Triplets book 4 Complete - Chapter 50
Triplets book 4 Complete Chapter 50: Triplets book 4 Complete Chapter 50. Wani santalelen matashi mai jini a jikka ne zaune a saman wannan dankareriyar…
3,357 words
Wani santalelen matashi mai jini a jikka ne zaune a saman wannan dankareriyar office chair ɗin nan, tsalelen matashi dogo da shi, daga kafafunsa dake sanye da wasu shegun black covers masu matuƙar kyau da tsada har izuwa kyakkywar dark black curly hairnsa dake kwance mashi har bayan wuya dukka tsadaddun kaya ne da suka amsa sunansu tsadaddun, komai na jikinsa kuɗi aka narka ba kaɗan ba, watch ɗin hannunsa kawai ma abin kallo, danƙareriyar diamond watch mai matuƙar ɗaukar idanu saboda kyalli ne, ɗayar hannunsa na sanye da wata ƴar siririyar diamond hand chain, akwai wani tsadadden diamond ring a ɗaya daga cikin kyawawan fararen ƴatsun hannunsa, baka iya ganin face nasa, saboda ya duƙar da kai ya kurawa wata hoto dake jikin jarida idanu. Black suit ce a jikinsa, ta yi matuƙar yi mashi tsantsar kyau, duba da yanayin fatar jikinsa kamar madara, hakan tasa ya yi wa suit ɗin matuƙar kyau sosai. Gashin kansa sai wani kyalli yake yi tamkar gashin kan Lion namu na Meesha.
Shiru ya zubawa wata hoto idanu yana kallo, idanuwansa na sanye da black glass mai matuƙar kyau wadda ta kara fito mashi da hasken face nasa, soft skin nasa tamkar madara, a kwance luwai luwai, ga wasu chains na zallar zinari masu bala'in kyau a wuyarsa wadda suka sauko mashi har saman chest nasa, fuskarsa a ɗaure tamau kamar hadari, alamar babu wasa a tattare da shi, tamkar yadda face ɗin Lion take a ɗaure kullum, haka nasa face ɗin ma take. Ba komai ya kurawa idanu ba face hoton Lion, bai taɓa sanin Lion ba sai a yanzu da Lion ɗin ya fito takarar neman shugaban kasa, a nan ne ya ga hotunansa a kafafen yaɗa labarai suna yawo, a news sai maganarsa suke yi tare da ɗaura ainahin hotonansa, ga postoci da aka yi mashi, kun san a da can baya ba kowa ya san ainahin face nasa ba, saboda da face mask yake yawo, so a yanzu babu face mask ake buga postocin siyasar tasa, ta hakan wannan matashi ya samu hotonsa na ainahi, abin ya yi matuƙar girgiza shi time da ya fara ɗaura idanunsa a kan hoton Lion ɗin, saboda babu wata banbanci dake a tsakanin face nasa tsawonsa komai nasa da ta Lion ɗin, time da abokinsa ya turo mashi hoton, lokacin da ya buɗe sakon abokin nasa, yana ɗaura idanunsa a kan hoton bai san time da ya miƙe tsaye a razane ba, da farko ya ɗauka hotonsa ne, sai daga baya da ya kalli na jikin hoton da kyau, sai ya lura Lion ya fishi murɗewar jiki, sannan ya fishi cika, kuma a jaridar an rubuta cewa ɗan takarar shugaban kasa na ƙasar America da ya lashe zaɓen primary election a halin yanzu, hakan tasa ya fahimci ba shi ne a jikin hoton ba, kama ce kawai da ta yi over, tun da gari ya waye ya zo office nasa ya fara aiki, tun da abokinsa ya turo mashi jaridar nan ya dakata da yin aikin komai, ya dakatar da kowa da samun damar ganinsa, ya zauna ya zubawa wannan hoto ido yana mamaki tare da al'ajabin irin wannan muguwar kamanni da take a tsakaninsu.
Abin ya yi matuƙar girgiza shi, ya aka suka yi irin wannan kama tamkar mutun guda haka? Abin ya yi mugu mugun tashin kansa ba kaɗan ba.
Tsadaddiyar wayarsa da take a gefensa ne ta fara ringing, har ta katse bai ɗaga ba, kira ta biyu ta sake shigowa, ita ma har ta katse bai ɗaga ba, sai a na uku ne ya ɗauki kiran. Kara wayar ya yi a kunnensa ba tare da ya ce uppan ba, sai a lokacin ne kuma ya ɗago kansa tare da ajiye jaridar hannun nasa mai ɗauke da hoton Lion, sannan ya koma ya jingina da jikin chair ɗin yana sauraron abin da ake faɗa mashi a cikin wayar. Haƙiƙa babu wata banbanci dake a tsakanin fuskarsa da ta Lion, duk da idanuwansa suna a cikin black glass, baka iya gane wani irin kalace da su, amma hakan ba zai hana ka ga tsantsar kamanninsa da Lion ba.
Ya ɗan jima yana sauraron abin da ake faɗa ta cikin wayar ba tare da ya amsa ba, sai ya ɗago hannu yana duba time a jikin dankareriyar watch dake a hannunsa. Calmly ya furta "Am coming". Da zazzaƙar muryarsa mai muguwar kama da ta Lion, Iya abin da ya furta kenan tare da katse kiran. Nisawa ya yi tare da ɗan ɗago da kansa da nufin ya miƙe tsaye. Turo kofar office ɗin Secretariyarsa ta yi tare da shigowa tana faɗin "Sir ARVIN you have some visitors from West Building, Zhongnanhai".
Shiru ya yi mata bai amsa ba, ganin haka yasa ta juya ta fita, da alama ta yi mashi farinsani, hakan yasa ta san fassarar shirunsa.
Wanene ARVIN. ARVIN dai shi ne Defence minister na kasar China bakiɗaya, wato ministar tsaro ta kasa, duk wani mai kaki a karkashinsa yake, idan ana maganar duk wani mai kaki kuma mai muƙami, to fa gaɓaɗaya ake magana, duk wasu jiga jigan Generals na sojoji, ƴan'sanda da dai duk wasu masu muƙami, harta General of the army's a karkashinsa yake, shi ne Minister tsaro gabaɗaya, mutun ne mai matuƙar girman kai, jiji da kai, isa, izza da kuma taƙama, mahaifinsa shi ne Senate president na ƙasar, yana da kanne biyu, namiji ɗaya sai mace ɗaya, namijin yana da shekaru 27 a halin yanzu, ita kuma macen tana da 13 to 14 years old, mutun ne miskili, ga kuma ɗan banzan farinjini kamar ba gobe, jama'a kowa son shi yake yi, yana tare da mahaifinsa da kuma mahaifiyarsa, bashi da aure, ko budurwa bashi da ita, saboda shi gani yake yi ɓata lokaci ne ma ya tsaya sauraton mata, haka zalika kanin nasa ma bashi da mata. Wannan shi ne ɗan takaitaccen tarihin Sir ARVIN.
Miƙewa ya yi tsaye, dogo da shi tamkar Lion ne yake tsaye a wajen. Hannu ya kai ya rufe laptop dake a gabansa, kafin ya ɗauki tsadaddun wayoyinsa har biyu ya nufi waje cikin takun nuna isa, tsantsar lafiya da kuma izza.
Yana fitowa gabaɗaya kananan ma'aikatan dake wajen suka fara duƙawa suna yi mashi mubaya'a, kun san halin Chinawa da iya duƙawa kasa su gaishe da mutum, ko sannu zasu cewa mutun sai sun ɗan dukar da kansu kasa, so yana fitowa haka suka fara duka mashi cikin girma da girmamawa, ko kaɗan bai ɗago idanu ya kalli ko mutun ɗaya ba, dama na gaya maku yana da bala'in girman kai.
Sai da ya fito harabar wajen ne wasu jiga jigan bodyguards masu ji da lafiya da karfi, su goma sha biyu ciff suka take mashi baya har zuwa wajen wani haɗaɗɗen parking space dake a wajen, gabakiɗaya bodyguards ɗin Chinawa ne, jajir da su kamar tsada, ga su da faɗi, basu da tsawo sosai, kamar yanda kuka sani ne, bodyguards ɗin suna sanye cikin black suit kamar yanda kowasu bodyguards suke sanyawa.
A hanzarce wani ƙosasshe kuma lafiyayyen bodyguard ya kai hannu ya buɗe mashi wata dankareriyar mota kirar *ROLLS-ROYCE* Fara tas da ita tana wani ɗaukar ido, sai ka rantse da Allah yanzu aka fito da ita daga laida, wasu luntsuma luntsumar sofas ne a cikin wannan mota masu matuƙar laushi, kun san idan aka ce luntsuma luntsuma, ana nufin masu lumewa da mutun saboda laushi da tsantsar kyau, wani irin azababben daddaɗar kamshin car perfume ne yake tashi daga cikinta, ga wani irin sanyi A.c dake tasowa, kai tsayawa zayyana maku haɗuwar wannan mota ma ɓata lokaci ne, dan ya wuce misali.
Cikin nutsuwa tamkar Lion haka ya shiga cikin motar ya zauna, zuciyarsa cike taf da tunanin wanene Lion? Meyasa suke muguwar kama haka? Why Lion ya yi kama ba da iya shi kawai ba, har da kanwarsa Pinky? Shi Lion da yake Americans, shi kuma da yake Chinese me haɗinsu? Ga ita ma Pinky da take nan. Abin ya dame shi sosai, haka bodyguards nasa suka shiga ciki sauran tsala tsalan motocinsa guda shidda dake a wajen.
A jere kai guda motocin suka tashi gwanin birgewa, kai daga gani kasan babba ne zai bar wajen, dan motocin nasu ma kawai abin kallo ne, a haka suka nufi tampatsetsen gate na ma'aikatar. Tun kafin su iso jiga jigan masu gadi sun wangale masu gate ɗin, da gudun gaske suka danna hancin motocin waje, motar ƴan'sanda mai lode da jam'ai har guda uku ne suka rufa masu baya tare da sakin jiniya tamkar filin yaki zasu tafi.
Kai tsaye..............
❤️🔥❤️🔥❤️🔥❤️🔥❤️🔥❤️🔥🔥❤️🔥❤️🔥❤️🔥❤️🔥❤️🔥❤️🔥❤️🔥❤️❤️🔥
*KINDADE KINA NEMAN ABUN DA ZAI SANYAKI QIBA,QIBA MEKYAU KIYI DIMIMI DUK INDA KIKA SHIGA BABU RAINI KINYI TA SIYA KINA ASARAR KUDINKI🤔 ALBISHIRINKI NAZO MIKI DA ABUN DA ZAKISHA BA TARE DA KINYI ASARAR KIDINKI BA 💃 Yana da matiƙar kyau sosai ko'ina naki zai chiko ki xama abar sha'awa duk mai buƙata ta nemeni ta wannan number 09067614054, kada ki bari ayi babu ke, kayanmu tested and trusted ne, guarantee ne*.
*KINDADE KINA NEMAN ABUNDA ZAI SANYA KISAMU XAMAN LFY TARE DA KWANCHIYAR HANKALI? TO BABYN HABIBI KIXO UMMU AFFAN TAXO MIKI DA SHAHARARRUN KUMA INGANTATTUN MAGUNGUNAN MATA, KAMA TUNDAGA KAN HUMRA, TURAREN WUTA, INFECTION KILLER, COLACCA, SAI KAYAN GYARA PAGE. KACA KACA. YALLAGWADA. JIGIDA. RUWA RUWA. BANI BANI. WOMEN JELL BATA BATA. DAFIN KAXA. TANTABARA. XABUWA. CICCIƁI. AND EXCLUSIVE, XUMA TASTED AND TRUSTED INA FARIN CHIKIN SANAR DA KU MUN FARA RAMADAN PROMO GAME BUQATA XA A IYA TUNTUBA NA TA WANNAN NUMBER 09067614054 JIGAWA STATE MUNA AIKAWA KO'INA CIKIN AMINCI DA YARDAR ALLAH, BABYN HABIBI KARKIMANTA DA KAYANMU FIRST CLASS NE, DAGA KANSA AN RUFE KOFA, YANA DA INGANCI NA WUCE TUNANINKI*.
❤️🔥❤️🔥❤️🔥❤️🔥❤️🔥❤️🔥❤️🔥❤️🔥❤️🔥❤️🔥❤️🔥❤️🔥❤️🔥❤️🔥❤️🔥
https://whatsapp.com/channel/0029VaMOfZZI7BeKXPU9gK2S
❤️🔥❤️🔥❤️🔥❤️🔥❤️🔥❤️🔥❤️🔥❤️🔥❤️🔥❤️🔥❤️🔥❤️🔥❤️🔥❤️🔥❤️🔥
TSARAWA DA RUBUTAWA......✍️
❤️FATEEMA ZAHRA MUSA (💫PRINCESS TEEMA💋)
*Domin samun damar karanta littafin nan daga farko har karshe zaki iya nemana ta wannan number 08161390581*
Date: 14/5/2024
E31
Kai tsaye Zhongguncu motocin suka nufa, katafaren unguwa ce wadda ta ji manya manyan tsara tsaran gine gine na zamani har ta ƙoshi, ko'ina ka ɗaga idanu ka kallah sai ka ji baka son kawar da kanka daga wannan wajen, tsaruwa iya tsurwa, haɗuwa iya haɗuwa, shunfuɗaɗɗiyar titin da ta keta cikin unguwar ma kawai ya isa mutun ya saki baki daga safe har yamma yana kalle kalle kayan alatun da aka shunfuɗawa wannan titi, abubuwa ne kala kala, wajen tafiyar mutun a kafa daban, wajen tafiyar keke daban, wajen tafiyar mota daban, haka titin nan yake, gwanin birgewa, baki ma ya yi kaɗan ya zayyano yadda haɗuwar titin take, sai dai ku kawata a ranku.
Tun da motocin Sir Arvin suka hau saman wannan titi babu wata mota da ta gifta har suka nufi wata dankareriyar gini na alfarma, wadda ake yi wa yaƙabi na karshen burin ɗan adam, kunsan ɗan adam da shegen buri over, to duk wani burinka idan ka sanya kafarka a cikin irin wannan gida fa shikenan angama, sai ka ji tamkar bama a duniya kake ba, bene ne hawa biyar, gini ne na tiles da glass, abin dai ba'a magana, gate ɗin gidan ma kawai abin kallo ne.
Tun kafin jerin gwanon motocin su iso an wangale masu tampatsetsen gate ɗin, da alama gate ɗin da na'ura take amfani, dan babu gateman a wajen sam.
Kai tsaye suka danna hancin motocin nasu cikin gidan a jere, wani tampatsetsen parking space suka nufa, ya haɗu ya gaji da haɗuwa, wasu shegun tsadaddun motoci ne maƙare a parking space ɗin, tamkar companyn kera motoci suka shiga, kowani mota ka ɗaga idanu ka kallah sai ka sake kallah, saboda tsabar kyau.
A jere waje guda motocin nasu suka dakata, tamkar abin haɗin baki haka suka kashe motocin gwanin birgewa, tare da fitowa lokaci guda, da alama already sun saba yin hakan ne.
Wannan bodyguard na ɗazun da ya buɗewa Sir Arvin kofar mota a office, shi ne nan ya sake zuwa ya buɗe mashi a yanzu ma. Yana buɗe mashi ya fito da sauri ya nufi tsadaddiya kuma haɗaɗiyar elevator su, cikin sauri yake tafiya tamkar wanda ya ƙosa da su iso gidan, kamar wani abin yana jiransa a ciki.
Haƙiƙa gidansu Sir Arvin ya wuce baki ya zayyano kyansa, kun fa san yadda ginin Chinawa yake, ba wasa ba! Sun iya tsara gini sosai.
A harabar gidan waɗan nan jiga jigan bodyguards ɗin nasa suka dakata cirko cirko kamar masu jiran umurnin su aiwatar da wani abin, su kuma ƴan'sandan nan sun wuce wajen wasu tsadaddun kujeru dake wajen wani tsalelen pili da aka kewaye da glass dan hutawa.
Hawa na biyu Sir Arvin ya wuce kai tsaye.
Wani irin haɗaɗɗen parlour ne mai girma wadda ya haɗiye luntsuma luntsuman sofas set har kala uku, komai na more rayuwa wadda ɗan adam mai bala'in buri zai buƙata da akwai a cikin wannan gida, dukiya ta yi masu mubaya'a ainun, wani irin azababben daddaɗar kamshi air freshener ne mai bala'in daɗi ne yake tashi a cikin parlourn, tsayawa zayyana maku kyan parlour ma ba zai yiwu ba, dan duk iya misalin mai misali ba zai iya misilta haɗuwar wannan parlour ba.
Yana sanya kafarsa a cikin parlourn wata kyakkywar yarinya mai matukar kyan gaske ta miƙe daga saman sofar da gudu ta nufo shi, jikinta na sanye da gown white color, iya cinyoyinta gown ɗin ya tsaya, ga gashin kanta tamkar na Arvin ɗin, babu wata banbanci dake a tsakanin fuskarsa da ta wannan yarinya, harta launin kwayar idanunsu da ya kasance sky blue shi ma iri ɗaya ne, sak dai shi ɗin take, tana rike da ƙatuwar chocolate a hannunta, sha take yi ta ji kararrawar kofar parlourn ta yi kara, alamar za'a shigo kenan, dama haka kofar take, kun fa san China karshe ce wajen kera abubuwa, to kofar shiga parlournsu ma idan aka taɓa za'a shigo sai ya sanar da waɗan da suke ciki cewa za'a shigo, duk da cewa kofar tana amfani ne da card or fingerprint, amma da zarar an taɓata sai ta sanar da na ciki ana shigowa.
Da gudu yarinyar ta tafi ta faɗa jikinsa tana yi mashi oyoyo. Tamkar ƴar baby haka ya ɗagata sama yana kallon face nata, sai sakin uban murmushi take yi baki duk chocolate.
"Pinky where's mum?". Ya faɗa can kasa kasa.
"She's inside her bedroom". Bai sake ce mata ko uppan ba ya wuce da ita zuwa wani katafaren haɗaɗen stair case, wanda yake amfani da remote, sai ka danna remote zai fito, idan ka hau zai koma ya naɗe kansa ya haɗe da p.o.p tamkar babu shi, ba zaka taɓa cewa da akwai stair case a wajen ba.
Yana hayewa wata katafaren parlour ya sake shiga, parlourn sak na kasar nan, sai dai shi wannan komai na cikinsa light ash ne na kasan kuma golden brown.
Cikin bed nasa ya wuce da ita a saman kafaɗarsa. Ya ilahi ya lillahi, wannan bedroom shi ake kira da karshen haɗuwa, katafaren king bed nasa ma kawai abin kallo ne, bare kuma sauran kayan more rayuwa da suke a ciki, Chinese carpet dake gaban bed ɗin tamkar audiga haka yake, duk in ka taka sai kafarka ta lume, wajen mirrornsa kawai ya ci rabin bango guda na ɗakin, dressing room nasa da glass aka yi ta tamkar na Lion, bedside drawers ɗinsa kusan irin na Lion, haka zalika lamp dake a saman bedside drawers ɗin suma haka, sai dai nasa milk color ne na Lion white, wani shegen bed sheet ne wanda ya amsa sunansa bed sheet na alfarma, shi ne shumfuɗe a saman bed ɗin, ga wasu kyawawan pillow masu matukar kyau da ɗaukar hankali.
Saman bed ɗin ya ɗaura Pinky tare da zama a gefenta ya fara cire tsadaddun covers ɗin da suke a ƙafarsa. Bayan ya kammala ya miƙe ya nufi toilet ya barta a wajen. Karisa hayewa saman bed ɗin ta yi tare da jawo pillow ta rungume, sannan ta cigaba da shan chocolate ɗinta.
After some minutes ya fito cikin wasu tsadaddun pajamas launin blue color, sai tashin wani fitinannen kamshi yake yi, har lokacin Pinky na kwance mashi a saman bed.
"Let's go and eat Pinky". Ya kai karshen maganar tare da nufar hanyar fita bayan ya sanya bedroom slippers a kyawawan kafafunsa, har lokacin babu alamar dariya a tattare da shi.
Da sauri ta diro kasa daga saman bed ɗin, da gudu ta tafi ta rungume shi ta baya, duƙa mata ya yi, a hanzarce ta haye saman bayan nasa, ya fita tsawo sosai ne yasa bata iya hayewa saman bayan nasa ba sai da ya duƙa mata, goyata ya yi tare da miƙewa tsaye suka nufi waje.
Kai tsaye dining room ya nufa, rayuwarsu sak kusan irin na gidansu Lion. Yana zuwa ya sauketa, dining room ɗin nasu ma duniya ne, kusan kamar na gidansu Lion, sai dai banbancin colors kawai, saman katafaren dining table ɗin shaƙe yake da abinci kala kala, kun san su suma basu girki kala ɗaya, sai su yi wajen kala goma ko sama da haka lokaci guda, ga kuma fruits a jere makil a wajen.
Wasu bodyguards guda uku ne suke tsaitsaye a wajen dining table ɗin, jiran umarni kawai suke yi su fara zuba abinci, sanye suke cikin suit bakake, fuskokinsu a ɗaure tamau alamar aikin gabansu kawai suke yi, babu wasa a tattare da su.
Saman haɗaɗiyar table chair ɗaya ya ɗaura Pinky kafin shi ma ya zauna a nasa chair ɗin kusa da ita. Ko da ya zauna sai da ya ɗauki 10mins kafin ya bawa bodyguards ɗin umarnin da su zuba mashi kalar abincin da yake buƙata, har a lokacin kuma tunanin Lion ne fal a cike a cikin ransa, yarasa dalilin da ya sanya ya ji yana matuƙar kaunar Lion ɗin, da kallon farko ya ji tamkar ya ɗaga jirgi zuwa U.s suka ga juna ido da ido, dan ya kara tabbatar da wannan kamannin nasu shin da gaske ne ko dai a hoto ne? Haƙiƙa zuciyarsa ta kamu da kaunar Lion, burinsa kawai ya je wajensa koma ta halin yaya. BABBAR MAGANA TAB!!!!.
Abincin kawai yake ci, amma hankalinsa kwata kwata baya wajen, yana kan tunanin Lion, barema da ya dawo gida ya kalli Pinky, sai abin ya kara tsaya mashi a rai sosai, dan sai ya kalleta tamkar Lion ɗin ya kallah.
Wani kyakkyawan matashi ne ya shigo dining room ɗin, shi ma sanye yake da pajama launin black color, sai tashin kamshi yake yi, yana kama da su, sai dai ba sosai ba, kuma shi launin idanuwansa brawn color ne.
Saman table chair ɗin ya zauna yana faɗin "Good afternoon bro". Da kallo sir Arvin ya bishi ba tare da ya amsa ba, Pinky ce ta ce "Good afternoon brother Handsome".
Da yake yana a kusa da ita sai ya kai hannu ya shafa kanta kafin ya bawa bodyguards ɗin umarnin da su zuba mashi abinci.
"Where's mum?". Handsome ya tambaya yana ɗaura wayarsa a saman table ɗin ta gefe.
"Mum she's inside her bedroom". Pinky ta bashi amsa. Abinci suka cigaba da ci cikin nutsuwa da kula, babu wanda ya sake yin magana daga cikinsu.
After some minutes wata ƴar caras cas ɗin mata ta shigo cikin room ɗin, tana sanye da doguwar riga mara nauyi mai matukar kyau da tsada, launin pink color, ƴar kyakkywa da ita, ga kyan jiki, da ganinta kasan ƴar China ce, sam bata yi kama da Arvin ɗin ba, ta dai yi kama kaɗan da Handsome.
Handsome da Pinky har suna haɗa baki wajen cewa "Welcome mummy".
Idanuwanta na'a a kan Arvin da yake ta faman tura abinci tamkar wadda aka yi wa dole, sai faman yamutse fuska yake yi.
"Son what's going on? What's wrong with you?". Cewar mum ɗin, ta yi maganar tare da zama a saman chair dake kusa da Handsome.
"Nothing" ya amsa mata da shi tare da miƙewa yana mai ɗaukar tissue daga wajen ajiyewa, hannunsa da ɗan ƙaramin kyakkywar bakinsa ya goge, sannan ya nufi barin wajen.
Binshi da kallo ta yi har sai da ya fice, sannan ne ta dawo da kallonta a kansu Handsome tana faɗin "What's going on here Handsome?".
Girgiza kai ya yi yana faɗin "Mum i don't know anything, yanzu na dawo nima".