Triplets book 3 complete By teema princess - Chapter 54
Triplets book 3 complete By teema princess Chapter 54: Triplets book 3 complete By teema princess Chapter 54. Bayan ya sanya glass ɗin ne ya ce da ita…
3,365 words
Bayan ya sanya glass ɗin ne ya ce da ita suje, bai tsaya sauraronta ba ya fice daga cikin motar, ya ɗan yi gaba ya barta a baya, tana fitowa samari suka fara kewayeta suka tare mata gaba, ga shi tayi irin dressing na karuwan ita ma, daga mai cewa jimana ƴan mata, sai mai cewa nariga, sun sha gabanta sun hanata bin shi, sai kakkauce musu take yi tana son wucewa sun hanata, da alama kuma dayawa daga cikinsu a buge suke, sun sha sun bugu sosai, sai wani layin maye suke yi mata, baki duk warin giya.
Ta ruɗe ta rasa ya zata yi, bata ankara ba sai ji ta yi an jawo hannunta ta faɗa saman kirjin mutu, tun daga yanayin faffaɗar kirjinsa ta fahimci shi ne, nufa cikin ainahin wajen ya yi da ita, tana manne a jirjinsa, dan ya lura idan ba rungumeta ya yi ba, ba zasu daina tare ta suna taɓa ta tare da shafe mata jiki ba, shi kuma baya son a gane shi, shiyasa bai yi yunkurin ɗagawa kowa murya ba, kawai ya rungumeta a kirjinsa dan su yi saurin kammala abin da ya kawo su.
Sosai ta kankame shi tana shakar numfashinsa, ɗan sauko da kansa kasa ya yi yana kallonta, sarkin tsoro duk ta bi ta tsorata, abin da bata saba gani ba, sai ya yi mata wani banbara kwai. Bayan sun shiga waje, sai kuma ya ji ba zai iya sanyata wannan aikin ba, ba zai iya sanyata zuwa ga mutumin dan ta fito mishi da shi ya kama shi ba, baya son shiga ya kamashi saboda wani dalili nashi na kansa, amfani da ita yake son yi wajen kama shi, yasan idan ya kalleta dole zai biyota, dan a haukace yake da neman sauran family'n Nawazudden da suka rage, ɗan raba jikinsu ya yi yana kallonta, yadda ta yi shigar tata marabanta da waƴan da suke wajen kaɗan ne, shi ba ma shigar kayanta ne a gabansa ba, idan ya raba jikinta da nashi kafin ta isa ga mutumin samari da dama zasu tare ta, zasu yi ta rungumarta suna shafata, ita kuma sarkin tsoro tsab zata ɓata musu shiri, dan zata iya waje baki ta yi ta ihu a cikin jama'a har komai ya lalace.
Shiru ya yi yana tunanin me mafita kenan? Dan tun da ya sako kafarsa a cikin nan ya ji gaskiya ba zai iya tura ta ba, ya zuba mata idanu, amma a zahiri ba ita yake kallo ba, tunani yake yi, da yake dai a cikin glass idanun nasa suke, sai ka yi, zaton ita yake kallo.
Wasu samari ne ke nufo in da suke, sun sha sun bugu suna ta tangal tangal suna layi tamkar zasu faɗi kasa, sun zo dai'dai kusa da su, cikin sauri ya mai data jikinsa ya rungumeta dan kada su bangajeta ta faɗi kasa ta fara yi mishi ihu a nan, wannan mai da ita da ya yi sai da ya ji shock ba kaɗan ba, dan da karfi ya jawota jikin nasa har sai da ta buge shi sosai a kirjinsa, waje ya juya da ita, cikin mota ya mayar da ita kafin ya fito ya rufe motar da key dan kada wasu ma su nufeta ta yi mishi hauka, takure jikinta waje guda ta yi tana kallon yadda ƴan mata da samari ke shagawagi a wajen ga uban kiɗa da yake tashi kamar zai ɗauke garin.
Ta yi lamo a jikin kujera tana tunanin me ya kawo su wannan waje kuma, me Lion zai yi a nan?, Bata ankaraba sai gani ta yi gabaɗaya wutar clubs ɗin ta ɗauke, zaro idanunta waje ta yi tana faman kallon guys dake ta kunna hasken wutar tsadaddun wayoyinsu. A cikin duhun ta ji an buɗe gidan baya na motar tasu, ba ƙaramin bugu ziciyarta ya bada ba, jin alamar shigowar mutun a gidan bayan ne yasa bugun gaban nata ya kara tsananta, sai ƙoƙarin dannewa take yi, lokaci guda kuma ta sauke wani nauyayyar ajiyar zuciya shaƙar numfashin mai ɗauke da daddaɗar kamshin perfume nasa da ta yi ne yasa hakan, ashe shi ne ya buɗe gidan bayan ya sanya mutumin da ya zo kamawa a ciki, ya yi wa mutumin ɗaurin goro tare da ɗaure mishi baki da wata tsumma wadda a wajen ya samu.
Gidan gaba ya zo ya shiga ya tada motar da gudun gaske suka bar clubs ɗin, har lokacin kuma wutar bai dawo ba, security dake wajen ma da karfin kakinsa ya yi amfani wajen wuce su, wato dai waya suka samu daga sama a kan akwai mota mai kira kaza zata zo fita, da ta zo a bata hanya ta fita, tun shigowarsu ya shirya hakan, lokacin da ya yi parking na mota kafin ya fito ya tsaya ya tura saƙo zuwa ga His excellency, shiyasa yana zuwa kawai aka bashi hanya ya fice abinsa.
Bai zame ko'ina ba sai gida, suna zuwa ya fito yana faɗin "Ki ɗauki abin da zaki ɗauka daga nan sai Kaduna". Ya kai karshen maganar tare da wucewa cikin gida dan ya ɗauki abin da yake da bukatar ɗauka, sun bar mutumin a cikin motar ɗaure ko motsi bai isa ya yi ba, dan ɗaurin mutuwa ya yi mishi, da sauri ita ma ta fito, har lokacin enginen wuta a kunne, zanensa da ta yi a baya ta ɗeba, tare da wasu hotuna da ta ajiye a drawersu, sai kayan haɗa tea na mum da take haɗawa dad ta ɗeba dayawa da dai sauran kayan da zata buƙata, trolley Jehan ta ɗauko ta shirya komai a ciki tare da nufar waje.
A cikin mota a wajen gate bakiɗaya ta isko shi, sanya trolley ta yi a cikin motar gidan baya kusa damutumin kafin ta dawo zata rufe gate ɗin, tana kokarin jan gate ɗin ta rufe sai ganin shi ta yi ya fito daga cikin motar ya nufota da nufin ya rufe gate ɗin, komawa baya ta yi ta tsaya tana kallon shi, ciki ya koma ya kashe engine tare da cire wayar sannan ya dawo ya rufe ƙaramin gate ɗin ta ciki da sakata kafin ya fito ya jawo babbar, wata danƙareriyar sarka ya sanya a jikin babbar gate ɗin, irin sarka ce da ake ɗaure manyan ɓarayi, ita ya fitar daga cikin boot na motarsa ya sanya wa babbar gate ɗin ta waje, sannan ya danna wata sabuwar kwaɗo da ya saya a shopping da suka yi ɗazun, sai da ya tabbatar ya yi wa gate ɗin ɗauri mai kyau kafin ya rufeta tare da juyawa ya nufi motar, da sauri ita ma ta juya ta shige ciki.
Da gudun gaske ya figi motar ya bar wajen, kai tsaye hanyar Kaduna suka nufa, sai sharara uban gudu yake yi tamkar zasu tashi sama, ita kuwa tuni ta lafe a jikin kujera sai barci abinta, duk wani checking point da ya wuce da karfin kakinsa ya yi amfani wajen wucewa ta yarda ba su tsayarda shi wajen bincikar motarsa da sauransu ba. Sai karfe 12 suka shiga Kaduna kai tsaye gida ya wuce, su Aseef sun jima da yin barci bayin Allah, ita ma Jehan tana can tana zuba barcin wahala Baiwar Allah, ta azabtu ba karya, ko wanka bata yi ba bare kuma cin abinci, tun wannan barci da ta yi time da Aseef ya kaita ɗakin, tun shi bata farka ba.
Suna shiga gidan ya miƙawa Mark mutumin, dan suna shiga cikin gidan Mark ya nufosu da sauri yana yi wa ogan nasa welcome, Mark ɗan amana, ɗan ba ruwana, yana bala'in kaunar ogan nan nasa, dan halinsu kusan ɗaya. Umarni ya yi mishi a kan ya ɗauki mutumin ya cigaba da kula da shi yana bashi hukunci mai kyau zuwa lokacin da Nawazudden zai diro Naija, dan yana son haɗesu waje guda ne, kafin ya san abin da ya dace ya yi next.
Ita kuma Rimsha, sai barci take zubawa abinta, ba ta da labarin sun iso gida ma, kashe motar ya yi ya fito zuwa cikin gida, har ya kai tsakiyar harabar gidan, sai ya tuna ashe da ita suke tare, ɗan juyawa ya yi ya gani ko Mark na kusa ya buɗe mota ya tasheta, sai yaga walam babu Mark, ba dan ya so ba ya juya zuwa wajen motar, kofar side nata ya buɗe yana tunanin wai menene ma sunanta oho, hannu yasa yana ɗan bubbuga jikin kujerar, shiru bata farka ba, ganin zata ɓata mishi lokaci ne, ga shi yana son zuwa ya yi wanka tare da cin abincin ya kwanta, hakan yasa ya saɓeta a kafaɗarsa zuwa cikin kawai.
Da yake dare ta yi sosai, shiru kake ji, bedroom nata ya kai ta, saman bed ya kwantar da ita, ba tare da ya bi ta kanta ba ko ya kalli in da take ba ya juya sai bedroom nasa. Kayan jininsa ya fara cirewa, ya rage daga shi sai short sannan ya nufi toilet dan yin wanka, yau har cikin ɗaki Mark ya kawo mishi abinci saboda TRIPLETS sun yi barci, babu mai kawo mishi.
Bayan ya kammala wanka, ya yi shiri cikin kayan barcinsa mai bala'in kyau da tsada, abincin Mark ya zuba mishi, ya ci mai ɗan yawa saboda yunwa da yake ji, bayan ya kammala ya sha lemu saboda abincin ta yi digesting, miƙewa ya yi ya nufi waje, shi kuma Mark ya kwashi kayan abincin ya nufi kitchen.
Palon kasa ya sauƙo, bedroom ɗin Areef ya fara shiga, tare ya samesu saman bed suna zuba barci, Aseef ga waya a hannunsa, da alama chatting yake yi barci ta yi awon gaba da shi, Allah sarki yana bala'in kaunar ƴan uwan nan nasa, ba zai iya yin barci ba tare da ya shigo ya duba lafiyarsu ba.
Saman bedside drawer ya zauna tare da fara karanto addua'o'i yana tofa musu, barci suke yi cikin kwanciyar hankali, dukkansu fuskokinsu ɗauke da annuri, da alama cikin matsanancin farinciki barcin ya ɗaukesu, gently ya karɓi wayar hannu Aseef tare da ajiyewa a gefe yana mai cigaba da tofa musu addu'a, zubawa ciwon Areef idanu ya yi yana kallon yadda ya shafa maganin a wajen, da kallo ɗaya ya yi wa wajen yasan Areef faɗa ya je ya yi ya fama wannan ciwon, har ya kai hannu kamar zai taɓa, sai kuma ya fasa dan baya son su tashi daga wannan barcin farincikin da suke yi.
Ya ɗan jima yana yi musu addua'o'i kafin ya miƙe, gently ya kaiwa Areef sumbata a goshi yana mai jin tsantsar kaunarsu a ransa, a nitse ya zagayo ta ɗayar ɓangaren da Aseef yake, shi ma ya bashi sumbata, cike da so da kaunarsu fal a cikin ransa ya wuce ya nufi nasa bedroom ɗin, saman bed nasa ya haye ya kwanta, duk a gajiye yake sosai, wayarsa ya jawo ya kashe kafin ya yi addu'ar barci ya shafa, a hankali ya lumshe dara daran blue eyes nasa, after some minutes idanuwansa a lumshe ya sanya hannu ya laluɓo remote ɗin Ac ya kara gudu tare da jawo bargonsa zuwa cikinsa ya kashe wutar ɗakin tare da kunna lamp dake bedside drawers masu bada wuta sky blue, babu jimawa barci ya yi awon gaba da shi, a hankali yake sauke numfashi cikin kwanciyar hankali, da gani ba ƙaramin jin daɗin barcin yake yi ba.
A ɓangaren gidan Abba kuwa, lokacin da Imran ya isa da jelly, dai'dai lokacin shi ma Akil ya danno hancin motarsa tare da Umaisha..............
❤️❤️TRIPLETS❤️❤️
*Duk wace ta karanta mini littafina ba tare da ta biyani hakkina ba Allah ya isa ban yafe ba, sai Allah ya tsayar da mu ranar da bata da abin da zata biyani face ladarta*
E43-44💋
A ɓangaren gidan Abba kuwa, lokacin da Imran ya isa da jelly, dai'dai lokacin shi ma Akil ya danno hancin motarsa tare da Umaisharsa, a tare suka fito daga cikin motocin nasu, ɗaukar jelly Imran ya yi dan idan ya ce ta tafi da kafarta, zasu jima basu shiga ciki ba, kun santa dama da iya zuzuta abu, tsabar iskanci idan ya ce ta taka kafa sai taki, yes tana jin zafi amma har da karawa ta yi, rufa musu baya su Akil suka yi, sai da ya isa tsakiyar palo ya sauƙeta tare da zaunar da ita saman sofa ya juyo ya miƙawa Akil hannu dan su yi musabaha.
Fuska ɗauke da fara'a Akil ɗin ya miƙa mishi hannu suka gaisaz Umaisha ta dawo kusa da jelly ta zauna tana faɗin "Yaya Imran ina wuni?" Da fara'a sosai a face nasa ya amsa da "Lafiya lou ya karfin jiki". Dan Akil ya gaya mishi bata jin daɗi, da lafiya ta amsa mishi. Gin motsinsu yasa Akila fitowa dan taga su waye ne, ganin sune yasa ta kurma ihu ta taho da gudu ta rungume Umaisha da jelly ta faɗa jikinsu tana dariya, zama Imran da Akil suka yi saman sofa mai zaman mutun uku Imran yana faɗin "Ke Heartbeat zaki yi ki karya mini mata ko? To maza ki tashi a jikinta bata da lafiya".
Rungumeta jelly ɗin ta yi tana faɗin "Aunty Akila wlh jikina ciwo yake yi mini". Kara rungume sosai Akilar ta yi tana yi mata sannu duk da bata san menene yake damunta ɗin ba, a wannan hali Ammie da Abba suka sauƙo daga sama suka samesu.
Da sauri Ammie ta kariso wajen tana faɗin "Ku nuna mini wace ce ƴar Maik a cikinsu?". Akila ce ta nuna mata Jelly, murmushi kaɗan ta yi dan idan baku manta ba, bata da yawan fara'a sosai, "A dole ƴar Maik ta zama haka ai, Maik namu, kai amma ina kewarsa wlh, ya ce Ammie idan kika kuskura yau kika yi mana irin miyar rannan sai na yi miki saki uku". Tana magana tana ɗan murmushi.
Kallon juna Akil da Imran suka yi suna mamakin mahaifiyar tasu, ya akayi yanzu kuma take son family'n Abbansu? Anya Ammie sune kuwa? Kai akwai dai wani abin, ita kanta Akila ta sha ruwan mamaki, kashe musu ido Abba ya yi akan kada su yi mata wata magana da bata dace ba, kada su kuskura su tuna mata ta taɓa cewa bata son family'nsa, dan idan suka tuna mata za'a iya samun matsala tun da yanzu ne ta sami lafiyar ba'a jimaba, to tana iya komawa ruwa idan suka mata wata magana. Ganin abin da Abban nasu ya nuna musu na su yi shiru ne yasa suka yi shiru suka danne mamakinsu.
Hannun jelly ta riƙo tana faɗin "Tashi na ganki, ai ƴar Maik ƴar ɗakina ce, babanki a hannuna ya zauna tun yana ɗan shekara 10 zuwa 18 sanan ya koma wajen Deen, saboda Deen ya matsa lallai dole ya koma wajensa, ban so rabuwa da shi ba a lokacin, amma ba yadda zan yi ne, Deen ya kureni a lokacin, sai dai ko da ya koma wajen Deen ɗin yana yawan zuwa wajena mu wuni dan ya fi son zama da ni shi ma". Miƙewa Jellyn ta yi da nufin ta bita zuwa saman nata kujerar, ƴar kara ta saka lokacin data fara ɗaga kafarta.
Cikin sauri Imran ya ce "Ammie bata da lafiya fa". Yana magana yana sunkuyar da kai kasa, tuna abin da Abba ya gaya mata na yaronta ya angwance ne yasa ta kalle shi tana watsa mishi harara, tare da riƙo hannun Umaisha dake ta binsu da kallo, mamakin Ammi ya hanata yin magana, ganin abin take kamar ba gaske bane, dan idan baku manta ba, ita ta gasu ba kaɗan ba a hannun Ammie, sai dai kuma ita Ammie bazata iya tuna cewa ta wahalar da ita ba, Allah sarki rayuwa kenan, yanzu ga shi Umaisha ɗin ta riƙeta a ranta sosai.
Rungumosu dukkansu biyu ta yi a gefe da gefen kafadarta tare da karisawa da su zuwa saman sofa mai zaman mutun uku a hankali, tare da su ta zauna tana mai tsananin jin kaunarsu a ranta, wai surukunta ne waƴan nan, matan ƴaƴanta, kai farinciki ba'a magana.
Zama saman sofa mai zaman mutun 2 Abba ya yi yana binsu da kallo, Akila dai ta lula duniyar chatting da sahibinta dan tun ɗazun yake ta tura mata saƙonnin soyayya da su flowers ta WhatsApp.
"Abban Imran bari mu haura sama da matar Imran ina zuwa". Cewar Ammie, ta kai karshen maganar tare da miƙewa ta riko hannun jelly'n dan ta mikar da ita, bayan ta miƙe ta ɗan rungumota suka nufi sama, dan ta san matsalar, Jellyn bata shiga ruwan zafi mai kyau bane, daga ita har Imran ɗin ba wanda ya yi tunanin idan ta shiga ruwan zafi tana gasa gaban nata da kyau zata sami sauƙi. Suna haurawa sama su kuma su Imran suka fara gaishe da Abban.
Bedroom nata ta wuce da ita, saman bakin gado ta zaunar da ita kafin ta nufi toilet, sai sannu take ce mata, ruwa mai zafi daidai ta haɗa mata tare da zuba mata wasu sinadarai nata da take amfani da su, ciki har da man zogale, da man zaitun, na tane wadda ta jima take amfani da su tun kafin ta sami wannan matsalar, bayan ta samu matsala bata amfani dasu, jiya Abba ya sake sayo mata su tun da ta dawo cikin hayyacinta, sai ta cigaba da amfani da su kamar da, suna gyara mace sosai, bayan ta kammala, daga karshe ta zuba mata ruwan jikakken sassaken mangoro da take jiƙawa, dan yana matikar kashe sanyin gabar mace ba kaɗan ba, bare ma ita jelly da take yanzu aka buɗeta, tana buƙatar ire iren su dan kada a sami wata matsala.
Dawowa cikin ɗakin ta yi, da kanta ta cire mata kayan jikinta, Jellyn bata yi mata kaddama ba, dan idan baku manta ba, ita jelly rainon namiji ne, duk da daddyn ya tsawatar mata a kan wada ta yarda wani ya taɓata ma bare ya cire mata kaya, amma ta san wannan maman Imran ne babu damuwa, kuma ita jelly bata da kunya ko kaɗan, shi ne yasa bata yi wani gardama ba, ta tsaya ta cire mata komai tas, ya rage daga ita sai pant ta kama hannunta zuwa cikin toilet ɗin, Allah sarki duniya kenan, yau ta sami sabuwar uwa, Allahu Akbar Allah mai yin yadda ya so da bawansa, ya bashi a lokacin da yake so, ya kuma karɓa a lokacin da yake so, ya karɓi mahaifiyarta tun ranar da ta zo duniya, yau kuma cikin ni'imarsa ya sake bata wata uwar, ba abin da zamu ce sai dai Alhadulillah.
Sai da suka isa bakin baf ɗin ne ta tsaya ta cire mata pant ɗin nata kafin ta ce to ta shiga, da yake jikin nata dai ba kwari, bata musawa Ammie ba, sai okey kawai take binta da shi, da yake da turanci Ammien take yi mata magana.
Da kyar ta iya zama a cikin ruwan saboda zafin shi, sai Weldon Ammien take ta ce mata, ganin ta ɗan jima ruwan yana ratsata sosai ne yasa Ammien ta fita zuwa palon kasa, hira ta samesu suna ta zubawa.
"Akila ta shi ki kawo mini kayanki ɗakina yanzu". "Okey my Ammie" . Ta amsa tare da miƙewa ta nufi saman. Dawo da kallonta a kan Akil Ammien ta yi tana faɗin "Son kar dai ka gaya mini abin da nake hasashe gaskiya ce?". Da sauri ya ɗago yana kallonta da mamaki "Ammie me kike hasashe kuma?" "Matarka ciki gareta mana". Ɗan kasa ya yi da kansa yana faɗin "E Ammie gaskiya ce, zai kai wata wajen biyu ma yanzu". Zaro idanu ta yi tare da nufar in da Umaisha ɗin take zaune tana faɗin "Wayyo shi ne a rasa wanda zai yi mini albishir a cikin ku? Ni yau ina zan saka kai'na saboda tsantsar farinciki, Allah nagode maka, ya Allah Alhadulillah". Tana magana ta rungume Umaisha ɗin sosai tana mai jin tsantsar farinciki, ita kuma Umaishar ta kasa sakin jiki da ita, sai ɗan murmushi da take yi, a zahirin gaskiya tsoron Ammie take yi kamar ta mutu, dan ma tafiyar Ammie sama da ta yi da jelly Abba ya ɗan yi musu bayani a kan abubuwan da suka faru a baya Ammien bata cikin hayyacinta ne, amma duk da haka ita ta kasa sakin jiki da Ita.