Kenza eBookz

Triplets book 2 complete - Chapter 76

Triplets book 2 complete - Chapter 76

Triplets book 2 complete Chapter 76: Triplets book 2 complete Chapter 76. Imran ne ya amsa mashi da shi ya hanata zuwa dan za su je shopping da sauran su,…

4,458 words

Imran ne ya amsa mashi da shi ya hanata zuwa dan za su je shopping da sauran su, sosai Areef ya ɓata rai in da ya yi wa Imran ɗin faɗa sosai akan kada ya kuskura ya sake wannan gangancin dan za su fita ya hanata zuwa school, ba za su hakura da fitar sai ta dawo ba, ita ma faɗa ya yi mata sosai akan kada ya sake jin ta yi hakan.

To ta amsa da shi sannan suka yi sallama, da kyar Areef ɗin ya miƙe dan ya rakasu, Imran yana ce mashi ya bari ya bari shi kuma ya ce a'a gara ya rinƙa takawa a hankali hankali zai fi mashi.

Haka dai ya rakasu har harabar gidan sannan ya dawo ya zauna a palon kasa dan ya ɗan huta, har cikin zuciyarsa ya rasa dalilin da ya sanya yake kaunar Rimsha, har mamaki abin yake ba shi, ta shiga zuciyarsa farat ɗaya, amma dai ba wa kansa yake yi wa kaunar tata ba, ɗan uwansa yake yi wa, dan shima Lion ɗin ya samu farinciki a rayuwarsa, su kuma kullun Lion ɗin yana cikin sanya su farinciki, shi ne dai bashi da mai sanya shi sai dai su ɗin, to yana da kyau ya samu gaskiya, duk da abune mai matukar wuya, amma Areef yana sa ran tabbas da izinin Allah za su yi nasara, tun da har Aseef ma ya sa baki za su yi nasara, yanzu dai fatan ya samu lafiya kawai yake yi.

Imran kuwa gidan Abbi ya wuce ya ɗauki Jelly, Hanan da kuma Akila suka wuce.

Wajen gyaran jiki suka fara zuwa aka yi masu su dulka da sauransu. Yaran nan sun dawo kamar wasu taurari, daga nan sai kunshi da aka zana masu mai shegen kyau, Rimsha kamar wata tauraruwa haka ta zama, ga wannan curly hair nata ya sha gyara sai santin shi su Akila suke yi, da haka suka wuce shopping in da ya saya masu atamfofi da laces dan baya son irin shigar da Rimsha take yi a gidan nan nasu, saboda ya lura sojojin nan sun fara saka mata ido, ga shi kuma wani lokaci suna fita su barta a gidan ita kaɗai, kada wata rana su fita sojojin su cutar da ita, kuma idan suka cutar da ita ko da Lion ya hukunta su ko kashe su ma ya yi sun riga da dai sun cuceta dai, abin da ya wuce ba zai dawo ba, to maganin bari kada a fara, kuma ya duba gaba ɗaya kayanta dukka kanana ne, abayas ɗin ma basu da yawa sosai, wannan dalili yasa ya saya masu atamfofi da laces dan ayi mata ɗinkin hausawa ta rinƙa dressing mai kyau tana rufe jikinta dan gudun matsala.

Daga wajen shopping ɗin suka wuce wajen ɗinki dan su bada kayan ɗinki. Da suka je Imran yaki yarda taila ya gwada su, shi da kansa ya karɓa ya gwadasu sannan ya gayawa tailan size nasu ya rubuta, sosai Rimsha ta ji daɗi da Imran ya yi hakan, domin dama a cikin zuciyarta ba yarda zata yi tailor ya taɓa ta ba.

Tailor ya faɗi kuɗinsa Imran ya yi mashi transfer sannan suka wuce suka nufi gida.

Sai misalin karfe 4 na yamma Imran suka dawo gidan Lion bayan ya mayar da su jelly da niki nikin kayan da suka saya gidan Abbi, ansha yawo ansha shopping da gyara, sun yi kyau fiye da tunanin mai tunani bare ma Rimsha kam ba'a magana, duk wanda ya kalleta sai ya sake waigawa ya kalleta.

Suna shiga cikin palo kamar yadda suka saba ɗakin Areef suka fara shiga, baya nan, da mamaki suka fita suka haura sama.

A Palon sama suka isko shi yana zaune saman sofa yana shan coffee. Kusa da shi Imran ya je ya zauna ita kuma Rimsha ta nufi bedroom nata dan ta ajiye niki nikin kayan hannunta bayan ta gaishe shi kenan.

"Wannan murna da faricnikin fa na menene?" Cewar Imran, yana tambayar Areef ɗin. Fuska ɗauke da murmushi Areef ya ce "Daga yanzu zuwa ko yaushe zaka iya ganin uncle Musharraf da nake gaya maka, baka ga babu motar Lion a waje bane? Ai ɗauko mani shi Mark ya je yi a airport".

Murmushi shima Imran ɗin ya yi zai yi magana kenan suka ji sallama a bakin kofar palon, a tare suka kai kallonsu wajen, Musharraf ne da Mark dake a bayansa ya yi mashi jagora ne zuwa cikin gida, sun je ɗakin Areef ɗin baya nan shi ne suka bi yo shi nan sama.

Sai murmushi Areef yake yi tare da yi masu iso, shi kuma Imran a razane ya miƙe tsaye yana faɗin "Yallaɓoi dama kai ne uncle Musharraf ɗin?". Sai lokacin Musharraf ya lura da Imran dake wajen, jinjina mashi kai ya yi alamar e shi ne.

Cike da murna ne ko tashin hankali ne Imran ya kasa gane wa, da karfi ya kwalawa Rimsha kira yana faɗin "Rimsha ki zo ga daddynki" ya yi maganar da turanci da yake yanzu ba su cika yin magana da hausa ba saboda su Areef ɗin da basaji, yaren, so sai turancin kawai ya bi bakinsu suma.

Wani irin miƙewa Areef ya yi yana mamaki daddyn Rimsha kuma? Allah sarki shine dalilin da ya sanya Areef yake kaunarta kenan.

Ita kuma jin abin da Imran ya ce ne yasa ta fito da gudu yayin da shima Musharraf ɗin ba shi da burin da ya wuce ya ganta ɗin, domin a nasa tunanin dukka family'n sa sun mutu basu raye, shiyasa time da ya dawo Nigeria ya ga gidansa a rufe da kwaɗo sai kawai ya zaɓi da ya bar kasar baki ɗaya tun da ba wanda ya rage mashi a cikin su mummy, kuma dama a tunaninsa yasan da wuya ƴan adawa su kyale mashi family'n sa tun da shima sun yi yunkurin kashe shi Allah ya tseratar da shi, wannan dalili yasa ya bar kasar gabaɗaya da nufin kuma ya barta kenan ba zai kara dawowa ba.

Ganin tabbas da gaske daddyn tane yasa ta kwansa a guje ta faɗa jikinsa tare da sakin kuka mai tsuma zuciyar mai sauraro, shi dai Areef ya kasa magana, sai ma murmushi da yake yi domin yanzu ya kara samun karfin gwiwa wajen taimakawa Rimsha akan abin sonta, tun da ta kasance ƴar cikin Musharraf to halin kirkinta ma ya wuci hakan domin duk abin da Musharraf ya rinƙa yi wa Aseef suna sane da shi, shi kuma Areef Allah ne kawai ya jarrabe shi da kaunar Musharraf ɗin ba ma wai dai abubuwan da ya yi masu ba.

Rimsha an sha kuka kamar ba gobe, shima Musharraf sai da ya yi kwalla, Areef da Imran ne suka rinƙa rarrashinsu, da kyar suka yi shiru, duk fa wannan abin da suke yi Lion yana bedroom nasa yana jinsu, sai aikin latsa waya yake yi kamar babu shi a gidan.

Bayan sun yi shiru komai ya lafa ne daddy yake tambayarta ina su mummy, nan take gaya mashi ita ma bata sani ba, ita kaɗai ta rage, daga nan ne sama sama ta shiga bashi labarin abubuwan da suka faru har izuwa yau, ya sha kuka kamar ƙaramin yaro. Akan siyasa aka tarwatsa mashi farincikinsa, wannan bala'i dame ta yi kama, kowa duniya kawai ya sa a gaba.

Shi dai Mark yana tsaye ne kawai yana binsu da ido dan ba jin me suke faɗe yake yi ba, shi dai kawai ya ga ana magana ana kuka, shima dai Areef kukan kawai yake ganin ake yi, bayan haka baya gane komai tun da ba yaren yake ji ba, amma dai ya fahimci labari Rimsha take bayarwa, sai daga baya bayan komai ya lafane an sha kuka an koshi sannan Imran yake mayarwa da Areef abubuwan da suka faru, sosai Areef ya jinjina kai tare kuma da yi wa kansa alkawarin idan ya samu lafiya dole ya bankaɗo gaskiya, dole ya yi bincike akan suwa ye suka yi wa Uncle nasa hakan, a cikin rayuwar Areef idan ka cire TRIPLETS nasa to Musharraf shine mutun na biyu da yake kauna, haka Allah ya jarabce shi, hakan kuma yasa ya yi alkawarin biwa uncle ɗin nasa hakkinsa, ba zai bar Nigeria ba sai ya yi wannan aiki koda kuwa ita zata zama aikinsa ta karshe a duniya ko a hukumance.

Shiru suka ɗan yi na ɗan lokacin, sai shesshekar kuka Rimsha take yi ta lafe a jikin daddynta, zama daddy ya yi ta zauna a saman cinyarsa tare da kwantar da kanta a kirjinsa idanunta sun yi jawur saboda kuka, suma su Imran komawa kowa ya yi ya zauna, Areef dai abin ya yi mashi daɗi sosai da Rimsha ya kasance ƴar Musharraf.

Katse masu shirun daddy wato Musharraf ya yi da tambayar a ina Rimsha take zama yanzu, wannan karon da turanci suke maganar. Nan Imran ya ba shi labari yadda ake ciki, ai kuwa daddy ya ji babu daɗi, cike da jin haushi kuma cikin yaren turanci dan ma Areef ya ji ba sai an fassara mashi ba, ya fara magana "Ba zai yi wu Rimsha ta zauna cikin zaratan maza haka ba, ba zan yarda da hakan ba, dan haka ta kwashe kayanta mu je na mai data gidana na nan Kd, ban yarda ta zauna a nan ba, maza tashi ki kwaso kayan ki mu tafi". Ya kai karshen maganar tasa cikin izza da nuna isa akan ya isa da ita.

Ita kuwa cikin zumuɗin ganin daddynta yasa ta miƙe ta shige ciki dan ta haɗo kayanta, sai faɗa daddy yake yi akan me Imran bai kai ta gidansu ba ko kuma gidan Abbi da zai kawo ta nan cikin maza, ga Areef bashi da lafiya kuma yasan halin turawan nan sarai wasu basu da hankali idan sojojin nan suka yi mata wani abin fa, idan baku manta ba Musharraf suna da kwantaciya a kasa tsakaninsa da Lion na marinsa da Lion ya taɓa yi, hakan yasa Musharraf ɗin baya son Rimshan ta zauna a nan dan sanin bakin halin irin na Lion.

Shi dai Areef sai ƙoƙarin dannan daddyn yake yi domin Lion na gida, shi kuma Lion idan yana waje ba wanda ya isa ya nuna yana da izza ko kuma ya nuna yana da iko da wani matukar yana waje, idan yana wajen to shine sarki, shi ne zai yi iko da kowa, idan ka yi gigin kin hakan to fa ka shirya kukan da mutuwa ta fi maka sauki, hmmm kuma ga shi a cikin gidan Lion ɗin daddy ke nuna izza yana magana son ransa har da nuna isa, ai da wuya daddy ya wanye lafiya da Lion ɗin.

Ai kuwa Rimsha tana fito da trolley ta akan su tafi Lion ya fito daga cikin ɗakin daidai lokacin kuma da daddy ya miƙe akan su tafi.

Tsare Musharraf ɗin da waƴan nan idanun nasa masu rikitar da ɗan adam ya yi, sannan gently in a cool voice ya fara magana "Ke wuce ki koma ciki, kai kuma wuce a mayarda kai in da ka fito, magana kake yi akan tana zaune a cikin maza ko? To kasani daga yau ta zama ƴar aikina, even gyaran bedroom ita zata yi, abinci komai dare idan ban ci ba to bazata yi barci ba dole sai ta kawo mani, kuma ta jira na ci sannan ta yi barci idan na bata izini, kamar dai yadda ka ga bodyguards na gida haka zata zama mana ƴar aiki, turawa basu da hankali ka ce ba? zan gwada maka kuwa, zaka ga karshen zama a cikin maza".

Cikin sauri Areef ya ce "No Lion please ka kyale shi ya zauna to, idan ya so sai su zauna da yarinyar tasa, you know fa ina kaunarsa....".

Wani kallo ya wurgawa Areef ɗin wanda ya sanya shi haɗiye maganar tasa ba tare da ya karisa ba. Tsawa ya daka masu akan ya gama magana Musharraf ya wuce a mai da shi Airport ya koma Washington DC, daga yau ya mashi hannu riga da Rimsha tun da har da nuna masu izza a cikin gidansa, to ya rabasu ya ga karshen tsiya, kuma dole ta zauna a cikin maza ta yi masu aiki domin ba shi kaɗai zata yi wa aiki ba, harda su Areef da su Mark sai ya ga karshe rashin kunyar Musharraf, zama cikin maza yanzu ta fara karo wasu sojoji ma zai yi su kara yawa a gidan su kai ko su 12 ta yadda zai tabbata yes a cikin zaratan mazan take zaune ita kaɗai mace bakinciki ya kashe Musharraf ɗin su gani.

Ba yadda Areef bai yi ƙoƙarin fahimtar da shi ba akan ya yi hakuri ya kyaye Musharraf, amma ina baya magana biyu, sai ma tsawa da ya kara daga masu wadda ta sanya Rimsha kwasowa a guje tare da sakin trolley ɗin nata ta rungume daddyn tana kuka kamar ranta zai fita, duk yadda take son zama kusa da Lion to bai kai rabin son kasancewa da iyayenta, tana son kasancewa da daddy ta da yanzu kewarsa ya yi mata katutu.

Shi dai Areef ya ji daɗi da Lion ya ce Rimsha ta zama ƴar aikinsa daga yau, amma bai ji daɗin raba uba da ƴa da ya yi ba, bai kyauta ba suna tsaka da kewar juna na tsawon watanni, yau da suka haɗu kuma ya zo ya raba su, abin ya ɓatawa Areef rai.

Shi kuma Imran cikin sanyin murya ya ce "Saif it's my uncle, pls stop telling him that, please and please, evan for the sake of me" ya yi maganar tamkar zai yi kuka, domin abin ya taɓa mashi zuciya sosai, ganin daddyn Rimsha yake yi tamkar Abbansa, kuma ya ji zafin rabasu da Lion ɗin ya yi shi da Rimshan.

Shiru Lion ya yi har kamar ba zai sake magana ba. Sun kwashe tsawon good five minutes a tsaye a wajen, sai kuka Rimsha ta ke yi, shi kuma daddy yana kankame da ita a kirjinsa.

Har sun fidda ran zai sake yin magana, sai kuma suka ji sexy voice nasa can kasa-kasa ya ce "I dnt care even if it's your father not your uncle, am done talking". Tashin hankali, zaro ido waje Imran ya yi ya rasa bakin magana, shi kan shi daddy raba jikinsa da tata ya yi yana kallon fuskar ta, taci kuka har ta godewa Allah, duk idanun nata sun kunbura luhu-lugu, har wani ja kasar idanuwan nata suka yi, saboda kukan da ta sha, shi kuma Lion juyawa ya yi ya koma bedroom nasa.

Areef kuwa girgiza kai kawai yake yi domin dama yasan in dai Lion na waje ka gwada izza a wajen to ba makawa sai ya saka ka kuka, a tsarinsa koma a ina koma waye shi ne sarki, ba'a isa a nuna isa a kusa da shi ba Musharraf ya yi kuskure.

Mark kuwa cewa daddy ya yi ya wuce su koma airport kada Lion ya sake fitowa.

Juyawa daddy ya yi a yaune yake dana sanin sanin su Lion da ya yi a rayuwarsa, cikin kunan rai tare da raunin zuciya ya ce "Imran ga amanar Rimsha, sannan a yau saboda Rimsha zan gaya maka cewa ni ne Hosain, na san kasan labarin kanin Abbanka Hosain, to ni ne, na gaya maka hakan ne kuma domin ka kula da Rimsha kanwar ka ce, kada ka bari komai ya same ta, sannan kuma kada ka gayawa su Yaya babba cewa Rimsha ƴata ce, kada ma ka gaya masu ka ganni, akwai dalili yin haka, sai Allah ya kaddara saduwarmu ko idan kun zo in da nake zan gaya maka komai, yanzu dai gata nan ka kula mani da ita". Ya kai karshen maganar tare da juyawa wajen Areef, shima ya bashi amarnar Rimsha sannan ya wuce zuciyarsa cike da tunanin ya Rimsha zata rayu a cikin shegun kafuran sojojin nan, ga shi Lion ya ce Za'a karo wasu sojojin, ya san halinsu sarai basu da imani, da tsawa kawai za su sanya Rimsha mutuwa ba tare da ta shirya ba, ga shi basu ɗauki zina kamar wata laifi ba ce, amma kuma kasan cewar tana hannun Areef da Imran yasa ya ɗan sami kwanciyar hankali tare da kwarin gwiwa akan da izinin Allah babu abin da zai same ta, sai dai kuma yana jin bugun zuciya idan ya tuna cewa ƴar aiki Rimsha zata zama, yasan babu wanda ya isa ya canzata a wannan ƴar aiki da Lion ya kira ta da shi, sai shi Lion ɗin da kansa, kuma yasan aiki a karkashin waƴan nan masu taurin zuciya ba karamin abu bane, Allah nema kaɗai yasan irin aikin da zata yi wa su Mark kuma, Allah dai ya sa ba barinta da wankin kayan aikinsu masu hangen bala'in tauri da takalmarsu za'ayi ba. Sai tunani kala kala Musharraf yake yi har suka fita.

Ita ma Rimsha kuka take yi kamar ranta zai fita, rungumeta Areef ya yi yana rarrashinta, tana ji tana gani daddy ya wuce ya fita, da sauri Imran ya bi bayansa dan ya raka shi waje, sai dai fa duk jikin Imran ya mutu jin cewa Daddyn Rimsha shine Hosain kanin mahaifinsu, lokaci guda Imran ya ji cewa lallai yana son sanin ainahin tarinhin abin da ya raba kan wannan family har haka, me ya rabasu kenan, wannan gaba na tun ba'a san za su zo duniya ba, sun rarrabu kashi kashi ta yadda yanzu ƴaƴansu sun ta so amma basu san cewa iyayensu bane, kenan bayan daddy ma akwai wani ne ko kuma yaya, shin su nawa ne ma a wajen iyayen nasu, ina Hassan ɗin Hosain ɗin yake?. Wannan shine tambayoyi da Imran yake yi wa kansa da kansa, wadda kuma ba wanda zai iya ba shi wannan amsa sai Abbansa, domin shi ne yaya babba a cikin su Abbin gaba ɗaya, yasan komai kenan.

Allah sarki Areef sai fama da rartashin ta yake yi, yau Rimsha ta ci kuka kamar ba zata rayu ba, har wani sarkewa numfashinta yake yi, gata ga daddynta amma an sake rabasu, ita ba ƴar aikin Lion da zata zama bane ma ya dameta, duk da ta san cewa yi wa Lion aiki babbar bala'i ce domin sai mai dakiyar zuciya irin sojojin nasa za su iya, amma dai duk da haka abin bai taɓa ta sosai ba kamar yadda rabata da daddy ya taɓata. Allah sarki sai kokarin Areef yake yi da ita akan kada ta suma.

Daga karshe ma zazzaɓi ne mai zafi ya rufeta kwance a jikin Areef ɗin, kafin Imran ya dawo jikinta ya yi zafi jau kamar wuta, da yake tana kwance a jikin Areef ɗin sai bai ji zafin da jikin nata ya yi ba, har sai da Imran ya dawo yana ƙoƙarin ɗagata daga jikin Areef ɗin dan ciwon dake jikinsa kada ta fama mashi, a nan ne ya ji jikin nata ya yi zafi kamar wuta.

"Subhanallah Rimsha lafiya, zazzaɓi ne fa a jikinki". Shine abin da Imran ya faɗa bayan ya ɗago ta. Yunkurawa Areef ya yi wadda gaba ɗaya jikinsa ta yi la'asar saboda raba uba da ƴa da Lion ya yi, tsawon watanni ba su tare wannan wace iriyar bakar zuciya ce a kirjin Lion? Shine tambayar da Areef ya yi wa kansa, mutun yana ji yana gani ya raba uba da ƴa suna kuka dukkansu amma ko kaɗan Lion bai ji wani alamar tausayi ba bare ya tausaya masu, tamkar ma ba shi ya yi hakan ba.

Hannu Areef ya kai ya taɓa wutarta, zafi jau kamar wuta, ko motsin kirki ta kasa yi, ta zama wata sukuku sai yadda suka yi da ita, duk yadda Imran ya juyata haka take juyawa tana daga kwance a jikinsa. Baiwar Allah.........

Ni kuma na dasa aya a nan sai mun haɗe gobe idan mai dukka ya kai mu, kada ku mance Book 2 saura page 2 yau ya kare, da zarar na kammala shi zan tafi hutu dan na ɗan huta, ba wani jimawa zan yi ba. Hot comments and likes Ma'assalam..✍️ [12/19, 5:43 PM] +234 906 579 6460: 💖💖TRIPLETS💖💖

E91-92💖

Hannu Areef ya kai ya taɓa wutarta, zafi jau kamar wuta, ko motsin kirki ta kasa yi, ta zama wata sukuku sai yadda suka yi da ita, duk yadda Imran ya juyata haka take juyawa tana daga kwance a jikinsa. Baiwar Allah.

Ɗagowa Areef ya yi ya kalli Imran ɗin kafin ya ce "Take her to hospital, ni ba zan iya dubata yanzu ba, because gaba ɗaya am very weak". Jinjina mashi kai Imran ya yi sannan ya saɓe ta a kafaɗarsa ya nufi waje da ita, shi kuma Areef ya koma ya zauna a saman sofa yana sauke numfashi a hankali.

Abin mamaki kuma abin al'ajabi shi ne da Imran ya zo fita gidan gateman ya hana shi fita, mamaki ne sosai ya kama shi tare da tambayar gateman ɗin akan me zai hana shi fita, cikin girmamawa ya ce "Am sorry sir oga ya ce kada na kara barin wani ya shiga ko kuma ya fita gidan nan ba tare da izinin sa ba, ko da kuwa kune". Imran ya gane matsalar wato yau ran Lion ya ɓaci, ba rashin lafiya ba ko mutuwa Rimsha zata yi sai dai ta mutu, dan mugunta da ganganma ya hana a fita da ita saboda yau babanta ya yi maga da izza kuma yana wajen, shine zai sauƙe akan ƴarsa kenan, Babbar magana.

Shiru Imran ya ɗan tsaya kafin ya juya kan motar ya dawo cikin gidan, haka ya sake ɗaukarta suka koma ciki domin yasan tun da Lion ya ce haka to fa ko Areef a wannan karon sai dai ya ce da Rimsha ta yi hakuri, amma babu wanda ya isa ya canza wannan magana daga ba za su fita daga gidan ba, lallai Lion ya shirya mugunta kenan.

A palon sama ya isko Areef a nan kuma ya gaya mashi abin da Lion ya ce, Areef bai yi mamaki ba domin kuwa ya san tun da suka yi haka da Musharraf tofa sai dai addu'a dan tabbas Musharraf ya ɗan ɓata mashi rai gaskiya ita kuma Rimsha sai dai suce Allah ya kwaceta daga hannunsa kawai, amma dai zata ci bakar wahala ba ɗan kaɗan ba.

Haka Areef ya daure ya ce da Imran ya ɗauko mashi A box a ɗaki bari ya duba ta, dama kunsan jami'ai irin haka ba su rasa iya wani sashe na aiki a ɓangaren lafiya domin kula da kansu idan bullet ya taɓa su ko makamancin hakan, to shima Areef hakan ne ya iya aikin likita duk da ba sosai bane.

Ɗakin Rimshan suka wuce, a nan Areef ya dubata tare da yi mata alluran zazzaɓi, amma fa sun sha dirama kafin ayi wannan aluran, sai da Imran yasa karfi ya danneta kafin nan Areef ya samu ya danna alluran ya yi mata, cikin alluran da ya yi matan kuma har da na barci domin ta ɗan samu ta huta wata kila idan ta tashi ƙwaƙwalwarta ta ɗan yi fresh.

A haka suka barota a cikin ɗakin tana barci suka koma palo suka zauna, sosai suka nutsa a duniyar hira a tsakaninsu, duk wannan abin da suke yi Lion yana jinsu domin ai a palon saman suke.

A ɓangaren gidan Abbi kuwa, bayan sun koma gida da suka yi sallar mangariba suka ci abinci ne suka wuce ɗakinsu while ita kuma Akila Akil ya zo ya ɗauketa ya mai da ita gida, yanzu ya rage daga Jelly sai Hanan, su biyu ne kawai a cikin ɗakin.

Yau wani irin wanka na musamman aunty ta ci, sai tariyo kalaman Akila a cikin ƙwaƙwalwarta take yi, wata magana da Akila ta sake gayawa Jelly safiyar yau ne ya tsaya mata a ranta, maganar kuma ba wata bace fa ce cewa da ta yi, ba sai kin tambayi mijinki wani irin dressing yake so ki rinƙa yi mashi ba, a cikin kayan da yake saya maki a nan zaki gane, idan ke amarya ce ki duba cikin kayan lefenki ki gani, abin da ya fi so shi zai saya maki dayawa, idan kuma kun jima da shi to zaki ga idan kun je sayan kaya zai yi ta cewa ki ɗauki kaza ki ɗauki kaza, to wani abin ba sai kin tambaye shi ba, da kansa zaki ga ya fi damuwa da saya maki irin shi dan yana so. Wannan magana ta tsayawa aunty a rai domin kuwa Abbi ya zu ba mata riga da wando masu shegen kyau sosai a cikin lefenta, a cikima ta ɗauki ɗaya daren jiya ta bawa Jelly, kenan Abbi yana son a rinƙa yi mashi dressing na riga da wando? Sannan ga uban wasu shegun kayan barci daya zuba mata wadda a kalla za su iya kai kala 20 saboda yawa, kenan shima Abbi yana so a rinƙa sanya mashi? Tabbas Akila ta faɗi gaskiya ko kala ne miji yake so zaki ga idan zaku sayi abu zai rinƙa ce maki ki ɗauki kalar can tafi kyau kuma zata yi maki kyau, bawai dan zata yi maki kyau ɗin bane, aa shi dai ya fi son ganinki da wannan kalar ne, amma sai kaga wasu mata dan ya ce ga kalar da zata yi maki kyau sai ta ce a'a ba zai yi mata kyau ba, aa ya yi haske sosai ko kuma ya yi duhu ko dai ya yi kalar fatar ta, complain dai kala kala idan bata son kalar abin da ya zaɓa mata ɗin, dama ba dan ya yi maki ke kyau ba yasa ya ce ki ɗauka, shi ne dai kalar da ya fi so, to dan haka sai mu lura.

Wasu shegun kayan barci Aunty ta ɗauko wadda kusan da su da babu duk ɗaya ne, haka ta sanya a jikinta kuma ta bi shawarar Akila bata sanya bra ba, ta sake su abinta, sai tashi wani fitinannen kamshi take yi, lokacin da ta shirya Abbi yana ɗakinsa baya nan, hakan yasa ta ɗauki wayarta tare da sanya hijabi ta fito zuwa ɗakin nasa, a lokacin ita kuma Ommu tana can tana saƙa ta yadda zata karɓi 10 million a hannun Akil ta hanyar Umaisha.

Bakinta ɗauke da sallama ta shiga cikin ɗakin Abbin, baya ɗakin yana toilet yana wanka, cire hijabin jikinta ta yi ta ajiye tare da nufar gaban mirror tana kara feshe jikinta da wasu kalar perfume ɗin nasa.

A haka ya fito ya sameta, bayan ta ya fara kallo, da farko ma ya zaci Ommu ce domin sirantar ko ace yanayin jikinsu kusan ɗaya, sai da ya ga tsawon da kuma tudun bayan ne ya fahimci ba Ommu bace, gabaɗaya kunya ta kama Aunty, bata saba ba, ta kasa juyowa su yi ido biyu da Abbin, har wani yarrrr jikinta yake yi saboda kunya.

Readers Also Read

More by Bilyn Abdull