Kenza eBookz

Triplets book 3 complete By teema princess - Chapter 49

Triplets book 3 complete By teema princess - Chapter 49

Triplets book 3 complete By teema princess Chapter 49: Triplets book 3 complete By teema princess Chapter 49. Can misalin karfe 4 na dare, karan sautin…

3,273 words

Can misalin karfe 4 na dare, karan sautin garuwar hakwaranta waje guda ne suka farkar da shi daga barci nasa, kun san dama shi bashi da nauyin barci, abu kaɗan ya yi motsi kusa da shi zai farka, rawan sanyi take yi sosai da sosai saboda sanyin asuba ya fara sauka, hakwaranta sai garuwa da juna suke yi, gabaɗaya ilahirin jikinta rawa yake yi, barci cike da idanuwansa sosai, da kyar ya warosu a kanta, lokacin kuma hasken wata ya ɗago sosai, shiyasa ma sanyin ta yi yawa, juyawa ya yi gabas da yamma babu wani abin da zai sake rufeta da shi, ba zai iya miƙewa zuwa cikin ɗaki ba, dan wani irin azababben barci dake damunsa, jikinsa sam babu kwari, bashi da zaɓi dole ya jawota jikinsa dan sanyin ya yi mata sauki, yasan ko ya ce ta tashi ta tafi ɗaki ɓata bakinsa zai yi, wannan uwar tsoro ai tana tashinta ma zata yi tsalle ta ɗane shi dan bala'in tsoro, haka ya jawota jikinsa ya kara tattare bed sheet ɗin gefen nata ya rufeta da kyau, shi kuma dai bai ji wani sanyi ba, hasalima zafi zafi kaɗa kaɗan yake ji, dama kun san su kam ai sarakan sanyi ne, sun saba da sanyin da ya ninninka wannan mai kankara ma. A haka dai suka cigaba da barcinsu, gently ya mayar da idanunsa ya lumshe su ba jimawa barci ya yi awon gaba da shi.

Bashi ya farka ba har sai karfe 5:30, a nan ma ba karamar dirama suka sha ba, taki rabuwa da shi, sai da ya daka mata tsawa sannan ta dawo cikin hankalinta tare da takurewa a saman mattress ɗin tana kuka ƙasa ƙasa, shi kuma ya wuce toilet ɗin daddy ya ɗauro alwala dan lokaci anata sallah a masallatai, bayan ya fito ne ita ma ta miƙe cike da tsoro ta nufi cikin, tana bala'in tsoron haɗuwa da wani dan dai bata yarda ba wasu mutanen ba, kuma tana tsoron Lion ɗin, haka ta daure baiwar Allah ta nufi bedroom nasu ita da Jehan, wanka ta yi sauri sauri ta fito ta shirya cikin wata ƴar doguwar rigarta wadda da kaɗan ya wuce gwiwarta, da rigar tana kai mata har kasa, amma yanzu da ta ɗauko shi ya yi mata guntu, dan an jima ai rabonta da kayanta na gidan, rigar tana da dogon hannu, jikinta kuma kamar rigar sanyi yake, ma'ana yana da kauri, sai dai ta roba ce, tana kama jiki, ta bi jikinta ta kwanta luf, shape nata ya fito sosai da sosai, daga shape na sama har na kasa.

Zumbulelen hijabi ta zumbula har kasa, da sauri ta fesa perfume ta fito ta nufi balcony ɗin, a lokacin kuma karfe 6 da rabi ta yi, in da ya shinfiɗa dadduna ta nufa, yana kwance saman mattress ɗin, da alama ya mayar da barci ne, dan akwai barci sosai a idanunsa, sam taki kallon in da yake. Sallah ta yi tare da zama ta fara askar har zuwa karfe 8, rana ya ɗago sosai, lallaɓawa ta yi cike da tsoro ta nufi kitchen nasu, zuciyarta sai dukan uku uku yake yi, haka ta wuce gawarwakin mutanen daren jiya ta nufi kitchen. Komai yana nan yadda yake, akwai gas akwai komai, kayan tea ɗin da mum take haɗawa dad ta buɗe drawer ta ɗebo, yunwa take ji sosai, wanke pot ta yi tare da zuba ruwa ta ɗaura tea ɗin.

Bayan ta ɗaura sai ta koma palo ta cire hijabin jikinta ta ɗaura saman sofa sannan ta dawo kitchen ɗin, tsayuwa ta yi kusa da gas ɗin har sai da tea ɗin ya tafasa dai'dai yadda take buƙata, cike da tsoro da kuma fargabar me zai je ya zo ta ɗauko cup ɗin daddynta guda biyu masu bala'in kyau ta zuba musu tea ɗin bayan ta tace kayan ciki kenan, saman tray ta jerasu, shi sai ta ɗauko mishi madara da suga tare da milo, dan black tea ne ta girka, zuciyarta sai harbawa yake yi ta nufi sama da kayan tea ɗin.

Bata same shi a wajen ba, kusa da mattress ɗin ta ajiye tray ɗin tare da juyawa da gudu zata bar wajen, dan ta tsorata rashin ganin shi a wajen, da yake tana gallon ƙasa ne sai ta yi karo da shi bata sani ba, faffaɗar kirjinsa kanta ya daka, shigowarsa wajen kenan ya je ya yi wanka ne ya shirya cikin wandon jeans baki da polo shirt sky blue, ya yi kyau over, ya saki gashin kannan nasa.

Baya ta yi zata faɗi ya sanya hannunsa ɗaya ya riƙo wuyar rigarta, hakan kuma ya yi sanadiyar bayyanar sunansa dake saman tudun tula tulanta, jawota ya yi ya tsayar da ita da kafafunsa kafin ya wuce zuwa wajen mattress ɗin, a gefe ya zauna tare da jawo wayarsa ya kira his excellency a kan ya sanya a turo ƴan sanda da fararen kaya su zo su kwashi gawarwakin nan da ya kashe jiya, abin da yasa ya kashe su dukka ba tare da bar ko guda ɗaya dan ya samu wasu bayanai daga wajen shi ba shi ne, su waƴan nan ba wani abin da suka sani fa ce a kirasu a waya a ce musu suje su kashe wane, hasalima basu san da waye suke waya ba, umarni kawai suke jira sai kuma diran kuɗi a account nasu, dan haka babu wasu bayanai da suka sani, kashe su shi ne dai'dai, shiyasa ya ɓarar da shegu, mugun iri ɓata gari.

Cikin sanyin murya cike da tsoro ta ce "Yaya Saif ga tea". Bai amsa ba kuma bai ɗago ya kalleta ba har His excellency ya ɗaga kiran nasa, kara wayar ya yi a kunnensa ya fara magana a nitse cikin kwanciyar hankali, yana fitar da words one by one, zuba mishi idanu ta yi tana kallon yadda yake motsa kyawawan lallausan red lips nasa, ba zaka taɓa cewa shi yake maganar ba, magana cike da class

❤️❤️TRIPLETS❤️❤️

*Duk wace ta karanta mini littafina ba tare da ta biyani hakkina ba Allah ya isa ban yafe ba, sai Allah ya tsayar da mu ranar da bata da abin da zata biyani face ladarta*

Dedicated to Maman Yasmin💋

E39-40💋

Cikin sanyin murya cike da tsoro ta ce "Yaya Saif ga tea". Bai amsa ba kuma bai ɗago ya kalleta ba har His excellency ya ɗaga kiran nasa, kara wayar ya yi a kunnensa ya fara magana a nitse cikin kwanciyar hankali, yana fitar da words one by one, zuba mishi idanu ta yi tana kallon yadda yake motsa kyawawan lallausan red lips nasa, ba zaka taɓa cewa shi yake maganar ba, magana cike da class.

Bayan ya kammala ya ajiye wayar a gefe tare da yin kasa da kansa kamar mai tunanin wani abin, daddaɗar kamshi su kaninfarin da chitta dake cikin tea ɗin sai dukan hancinsa yake yi, har ga Allah kamshin ta yi mugun yi mishi daɗi, ita kuma tana tsaye kamar wata soja, wani irin kara suka ji tamkar fashewar glass a palon kasa, a guje ta watso ta haye saman mattress ɗin ta ɓuya a bayansa, har da kankame shi ta yi, mamaki ne ya kama shi, wai wannan wace iriyar yarinya ce, tsoronta ya yi yawa, ko motsawa bai yi ba. Sun ɗan ɗauki lokaci a haka kafin ya yunkura zai miƙe dan ya je ya ga menene ya fashe a palon.

Kankame shi sosai ta yi, ba ƙaramin haushi ta bashi ba, ya tsani mutun matsoraci, a ɗan fusace ya juyo tare da fisgota da karfi, gabaɗaya ta tafi sai saman faffaɗar kirjinsa, damko wuyarta ya yi yana ƙoƙarin fara magana, zaro idanunta waje ta yi a matukar tsorace, ba ƙaramin kyau razananniyar face ɗin nata ta yi mishi ba, musaman ma da ta zaro idanun nan nata, ga su sleeping eyes dara dara, ga su farare tas kamar audiga, ya tsani ganin matsoraci, amma yau fuskar matsoraciya ya burge shi, tsoron ya yi wa face ɗin nata kyau, sake ta ya yi tare da miƙewa ya nufi palon kasan, ita kuma kwanciya ta yi a wajen ta takure waje guda, jikinta sai wani kerma yake yi.

Babu kowa palon kasa, daga in da yake tsaye ya hango cikin kitchen, ashe cup ɗin daddy da ta ɗauka bata mai da drawer da kyau ta rufe ba, kuma ta jawo tray ɗin cups ɗin baki baki dan tsawonta bai karisa kaiwa can ba, to shi ne tray ɗin ya faɗo gabaɗaya glass cups ɗin suka fashe, guntun tsaki ya ja tare da juyawa ya koma saman.

A in da ya tashi ya koma ya zauna, cup ɗin tea ɗaya ya ɗauka cikin natsuwa ya ɗan zuba sugar kaɗan ya fara sha, dan kamshin tea ɗin ya yi mugun tafiya da shi, haka zalika ɗanɗanon tea ɗin ta yi mishi daɗi, kuma yunwa yake ji sosai yasa shi ya sha, idan baku manta ba, bai ci abincin daren jiya ba. Ba ƙaramin daɗi ta ji ba, Lion ya sha tea ɗin da ta girka mishi, har wani nauyayyar ajiyar zuciya ta sauke, tare da miƙewa zaune a tsakiyar mattress ɗin tana ɗan satar kallon shi, da yake suna kusan a jerene waje guda, sai dai da ɗan rata a tsakaninsu.

Wayarsa ce ta fara kara alamar shigowar kira, yana dubawa sai yaga Aseef ne, nisawa ya yi, ba ƙaramin daɗin kiran nan ya ji ba, yana kewarsu sosai da sosai, ɗaukar kiran ya yi, suna haɗe su dukkansu biyu kwance a saman bed nasa, cool murmushi Aseef ya saki, shi dai Areef bai da yawan fara'a, amma akwai kyan zuciya kamar me, zuciyar zinari ke gare shi, ba kowa da kowa yake samun ni'ima da baiwar zuciya irin makamanciyar tasa ba.

Kamar abin haɗin baki, har suna rige rigen tambayar ina Rimsha, Lion ya ɗan yi mamaki, wai ba za su tambaye shi ya yake ba, ya ya isa garin da ba nasu ba, ya ya kwana, sai ina Rimsha suke tambaya?, Ko gaisawa basu yi ba, su dai ina Rimsha kawai, lallai Rimsha ba ƙaramin samun damar mallake zuciyar ƴan uwansa ta yi ba,.

Shiru ya yi musu bai tanka ba, turo baki Aseef ya yi tare da saka mishi kukan shagwaɓa a kan lallai shi sai an nuna mishi Rimsha. "Ka sha maganinka Areef?" Shi ne abin da ya ce dasu, gyaɗa mishi kai ya yi yana mai kara tambayarsa dan Allah ina Rimsharsu take. "Yau ya kamata ka cire bandejin dake wajen ciwon ai, yanzu komai normal ne". Ya sake faɗa a sanyaye, tamkar bai ji tambayarsa Rimsha da suke yi ɗin ba, amsa mishi da okey Areef ɗin ya yi tare da sake tambayarsa ina Rimsha a karo na uku.

Shiru ya yi bai amsa ba, cikin zoyala Areef ɗin ya sake cewa "Wai Saif me ya faru ne na ganka kamar sabon ango? Sai wani kyalli face naka take yi, ko dai garin Abujan ne ta yi daɗi sosai?". Kwashewa da dariya Aseef ya yi yana faɗin "Ni dan Allah ka nuna mini my Rimsha, ita nake son gani, idan ba haka ba, wlh bani ba cin abinci yau". Ya san halin Aseef sarai, zai aikata ya ki cin abincin.

Dogon numfashi ya ja tare da sauƙewa a hankali, ya fahimci ba za su barshi ya yi numfashin or ya sha iska ba matikar bai nuna musu in da take ba, da alama kuma idan bai nuna musu ita ɗin ba, ko abinci ba zasu ci ba, yadda suka kafe da sanyin safiyar nan suke wani tambayarsa ita, wannan kenan dan ita suka kira shi ba dan lafiyarsa ba, ita suka kira su kallah ba wai su tambaye shi ko ya isa lafiya ba, lallai ma sun shahara, yanzu Rimsha ta zama kamar kishiyarsa a zuciyarsu.

Gently ya ɗan waigo tare da ɗago dara daran blue eyes nasa ya sauƙesu a kanta, tana zaune shiru kamar mai tunanin wani abin, ba karya ta yi kyau sosai cikin kayan jikin nan nata, gabaɗaya shape nata sun bayyana, ga shi ba'a magana in dai wajen shape ne, akwai shi sosai, ƙasa ta yi da kanta dan kada su haɗa idanu, yatsun hannunta ta fara wasa da shi kamar wata mara gaskiya, zazzaƙar sexy voice nasa ne ya ratsa dodan kunnenta, calmly ya furta ta zo nan, ba musu ta matso gefen shi sosai tana wani yin kasa da kai, Aseef yana ganinta ya furta "Our Queen!" Shi kuma Areef ajiyar zuciya ya sauke.

Jin muryar Aseef yasa ta ɗago kanta, wani irin kyakkyawar kayatatcen cool murmushi ta saki wadda sai da dimple nata suka yi wani irin lotsawa na musamman, siririn wishiryarta dake tsakanin fararen hakwaranta ya bayyana, ba zaka taɓa cewa abinci ko wani abin ya taɓa ratsa cikin hakwaran nan nata ba saboda haskensu, sai kyalli suke yi, suna shan wankewa ne da kayan wanke baki masu inganci, shiyasa suke tas.

Shagwaɓe murya ya yi yana faɗin "Our Queen ina missing naki over wlh, yau ba zanci first spoon naki bafa". Ita ma shagwaɓe murya ta yi kamar dai yadda ya yi mata magana, tamkar zata yi kuka ta ce "Nima ina kewarku sosai, Yaya Areef dan Allah ku shigo mota kawai ku biyo mu, zan fi jin daɗi, yanzu wlh ina tsoron gidan sosai, akwai wasu mutane, dan Allah kuzo zan fi jin sanyi". Yadda tayi maganar sai da ta sanya Lion ɗin waigowa ya kalleta, ga shi tana magana dimple nata na wani irin lotsawa, duk wanda ya kalleta sai ta burge shi, ga shagwaɓa da take zubawa Aseef, abin ba'a cewa komai, yau har cikin zuciyarsa sai da ya ji ta burge shi, kawar da kallonsa ya yi daga kan nata tare da cigaba da shan tea ɗin nasa ya kawar da wayar daga face nasa zuwa saitin tata.

"Kina so mu zo ne my Rimsha?" Cewar Areef, da sauri ta gyaɗa mishi kai alamar e, "To shikenan zamu zo, amma ke da kike tare da Lion me abin tsoro? Kada ki damu, ni nasan waye ɗan uwana, yana kaunarmu kuma yana kaunar dik abin da muke kauna, muna kaunarki ya sani, ba zai yaɓa watsa mana kasa a idanu ba, yana son gamin mu cikin farinciki fiye da kansa, so ki kwantar da hankalinki, dole zai baki farinciki dan yasan idan ya yi hakan kamar mu ya yi wa, in kin yi farinciki tamkar mune muka yi, akasin hakan ma, mune muka yi"......... A nan wajen Areef ya yi amfani da basira ne ya ɗaure Lion da magana, ya gayawa Rimsha Lion yana sonsu fiye da kansa, dan haka zai kula da ita, ya san cewa idan ya faɗi hakan, kenan suna da kwarin gwiwa sosai a kan shi, hakan zai sa Lion ɗin ya bata kulawa dan kada ya watsawa ƴan uwan nasa kasa a idanu, Areef ba dai basira ba, akwai basirar na wuce misali.

Zata yi magana Lion ya miƙa mata waƴar tare da miƙewa ya bar wajen zuwa ɗakin daddynta, yana tafiya Areef ya ce "Kina ji sister?" Gyaɗa mishi kai ta yi alamar e tana ji, "Lion ba ya cin abincin restaurant, ba ma zai taɓa ci ba komai wuya komai daɗi, duk in da zai je in dai ba mai yi mishi girki, to Maltina da kyau sune kawai suke zama abincinsa, dan su hannun baya taɓa cikinsu a cewarsa, kinga kwai ma ko an dafa ai ba'a taɓa cikin ba sai bayan, bayan kuma ɓarewa za'ayi a zubar, dan haka ki rinƙa dafa mishi kwai, dan Allah kada ki bari ɗan uwana ya zauna da yunwa, wlh bashi da juriyar yunwa, sai dai baya cin abinci sosai, iya Maltina idan ya sha, yana iya ƙoshi, amma idan lokacin cin abincinsa ya yi zai shiga damuwa dan baya jure yunwa, ki rinƙa bashi Maltina da kwai, na san ba zai iya cin abincinku na Nigeria ba, dan haka ba sai kin sha wahalar girkawa ba kin ji ko?" "To yaya Areef amma yanzu da na bashi tea namu na nan ya sha wlh, ka ga cup nashi ma har ya kusa shanyewa, kaɗan ya rage".

Ba Areef kawai ba, har ta Aseef sai da ya zaro idanu waje, anya kuwa,? Aseef ya tambayi kansa da kansa a cikin zuciyarsa, Areef kuwa cewa ya yi "Ba abin mamaki bane dan ya sha, na san yunwa yake ji shiyasa ya sha, na gaya miki baya da juriyar yunwa ko kaɗan, dole zai sha dan bashi da mafita, ba zai iya cin abincin waje ba duk wuya duk daɗi, yanzu kuna da Maltina a gidan naku ne ko babu?". Ɗan waigawa ta yi tana kallon shi yana nufota ya fito daga bedroom na daddynta, "Yaya Areef babu, babu Maltina kuma babu wuta a gidan". Zai yi magana Lion ya miƙa mata hannu a kan ta bashi wayarsa, babu musu ta miƙa mishi cikin girmamawa a kuma nitse.

"Areef zan fita ne, sai na dawo". Ya kai karshen maganar tare da katse kiran ba tare da ya jira amsarsu ba, pistol gun da ya ajiye daren jiya ya ɗauka ya nufi hanyar palon kasa dan ya sauƙa fita zai yi zuwa unguwa. Zazzaƙar muryarta ne ya katse shi tare da sanya shi juyowa babu shiri. "Yaya Saif tsoro nake ji, dan Allah kada ka fita ka barni, ina jin tsoron gidan sosai". Ta yi maganar a nutse, a shagwaɓe, can kasa kasa kuma, sannan ta yi maganar tana sunkuyar da kai katsa dan bata son kallon face nasa bare ma taga action ɗin da zai ɗauka.

Shiru ya ɗan kalleta na ƴan sakanni, maganar Areef ne ta dawo mishi kunnansa, yana son mu fiye da kansa kuma yana son farincikinmu, ba zai taɓa bari ki shiga kunci ba, dan yasan idan kin yi farinciki to tamkar mune muka yi, tuna hakan yasa ya juya ya cigaba da tafiya, binshi da kallo ta yi idanunta sun ciko tab da kwallah, tana bala'in tsoron zaman gidan ita kaɗai, bai juyo ba kuma bai yi mata magana ba har ya sauƙa ya fita daga palon baki ɗaya, juyowa ta yi ta balcony tana kallon shi ya zo wajen motarsa, shiru ya ɗan tsaya bai shiga ba, can kuma sai ya ɗago kansa sama kamar yasan tana kallon shi, da hannu ya yi mata alama a kan ta zo su tafi, da sauri ta miƙe, tsabar murna bata ma san lokacin da hawayen da suka cika mata idanu suka zubo ba, ɗakinsu ta koma ta ɗauko ɗan ƙaramin farin hijabi ta sanya a saman kanta, ta yi kyau over, baiwar Allah ko tea ɗin ma ita bata sha ba, kuma tana jin yunwa sosai kamar ta mutu, amma ba halin ta ce zata tsaya shan tea ɗin, dan ba zai jirata ba.

Ta wutsiyar idanunsa yake kallonta tun da ta fito, sai da ta kariso gabansa, calmly ya ce ta buɗe musu gate, da okey ta amsa mishi tare da wucewa ta je ta buɗe gate ɗin, shi kuma ya shiga motar ya tada ta, waje ya nufa, bayan ta fita ne ya tsaya yana jiranta, sai da ta rufe gate ɗin sannan ta zo da sauri ta shiga gidan gaba, sai tashin kamshi take yi.

Da gudu ya ja motar, bayan sun kusa kaiwa babbar gate ne ya ciro face mask ya sanya a face nasa, dan yasan idan sun isa gate ɗin sai ya sauƙe glass ɗin motar, miƙa mata face mask ɗaya ya yi a kan ta saka, dan baya son su tsayar da su tambayarta yaushe ta dawo da sauransu, dan ba wanda bai san ƴaƴan Nawazudden ba a wajen, suma masu tsaron babbar gate ɗin sun santa tun da kullum daddy na kaisu school.

Readers Also Read