Triplets book 2 complete - Chapter 60
Triplets book 2 complete Chapter 60: Triplets book 2 complete Chapter 60. Bayan ya gama waya ne ya dubi Areef dake bin shi da kallo a nutse ya ce "Yanzu…
4,471 words
Bayan ya gama waya ne ya dubi Areef dake bin shi da kallo a nutse ya ce "Yanzu dai ka bar CIA har abada, kuma kasani sai na baka hukunci mai tsanani na laifin sayar da rayuwar ka da kayi, kana tunanin rayuwar taka ce kai kaɗai? Baka san cewa muma muna da hakki a kan ka bane? Iyayenka fa? Duk baka yi tunani akan wannan ba, good ka kyauta daka bani bakar wahala, ban taɓa aiki mai wahala ba irin aikinka, good 2 weeks na ɗauka ko barci bana samu bare kuma cin abinci all because of you, babban abin haushin ma sai ina bincinken ina kake sai na sake cin karo da wata ɓarna da kayi, dole na dakata nayi settle komai, kayi abubuwan dana kashe wutar bansan adadi ba, Allah dole na hukuntaka saboda gobe, ko da sunan wasa kada ka sake yi mana irin wannan gangamin, baka tunanin wani hali Aseef zai shiga? Bawan Allah da bai san komai ba sai kaunar mu, baya magana ɗaya biyu ba tare da ya kira mu a ciki ba, duk baka tuna haka ba kenan!".
Ya kai karshen maganar tare da miƙewa ya fice daga cikin ɗakin. Shiru Areef ya yi yana tunani, shi da kansa ya san ya yi babban kuskure, yasan cewa idan wani abin ya same shi to ba makawa daddy mutuwa zai yi, bayan daddy kuma Aseef, Aseef shine mutun na biyu da zuciyarsa zata iya bugawa idan ya ji wani abin ya same ni, gara Lion yana iya jurewa, amma shima sai ya ji ajikinsa ba kaɗan ba, babu wani ɗan adam da ya isa ya ce tun da rayuwarsa ne zai yi abin da ya ga dama da ita, hakan ba zai yi wu ba, saboda akwai haƙoƙin mutane da dama a tattare da wannan rai ɗin naka, na farko Ubangijin mu, Allah ya bamu wannan rayuwa ne domin mu bauta mashi ba dan mu sai data ga wani ko wata ba, bayan nan akwai iyayenka, suna da hakki akan wannan rai ɗin naka, sannan ƴan uwanka, to kada ya zama kana tunanin cewa ai ranka ne kana da damar yin abin da kake so da shi, a'a ba haka bane!!.
Yau sosai Areef ya yi nadama ba kaɗan ba, har hawaye sai da ya zubar, kuma a shirya yake da ya karɓi duk wani hukuncin da Lion zai yi mashi, domin yasan ya aika babbar kuskure mai girma, da ya mutu ta wannan hanya da bashi da amsoshin da zai bawa Aseef da daddy a ranar gobe kirayama dan dai yasan mawuyacin abune su biyun nan su rayu bayan mutuwarsa, sannan ba shi da amsar da zai bawa Ubangijin sa.
A ɓangaren su Jehan kuwa, barcine ya yi awon gaba da su dukkansu tun lokacin bayan da suka gama rikici da wannan Alhajin.
Barcin awa biyu suka yi Jehan ta farka, nan ta sami Aisha idabunta biyu itama ta farka tana zaune ta buga uban tagumi.
"Aisha me yake faru na ganki kin yi shiru haka?" Ta tambaya tana kare mata kallo.
Nisawa Aisha ta yi kafin ta matso ta ruƙe hannayen Jehan ɗin cike da damuwa tab a ranta ta ce "Jehan zan gaya maki ainahin abubuwan da suke faruwa a cikin gidan nan wadda ba kowa ya san da hakan ba, da farko abin da yasa ban gaya maki ba dan ina tunanin kema kamar mu ce, kema hakura zaki yi ki bada jikinki domin bamu da wata mafuta, wannan gidan da kike gani ba gidan arziki bane, wlh Allah wannan gidan bala'i ne Jehan, na san idan suka san cewa nasan wannan sirrin za su iya kashe ni ko dai su jefar da ni, kai da wuya ma su jefar da ni nasan kashe ni za su yi, Jehan sanadiyar cetar Maryam da kika yi tasa na samu karfin gwiwa na cewa sanadiyyar ki zamu iya barin gidan nan har mu kai kara ga hukuna cewa ga abin da ake yi a cikin gidan nan..."
Dakatar da ita jehan ta yi da cewa "Kin san hanyar fita daga gidan nan ne?" Girgiza kai ta yi tana faɗin "Kamar yadda aka kawo ki da tsakar dare, haka ake kawo kowa da tsakar dare, sannan babu wani alhajin da ya isa ya fita da ke da rana sai da daddare, bugu da kari magana ta gaskiya babu wanda idan ya shigo gidan nan yake sha'awar fitarta, shiyasa hajiya bata damuwa take bari a fita da ƴan matan, dan tasa ta asirce su ba zancen fita, amma na sha mamaki tun da na ga kin ceci Maryam nasan dole akwai nasara a tattare da ke, wlh asiri suke yi wa mutun ya zauna a cikin gidan nan, ina da tabbacin hakan ne, ka zauna kayi ta bada jikinka, lokacin dana fara yin hakan, da aka kawoni ina sabuwa, duk time dana kwanta da wani, zan kwanta ne cike da annashuwa da farinciki, idan mun gama abin da zamu yi kuma nadama tare da dana sani ne zai biyo bayan abin a tattare da ni".
Shiru Jehan ta zuba mata idanu tana jiran ta ji me yake faruwa. "Jehan kamar yadda kika sani ne ana fita da yarinya, Alhazawan nan suna zuwa da ita su kwana da ita a hotel da sauransu, amma fa ki sani ba kowani Alhaji bane yake zuwa ya kwanta da yarinya dan biyar bukatar kansa, a'a akwai masu zuwa su kwanta da yariya dan bokansu matsafansu sun basu wani abin su zaubawa mace a cikin cikinta dan samun kuɗi ko nasara ko dai wani biyan buƙatunsu, kuma duk wannan hajiya ta sani, domin kafin ya fita da yarinya sai ya bawa hajiya makudan kuɗaɗe ya gaya mata ga irin aikin da zai yi da yarinyar, da yake ba ƴaƴan ta bane, sai ki ga ta yarda ta karɓi kuɗin ta bada yariyar, ki sani fa wannan abin da suke zubawa mace a cikin cikinta wlh idan ya yi wuta in suka dawo da yarinya ta kara kwana biyu sai gawa, akwai kawata da muke wannan ɗakin kafin ku zo sunanta Zuwaira, yarinyar nan so silent, bata da hayaniya, to ranar da wani aljaji ya tafi da ita da daddare, bai dawo da ita ba sai washegari da daddare, lokacin da ta dawo nan wlh sai kin matsa mata kwallah, a nan ne take bani labarin abin da yake faruwa, domin ta ji duk yadda Hajiya ta yi da wannan alhajin, ta ji yadda suka yi da hajiyar daɗi, kuma ita ma ta gani da idanunta, lokacin da ya gama amfani da ita, ta ga wani bakin abu a cikin gabanta kamar garin lepton, abin ya so ya yi kama da kasa haka, tun daga lokacin ta fara jin ciwon ciki, shi kuma alhajin ya ɗauki kuɗi makudai ya bata sannan ya ce ta je ta yi wanka, haka ta je ta yi wanka ta wanke gabanta ta zo ta kwanta, da yamma ya sake dawowa ya yi amfani da ita ya sake zuba mata wannan abin, ga shi na safe da ya zuba mata ma sai ciwo cikinta yake yi mata, haka ba imani ya sake mafani da ita ya zuba mata, wlh yarinyar nan in takaice maki bata yi kwana biyu da dawowa ba ta rasu, hajiyar daɗi ta sa aka fita da gawarta ban san ina suka kai ba, cos a yanzu ba kowa yake yin zinar ba ma tsakani da Allah, wasu musamman ma manyan mutanen nan, wlh wani abin suke sanyawa mutun a jiki dan samun wani abu da suke nema, wani kuma su lalata mashi hanji ya ruɓe ya mutu, wani abin kuma idan suka saka maka ka haukace daga nan a rasa gane kanka, to yanzu dai ya kamata masu yin zinarma su kula dan yanzu ba zina kamar na da ake yi ba, kinga a ɗakin bayan mun nan, yarinya ƴar shekara goma sha huɗu wani alhaji ya ɗauke ta, yarinyar nan ya tafi da ita, wlh jehan virgin ce yarinyar nan, bata san komai ba, ga ƙananun shekaru, dan rashin imani ya je ya yi amfani da ita ta gaba da kuma ta baya, kuma ya zuba mata wani abin ta bayanta, wlh karki so kiga yadda yarinyar nan ta kare a cikin gidan nan, Allah sai kin yi mata kuka, kuma ita kam ma marainiya ce, iyayenta sun rasu ta gudun wa wahalar matar uban tane, ranar da yarinyar nan ta rasu na yi mata kuka ba kaɗan ba, so akwai abubuwa sosai da suke faruwa a cikin gidan nan, ciki kuma har da sayar da ƙodar mutane, sannan akwai kwashewa ƴara kayan cikinsu, abubuwa dai wayan da ba za su kirguba JEHAN laifukan da ake yi acikin gidan nan ba za su faɗu ba, a kama yaro aje a sayar da ƙodarsa makudan kuɗaɗe, idan ya fara rashin lafiya ko yarinya ta tashi a aiki sai aje wani garin a jefar da ita, kuma mafi yawancin lokaci idan sun cirewa yaro ƙodarsa ne suke zuwa wani garin su jefar da shi, sai ki ji ana cewa an tsinci yaro ɗan gari kaza a gari kaza, amma an tsinceshi lafiyarsa kalau ana neman iyayensa, ba wata lafiyarsa kalau, ba ta yadda za'ayi su saci yaro kuma su kai shi wani gari su jefar da shi ace ba wani abin da suka yi mashi, dole akwai dai wani abin, kamata ya yi idan yaron ku ya ɓata kuka gane shi, first abin da zaku fara yi akai shi asibiti ku biya ko nawa ne a chaje maku shi fes, ku tabbatar babu wani abin da ya rasa daga wani sassa na jikinsa, sannan kuce lafiyarsa kalau, domin akwai wani abin da idan aka cire a jikin mutun ba lallai ne ya yi ciwo a bayyane ba, kuma ma ya kan iya ɗaukar tsawon lokaci bai yi ciwo ba."
WATA SHARI'AR SAI A LAHIRA, ALLAH ALHADULILLAH DA YA KASANCE AKWAI LAHIRA, RANAR DA ZA'A KWATAWA MARA KARFI HAKKINSA A WAJEN MAI KARFI, RANAR DA DUK WANI AZZALUMI ZAI ƊANƊANI KUƊARSA, ALLAH KA MANA SAKAYYA DAIDAI DA ABIN DA AKE YI MANA, WANI ABIN IDAN KANA JINSHI WLH SAI KA RANTSE DA ALLAH BA A DUNIYA KAKE BA, DUK WANDA YA GA YANA ZAUNE LAFIYA ACIKIN GIDANSA, YANA CI KO MA YAYA NE YANA SHA KO BA YAWA, TO YA GODEWA ALLAH KUMA YA ZAUNA A IN DA YAKE, WANNAN BALA'IN TA DUNIYARMU TA YAU SAI DAI ALLAH YA KAWO MANA SAUKI. TO IYAYE NA JUYO TA KANKU KALUBALE GARE KU WAƳAN DA ƳAƳAN SU SUKE ƁATA DA KUN GANE SU SHIKENAN AN WUCE WAJEN, AZO YARO KWANA ƊAYA KWANA BIYU YA ZAMA BABU SHI YA MUTU, TO DAN HAKA SAI KU KULA, A KULA DA YARA MASU ZUWA MAKARANTA, DAGA MATA HAR MAZA, YANZU SAYAR DA ƘODAR MUTANE HAR A ASIBITOCI ANA YI SOSAI, SAI A YI MAKI KARYAR ZA'AYI MAKI AIKI WATA MATSALA NA DAMUNKI, DAGA NAN SU SACE MAKI ƘODA, TO DAN HAKA SAI KU KULA, DA ZARAR AN YI MAKI AIKI A WANI ASIBITIN KIKA SAMI LAFIYA, TO KI GARZAYA MAZA IZUWA WATA ASIBITIN DAN A YI MAKI SCANNING NA KAYAN CIKIN KI, KI TABBATAR KOMAI YANA NAN KAFIN KI SAMU KWANCIYAR HANKALI, ALLAH YA MANA MAI KYUA!!!.
STORY💖
Yau dai Jehan ta ji abin da ya kwance mata lissafin ƙwaƙwalwar ta, tunani ta fara yi tabbas akwai wata kawarta Zuhra da ta taɓa gaya mata cewa an sacewa yayan mamanta ƙodarsa a asibiti yanzu haka sun kai kara kotu da suka gane kenan, ashe abin da gaske ne sosai har haka, wato Hajiyar daɗi har da dillancin ƙodar ƴaƴan mutane suke yi kenan? Wannan wace iriyar bala'i ce, wato su kuma Alhazawan nan sai su zubawa ƴar mutane kayan tsafi a cikin cikinta saboda son abin duniya, siyasa ko dai kuɗi ko wani buƙata, innalillahi wa inna ilaihir rajiun wato dai kowa kuɗi kowa kuɗi, ko ta halin ƙaƙa sai anyi kuɗi, wannan bala'i da yawa take, yanzu bayan laifin zinar ma har da na shirka suke haɗawa waje guda, ga laifin cutar da yayan mutane a zuba masu wani kayan tsafin a ciki, ya ilahi ya lillihi wannan duniya ina zaki je damu, TO MATA MASU ZINA SAI DAI MUCE A KULA, IDAN BA HAKA BA ZAKI MUTU BA TARE DA KIN SAN DALILI BA, KU TUBA KU DAINA DOMIN SAMUN RAHMA WAJEN UBANGIJIN KU, KUMA KU TSIRA DAGA SHARRIN IRE-IREN WAYAN NAN ABUBUWA, WANNAN MA KAƊAN KUKA JI, AKWAI ABUBUWA DA DAMA DA AKE YI TA HANYAR ZINA WADDA ZAI ZAMA SANADIYAR RAYUWARKI CIKIN ƘANƘANIN LOKACI, TO DAN HAKA AKULA A TUBA KO DAN A TSIRA DA RAI.
Ko motsin kirki Jehan ta kasa, tunaninta kawai ta ya ya za'ayi ta ruguza gidan Hajiyar daɗi, tabbas ko mutuwa za ta yi sai dai ta mutu amma ba zata bar wannan gida ba sai ta rusa shi, ya zama mata dole ta azabtar da rayuwar Hajiyar daɗi, ta jata akan titi, ta yi rayuwar walaƙanci, bai kamata wannan tsinanniyar mata ta yi mutuwar farad ɗaya ba, dole ta azabtu matuka, to ta wani hanya ya kamata mu fara? JEHAN ta tambayi kanta a cikin zuciyarta, yayin da ita kuma Aisha ta zuba mata idanu tana jiran ta ji me zata ce.
Sun jima a haka kafin su Adiva su farka daga barcin da suke yi, ganin su jugum-jugum yasa Adiva ta tambayi menene yake faruwa? Jehan bata ɓoye mata ba ta gaya mata dan ta samu haɗin kansu su san yadda zasu rushe wannan gida na azzalumai.
A haka Zinariya ta shigo ta same su, umarni ta bawa Adiva akan ta shirya da daddaren nan zata yi baƙo, rai a matuƙar ɓace Jehan ta ce "Babu in da Adiva zata je".
Kallon sama da ƙasa Zinariya ta yi mata kafin ta ce "To sai ki hana mu gani" ta kai karshen maganar tare da juyawa zata fice daga ɗakin.
Dakatar da ita Jehan ta yi da cewa "Ke tsohuwar kilaki, ina mai tabbatar maki da hakan, kuma zaki gani, ba ma Adiva ba, duk cikin mu huɗu dake a cikin ɗakin nan babu wanda zai sake zuwa wajen wani tsinanne kafurin banza, idan kuma kuka matsa sai kun alaƙanta mu da hakan, to wlh ina mai maki rantsuwa da sunan Allah sai na zama sanadiyar rayuwar duk wata marakunya da ta shigo gaya mana akwai baƙo, bayan haka kuma mu haɗa da baƙo duk sai munci ubanku, ƴan iska tsinannu, wlh ina da tabbacin babu abunda kuka isa ku yi mana, domin babu in da karya ta taɓa ɗauruwa akan gaskiya, tun daga farko Al Qur'ani mai girma har karshe ta, maganar Allah ne a cikinta, kuma babu a in da Allah ya yi alkawarin taimakawa azzalumai, sai dai ma ya ruguje daular zalunci, wlh idan baki tuba kin koma ga Allah ba sai kin yi mutuwar walaƙanci, mutuwar kare ma sai ta fi taki daraja, shegu kafuran banza tsinannu, duk abun da kuka ga dama ku zo ku yi Mani, kuma ina son ki buɗe kunnanki da kyau ki saurare ni dukana da kuka yi wlh baku yi shi abanza ba, ki jira kiga karshen iskanci, ku karyar iskanci kuke yi, da JEHAN kike magana, ƴar fari a wajen jaru kuma jajirtatcen jan wuyar namiji, ubana ɗayane tamkar da dubu, baya da tsoro gaskiya kawai ya sa a gaba ya kuma riƙeta, to akan haka ya renemu, ki rubuta ki ajiye wlh nice zan zama sanadiyar rugujewar wannan gidan".
Duk wannan magana da take yi cikin harshen turanci ta yi shi, hakan yasa Zinariya bata wani fahimci kan zancen ba, dan bata yi wani karatu ba, amma dai ta gane zaginta Jehan take yi, dan haka sai ta dawo cikin ɗakin rai a makutar ɓace ta ɗaga hannu zata mare ta.
Yau iya ɓacin rai ran Jehan ya ɓaci, jikinta har ɓari yake yi saboda baƙinci, zuciyarta sai tafasa yake mata, idanunta sun rufe bata ji bata gani, yau zuciyarta ta bushe babu alamar tsoro ko kaɗan a cikinta, dan duk zuciya mai imani idan ta ji abin da ake aikatawa a gidan Hajiyar daɗi sai ta girgiza, a fusace ta ruƙe hannun Zinariya tare da zabga mata wani mahaukacin mari mai doɗe kunne na wucin gadi, wani irin dum Zinariya ta ji, kunnuwanta sun daina jiyo mata sautin komai saboda marin da ta sha wajen D.P.O.
Wani irin daɗi su Adiva suka ji, dama ita Adiva tasan halin jenan sarai akwaita da ɗaukar zafi kuma bata ɗaukar raini ko kaɗa, idan ka kawo mata wargi yanzun nan zata sa kayi nadama, akwaita da jan ajinta bata shiga abinda bai shafeta ba, ko wanda ya shafetan ma idan ba mai girma sosai ba bata kula shi, mace ce ita mai class sosai.
Good 3mins Zinariya ta ɗauka tsaye a wajen dafe da kuncinta tana hawaye, kwata-kwata bata iya jin sautin komai kunnenta ya doɗe, Jehan kuwa tana tsaye tana huci kamar wata zakanya, yau sun kureta, bata san laifin da suke aikatawa ya kai har haka ba.
Bayan minti biyar ne Zinariya ta dawo daidai, sai ta yi yunkurin damkar wuyar jehan ta daketa, ai kuwa Jehan bata bata wannan damarba zullewa ta yi tare da kwashe kafafunta sai ga Zinariya a kasa ta zube.
Cikin fushi ta miƙe ta nufi waje tana faɗin "Ki jirani ina zuwa". Guntun tsaki Jehan ta ja kafin ta ce "Sai kin zo ɗin, ina jiranki, fita ɗakin nan ne babu wace zata sake fita dan wani ɗan iska banza ya zo ganinta, wlh idan kuka yi wasa duk sai mun dafa ruwan zafi mu saluɓe fatar jikin duk ɗan iskan da ya zo gidan nan yayi gigin tunkarar mu da sunan ya zo biyan buƙatarsa, ba dai muna da cattle na dafa ruwan zafi a nan ba, to ku jira ku ga sabon ta'addancin ƴan mata, ƴan iskan kawai, ai karyar iskanci kuke yi, wlh duk ƴan gidan nan sai na hure masu kunne na yi masu wa'azi su farka mu haɗa karfi da karfe muci uban ku dan ubanku. Tana magana tana huci, haka ta koma bakin gado ta zauna tana jiran Zinariyar ta dawo, yau ashirye take ta ci uban duk wanda ya kawo mata wargi.
(TO FAH BABBAR MAGANA JEHAN DAI TA ƊEBO DA ZAFI, TAYI ABU CIKIN FUSHI, NI DAI NA HAƊA KAYANA ZUWA GIDAN ABBI DAN JIN YA AKE CIKI, WATA KILA KAFIN MU DAWO ZINARIYA TA DAWO MUGA SHOW TSAKANINTA DA D.P.O. TA MAMAN YASMIN.)
💖GIDAN ABBI💖
A ɓangaren Akila, duk ta gama ruɗar da Irfan, bawan Allah ya kasa hakuri miƙewa ya yi ya zura jallabiya a jikinsa sannan ya nufo kofar fita.
Yana fita bai tsaya ko'ina ba sai cikin gida, waya na makale a kunnensa yana karɓar sakon kalamai nata tare da shagwaɓa kala kala, a palo ya isko Abbi, Aunty, Imran, da kuma Rimsha da take cin abinci Imran ya tasa ta a gaba.
Bai wani bi ta kansu ba ya wuce ya haura sama, da kallo Abbi ya bishi kawai, bai wani damu ba kuma bai tambaye shi ina zai je ba.
Bai yi sallama ba kawai ya faɗa ɗakin, Aafia da Hanan suna zaune a ta bakin gado suna hira, ita kuma Akilar ta bawa kofar shigowa baya tana rungume da pillow a kirjinta, ga waya na makale a kunnenta yayin da hannunta ɗaya ke a jikin headboard na gadon tana wasa da yatsunta, sai hira take zuba mashi.
Da hannu ya nunawa su Aafia hanyar fita daga cikin ɗakin ba tare da ya yi magana ba, ba musu suka fice da sauri.
A hankali ya tako zuwa bakin gadon, cikin dabara ya haye saman bed ɗin tare da matsowa kusa da ita, bata taɓa zaton zai zo ba, sai zuba mashi shagwaɓa take yi, jin ya yi shiru baya magana ya sa ta kara shagwaɓe murya ta ce "Yaya Irfan shine ka barni ina ta magana ka yi shiru ko? To wlh na yi fushi kuma ba zan ci abincin dare ba, ba zan sake kula ka ba". Tana magana tana turɓune fuska irin na shagwaɓa
Zuba mata ido kawai ya yi yana kare mata kallo ya kasa magana, ba abin da yake kallo sai kyakkyawar sajenta dake kwance a gefen lallausan kumatunta, yana ɗan kawar da idanunsa karaf sai kan breast nata da yake tana kwance wuyar rigar tata ta ɗan yi kasa, hakan kuma ya yi daidai da juyowanta dan ta duba wayar ta gani ko ya katse kiran ne tun da ta ji shiru.
Karaf suka yi ido huɗu, ba ƙaramin tsorata ta yi ba, a zafafe ta wage baki zata yi mashi ihu dan a tunaninta aljanine, cikin sauri ya sanya hannunsa ya rufe mata baki yana girgiza mata kai.
Dafe kirjinta ta yi tare da fara ruwan hawaye dan har ga Allah ta tsorata sosai, a hankali ya zame hannun nasa daga bakin nata, kasa kasa ya ce "Sorry, am so so sorry".
Kuka ta sa mashi tana bubbuga kafa a saman gadon, hannu ya kai ya fara goge mata hawaye yana faɗin "Tuba nake yi my heartbeat, ba zan kara ba".
Turo baki ta yi tare da zuro kafarunta kasa zata sauƙa daga gadon, da sauri ya riƙota yana faɗin "Ina kuma zaki je? Ba nace na tuba ba?".
Kara shagwaɓe murya ta yi ta ce "Ni ka sake ni mun ɓata da kai ai, tun da zaka zo ka tsorata ba abin da na yi maka".
"Haba matar Mijinta, yanzu fa kika gama ce mani ke jarumace ko dai kin mance ne?".
Wani irin kallon soyayya ta yi mashi wadda ya sanya shi sauƙe nauyayyar ajiyar zuciya, juya fararen idanunta tayi tare da turo baki kamar biro ta kara narke murya ta ce "Yaya Irfan Allah ba zan kyaleka ba, sai na rama".
"Kai heartbeat ki rufa mani asiri, yanzu ma baki ce zaki rama ba ma ya na kare dake bare kuma kin ce zaki rama, ai sai ki haukatar da mijin naki".
Saboda iya shege irin nata sai ta sanya hannu ta rufe fuskarta ta na faɗin "Yaya Irfan ni kunya nake ji idan kana zancen mijin nan, ni ka daina bana so, idan ba haka ba Allah kuka zan yi maka".
Akila ta gama tafiya da imaninsa, bawan Allah bai taɓa yin soyayya ba sai akan ta, ya so Ayla sosai amma ba su yi soyayya ba, abun da bai saba ba sai ya ke jin sa a wata duniya ta musamman, ga shi kuma ya yi sa'a ya haɗu da kwararriya a fagen soyayya, ta kware sosai, idan tana magana ma har wani lanƙwasa magana take yi kamar dai Hajiya Batula da mijinta, kamar yadda take gaya maku Hajiya Batula take yi, ita ma yanzu haka take yi wa Irfan, ko kiran sunan sa zata yi sai ta wani lanƙwasa sunan ta sanya mashi salo na musamman, hakan ba ƙaramin kara rikita shi yake yi ba, shiyasa ya fito ya zo domin yaga yadda take maganar nan da idanunsa dan ya tabbatar da cewa ita ɗin ce ba wata ba.
Sai dai fa, akwaita da bala'in kunya sosai da sosai, amma fa kunyar ba asalin kunya da kuka sani bane, wannan shi ake kira da kunyar rashin kunya, domin da gangan take cewa tana jin kunyar domin ta kara haukata masoyin nata, da gangan take rufe ido ta rinƙa ce mashi bata so tana jin kunya dan ya kara narke mata, mafiya yawancin maza suna son hakan, kaso 80 cikin ɗarinsu suna son irin hakan, sai macen da ta iya fahimtar sune zata gane hakan, ita Akila da yake ta yi degree a fagen soyayya duk ta gama sanin lagon maza, hakan yasa take yi wa Irfan wannan tsiya wai tana jin kunya.
"Heartbeat kina kara mani soyayyarki sosai a cikin zuciyata".
"Yaya Irfan na ce maka Allah kunyar maganar nan nake ji fa, wai ba zaka daina yi mani ba?" Ta faɗa tana kara rufe fuskarta da hannunta sosai.
Riƙo hannayen nata ya yi ya buɗe fustar tata yana faɗin "To waye ne yanzu ya gama ce mani zai bani abincin dare a baki?".
Ƙoƙarin tashi ta yi dan ta gudu, wai kunya take ji, riƙota sosai ya yi ya dawo da ita ya zaunar yana faɗin "Eyeee wato a awaya ba'a jin kunya har da cewa za'a bani abinci a baki, shine yanzu kuma gani ido da ido a maimaƙon a zubamani kalamai masu daɗi da suka fi na waya shine zaki gudu ko?".
Kawar da kallonta gefe ta yi ba tare da ta yi magana ba,
"Au ba zaki yi wa mijin naki magana bane?".
Shiru ta yi mashi taki yin magana, hancinta ya ɗan ja tare da sakin hannayen nata ya diro kasa daga saman gadon ya koma saman bedside drawer ya zauna yana faɗin "To juyo mu yi magana kin ji gimbiyata? Heartbeat namu gaba ɗaya".
Ba musu ta juyo suna fuskantar juna sai dai taki yarda ta haɗa idanu da shi, kasa take kallo abinta.
Hira ya fara janta da shi dan ta saki jiki su zuba soyayya son ransu.
A ɓangaren Akil kuwa sosai suke murjan juna shida Umaisha a cikin mota, duk ta kiɗima shi ya fita a hayyacinsa, bashi da wata buƙata da ya wuce ya ji shi a cikin jikinta, Akil irin jarababbun mazan nan ne na ƙin karawa.
Shi ma daddyn Jelly romancing nata ya yi sosai amma bai kai ga shigarta ba, saboda ya yi wa kansa alkawarin sai ta kara girma, sosai ta rinƙa yi mashi kuka akan breast nata suna yi mata ciwo, duk bakinsu ya yi ja sun sha murza.
Rarrashinta ya fara yi yana bata hakuri akan ba zai kara ba, rungume shi ta yi tana faɗin "Daddyna ina son duk wani abin da kake so, amma wannan yana yi mani zafi ne sosai".
Runtse idanunsa ya yi dan baya son su haɗa ido, kasa kasa da kyar ya ce "Baby anya zaki iya ɗaukar ciki kuwa? Gaskiya kin cika ragwanta sosai" ya kai karshen maganar tare da sauƙa daga kanta ya koma gefe ya kwanta yana kara jawota jikinsa.
"Daddy dama ina son in tambaye ka". Jinjina mata kai ya yi alamar yana jinta domin ba zai iya cigaba da yin magana ba.
"Daddy na na ji ance idan mutun ya yi aure ne yake samun ciki ya haihu, tom nikuma naga har yanzu ban sami cikin ba kuma ban haihu ba, ina son kuma na haifi baby Nima".
A hankali ya waro wayan nan dara daran idanun nasa wadda suka sauya launi akan face nata, da kyar ya iya fara magana "Baby kina son Haihuwa ne?" Gyaɗa mashi kai ta yi alamar e.
Jinjina mata kai ya yi kafin ya ce "Zaki haihu In Sha Allah amma sai kin kara girma, yanzu ba zaki iya ɗauka na bama bare kuma baby". Shiru ta yi tana nazarin kalamansa,