani suke kamar su Nasir zasu dawo, yau sunga bone, ko sallar asuba sun kasa tashi suyi a lokacin da ake kiran Sallah, dan suna ganin kamar su Nasir na waje, har sai da gari yayi haske sannan Jehan ta iya samun dama ta saki gwaggo jikin su sai kerma yake suka fito waje, ba karamin tsorata sukayi ba ganin mum kwance a kasa, ga hannun ta nan da zanen shatin kafar mutun, da alama a garin gudune ɗaya daga cikin abokan Nasir ko shi da kan sa Nasir ɗin suka takata a hannu ta.
Jiki na kerma gwaggo ta ɗebo ruwa ta yayyafa mata, dogon numfashi taja tare da tashi a birkice tana faɗin "Ina Jehan dan Allah karku mata wani abun, duk abun da zaku mata ni ku min, dan Allah marainiyar Allah ce" turus gwaggo ta tsaya murya na rawa tace "Me kika ce Maryam? Marainiya kuma Jehan ɗin ce marainiya?" Sai lokacin mum ta dawo cikin hayyacin ta jin muryan gwaggo, a hankali ta gyaɗawa gwaggo kai kafin tace "Eh marainiya" a ruɗe gwaggo tace "ban gane marainiya ba kimin bayani" dogon numfashi mum taja tare da saukewa a hankali, cike da tashin hankali ta fara magana "Eh Aunty A'isha, tun ranar da yan sanda suka ɗauki daddyn Jehan, bai jima da tafiya ba yamin massage a kan cewa ba yan sandan gaske bane suka ɗauke sa haɗin bakine, abokan hamayya ne suka shirya masa hakan, kuma kashe shi zasuyi dan haka mu gudu, mu tseratar da rayuwar mu dan a halin yanzu ma, sun ɗauki hanyar Niger da shi kuma tabbas kashe shi zasu yi dan hakan suka shirya addu'ar mu kawai yake buƙata san nan kamar yadda ya faɗa min mu gudu dan muma ba zasu barmu ba saboda ba iya takarar sa suke so ba har da dukiyar sa, shi yasa da Shitu yazo yace mu tafi ban musa ba naje na ɗauko mana kayan mu dan mu gudu, tun da already daddyn Jehan ya sanar da ni, shi yasa ban takura Shitu a kan ya faɗa min ina daddyn Jehan yake ba, dan banson jin yadda suka kashe shi" murya na sarkewa sai haɗe words gwaggo keyi tace "To waya ce miki sun kashe shi? Da zaki fara kiran Jehan marainiya" "Sun kashe shi Aunty A'isha, sun kashe shi, dan in kika lura da yanayin da Shitu ya shigo gida a ranar, duka da gindin bindiga ce fa a goshin sa, shi da yabi daddyn Jehan daga baya ma kenan, kin ga kenan shima Shitu kashe sa suka so yi Allah yasa ya kubce musu yazo ya kubtar da mu, ba dan haka ba da dukkan mu mun mutu" jin mum tace an kashe daddy yasa Jehan fasa ihu ta sulale kasa sumammiya.
Mum da gwaggo har suna haɗa hannu waje rungumo Jehan ɗin suna kiran sunan ta a rikice, shiru Jehan bata motsa ba, zaro ido mum tayi ta fara hawaye tana faɗin "Shi yasa naki faɗa muku tun da jimawa Innalillahi wa inna ilaihir rajiun dan Allah Jehan ki tashi" ita kam gwaggo ta kasa magana abubuwan sun haɗu sun cushe mata waje guda, ta rasa ina zata sanya rayuwar ta taji sanyi a ranta, kan ta sai sara mata yake duniya na juya mata wani irin duhu take gani yana gelmawa ta cikin idon ta wannan wace irinyar masiface, ita kuwa mum kokarin danne abun take dan bata son abubuwan su mata yawa ta samu matsala ko dan saboda Jehan zata yi kokari ta danne da ta kula da ita, sai dai abubuwan sun mata yawa ga rasuwar daddy ya dawo mata sabo ga ɓatan Rimsha yanzu kuma ga Jehan, ta yanke jiki ta faɗin.
Duk yadda mum ta kai ga son ta danne abun ta kasa nan take taji zuciyar ta na harbawa da karfi karfi kamar zai fasa kirjin ta ya fito waje, lokacin guda taji kan ta ya mata nauyi, wani irin duhun ta gani ya kilma mata a cikin idon ta, kamar fanka haka taga duniya na juya mata, idon ta ya fara ganin mata daddy na kiran ta, kan tayi wani yunkuri ta zube kasa rungume da Jehan a kirjin ta, ihu gwaggo tasa kamar zararriya haka ta bazama Kitchen ta ɗebo ruwa a kofi tazo ta zuba musu a kan su.
Dogon numfashi Jehan taja tare da sauke wa a hankali kafin ta fara kuka, yayin da ita kuma mum ko motsi bata yi ba, kara ɗebo ruwa gwaggo tayi ta zuba mata nan ma shiru ba ta motsa ba, jijjigata gwaggo ta fara yi tana kiran sunan ta, amma ina ko motsi bata yi ba, sosai Jehan ke kuka tana kiran mum yanzu ta bar ta batun daddy ta koma kiran mum dake gaban ta.
Sadiq yazo zai shiga gidan su Jehan dan yaje ya ɗebawa su mum ruwa kenan Yusuf ya kwala masa kira ta bayan sa, da sauri ya juya yana kallon Yusuf ɗin "Yaya Sadiq ina zaka je? Kazo muje mu gaishe da Fadil yanzu kanin sa ke faɗa min wai ya samu karaya a kafa jiya da daddare a wajen hanyar sa ta dawowa gida" zaro ido Sadiq yayi yana faɗin "Allah sarki to kaje ina zuwa bari na ɗebawa su mum ruwa" to Yusuf yace tare da wucewa ya nufi hanyar gidan su Fadil, shi kuma Sadiq ya shige cikin gidan su Jehan.
Ganin gwaggo da Jehan na ta kuka suna kiran sunan Mum dake kwance a kasa bata ko motsi ne yasa Sadiq karisawa wajen da gudun gaske yana faɗin "Lafiya me ya same ta" tsabar ruɗu da tashin hankali Jehan bata san lokacin da ta riƙo Sadiq ba, cikin fitar hayyaci take faɗin "Dan Allah dirty boy ka taimaki mum ɗina karka bari ta mutu please" kasa motsawa Sadiq yayi saboda irin riƙon da Jehan ta masa gaba ɗaya yaji sa wani iri ta kashe masa jiki, ita kuwa sai jijjiga shi take tana kiran "dirty boy ka taimaki mum ɗina" sai da gwaggo ta janye Jehan ɗin daga jikin Sadiq ta rungume ta sannan Sadiq ya samu dama ya iya juyawa ya fice daga gidan, yaje ya kira ɗan sahu.
Har kofar gida mai a daidaita sahu yazo, Sadiq ya kira maman shi tazo ta taya gwaggo suka ɗauki mum suka sata cikin a daidaita sahun, gwaggo da maman Sadiq suka shiga a daidaita sahu suka riƙe mum ɗin, shi kuma Sadiq ya riƙe hannun Jehan dake ta faman kuka yace mata suje bakin hanya su tari wani a daidaita sahun subi bayan su tun da wannan ba fili, ba musu Jehan ta bishi sai kuka take kamar ranta zai fita,
Wani a daidaita sahu Sadiq ya tara musu suka shiga gidan baya, sai kuka Jehan keyi suka bi bayan su mum.
Ko da suka isa Hospital ɗin an rasa wa zai biya mai a daidaita sahu kuɗin sa sakamakon babu wanda yake da kuɗi a jikin sa, ganin haka mai a daidaita sahu da ya ɗauko su mum yace ya yafe musu, shi kuma wanda ya ɗauko Jehan da Sadiq yace a'a shi da ba zai yafe ba kawai a biya sa hakkin sa san nema ya fito ba taimako ba, a wannan marra da wahalar rayuwa da jama'a ke ciki ko biyar ba zai iya yafewa wani ba saboda shi family man ne, sai zare ido Sadiq yake dan bashi da ko biyar, while su kuma su gwaggo sun shige da mum ciki Jehan ma tabi bayan su, sun bar Sadiq tare da yan sahu, sai faman sosa kai yake yana zare ido, ganin haka yasa ɗan sahun da ya ɗauko su mum ya biya wancan ɗin, sai godiya Sadiq ke masa, yace "Kar ka damu abokina Allah dai ya bawa mara lafiyar ku lafiya, ai talauci bata hana ka taimaki wanda yafika bukata idan kana da hali, talauci ba hauka bane Allah dai yasa mu dace Allah ya mana karshe mai kyau" Amin Sadiq ya amsa dashi, sai zuba godiya yake har ɗan sahun ya tafi.
Sai bayan ɗan sahun ya tafine Sadiq ya tuna basu rufe gidan su Jehan ba sun bar ko ina a buɗe, sosai tashin hankali ya bayyana a kan face ɗin sa kar a shiga a musu sata, da yar gudun sa ya shiga cikin hospital ɗin dan yaje yaga halin da mum take ciki sai yazo ya koma ya rufe musu gidan.
Zaune a saman benci ya isko su gwaggo sun zaunar da mum suna zazzaune suma, cike da mamaki yace da manan sa "mama ina likitocin kuma? Ya baku shiga ciki ba" kamar maman Sadiq zatayi kuka tace "wai sai mun yanki kati, Jehan taje yanko mana" shiru Sadiq ya ɗan yi kafin yace "To mama bari naje na rufe musu gidan dan mun ruɗe mun tafi munbar gidan ko ina a buɗe" zaro ido waje maman sa tayi tana faɗin "Kayi sauri babana innalillahi kash munyi ganganci Allah dai yasa ba baun da zai faru, Allah ya kau da idon masu dogon hannu kayi sauri kaje ka rufe musu" dai dai lokacin Jehan ta dawo tana faɗin "Wai katin sai da kuɗi" gwaggo ce tace "Ina ATM naki ki basu su cire mana" da sauri Jehan ta wuce face nata sanye da fake face tana faɗin "ATM ɗin yana gida bari naje na ɗauko" da sauri Sadiq yabi bayan ta dan yasan ba sanin hanya tayi ba, yayin da ita kuwa mum take ko mutuwa tayi ne oho ba wanda ya sani, gashi likitoci sunki kulata wai sai an yanki kati sannan su bi layi wajen ganin dr kafin ma a yanke musu hukuncin ko gado za'a basu ne ko magani.
A ɓangaren su Jehan kuwa a daidaita sahu Sadiq ya sake tara musu suka shiga suka koma gidan su Jehan ɗin.
Kai tsaye ɗakin Jehan ta nufa, ba shiri taja birki tana ganin yadda a ka watsa musu ɗaki an zubar mata da kayan ta dake cikin trolley dukka, har kayan dake cikin bayi ba'a bari ba an watsar, kasan cewar tana sauri ne yasa ta zura hannun ta cikin aljihun trolley ɗin ta dake yashe a tsakar ɗakin, ta ɗauko ATM card nata, haka ta bar ɗakin a watse ta nufi hanyar fita
Har ta kai bakin kofa sai ta juyo wai bari ta ɗauki wayar ta, da mamaki sai bata ga wayoyin ba dukka biyu, daga nata har na Rimsha, kasan cewar sauri take yasa bata wani tsaya neman wayoyin ba ta wuce ta nufi bedroom na mum dan ta ɗauko ATM card na mum ta haɗa da nata ko da kuɗin account nata ba zai isa ba, dan ba wani kuɗin kirki ya rage a account ɗin nata ba.
Nan taga ikon Allah dan watsa ɗakin mum da a kayi yafi yadda a ka watsa nasu, haka ta tsallake kayan ta wuce ta duba ATM card na mum ta ɗauko ta fice daga ɗakin cikin sauri.
Sadiq na tsaye a harabar gidan yana jiran ta bai san meke faruwa ba kuma itama bata sanar da shi ba, tana fitowa suka fice daga gidan tare da rufe ko ina na gidan, suka nufi bakin hanya
Suna tafiya ne Sadiq yace mata "da kika sanya face ɗin nan kin canza ba wanda zai ce kece" bata gane me ya faɗa ba sai dai kawai tace masa "Okey" shiru ya mata har sukaje wajen mai POS ta miƙa ATM nata tace ya bata 20k cikin sauri mai POS ya ciro mata kuɗi kasan cewar yaga kamar suna sauri, ansan kuɗin tayi tare da ATM nata suka wuce suka hau a daidaita sahu suka koma asibiti.
Kamar yadda suka bar su mum haka suka dawo suka same su, sauri sauri Jehan taje wajen sai da kati ta miƙa 1k nan suka haɗa mata kati Sadiq na tsaye a gefen ta, suka miƙo mata kati da canji, kati kawai ta ansa bata ansa canji ba tace bata buƙata, hannu Sadiq yasa ya ansa mata canjin 800, ya miƙa mata a wulakance tace bata buƙata ta bashi, bai damu ba ya zura kuɗin cikin aljihun sa suka wuce suka koma wajen su mum dan su samu damar ganin likita.
A takaice dai sun ga nurse sannan an basu gado a kan mum ta kwanta likita zai zo ya dubata, Jehan ce ta biya kuɗin gadon suka shiga da mum ciki, kwalla Jehan ta fara yi ta zauna kusa da mum ta riƙo hannun ta tana karan to mata duk addu'ar da yazo bakin ta, while su kuma maman Sadiq da gwaggo suna zaune daga ɗan gefen gadon ta kafan mum sunyi tagumi jugum jugum gwaggo na hawaye ta sunkuyar da kan ta kasa, shi kam Sadiq bakin window ɗakin yaje ya tsaya ya dafe kan sa suna jiran dr yazo ya duba mum suji meke damun ta gashi dai ko motsi bata yi kamar ta mutu.
To bari mu leƙa Rimsha kafin dr yazo muji meke damun mum
👹DAULAR MUTUWA👹
Zaune a wajen Rimsha ta kwana, ko motsi bata iyayi saboda matsanancin yinwa da kishin ruwa da take ji, yau kwanan ta na huɗu kenan ba abinci ba ruwan sha, duk da cewa kwana biyu daga ciki a sume tayi su, sosai Ayla ta tausayawa Rimsha duk da cewa bata san labarin taba bata san daga ina Rimsha ɗin ta fito ba, amma dai tana ji a jikin ta tabbas Rimsha bata saba da rayuwar wahala ba, ba yar gidan malam Shehu bace, daga ganin fatar jikin ta da yar gidan hamshakin mai arziki tayi kama ko dai yar gidan sarauta ko yar gidan wani shugaba, haka Ayla ta rinƙa ayyana Rimsha yar gidan wanene a ranta, har rana ya ɗaga, kwata kwata Rimsha bata iya magana ko motsa bakin ta bata iya yi.
Sai da rana ya ɗago sosai ne sannan magicians ɗin suka zo suka buɗe wa su Rimsha kofar ɗakin nasu suka turo musu abinci, sannan suka fice suka bar kofar a buɗe, da sauri Ayla ta jawo kayan abincin ta ɗauki jug ɗin ruwan da suka kawo masu da sauri ta kafawa Rimsha a bakin ta, da kyar Rimsha take iya haɗiyar ruwan saboda wahala da ta sha
Ka ɗan ta sha ruwan ta fara kwarara amai tana tari, da sauri Ayla ta riƙe ta tana ɗan bubbuga mata baya, sosai Rimsha tayi aman ruwan da tasha kafin ta koma ta jingunu da jikin bangon, sakin ta Ayla tayi ta matso kusa da Kausar dake kwance rai a hannun Allah itama saboda yinwa, haka Ayla ta ɗago kan ta ta fara bata ruwan, itama Kausar kamar Rimsha kaɗan ta sha ruwan ta fara amai.
Sai bayan sun ɗan huta sannan Ayla ta sake basu ruwan kaɗan kaɗan, a wannan karon basu yi amai ba..
Share fisabilillah 👏
To masu karatu sai mun haɗu gobe idan mai dukka ya kai🤪
B 💞Star Lady💞
TRIPLET'S💞
*THE BEGINNING*
💞STAR LADY💞
WhatsApp me for more information 09162620621
Episode 24
Sai bayan sun ɗan huta sannan Ayla ta sake basu ruwan kaɗan kaɗan, a wannan karon basu yi amai ba, yau dai Ayla bata ci abincin ba ta kyale musu a kan su suci tun da ita taci jiya kasan cewar abincin ba yawa, kallon abincin da kyau Rimsha tayi kafin ta ɗago ta kalli Ayla cikin raunanniyar murya tace "Ayla wannan miyar ai kamar naman mutun ne a ciki" gyaɗa mata kai Ayla tayi kafin tace "Eh naman mutun ne a ciki, nima kullun iya shinkafar kawai nake ci bana sa miyar, sai kuma fruits ɗin nan shima ina cinyewa" shiru Rimsha tayi tana mamakin a ran ta tana faɗin "Wa ina zubillah ya Allah ka kawo mana ɗauki, ya Allah dan karfin mulkin ka, dan karfin izzan ka da girman ka ya Allah ka tarkatsa wannan gida na azzalumai cikin gaggawa, ya Allah ka kawawo bayin ka musulmi ɗauki, Allah kayiwa wa'yannan azzaluman hukunci mai tsanani tun a duniya, ya Allah kai ka ɗai kasan adadin rayukan bayin ka da ya salwanta a nan" zuba mata ido Ayla da Kausar sukayi suna kallon yadda ta zubawa abincin dara daran sleeping eyes tana tana zancen zuci.
Ganin ta ki dai na kallon abuncin ne yasa Ayla ta ɗan taɓa ta, ɗago dara daran sleeping eyes nata tayi ta kalli Ayla ɗin "Kuci shinkafar mana, baiwar Allah ni gashi baki faɗa mana sunan ki ba ma" cewar Ayla, lunshe ido Rimsha tayi tare da mayar da kan ta ta jingina da jikin bangon ɗakin tana sauke ajiyar zuciya a hankali.
Cikin sanyin murya tace "Sunana Rimsha kuma ni ba zan iya cin wannan shikafar ba, dana ci namar mutun gara yinwa ta kashe ni" girgiza kai Ayla tayi kafin tace "A'a ni bance kici namar ba miyar ma gaba ɗaya bance ku ciba iya shikafar kawai nace kuci sai kuci fruits ɗin, shi kuma miyar ku kyale musu abunsu zasu zo su ɗauka anjima, kuci da wuri mu fita waje mu sha iska, muyi hira da sauran yan gidan zuwa yamma za'a rufemu" kanta na jingine da jikin bangon ba tare da ta ɗago ba ta waro dara daran sleeping eyes nata a kan face ɗin Ayla kasa kasa tace "Ni ba zanci shinƙafar bama, dan ko nace zan ci amai kawai zanyi dan haka kawai kuci" tayi maganar cikin harshen turanci, kallon kausar Ayla tayi kafin tace "Matso kici kinji?" ba musu Kausar ta matso ta fara cin gayan shinkafa babu miya
Ɗaukan Apple Ayla tayi ta sanyawa Rimsha a hannu tana faɗin "kiyi hakuri kici wannan kinji?" rike apple ɗin Rimsha tayi tana matsar kwalla haka ta kai apple ɗin ɗan bakin ta, ta ɗan ciza tana matsalar kwalla.
Haka Rimsha wannan apple ɗin kawai taci yayin da ita kuma Kausar taci shikafa fari ba miya sannan suka haɗa da fruits ɗin ita da Ayla su kaci.
Bayan sun gama ne Ayla tace suzo su fita waje, make kafaɗa Rimsha tayi tana faɗin "No i can't go anywhere" "Kiyi hakuri muje mu ɗan kalli hasken waje kinji ko" Ayla tayi maganar a raunane
Da kyar Rimsha ta iya dafa bango ta miƙe suka nufi waje sai dafa bango take suka fito tsakar gidan, nan fa Rimsha taga duniya ga yara nan har da manya mafiyawancin su suna zaune ne a bakin kofar ɗakin su, dukkan su suna bushe kallo ɗaya zaka musu kasan suna cikin yinwa da wahala.
Saman wata yar benci Ayla ta wuce taje ta zauna ta zubawa yan gidan ido wadda ko wace ke zaune a kofar ɗakin ta, duk yinwa ya cinye su, sun rame sun bushe sun zama kamar kashi da rai, ko maganar kirki basa iyayi, saboda yinwa mafi yawancin su basa cin abincin gidan kasan cewar da naman mutun ake miyar sai dai suci fruits wasu suci da gayar shinkafa wasu kuma suci fruits zalla amma basa taɓa shan miyar,
kusa da Ayla Rimsha ta zauna tana bin gidan da kallo tana mamaki a ranta.
Can idon ta ya hango mata wani mutun dake zaune ya haɗa kai da gwiwa yayi shiru, zuba masa ido Rimsha tayi na yan mintoci kafin ta miƙe da kyar ta nufesa a tsorace Ayla tace "Meesha karkije wajen mutumin nan fa zai iya marinki dan bai da mutunci ko kaɗan" a ta kai ce Rimsha tace "Sunana Rimsha ba Meesha ba" da sauri Ayla tace "Irin sunan wata friend na a islamiyar mu ne gare ki kuma ita Meesha muke ce mata shiyasa na kiraki hakan amma kiyi hakuri yanzu dai ki dawo karki je wajen sa" shiru Rimsha tayi kamar bata ji me Ayla ke faɗe ba ta wuce abun ta ta nufi mutumin tana jan kafa da kyar.
A gaban sa ta tsugunna cikin sanyin murya tace "sannu" shiru yayi bai mata magana ba kuma bai ɗago ba, sake mai mai ta maganar nata tayi nan ma bai ɗago ba, sai a karo na uku ne ya ɗago a zafafe yana zaro ido ya ɗaga hannu zai mareta kenan, a sukwane ta rimtse idon ta a hankali ta furta Wayyo Allah na, zaro ido sukayi dukkan su lokaci guda jin Rimsha ta iya furta sunan Allah, cikin sauri shi ma mutunmin ya kwatanta ko zai iya kiran sunan Allah amma ina ya kasa, ita ma Rimsha tayi kokarin sake kira amma ina sunan yaki fitowa, haka ta hakura ba dan taso ba
Zuba mata ido mutumin yayi kafin yace "Ya sunan ki" cikin nitsuwa tace masa "Rimsha" a hankali ya mai mai ta sunan, ba karamin mamaki su Ayla suka shaba ganin Rimsha na hira da mutumin nan, "Kai fa ya sunan ka?" Ta tambaya tana tsare sa da dara daran sleeping eyes nata, kasa kasa yace "Mustapha" shiru suka ɗan yi na yan mintoci kafin yace "Ya akayi kika zo daular mutuwa gidan da ba'a shiga a fita, duk wanda ya shiga to kai tsaye zai tafi in da ba'a dawowa?" Hawaye Rimsha ta fara yi ta fara bashi labarin yadda a kayi ta tsinci kan ta a daular mutuwa, sosai ya tausaya mata, sai dai abun mamaki shi da ta tambaye sa ya akayi yazo nan, ya kasa faɗa mata dan ya kasa tuna komai, yayi mamaki sosai ma jin ita ta iya tuna yadda a kayi ta shigo gidan, shiru yayi ya zuba mata ido yayin da ita kuma take ta kokarin tuna wani abu mai muhimmanci daga cikin rayuwar ta, amma ina ta kasa tunawa, haka suka yita hira da Mustapha har rana ya ɗago sakiyar duniya, ma'ana azahar tayi kenan, lokacin azahar na cika Rimsha ta fara jin gaban ta na faɗuwa, dan har da Sallah sun mantar da ita sai dai da yake abun na jikin ta da time yayi zata ji jikin ta har kerma yake sai dai ta kasa gane hakan.
Bayan sun yi sallama da Mustapha ta koma wajen su Ayla ta zauna saman bencin in da ta tashi, cike da mamaki Ayla ta tambaye ta a kan hirar me sukayi da mutumin nan, nan ta basu labari sama sama, sun sha mamaki sosai dan Mustapha ba ya yiwa kowa magana a gidan kullun yana zaune shiru kamar kurma.
Suna zaune a wajen har mamallakin bencin yazo wato mai gadi su mai kula da su a part ɗin nasu, gidan Part by part ne kowani Part su barbushi suna ajiye mutun ɗaya mai kula da yan wannan part ɗin
kallo ɗaya Rimsha ta masa taji ta tsani mutumin nan, bata son kallon sa, wani mummuna da shi mai kiran samudawa sai dai da alama cikakken mutun ne ba aljani bane, matsa masa gefe Ayla tayi a kan ya zauna, washe baki yayi yana faɗin "Kiyi zaman ki bari na zauna a kasa dan naga yau da baki kika zo da alama munyi sabbin baki kenan" dariya Ayla tayi ka san cewar sun saba da mutumin tace "Kai dai duna bari yau na haɗu da yan uwana ne" kara washe baki yayi kafin yace "Suma musulmai ne kenan?" Jin ya ambaci sunan musulunci yasa Rimsha ta ɗago a sukwane tana kallon sa yayin da ita kuma Ayla tace "Me kuma musulmai" kallon tsab yayiwa Ayla kafin yace "Kema an juya miki tunani kenan?" Shiru Ayla ta yi dan kwata kwata ta dai na fahimtar abun da yake faɗa, ita kuwa Rimsha da Allah yasa tunanin nata bai gama tafiya dukka ba abun yana mata kamar gizo ne yazo ya koma, wani lokaci har sunan Allah tana iya kira wani lokaci kuma tayi kokarin kira amma sai ta kasa, hakan ku ya samo asali ne saboda addua'o'i da mum ta biya kuɗi a ke ta mata ga saukan Al Qur'ani mai girma da ake ta mata hakan yasa ita kaɗai ta saura a gidan mai iya kiran sunan Allah time to time, kuma time to time tana iya tuna wasu abubuwa masu muhimmanci da ko wani musulmi ya kamata ya kasance yana aikata su wato askar.