Kenza eBookz

Triplets book 4 Complete - Chapter 71

Triplets book 4 Complete - Chapter 71

Triplets book 4 Complete Chapter 71: Triplets book 4 Complete Chapter 71. Shi kuwa Areef bawan Allah, kwata kwata Jehan taki yarda ma ta sake haɗa hanya ɗa…

3,272 words

Shi kuwa Areef bawan Allah, kwata kwata Jehan taki yarda ma ta sake haɗa hanya ɗa shi ne, ko ya shigo wajen gwaggon sai ta yi kamar bata gan shi ba, idan tana kwance ne sai ta juya masu baya ta rufe idanu, idan kuma tana zaune ne sai ta kwanta ta basu baya, haka take yi.

Areef ɗin ya yi magiya har ya godewa Allah, amma taki sauraronsa, taki ma ai su haɗa ido, gwaggo kuma ta bi bayanta, dan haka yana cikin damuwa sosai bawan Allah.

Rimsha da Lion kuwa soyayyarsu suke zubawa son ransu mai tsabta, kamar zasu cinye juna dan so.

Zaɓe yana ta matsowa sosai, sai kara samun nasarori Lion yake yi, su His Excellence dai kamar babu su a duniya, sun yi cif, sai dai Lion duk abin da yake yi yana lura da lamuransu, dan ba shirun lafiya suka yi ba, bare ma yanzu da suka gane cewa Dr William na gaskiya da sir Safwan basu a hannunsu, sai suka kara ɗaura ɗamarar hallaka gabaɗaya familyn Dr William ɗin, sannan kuma suka ce shi ma uncle Herry da yake hannunsu wanda shi ne sarkinsu a yanzu, ya gaji Jacob, ya karɓi karagar mulki, dama idan baku manta ba shi ba wai an sadaukar da shi ne dan a kashe shi ba, a'a shi dan ya gaji karagar mulkin Jacob aka sadaukar da shi, to yanzu shi ne sarkin Daular tasu, shi yake mulkarsu, to shi ma yanzu suna kullah yadda za'ayi su kashe shi, dan sun san idan Lion ya juyo ta kansu ba zasu yi saura ba, shi ne yasa suke hanzari su aiwatar da abubuwansu cikin lokacin kafin komai ya kwaɓe musu, hakan ce ma tasa basu wani bi ta kan siyasar sosai ba, suna ƙoƙarin yadda za su kamo gwaggo ne su kasheta, dan a cewarsu gwaggo ita ce bangon rayuwar gabaɗaya familyn, idan suka kasheta dole kowa ya girgiza ya yi kuka sai idanuwnasa ta kumbura, hakan zai sa Lion ya yi laushi a cewarsu, to shi ne suke shirin yadda za'ayi su ɗaukota ba tare da ɓata lokaci ba, daga ita kuma suka ce sai Rimsha, ita ce ta biyu kafin su ɗauki su Dr Salman and Dr William.

E lallai su Anderson sun shirya sanya ilahirin familyn Dr Salman kukan jini ma bana hawaye ba, sai dai muce Allah ya tsare mana familyn Dr Salman ɗin mu kawai, ga shi sai sha'aninsu suke sha basu san me ake shirya masu ba, Allah sarki.

To yau dai Aseef yazo har wuya, hakurinsa ta kare, da misalin karfe 9 na dare, shirye yake a cikin kayan barcinsa masu kyau da tsada, kai tsaye part na gwaggon ya nufa. A tare ya sameta da ƴan matan nata suna hira, ita kuma Aafia ta basu baya tana kwance a saman bed tana chatting da Uncle T a Whatsapp ta wayar gwaggon, ya yi ya yi da ita a kan tafito waje suga juna, amma taki fitowa, ta maƙale a saman bed tana zuba mashi tsiya, ya ce idan bata fito ba shi zai zo ai ya ɗauketa, hakuri ta fara bashi tana ce mashi sai zuwa anjuma zata fito, dan tasan halinsa sarai, zai iya shigowa ya ɗauketa ɗin kamar yadda ya faɗa.

A bakin bed ɗin Aseef ya tsaya yana faɗin "Momma tazo mu tafi mana tun da dai yanzu komai normal ta ji sauki".

Gwaggon na ƙoƙarin yin magana, cikin sauri Akilar ta riga ta da cewa "Wlh ni gwaggo a'a, a nan zan zauna kawai, ni ba zan bishi ba, ya tafi abinsa".

Kallon shi gwaggon ta yi kafin ta ce "Shikenan ɗan autan mommansa, jeka ka barta a nan ɗin tun da ta ce ba zata bika ba, ka barmun ita ɗin a nan kamar yadda take so". Ta kai karshen maganar tare da kashe mashi ido ɗaya kamar ba uwa da ɗa ba.

Murmushi ya yi tare da manna mata sumbata a goshi kafin ya juya

FATEEMA ZAHRA MUSA A-K-A PRINCESS TEEMA TAKU CE TA AMANA🔥

❤️🔥❤️🔥❤️🔥❤️🔥❤️🔥❤️🔥🔥❤️🔥❤️🔥❤️🔥❤️🔥❤️🔥❤️🔥❤️🔥❤️🔥❤️🔥

*KINDADE KINA NEMAN ABUN DA ZAI SANYAKI QIBA,QIBA MEKYAU KIYI DIMIMI DUK INDA KIKA SHIGA BABU RAINI KINYI TA SIYA KINA ASARAR KUDINKI🤔 ALBISHIRINKI NAZO MIKI DA ABUN DA ZAKISHA BA TARE DA KINYI ASARAR KIDINKI BA 💃 Yana da matiƙar kyau sosai ko'ina naki zai chiko ki xama abar sha'awa duk mai buƙata ta nemeni ta wannan number 09067614054, kada ki bari ayi babu ke, kayanmu tested and trusted ne, guarantee ne*.

*KINDADE KINA NEMAN ABUNDA ZAI SANYA KISAMU XAMAN LFY TARE DA KWANCHIYAR HANKALI? TO BABYN HABIBI KIXO UMMU AFFAN TAXO MIKI DA SHAHARARRUN KUMA INGANTATTUN MAGUNGUNAN MATA, KAMA TUNDAGA KAN HUMRA, TURAREN WUTA, INFECTION KILLER, COLACCA, SAI KAYAN GYARA PAGE. KACA KACA. YALLAGWADA. JIGIDA. RUWA RUWA. BANI BANI. WOMEN JELL BATA BATA. DAFIN KAXA. TANTABARA. XABUWA. CICCIƁI. AND EXCLUSIVE, XUMA TASTED AND TRUSTED INA FARIN CHIKIN SANAR DA KU MUN FARA RAMADAN PROMO GAME BUQATA XA A IYA TUNTUBA NA TA WANNAN NUMBER 09067614054 JIGAWA STATE MUNA AIKAWA KO'INA CIKIN AMINCI DA YARDAR ALLAH, BABYN HABIBI KARKIMANTA DA KAYANMU FIRST CLASS NE, DAGA KANSA AN RUFE KOFA, YANA DA INGANCI NA WUCE TUNANINKI*.

❤️🔥❤️🔥❤️🔥❤️🔥❤️🔥❤️🔥❤️🔥❤️🔥❤️🔥❤️🔥❤️🔥❤️🔥❤️🔥❤️🔥❤️🔥

https://whatsapp.com/channel/0029VaMOfZZI7BeKXPU9gK2S

❤️🔥❤️🔥❤️🔥❤️🔥❤️🔥❤️🔥❤️🔥❤️🔥❤️🔥❤️🔥❤️🔥❤️🔥❤️🔥❤️🔥❤️🔥

TSARAWA DA RUBUTAWA......✍️

❤️FATEEMA ZAHRA MUSA (💫PRINCESS TEEMA🔥🌹)

*Domin samun damar karanta littafin nan daga farko har karshe zaki iya nemana ta wannan number 08161390581 ban da kira*

Date: 5/6/2024

E46

Murmushi ya yi tare da manna mata sumbata a goshi kafin ya juya ya fice daga cikin ɗakin.

Yana fita ita ma Aafia ta miƙe zaune tare da zuro kafafunta kasan bed ɗin tana faɗin. "Gwaggo zan je parlour, uncle T ne yake kirana".

Siririn murmushi gwaggon ta yi kafin ta ce "To a dawo lafiya, ke kuma Akila zo mu je bedroom naku mu yi sirri". Ta kai karshen maganar tare da miƙewa ta yi gaba.

Sai aikin turo baki Akilar take yi ta miƙe tabi bayanta. Suna fita ba'a fi da minti biyar ba sai ga Areef ya shigo cikin bedroom ɗin bakinsa ɗauke da sallama.

Jehan na jinsa ta yi maza ta lumshe idanuwanta gam, dan ma ya ɗauka barci take yi. Saman bedside drawer ya zauna, tun da ya shigo idanuwansa suna a kanta, sanye yake shi ma da kayan barci a jikinsa, ya yi kyau sosai, sai dai ƴar rama da ya yi na rashinta a kusa da shi, yana cikin damuwa sosai, sai tashin fitinannen kamshi yake yi sosai.

Yana ƙoƙarin yi mata magana ne wayarsa ta fara ringing, cirota daga aljihun wandon barcin nasa ya yi. Mamaki ne ya bayyana a saman face nasa lokaci da ya kalli saman screen ɗin wayar, new number ce take kiransa.

Shiru ya ɗan yi, kamar ba zai ɗauka ba, sai kuma dai ya yi picking tare da sanya wayar a Hand-free. Daga ɗayar ɓangaren muryar mace ce ta ambaci "Hi dear".

Jin haka yasa cikin sauri ya cire wayar daga hand-free ɗin yana mai kallon Jehan ɗin da kyau da kyau, dan baya son a kara ɓata mata rai, ya sani sarai ranar ma da mace ta kirasa basu wanye lafiya da ita ba, dan haka sai ya katse kiran ma mai gabaɗaya ya kuma kashe wayar.

Cikin aljihu ya mayar da wayar kafin ya miƙe tsaye tare da gyara hannun rigarsa, sannan ya shammaceta ya ɗauketa can cak suka nufi waje.

Bugawar da zuciyarta take yi ne yasa bata yi mashi rigima a kan ya sauketa ba, ta ji muryar mace a wayarsa, hakan yasa har wani bada dum dum kirjinta ya yi, shi ne yasa da ya ɗauketa bata iya yi mashi gardama ba, dan tana cikin yanayi mara kyau.

Bai direta a ko'ina ba sai a saman bed nasa, yana sauketa kuma ya yi saurin kashe wutar ɗakin tare da kara gudun A.c. tana kwance shiru tamkar mai yin barci, duk abin da yake yi tana jinsa, kawai bata jin ra'ayin yi mashi magana ne.

Hayewa saman bed ɗin ya yi tare da jawo masu lallausan bargonsa, sannan ya jawota jikinsa. A tare suka sauke nauyayyar ajiyar zuciya, su dukkansu sun yi kewar juna, amma sai rigimar tsiya su yi ta wahalar da kansu abanza. Cikin nutsuwa ya fara magana kasa kasa kamar mai yin raɗa. "Baby i know baki yi barci ba, kina jin duk abin da nake yi, please ki yafe mun mana, kin san halin da nake a ciki kuwa? Zan iya mutuwa fa, please kin ji?".

A kule ta ce mashi. "To wacece kuma ta kira wayarka yanzu?".

Wani irin dariya ne ya so kubce mashi, amma sai ya danne, dan kada ya kara laifi a kan laifi, yasan idan ya kuskura ya yi mata dariyar nan to fa sai an jisu a rana, Jehan sarkin rigima, uwar kishi kuma. "Baby i don't know her, kawai new number na gani, kuma ai ga wayar nan ki duba mana ki gani, you should have call her and ask her ma idan kina so, ask her a ina ta sami numberta zata gaya maki". Ya kai karshen maganar yana ɗan shafa bayanta.

Shiru ta yi mashi bata sake kula shi ba. Ganin hakan yasa ya fara yi mata raɗa tare da kalamai masu sanyaya zuciya a cikin kunnenta. Sai dai kuma sam taki kula shi.

Da yake ɗan yi ne kuma ya iya duniyanci, tuni yasan yadda zai yi ya shawo kanta har ma ta mance da fushin da take yi ta biye mashi, bata ma san lokacin da suka fara wasa da juna ba, sai dai har lokacin da akwai tsoronsa cike tap a ranta, amma ta danne ta biye mashi dan dole ba dan ta so ba.

A ɓangaren gwaggo da Akila kuwa, nasiha mai ratsa jiki ta je ta yi mata, sannan ta ce to ta yi wanka ta shirya maza ta wuce wajen mijinta. Haka kuwa aka yi, ta yi wanka tare da shiryawa cikin wasu kayan barcin, sai tashin kamshi take yi ta nufi bedroom nasa.

Yana kwance a saman bed yana latsa waya, hira yake yi da Haroon abokin karatunsa. Kasa kasa kamar mai ciwon baki ta yi sallamar tata.

Bata jira ya amsa ba kawai ta shigo cikin bedroom ɗin, bata kula shi ba ta nufi saman bed ɗin kawai ta kwanta ta baki bakin gadon, sai aikin turo baki take yi.

Ɗaura wayar tasa a saman bedside drawer ya yi tare da matsowa kusa da ita, tamkar zai sa mata kuka ya ce. "Heartbeat yanzu fushi kike yi da ni? Ni ɗin naki? Shagwaɓatinki ne fa!".

Kin kula shi ta yi, sai ma runtse idanuwanta gam da ta yi. Hannunsa ya kai ya jawota jikinsa, sannan ya cigaba da cewa. "Please my heartbeat ki dai'na fushin nan kin ji? Please ki yafe mun mana, na tuba fa, kuma ai ba laifina bane, kece nan kika yi daɗi dayawa, shi ne yasa duk na ruɗe". Yana magana yana turo mata baki tare da shafa mazaunanta.

Duka ta fata kai mashi a saman kirjinsa tana faɗin. "Wato ma daɗi nayi maka ko? Lallai Heartbeat ka iya mugunta, da na mutu fa?".

Hannun nata da take dukan nasa da shi ya riko yana faɗin. "Bazaki mutu ba, kin manta da cewa tare zamu mutu ne? Idan kika mutu ai dole na biki, kin san adadin son da nake yi maki kuwa? Kin san ya nake ji a zuciyata kuwa? Allah Heartbeat ba zan iya jure rashinki ba, please ki yafe mun".

Kara shigewa jikinsa da kyau ta yi kafin ta ce. "A'a ba zan yafe maka ba gaskiya, sai ka yi mun tausa to".

Da sauri ya ce "Tausar ita kaɗai kike so?". Kai kawai ta gyaɗa mashi alamar e ba tare da ta yi magana ba.

Miƙewa ya yi zaune tare da fara yi mata tausar babu kama hannun yaro, yana yi yana kallon face nata. Sai da ta gajiyar da shi sosai, sannan ta ce to ya isa ya zo su kwanta. A hanzarce ya mannata da jikinsa suka fara aikin da suka saba, suna yi suna zubawa juna shagwaɓa kamar ba gobe.

A ɓangaren Aafia kuwa, a parlourn kasa ta sami uncle T, daga shi sai kayan barci a jikinsa, hannunsa na rike da cup mai ɗauke da coffee, ya saki kyakkyawar gashin kan nan nasa har baya, sai tashin kamshi yake yi.

Tun da ta sako kafarta a saman stair case ɗin ya tsareta da idanu yana kallonta, sanye take a cikin kayan barci ita ma, sai dai ta ɗaura hijabi mai ɗan girma zuwa laps nata a saman, sai tashin daddaɗar kamshi ita ma take yi.

A saman sofa ɗan nesa da shi ta zauna tana yi mashi barka da dare. Ɗaura cup ɗin hannunsa a saman table dake a kusa da shi ya yi kafin ya amsa mata tare da ce mata ta dawo kusa da shi mana.

Kai ta girgiza mashi alamar a'a a in da take ɗin nan a nan zata zauna. Miƙewa shi ya yi ya koma kusa da ita ya zauna, yana ƙoƙarin fara yi mata magana suka jiyo muryar Dr William ta bayansu yana faɗin. "Sudais baka kwanta ba har yanzu?".

Shiru Tga ɗin ya yi yana tunanin sunan Sudais, da alama shi ma an mantar da shi addinin Musulunci, bare kuma yanzu da su Anderson ɗin suka juyo da aiki a kansu, so da wuya ya iya tuna sunan, shi kuma Dr William kunga yanzu ya koma ainahinsa, a yanzu shi cikakken musulmi ne mai ilimin addini dai'dai gwargwado.

Ganin ya kasa iya tuna sunan ne yasa kawai ya amsawa yayan nasa da cewa suna hira ne da matarsa, amma yanzu ba jimawa zasu shiga. Kamar Dr William ɗin zai sake yin wata magana, sai kuma ya fasa ya juya izuwa saman kawai.

Nisawa uncle T ɗin ya yi, haka suka cigaba da zuba hira cikin nuna tsantsar so da kulawa.

A ɓangaren Lion and Rimsha kuwa, abin ba'a magana, idan aka ce shakuwa ma an rage, sun haɗe sun zama chewing gum abinsu, zuba soyayyarsu suke yi son ransu, sam Lion baya jin kunyar kowa, a gaban kowa zai ɗauki matarsa su wuce ɗaki, yanzu ta fara sabawa da Brady, har aikansa tana yi ya kaiwa Jehan ko gwaggo abu, sai dai bata taɓa yarda ya hau mata jiki, ɗan nesa nesa dai ake abotar.

After some months.

Election time.

An yi zaɓe lafiya lou Alhamdulillah, gabaɗaya kasa ta rikice zaɓen da aka yi, kowa burinsa kawai ya ji sakamako, ga shi Lion ya tashi kan al'umma ya jijjiga kowa da kowa a in da ya tsayar da daddyn Rimsha a matsayin mataimakinsa, dama da biyu ya ce ayi wa daddyn Rimshar ktakardan ɗan kasa da komai da ya shafi doka, ashe abin da yake shiryawa kenan, masu cewa baya son daddyn Rimsha yanzu ya rufe masu baki, dama shi wlh yana kaunar daddyn nata kamar yadda yake kaunarta, musamman ma da gwaggo ta ce tafi son daddyn sama da kowa a cikin ƴan uwanta, sai ya kara son shi sosai, rashin jituwa da basu samun nan kuma hakan ta samo asali ne da dukkansu suna jiji da kai, izzar bala'i ke garesu, shiyasa ba zasu shirya ba, ba zasu zauna waje guda ba, dan ba wanda zai yarda ya duƙawa ɗan uwansa a cikinsu.

Gabaɗaya faɗin U.s ta girgiza na jin cewa bakin fata Lion ya fitar a matsayin mataimakinsa, sannan kuma a halin yanzu kasa ta dulmuye cikin kura na jiran sakamakon zaɓe, shi kuwa Lion hankalinsa a kwance yana gida tare da rigimammiyarsa, ya sakata a gaba yana ta kallon kayarsa, ta wani kara kyau abinta, ta yi ƙiba dumur mur da ita, komai nata ya kara cikowa, sai aikin zuba mashi shagwaɓa take yi yana biye mata.

Kwance suke a saman bed nasa, tana kwance a saman Lion chest nasa tana aikin zuba mashi kukan shagwaɓa a kan lallai ita sai dai su tafi yawo, sai dai ya kaita bakin ruwa su je su huta a can, tana son zuwa bakin teku.

Kawai ya zuba mata idanu ne yana kallon ɗan bakin nan nata, sai aikin turo shi take yi, ya kasa iya ce mata ko uppan.

Ganin bashi da niyar yi mata magana ne yasa ta yunkura zata bar jikin nasa. Da sauri ya riƙota yana faɗin. "Zaki fara ko?".

Kamar zata yi kuka ta ce. "Noorish kai ne fa ka fara, kaki ka canza hali, nafi 30 mins ina yi maka magana amm kaki ka ce mun ko uppan, to ya kake son nayi? Sai dai nayi ta magana ni kaɗai kamar mahaukaciya?". Ta kai karshen maganar idanuwanta sun ciko tab da kwallah.

Lumshe idanuwansa a hankali ya yi tare da ɗan sake buɗesu a kanta, sumbata ya fara kaiwa ɗan bakin nata kafin ya fara magana kasa kasa a nutse. "I really like your lips my Meesha, sarkin rigima, kina ji ko? Ni ban iya godon magana bane, amma i will try my best wajen ganin ina amsa maki, and maganar muje yawo kuma zamu je, amma ba yanzu ba, kinga gobe za'a saki sakamakon zaɓe, fitarmu a yanzu babban haɗari ne, ki bari sai komai ya lafa, zamu je duk in da kike so Queen of my heart".

Tsananin farinciki ne ya bayyana a saman face nata, wani irin cool murmushi ta sakar mashi tare da bashi hot sumbata a saman lallausan lips nasa. "I really love you my Noorish, king of my heart".

Tongue nasa ya fitar tare da fara aikin lasar lips ɗin nata yana mai jin tsananin kaunarta tana kara ratsa shi, a haka manne da juna suka yi barci, tamkar zasu shige cikin jikin juna.

Washegari da safe, gabaɗaya kasa sun zuba idanu suna jiran sakamaƙon zaɓe da za'a saki, kowa yana fatan Allah yasa nasa zaɓin ya ci, while su kuma su Anderson suna can suna faman yadda za'ayi ko ta halin ƙaƙa ne su ɗauko Gwaggo, har yanzu sun kasa iya ɗaukarta, saboda yawan zama da alwala da take yi, ga askar na safiya da maraice wanda duk wuya duk daɗi bata bari ya wuceta bata yi ba, haka shi ma zama da alwalar, duk wuya duk daɗi da alwalarta take tare, hakan yasa suka kasa iya ɗaukarta, sai suka koma suna rakuɓe rakuɓe suna neman wanda zasu ɗauka a cikin gidan, wanda yake kusa da zuciyar Lion sosai.

Maryam kuwa an sallamota daga aaibiti ta dawo gida, tana part na gwaggo, Areef ya ɗauko masu aiki mata guda biyu suna kula da ita. Ita kuma Adiva har yanzu tana wajen Sheikh Sultan, yana ta fama dan ya ga ya ceto baiwar Allahn nan.

Uncle T da Aafia soyayya ta yi nisa, gwaggo ta ce dole su je Nigeria neman aure wajen Abbi, daddyn Rimsha ya ce zai aurar da ita a nan ɗin kawai, ba sai sun je ba, gwaggo ta ce a'a masu son zuwa Nigeria suna dayawa, dan haka a can za'a je a nemi aurenta a kuma ɗaura kafin nan su dawo. Ba yadda zasu yi da ya wuce su yi na'am da zancen gwaggon kawai, yanzu sun shirya a kan cewa dama bayan zaɓe zasu je, daga nan gwaggo da mummyn Rimsha zasu wuce Dubai su yi wa su Rimshar sayayyar kayan lefensu da ba'ayi masu ba.

Yau dai gabaɗaya U.s ta yi tsit suna jiran jin sakamakon zaɓe daga wakilan zaɓen, shi kuwa Lion yana kwance a saman sofa ya tada kai da laps na Meesharsa suna kallon news ɗin a Tv, sai sanya mashi chip chop a baki take yi, yana tauna a hankali, tana rike da kwalin chip chop ɗin a hannunta, ita bama news ɗin take kalla ba, face ɗin mijin nata kawai take ta kallah, shi kuma yana kallah Tv.

Readers Also Read

More by Bilyn Abdull