Triplets book 4 Complete - Chapter 3
Triplets book 4 Complete Chapter 3: Triplets book 4 Complete Chapter 3. Rigar jikinsa ya fara cirewa kafin ya fito da wata ƴar ƙaramar camera da yake son…
3,366 words
Rigar jikinsa ya fara cirewa kafin ya fito da wata ƴar ƙaramar camera da yake son ɗaukarta video da shi. Kunna ta ya yi, daga in da suke ya miƙa hannu, ya ɗaura camerar a saman sofa ta yanda zata ɗauki ita gwaggo amma ban face nasa.
Bayan ya cire rigar jikinsa sai ya zame kafafun nasa daga wuyar tata tare da cire wandonsa.
Tsabar ta taku a wajensa, ko motsawa ta kasayi, da kyar take numfashi. Damko kafafunta ya yi bayan ya kammala cire wandon ya rage daga shi sai short. Sake gyara camerar ya yi kafin ya hau kanta da nufin ya yi abin da ya zo yi.
Sai a lokacin ta fara dawowa cikin hayyacinta, ƙoƙarin ture shi ta fara yi, shi kuma yana ƙoƙarin cire towel na jikinta. Ganin ba zata iya ture shi daga kanta ɗin bane yasa ta ɗaga idanunta sama, tana hawaye ta fara magana kamar haka. "Ya Ubangiji ina tawassuli da sunanka tsarkaka, na sani babu wanda ya isa ya yi mini abin da baka kaddara mini ba, babu kuma wanda ya isa ya hana abin da ka kaddara mini, ya Allah dan darajarka da karfin mulkinka, kada ka bari wannan bawa naka ya buɗe abin da ba hakkinsa ba, idan har musulcina gaskiya ce, dominka kuma nake yi, to ya Allah ka kare mini mutuncina! Na baka amanar kai'na, Allah ka jikaina, ka ji tausayina, bani da wayo bani da dabara, kana gani babu abin da nayi wa wannan azzalumi zai zalunceni, ya Allah tun daga farkon Alkur'ani mai girma har karshe wanda ta kasance maganaka ne a ciki, ya Allah babu a in da kayi alkawarin tallafawa azzalumi, Allah ka fini sanin cewa shi azzalumi, ina mai rokonka da tsarkakekkiyar zuciya da kuma yakinin kai kaɗai zaka kareni daga zaluncinsa, ka kare ni ya Ubangijin sammai da kassai!". Sai zuba adduarta take yi a cikin zuciyarta cike da tawassulin Allah zai karɓa mata, tana ta kuka hawaye wani na bin wani, sam tama dai'na jiyo abin da Dr William ɗin yake ƙoƙarin yi mata, hankalinta har ya fara barin jikinta saboda nutsawa da ta yi wajen adduo'i da take yi.
Yana ƙoƙarin shigarta sai kuma ya tsaya cak, tamkar wanda aka yi wa allura, haka ya ji a jikinsa, nan take jikinsa ya mutu, ji ya yi wani irin mugun tausayinta ya shige shi lokaci guda. Dawo da kallonsa a saman face nata ya yi, sai kuka take yi babu kakkautawa.
A hankali ya sauka daga jikin nata ya koma gefe yana kallonta.
Jin nauyi ya bar jikinta ne yasa ta dawo cikin hayyacinta. A hanzarce ta zaro idanunta waje sosai. Ganin ya sauka daga kanta ne yasa ta yunkura da iya karfin da ya rage mata. A ɗari ta miƙe tsaye dan ta gudu.
Wannan miƙewa da ta yi tasa ya ji wani irin azababben sha'awarta ta motsa mishi kuma, abin ku da shaiɗan, nan take ya ji karfi ya zo mishi. Cikin zafin nama shi ma ya miƙe tare da tare gabanta. Har lokacin bakinta a toshe, rikota ya yi ta kafaɗa. Duka ta fara kai mishi tare da ƙoƙarin juyawa ta gudu cikin ɗaki tun da fita waje dai ya gagara. Shi kuwa hannunta ya fara ƙoƙarin kamawa dan ya ɗaure.
Yana ƙoƙarin ɗaure mata hannun nata ne ta juyo da karfin gaske a in da ta faɗa saman faffaɗar kirjinsa. Wani irin azababben kifiya na wani yanayi ne ya caki kahon zuciyarsa. Wani irin diff ya ji komai ya ɗauke mishi na wucin gadin, sakamakon saukar kyawawan tula tulan breast nata da ya ji a jikinsa, ga shi kuma shima babu kaya a jikin nasa, sai short. Ita kuwa dafa kafaɗunsa ta yi tare da barin jikin nasa, a hanzarce ta nufi kofar fita, dan ta gudu ta bar gidan, tana tafiya tana ƙoƙarin kwance handkerchief da ya ɗaure mata baki da shi.
Kamar daga sama taga mutun a gabanta, har lokacin bata gama kwance handkerchief ɗin ba, ba halin ta yi mishi ihu.
Zuba mata idanu ya yi yana kare mata kallo from head to toe, tun da suke haɗuwa bai taɓa tsayawa ya kalli ya face nata yake ba, sai yau. Wani baƙon yanayi ya ji a tattare da shi, ji ya yi ba zai iya yin abin da ya kawo shi ɗin ba, ya ji ma ko wani ne ya zo zai yi mata hakan, to fa sai in da karfinsa ya kare, zai tsaya mata sosai!!. BA DOLE KA TSAYA MATA BA, AN GAYA MAKA ADDU'A WASA NE? ALLAH AI YA WUCE TUNANIN MAI TUNANI, DUK WANDA YA CE YA MIƘA LAMURANSA GA ALLAH, TO ALLAH KUMA ZAI KULA MISHI DA KOMAI, NAKA WASA NE DR WILLIAM, ALLAH IDAN KA YARDA ALLAH SHI YAKE YIN KOMAI, TO FA KAI DA BAKINCIKI A RAYUWARKA KUN YI HANNUN RIGA, ALLAH UBANGIJI KA IYA MANA DA IYAWARKA, MU BA ZAMU IYA BA, BAMU DA TSUMI BAMU DA DABARA!!.
Ganin face nata yasa ya faɗa zazzafar soyayyarta. Kyafta idanunsa sau biyu ya yi yana mai cigaba da kallonta.
Ganin hakan yasa a guje ta raɓa gefensa dan ta wuce ta fita waje. A hanzarce ha riko hannunta ta sama wajen gwiwar hannu. Fisgota da karfi ya yi, luuu ta tafi ta faɗa jikinsa. Zubawa face nata idanu ya yi na ƴan mintoci kafin ya kai hannu ya kwance mata handkerchief ɗin daga bakinta.
Karo na farko da ta saurari zazzaƙar muryarsa da kyau, a in da ya ce mata ta yi mashi shiru, shi babu abin da zai yi mata.
Dogon numfashi ta ja tare da sauke nauyayyar ajiyar zuciya, tsabar jin sanyi a ranta da ta yi na jin ya ce ba zai yi mata komai ba, bata ma san time da ta kwantar da kanta a saman kirjin nasa ba, sai sauke ajiyar zuciya tare da nisawa take yi.
Shi kuwa, ta kara gefa shi cikin yanayi mai wuyar fita, ga shi daga ita sai towel, kasa jurewa ya yi, sai da ya sanya hannu ya rungumota da kyau a jikin nasa. Jin hakan yasa ta yi kokarin barin jikin nasa. Amma sam bai saketa ba, ya kankameta sosai tamkar mallakinsa ce ita.
Da ɗan ɗaga murya ta ce mishi lafiya?. Muryarsa can kasa kasa yana sarkewa, ya ce mata babu komai. A takaice ta ce to ya saketa, ba musu ya saketa ɗin yana binta da idanu.
Da sauri ta wuce izuwa cikin bedroom nata dan ta sanya kaya. Binta da kallo ya yi, yana kallon yanda mazaunanta suke juyawa idan ta taka kafarta.
Sai da ta kurewa ganinsa ne ya sauke nauyayyar ajiyar zuciya tare mai da kayansa da ya cire a jikinsa, sannan ya koma saman sofarta ya zauna. A hankali ya jingina kansa da jikin head na sofar tare da lumshe idanu yana jin wani irin kaunarta daga kallon farko tana shigar shi.
Ya kai 20 mins a zaune a wajen yana tunani. Kamar daga sama ya ji zazzaƙar muryarta tana faɗin "To me ka zo yi a gidana? Ya kuma baka tafi ba?". A hankali ya waro idanuwansa da suke ja sosai a kanta. Tana shirye cikin kayan barci riga da wando pink color masu kyau. Kirjinta kawai ya zubawa idanu ya rasa amsar da zai bata.
Muryar tata ce ta sake katse shi da cewa, lafiya yake kuwa?. Bai san time ɗin da ya ce mata "Please can i have a green tea?". Shiru ta yi tana ɗan tunani.
Tamkar zata ce mashi babu, sai kuma ta kasa faɗin hakan, dan ita mafa, tun a ranar farko da ta fara ganin shi ta faɗa mishi, ta ji tana son shi, kawai dai bata bawa hakan dama bane yasa bai yawaita a cikin zuciyarta ba, amma kam ba shakka ta faɗa!.
Wucewa izuwa kitchen ta yi ba tare da ta sake ce da shi uppan ba. Green tea ɗin ta haɗa mishi, ita kuma ta haɗa nata black tea. A saman wani kyakkyawan plate ta jere two cups ɗin, cikin natsuwa ta ɗauko tare da fitowa zuwa palon.
Yana zaune a in da ta barshi, bai ko motsa ba. Kawo mishi plate ɗin saitinsa ta yi dan ya ɗauki tea ɗin nasa. Ba musu ya ɗauka tare da ce mata thank you. Jinjina mishi kai ta yi ta wuce zuwa saman sofa dake ɗan nesa da shi ta zauna.
Cikin natsuwa ta fara shan tea ɗin nata. Sai kallonta yake yi, ya kasa shan nasa. Sarai ta lura da hakan, amma sai ta basar ta cigaba da shan nata.
After some minutes, ta gama shan nata tsab, shi kuwa rabi ya sha, dan dama ba tea ɗin yake so ba, mai tea ɗin yake son ya yi ta kallo.
A nutse ta ce mishi to ya tafi gidansu mana, tana so ne ta kwanta dare ya yi. Har lokacin da akwai tsoron shi sosai a kwance a cikin idanuwanta.
Zuba mata idanu ya yi na ƴan mintuna kafin ya fara magana cikin sanyin murya. "Dare ya yi sosai, kuma ni ina jin tsoron hanyar komawa, ga shi ban zo da mota ba". A shagwaɓe sosai ya yi maganar.
Bata san time ɗin da dariya ya kubce mata ba, wai dare ya yi sosai yana jin tsoron hanya, lallai ya iya tsara magana, har da wani shagwaɓe murya, ko waye ya koya mashi shagwaɓa kuma? Ta tambayi kanta. Ta sani ba wani tsoron hanya, kawai iskanci ne irin nasa, da ba da kafafuwansa ya zo ba?.
"A'a babu komai a hanya kawai ka tafi". Ta faɗa tana kwaikwayon muryarsa na shagwaɓar da ya yi maganar. Ɗaura cup ɗin tea ɗin ya yi a saman table da yake kusa da shi. A nutse cikin shagwaɓa ya ce "A'a, Please ki bari na yi ta kallonki, kin ji ko?". Zaro dara daran idanun nan nata ta yi, tana faɗin "Kallona kuma?!". Gyaɗa mata kai ya yi tare da gera ɗaya.
Cool murmushi ta sakar mishi kafin ta ce "Meyasa to?". Shiru ya ɗan yi kafin ya ce "Because you are so cute, very very beautiful baby!". Oho god, jin ya yabeta tuni ta kara afkawa tekun son shi, dan ya fi karfin kogin so wannan, sai dai teku.
Sam bata ma san time ɗin da ta ce mishi "Same, you are very very beautiful, handsome guy, i really like your eyes color". Ɗan zaro mata su ya yi. Da sauri ta runtse idanunta dan sun bata tsoro ganin yanda suke kyalli.
Muryarsa ta tsinkayo cikin kunnenta yana faɗin "I really like your eyes, your lips and your everything".
Waro idanuwan nata waje ta yi tana kallon yanda ya jingina kansa da jikin head na sofar yana binta da shanyayyun idanuwansa tamkar wanda ya yi shaye shaye. Abokan faɗa sun shirya yau kam, har ma suna ƙoƙarin zama cikakkun masoya na gaskiya.......KADA KU YI COMPARING RAYUWAR NAN NIGERIA DA NASU NA CAN, DAN AKWAI MUGU MUGUN BANBANCI, RAYUWARMU DA TASU BA ƊAYA BACE SAM, SO KU DAI'NA KALLON RAYUWAR TRIPLETS DA FAMILYNSU, MA'ANA SU DR WILLIAM KENAN, KU DAI'NA KALLONSU TA SIFFAR TAMU RAYUWAR, DAN BA HAƊI, AL'ADU DABAN DABAN!!.
Hannu ya miƙa mata a kan ta zo, bata musa mishi ba dan kada ku manta girman Russia ce ita ma, da ita da shi duk zani ne ta tadda muje, tafiyar duk ɗaya ce. Miƙa mishi nata hannun ta yi. Cikin nutsuwa ya jawo hannun nata alamar ta zo gare shi. Miƙewa ta yi tare da nufarsa.
Tana ƙoƙarin zama a gefensa ya yi saurin zaunar da ita a saman cinyarsa. A tare suka sauke nauyayyar ajiyar zuciya. Hannunsa dukka biyu ya ɗaura a saman shafaffen cikinta tare da ɗan jawota baya ta kwanta a saman kirjinsa.
Ɗan leƙo face nata ya yi yana faɗin "You are the best and you are special beb!, Kuma rigimammiya". Ɗan juyowa gare shi ta yi, suna ɗan fuskantar juna kafin ta ce "Why you say that?".
Ɗan shafa shafaffen cikin nata ya fara yi a hankali yana haurawa sama kafin ya ce "Ban taɓa tunanin zan kula mace ba a rayuwata, infact ni ban san menene ma yake sanyawa a so mace ba, bani da aboki, bani da kawa, only my brother Herry, shi ne kawai na kusa da ni, i have one sister, Josephine, even her ba zan ce maki ga yanda jikinta yake ba a yanzu, because in kin ganta a area da nake ma, to dad ne ya ce ta kirani or something like that".
Ɗan kwanciya ta yi a gefen kirjinsa tana faɗin "But why some peoples are calling you dangerous boss?. In the first place ka nuna mani you are the boss ɗin da gaske, and now kuma naga har da shagwaɓa ashe ka iya?".
Shiru ya ɗan yi kafin ya ce "Ni ruwa biyu ne ai, a gida wajen mum da dad ina yi musu shagwaɓa, amma idan na baro wajensu, ba zaki taɓa cewa ma ina yin magana ba, bare shagwaɓa, kin taɓa kallona a class ina magana da wani ne? Or ina surutu?".
Girgiza mashi kai ta yi alamar a'a.
Shafa gefen lallausan kumatunta da ɗayan hannunsa ya yi yana faɗin "Haka nake to, bana magana da mutane, kuma sunan dangerous, wait small, zaki san daga ina sunan ya samo asali kin ji?". Jinjina mashi kai ta yi tare da ɗan yunkurawa zata bar jikin nasa.
Da sauri ya riketa yana kallon face nata. "Where are you going?". Da hannu ta nuna mashi saman sofarta ba tare da ta yi magana ba.
"Saman jikina ɗin babu daɗin kwanciya ne?". Ya tambaya yana mai do da ita jikin nasa.
Girgiza mashi kai ta yi kafin ta ce "Akwai daɗi, amma ai kaga babu kyau ko? Mum ta hanani yin hakan". "Why mum zata hanaki kuma? Is there any problem akan hakan?". Ya yi tambayar da mamaki bayyane karara a saman face nasa, dan su rungumar juna, kiss, da sauransu ba wani abin bane a wajensu, shi ne yasa yake mamaki da ta ce zata bar jikin nasa.
"No any problem, kawai dai yin hakan kuskure, mum ta ce addini ya yi hani da hakan, so ni ba wani ilimin addinin nake da shi sosai ba, amma na iya karatun Alkur'ani mai girma sosai, saboda shi mum ta fi koya mini, amma dai koma me, is better na yi abin da ta ce koma yaya ne ko?".
Maimaita kalmar addini ya yi kafin ya tambayeta ita a wace addin take.
"I am a Muslim, what about you?". Ta bashi amsa with her full confidence.
Murmushi kaɗan ya yi, wanda da ka gani kasan dole ya ƙaƙalota, dan murmushi bata da gurbin zama a face nasa, duba da yanayinsa ba mutun ne mai fara'a ba sam sam.
"Am a Kristen, my name is William". A hanzarce ta miƙe daga jikinsa jin abin da ya ce, bata taɓa tunanin shi krista bane, duba da yanayin irin fuskarsa, yana da face mai kyalli sosai, idan ka ganshi, zaka yi tunanin yana sallah.
"Why are you avoiding me like that dan na ce am a Kristen? Shin da kika ce mini ke musulma ce did i do something like that to you?".
Girgiza mashi kai ta yi, sai kuma da ya yi magana ta fahimci ta yi kuskure na irin gudunsa da ta yi lokaci guda haka, yin hakan zai sanya ko da yana son shiga addinin musulunci ma, sai ya fasa, saboda zai ce dama haka musulmai suke? Dama basu son wani addini idan ba nasu ba?. Bai san mu musulmai kowa ma muna kaunarsa ba, kuma muna zaman lafiya da shi, addininmu mai sauki ne, addininmu mai ni'ima ne wanda ya bamu damar zama waje ɗaya da wanda ba musulmi ba, mu yi zaman mutunci, kamar da ƴan uwanmu musulmai muke tare, musulmai ne kawai za'a ci hakkinsu kuma su hakura, su yafe, su cigaba da zama da mutun, ai addinin musulunci babu biyunsa a duniya, ya yi ne kawai babu mai musawa sai dai wanda baya son gaskiya.
Shiru ta ɗan yi tana ƴan kame kame, ta rasa abin yi. A lokacin sam bata da wani ilimin addini sosai, haddan Alqur'ani mai girma ne kawai gareta, shi ɗin ma ba dukka ba, kuma bata san fasarar ko sururori biyu daga ciki ba, so hakan yasa ta rasa me zata ce mishi, sai dai ƴan kame kame, ilimin boko ya fi yawaita sosai fiye da misali a kanta sama da na addini, matsalar da aka samu kuma shi ne, ita bata wani zauna da su Brr Naurat sosai ba, secondarynta ma, boarding school ta yi, so bata sami lokaci da iyayenta sosai ba, shi ne yasa.
Ganin haka yasa shi ya miƙe ya koma saman sofar da take zaune. Kusa da ita ya zauna tare da ɗan riko hannayenta, cikin sanyin murya ya ce "Please kada ki gujeni, kin ji? I really love you the way you are, please love me the way i am, don't be angry because am a Kristen my angel, you hear?".
Wani sanyi ta ji a ranta na jin kalamansa, ta ji daɗi sosai, hakan yasa ta ji cewa zata iya janyo shi a jiki har ya karɓi addinin musulunci. Dan haka sai ta juyo da kyau suna fuskantar juna, cikin sanyin murya ta ce "I really love you the way you are, so don't worry!".
Sakin hannayen nata ya yi tare da buɗe mata hannu alamar ta zo gare shi. Ba musu ta faɗa jikinsa tana ɗan murmushi, shafa bayanta a hankali ya fara yi yana mai jin daddaɗar yanayi a tattare da shi.
"What is your name?". Muryarsa ya daki dodan kunnanta.
"A'isha". Ta bashi amsa, ɗan ɗago haɓarta ya yi yana faɗin "Nice nema, but can i call you my angel or my beauty?". Jinjina mashi kai ta yi alamar e. Ɗan kara matseta a jikinsa ya yi tare da sumbatar goshinta.
Haka suka kasance suna ta hira dan sanin juna har wajen karfe ɗaya na dare. A nan ne ta ce mishi barci take ji, zata je ta kwanta. A kunne ya raɗa mata a kan cewa tare zasu kwanta a gado ɗaya, Okey ta ce mishi.
Miƙewa ya yi da ita a jikinsa a in da ya gyara ɗaukarta da ya yi, ya zamana ya ɗaurata a saman kirjinsa, suka nufi cikin bedroom ɗin nata. Bai sauketa a ko'ina ba, sai a saman gadonta, murmushi ta sakar mashi kafin ta ce ta gode.
Hayewa gadon shi ma ya yi, daga ɗan gefen da shi ta kwanta, ya so tambayarta me yasa har yanzu take gudun shi, amma sai kuma ya basar bai tambaya ba, sai ma ya juya mata baya, dan ya lura tamkar tana cikin damuwa na kwanansu gado guda.
A can gidansu kuwa, su Uncle Herry sai neman shi suke yi, sun je bedroom nasa baya nan, hankalin daddynsu ya tashi, ga shi ya bar musu wayarsa ma a gidan, mum ɗinsa har da kuka ta rinƙa yi, tamkar yaro ne karami William ɗin, mutumin da ya kai 24 years a duniya, amma sun ɗaga hankalinsu har haka, da yake shi gaskiya ba mai yawan fita bane na farko, na biyu idan ma zai je party ko gidan rawa, yana gayawa mum ɗin nasa shi fa ya tafi waje kaza, kuma ba zai dawo ba sai time kaza, idan ya ce hakan, to time ɗin na yi zai dawo abinsa, hakan tasa suka ɗaga hankalinsu sosai da basu gan shi ba.
Shi kuwa shiru ya kwanta ya kasa yin barci, baya son gaya mata ne or ta gane, amma ji yake yi tamkar a cikin keji yake, gidan nata ya yi mishi ƙarami over, duk ya takura, dan fa su gidansu, gida ne na madarar kuɗi, babban yayan daddynsu shi ne president mai ci a yanzu, ga uban kuɗi da suke da shi na wuce misali, gidansu aljannar duniya ce guda, bedroom nasa kawai ya kai girman gidan nata gabaɗaya har da palo da kitchen, so bai saba da ƙaramin waje haka ba, duk sai ya takura.
Ita ma ta kasa barci saboda tsananin tsoronsa, sai taga kamar idan ta yi barci, zai yi mata wani abin, dan fa gani take yi kamar fyaɗe ya zo yi mata kamar yanda ya nuna mata tun farko.