Kenza eBookz

Triplets book 4 Complete - Chapter 57

Triplets book 4 Complete - Chapter 57

Triplets book 4 Complete Chapter 57: Triplets book 4 Complete Chapter 57. A hankali ya fito da tongue nasa ya fara aikin lasar hawayen nata. Rungumarsa…

3,308 words

A hankali ya fito da tongue nasa ya fara aikin lasar hawayen nata. Rungumarsa sosai ta yi a jikinta tare da cusa kanta a cikin kirjinsa tana sakar mashi kuka mai sauti.

Sosai ya rikota tare da fara rarrashinta, da iya gaskiyarta yau take kuka, babu makirci ko kuma tsiya, iya gaskiya yau take yin kukan, wani irin azababben sonsa ne ya ninkun mata a cikin zuciyarta.

Rarrashinta ya rinƙa yi har sai da ya samu ta yi shiru, sannan ne ya jawo plate na abincin suka cigaba da ci a tare. Sai da suka ƙoshi tab, sannan ta tattare komai ta fitar waje, da kallon so da kauna ya bita har ta fita ta dawo.

A kusa da shi ta zo ta zauna, cikin nutsuwa ta ce mashi "Yah Areef am coming, zan je bedroom namu ne". Murmushi kaɗan ya sakar mata kafin ya gyaɗa mata kai alamar to, mikewa ta yi ta nufi waje, sai dai kafin ta fita sai da ta kashe wutar ɗakin, bai damu ba ya miƙe ya haye saman bed ya kwanta yana jiranta.

30 mins a tsakani, yana kwance shiru cikin duhu, sai jinta ya yi a saman jikinsa tana tashin wani fitinannen kamshi mai sanyayya zuciya. Wani irin nauyayyar ajiyar zuciya ya sauke kafin ya kai hannu ya rungumota sosai a jikin nasa, kasa kasa ya furta "Dama na ce your special my baby".

Face nata ta matso da shi dab da tasa, kasa kasa kamar mai raɗa ta fara magana "Like the way you're special ba? Kai makura ne my husband, I really love you more than your expectations".

Tsabar daɗi wani irin juyawa da ita ya yi, ya zamana ya yi mata rumfa da faffaɗar kirjinsa, lips nata ya fara tsotsa cikin salo, cike da kwarin gwiwa ta fara taya shi ita ɗin ma. Haka suka raba dare suna aiki ɗaya, sai wuraren karfe 2, sannan ya rabu da ita, ya je ya yi wanka, ya fito ya fara sallar dare, ita kuma duk ya gama kashe mata jiki da wasanninsa, ya wahalar da ita son ransa, hakan yasa yana kyaleta ta jawo bargo ta shige, ba jimawa barci ya yi awon gaba da ita. Ba shi ya kwanta ba sai wuraren karfi biyar da ya yi sallar asuba, sannan ne ya ɗan kwanta dan ya ɗan yi barcin awa ɗaya kafin su wuce gidan Hjyr daɗi.

Da misalin karfe 6 suka shirya shi da ita, ita ta koma bedroom nasu ta shirya a can, shi kuma ya shirya a nasa, bayan sun kammala shiri dukkansu suna fitowa suka haɗu da juna a parlourn sama.

Cool murmushi ta sakar mashi tana sunkuyar da kai kasa, abubuwan da suka faru daren jiya na sambatun da ya rinƙa yi mata ne ya dawo mata cikin ƙwaƙwalwarta, duk sai ta ji kunyarsa ya kamata, ga shi ita ma tai ta yi mashi kuka a kan ya bari ba zata iya jurewa ba.

Tsayuwa suka yi shiru a tsakiyar parlourn, ya tsareta da idanu babu ko kyaftawa, ita kuma ta sunkuyar da kanta kasa tana ɗan murmushi. From head to toe yake kare mata kallo, atamfar Rimsha ce ɗinki riga da sket a jikinta, kasancewar kayan Rimsha ce, sai kayan suka kamata sosai, duk wasu shape nata yana bayyana ne, a Duniya Areef yana tsananin son yaga ta sanya atamfa, kyau yake yi mashi sosai, yana son mace ta yi dressing na Hausa Fulani, hakan yasa idan ta sanya zai ɓata lokaci mai tsawo yana kallonta.

Jin bai ce komai ba kamar babu shi a wajen ne yasa ta ɗan ɗago idanuwanta dan ta saci kallonsa, yana a cikin dressing nasu kamar kullum, wato shigar kananar kaya, ya ɗaure gashin kansa a baya.

Tana ɗago idanuwa suka yi 4 eyes da shi, da sauri ta yi kasa da kanta tana mai kara faɗaɗa murmushin dake a saman face nata. A hankali ya tako kafafunsa ya matso kusa da ita, kafin ta ɗago ta kalle shi ya jawota jikinsa.

A tare suka sauke nauyayyar ajiyar zuciya, haɓarta ya ɗago suna fuskantar juna, ɗan bakinsa ya kai saman tata, ya shanye mata lips balm data sanyawa lips nata dikka, sannan ya saketa yana wurga mata kallon waye ya ce ta sanya lips balm ɗin?.

Juya fararen idanuwanta ta yi tare da kwace hannunta ta wuce gaba bata ce mashi komai ba, da kallo ya bita har sai da ta shige bedroom na gwaggo tukun nan ya bi bayanta.

Gwaggo na zaune a saman bed suna hira da Aafia da kuma Rimsha, magana suke yi a kan zasu je wajen gyaran jiki kafin gobe su wuce U.s, Rimsha ta ce tana son ayi mata kunshin flowers masu kyau, daga hannunta har wuyarta, da alama da gangan ta buƙaci yin haka. (Rimsha anya kuwa?🤔 Na dai yi shiru babu ruwana, amma dai kada a mance our Lion baya son ƙunshi🥲🧐)

Saman bedside drawer ya zauna, ita kuma Jehan gefen bed ta haye ta zauna. Cikin girmamawa ya ɗagawa gwaggo gaisuwa.

Wani irin tsananin farinciki gwaggon ta ji na ganinsu a tare da ta yi, wani sanyi ta ji zuciyarta yana yi mata, hakan yasa ta amsa gaisuwar tasa tana farinciki, sannan ta ɗaura da tambayarsa ko ya yi magana da Lion? Dan tana ta kiran numbersa a kashe.

A takaice ya amsa mata da cewa kafin Lion ɗin ya baro kasar China ya yi mashi massage a kan jirginsu zai ɗaga zuwa U.s, so wata kila basu sauka bane yasa numbersa a kashe, amma dai babu damuwar komai ta kwantar da hankalinta.

Shiru ta ɗan yi kafin ta ce "Ka yi magana da Auta na ne?". Ɗan kawar da kansa ya yi yana faɗin "Ai idan kina son yin magana da autanki sai kin nemo Heartbeat ta baki wayarta, idan ba haka ba ko kin kira shi ba zaki same shi ba! Wayarsa bata zaman banza, kullum a kan call yake, kawai ki nemo Heartbeat ta haɗaku".

Murmushi ta yi tana faɗin "A'a in dai yana lafiya kyale su suyi ta yi, ba ma sai kun nemo mani Akila ba, barshi ya ji daɗinsa abinsa". Ta kai karshen maganar tare da shafa kan Jehan dake zaune tana ta faman satar kallon mijin nata, tamkar wani ya ce zai kwace mata shi.

Miƙewa ya yi tare da miƙawa Jehan ɗin hannunsa ɗaya a kan ta kama ta miƙe yana faɗin "Momma bari mu je, take good care of yourself, zamu dawo anjima".

Miƙa mashi hannu Jehan ɗin ta yi, rikota ya yi tare da jawota jikinsa, ko kunyar gwaggon basu ji ba a haka suka fice gwaggon tana yi masu Allah ya kiyaye su dawo lafiya. Da harara Rimsha ta bisu kamar su ne suka yi mata laifi, ita kuwa Aafia miƙewa ta yi tare da cewa da gwaggon tana zuwa.

Waje ta fito, ba komai ne ya fito da ita waje ba kuma face ta duba ko zata ci karo da Tga, dan da tunaninsa ta kwana, ya tsaya mata a rai, dama shi ne first love ɗinta kafin Dr Nawid.

Garden ta nufa, a hankali ta lallaɓa ta shiga, tamkar wani zata leƙa. Babu kowa a ciki, zama a saman sofa ta yi tana tunanin rayuwa.

30 mins a tsakani tana zaune tana tunani, kamar daga sama ta ji an taɓata. A hanzarce ta ɗago kai, daga shi sai pajama launin milk color a jikinsa, fuskar nan dai kamar kullum, a ɗaure kamar hadari, sai tashin daddaɗar kamshi perfume yake yi.

Ganinsa yasa ta miƙe tsaye da sauri, cike da tsantsar tsoronsa ta raɓa gefensa zata wuce, tana tsananin sonsa, kuma tana tsoronsa, dan dama da face ɗin Lion dana Tga da kuma Mark idan kaci karo dasu dole ka ji tsoronsu, saboda babu alamar wasa ko kaɗan a tattare da su, yanzun nan zaka nemi nutsuwarka ka rasa! Saboda kwarjini.

Hannunta ya riko tare da juyowa gareta da kyau "Where are you going?". Ya faɗa a sanyaye.

Girgiza mashi kai cikin tsoro ta fara yi, ta kasa iya buɗe baki ta yi magana. Binta da kallo ya fara yi from head to toe, wani irin yanayi ya tsinci kansa a ciki. Sun jima a haka, sai ƙoƙarin kwatar hannunta take yi, amma ta kasa, daga karshe ma jawota jikinsa mai gabaɗaya ya yi. Fargaba da faɗuwar gaba tare da tsorata yasa numfashinta ya ɗauke diff ta sume mashi a jiki. Sai a lokacin kuma ya dawo cikin hayyacinsa.

Rikota da kyau ya yi tare da ɗaukarta cak zuwa saman sofa ya kwantar da ita, mamaki kansa yake yi a kan meya haɗa shi da wannan yarinya bakar fatar kuma? (Ni kuwa nace mashi ai dama mu bakaken fata muguwar shiga rai gare mu😒 wlh duk in da muka shiga dai sai an zauna da mu, kuma ko ba'a so sai an kaunace mu, kalar baiwar ƴan Nigeria kenan!!😏😌)

Zama ya yi a gefenta yana ta kallonta kawai.

A ɓangaren su Areef kuwa, suna fita Abuja suka nufa, kai tsaye gidan Hjyr daɗi ya nufa, tamkar ya san hanya, sai mamakinsa Jehan take yi, ita da farko a tunaninta ta yi mashi wayo, zata sanya shi yazo gidan ya fitar da su Adiva, bata san cewa already Areef kam ya wuci nan ba, ya wuce tunaninta.

Sam ba da niyar tarwatsa gidan na Hjyr daɗin ya zo ba, su Adiva kawai yazo ɗauka, saboda a binciken da ya yi tarwatsa wannan gida sai an shirya, dan haka sai sun koma U.s, idan suka gama da case ɗin zaɓen nan nasu Lion, daga baya zai shirya yadda za'a ruguje wannan tsinannen bakin kazamin gidan.

Kai tsaye ya danna motarsa har cikin gidan abinsa, a tare suka fito da shi da ita bayan ya yi parking. Jehan bata karasa tsinkewa da mamaki ba sai da ta kalli yasan hanyar shiga har can cikin in da suka yi rayuwa a baya, tafiya yake yi cikin nutsuwa tamkar wanda zai shiga cikin gidansu, ko a jikinsa.

Kai tsaye office na Hjyr daɗin suka nufa, sun kuma yi sa'a tana nan, ta hakimce a saman office chairta, ta ɗaura kafa ɗaya bisa ɗaya, sai wani taunar chewing gum take yi.

Ko sallama bai yi mata ba, kawai ya afka abinsa, dan sallama ta masu daraja ce, ita kuma kazamar kadangariyar bariki ina ta ga wani daraja?. Ita ma Jehan ɗin ciki ta bi shi. Ba tare da ɓata lokaci ba ya ce da ita ina su Adiva?.

Tun daga yanayinsa da ta kallah yasa ta sha jinin jikinta, dan bata ga wajen wasa a tattare da shi ba, sai dai kuma da yake ƴar duniya ce, sai ta nuna ita bata san akan me yake magana ba, ta nuna ita fa sam bata san su waye kuma Adiva ba, hasali ma ita dillaliyace mai fitar da ma'aikata masu yin aikatau izuwa kasashen waje, bayan haka ita bata da wata sana'a.

Kallon Areef ɗin Jehan ta yi tana faɗin "Yah Areef ka bani izini ni zan tuna mata da su waye ne su Adiva". Jinjina mata kai ya yi. "Na baki izini my D.P.O".

Cool murmushi ta sakar mashi kafin ta tako izuwa gaban Hjyr daɗin, kallon sama da kasa ta yi mata kafin ta sanya hannu ta ɗauketa da wani gigitaccen mari. Wani irin ihu Hjyr daɗin ta kurma. "Weeeee hooooooo ni zaki mara Jehan?!".

Kallon Areef Jehan ɗin ta yi ta ce "Yah Areef kaga yanzu ta tuna sunana, saura nasu Adiva, in kara saitata a kan hanya ne?".

Jehan ba dai karfin hali ba, shi mamakin jajircewarta a kan gaskiyarta ma yake yi, ko zaka kashe Jehan sai dai ka kashe ta, amma ba zata taɓa kaucewa gaskiyarta ba, bata da tsoro a zahiri, ga karfin halin, yanzu da wata ce ko kusa ko alama ba zata iya marin mace babba kamar Hjyr daɗin nan ba, koda kuwa ace bata da kirki, wlh ba zata iya marinta ba, duk da tasan akwai mai tsaya mata a wajen, amma Jehan with her full confidence ta ɗauke ta da mari, kuma har tana ikirarin kara mata wani.

A tare su Zinariya da ƴar gold suka shigo cikin office ɗin, jin Hjyr ta yi ihu ne yasa suka shigo da gudu, sun warke daga dukan haukar da Jehan ɗin ta yi masu before ta fita daga gidan.

Ganin su Jehan ɗin yasa suka tsaya cirko cirko suna kare mata kallo, ko kallon in da suke bata yi ba ta ce "Ke Hjyr daɗi kike ko waye? Zaki gaya mana in da su Adiva suke ne ko sai na kara maki wani marin?". Yadda ta yi maganar tamkar wata hamshakiyar hukuma mai doka a hannu, cike da confidence abinta.

Zinariya ce ta ce "Au Jehan kin dawo kenan? To kuwa yau zaki ci ubanki ne, babu mai karbarki shegiya!". Sam basu lura da Areef ɗin a wajen ba, duk hankulansu na'a kan Jehan da Hjyr kawai.

Wani kallon walaƙanci Jehan ɗin ta wurgawa Zinariyar kafin ta ce "Keeeeee ni bance zaki ci ubanki ba sai kece zaki ce zan ci ubana? Kin manta karon mu ta farko kenan? To a da can baya ma kenan, bare kuma yanzu da ke ko da ido kika ganni kin san na wuce dukan kato ko katuwa, sai dai dukan ruwan sama da kuma iyaye wanda suma nasan ba zasu ɗaura hannunsu mai albarka a jikina da nufin duka ba, sai dai su ɗaura hannunsu a jikina dan su samin albarka, ke yanzu kinsan zaren ba kalar yadin bane, ni yanzu bani da lokacinku, kawai ku bani su Adiva nake so, banzaye kazaman banza, sai warin bleaching kuke yi, kamar mutun ya yi amai, shashasshu, karyoyi, kadangarun bariki masu bakin iyaye kawai!!".

Hannu Zinariyar ta cire zata zabga mata mari, cikin hanzari Jehan ɗin ta yi ƙoƙarin kai hannunta ta tare mari, sai dai bata kai ga yin hakan ba Areef dake tsaye a gefe yana binsu da kallo yana mamakin confidence irin ta matar tasa ya rigata, damke hannun Zinariyar ya yi tare da ɗauketa da wani gigitaccen mari da ɗayan hannunsa, kafin kuma ya sauke hannun nasa daga marin da ya yi mata ɗin, tuni numfashinta ya ɗauke diff ta sume, dama kunsan ita Zinariya ƴar a lallaɓace, duk duniya ya cinyeta, ta zama ragwaɓaɓɓiya, maza sun yi bidirinsu a kanta ba iyaka, babu wani abin azo a gani da ya saura a jikinta, sai uban talauci, ga muni da bleaching kamar ya kashesu, shegu sai wari suke yi, sun sayar da duk wasu albarkatun da ni'imar da Allah ya yi wa jikinsu, amma har yau sun kasa yin dukiya, kullum suna cikin talauci, dama in dai ta hanyar saɓon Allah ne ba zaka taɓa yin arziki ba, sai dai ka rasa komai naka, daga karshe ka faɗa cikin musifa, ga tsinuwar Mala'iku ga kuma fushin Ubangiji, bugu da kari ga azabar da Allah zai maka, me ribarka na saɓawa Allah to? Tun farkon duniya har kashenta babu wanda ya taɓa cin riba a saɓon Allah, hakan ma ta isa bawa ishara da kuma aya mai girman gaske, duk wanda ya saɓawa Allah tasa bata kyau, Allah ka iya mana ka mana mai kyau, su dai su Zinariya tasu bata yi kyau ba sam sam.

Ganin ta sume ne yasa ya saki hannun nata ta zube kasa wanwar kamar wata kayan wanki, guntun tsaki ya ja tare da ɗago da kallonsa a kan Hjyr daɗin. Duk sun yi wani tsuru tsuru da su, tsantsar tsoro ya bayyana a saman face nasu. Jiki na rawa Hjyr ta fara ƙoƙarin kiran waya dan mutanenta masu ɗaure mata gindi su kawo mata agaji.

Shiru Areef ɗin ya yi mata, ko a jikinsa, dan yasan call ba zata tafi ba a wannan gida dai, bai shigo ba sai da ya shirya, tsawon watanni huɗu yana bincike a kansu, ya sha aiki kafin ya iya gane komai a kansu, har waɗan da suke ɗaure mata gindi a kasar duk ya sansu, sai dai a yanzu bashi da isasshen lokacin da zai tsaya ya ce zai bisu ɗai ɗai ya kashesu, saboda kurar da suka tayar a U.s ma kawai ta ishesu, ga zaɓe na gabatowa, bugu da kari a yanzu basu da goyan bayan His Excellence, hasalima faɗa suke yi da shi, kuma wasu manya ne daga cikin manyan kasar suke tallafawa Hjyr, so dole sai a gwamnatance za'ayi maganinsu, hakan yasa kawai ya bar batun rushe gidan sai bayan zaɓen U.s, su Adiva ɗin ma abin da yasa ya zo ɗaukarsu shi ne, Jehan tana damuwa sosai a kansu kullum, yasan da hakan, sannan Adiva ƴar uncle ɗin su Jehan ɗin ce, ba zai so wani abin ya sameta ba, ko dan amanar da mahaifinta ya rike wa daddyn Rimshar, shi ne yasa yazo ɗaukarsu kawai.

Sam call yaki tafiya, ganin haka yasa Hjyr ta fara ƙoƙarin gudu ta fita daga cikin office ɗin, ita ma ƴar gold ƙoƙarin guduwa ta fara yi dan ta fita.

Tsawa ya daka masu wanda yasa dole suka dakata, cikin fusata ya ce ko ta gaya mashi a in da su Adiva suke, ko kuma ya kasheta a nan ya kashe banza! Shi su Adiva kawai ya zo ɗauka, babu ruwansa da su.

Bata da zaɓin da ya wuce ta gaya mashi, murya na rawa ta gaya mashi cewa Maryam tana cikin ɗakinsu bata da lafiya, ita kuma Adiva jiya a daddare an fita da ita.

Idan ransa ya yi dubu to ya ɓaci a wannan lokaci, sam bai san time da ya ɗauke Hjyr da wani ɗan iskar matsiyacin mari ba.

Wani irin ihun azaba ta saki, tsabar azaba bata ma san time da bakinta ya furta masu address ɗin in da aka kai Adiva ɗin ba, sake kara mata wani matsiyacin lafiyayyen marin ya yi, sai gata a kasa ta zube kamar kayan wanki, kamar wata mushen doki.

Ita kuwa Jehan tana jin abin da ta ce ta juya a guje ta nufi ɗakin nasu tun da already ta san hanya. Ƴar gold kuwa, tuni idanu ya rai'na fata, jiki sai kerma yake yi, tana jiran ta ji nata saukar marin. Sai dai bai bi ta kanta ba, juyawa ya yi ya bi bayan Jehan ɗin.

A kwance rai a hannun Allah suka isko Maryam, sam bata a cikin hayyacinta, bata iya gane su waye ne ma a kanta, ga dai idanuwanta a buɗe, ta yi wani uban rama tamkar wata figaggiyar kaza mai kwanci, harta gashin kanta sai da ya sauya launi, sai Allah ne kaɗai yasan me wannan tsinanniyar Hjyr ta yi mata, ko da Jehan ta ambaci sunanta ma, sam bata iya amsawa, bata iya magana, kusan irin ciwon da A'isha ta yi suka je suka jefar da ita, to kusan hakance ita ma Maryam ɗin take fama da shi.

A hanzarce Areef ɗin ya ɗauketa cak, dan gani suke tamkar zata mutu kafin ma su fita da ita daga cikin gida, dan idan baku manta ba a tsakanin ginin farko ba gidan da kuma in da su Jehan ɗin suke da akwai tazara mai yawa, hope baku manta yadda tsarin ginin gidan yake ba?.

A hanzarce suka fito da ita, bai sake bi ta kan kowa da yake a gidan ba suka fice. A gidan baya na motarsu suka sanyata, da gudu Jehan ta shiga gidan gaba, shi ma ya shiga mazaunin driver, a haukace ya tashi motar suka bar gidan.

Ita kuma Hjyr daɗi tana baje a kasa kamar mushen doki, sai Allah ne ma kaɗai yasan tana raye ko ta mutu, haka zalika ita ma Zinariya, sun ji hannun maza, ƴar gold kuwa, gabaɗaya a tsorace take, sai mamaki take yi ta yaya aka yi su Areef suka iya shigowa wannan gidan nasu da mutane basu iya ganinsa sai wanda Hjyr ta zaɓa zai shigo mata? Abin ya ɗaure mata kai, basu san cewa a shirye da addu'a sosai Areef ɗin ya zo ba.

Readers Also Read

More by Bilyn Abdull