Triplets book 2 complete - Chapter 6
Triplets book 2 complete Chapter 6: Triplets book 2 complete Chapter 6. Tana kitchen Akil ya dawo bata sani ba, bedroom na su ya wuce hannun sa riƙe da…
4,478 words
Tana kitchen Akil ya dawo bata sani ba, bedroom na su ya wuce hannun sa riƙe da wani katon trolley yana ja, dan shi saboda kishin sa bai yarda mai gadi ko mai bawa flowers ruwa ko driver su taya shi ɗaukan kayan matar sa zuwa cikin gida ba, a'a da kan sa ya jido komai zuwa cikin bedroom na su.
Yasha mamakin ganin Umaisha bata ɗakin, shi da yayi tsammanin zaizo ya same ta kwance, dan bata jin daɗi, sai kuma yazo yaga bata nan.
Bayan ya gama shigo da kayan, toilet ya fara leƙawa, wayam ba ta ciki, hakan yasa ya fito waje dan ya duba ta.
Lokacin da ya fito palo, lokacin ita ma Ammie ta fito daga bedroom nata, ta sauƙo ƙasa
"Ammie where is my wife" ya faɗa yana ɗan waige waige kamar mai neman wani abu, Murmushi makirci Ammie tayi kafin tace "Ashe yarinyar nan yar albarka ce Akil am, ni ban sani ba, na dage ka rabu da ita, ashe yar halak ce, tun ɗazun ta fito ta fara shara da mopping, nayi nayi ta bari amma taki, tace ita kam tana son taga tana yimin aiki, dan a matsayin uwa ta ɗauke ni, tana cikin Kitchen tana faman gyarawa", murmushi shima yayi kafin yace "Ai daman Ammie na faɗa miki, zaki so ta In Sha Allah dan tana da hankali" kara faɗaɗa murmushi ta Ammie tayi tanan faɗin "Ai tunima na kamu da son ta, yarinya yar albarka haka, ina hana ta aikin nan, yarinyar nan tace sai dai na kyale ta tamin, nace ta bari bata da lafiya, amma taki tace zatayi, har da kuka ta samin, kamar yadda kaga Akila ke yimin ita ma haka ta min, baiwar Allah a uwa ta ɗauke ni" shima kara faɗaɗa murmushin sa yayi yace "To yanzu dai ta bari tazo taci abinci tasha magana, sannan tazo ta ci-gaba" shiru Ammie ta ɗan yi kafin tace "Eh hakan ya kamata" wucewa yayi ya nufi kitchen ɗin ba tare da ya sake magana ba, harara Ammie ta bishi da shi, a zuciyar ta tana faɗin "Sai ka koreta da kan ka, In Sha Allah, ko kuma ita da kan ta, ta gudu"
Umaisha na aikin wanke-wanke tana kuka, kusa da ita yazo ya tsaya, tare da rungumota ta baya yana faɗin "Ke kika jawa kan ki, kin san baki da lafiya me na cewa lallai sai kin yi aiki? To gashi yanzu kina yi kina kuka, nasan kuma dole daman kiyi Kuka, saboda ba koshin lafiya gare ki ba, yanzu dai ajiye aikin muje na baki abinci, kici ki sha magani ki ɗan huta, sai ki dawo ki ci-gaba da aikin" ajiye soson wanke-wanken dake hannun ta tayi, tare da kunna pampo ta wanke hannun ta, sannan ta juyo ta rungume sa da kyau tana kara faɗaɗa kukan da take
A ɗan ruɗe yace "Lafiya? Me kuma ya saki kuka?" Yayi maganar yana ɗago haɓar ta, cikin kuka tace "Yaya Akil dan Allah ka mai dani gida kaji?" Hannu yasa yana goge mata hawayen dake zubowa yana faɗin "Ya isa haka, kiyi shiru, zan kai ki gida amma ba yanzu ba, kiyi hakuri sai bayan sati biyu kinji ko?" Gyaɗa masa kai kawai tayi bawan dan ta gaji da rokan sa ba, a'a sai dan bakin ta ya mata nauyi, ta sha wahala, tun da Akil yayi dis virgin ɗin ta take cikin wahala da azaba, ta gala bai ta sosai, tasha wahala.
Hannun ta ya riƙo yana faɗin "Muje ko?" Da kyar ta iya ɗaga kafa ɗaya, tana kara sautin kukan nata, ganin haka yasa ya ɗauke ta cak ya fice daga kitchen ɗin.
"Akil me ya faru? Lafiya ka ɗauko ta haka?" Cewar Ammie tayi maganar cike da nuna damuwa na makirci, "Ammie kafar ta ke yi mata ciwo" ya faɗa yana haurawa sama, bin sa da kallo takaicin Ammie tayi har ya shige part ɗin sa.
Saman sofa ya zaunar da Umaisha yana faɗin "Sorry my wife" sai jan hanci take, alamar tasha kuka har ta koshi.
Abinci ya ɗauko mata, da kan shi ya zauna kusa da ita, ya fara bata a baki, tana ci tana kallon cikin idon sa, lokaci guda taji mugun son shi na shigar ta, "Ke wai me yasa kike yawan kallon fuska nane?" Ya tambaya yana kallon ta shima, shiru tayi ba tayi magana ba, dan bata da amsar da zata bashi "Ba za kiyi magana ba?" Nan ma shiru tayi, kuma ba ta daina kallon nashi ba, "Ki dai na kallo na, kada ki haifa min baby mai kama dani, dan ni mai kama dake nake so" nan ma shiru ta masa, still har lokacin ko kyafta idon ta ba tayi ba, ta tsare sa kawai tana kallon sa, duk abubuwan da yake faɗa ma, basa shiga kunnan ta, tana can duniyar tunanin son da take masa, da kuma yadda za tayi ta bar wannan gida, dan zaman ta da Ammie ba zai yiwu ba.
Hannu yasa ya rufe mata ido yana faɗin "Zan rinƙa saka nikaf kada ki kwashe min kyau na, da wanan irin kallon naki" murmushin cikin kuka tayi har sai da ta sanya shi sauke nauyayyar ajiyar zuciya, uhm soyayya daɗi.
Sosai ya ɗura mata abincin nan, sai da ya tabbatar ta koshi, sanann ya ɗauko maganin ta ya bata, bayan ta sha, ya ɗauke ta zuwa toilet, da kan sa ya mata wanka, yana yi yana tsokanar ta, har suka gama suka fito, ya buɗe trolley da ya sayo mata kaya, ya ciro mata wani dogon riga mara nauyi, ya bata ta karɓa ta sanya.
Bayan ta gama shiri, yace ta hau gado ta kwanta, ba musu ta haye gado ta kwanta tana jin matikar kaunar mijin nata har cikin ranta, shi ba mugu bane kamar yadda take tunani, idan ka fahimce shi zaka ji daɗin zama da shi, shi raini ne baya so, kuma yana son a nuna masa shine a sama da mutun, yana son abashi kulawa, kuma a nuna masa ya isa da mutun, baya son a masa jayayya da maganar sa idan yayi, ya fison da yace abu ace masa to, kuma baya son ya kawo abu ya baka kace masa color ko wani abu bai yi maka ba, a takaice dai shi ka nuna masa shine boss, idan kayi haka zaku zauna lafiya, zai maka abun da ma baka taɓa tunani ba na alkhari da kyautatawa.
Har ta fara barci sai taga yana kokarin fita, zubur ta miƙe zaune tare da saka masa kuka tana faɗin "Yaya Akil dan Allah karka fita" juyowa yayi yana kallon ta da mamaki, ganin da gaske take masa kuka har da hawaye yasa ya dawo kusa da ita ya zauna tare da ɗan rungumota kaɗan yana faɗin "My wife me yasa kike kuka?" Kankame shi tayi tare da kara faɗaɗa kukan nata, dan tasan yana fita Ammie zata zo ta saka ta aiki, kuma jikin ta na mata ciwo "My wife kiyi magana mana, me yasa kike kuka?" Cikin kuka tace "Yaya Akil dan Allah kada ka fita, ka zauna kaji?" Mamaki ne ya kara kama shi, hannu yasa ya ɗago haɓarta yace "Wajen bappa zanje fa, yaya Imran ya aike ni, yace lallai naje gidan ku na duba masa ina bappa Maik ya kai Jelly, dan kullun idan suka kira shi, sai yace musu ko tana barci ko ta tafi shopping da Aafia, shine yaya Imran yace naje na duba masa, dan ya shiga damuwa sosai yana ji a jikin sa kamar ba lafiya ba, akoi abun da bappa Maik da kuma Abbin ku suke ɓoye masa, ki bari naje na dawo, ba zan jima ba kinji?" kara kankame shi da kyau tayi tana cusa kan ta a kirjin sa, cikin kuka tace "Ni dai a'a wlh ban yarda ba, sai dai mu tafi tare, ko kuma ka zauna babu in da zaka je" lokacin guda yaji wani bakin ciki ya ziyarci zuciyar sa, ba komai ne ya hassasa hakan ba, face cewa da tayi ya zauna babu in da zashi, a nashi ganin ta raina shi umarnin ma take bashi, dan haka sai ya daka mata tsawa "Ni zaki gayawa abun da zan yi? Wato umarni ma kike bani, na zauna babu in da zanje, to baki isa ba, ke mata tace a karkashi na kike nine zan baki umarnin ba kece zaki bani ba, I am the boss here" ya kai karshen maganar tare da kwace jikin sa daga riƙon da ta masa, ya miƙe ya fice daga bedroom ɗin yana wani hucin ɓacin rai, yau Umaisha ta raina shi.
Oh Akil manya, wannan ma bashi ne babba a gidan ba, idan da shine Imran kam, ai da shikenan an shigesu, mutun sai bala'i son girma, Umaisha aiki na gaban ki, babba kuwa. Masu karatu mukoma wajen First lady wato Rimsha, Meesha, Siha, first lady, duka sunan tane, ɗaya tamkar da dubu in ji daddy ta, bari mu leƙo ta mu dawo.
Ayla da Kausar tas suka take abincin nan, Kausar kam har da lashe kwano da harshen ta, tas tayi wa kwanon kamar an sanya ruwa an wanke kwanon miƙewa tayi hannun ta riƙe da kwanon tuwo dana miyar duka bayan ta gama lashewa "Ina zaki je Kausar?" Cewar Rimsha, kumbura kumatu tayi tana ɗan jujjuya ido tace "Zanje in ce su kara min abincin mana" salati Ayla tasa tana tafa hannu, Rimsha kam ta rasa bakin magana dan Kausar tafi karfin ta, daman haka Kausar take, a daular mutuwa ne take kamar malama, tab lallai daman idan kuna cikin wahala da kunci baka taɓa gane halin mutun, sai kun samu freedom ko yaya ne.
Suna tsaka da tunani, basu san lokacin da Kausar tayi wuce wan taba, basu fargaba sai ganin Kausar sukayi da wani kula a hannun ta, zama tayi a in da ta tashi, ta bude kulan abun ta ta fara cin abincin "Ke Kausar waya baki wannan abincin?" Cewar Rimsha, turo baki tayi tace "Gani mana nayi na ɗauka" salati Ayla tasa tana faɗin "Wlh abincin yaron sarki ne, kuma bashi da mutunci mashayin giya ne lamba ɗaya, shekaran jiya dana zo gidan nan, wlh ya kusa yimin fyaɗe dan yasha ya bugu, da kyar maman sa ta kwace ni a hannun sa"
ina ai su Ayla zancen su kawai suke ita kausar bata tare da su, loma kawai take kaiwa baki abun ta, hannu baka hannu kwarya, har wani lumshe ido take, saboda daɗin miyar matar sarki, hannu Ayla tasa ta janye kulan abincin daga gabar Kausar, ta rufe tana faɗin "Ke so kike a koremu daga gidan nan ko? To wlh ki dawo cikin hankalin ki, kin samu sun bamu abincin da masauki ba zamuyi taka tsantsan dan mu samu mu rabu da su lafiya ba" turo baki Kausar tayi kafin tace "Ori dafun" kallon Rimsha Ayla tayi, sannan ta dawo da kallon ta kan Kausar tace "Ke kika san shi" murmushi Rimsha tayi kafin tace "Ita ta san me kuma Ayla" "Ita ta san shi Ori dafun ɗin mana" dariya Rimsha tayi kafin tace "Kai amma fa idan baka jin yare akoi abu, dan a mahaukaci kake ɗaukan mai yin wannan yaren" miƙewa Ayla tayi, ta wuce kitchen na matar sarki taje ta mai da kulan abincin ta dawo ta zauna.
"Ayla dan Allah kiji mana ba gaskiya na faɗa ba, nace mu tara kuɗi mu tafi wajen GAR ɗin Meesha, dan yadda take bamu labari kinga ai mai kuɗi ne, idan mukaje zamu samu kuɗi, amma meesha tana min dariya" ita ma Ayla dariya ta kwashe da shi tana tafa hannu
kallon sama da kasa a cikin duhu Kausar tawa Ayla kafin tace "Ke ma a mahaukaciya kika ɗauke ni kenan?" Girgiza kai Ayla tayi kafin ta tsagaita dariyar tace "Haba Our Aunty yar lukuta, ni na isa in ɗauke ki a mahaukaciya? A'a bamu isa ba ai, kawai abun ne abun dariya, ke daga kinji cikin ki ya ɗauka yayi nauyi shikenan baki da wani case sai ki hau zuba zance mara kan gado, yanzu da kike wannan magana ma, uban wa zai bamu kuɗi, mu samu mu samu kuɗin mota mu koma wajen iyayen mu ma, tukun nan mana, kafin mu fara tunanin zuwa wani waje" shiru Kausar tayi bata sake yi musu magana ba dan gani take su duka basu hangi abun da take hango musu na kuɗin da zasu samu idan sukaje wajen GAR ba, amma ita dai koma ne tasawa ranta, sai taje wajen GAR.
"Ayla ya akayi kika fita daga daukar mutuwa?" Cewar Rimsha, Ayla za tayi magana, wani matashi ya shigo da irin Mp manyan nan, kiɗa na tashi na wakan yarbawa, ana wakar omomo maryamo ashokine lule ashokine lule.
Kamar wadda aka tsikara haka Kausar ta miƙe ta fara dikar rawa, irin nasu na yarbawa tana biye wakar, abun ku da yarba, shima matashin ajiye mp yayi suka shiga tika rawa tare da Kausar, yau Rimsha taga ikon Allah daman haka Kausar take, tirkashi, ita kam Ayla kwana biyu da tayi a nan ta saba ganin fiye da haka ma, mace da namiji suna rawa suna rungume juna haɗuwar titi rabuwar gate.
Sai wani kasa suke suna sama, Kausar da matashin nan, kamar wasu zabbi, kan kace me matar sarki ta fito daga nata ɗakin, tana karkaɗa jiki kamar kaza na karkaɗa fuka fukin ta, abun ma dariya ya bawa Ayla, yadda yau kuma matar sarki ta fito da wani sabon salon rawa na daban
Rimsha da Ayla sun shagala da kallon wannan chasun na su matar sarki, basu ankara ba sai ganin Kausar sukayi ta riƙo hannun Ayla tana faɗin "Taso ki taka mana" ba musu Ayla ta tashi dan wani lokaci idan matar sarki tana rawa, tana riƙo hannun ta suyi tare, a kwana biyun da tayi tare da su, shiyasa yanzu ta fara sabawa da rawan nasu.
Jawo Rimsha ma Kausar tayi suka riƙe hannu suna biyewa Kausar tana ta wani jijjiga su, ita kam Rimsha duk ta in da Kausar ta ja ta, bin ta kawai take kamar wani igiya, babu wani action ba komai, zololo zololo take bin ta dan bata saba ba.
Sun ɗauki 45 mins suna chashewa kafin nan, su zube kasa a wajen suna mai da numfashi, matar sarki kam bata yi rawa sosai ba, bata fi 20mins ba ta tafi ta basu wajen. Bayan sun zauna ne, matashin ya kashe kiɗan yana kallon su a cikin duhu, duk da cewa akoi hasken wata, amma ba sosai ba
"Alay yaushe mukayi baki?" Cewar matashin, yayi maganan da broken English, Ayla zatayi magana Kausar ta rigata cikin harshen yarbanci tace "Sunan ta Ayla ba Alay ba" murmushi tayo yayi kafin yace "Ba zan iya faɗa hakan ba, shiyasa nake ce mata Alay" shiru Kausar ta ɗan yi kafin tace "Okey boder daga nan zuwa ilorin akoi nisa?" Yayi mamakin jin yadda Kausar ke yarbarnci reras, dan haka sai ya kunna wutar mp sa mai bala'i haske dan yaga fuskar ta da kyau.
Sai dai kunna wutar da yayi ta ja mashi matsala, domin kuwa yana haske su, yaji duk duniya ya samu mata, tun da idon sa ya sauƙa a kan Rimsha shikenan, sai dai kuma ko da ya haska mata wutar a ido, tsawa ta daka masa da karfi wadda sai da gaba ɗayan su suka tsorata. Da sauri Ayla ta dafa ta tana faɗin "Rimsha lafiya?" Ture hannun Ayla tayi, cikin tsawa tace "Kada ku sake haska min haske a ido" Kausar ta tsorata sosai domin wanna ba muryan Rimsha bane kwata kwata, cikin sauri Kausar tayi baya, yayin da shima matashin ya kashe hasken mp nasa yana faɗin Sorry, shi da yake bai san kalar muryan Rimsha ba, sai yayi tunanin ko dai haka muryan ta yake, su kuma su Ayla already sun san yadda voice nata yake, shiyasa suka tsorata dan sunji wannan murya da tayi magana da shi yanzu dai ba muryan ta bane.
Tirkashi meyake shirin faruwa kenan, anya Rimshan gaske ce a wajen, idan ba Rimshan gaske bace, ina ta gasken take, meke faruwa da wayan nan yan matan ne? ya akayi Ayla ta riga su zuwa kauyen nan? Ya akayi ta kuɓuta daga hannun su Barbushi? Hmmm akoi cakwakiya mu dai je zuwa dan muga yadda zata kaya, tsakanin wayan nan yan mata.
💞💞TRIPLET'S💞💞
💔💔Episode 7-8💔💔
Ɗan baya kaɗan itama Ayla tayi dan ta tsorata jin yadda muryan Rimsha ta sauya lokaci guda, kallo juna suke cikin duhu, tayo kuma da bai san meke faruwa ba, sai ya washe baki yace "Alay wayan nan bakin naki da alama suna da faɗa" shiru Ayla ta masa, dan tsoron magana ma take, kada tayi wani magana kuma ya zama faɗa tsakanin ta da Rimsha.
Kausar ce tace "Boder baka bani amsa taba?" "Amsar me fa?" Ya tambaya yana kokarin tashi daga wajen "Amsar daga nan zuwa ilorin akoi nisa" hanyar fita daga gidan ya nufa yana faɗin "Babu nisa, daga nan zuwa cikin lasoju naira 200 ne daga lasoju zuwa eyankorin shima 200 ne daga eyankorin zuwa cikin Ilorin wato gari alimi 150 ne kuɗin transport kinga kuwa ai ba nisa" cikin sauri tace "A'a mu ba cikin Ilorin bama zamu shiga, a eyankorin zamu tsaya, a nan gidan mu yake" dai dai zai fita gidan yace "Naira 400 zai kai ki can ai" sosai Kausar taji daɗi, sun kusa isa gidan su.
Ita kuwa Ayla tunani take sosai a kan Rimsha menene ya sauyawa Rimsha muryan ta cikin kankanin lokaci haka, matsowa Kausar tayi ta dafa Rimsha tana faɗin "Meesha kin ji mun kusa isa gida ko?" A hankali kasa kasa Rimsha tace "Ke dai kin kusa isa gida, ni kam da saura na sosai" jin Rimsha tayi magana da normal muryan ta ne yasa Ayla matsowa kusa da ita tana faɗin "Meesha muje mu kwanta ko? Dare nayi sosai" suna kokarin miƙewa babban ɗan sarkin ya shigo cikin gidan yana wani tafiya yana bonshin wando na faɗu wa ya riƙe gefe.
Kai tsaye kitchen ya nufa yaje ya ɗauko abincin sa wanda Kausar ta ɗauka ta fara ci.
A inda tayo ya tashi a nan shima olohunwa wato ɗan sarkin yaje ya zauna tare da buɗe kulan abincin, ya zurma hannu ciki ya fara kai loma, babu ko wanke hannu.
Sosai Ayla tayi godiya ga Ubangiji da Allah yasa olohunwa ban gane cewa Kausar taci masa abinci ba. Lallaɓawa sukayi suka miƙe suka nufi wani ɗaki wanda ya kasan ce shine ma saukin su.
Babu komai a cikin ɗakin sai tabarman mai ɗan girma, da pillow guda ɗaya, sai godiya ga Allah suke, dan hakan ma ba karamin daɗi suka ji ba, domin a daular mutuwa ko taburman ma basu samu ba.
Addu'ar barci sukayi tare da kwanciya suka saka Rimsha a tsakiyar su, kasan cewar ita ce karama, dan a shekaru dukan su Ayla zata girme musu, dan ita zatayi 15 years, ita kuma Kausar 14 to 15, Rimsha ce karama mai 13 years, sai dai duk cikin su babau wacce ta fara period har yanzu, amma dukan su, sun fara kirgan dangi, Ayla kam ma har ta fara zama yan mata.
"Ayla baki faɗa mana ya akayi kika bar daular mutuwa ba" cewar Rimsha, shiru Ayla bata amsa musu ba, sake mai-mai ta tambayar Rimsha tayi, nan ma shiru Ayla bata amsa ba, hannu Rimsha tasa ta ɗan bubbuga Ayla tana faɗin "Me haka Ayla? Ki bani amsa na mana, sai magana nake, amma kinyi banza dani" shiru Ayla ba tayi magana ba, haurar da hannun ta sama Rimsha tayi tana laluɓar fuskar Ayla dan taji idon ta arufe ne ko abuɗe ne, dai-dai cikin Ayla taji wani abu kamar dutse gashi da girma kulu lu, a sukwane ta miƙe zaune tana faɗin "Ayla me a cikin ki?" Shiru Ayla ba tayi magana ba, gashi ɗakin da duhu, cike da tsoro Rimsha tace "Kausar ki taɓa cikin Ayala kiji wani abu kamar dutse" ita ma Kausar ɗin shiru batayi magana ba, hannu Rimsha ta sake kaiwa saman cikin Ayla, sai taji wayam babu komai, wannan dutsen ya ɓace, jijjiga Ayla ta fara yi da karfi tana kiran sunan ta "Ayla!! Ayla!! Ayla" cike da ruɗu da tashin hankali, dan a tunanin ta Ayla mutuwa tayi, tun da yanzu suka kwanta ba jimawa, amma ace Ayla tayi shiru kamar wadda ta mutu.
Ta kai 5mins tana jijjiga Ayla da karfi tana kuka, ga kuma Kausar ita ma kwance bata jin su, kuma bata motsi, ganin sunki tashi ne yasa ta miƙe da gudu zatayi waje, kamar a mafarki taji Ayla na cewa "Rimsha ya naji kamar kina magana?" Tashin hankali "What!!? Rimsha ta faɗa a tsorace, miƙewa zaune Ayla tayi za tayi magana, matar sarki ta shigo ɗakin hannun ta riƙe da ɗan ƙaramin fitilla irin mai amfani da battery remote ɗin nan, tazo ta ajiyewa Ayla a in da ta saba ajiye mata tana faɗin "Ya ke kuma kike tsaye" tayi maganar cikin harshen yarbanci, kasan cewar ita Rimsha bata jin yarbanci sai tayi shiru bata amsa ba, kamar a mafarki Kausar da Rimsha ke ta kira tun ɗazun tace cikin harshen yarbanci "Meesha bata jin yarbanci" shafa kan Rismha matar sarkin tayi tace "Fine girl" sannan ta wuce ta fice daga ɗakin.
Dawowa Rimsha tayi ta zauna kusa da Ayla tayi shiru tana mamaki, me yasa duk lokacin da ta tambayi Ayla ya akayi ta fita daular mutuwa sai wani abun ya gipta, kuma da alama Ayla bata son sanar da su ta yadda ta fito daga daular mutuwan, dan da farko da suka tambaye ta, tace musu sai sun huta, na biyu kuma tayo yazo, yanzu kuma gashi ta sake tambayar ta daga ita Ayla ɗin har Kausar duk sunyi kamar sun suma, basa jin komai, anya ba wani abu kuwa.
To masu karatu me kuke tunani game da Ayla, Kausar, da kuma Rimsha? Mu haɗu a comments section.
A takaice dai a wannan dare Ayla bata samu damar sanar da su ya akayi ta fita daga daular mutuwa ba, haka zalika ita kuma Rimsha bata dai na tunanin yadda akayi Ayla ta fito daga daular mutuwa ba kuma ya akayi ta kasa faɗa musu ta yadda ta fito.
Kasa barci Rimsha tayi tana tunani, su kuwa Kausar da Ayla tuni sunyi barcin su abun su, sai can tsakiya dare sannan barci ɓarawo ya ɗauki Rimsha tunani cike fal ranta.
A ɓangaren Jelly kuwa, yau gidan babu kowa, Hajiya ta tafi super market yi musu shopping, Nawid yana Katsina gidan kakanni sa, shi kuma Abbo bai dawo ba, ita ka ɗai ce zaune a palon Hajiya, tayi zaman yan bori, ta baje abun ta, kafa ɗaya can ɗaya nan, tayi ɗai-ɗai, ta tasa abubuwa a gaban ta, irin su chocolate, Ice cream, yogurt, soyayyen naman kaza, sweet da sauran su,
Gaba ɗaya ta damalmale wannan ɗan bakin nata da ice cream, har gemun ta, duk sai da ya samu ice cream sai taunan naman kaza take, ga wani cinyar kaza a hannun ta, tana ci tana kaɗa kai tare da lumshe idanun ta irin santi na ɗeban ta. Jikin ta na sanye da wandon jeans pink color da yar riga mai karamin hannu white color, ta sanya turban cap pink mai shegen kyau a kan ta.
Da sallama Abbo ya shigo palon, bata san ma ya shigo ba, dan da alama sai an mata weji, idan ba haka ba zata iya kwacewa, nama yayi daɗi baji ba gani, shi kuwa wani sanyi yaji ya ziyarci zuciyar sa, lokacin da ya ɗaura idon sa a kan ta, kasan cewar yasan Hajiya bata nan, hakan yasa ya kariso cikin palon da sauri
Kusa da ita ya zauna, a kasa kenan, har lokacin Jelly bata san da shigowar saba, hannu yasa ya ɗauki nama ɗaya zai kai bakin sa, cikin sauri ta riƙo hannun sa, ba tare da ta kalle shi ba, tana ta faman kaɗa kai alamar santi idon ta a lumshe tace "Ajiye shi" yar murmushi yayi kafin yace "Baby nine fa" "Kai waye? Nace ka ajiye shi kawai" ta faɗa, har lokacin bata buɗe ido ta kalle shi ba, "Abbon kine fa" sai lokacin ta buɗe ta kalle shi, sakin hannun nasa tayi tana faɗin "Cemin zakayi old man" zaro ido yayi yace "Daga ina yau kuma kika jiyo old man?"
Roban wani Ice cream ɗin ta ɗauko ta buɗe ta fara dumbutsan ice cream ɗin da hannu tana kaiwa bakin ta, har gemun ta duka yana shafa, cike da santi tana kaɗa kai tace "A Tv naji, wai idan mutun ya tsufa old man ake ce masa, dan haka daga yau sunan ka kenan" murmushi yayi ya sanya hannun sa yana shafo wuyar ta, yana faɗin "Idan dai kece zaki cemin old man ɗin ina so ai" a sukwane ta miƙe tsaye tana faɗin "Kwarto jama'a Kwarto" zabura shima yayi ya miƙe tsaye yana faɗin "Ina kwarton yake?!!" Da hannu ta nuna shi tana faɗin "Ga ka nan, wayyo Kwarto" tsawa ya daka mata ganin tana kokarin tara masa jama'a "Ke waye yace miki ni Kwarto ne? Tukun nan ma aina kika ji sunan Kwarto?" Turo baki tayi kafin tace "A Tv naji mana, nagani wata mata da wani mutun yazo zai taɓa ta shine tayi ihu tace kwarto ne, mai neman mata, shine jama'a suka kama shi suka masa duka, kai ma yanzu kazo zaka taɓa ni dan haka kai kwarto ne, wayyo jama'a kwarto nima kuzo ku taimake ni ku kama shi ku masa ɗan iskan duka!!" Da karfi tayi ihu, ganin da gaske take, kuma yasan halin ta, idan duniyar nan duka zai bata, bazata taɓa yin shiru ba sai lokacin da taga dama, dan haka sai ya kwasa a guje yayi cikin bedroom na shi ya banko kofa, yana mai dana sanin barin ta da suke tana kallo, yarinya sai kaifin ƙwaƙwalwan bala'i, kome ta gani a Tv ta riƙe a kwakwalwan ta, amma kuma idan aikin arziki ake koya mata bata ɗaukan komai.
Duk da ya gudu Jelly bata dai'na ihun kwarto kwarto ba, har su maman Afnan suka shigo ihu kwarto take, sai tambayar ta ina kwarton yake suke, amma Jelly taki kula su, dan Hajiya tace kada tayiwa kowa na gidan magana, shiyasa bata kula suba, ihun ta kawai take tana bubbuga kafa a kasa tana yarfe hannu.
Da dai sukaga Jelly fa kamar ta haukace sai suka kama kan su, dan daman suna zargin Jelly da taɓin hankali, to yau dai sun tabbatar, sai tsaki maman Afnan take jelly ta ɓata mata rai, yarinya ita kaɗai a ɗaki ta kama ihun kwarto kamar ba lafiya ba a cewar su.
Ita kuwa Jelly sai da tayi ihun kwarton ta mai isar ta sannan ta koma ta zauna ta ci-gaba da ɗure ɗuren abubuwan da take, idan ka ganta sai ka rantse da Allah ba itace tayi wannan ihu yanzu ba.