Triplets book 4 Complete - Chapter 60
Triplets book 4 Complete Chapter 60: Triplets book 4 Complete Chapter 60. Kasa wanwar halintar ta zube, nan take ta rikiɗa ta koma ainahin halittar mutun.…
3,177 words
Kasa wanwar halintar ta zube, nan take ta rikiɗa ta koma ainahin halittar mutun. Cikakken namiji ne kuma babban mutun, ba kowa bane kuma face Abbon Nawid!! Tashin sense, dama kenan nan ne wajen tsafinsa kenan? Meyake yi da ƴan matan idan ya kawosu nan? Ga dai Adiva ko me ya yi mata? Ta mutu ne ma ko tana raye?.
Kawar da kallonsa daga kan Abbon Areef ɗin ya yi, ya mayar da kallon nasa a kan Jehan da ta miƙe tsaye cikin fitar hayyaci, gabaɗaya a birkice take, waje ta nufa da gudu. A hanzarce ya rikota tare da jawota jikinsa yana ambatar sunanta kasa kasa. Baiwar Allah wannan kururuwar da Abbon ya kurma lokacin da yake wannan halintar ne ya birkita mata kwakwalwa.
Jin ya ambaci sunanta yasa ta dawo dai'dai, ƙanƙanme shi ta yi tare da sakar mashi kuka mai tsuna zuciyar mai sauraro, rarrashinta ya fara yi cikin nutsuwa yana mai da numfashi.
Wani irin jijjiga ɗakin da suke ɗin ya fara yi, almace na yana son rugujewa. Saketa ya yi a hanzarce tare da cire mayafin jikinta duk da babu girma ya rufe Adiva ɗin da shi, sannan ya ɗauketa cak ya ce da Jehan ɗin zu je, su yi sauri su fita gidan zai ruguje, domin Abbon ya mutu duk wasu kambun tsafi ya karye, so dole gidan ya ruguje.
A takaice dai da kyar suka iya sha daga cikin wannan gida, saura kaɗan ginin ya ruguje da su, Allah ya taimaka suka fito. A gidan baya na motar ya kwantar da Adiva ɗin, sannan suka shiga gidan gaba, a guje ya figi motar suka ɗauki hanyar da suka bi suka zo. Gidan tsafin Abbo kuwa ya ruguje gabaɗaya da gawarsa a ciki.
A can gida kuwa, gwaggo, Rimsha, Akila da kuma Aafia, sun shirya tsab suka nufi wajen gyaran jiki tare da kunshi haɗe da wankin kai. Tga ne zai kai'su, sai kallon Aafia yake yi, yana tuna sumar da ta yi a jikinsa a garden, bayan farfaɗowarta da yadda ta zaro mashi idanu da ta farfaɗo ta gan shi a gabanta, ta tsorata sosai shi ne ta tashi ta gudu cikin gida, bai hanata ba dan kada ta sake sume mashi.
Yau sun ci kwalliyar Abayas, sun yi matuƙar kyau da su, Rimsha dai sai ɗingisa kafa take yi, tun da suka fito Tga ɗin ya tsare Aafiar da idanu, sun zo zasu shiga cikin motar a gidan baya, ya yi maza ya buɗewa gwaggo karfin motar yana faɗin Aafia ta shiga gaba ba sai sun yi mota biyu ba, su tafi a ɗayar ma ya wadatar.
Cikin hanzari Aafiar ta ce "A'a ni ba zan shiga gaba ba gaskiya, sai dai Akila ko Rimsha su shiga gabar, ni a baya zan zauna".
Why ya tambayeta yana tsareta da idanu.
Kawar da kanta daga kallonsa ta yi tana jin zuciyarta na bugawa da sauri sauri.
"Ni matar mutun ce, dan haka ba zan shiga gabar mota da mijin wata ba, dan Heartbeat bai yarda da hakan ba". Cewar Akila, ta kai karshen maganar tare da wucewa ta shiga gidan baya abinta, tana ta aikin latsa waya.
Guntun tsaki Rimsha ta ja kafin ta ce "Uncle T gaya masu ni haramun ce ma shiga gabar mota idan ba motar yaya Saif ba, kuma ko motarsa ɗin ma sai dai idan shi zai tuƙa ne zan shiga gaba". Cikin masifa ta yi maganar, kamar mai jin haushin wani.
Me gwaggo zata yi idan ba dariya ba? Su Rimsha manya, akwaita da iyayi idan ya gameta, barema yanzu da take jin haushin Lion, sai abin ya shafi kowa, kowa masifa take yi mashi, yanzu shi dai Uncle T uncle nata ne fa, tun da Uncle ɗin Lion ne, amma har da shi yau ya sha masifar, dan hawai tana jin haushin Lion.............😂
"A'a Rimsha ai dama ko da kowa zai shiga gabar motar wani ai banda ke". Cewar Tga ɗin, dan ya san halin Lion sarai, ya san shi da bakar kishi, dan haka shi ko da sunan wasa ma baya fatan Rimsha ta shiga mashi gabar mota, yana da tabbacin yanzu ma ba dan gwaggo ba, da wlh Rimsha ba zata tako ko tsakar gidan nan ba, saboda Lion fa karshe ne a ɗan banzan bakin kishi.
"Aafia to ki shiga gaban mana kawai". Cewar gwaggo, ta yi maganar ita ma tana shiga cikin motar gidan baya kenan.
Ɗan turo baki kaɗan ta yi. "A'a gwaggo ni nafi son baya ne". "Meyasa to?". Gwaggon ta tambaya.
"Saboda ni uncle T tsoro yake bani". "Meyasa nake baki tsoro?". Ta tambaya yana rufe Kofar motar gidan bayan, dan su gwaggon sun kammala shiga, saura ita kaɗai suka bari a waje tsaye kamar mara gaskiya.
Tsareta da ido ya yi yana jiran amsa, ƴan kame kame ta fara yi mashi. "Okey now sai ki shiga kawai tun da baki da wani sauran option". Ya faɗa tare da buɗe mazaunin driver zai shiga.
Turo baki ta yi kamar ta ce ta fasa zuwa, amma saboda tana son ayi mata gyaran jiki da kuma kunshi, sai ta hakura ta shiga, tun da Dr Nawid ya rasu bata sake yin kunshi ba, har ta gama takaba da jimawa, kafin Dr Nawid ya rasu kullum cikin yin kunshi da gyaran jiki take, Allah sarki rayuwa kenan.
Tun da ya fara tukin motar yake aikin kallonta ta cikin mirror motar, jefi jefi ita ma tana satar kallonsa ta gefen idanu, sai dai tafi mayar da hankalinta a saman titi.
Wajen gyaran jikin da suka je last time, nan suka je yauma, har cikin wajen ya bisu, gwaggo tana ganin yadda yake ta aikin kallon Aafia kamar wadda aka bashi gadinta, daga nan ta ce tafiya da Aafia U.s ya kamasu, dan ko basu tafi da ita ba sai Tga ya dawo ya ɗauketa, gara ma kawai su sassautawa bawan Allah kawai su wuce tare da ita, idan sun je komai ya dai'dai ta sai ya musulta kawai a ɗaura masu aure a can, dama bai kamata su bar Aafiar a Nigeria ba, duba da abubuwan da suka rinƙa faruwa da ita a baya, bare kuma yanzu da ta yi aure mijinta ya rasu, ai tana bukatar kulawa ne fiye da can baya, kowa kuma yasan Aunty dai ba zata iya rike Aafia ba, saboda suna ganin bata yi wani karatun kirki ba, so bata waye ba a ganinsu, ita kuma Hjy Hadiza ai bama sai na sake faɗa ba, kun sani tana can tana yawon ta zubar ɗinta, so bazata bi ta kan Aafiar ba, Abbi ba zama yake yi ba, shi ma daddyn Jelly zai koma Kano abinsa, dama a can ya fi wayo, Irfan ya koma school, gidan yanzu babu kowa, dama solution dai kawai gwaggon ta ɗauketa ko kuma su mayar da ita gidan Abba wajen Ammie, tun da ita ma Ammien ba baya ba, ta iya bada tarbiya kuma tana da zafin sosai, ita ce zata iya zama da Aafiar duk da ba ita ta haifeta ba, amma yanzu tafiya da ita U.s ma ai dole ne, dole ayi mata password da komai da komai duk a yau ɗin nan!.
Yau ma dai kamar ranar, kusan wuni zumbur suka yi a wajen gyaran jikin, sai dai fa sun sha gyara, Rimsha dai bata fasa ba, sai dai aka yi mata flowers na zane har wuya abinta, a tafin hannunta ma ta bada kalar zanen da take so ayi mata, ta yi wani irin fitinannen kyau, amma wa ƴan Nigeria ta yi wa kyan, dan su dai TRIPLETS basu son kunshi, ita ma Akila ta biyewa Rimsha aka zana mata har wuya, da yake ita bata san da cewa Aseef baya son ƙunshin ba. (Ni kuwa nace lallai U.s zata kama da wuta, dan duk son da Aseef yake yi mata sai ya goge ƙunshin nan da chemical 😂 yo ni ina ruwana? Ina da Maltina mai sanyi a fridge ai😏)
Wlh kamar ka sace Rimsha saboda tsananin kyau, an kara tsatso mata kyan fatarta da gyara, sun yi wani luwai luwai da su, gwaggo dai bata daddara ba, a karo na biyu ta sake bari an yi wa Rimsha gyara na musamman, ita ma Akilar haka, ita fa gwaggon bata san da cewa kyan da Rimshar ta yi wancan karin ne ya fara ruɗar da Lion ba a wancan ranar ma, ita ta ɗauka sai da ya shigeta ne ya gigice, bata san daga kallonta ma da ya yi bane ya gigice ɗin, sai ta bari aka sake zuba masu gyara na musamman, sun yi kyau kam, Akila ba'a magana, sai tashin wani fitinannen kamshi suke yi, dan anyi masu wankar turare.
Da yake Tga yana zaune a parlourn wajen ne bai bisu can ciki ba, saboda gyaran jikin da za'ayi masu sai a can cikin bedroom, dan sai an shafe dukkan jikinsu da kayan gyara da sauransu, shi ne yasa ya zauna a parlourn saman sofa yana jiransu. Time da suka fito shi da kansa sai da ya miƙe tsaye yana kallonsu, sun zama kamar wasu taurari masu matuƙar hasken gaske, sai dai kuma shi ma baya son ƙunshi, da alama hakan a jininsu yake, ko kuma saboda Lion baya so ne ya dasa masu tsanar abin suma, saboda kada ma su kawo mashi a arear da yake.
Sai kallon Aafia yake yi tamkar wani ya ce zai ɗauketa, ita kuma sai faman ɓoyewa take yi kada su haɗa ido, dan ita tsoron ash eyes nasan nan ma a zahiri take yi, gara a Tv tana iya kallonsa sosai, a zahiri sai idanun suna bata tsoro, tana ganinsu suna wani haske, a haka ma dan bai taɓa zaro mata su ba. (Ni kuma nace dan bata taɓa yin 4 eyes da blue eyes na Lion bane, ai da sai ta kusa fitsari a wando, musamman ma ace da daddare, kuma ya zarosu😂 ya kuke gani?😂)
Gaba ya yi suka rufa mashi baya, gidan baya na motar ya je ya buɗewa gwaggo. Kamar yadda suka zo haka suka shiga a komawar ma, wajen shopping suka nufa. Abubuwa sosai suka saya, komai da suka yi Tga ne yake ta aikin biyan kuɗi, sai da suka kammala komai suka dawo gida.
Suna dawowa kuma suka hau shirin tafiyar da zasu yi gobe, sam ba zama. Su kuwa Areef da Jehan da kyar motar nan tasu ta iya mayar da su wajen asibitin da Maryam take a kwance, suna zuwa suka miƙawa likitocin Adiva ɗin ma, dan a ɗan yi mata dressing su sami ta yadda zasu wuce Kd da ita, daga nan suma ya yi masu password and visa, dan ya ce ciwon nan nasu sai kwararrun likitoci, Allah ma yasa da jet ɗin Lion zasu tafi, dan yana isa U.s ya sake sanyawa aka tashi jet ɗin dan ya zo Nigeria ya ɗaukesu, ba jirgin kasuwa zasu bi ba, saboda tafiya mai gabaɗaya zasu yi, sun sallami Nigeria kenan.
Ko da suka koma asibitin ba laifi, jikin Maryam ɗin da ɗan dama dama, ba kamar yadda suka ɗauko ta ba, sai dai har yanzu ba'a iya gane menene ainahin abin da yake damunta ba.
Karbar Adiva ɗin ma suka yi, duk da basu da tabbacin tana raye ko ta mutu, fitowa Areef da Jehan ɗin suka yi daga cikin hospital ɗin, dan su je su nemi abin da zasu ci, almost 12 na rana yanzu basu karya ba, gara shi Areef zai iya jurewa, ita kam Jehan ba zata iya ba, sai kukar yunwa take yi mashi, ga uban gajiya, duk a galabaice suke.
A takaice. After some hours.
Sun koma Kaduna lafiya, a lokacin Tga ya yi wa su gwaggo jagoranci sun gama duk wasu shirye shiryen da zasu yi, suna isa gida ya bawa Tga ragamar yi wa su Maryam ɗin shirye shiryen tafiya, ya yi masu na majinyata ya ce mashi, dan komai ya tafi normal cikin sauri.
A bedroom na Aseef dake a kasa Areef ɗin ya kwantar da Maryam da kuma Adivar, sannan ya sanar da gwaggo da ta ɗan kula da su, ta cigaba da duba lafiyarsu zuwa gobe su tafi.
Haƙiƙa gwaggon ta tausaya masu, har kwallah sai da ta matsa masu duk da bata san meyafaru da su ba, ta yi masu kwallah sosai, a haka ma dan dai bata gansu tun ɗaukosu da aka yi ba, yanzu ai sun ɗan yi kyan gani.
Bedroom nasa Areef ya wuce, wanka ya yi tare da fitowa ya shirya, sannan ya biya bashin sallar azabar da kuma la'asar da ake binsa.
Bayan ya idar sai ya zauna a bakin bed nasa tare da ɗauko wayarsa da ya fita ya barta a saman bedside drawer, ba da ita ya tafi ba. Number Lion ya fara kira bayan ya kunna wayar, a lokacin kuma Lion ya tashi daga barci ya baro wayar a cikin bedroom nasa, ya fita zuwa parlourn kasa dan ya sanya a fitar da gawar Dr Cherish zuwa mortuary, so baya tare da wayar tasa, two miss call Areef ɗin ya yi mashi, ganin bai ɗauka bane yasa ya kyale shi tare da yunkurawa zai mike.
Kasa miƙewar ya yi, bai san time da ya koma ya zauna ba yana mai binta da kallo, tsaye take a bakin kofar shigowa cikin bedroom ɗin, hannunta ɗauke da kayan abinci, ta yi wanka ta canza kaya izuwa kananan kaya, wandon jeans fari tas da T-shirt maroon color, ta yi matuƙar kyau sosai da sosai, ta gyara gashin kanta, sai kai mashi karo daddaɗar kamshi perfume nata yake yi.
Duba time ya yi karfe 5 saura ƴan mintoci, wani irin murɗa mashi cikinsa ya yi, saboda yunwa, dama abincin zai tashi ya je ya ce ta kawo mashi, sai kuma gata ta zo.
Karisowa cikin ɗakin ta yi bakinta ɗauke da sallama, har ƴar rama sai da ta yi, saboda shiga damuwa na halin da su Adiva ɗin suke a ciki. Sam basu ɓata lokaci ba wajen cin abincin a tare, dan suna jin bakar yunwa over.
Bayan sun kammala sai suka zauna hirar yadda aka yi ta tsinci kanta a gidan na Hjyr daɗin.
Da daddare misalin karfe 8 bayan sallar isha kenan, gabaɗaya family sun zo yi masu sallama, su Abban Imran duk sun zo, a nan ne gwaggo ta sanar da Abbi cewa zasu tafi da Aafia, bai ce komai ba, saboda gwaggo yayarsa ce, ba zai iya ja da hukuncinta ba idan ta yanke, dan haka sai ya ce Allah ya kaisu lafiya kawai.
Sun sha hira da family kamar ba gobe, Akila sai kuka take yi akan wai ba zata iya rabuwa da Ammienta ba, har da cewa ita gaskiya ba zata bi su gwaggo ba, zata zauna da Ammienta ya fi mata daɗi. (Ni kuwa nace iskancin kawai, anjuma kaɗan zaku ganta da waya tana faɗawa Heartbeat ta ƙosa ta ganshi😂 mu da mun san komai😏 yo Aseef da Akila ai sai Allah, halinsu sai su😌)
Sai aikin rarrashinta Ammien take yi, haka shi ma Abba, sai rarrashinta suke yi.
Suna a tare cikin farinciki Akil ya kirasu a waya ya sanar dasu Umaisha ta haifi ɗa namiji yanzu, murna a wajensu ba'a magana, Ammien tafiya ya kamata zuwa Madina kenan, su Umaisha anzama maman baby, Akil kuma za'a dawo sabon aiki.............😂
A takaice dai family basu bar gidan ba har karfe 10 na dare, sannan suka yi masu sallama a kan da safe zasu zo su rakasu zuwa airport, sai bankwana ake yi kamar antafi kenan, Rimsha har da rungumar Ayla tana kuka, Malika ma tana wajen, sai dai babu mai ganinta, harta Rimshar ma bata san da zamanta a wajen ba, dan bata bayyanar masu yadda zasu ganta ba.
Ammien dai baki har kunne ta sami jika, ga shi Akil ya turo masu hoton babyn, yaron kamarsa ɗaya sak da Akil ɗin......... Ni dai nace Allah yasa ta tsaya a iya kamar ta fuska, kufa my readers?.
Bayan kowa ya wuce gida, yanzu gidan ya rage daga Areef and Jehan wadda suke cikin ɗakinsu, sai Dr Salman da Brr Naurat suma suna ɗakinsu, Adiva da Maryam suna a kwance a ɗakin Aseef, ko motsi basa yi dukkansu biyu, sai dai jikin ba laifi ya ɗan yi kyau. Gwaggo da Aafia suna ɗakin gwaggon, Akila tana bedroom nasu manne da waya tana yi wa Aseef kuka a kan ita fa wlh gobe ma ya yi mata nisa, ta ƙosa da gan shi, kamar ba yanzu ta gama cewa ita ba zata je U.s ba, zata zauna da su Ammienta, sai rarrashinta yake yi, suna nan dai suna aikin da suka saba, ita kuma Rimsha yau ɗakin mummynta ta tafi, saboda ta san Lion ya zai kira gwaggo a waya, sai ta gudu ta koma wajen mum ɗinta, dan ma kada gwaggon ta ce ta karɓi wayar su gaisa, ga shi ba zata iya ce da gwaggon a'a ba, shi ne yasa kawai ta gudu abinta.
Ta je kuma ta sami mum idanunta biyu, zama ta yi a saman bed suna hira, sai nasiha mum ɗin take kara yi mata, tana kara tunantar da ita mahimmancin miji da kuma hakkokinsa a kanta, sannan tana kara koyar da ita dabarun zaman gidan miji, tana ta koya mata abubuwa dai kala kala, haka suka raba dare har wuraren karfe 2 suna hira na tsakanin uwa da ƴa, sai da mum ɗin ta ce yanzu kam su yi barci, tun da da asuba jirginsu zai ɗaga.
A gado ɗaya suka kwanta, sai dai ita dai Rimsha bata yi barci ba, saboda tunanin Lion, haka zalika shi ma bai yi barci ba, ya kasa iya yin barcin ba tare da ya ji muryarta ba, ya kira gwaggo kuma ya kasa iya tambayar ina take a bata su yi waya, saboda jikinsa yana bashi cewa fushi take yi da shi, so yasan ba lallai ta yarda ta yi waya da shi ba, shiyasa ya daure bai tambayi ina take ɗin ba, ya bari kawai gobe ai zata zo har in da yake.
A takaice dai dukkansu haka suka kwana cikin kunci, sun kasa yin barci har aka kira sallar asuba. Suna yin sallah kuma su Abban Imran suka zo rakasu zuwa airport, ansha koke koke kam kamar babu gobe, shi dai Areef sai binsu da kallo kawai yake yi, wani maganar ma da Hausa suke yi, shi kuma baya ji, dan haka sai ya zama ɗan kallo shi da Tga.
An jima ana koke koke da sallama da juna tun daga gida har airport kafin su wuce zuwa cikin jirgin, Abban Imran ɗin Areef ya dankawa makullan gidan Lion ɗin, suna tsaye suna kallonsu har sai da jirgin ya ɗaga, sai Allah ne kuma yasan yaushe zasu sake ganin juna, Dr Salman da Brr Naurat ma da su aka wuce, dan Lion ya ce lallai dole su dawo U.s, dan yana da bukatar ganin kakanninsa a kusa da shi, hakan yasa suka wuce da su, Abban Imran ya so a bar mashi iyayensan a nan ya kula da su, amma ba yadda ya iya, dole ya hakura aka tafi da su.