Kenza eBookz

Triplets book 2 complete - Chapter 49

Triplets book 2 complete - Chapter 49

Triplets book 2 complete Chapter 49: Triplets book 2 complete Chapter 49. Yana shigowa Nigeria da kallo ɗaya yan daban Nigeria suka yi mashi suka kama shi,…

4,369 words

Yana shigowa Nigeria da kallo ɗaya yan daban Nigeria suka yi mashi suka kama shi, suka ce lallai ba ɗan ta'adda bane wannan, ya gaya masu waye ya turo shi, daga karkashin wace hukuma yake, wannan shine abin da ya sa Lion ya jinjinawa kaifi kwakwalwa ta yan Nigeria, yan kasashe da dama basu iya gane cewa James ba ɗan ta'adda bane, babba ne a cikin hukumar CIA, amma yan Nigeria da kallo ɗaya sun yi ram da shi, abin ya sa Lion ya jinjinawa Nigerians. Shi kuma wanda yan ta'addan nan suka yiwa yanka rago, ba kowa bane fa ce shine DIA babban mataimakin James ɗin ne awajen aiki, lokacin Lion ya gane hakan ya yi farinciki ganin James ba ɗan ta'adda bane, so kuskuren da James ya yi a wajen shine yadda ya shiga cikin yan ta'addan tsundum, kuskure na biyu kuma ɓoye masu da yake yi, kuskure na uku kuma sayar da rayuwarsa da ya yi. Duk guje gujen da yake yi yana yi ne dan kada TRIPLETS nasa su gane ne, saboda yasan ba za su taɓa yarda da hakan ba, kuma yanzu ma ba za su yarda da hakan ba, ya yi aiki sosai wadda ko General ba zai gwada mashi aiki ba, wannan dalili yasa Lion ce wa Tga James ya fi karfin sa, abin da ya yi abune mai kyau amma Lion ba zai taɓa yarda da hukumar CIA ba domin a yanzu haka James ba mallakin su bane, mallakin CIA ne domin ya riga da ya sayar masu da kansa. BABBAR MAGANA, A TAKAICE WANNAN SHINE WANENE JAMES DA KUMA HALIN DA YAKE CIKI A YANZU, KO BAN ZURFAFA BAYANI BA ZAKU IYA FAHIMTAR INA AKA DOSA!! MU KOMA CIKIN LABARINKU.

Story

Shiru ya yi na tsawon mintoci kamar 10 haka kafin ya fara magana gently. "Prof James ba ɗan ta'adda bane, kamar yadda ka ɗauka, amma dole zan hukunta shi, dole ya karɓi hukunci mai tsanani domin ya yi mani laifi" Zaro ido Imran ya yi yana faɗin "Ban gane ba dan Allah ka yi mani baya ni dallah dallah". Shiru ya yi, ya ɗan jima a haka kafin ya bawa Imran labari sama-sama kamar yadda dai na gaya maku waye James ɗin.

Ba ƙaramin daɗi Imran ya ji ba, sai dai kuma idan ya tuna cewa Lion ya ce sai ya yi mashi hukunci mai tsanani na sai da kansa wa CIA da ya yi, sai gaba ɗaya ya ji kuma jikinsa ya mutu, baban damuwar ma ba su san iya kar abubuwan da CIA suka sanyawa James ɗin ajikinsa ba, sai dai Lion yana bincike akan me da me suka yi mashi, dan ya san ta yaya za su iya samu su fitar da shi daga hukumar.

(Ni kuma na haɗa kayana zuwa wajen RIMSHA wata kila kafin na dawo su Lion sun ɗan gama jira)

🔥RIMSHA🔥

Sai zumuɗi take yi yau ta je school, fuskarta har wani kyalli yake yi saboda tsantsan farincikin dake a tattare da ita. Karfe 2 na rana daidai ta dawo, Akil ne ya je ya ɗauko ta, duk da busyn nan da yake a ciki, hakan bai hana shi kula da amanar da Imran ya bashi ba, ko da ya ɗauko ta bai tafi ba, ya tsaya yana kallonta har ta shiga part ɗin Imran, sannan ya juya kan motarsa dan suje su san yadda za'a kai kuɗin karɓar Aafia da Rufee, da farko yan ta'addan sun ce da daddare za'a kai kuɗin, daga baya kuma suka sake fasawa wai da rana za'a kawo, hakan yasa ya ce to shi zai kai ya karɓo A'afia ɗin. Kada ku mance Jinin Umaiya basa taɓuwa ta daɗi

Ko menene a jinin Umaiya oho? Waye ma ita ɗin? Mu je dai zuwa akwai labari agaba.

Rimsha tana shiga cikin palon yaya Imran ta tarar da Akila, a lokacin ta gama yi musu girki ta yi wanka.

Tana ganin Rimsha da sauri ta zo ta rumgumeta tana faɗin "Welcome my dear" ita ma Rimsha rungumarta ta yi tana mata oyoyo tare da tambayarta ya gida, nan ta ce mata ai ita ma karfe 12 ta dawo daga school, shine ta ce bari ta yi masu girkin abin da ta iya dafawa wato shinkafa da miyar steew, ita ma Umaisha yanzu da Akil ya fahimci me yake faruwa tsakaninta da Ammie sai idan zai fita, sai su fita tare ya kawo Part ɗin Imran ya ce ta zauna kada ta koma Part nasu sai ya dawo, abin da ya sa kuma bai kai ta gidan saba, saboda babu kowa kuma yanzu yana busy ba zama yake yi ba, ita kaɗai a gidan zata ji tsoro sosai, ya ce sai ya gama abin da yake yi, ma'ana kenan sai sun gama da case ɗin Aafia, zai mai data gidan nasa kafin su koma Madina, hakan yasa yake barinta suna zama a tare gaba ɗaya a part ɗin Imran ɗin tun da shi baya nan.

Wanka Rimsha ta fara shiga kafin komai, ko da ta je yin wanka sai faman shafa sunan Lion take yi, ita kaɗai kamar zautatciya sai murmushin take yi a toilet, har wani lumshe ido take yi kamar shine yake shafa mata wajen, abin da ya bata mamaki kuma ya ɗaure mata kai shine yadda akayi sunan yake matsawa zuwa saman tula-tulan da kyau a nata ganin, bata san cewa asali ma akan su ta yi zanen ba, lokacin dai basu girma bane suna kanana, sai take ganin kamar baa kansu bane, abin da bata sani ba shine, kullun breast ɗin nata kara cikowa suke yi, wajen da ta yi rubutun yanzu duk ya ciko sosai, shiyasa take ganin kamar rubutun na matsawa ne.

Bayan ta yi wanka ta ɗauro alwala ta fito ɗaure da towel a kirjinta, sai santin dark black curly hair ta Akila da Umaisha suke yi, ga shi jiya sun sha gyara gashin har wani kyalli yake yi, kunshintan nan ba'a magana.

Shiryawa ta yi tsab cikin Pakistan wando fari rigar blue gyalen ma blue, ba karamin kyau ta yi ba, sai ta saje da indiyawa abinta, simple make up ta ɗan yi tare da feshe jikinta da perfume ta zo ta yi sallah.

Bayan ta idar ne Akila ta ce suje su ci abinci, to ta amsa da shi dan dama tana jin yunwa sosai, 1k ɗin da Akil ya bata dan sayan abu a school, bata sayi komai ba, ta dawo da shi a jakarta, dan bata saba ba, abin da ta saba shine tafiya da abinci daga gida, kuma yau saboda zumuɗi bata ɗauki abincin ba, duk kuɗin da daddynta yake da shi bai koya masu saye sayen abin da ake sayarwa a shop na cikin school nasu ba, hakan yasa yanzu ko ba'a basu kuɗi ba sun saba, duk wani kayan cima su biscuit, chocolate, har ice cream, yogurt duk daga gidan mun ɗin su ke shirya ma su a lunch box ɗin su, KUMA HAKAN YA FI SHINE DAIDAI, KADA A SABA BAWA YARO KUƊI, KODA BISCUIT ƊIN NE ARINƘA SAYA MASHI SAI ANA SANYA MASHI A BOX ƊIN NASA, DOMIN BAKA DA TABBACIN ZAKA RAYU DA YARONKA HAR YA KAI MUNZALIN YIN HANKALI, TO YA DAI KAMATA DUK ABIN DA YAKE SO ASAYA A BASHI, KADA A RINƘA BASHI KUƊIN KAI TSAYE!!!

Suna ƙokarin fita daga cikin ɗakin ne wayar Rimsha ya fara kara, haka kawai ta ji gabanta na faɗuwa, kamar ba zata ɗauki wayar ba, sai kuma ta koma ta je ta ɗauka, new number ta gani, zubawa number ido ta yi tana mamakin ita dai tasan cewa Yaya Ahmad da Aunty Akila ce kawai ke da number wayarta, ko Imran bata da number wayarsa, tana ta tunane tunane har wayar ta katse, yana katsewa sai ga saƙo ya shigo, Ki kunna data, shine kawai abin da aka rubuta a saƙon.

Cike da tsoro ta kunna data, tana kunnawa video call yana shigowa tare da wani sakon a WhatsApp, sakon ta fara karantawa da wannan number kuma. Yaya Imran ne ki ɗauki kiran, a wajen heartbeat na karɓin number ki, shi abin da ta gani a WhatsApp ɗin. Bata san time da murmushi ya suɓuce mata ba, da har ta tsorata sosai.

Picking na video call ɗin ta yi tana murmushi, wani irin muguwar kaɗuwar gaba ta ji lokacin da dara-dara sleeping eyes nata suka sauƙa akan Lion ba yaya Imran ba, yana zaune a gefen gadonsa yana ɗan latsa wayarsa, kansa na a kasa, da alama abu mai muhimmanci yake yi, da alama kuma bai san Imran ya sa mashi camera ba, har wani shocked ta ji jikinta ya yi, ta kasa motsawa, yau ga shi nan a gabanta ba face mask, kamar a mafarki, sai faman lumshe dara-dara blue eyes nasa yake yi, kamar mai jin barci, wayan nan zara zaran eyelashes ɗin nasa, da ya lumshe ido sai ki gansu kamar ya sanya na kari sabo tsawon su.

Hannu tasa ta toshe bakinta tana bin jikinshi da kallo shi kuma Imran yana bin fuskar ta da kallo, yana jin matsanancin farinciki yau ya sakata farinciki, zuba mata ido kawai ya yi yana kallon yadda take bin Lion da kallo, da wayan nan dara daran sleeping eyes ɗin nata, kwata-kwata bata kawo a ranta cewa Imran ɗin yana kallonta ba, dan kunga ya juya mata cameran.

Ganin ta yi shiru tana kallon waya ba wani motsi ne yasa Akila ta zo ta leƙa wayar tana faɗin "Me kike kallo kika natsu haka kodai....." Bata karisa maganar ba ta ɗauke wuta sakamakon sauƙa da idon ta ya yi akan Lion, ita kuma Umaisha tuni ta yi waje tun lokacin da Akila ta ce su tafi cin abin, sai tayi gaba.

Suna tsaka da kallonsa basu ankaraba sai gani suka yi ya ɗago wannan fusataccen fuskar nasa, kai tsaye kuma sai kan Imran ya sauƙe idanunsa, yadda kasan su yake kallo saboda saitin cameran yake kallo, razana tasa Rimsha ta saki wayar tata ta faɗi kasa, ba ita kaɗai ba har ta AKILA kwarjininsa ya razanata sosai da sosai, da kyar ta iya jan numfashi tare da haɗiyar wata wahalallen yawu ta ce "Rimsha aiki na gaban ki, wlh dole ki suma ashe haka yake da bala'in kyau, kai kai kai tab sai ki shirya wannan fusataccen fuskar kamar zaki, gaskiya sai kin dage, innalillahi kina ganinsa, wlh ni da nake kallonsa cikin face mask ban zata haka bala'in kyau nasa ta kai ba, ga gwarjinin bala'in, ni nayi nan Allah yasa kada na kara ido huɗu da shi, ya tsaya a iya nan kawai". Ta kai karshen maganar tare da nufar wajen.

Har ta kai kofar fita kuma sai ta ga Rimsha fa ba ta motsa ba, da sauri ta dawo ta taɓa ta tana faɗin "Ke lafiya?" Ashe suman tsaye ta yi, irin abin nan da ake cewa fitar ruhi na yan mintuna, shi Rimsha ta yi, kamar wadda ta suma haka ta kasance, bata ji kuma bata gani, sai da Akila ta zaunar da ita saman bed tare da kawo mata ruwan sanyi dan tasha zuciyarta ya yi sanyi, kafa mata robar ruwan ta yi a bakinta bayan ta buɗe, tanayi yana yi mata dariya, cike da zolaya ta ce "Rimsha dama ba za ki iya ba kika fara? Tab ai kuwa tom da sauran suma a gabanki, Allah ya nuna mani ranar da zai ga zanen nan kuma in ga ta tsiya, wata kila mutuwa zaki yi ranar ko? In Sha Allah sai ya ga zanen nan zaki yabawa aya zakinta kuwa, ke ba yar soyayya ba" tana magana tana dariya.

Rimsha kuwa sai da ta ɗauki good 20mins kafin ta iya dawowa daidai ta watsake, da taimakon Akilar, bayan ta watsake ma ta jima zaune a wajen, ita wannan fusataccen fuskar tasa ce ke matukar razana ta, idan ta kalli wannan fuska sai ta ji kamar ita ya zo kashewa, bayan fuskar kullun a fusace ga kuma bala'in kwarjini a tattare da shi, sannan ga dara-dara idanunsa masu wani irin yanayi na rikitar da wanda ya kalla, abin sun haɗu da dama ne akan fuskar tasa.

Bayan ta tawo daidai ne suka lallaɓa zuwa palo, Akila ce ta dawo ta ɗauki wayar suka wuce Palo.

Suna zama Akila ta fara dube dube a wayar, sai taga hotuna da videos nasa kusan guda 20 Imran ya turawa Rimsha, wata hoton ma tun suna school.

Ba karamin rikicewa suka yi ba, kuma bin da ya kara rikita su shine hoton TRIPLETS da Imran ya toro, James ne ya ɗauke su hoton suna kwance a saman katafaren bed ɗin Lion ɗin , har ma da wani shot video da James ɗin ya ɗauke su suna a bedroom na Lion, Michael yana kwance saman bed yana zancen yana son kuɗi, shi kuma Lion yana zaune a befen bed ɗin a lokacin yana latsa laptop, James ɗin kuma yana faman serving na Lion abincin, bayan ya ɗauke su su biyu, sai ya juyo da camerar ya ɗauki kansa.

Wannan hoto da video na TRIPLETS ba karamin tashin kan su Rimsha ya yi ba, dama su uku ne, shine abin da suka iya faɗa kawai, ga su da yake jini ba wasa ba sai su ka yi masu kallon kama ɗaya, sun razana sosai.

Wunin yau dai abin da suka yi ta kallo kenan, kuma ganin videos ɗin da pics ɗin yasa Rimsha ta rage tsoron fuskarsa, saboda ta yi ta gani sosai, ta wuni tana gani.

(Yau fa Rimsha duniya ta samu, an samu sabon Film, Imran nata kara hura mata wuta, zaki yi bayani, ki biye mashi ke dai ya kai ki ya baro, ki zama ba tsuntsu kuma ba tarko, dan ina da tabbacin daga ke har Imran ɗin naushi ɗaya ya isa Lion ya tura ku in da ba'a dawowa🤣)

Bari mu waiwaye gidan ABBI tun da ita dai Rimsha yau duniya ta samu.

Wani uban kwalliya ta ci, da yake ita mace ce mai gyran jikinta sosai, tana shan kunun larabawa, wato alkama da farar shinkafa, sai hakan yasa ba zaka taɓa cewa ta haifi su Irfan ba, ga shi ba laifi tana da kyanta daidai gwargwado kuma ya haɗu da gyara, dan gaskiya Hajiya Hadiza tana kashewa jikinta kuɗi ba wasa, shiyasa take bala'in shiri da Hajiya Batula wadda ta kasance kanwar su Abbi ce, ita ce autar su, tana aure ne a Maiduguri, duk wata macen da take gyaran jiki a kusa da su, zaka tarar da wuya idan bata san Hajiya Hadiza ba, gata da son kunshi, makirci, kistsa, ba abin da bata iya ba.

Yau wasu shegun riga da sket ta saka, sai ta dawo kamar yarinya yar 25 years, tayi kyau ba karya, akwai ta kuma da son cin chewing gum, haka ta zuba wasu shegun chewing gum nan a bakinta masu bala'in kamshi, sai wani kas-kas-kas take abinta, kayan nata sun bi shap ɗin ta sun zauna, da yake akwai shape ɗin, ita Umaisha ta gado akwai sss sosai, saboda tsabar gyara har surgery na tumbi ta biya aka yi mata, sai cikin nata ya koma plat kamar na budurwa yarinya karama, hakan ya bata daman sanya duk irin ɗinkin da take so kuma ya zauna mata daidai, sai tashin wani shu'umin kamshin perfume na Hajiya Batula da ta haɗa nata take yi, tana kwance saman bed nata tana ɗaura kafa ɗaya bisa ɗaya tana wani shan kamshi, sai da ta ji fitowar Abbi sannan ta sanya wani shegen flat shoe a kafarta mai shegen kyau ta fito waje.

Tana fitowa suka haɗu da shi da aunty zai wuce Aunty zata raka shi, tsabar iya kirsa da makirci har kasa ta tsugunna irin ladabin nan ta ce "Ina wuni sahibina?" Kamshin perfume ya daki hancin Abbi, tsabar kyan da ta yi ma da farko bai gane wace ce ba ce, ya ɗauka wata baby yar cakwai ce, sai da ya ji Muryarta ya gane.

Bata barshi ya yi dogon tunani ba ta miƙe tare da karɓar jakar hannun Aunty tana faɗin "Kai kanwata bari na hutasheki, kinga kin jima kina yi mashi rakiya, yau bari na karɓa maki, ki huta kema, amma sahibina gaskiya wannan kanwar tawa akwai ta da kirki, baka ga da na dawo gidan nan yadda ta rinƙa ɗawainiya da ni ba, har da ce mani fa ta yi na zaɓi ɗakin da nake son zama, gaskiya ina kaunar ta sosai sahibina, dole kuma na kula da ita" ta kai karshen maganar tana jan mashi dogon hancinsan nan.

Yau Aunty taga karuwanci da tsakar rana ido da ido, Allah sarki Abbi Hajiya Hadiza bata bari ya yi wani yunkuri ba, ta yi saurin saye bakin nasa da salon kirsan ta, ya sami wasu abubuwa da Aunty ke jin kunya bata yi mashi, irin wasa da sauransu, har wani jan hancinsa hanjiya Hadiza ke yi, tana wani langwaɓar mashi da kai kamar yarinya, nan take ta rikita bawan Allah nan.

Har yana haɗe words wajen ce mata "Khadija yaushe kika dawo?" Jin haka ya yi mata magana a nutse ba da faɗa ba yasa ta kara narkewa da kashe murya (kamar tsohuwar kwartuwa) tana zuba mashi kirsa da makirci, Aunty dai yau taga tsantsan bariki data ci uban na Rufee, har wani shafa mashi wuya Hajiya Hadiza take yi, da yake ta yi wa kayanta farin sani, ita kuma Aunty kunga bakuwa ce, ba komai ta sani ba, Hajiya Hadiza ta san lagonsa fes, tasan ta yadda zata bi da shi ta zautar da shi.

Da Aunty taga ana ƙoƙarin runguma a gabanta sai ta sa kuka ta juya ta koma ɗakinta. Ɗan waigawa ya yi ya kalleta yana faɗin "Me ya faru Halima?" Ya zauce da kirsan Ommu har baya son yin magana sosai.

(Mata bala'in ne wata zubin, kai kuji makirar mace tab🤔🥺)

Cike da kirsa da makirci ta ce "Sahibi ka je ka rarrasa mani kanwata ta yi shiru, tana da kirki bana son ta ɓata rai" tana magana tana rungume shi, shiru ya ɗan yi, shi kaɗai yasan me yake ji.

"Hadiza wai yaushe kika dawo ne?" Shine abin da ya iya faɗa, kara shigewa jikinsa ta yi tana shagwaɓe fuska tare da turo baki kamar yarinya ta ce "Sahibi wai meyasa kake tambaya ne? To koma me ka je wajen aiki ka dawo akwai wani abin dana tanada maka, sannan sai mu yi hiran ko rabin raina? Yanzu dai kafin ka tafi ka rarrashe mani kanwata ka ji?".

Bawan Allah nan ya rasa bakin magana, domin harshen Ommu karfi ke kareta kamar reza, haka ya juya ya karɓi umarnin ta zuwa wajen Aunty dan ya rarrashe ta.

Yana tafiya ta saki wani shu'umin murmushi kasa-kasa ta ce "Yarinya da Hadiza bage maganin maza kike yi, ke baki ma ji sunan ba, maganin maza, sai na dafaki ta hanyar da ba wanda zai taɓa yarda kina dafuwa, ke yau kika gani, mu kuma mun ga jiya munga yau har ma da shekaran jiya, ki jira ki gani, Hadiza bata zama da kishiya, nan gidana ne ni kaɗai". Ta kai karshen maganar tare da wucewa cikin ɗakinta tana ayyana yadda zata rikita Abbi da yamma idan ya dawo.

(Tofa Aunty gara maki Rufee da wannan hamshakiya, ba abin da za mu ce sai dai Allah ya kuɓutar da ke😭)

Kuka Abbi ya iskota tana yi, ta haye saman bed nata tana kuka, gefenta ya zauna yana faɗin "Halima lafiya kuwa?".

Cikin kuka ta ce "Haba Abbi akan me zaku ci mani fuska haka?" Yar dariya ya yi kafin ya ce "Haba Halima! Kefa kika bawa Hadiza dama ta zaɓi ɗakin da take son zama, bai kamata yanzu kuma ki dawo sheɗan yana zuga ki kice wani abin ba, kamata ya yi kema ki so ta kamar yadda ta so ki, kuma kamar yadda kika faro tun farko, ki duba ki gani fa yadda take yabon ki, baki ga matsa mani da ta yi akan lallai sai na rarrashe mata kanwarta kafin na fita ba, amma ki yi hakuri, idan na dawo zamu zauna mu yi magana kin ji ko?" Bai jira amsarta ba yana kai karshen maganar ya manna mata kiss a goshi ya miƙe ya fita.

KADA KU GA LAIFIN ABBI, MAKIRAR MACE BA WASA BA, KAWAI KU TAYA AUNTY ADDU'AR ALLAH YA KWACE TA, AMMA MAKIRAN MATA SUN WUCI TUNANIN MAI TUNANI, BA BOKA BA MALAM SUKE MALLAKE GIDA, SU KUMA JUYA DUK WANDA SUKE SO, KUNA DAI GANI TA HANA ABBI MAGANA, SAI WANI RUFE MASHI BAKI TAKE YI, DUK WANI ZAFIN NAMIJI SAI DAI IDAN BAI HAƊU DA MAKIRAR MACE BA, TUNI ZATA JUYA SHI, KO SHEƊAN TSORON MAKIRAN MATA YAKE YI BARE MUTUN, ALLAH DAI YA RABA MU DA IRIN SU

Yana fita aunty ta kara rushewa da wani sabon kukan tana faɗin "Ya Allah na wannan wace iriyar masifa ce, matar nan tun zuwanta ta ce bata so na, hasali ma bata kula ni ba, amma yanzu ta zo ta ce mashi wai tana so na, kuma zata kula da Ni, har da wani cewa nayi ɗawainiya da ita na bata zaɓin ɗaki, ta kashe ni ta gama da ni, Allah ka mani sakayya da gaggawa!!!"

KUNJI ABUN DA YA FARU DA AUNTY JIYA KENAN BA RI MU DUBA WAJEN SU IRFAN MU DAWO.

Daga karshe dai Irfan da ya gama waya ya buɗewa daddyn Jelly kofa tare da gaya mashi yadda suka yi da bandits ɗin, sannan kuma ya ce Akil ya ce zai bada kuɗin, zai cire daga Account nasa, sai su kai su ɗauko Aafia ɗin. Har wani nauyayyar ajiyar zuciya daddyn Jelly ya sauƙe dan ba karamin tashin hankali ya shiga ba, ƴa budurwa a hannun yan bandits ɗin nan, abin dole akwai tashin hankali.

ALLAH SARKI BA KU MA SAN AN GAMA LALATA MATA RAYUWA BA😭.

AFTER SOME HOURS👌

Aunty da Ayla ce zaune a palo suna hira, yanzu sun ɗan samu sauki a ransu tun da su Akil za su je ɗauko Aafia ɗin.

Sai hira suke yi Aunty na kara koya mata yadda zata zauna da mijinta, yadda zata yi da daddyn ta.

A wannan hali ya shigo bakinsa ɗauke da sallama ya same su, saman sofar kusa da babynsa ya zauna yana faɗin "Sadiya me ya same ki naga idon ki sun kumbura sun yi ja haka?" Murmushi ta yi kafin ta ce "Babu komai yaya Maik".

Shiru ya ɗan yi kafin ya ce "Saboda A'afia ce?" Girgiza mashi kai ta yi alamar a'a ba komai.

Dawo da kallonsa kai Ayla dake ta faman ɓoye fuska ya yi "Baby wai har Yanzu baki dai na jin kunya ta bane?".

"Ina wuni daddy" shine abin da ta ce mashi, hannu yasa ya ɗan buge mata baki, cikin sauri ta rufe bakin nata da hannun ta tana yin kasa da kanta.

Dariya Aunty ta yi kafin ta ce "Kun dai fi kusa ni bari ma na kawo maku abinci ku ci sai ku ji daɗin yin hirar" cikin sauri ya ce "A'a Sadiya ba sai kin kawo ba ni ba zan ci ba". Bawan Allah damuwar rashin A'afia da kuma halin da suka sami labarin tana ciki ne ya hana shi cin abincin.

"To idan ma ka ƙoshi ai babyn taka bata ƙoshi ba, taki cin abinci tun safe" ta kai karshen maganar tare da miƙewa ta nufi dining table dan ta ɗauko mashi abincin.

"Baby baki ci abinci ba, me yasa?" Ɗan satar kallon shi ta yi, nan take kuma abubuwa da Aunty ke gaya mata akan abin da zata rinƙa gaya mashi, ya faɗo mata a cikin ƙwaƙwalwarta, tuna haka yasa sai ta ce "Kai nake jira daddy muci tare". Ɗan waro dara-daran idanun nan nasa waje ya yi yana faɗin "Haba dai?" Ya yi maganar cike da jin daɗin furucin ta da kuma tsantsan kaunar ta. Gyaɗa mashi kai kawai ta yi yana murmushi.

A gabansu aunty ta zo ta ajiye mashi tray ɗin abincin tana faɗin "To aci lafiya" ta kai karshen maganar tare da hayewa sama ta ba su waje.

Ƙoƙarin fara zuba masu abincin ya yi, cikin sauri ta sauƙo ta karɓe shi tana faɗin "Daddy ka bari na zuba mana, ba aikin ka bane ai" ɗan leƙo fuskarta ya yi yana faɗin "Ya naga yau kin kara tsantsan kyau ne?" Hannu tasa ta rufe fuskarta tana dariya.

Riƙo hannayen nata ya yi, har yanzu ya kasa dai'na taɓa mata hannu saboda da haka suka saba, ya saba riƙeta, amma dai yanzu baya yarda ya rungumeta idan yana rarrashinta, sai dai ya goge mata hawaye kawai.

Janye hannun nata daga kan fuakarta ya yi yana faɗin "Ni da fuskar baby na ne zaki rufe Mani? Ina ruwan ki?" Zata yi magana kenan wayarsa ta fara kara, cikin sauri ya saketa tare da fito da wayar daga aljihunsa domin dama yana jiran kiran su Irfan dan ya fita zai je ya haɗu da Akil su je wajen yan bandits ɗin kai kuɗin.

Miƙewa tsaye ya yi tare da yin picking call ɗin yana kara wayar a kunnansa,.

A ruɗe Irfan ya fara magana cike da tashin hankali.

"Hello bappa, mun samu nasarar karɓo su Aafia sai dai kuma kamar fa ta rasu bata da rai, bata numfashi, amma dai mun nufi hanyar asibiti da su yanzu, ka same mu a can, kuma dan Allah kada ka gayawa Abbi, ka bari tukun nan sai mun ji me likitoci za su ce, dan ina ji a jikina doguwar suma ta yi" ai tun Irfan bai karisa magana ba daddyn Jelly ya fice cikin sauri.

Kai tsaye part nasu ya koma ya ɗauki key ɗin motar Irfan ɗin ya shiga da gudu ya bar gidan, yana tafiya a hanya ne Irfan ya tura mashi address ɗin asibitin, ba ɓata lokaci ya isa can.

Wani katafaren private hospital ne, yana isa kuma lokacin motar Akil ɗin ta danno hanci cikin asibitin, a tare suka yi parking na motocin a parking space na hospital ɗin.

Akil ya riga kowa fitowa, fuskar nan tasa babu alamar sauki ko kaɗan, yau a ɗaure take tamau, haka suka fito da Aafia da kuma Hanan, Aafia kamar babu rai a jikinta, fuskar nan ta yi wani Yellow kamar bata da jini, ita kuma Hanan bata suma ba, idon ta biyu.

Readers Also Read

More by Bilyn Abdull