Kenza eBookz

Triplets book 2 complete - Chapter 41

Triplets book 2 complete - Chapter 41

Triplets book 2 complete Chapter 41: Triplets book 2 complete Chapter 41. Tsare Dr da ido kawai Imran ya yi yana jiran cikakken bayanin menene asalin…

4,430 words

Tsare Dr da ido kawai Imran ya yi yana jiran cikakken bayanin menene asalin damuwarta. Cigaba da magana Dr ya yi "Imran akwai abin da sister take so, wadda ya tsaya mata a zuciya sosai, wannan shiya haifar mata da matsalar yawan razana rashin kuzari har ma da zazzaɓi, tana da damuwa sosai kuma ni ina ganin rashin yan uwan nan nata ne, yana da kyau ku ja ta ajiki sosai domin ku rage mata raɗaɗi, dan ma yarinyar tana da karfin imani sosai ba dan haka ba, idan wata ce wlh da mutuwa za ta yi, ba uwa, ba uba, ba yar uwa, kuma dukka lokacin guda, bayan kuma a baya a tare suke rayuwa, kai abin ba karamin abu bane, pls Prof ku ja ta ajiki, ku cire mata danuwa da tunanin da take a ciki, kada ku bari wani abu ya rinƙa razana ta ko tsorata, idan ba haka ba zata rinƙa yawan suma wadda hakan kuma zai iya taɓa kwakwalwarta, bayan haka kuma zai iya sawa ta yi paralyzed (palarais,) saboda yawan faɗuwa da zata rinƙa yi, duk wani abin da take so, dan Allah ku yi kokari ku bata shi da sauri, ni ba zan ɓoye maka ba Prof ina sonta, ina sonta fiye da son da nake yi wa Jehan, tun lokacin da na ganta na ji na fi sonta akan Jehan, idan ba damuwa zan so ka bani izinin in ɗan rinƙa kasancewa kusa da ita, domin na kara kwantar mata da hankali, a yanzu kai ne uwa kuma ubanta, so ina neman izini daga wajen ka dan neman soyayyarta" . To fa Babbar magana ga A'A SALAHUDDEEN ga kuma DR NAWID dukka kuma friend ya kuke ganin abin zai kasance? Kada kuma ku mance ita Lion take so.

Allah sarki Imran shima a nashi tunanin rashin su mum ya sanya ta a damuwa haka, bai san da dakon soyayyar da ta yi na shakara 7 ba, basu kawo hakan a zuciyar su ba kwata-kwata, ba su ma taɓa tunanin tasan Lion ba, shi Nawid ya ga zanen da ta yi a kirjinta lokacin da yake dubata, sai dai ba dukkan zanne ya fito ba, ya so jan rigarta kasa kaɗan dan yaga zanen sai dai kasan cewar a lokacin idanunta biyu kuma son aure yake mata ya sa bai yi gigin yin hakan ba, dan saboda kada ta yi mashi mummunar fahimta, shiyasa sai ya bar zancen amma ya so ganin me ta rubuta a wajen, kuma ya yi alkawarin in dai ya samu dama sai ya gani.

"Dr In Sha Allah zan yi kokarin ganin na sanya Rimsha farin ciki sosai, sai magana ta gaba kuma I knew kai mutumin kirki ne, idan har ka iya samun soyayyar Rimsha to wlh ko da iyayenta sun bayyana zan tsaya maka, duk abin da zai sanya ta farin ciki ina maraba da shi a Yanzu, dan haka idan har Rimsha zata yi farin cikin kasancewa da kai, to ina maraba da kai, duk lokacin da ka zo gida zaka samu ganinta, all the best my dear" ya kai karshen maganar tare da miƙawa Dr hannun, miƙo mashi shima Dr ya yi suka bugi juna kamar yadda suka saba lokacin suna primary school.

"Amma Dr ba wani magani ko wani allura da za ku bata ne?" Cikin sauri Dr ya ce "Akwai sosai ma, yanzu ma na ɗaura mata karin ruwa domin akwai maleria a jikinta sosai, ina ga gidan da ta zaunan nan sauro sun taɓata, amma zamu yi treatment yanzu kuwa". Imran zai sake magana wayarsa dake a cikin aljihunsa ta fara kara.

Cikin sauri ya ciro wayar tare da bin screen ɗin da kallo, dan a tunaninsa Lion ne. A'A SALAHUDDEEN shine sunan da ya bayyana akan screen ɗin wayar, murmushi ya yi kafin ya ce "Dr ga mutumin yana kira, shima yana fama da halin da muke cikin, wato soyayya, Allah dai ya fitar da mu lafiya" ya kai karshen maganar tare da yin picking call ɗin.

Tun bai yi magana ba Ahmad ya riga shi da cewa "Yau ba ko sallama dan Allah Prof ka tashi zuwa Katsina ka je ka duba mani Queen of beauty ko tana lafiya ne, tun jiya bata ɗaukar wayata, ina ji a jikina wlh bata da lafiya, zan yi ta ƙoƙarin kiranta da ta ɗauka zan tambayi address kawai na turoma ka je ka gan mim ita ka jimin meke faruwa ne".

Yar dariya Imran ya yi kafin ya ce "Kai AA wlh baka da damuwa, ta ya za'a yi ka bari son macen da baka da tabbacin zaka sameta, ka bari ya shiga zuciyarka da kallon ɗaya haka? Bafa kasan wacece ita ba, wata kila ma matar aure ce, duk baka yi tunanin hakan ba, kai dai kawai daga ganin kyakkyawa, baka san halinta ya yake ba, to ni wai a ina ma ka haɗu da ita ne? A Abuja ko ina? Ni dai ba zan fasa gaya maka ba, ka rabu da ita, ka kama dahir, dama nace idan ka rabu da ita sai na baka number kanwata first lady ku kulla soyayya, to ita ma na mata miji yanzu nan, sai dai na baka heartbeat, ita ma idan ka yi wasa Irfar zai maka kafa dan naga kwana biyun nan sai wani tambaya ta yake yi ya take kamar bai san Hanyar in da take ba, jiya ma har da cewa na bashi number ta, to gara ka yi sauri ka kama dahir". Ya kai karshen maganar yana murmushin shakiyanci shida Nawid sai ɗaga gera suke suna guntse dariya, domin duk abinda Ahmad yake faɗe, Nawid na jin shi, Imran ya kure Volume na wayar.

"Kai Prof wlh bana son iskanci, kuna tare da Dr ko? To wlh ku fita ido na, nabi first lady da kuma heartbeat da gudu, ku baku san zafin so bane wlh, da kun sani da ba zaku ce na rabu da wadda zuciyata ke muradi ba, kun sani ni ban taɓa soyayya ba sai akanta, ko irin soyayyar secondary da ake yi ma ni ban yi ba, a kanta na fara sanin menene so, to dan Allah ku taimaka mani kada na mutu kun ji good friends my bloods". Dariyar da suke guntsewa ne suka tuntsure da shi, cike da shakiyanci Imran ya ce "Kawai ka hakura ka cigaba da shan lemon tsami" Nawid ne ya kai mashi duka a baya suka sake kwashewa da dariyar iskanci.

Ji Ahmad yake yi tamkar ya shaƙosu dan haushi, yana gaya masu damuwarsa suna mai da shi ɗan iska, suna mashi dariya.

"Wai me haka ne Prof? Ni na ce maku auren rage zafi zan yi ne? Son ta fa da gaske nake yi, haba mana bai kamata ku mani haka ba" ya yi maganar kamar zai saka ihu dan haushi.

Tsagaita dariyar Imran ya yi yana faɗin "Wai ka mance lokacin da nake gaya maka matar da zan aura kuma jinina ta ɓata ne? Ka manta me ka rinƙa yi Mani? Ina a nan ka ce mani wai sai na hakura na koma shan lemon tsami shine nima nake mai da maka da abin da ka rinƙa yi Mani".

Shi dai Nawid ɗan gulma sai murmushi yake yi yana jinsu, dan in dai irin wannan iskancin ne sun saba, da A'A da Imran, a baya idan Imran yana bashi labarin Jelly'n sa sai AA ya rinƙa cewa shi wlh bai ga macen da zai so ba a duniyar nan, shi yafi karfin ya ce wa mace yana sonta, sai dai ita ta ce tana son shi, ba kalar tsiyar da ba su yi wa Imran ba a lokacin, har ce mashi suke zai daina shan lemon tsami kenan, idan ya ce masu dama shi baya sha, sai A'A ya ce to idan baya sha meyasa zai yi aure, ba ya ga ji ne da danne abin ba, su yi ta dariya suna mashi tsiya, idan ya gaji ne sai ya tashi ya fita ya basu waje, to suma yau Allah ya kama su, kuma dukkansu akan mace ɗaya, ya kuke ganin wannan abota ta su za ta kasance? Kada ku mance abokaine tun na yaranta, tare suka yi primary school zuwa secondary daga nan suka rabu, Imran ya bar kasar, bayan wani ɗan lokacin suka sake haɗuwa shi da AA Salahuddeen a Harvard University, shi kuma Nawid a India ya karisa karatunsa, sai bayan sun dawo Nigeria suka sake haɗewa, dan dama already sun san gidajen juna, ba jimawa kuma Imran ya sake komawa dan yin degree ɗin sa ta biyu, dukka a Harvard University, shi kuma A'A England ya wuce, suka sake rabuwa, amma kullun suna waya da juna, suna matuƙar kaunar juna.

Tsuke fuskar Ahmad ya yi ya ce "Haba Prof ka ajiye duk abin da ya wuce, yanzu dai ka fuskanci matsalata dan Allah" jinjina kai Imran ya yi yana faɗin "Tom Shikenan yanzu dai ka bari sai ka zo ɗin, ni yanzu ina sauri ne kasan GAR ya zo Naija, to kuma ba sai na gaya maka ba, ka dai san halinsa, wlh tun jiya ya fita gida wai gidan bata yi mashi ba, ni bansan ina ya tafi ba, so zan je duba shi ne".

"What!!!" Nawid da Ahmad suka furta a tare, tare da miƙewa tsaye kamar suna a waje guda, kamar kuma abin haɗin baki.

Shi dai Nawid a Tv ya san GAR sai kuma ya taɓa ganinsa sau ɗaya da ya kaiwa Imran ziyara, lokacin yana degree ɗin sa ta biyu, shi kuma A'A SALAHUDDEEN makaranta ɗaya suka yi karatu.

"Kwairai kuwa GAR a Nigeria ni kai na lokacin da ya kirani ya ce mani zai shigo Nigeria karfe 3, wlh ba karamin shock na yi ba, ba don na mashi farin sanin cewa baya faɗan abin da ba haka ba, kuma bamu wasa a lamarin sa ba, wlh da na ce ba haka bane ko kuma wasa yake yi Mani, amma da yake shi dai kunsan magana ɗaya yake yi, kuma ba wasa a lamuransa ko kaɗan shiyasa ma na yarda, karfe 3 kuwa sai ga jirginsu ya sauƙa lokacin kuma already ina airport ɗin, har yau mamakin abin bai sake ni ba, duk da na ganshi da idona ni na ɗauke shi zuwa gida, kuma na san me ya zo yi, amma wlh har yanzu ina mamaki ina ganin abin kamar a mafarki ne".

Ahmad murya har wani watsakewa ta yi nan take ya koma normal da sauri ya ce "Kai gaskiya Prof ka ciri tuta, har muka gama school guy nan bai taɓa daga ido ya kalle ni ba, ban san ya akayi kai yake son ka ba, kuma duk lokacin muna tare, zai zauna da kai tare, amma da zarar munzo mun same ku kuna zaune zai tashi ya bamu waje, ban san me yasa ba, kuma wlh ina masifar kaunar guy ɗin, ko sau ɗaya bai taɓa yi mani magana ba, duk da cewa kai ma ba magana ya cika yi da kai ba, amma dai yana zama da kai waje guda, dan Allah Imran a wannan lokaci ka saka baki mu zauna da shi, ko sau ɗaya ne mu yi magana". Dogon numfashi Imran ya ja tare da sauƙewa a hankali.

Cike da damuwa ya ce "A'A a baya ma Saif bai tsaya ya yi magana da ku ba bare kuma yanzu da yake babban soja? Kada ka mance a baya fa lokacin bai kai haka ba amma yana da bala'in izza ina ga kuma yanzu? To wlh a yanzu izza da miskilancin Lion ta ci uban na da, ni ma ina da tabbacin Allah ne kawai ya jarabce shi da kaunata, da ya rabu da ni, kuma abin da ya sanya ni na musultat da shi, so yanzu ya san yana kan hanya ma daidaiciya kaga kuwa ba zai taɓa mantawa da ni ba, domin ni na nuna mashi daidaitacciyar hanya, ina ga wannan dalili yasa ma Allah ya jarabce shi da kaunata, kuma yasa har yanzu bai dai na kula ni ba, sannan kuma abin da ba ka sani ba game da Lion, wlh duk kansu har Michael suna da zuciya mai kyau, ba su mance alkhari, kawai dai dan suna kafurai ne, shiyasa ba zaka yi zaton hakan ba, amma ba dan haka ba suna da zuciyoyi masu kyau, musamman ma James yana da kirki sosai, shi Lion ne dama ya fisu taurin zuciya, amma shima lokacin ɗaya daɗin kira'ar Alqur'ani mai girma da nake yawan yi a school Allah yasa ya ja hankalinsa ya yadda da Ni, so ni yanzu wlh ba zan iya tinkararsa in ce kana son yin magana da shi ba gaskiya, saboda na san ma ba zai yi wu ba, kawai ka yi hakuri, ni yanzu zan tafi za mu yi waya idan na isa gida". Daga nan suka yi sallama ya kashe wayar jiki a mace.

Sai mamaki da al'ajabi tare da jimami Nawid ya ke yi, wai GAR ne a Nigeria. Taɓa shi Imran ya yi, yar firgita ya yi tare da dawo da kallonsa kan Imran ɗin, a hankali ya koma ya zauna saman chair nasa yana faɗin "Dan girman Allah Prof ka taimaka ka haɗa ni da shi, ko hoto mu ɗauka" Shiru Imran ya yi yana tunanin taya zai fara tinkarar Lion da zancen, domin ya san halin kayansa, ba yau suke tare ba, Allah ne kuma ya haɗa zuciyoyinsu, Allah ne ya kaddara wa Lion Kaunar Imran ta sanadiyar kira'ar Alqur'ani mai girma da yake yawan zama yana yi a Library su, shi kuma Lion yana zama karatun a wajen, daga haka suka haɗu, daga haka Alqur'ani mai girma ta fara shiga zuciyarsa har ya ji yana son karantata, bai karɓi Addinin Musulunci ba har sai da ya samu ilimi mai zurfin gaske dan gane da addinin, sai da ya yi haddar Alkur'ani mai girma sannan ya haddace manya-manyan daga cikin littafan musulunci, ya jima yana nazari akan addinan guda biyu domin ya tantance ta gaskiya, baya yanke hukunci haka kawai da ka, sai ya yi nazari da bincike, wannan dalili yasa, ya samu ilimi sosai akan musulci haka akan kiristanci, daga karshene ya yanke wa kansa hukuncin da ta dace da shi, ya karɓi Addinin Musulunci bayan ya gano cewa ita ce ta gaskiya, amma bai wani jima da musulta ba, ya dai ɗan jima da fara bincike a kan addinan guda biyu.

Story💖

"Nawid duk da nasan Lion yana kaunata ba zan iya tinkararsa da maganar ba, saboda na san ba zai yi ba, idan baka sani ba ma yau ka sani familynsu gaba ɗaya basa son mutane ko kaɗan, ka taɓa ganinsa tare da wani ko a Tv ne bayan James ko Michael?" Girgiza kai Nawid ya yi alamar a'a "To ka gani, amma dai In Sha Allah zan yi ƙoƙarin ko da da idone ka ganshi kafin ya koma" to Nawid ya amsa mashi da shi tare da zuba mashi ruwan godiya sannan suka yi musabaha Imran ya miƙe ya nufi in da Akila ke kwance yana faɗin "Za mu iya wucewa da sister yanzu ne?" "A'a Prof na yi mata karin ruwa, sai dai zuwa yamma irin karfe 4 haka" To Imran ya amsa da shi tare da tashin Akila daga barci a kan su tafi, nan fa ta ce a'a ita kam zata zauna da Rimsha gaskiya, ba dan ya so ba haka ya wuce shi kaɗai ya barsu amana a hannun Nawid ya tafi neman Lion.

Yana tuki yana tunanin ai na zai fara neman Lion ne ma wai, dan dai yasan bai koma ba yana nan Nigeria, sai ya wo yake yi da motarsa bai san ina ya nufa ba, wata hanyarma sau biyu yana kewaya wa ya sake kewayowa, duk ba tare da ya sani ba, hankalinsa na can cikin tunani.

Wayarsa da ke a zaune a gefensa ne ta ɗan yi kara alamar shigowar saƙo, cikin sauri ya ɗauki wayar, ganin sunan Saif ya sa ya gangara gefen titi ya tsai da motar.

Buɗe massage ɗin ya yi ya fara karantawa, address ne a rubuce a jiki tare da faɗin kasame ni yanzu, jinjina kai Imran ya yi yana faɗin Alhadulillah a ransa. Cikin sauri ya juya kan motar ya nufi wannan address ɗin.

💖UNGUWAR ISHAKU ROAD💖

Tampatsetsen gida ne na gani a faɗa, hawa ɗaya ne, irin dai manya-manyan gine-ginen na nan Naija, gaba ɗaya komai dake a cikin gidan daga waje a ka shigo da su, ginin ya tsaru sosai, irin gidan nan ne da akeyi a shirya komai su Furnitures da komai sai a sai da haka, to shine, sai mamaki Imran ya ke yi, yaushe Lion kuma ya san Nigeria har ya iya zuwa ya sayi gidan nan? Yana ta tunani har ya iso bakin gate ɗin, horn ɗaya ya yi, da ya ga ba a buɗe mashi ba sai ya san e lallai babu mai gadi, hakan yasa ya fito da kansa ya shiga cikin gidan, ya wangalewa kansa katafaren gate.

Bayan ya buɗe sai ya dawo ya shiga motarsa ya ja izuwa cikin gida, tsayawa zayyana maku yadda kawatuwan cikin gidan nan ya yi zai cinye mana ɗan sauran filin dake a gare mu, ku kawata yadda manya-manyan gine-ginen mu suke a ranku.

Kai tsaye parking space ya wuce, bayan ya kashe motar ne ya fito ya nufi tampatsetsen kofar da zata sadaka da cikin palon, daidai zai shiga kamar an ce ya ɗago kai sama, can ya hango Lion tsaye a balcony daga shi sai Short a jikinsa, dama Imran ya san halinsa akwai shi da san tsayuwa a balcony yana kallon yanayin gari daga ta sama.

Shiru ya ɗan tsaya yana tunanin ko dai ya koma ya kwaso mashi kayan sa ne, dan yadda ya ganshi da short ɗin nan ya san ya yi wanka ne, kuma ba zai iya mai da kayan da ya cire ba, kayan da ya zo da su kuma suna gidan su Imran ɗin, da alama kuma bai fita ya sai wasu kayan ba, ba karamin aikin shi bane yanzu ya ce kayan Nigeria ba su yi mashi ba, duk da cewa rabi da kwatan kayan Nigeria ma daga waje ake shigo da su.

Ganin ba abin da tsayuwa zata kara mashi ne yasa ya shige cikin gidan kawai yana duba time a agogon hannunsa. 1:30 lokacin sallar azahar ta yi.

Wow gaskiya palon kasar nan ta haɗu sosai, kusan komai na cikin palon fari ne da ash color, sai tashin kamshi perfume ɗin jikin Lion take yi, da alama ya ɗan zauna a palon, gaba ɗaya furnitures dake a cikin palon set biyu suna cikin ledojinsu ba'a ɓuɗe su ba, komai tsab-tsab da yake sabbine, kuma sai da aka share aka gyara mashi komai kafin ya shiga ya zauna.

Abin da ya faru bayan ya baro gidan su Imran, kai tsaye bakin titi ya wuce, a nan ne ya tsaya ya kira kakansa a waya a kan ya kira President na Nigeria yana buƙatar number dillalai masu dillancin gidaje, His Excellency ya tambaye shi me kuma haɗin sa da Nigeria, nan ya ce da His Excellency Nigeria ya zo, sosai His Excellency ya yi mamaki sannan ya ɗaura da cewa to ya sauƙa a gidan Gwamnati mana, a'a ya ce baya buƙata domin aikin sirri ya zo yi, shi kawai number yake buƙata, ba tare da ɓata lokaci ba aka fara aiki a kai, cikin kankanin lokaci kakansa ya gama komai, har in da yake dillalan suka zo da motarsu suka same shi, bayan ya turawa kakansa address ɗin wajen ta hanyar tambayar sunan wajen. Kin shiga motar ya yi ya ce ba ta yi mashi ba, nan ma sai da His Excellency ya sa aka tura mashi wata dankareriyar mota daga gidan gwamnan Kaduna, su dai sai karɓar umarni suke da sun tambayi waye ne sai ace ba ruwansu.

*Abun ku da kuɗi da kuma karfin mulki, kada ku mance Nigeria dai a kasan Usa take, dama kullun sai yadda suka yi da mu😭 su mulki kasarsu kuma su kulkemu, abin da suke so shi ya zama dole gwamnatin mu ta yi😭 hakan yasa a cikin wannan dare a ka yi wa Lion komai dan dole.*

To daga nan ne suka wuce ya je ya ga gida je, wajen gidaje biyar aka nuna mashi, duk ya ce basu yi mashi ba, da kyar ya karɓi wannan gidan, ita ma lallaɓawa kawai yake yi ba wai dan ta yi mashi ba, haka dillalan suka saka yaransu suka share mashi ko'ina aka gyare tsab, ya shige, kuma har suka gama aikin ba wanda ya samu damar sanin wanene shi, saboda akwai face mask a fuskarsa, kuma ma bai tsaye a in da suke ba. Wannan shine abin da ya faru

Mu koma kan story.

💖Imran💖

kai tsaye staircase ɗin ya nufa yana sauri sosai. Da sallama ɗauke a bakinsa ya shiga palon saman, ɗakuna uku ne a cikin palon, tunanin ta balcony da ya hango Lion ya yi, daddɗar Kamshin perfume ɗin Lion ɗin ne ta isar mashi da sakon ga ta in da Lion ɗin yake, cikin sauri ya nufi in da kamshin ta fi yawa, yana tafiya yana jinjinawa karfin perfume ɗin nan, domin kwata-kwata yau Lion bai sanyata a jikinsa ba, saboda ya baro ta a gidan su Imran ɗin, tun wadda ya sanya jiya ne ta bule gidan da daɗin kamshi.

Sallama ya mashi kafin ya shiga cikin ɗakin, kai tsaye balcony ya nufa, Lion na tsaye, yana kallon birnin Kaduna, kyakkyawar halittar jikin nan nasa a waje, dan short ɗin nasa ma, iya rabin cinyarsa ta tsaya mashi, subhanallah kyawun ainahin surar Lion ba zata iya zayyanuwa a baki ba, saboda ta wuci baki ya faɗe ta, sai wanda dai ya gani a zahiri, soft skin ɗin nan nasa sai wani kyalli na musamman yake yi, ga bala'i laushi kamar bai taɓa fita waje ba, kamar fatar jariri, wannan kwantacen bakin gashi siɗif ɗin dake kwance a saman cinyoyinsa da hannayensa, ba karamin kyau ta yi ba, ga wani gashin a kwance a buɗaɗen faffaɗar kirjinsa, damatsan hannunsa kuma ba'a magana sai wanda ya gani, kallon kasa yake yi wa garin Kaduna, irin mutun ya sunkuyar da kansa kasa ya kuma ɗaga idanuwansa yana kallon waje, to haka ya yi shima,

Imran yana zuwa ya miƙa mashi hannu dan su gaisa, ba tare da ya kalle shi ba ya miƙo mashi nasa hannun suka gaisa.

Shiru suka tsaye kamar kurame, wayar Lion dake a cikin ɗakin ne ta fara kara tana kira mashi number mai kiransa tare da suna da location, Imran na kokarin zuwa ya ɗauko mashi wayar, ya dakatar da shi ta hanyar ɗaga mashi hannu alamar baya buƙata, bari Imran ya yi suka ci-gaba da tsayuwa shiru.

Kira ta farko ta yanke ta biyu ta shigo, ita ma ta yanke sai a karon na uku ne ya juya a nutse ya nufi cikin bedroom ɗin, girgiza kai Imran ya yi yana addu'ar Allah ya shirya mashi Lion, wato haka ya ke yi shiyasa su yi ta kiran shi baya ɗagawa, sai lokacin da ya ga dama sai ya kira su. Lion duniya

Yana zuwa ya duba wayar Tyrone ne ke kiransa, picking ya yi tare da kara wayar a kunnansa ba tare da ya yi magana ba, ya zauna a saman gefen katafaren gadon dake a cikin ɗakin.

Ya ɗauki good 5mins wayar na kunnansa bai yi magana ba, da alama yana sauraron abin da Tyrone ɗin yake faɗe ne, a haka ya sake kara 2mins sannan ya cire wayar daga kunnansa ba tare da ya yi magana ba ya katse kirar, daidai lokacin Imran ya kariso cikin ɗakin.

Saman bedside drawer ya zauna yana faɗin "Ya akayi ka samu wannan gidan a cikin daren da ka fita?" Shiru ya yi yana rubutu a wayarsa, da alama sako zai tura.

"Saif ka yi breakfast kuwa?" Sai lokacin ya ɗago da kallonsa a kan fuskar Imran ɗin, kallo ɗaya ya yi mashi wadda bata fi second 2 ba, ya kawar da kallon nasa izuwa kan wayarsa.

"What is wrong with you Prof?" Shine abin da ya furta cikin sanyin murya, ajiyar zuciya Imran ya sauƙe tare da jan numfashi, dama yasan da kallo ɗaya Lion zai gane yana da damuwa, dan shi haka yake kawai bala'in kaifin kwakwalwa, da gane abu cikin ƙanƙanin lokaci.

"Amana ta ce bata da lafiya shiyasa, bana cikin mood". Daga nan bai sake magana ba shima Imran ɗin bai sake yin wata magana ba, tsawon minti 20 a haka sannan Lion ya fara magana cikin sanyin murya.

"Gaskiya Prof ban taɓa jinjinawa ko wace kasa ba bayar tamu, amma a yau na jinjinawa Nigeria da yan cikinta".

*Ni ko nace ba dole ka jinjina mana ba, ai mu saboda baiwar mu ba kalar iskancin da ba mu iya ba, idan musulci ne to mun fi kowa, haka tsiya da kaifin ƙwaƙwalwa, basira, son Allah da annabi, zalunci, ta'addancin, taimakon wata ƙasa, mu bada rayukanmu kan taimakon abin da ma bai shafemu ba, bayan ga matsala a cike a kasarmu, mun kasa kula da ita dan warwareta, sai shiga harkar da ba tamu ba, kai mu fa idan aka mana tsiya har president bamu kyalewa zage shi muke yi fes, kuma haka idan muka zage shi zai sa a nemo mu a duk in da muke, a kamo mu a ladabtar da mu, amma an kasa neman in da bandits suke a kwamuso su😭 a mana maganin su, anya wannan abin?, a Nigeria ne aka je gasar karatun Alkur'ani mai girma ɗan Nigeria ya buge manya-manyan larabawa ya ɗauko mana first ya dawo mana da ita, mu baiwar mu wlh ta wuce misali, a Nigeria ne zakaga an taɓa annabi musulmi sun fita a guje kamar mahaukata, amma hauka na son manzon Allah, a Nigeria ne zaka ga ɗan bandits ya shigo gida ya ce maka ka fita zai yi amfani da gidan, a Nigeria yan bandits suna da damar rike bindiga su kashe al'umma, amma kuma al'umma basu da damar riƙe bindiga ko wani makami dan su kare rayukansu da dukiyoyinsu, ƴaƴa da matansu😭, kai mu fa baiwar mu bata faɗuwa da baki, sai dai Allah ya mana Albarka kawai, amma ko mai muka ce za muyi, to mune a kan gaba, am proud to be Nigerian💪*

Story

Yar dariya Imran ya yi kafin ya ce "E haka ne gaskiya akasar mu babu abin da bamu da shi, ta ko wani ɓangare mun haɗa". Shiru ya ɗan yi kamar mai nazarin wani abin, still har lokacin hanunsa na a kan wayarsa yana typing.

Readers Also Read

More by Bilyn Abdull