Triplets book 4 Complete - Chapter 40
Triplets book 4 Complete Chapter 40: Triplets book 4 Complete Chapter 40. Ciro wayar daga kunnensa ya yi, a in da ya duba time 9:30pm, dare ta fara yi.…
3,357 words
Ciro wayar daga kunnensa ya yi, a in da ya duba time 9:30pm, dare ta fara yi. Calmly ya ce "Where are you now?". Ya yi maganar muryarsa cike da kishi tab, dan kada ace yanzu tana waje harabar gidan, duk da ya hanata fita, amma ya san halinta sarai, yanzu ba ƙaramin aikinta bane ta fita tsakar gida suna waya.
"Am inside your bedroom holding your pillow after i sleep on your bed".
Ajiyar zuciya ya sauke kafin ya yi kasa da murya sosai kamar wani yana yi masu laɓe. "Muyi video call?". Ya faɗa yana mai da kallonsa a kan Aseef da Areef dake a saman bed nasa suna kwance, sun haɗe kai waje guda, da alama wani abin Aseef yake nuwa Areef a wayarsa da ya sanya suka haɗe kan nan nasu waje guda.
"Allah Noorish ni kunyarka nake ji, ba zan iya yin video call ɗin nan ba, ina kewar face naka over, amma ni ba zan iya watching naka kana watching nawa like film ba". Ta yi maganar a tsananin shagwaɓe. Shiru ya yi yana tunanin irin tsananin kewarta da yake yi, abin ba'a magana.
Jin ya yi shiru ne yasa ta ce "Sorry Noorish tom mu yi video call ɗin". "No just leave it kawai, bana son abin da baki so, gobe zan zo na ganki ai".
Cool murmushi ta saki kafin ta cigaba da zuba mashi shagwaɓa yana biye mata shi kuma, sai karfe 2 dai'dai barci ya ɗauketa, sannan ne ya katse kiran tare da miƙewa ya komo cikin bedroom ɗin. Aseef da Areef already sun yi barci tun karfe 1, suma hira da matansu suke yi a waya har barci ya ɗaukesu ruke da wayoyi a hannu.
Saman bed ɗin ya haye tare da tattare wayoyin nasu ya ɗaura a saman bedside drawer, sannan ya gyrawa Aseef kwanciya ta hanyar sauke hannunsa da ya ɗaurawa Areef a fuska, sun wani jeru a saman bed ɗin tamkar sun san barci zai ɗaukesu.
Ɗan bakinsa Lion ɗin ya kai ya bawa kowannansu sumbata a goshi, a hankali ya motsa laɓɓansa ya fara tofa masu addu'ar barci, dan yasan barci babu shiri ne ya ɗauke su, ko addu'a basu yi ba, dan haka bawan Allah sai shi ya yi masu addu'ar tare da shafa masu bayan ya kammala. Rayuwarsu idan suka haɗu su uku waje guda ko makiyinsu ne sai sun burge shi, rayuwarsu yaruwa ce mai cike da darusa da dama a cikinta, shi kansa kaunar juna da suke yi babban darasi ne mai matuƙar girma a rayuwar ƴan uwa, bugu da kari ga matuƙar fahimtar juna dake a tsakaninsu, ga hakura da abin da ɗaya baya so, ba wai dan basu so ba, duk yanda suka kai ga son abu, idan ɗayansu baya so, to suna iya hakura, dan su girmama ra'ayin juna, suna respecting na juna, ba su nuna kamar ma shekarunsu ɗaya, idan Lion ya ce su bar abu, to suna bari, idan Areef ya ce su bar abu baya so, to suna bari, haka shi ma Aseef ɗin, idan ya ce su bari, suna bari koda basu so, dan kawai su girmama ra'ayin juna, kuma ta hakance kawai zasu samawa kansu shakuwa da kaunar juna, rashin girmama ra'ayin juna babban barazana ce ga shakuwa da kuma zaman tare da mutane, so su suna kiyaye wannan sosai a tsakaninsu, ga shi idan sun haɗu suna zuba wasa son ransu, su yi ta zolayar juna, abin gwanin birgewa, baki ma ba zai iya zayyano irin birgewar ba, ace mutane su taso lokaci guda, a haifesu tare TRIPLETS kamar haka, shekarunsu ɗaya, amma suna irin wannan rayuwa mai cike da kawa da ɗaukar hankali tare da ɗaukar darusa, ai abin dole ya burge, shekarunsu fa ɗaya, ya zaki ji idan aka ce ƴaƴanki ne hakan? Ƴaƴanki ne suke tsanani kaunar juna tare da haɗin kai da son farantawa juna irin haka? Ranar da kika mallaki kamarsu ya zaki ji? A yanzu shakuwa tsakanin ƴan uwa ta yi karanta a zamanin nan, sai kiga yarinya budurwa tana da yayarta mace a gida, amma ta fito neman shawara wajen kawaye, to menene amfanin sister taki ko mahaifiyarki? Abin yana yi mani ciwo sosai, bana son naga ƴan uwa suna koda faɗa ne haka, ina kaunar naga ƴan uwa masu son juna koda kamar rabin yanda TRIPLETS suke son junansu ne, su yi komai a tare, su yi shawara a tare, su yi abinsu su rufe su binne kayansu ba tare da kowa ya ji ba, su yi wasa da dariya, su kaunaci farincikin juna, su girmama ra'ayin juna, akwai tsananin daɗi haka, dan Allah my peoples kowa ya kaunaci ƴan uwansa, babu abin da hakan zai rageku da shi face ma wani kara samun kusanci da Ubangiji da zaku yi, saboda idan kuka shaku sosai, zaku runƙa ƙoƙarin ganin kun zauna kunyi tunanin abin da zai taimaki rayuwarku, zaku yi ƙoƙarin gina kanku a kullum, ku gwada ko da rabin soyayyar dake a tsakanin TRIPLETS wa ƴan uwanku, zaku ji daɗi, kuma zaku sanyawa PRINCESS TEEMA taku ta amana ruwan albarka!!!.
Bayan ya kammala tofa masu addu'ar ma sai da ya sake basu hot sumbata, sannan ya miƙe ya sauko kasa daga saman bed ɗin. Jibgegiyar duv nasa ya jango ya rufesu zuwa iya cikinsu, sannan ya ɗan kara masu gudun A.c kaɗan kafin ya wuce ya nufi cikin katafaren dressing room nasa, kada ku mance yanzu fa ya dawo ɗaularsa na Washington, ba irin gidansa na Naija bane, wannan dressing room nasa na nan ma kawai ta fi girman palournsu na Naija, Already kun san komai.
Kayansa ya fara shiryawa, sam bai gayawa Aseef a kan gobe zai wuce Nigeria ba, shammatarsu yake son yi ya tafi abinsa, idan ba hakan ya yi masu ba, ba zasu taɓa shiryawa da Aseef ba, dan sai Aseef ɗin ya ce zai bisa, shi kuma baya son hakan, a nan yake son barinsu, dan akwai gagarumin aikin da Areef yake yi mashi, aikine na sirri, kun san Areef fa sune sirri, to aiki ya haɗa shi da shi, yasan idan ya ce su je Naija a tare, to ba zai yi mashi aikin a kan lokaci kuma yanda ya kamata ba, saboda Jehan da Momma, zai biye masu su yi ta shirirta, shi ne yasa gara ya barsu a nan, shi kuma Aseef abin da yasa baya son su koma Naija a tare, dan baya son su baro Areef ɗin shi kaɗai a cikin gidan, ba zai ji daɗi ba, shi ne yasa zai bar mashi Aseef ya ɗebe mashi kewa kafin ya dawo.
Tsab ya shirya duk wani abin da zai buƙata, ya haɗa komai kafin ya fito izuwa saman bed ɗin, sun zo sun cika mashi bed, yau a bedroom nasa za su kwana, haka ya kwanta a kusa da su bayan ya yi addu'ar barci, tun bai kai ga tafiya ba har ya fara kewarsu, su ɗin jini ne da hanta bayin Allan, ko ina cikon QUADRUPLE ɗin nasu yake? Ya mutu ne ko yana raye? Allah masani sai kuma alƙalamina Ni PRINCESS TEEMA taku ta amana, dan haka mu kasance a tare kawai dan jin komai.
Yana kwanciya ba jimawa ya yi barci abinsa.
A gida Nigeria kuwa, washegari gwaggo ta gayawa Tga da akwai in da zai kai'su. Cikin girmamawa ya ce mata Lion ya gaya mashi tun jiya. Tun da Tga yake a rayuwarsa bai taɓa girmama wani in ma mace ko namiji bayan Lion da yake ogansa ba, sai a kan gwaggo, har cikin ransa yake jin Kaunar gwaggon, tun da ya ji cewa ita ce ainahin mahaifiyarsu Lion, daga nan ya ji yana mugu mugun respecting nata.
Shiryawa suka yi, gwaggo, mummyn Rimsha, Jehan, Akila, and Rimsha, TGA ya ɗaukesu a mota suka bar gidan, shi kuma daddyn Rimsha a yau ya bar kasar, dan Lion ya ce mashi ya zo Washington ya samu Areef da akwai abin da zasu yi a tare. (Sai shiryawa su his excellence kitimurmura Lion yake yi fa, kome su Areef suke sake shiryawa kuma?🤔 Namu ido ko my peoples?.)
Kai tsaye wani katafaren shop na gyaran gashi, lalle da kuma kitso gwaggo tasa Tga ya wuce da su. Ko da suka isa wajen yaki yarda ya jiransu a mota, har cikin wajen ya rakasu, dan ya tabbatar suna cikin lafiya da tsaro, ya tabbatar babu abin da ya samesu, dan haka sai ya bisu har ciki, sai kallon shi tsala tsalan ƴan matan da suka zo wanke kai suke yi, manyan mata ne masu ji da class, ƴaƴan manya, dan shop ɗin bana yara bane, na manyan mata ne.
Shi kuwa Tga abin da kuka sani ne, kallo wannan ma babu wacce ta samu ya ɗaga idanu ya kalleta, dan shi bai ma san suna yi ba, ga fuskarsa tamkar ta shanu, ya wani murtuketa gam, babu alamar ya taɓa sanin menene murmushi ma, sak face ɗin Lion haka yake shi ma, abu ne da kuka rigada kuka sani.
Duk waɗan nan awannan da su Rimsha suka kwashe ana zuba masu zanen flowers na lalle mai bala'in kyau tare da gyaran gashi, duk yana tsaye bai ko motsa ba, kuma sam bai zauna ba, yana tsaye a matsayinsa na cikakken soja mai jini a jika, yana ta kula da su, dan Lion ya jaddada mashi a kan ya kula da su over, shi ne yasa yake ƙoƙarin jaddada hakan.
Sam Rimsha ta mance da cewa Lion baya son lalle, haka ta bari aka zuba mata zanensa ya fito reras, ya yi matukar kyau na wuce misali.
Ita gwaggo a tunaninta gabaɗaya TRIPLETS zasu zo a tare, shiyasa ta tattaro har da su Jehan ɗin dukka dan ayi masu gyaran kai, bata san iya Lion ne kawai yake hanya ba.
Haka suka gama abin da za su yi, suka je shopping suka yi sayayya, Lion yasa Imran ya biya kuɗi ta hanyar yi wa masu shops ɗin transfer, sannan suka nufi gida, sai murna Rimsha take zabawa, baki yaki rufuwa, an zuba mata lalle kam kamar ba gobe.
Sai da suka koma gida ta shiga bedroom ɗin na Noorish ɗin nata dan ta yi wanka ta yi sallar azzahar, a nan ne ta tuna cewa Noorish baya son lalle, nan take hankalinta ya yi mummunar tashi na wuce misali, wani irin tukukin bakin ciki ta ji ya taso mata, kullum tana damunshi a waya akan yazo ta yi kewarsa, ya taso yana zuwa kuma ta je ta yi abin da zai bakanta mashi rai, sam bata ji daɗin hakan ba. Zama ta yi a saman bed ta murji kukanta iya son ranta, sai da ta ji kanta ya fara yi mata ciwo ne ta hakura, ga kan nata ya sha gyara na gasken gaske kuwa, sai wani kyalli curly hair nata yake zubawa, kamar ka sace ta ku gudu, ta yi kyau ne har ta gaji da kyau, dole ma Noorish ya ruɗe idan ya zo ya ganta.
Bayan ta gama murzan kukan ne ta miƙe ta nufi toilet, wanka ta yi tare da fitowa ta shirya, sannan ta yi sallah kafin ta fita zuwa kitchen ta ɗebo abinci, ta dawo cikin bedroom ɗin nasa ta zauna ta fara cin abincin nata, suma su Jehan abincin suke ci a bedroom na gwaggo.
Bayan ta ci ta yi nak, sai ta hau gyara mashi bedroom ɗin babu kama hannun yaro, da ta kammala sai ta rufe ko'ina tare da zuba mashi air freshener irin wanda yafi kauna, ta bulbula son ranta, tana kammalawa ta wuce bedroom ɗin mummynta.
Babu kowa a cikin ɗakin, dan haka sai ta dawo bedroom na gwaggo. A nan ta samesu dukkansu, mummynta da gwaggo suna a zaune a saman bedside drawers dake gefe da gefen bed ɗin, ita kuma Brr Naurat tana zaune a saman bed ɗin, Jehan ta tada kai da cinyar Brr Naurat, ita kuma Akila tana kwance a gefe guda tana aikin latsa waya, sai sakin uban murmushi take yi, da alama ita da Heartbeat nata suke chatting, dan minti minti sai kuga ta turo baki alamar kalmar shagwaɓa ya turo mata, sai magana Brr Naurat take yi mata, amma ina hankalinta na'a kan wayar, sai da mummyn Rimsha ta miƙe ta kwace wayar, sannan ne ta farga ashe ma a cikin mutane take.
Rufe fuska da hannunta ta yi tana dariya kasa kasa. "Akila sarkin soyayya ba". Cewar mummyn Rimsha, ta yi maganar cikin zolaya........ Hmmm Mummyn Rimsha fa bata san cewa Rimshar tattabara ce uwar soyayya ba, dan bata san yanda take birkitawa General of the army's kuma ɗan takarar shugaban kasa a yanzu lissafi ba ne, duk ta susutar da bawan Allah, ya fita waje ya yi wa mutane zarra, idan ya dawo gida kuma ya cigaba da biyewa Rimsha ya zama kamar wani ƙaramin yaro, oh Rimsha duniya ne wlh, mum tana cewa Akila sarkin soyayya, ai ga sarkin soyayya kam nan ta fito daga cikinta.
"Ku bani hankulanku waje guda". Cewar Brr Naurat. Nutsuwa suka yi tare da tattare mata hankulansu, Rimsha dake a tsaye ma Brr ta ce tazo ta zauna, dama magana za'ayi a kanta ai, dan ita ce mijinta yake hanyar dawowa yau, ita za'ayiwa nasiha, su Jehan dai zasu ji nata ne kawai kafin azo yi masu nasu idan mazansu zasu dawo.
Shiru suka nutsu kamar ba su ba, da Brr Naurat da gwaggo ne suka fara yi masu nasiha mai ratsa zuciya ta sanya zuciya yin laushi, sai da suka gaya masu girman Allah, suka tausasa masu zuciya, sannan suka fara gaya masu menene miji ma first, kafin suka gaya masu hakkokin miji da yake a kansu, daga karshe suka ɗaura da zancen biyayya, kada su kuskura su ɗaga muryoyinsu ya fi na mazajensu sauti, yin hakan ya kansa mace ta shiga tsinuwar Mala'ikun Allah ta'ala, kome zai yi masu su daure kada su ɗaga mashi murya, Allah baya barci yana ganin komai da yake faruwa, su kula sosai da mazajensu, su kasance masu sanyasu farinciki na wuce misali, su yi masu duk abin da suke so matuƙar bai saɓawa Allah ba, koda su basu so, to su daure su yi mashi biyayya, ranar gobe kiya zasu samu kaso mai tsoka a wajen Allah, zasu shiga rahmar Ubangiji a lokacin da ubangijin al'arshi ya sauko da rana dai'dai kawunan mutane, to a wannan lokaci Allah zai sanyasu cikin karkashin inuwar al'arshinsa, dan haka su dage sosai, su jure su yi hakuri, duniya ba madawwama bace, lahira ita ce madawwamiya, dan haka su nemi madawwamiyarsu ta yi kyau, kada su biyewa duniya lokaci kaɗan yake a gareta.
Sun sha kuka sosai, barema Rimsha, tafi kowa yin kuka a cikinsu, ita kuwa Jehan hawayenma bai gama barin kusa da idanunta ba, da alama ƙaƙalo kukan ma ta yi (ni ko wai menene zai sanya zuciyar Jehan da Lion yin laushi sosai ne?🤔 Wai duk wannan abin Jehan bata yi laushi ba?🤔 Kukan ma ƙaƙalo shi ta yi dan kada ace bata yi ba😂 kai jama'a Jehan dai har gobe da sauranta, shi dama Lion ba'a sanya shi a lissafi, dan ni na juya na juyo banga abin da zai sa zuciyarsa ta yi laushi ba, dan ko yanzu Rimsha ta yi mashi ba dai'dai ba zai bata a jikinta ne, sai dai daga baya ya yi dana sani, amma zuciyar nan tana nan babu abin da ya ragu a jikinta)
Akila ma ta sha kuka sosai, daga haka har barci ya ɗaukesu.
After some hours.
Bayan sun yi sallar mangariba da issha ne Rimsha ta je wajen mummynta, dan dama mum ɗin ta ce mata ta sameta a ɗakinta. Tana zuwa mum ta zaunar da ita a bakin bed ta hau yi mata tata nasihar, ta ɗaura daga kan nasu Brr Naurat, duk wata kunya ajiyeta a gefe mum ta yi, ta rungumi ƴarta ta koya mata yadda zata zauna da mijinta lafiya, harta abin da yafi sanya namiji farinciki sai da mum ta gaya mata, ta ce ba zata tsaya nuna jin kunya ta cuci ƴaƴanta a banza ba, su je gidan miji basu san yanda zasu kula da mijinsu ba, aure ya zo ya yi ta tangal tangal, gara mata ta ajiye kunya, ta jasu a jiki, ta gaya masu komai dallah dallah, hakan ne kawai zai bata daman samun kwanciyar hankalin kasancewarsu a gidan miji, barema Rimsha da take ƴar yarinya, ga mijin nata ba irin sauran maza bane ba, ai dole sai an koya mata abubuwa dallah dallah, ɗan gara Jehan ma ta ɗan girma.
Haka ta rinƙa yi mata nasiha sosai har sai da gwaggo ta zo ɗakin ta samesu, sai kuka Rimshar take yi sosai, gwaggon ce ta rarrasheta sannan ta ce tazo su tafi bari ta shiryata dan mijin nata ya iso. Wani irin daɗi ta ji Noorish nata ya iso, kamar zata tambayi gwaggon ina yake, sai kuma ta danne ta fasa dan ganin idon mummynta, da gwaggo ce kawai sai ta tambayeta ina yake, amma tun da mum tana nan, sai ta danne bata tambaya ba.
Riko hannunta gwaggon ta yi tare da mikar da ita suka nufi waje suna yi wa mum sai da safe.
Fitowa suka yi daga side na boys quarters ɗin suka nufi cikin gidan. Sosai Rimsha ta yi mamakin ganin tsadaddun sabbin motoci dal dal har guda uku a parking space na gidan, motoci ne da suka amsa sunansu motoci masu numfashi, ko ba'a gaya mata ba, tasan dole su ne suka ɗauko Noorish nata daga airport.
Wucewa suka yi izuwa cikin gida, tana sanya kafarta a palourn kasa kamshin perfume nasa ne ya fara dukan kofofin hancinta, sai ka rantse da Allah yanzu ya wuce a wajen, amma kuma ya jima da wucewa zuwa sama, dan Rimshar tana fita zuwa wajen mummynta, shi kuma yana shigowa, kasancewar tana part na boys quarters ne yasa bata ji diran motocin nasu ba, dan boys quarters ɗin ta baya yake, kuma motocin sabbi ne dal masu matuƙar tsada, kukansu a hankali yake fitowa, shi ne yasa basu ji ba.
Haurawa sama suka yi, kai tsaye bedroom na gwaggo gwaggon ta wuce da ita, shi kuma Lion yana cikin nasa bedroom ɗin, ya yi wanka yana sanye cikin kayan barcinsa tsadaddu masu kyan gaske, launin white color, ya zauna a balcony yana amsa waya nasu Aseef, sai kuka Aseef yake yi mashi a kan ya shammacesu ya tafi, shi dai Areef ya sani tun time da Lion ɗin ya bar gidan, Aseef ɗin suka ɓoyewa, sai yanzu ya sani, shi ne yake cewa shi wlh ba zai yarda ba, to rigimar da suke yi da Lion ɗin kenan.
Wanka gwaggo tasa Rimsha ta yi, bayan ta fito, gwaggon da kanta ta shiryata cikin wata dankareriyar doguwar riga mai matuƙar kyau, da suka fita da Tga ne gwaggon ta saya masu su ukun dukka iri ɗaya, da yake du Jehan mazajensu basu zo ba, sai ta ajiye masu nasu, ita kuma Rimsha suka hau shiryata, sai ta fito cas kamar wata ƴar tsana a cikin kayan, ta haɗu iya haɗuwa, gwaggo bata yi mata make up ba, ta ce su bar mata natural beautynta tafi kyau a haka.
Sai tsiya Akila take yi mata, sai kus, kus suke yi na munafurci, Akila tana gaya mata wasu zantukar a kunne, ita kuwa Jehan tuni ta fice zuwa bedroom nasu dan ta yi waya da Areef nata, ita kuma Akila ta tsaya ganin gulma, sai da aka yi wa Rimsha komai a gaban idanuwanta, gwaggo ta rufawa Rimshar wani haɗaɗɗen kuma tsadadden mayafi wanda ta feshe shi da tsadaddun Dubai perfume, ta rufa mata a kai ya sauko har saman face nata, tamkar za'a kai amarya, sai tsokanarta Akila take yi wai ta zama sabuwar amarya, gwaggo ta mai da ita sabuwar amarya.
A kule ta ce "Aunty Akila dama can ni sabuwar amarya ce, kuma kullum a sabuwa nake, ni ba zan zama tsohuwa ba bare yaya Saif ya auri wata".
Dariya sosai Brr Naurat ta kwashe da shi, Rimsha manya iyayen soyayya, wato dai bazata tsufa ba bare yaya Saif ya kara wani aure. Kuka ta saka masu, saboda Brr Naurat tana yi mata dariya.