Kenza eBookz

Triplets book 3 complete By teema princess - Chapter 107

Triplets book 3 complete By teema princess - Chapter 107

Triplets book 3 complete By teema princess Chapter 107: Triplets book 3 complete By teema princess Chapter 107. Aseef da Akila ma sai zuba barcinsu suke…

3,263 words

Aseef da Akila ma sai zuba barcinsu suke yi. Wannan gida dai kun sani ba sai na sake faɗa ba, gida ne na yara jiki dukka madara iyaye jiki dukka madara, ba ƴaƴan malam shehu ba ne, sai su yi ta zuba barcinsu son ransu, sai time da suka ga dama suke tashi, ba wanda zai tashesu daga barci, idan yunwa ta tasheka ma to sojoji masu yin girki dai sun gama aikinsu, bayin Allan tun karfe 7 suke gama komai su jere a saman table, amma mutanen gidan nan ne su zo su ci ya zama tashin hankali, wasu ma sai 12 suke cin abincin, irinsu daddyn Rimsha kenan, ita kuwa Jehan duk time ɗin da ta tashi barcin take ci. Haka suma Aseef da Akila, duk time da suka tashi suke ci. Shi kuwa daddynsu Lion, wani lokaci ma ba cin abincin safen yake yi ba, sai dai su sha green tea shi da uncle Herry. Mutane ne dai gasu nan kala kala, iri irin ra'ayi sun iya, kowa da kalar tasa, ba zaka taɓa sanin ina ma suka dosa ba, kowa kawai abin da ya zo mishi cikin ƙwaƙwalwarsa yake aikatawa. Shi John ma ai dama sai ya sha giya ya bugu da daddare tukun nan yake yin barci, shiyasa idan ya fara barcin safe baya tashi da wuri, wani lokaci sai karfe 2 ko 3 na rana, sai lokacin da giyar ta sake shi, ga shi baya yi mata shan wasa. Shi kuwa Jay ɗan ba ruwana, matarsa yake kira a waya su yi ta zuba soyayya har dare ya tsala, wani lokaci ma sai asuba ya gabato yake hakura su yi barci, shiyasa shi ma baya tashi da wuri, sai ya kai 10 or 11, kai a takaice ma duk gidan ba mai tashi barci kasa da karfe 8 sai masu aiki, sojoji, sai kuma Lion da shi dama bai damu da yin barcin safe ba. Lokacin da Rimsha take zuwa school ne tana tashi da wuri.

Yanzu ma duk sai zuba barcinsu suke yi, shi uncle T tun ranar da ya zo, ya saka kafa ya bar gidan bai kara dawowa ba, ya tafi yawonsa, sai Allah kaɗai ya san mishi in da ya tafi.

Da misalin karfe 11 dai'dai ta farka daga barci. Ko da ta farka ta jima a kwance har 11:30, sannan ne ta lallaɓa a hankali ta sauko kasan bed ɗin, ta nufi toilet. Wanka ta yi tare da dawowa ta shirya cikin wandon jeans baki da t-shirt maroon. Ta yi kyau sosai, dama ita bata son manyan kaya, kuma dama bata saba sakawa ba idan baku manta rayuwarsu a baya ba.

Fitowa ta yi ta nufi bedroom ɗin daddynta, a duk tunaninta zata sami Areef a wajen, dan yau da kewarsa da kuma tunaninsa tare da begen son ganinsa ta tashi. Amma ko da ta shiga baya nan, daddyn nata kawai ta samu kwance a saman bed yana latsa wayarsa, sai murmushi yake yi. Chatting suke yi da Rimsha, amma sam bata gaya mishi sun ɗauko Na'urat ba, dan Lion ya ce kada ta gayawa kowa, hakan yasa bata faɗa ba. Sai zubawa daddyn nata shagwaɓa take yi a kan tana kewarsa, shi kuwa ya ce mata ba wani nan, ba tana tare da GAR ba? Yasan ba wani kewarsu da take yi, kawai wayancewa take son ta yi mishi dan ya ce mata yana kewarta.

Voice ta yi mishi a in da take zuba mishi kukan shagwaɓa a kan lallai ita wlh tana kewar shi over. Guntun tsaki Jehan ta ja tana ji kamar ta damƙo Rimshar nan ta bata a jikinta, saboda a cewarta duka Rimsha take so, wani kayan takaice har da kuka a cikin voice ɗin. Shi dai daddy da yake ya san matsalar baby Jehan ɗin tasa, sai ya miƙe zaune tare da ajiye wayar a gefe yana ce mata sarkin rigima an tashi?.

Turo baki ta yi tana ce mishi "Good morning dad." "Morning my daughter how are you doing?." Shiru ta ɗan yi kafin ta ce "Daddy i wanted to eat something, am feeling hungry." Ta kai karshen maganar tare da miƙewa ta nufo palo. Kasa ta nufa dan a can table na kasan ake jere abinci. Zuba kalar wanda take so ta je ta yi, ga abincin kala kala sama da kala goma jere cike a saman table ɗin, zaɓa ta yi wanda ya yi dai'dai da ra'ayinta, sannan ta ɗeba tare da haɗo duk wasu abin da zata buƙata ta koma saman.

Bedroom ɗin daddy ta koma, saman lallausan carpet na kusa da bed ɗin ta zauna tare da zube abincin a kasan, har lokacin bata cire tsammani Areef zai shigo cikin ɗakin ba, sai dai kuma har ta ci abincin ta kammala sam bai shigo ba.

Hira suka yi ta zubawa da daddy bayan ta kammala har zuwa azahar, a nan ne suka yi sallama ta koma bedroom nata dan ta yi sallah. Shi ma daddy ya miƙe ya shiga toilet.

Bayan ta idar da sallah ne sai ta fara tunanin to yau ina Areef ya je? Kuma ga daddynta a gida bai fita ba bare ace sun fita tare, to shi ina ya je?. Haka dai abu ya fara tsamari har zuwa la'asar bata gan shi ba, ta kuma kasa tambayar daddynta ina yake, ta kasa cin abincin rana, ta shiga damuwa sosai da sosai na wuce misali.

Hayewa saman bed nata ta yi da yamma kenan bayan ta yi sallar la'asar. Duk ta damu fiye da tunanin mai tunani, kwanciya shiru ta yi tana tunanin abubuwan da suka rinƙa faruwa a tsakaninta da shi, bata san time da ruwan hawaye ya fara bin kuncinta ba, ta kasa goge hawayen, haka ta barshi ya cigaba da zuba, idan ta rufe idanu face nasa kawai take gani yana murmushi, tana jin yunwa amma ta kasa iya cin abinci.

Wasa wasa har ta yi sallar isha bai dawo gidan ba, abin ya isheta har ta fito zuwa bedroom nasa dan ta duba shi. Ko da ta je babu shi babu alamarsa. Bedroom nata ta koma, yau ta kasa zuwa su yi hira da daddynta ma.

Tana zuwa ta haye saman bed nata ta hau kuka, yunwa kamar zai kasheta amma sam ko kallon in da abincin yake ma ta kasa, ga shi bata da phone numbersa. Hawaye ne wani na bin wani a saman kuncinta tana daga kwancen, Allah sarki wlh har faɗawa ta yi na wuni ɗaya, har ta ɗan rame, idanunta sun kara fitowa sosai, kun san idan mutun ya rame idanunsa suna kara girma, to ita ma hakan ce ta kasance da ita.

Har karfe 10 na dare bai dawo ba, ita kuma bata dai'na ruwan hawaye ba, ga uban yunwa, sai dai idan ta gaji da kwanciya ta juya ta nan, idan ta sake gajiya ta juyo, duk ta jike lallausan pillownta da hawaye. Duk wannan halin da ta shiga daddynta yana sane da ita, amma sam bai kulata ba, saboda shi da kansa ya ji daɗin abin da Areef ɗin ya yi mata, yanzu ai zata san cewa yana da matsayi a cikin zuciyarta.

Tana tsaka da kukanta hawaye wani na bin wani, ta luluƙa duniyar tunaninsa. Tamkar daga sama ta ji ana goge mata hawaye, sam bata ji shigowar mutun ba. A hanzarce ta waro idanunta sosai tare da miƙewa zaune. 4 eyes suka yi da shi yana zaune saman bedside drawer, hannunsa na rike da handkerchief fari kal mai bala'in laushi kamar audiga.

"Jehan meyasame ki kike kuka?." Kai Areef ɗan duniya ne number ɗaya, wato ya nuna irin shi bai san komai ɗin nan ba.

Wani irin harara ta wurga mishi da idanunta da suke jawur saboda kukanta da ta ci ta koshi. A hanzarce ta diro kasa daga saman gadon tare da nufar hanyar barin ɗakin wai bata son ganin shi. Cool murmushi ya saki tare da miƙewa da sauri ya tare gabanta.

"Jehan What is wrong with you ne? Ina yi miki magana, you have to be amsa me first before ki fita ko? Ko kin manta ni yayanki ne?." Haushi tamkar ta rataye kanta, raɓawa gefensa ta yi zata wuce tana wani hucin da ita kanta bata san dalilin yin shi ba.

❤️PRINCESS TEEMA💋......✍️

Sake tare gabanta ya yi tare da zube gwiwowinsa a kasa ya kuma kama kunnensa yana faɗin "Am so so sorryyyyyyyy my sister, bana son naga sister ta cikin ɓacin rai, yanzu kinga na duka kasa ina baki hakuri, to kiyi hakuri ki tsaya ki gaya mini waye ya taɓaki muje na rama miki? Ai yayanki yana nan." Da gudu ta juya ta koma saman bed ɗin nata tare da faɗawa tana sakin wani irin kuka mai tsuma zuciyar mai sauraro, wanda ita kanta bata san dalilin yin kukan nata ba.

Da sauri ya miƙe ya rufa mata baya, saman bed ɗin ya hau dan kukan nata har cikin ransa yake ji, ba zai iya jurewa ba. Ɗagota ya yi tare da mannata da kirjinsa yana tallaɓo kanta da kyau da kyau.

Idanunta a rufe ta fara kai mishi dukan huce takaici, tana yi tana kukanta, kankameta sosai ya yi a jikinsa yana bubbuga bayanta alamar rarrashi, sam taki yin shiru dan kukan zuciya take yi, tana yi tana wani irin shessheƙa wanda zai nuna maka zuciyar mutun a kusa yake, an kure hakurinta.

Ganin haka ne na taki yin shiru ne yasa ya kwanta da ita tare da yi mata rumfa da faffaɗar kirjinsa a in da ya haɗe bakinsu waje guda ya fara kissing nata. Tamkar an ɗauke wutar nepa haka ta dakata cak da kukan da kuma dukan nasa da take yi.

Da sauri ta kai hannunta saman idanunta ta murjesu da kyau, dan ta tabbatarwa da kanta ba fa mafarki take yi ba, tabbas namiji ne yake kissing nata. Wani irin azababben bakin ciki ne ta ji, a kule tasa karfinta dukka ta ture shi daga kanta. Da yake bai saka karfi a wajen kwanciyar tasu ba, dan bai yi tunanin zata ture shi ba, sai ya zamana da ta ture shi ɗin ya kuma turu, ya sauka daga kanta. A zafafe ta diro kasa daga saman gadon tare da nufar waje da gudu tana sakin kuka mai tsuma zuciyar mai sauraro.

Gabaɗaya ya kasa mikewa ya bi bayanta, duk kasala ta sauka mishi a jikinsa, kwanciya kawai ya yi a saman bed ɗin yana sauke numfashi a hankali hankali, da haka har barci ɓarawo ya ɗauke shi a wajen.

Ita kuma bedroom na daddynta ta shiga da gudu tana kuka. Tana zuwa ta faɗa jikin daddyn nata. Hankali a tashe yake tambayarta menene yake faruwa? Ko dai wani abin ne ya sami Areef. Cikin kuka take gaya mishi wlh Areef ɗan iska ne, kiss ya yi mata.

Sam daddy bai san time da murmushi ma ta subce mishi ba, Areef da Jahan abin nasu ma sai ka rasa ta ina zaka ɓullo musu, amma dai yau kam bari ya kashe wannan wutar bakiɗaya. Rarrashinta ya fara yi tare da bata labarin Areef fa mijinta ne, shi ba ɗan iska ba ne, matarsa ya taɓa. Karo na farko a rayuwarta da ta ji wani azababben kunya ya kamata. Hannu tasa ta rufe fuskata tare da miƙewa da gudu ta bar ɗakin, sai yanzu ma take jin kunyar abin da ta gayawa daddyn nata. Shi dai daddy ina ruwansa da iya shegensu? Ba dai ya gaya mata gaskiya ba yau? To ta je su karata a can, ƴan rigima ne ai dukkansu biyu daga ita har Areef ɗin.

Bedroom nata ta koma, a nan ta same shi ya yi mata barci a saman bed nata, bawan Allah ya gaji sosai. Kusa da shi ta zo ta zauna tana kare mishi kallo. Ita da kanta ta san Areef yama wuce irin mazan da mata suke burin mallaka, kyakkyawan gaske, natural beauty. Yana ta zuba barcinsa cikin kwanciyar hankali.

Kayan jikinsa ta fara bi da kallo, da alama daga dawowarsa ko bedroom nasa bai shiga ba ya zo wajenta, dan ba kayan barci bane a jikinsa, shi ma da tsananin kewarta ya wuni. Wandon jeans ne da polo t-shirt a jikinsa, sai takalma Booth a kafarsa.

Miƙewa ta yi a hankali tare da komawa kusa da kyawawan kafafunsa. A nutse ta kwance igiyar takalmar nasa tare da cire mishi su, ta ajiye a kasa. Ɗan motsawa ya yi kamar zai farka, tsit ta yi tana kallon shi. Bai farka ba sai dai ma ya gyara kwanciyarsa, ya cigaba da barci.

Ta jima tana ta kare mishi kallo kafin ta miƙe ta ɗauko bargo da pillow ta dawo kasa ta kwanta abinta, ta bar mishi gadon, duk yunwan da take ji ma ta neme shi ta rasa, da haka barci ya ɗauketa ita ma cikin farinciki.

Washegari da asuba, ko da ta farka sai ta kalleta a saman bed, shi kuma baya ɗakin, ko ba'a gaya mata ba ta san shi ya mayar da ita sama gadon. Dama kun san su TRIPLETS sun saba sallar dare, ya farka dan ya yi sallah ne ya ganta kwance a kasa, shi ne ya mayar da ita saman bed shi kuma ya koma bedroom nasa.

Ta ji daɗi sosai. Toilet ta nufa, wanka ta fara yi kafin ta ɗauro alwala. Bayan ta idar da sallah ta sake kwanciya dan ta yi barcinta. Ba ita ta farka ba sai karfe 9.

Wanka ta yi ta shirya cikin kananan kaya ta nufo waje dan ta je ta gaishe da daddynta, ta kuma yi breakfast, dan da wani azababben yunwa ta tashi. Dai'dai zata shiga bedroom ɗin na daddy shi kuma yana fitowa. Ɗaure fuska sosai ta yi tare da wucewa bata ce mishi ko sannu ba. Shi ma ɗaure fuska ya yi ya wuce abinsa.

(Areef bai san Jehan ta san cewa shi mijinta bane yanzu, har da ɗaure mata fuska ya yi, ya wuce, irin yanzu ya zama yaya babban nan, boss baya son raini, lallai yanzu ne ma za'a fara sabon dirama, kuma sabon wasa, da alama ita ma zata wana shi.😂)

Sai dai fa daga shi har ita ɗin suna wucewa kuma suka sake juyowa a in da suka lallaɓo a hankali dan su zo su leƙa juna. Yana leƙo cikin bedroom ɗin daddyn ita kuma ta leƙo waje, karaf suka haɗa ido. A sukawane ta juya da sauri dan ta wuce ciki.

Cikin zafin nama ya rikota yana mai jawota jikinsa. Duka ta kai mishi a kirji na huce haushi meyasa ya leƙota. Kama hannun nata ya yi tare da kaiwa ɗan bakinsa ya sumbata yana faɗin.

"Da ni da ke waye ne ya leƙo wani da kike jin haushi? Kawai kinga handsome guy ya wuce kin kasa hakuri kin zo zaki leƙa shi ko? To Allah ya kamaki." Wani irin kallo ta wurga mishi kafin ta ce "..............

❤️🔥❤️🔥❤️🔥❤️🔥❤️🔥❤️🔥🔥❤️🔥❤️🔥❤️🔥❤️🔥❤️🔥❤️🔥❤️🔥❤️❤️🔥

*KINDADE KINA NEMAN ABUN DA ZAI SANYAKI QIBA,QIBA MEKYAU KIYI DIMIMI DUK INDA KIKA SHIGA BABU RAINI KINYI TA SIYA KINA ASARAR KUDINKI🤔 ALBISHIRINKI NAZO MIKI DA ABUN DA ZAKISHA BA TARE DA KINYI ASARAR KIDINKI BA 💃 Yana da matiƙar kyau sosai ko'ina naki zai chiko ki xama abar sha'awa duk mai buƙata ta nemeni ta wannan number 09067614054, kada ki bari ayi babu ke, kayanmu tested and trusted ne, guarantee ne*.

*KINDADE KINA NEMAN ABUNDA ZAI SANYA KISAMU XAMAN LFY TARE DA KWANCHIYAR HANKALI? TO BABYN HABIBI KIXO UMMU AFFAN TAXO MIKI DA SHAHARARRUN KUMA INGANTATTUN MAGUNGUNAN MATA, KAMA TUNDAGA KAN HUMRA, TURAREN WUTA, INFECTION KILLER, COLACCA, SAI KAYAN GYARA PAGE. KACA KACA. YALLAGWADA. JIGIDA. RUWA RUWA. BANI BANI. WOMEN JELL BATA BATA. DAFIN KAXA. TANTABARA. XABUWA. CICCIƁI. AND EXCLUSIVE, XUMA TASTED AND TRUSTED INA FARIN CHIKIN SANAR DA KU MUN FARA RAMADAN PROMO GAME BUQATA XA A IYA TUNTUBA NA TA WANNAN NUMBER 09067614054 JIGAWA STATE MUNA AIKAWA KO'INA CIKIN AMINCI DA YARDAR ALLAH, BABYN HABIBI KARKIMANTA DA KAYANMU FIRST CLASS NE, DAGA KANSA AN RUFE KOFA, YANA DA INGANCI NA WUCE TUNANINKI*.

❤️🔥❤️🔥❤️🔥❤️🔥❤️🔥❤️🔥❤️🔥❤️🔥❤️🔥❤️🔥❤️🔥❤️🔥❤️🔥❤️🔥❤️🔥

https://whatsapp.com/channel/0029VaMOfZZI7BeKXPU9gK2S

❤️🔥❤️🔥❤️🔥❤️🔥❤️🔥❤️🔥❤️🔥❤️🔥❤️🔥❤️🔥❤️🔥❤️🔥❤️🔥❤️🔥❤️🔥

TSARAWA DA RUBUTAWA......✍️

❤️FATEEMA ZAHRA MUSA (💫PRINCESS TEEMA💋)

*Domin samun damar karanta littafin nan daga farko har karshe zaki iya nemana ta wannan number 09162620621*

82

❤️Dedicated to myself.....✍️💋

"Da ni da ke waye ne ya leƙo wani da kike jin haushi? Kawai kinga handsome guy ya wuce kin kasa hakuri kin zo zaki leƙa shi ko? To Allah ya kamaki." Wani irin kallo ta wurga mishi kafin ta ce "Au da gaske?." Gyaɗa mata kai ya yi yana faɗin "E mana". Shiru ta ɗan yi Kafin ta ce "Okey rufe idanunka bari na gani da ni da kai waye ne ya leƙo wani".

Kasa kasa ya ce "Wayo zaki yi mini ne yauwa?." Juya idanunta sama ta yi tambayar mai tunanin wani abin. Shiru ya zuba mata idanun yana kallonta tare da kara kankameta sosai.

Ɗan ɗago kafafunta ta yi dan tsawonta ya yi daidai da na shi, amma bata iya cinwa kunnensa ba, magana take son gaya mishi dama. Ganin hakan yasa ya ɗan rakwafo kaɗan dan ya bata damar faɗan abin da take son faɗa. Kara ɗaga kafafunta ta yi a in da ta cinwa kunnen nasa. Kasa kasa kamar mai raɗa ta fara yi mishi magana a cikin kunnen nasa. Zaro idanu waje ya yi yana sauraronta, bai san time da ya saketa daga rungumar da ya yi mata dan ya sami damar kallon face nata ba.

Shafa gefen kunatunsa ta yi tare da wucewa da sauri izuwa cikin ɗakin daddyn nata tana murmushi. Shi kuma sai Allah kaɗai yasan me ta gaya mishi da ya sanya shi ya yi suman tsaye, kamar ba shi ba, haka ya lula duniyar tunani.

Almost 2 mins yana tsaye a haka kafin daga bisani ya bi bayanta izuwa bedroom ɗin. Kwance saman bed ya iskota tana zubawa daddy hira.

Kusa da ita ya zauna yana faɗin "Uncle wannan Jehan ɗin ko?." "Me kuma ta sake yi maka?." Zai yi magana suka haɗa ido da ita, kashe mishi ido ɗaya ta yi tare da haɗa mishi da harara. Shiru ya ɗan yi, can kuma kome ya tuna, sai ya saki cool murmushi tare da miƙewa yana faɗin "Uncle tom ka ce ta kawo mini breakfast na ɗaki, ba zan iya ci a palo ba."

Zaro idanu ta yi tana faɗin "A'a daddy, gaskiya ni ba zan je bedroom nasa ba". Kallon shi daddyn ya yi tare da cewa "Just ka bata umarni kai tsaye, daga yau ba sai ka ce nace mata ta yi kaza ba, ka wuce sai ka sani na saka ta yin abu, idan ka ce ta yi ma ya wadatar."

Matsowa ya yi tare da sumbatar daddyn a kumatu yana faɗin "Love you my uncle" "Love you too my son." Harara ta bishi da shi tana turo baki. Kashe mata ido ɗaya ya yi yana mai cigaba da murmushi.

Ficewa ya yi daga ɗakin abinsa. Yana fita daddyn ya ce ta tashi ta je ta kai mishi abincin. Ba dan ta so ba ta mike, sam bata son su keɓe saboda tasan abin da ta gaya mishi a kunne ba zai barta ba, sai ya yi mata ba dai'dai ba. Kamar zata yi kuka ta nufo wajen.

Saman table na palon kasa ta nufa, abincin da ranta yake so ta haɗa mishi tare da ɗauka ta nufi ɗakin nasa. Bakinta ɗauke da sallama ta shiga, yana zaune a bakin bed nasa yana waya da Lion a kan gobe zasu shigo Nigeria, sai murna yake yi, ya yi kewar Lion ɗin sosai, ya jima bai ji rigimar Rimsha ba, ga shi yanzu ta zama rigimammiya number ɗaya.

Readers Also Read