Triplets book 4 Complete - Chapter 76
Triplets book 4 Complete Chapter 76: Triplets book 4 Complete Chapter 76. A takaice haka suka shirya rundunar sojoji guda, tamkar waɗan da zasu tashi…
3,366 words
A takaice haka suka shirya rundunar sojoji guda, tamkar waɗan da zasu tashi duniya, a wannan rana suka nufi wannan ƙungurmin bakin dajin, sun yi shahada dan kawar wa da kasarsu ɓata gari bayin Allah.
Shi kuwa Lion dukufa ya yi da yi masu addu'a tare da fatan Allah ya dawo mashi da su lafiya, ba halin ya bisu ne da wlh ba zai iya bari su tafi su kaɗai ba, dole ce tasa ya zauna shi, domin kujerar President ba wasa ba, ya sanya Sheikh Sultan sai yi masu addu'a yake yi babu kama hannun yaro.
Wasa wasa sai da suka shafe watanni kamar yadda suka faɗa kafin su tafi, ga shi shi Areef ma ko sallama da Jehan bai yi ba, ya barta tana barci, kuma da gangan yaki tashinta, dan yasa zata tsayar da su ne ta hanasu tafiya a kan lokaci, zata yi ta yi mashi kuka tasa ya tafi da tunaninta tare da damuwa a ransa, shi ne yasa kawai ya bawa Lion ɗin amanarta sannan suka wuce.
Tun da suka tafi kuma gabaɗaya wayoyinsu bata aiki, ba network a wajen, babu wani connection da suke samu tsakaninsu da ƴan uwa, shiru kake ji tamkar an ɓallawa sama harara.
Har Akila ta haifi ƴaƴanta santala santalan guda uku, wato TRIPLETS, dukkansu kuma maza kyawawan gaske, su Areef shiru basu dawo ba.
Sai dai fa ranar haihuwar Akila an yi ƙaramin yaki ba kaɗan ba a gidan, dan kuwa sun ga dirama wajen Aseef, likitoci jiga jigai aka ɗebo daga hospital ɗin Dr William, aiki aka yi mata aka cire ƴaƴan, ba zata iya haifarsu da kanta ba, ba yadda ba'ayi da Aseef ba a kan ya tsaya a waje, ya ce wlh ba zai tsaya ba, ɗakin ya shige abinsa, ya je ya zauna kusa da Heartbeat ɗin tasa, ya ɗaura kanta a saman laps nasa tare da ƙanƙame hannunta yana ta kallon duk wahalar da take sha, ya sha kuka kam hawaye bibbiyu, sai faɗi yake kada likitocin nan su yarda su bari ta mutu, idan ta mutu sai ya kashe su ɗaya bayan ɗaya suma, sai kace su ne suka ɗaura mata ciwon, yana neman sauke haushi a kansu.
Ai su gwaggo sunga ikon Allah, dan fa Aseef ya yi masu karamar hauka, dan ma Allah yasa aiki aka yi mata, da da kanta zata haifesu ai da ina ga zuciyarsa ce zata buga idan yaga halin da zata shiga, aikin ma ya bi ya wani ƙanƙameta ya takurawa likitoci basu samu su yi aikinsu yadda ya kamata.
Sai dai kuma fa abin dariya abin takaici, ana ciro mashi baby's ɗin ya saketa ya koma wajen yaran abinsa, wai ya je ganinsu, har ya manta yanzu ya gama zubar mata da hawaye har yana cewa shi fa baya son baby's ɗin, ya fi sonta, dan haka shi a ceci rayuwarta kawai, ba ruwansa da baby's ɗin, har da cewa ba zasu sake haihuwa ba daga wannan, amma da yake ɗa mai daɗi ne, ana cirosu har ya manta da surutan da ya rinƙa yi a kan nasu, ya wani shige gaba yana ta kallon yaran, sai tsallara ihu suke yi, shi kuma sai masifa yake yi wa likitocin a kan su saka mashi yara su yi shiru ko kuma ya hukuntasu, dan shi ba zai iya hakuri ya ji baby's nasa suna kuka ba.
Izuwa yanzu dai kowa na family ya dai'na mamakin halin Aseef, sun zuba mashi ido kawai suna kallon ikon God, dan ya wuce tunaninsu, daga wannan sai wannan, a kan waɗan nan TRIPLETS ɗin nasa zai iya kashe mutun.
A gaban idanuwnasa aka yi wa baby's and maman baby's komai, yana tsare da kayansa yana kallonsu. Ko da aka gama gyara su ma ya hana family ɗaukar yaran, wai kada su yi su karya mashi yara, dan kashin yaran ba kwari ne da shi ba.
Gwaggo kawai ya yarda ya bari ta ɗauki na farko da aka fara haifa, dukka yaran wlh kama da Aseef ɗin sak suke yi, kamar an tsaga kara, babu wanda ya ɗauko Akilar, harta kwayar idanuwansu da yake brown irin nasa, duk sai suka fito a turawan, babu kalar Akila a cikinsu.
Ita kuma Jehan tana nan tana aikin tura uban ciki haihuwa ko yau ko gobe, ga cikin nata ita ma kato da shi, an yi mata scanning, sai dai ta ki yarda kowa yaga result ɗin abin da yake a cikin nata, ta ɓoye kayanta, daga ita sai gwaggo suka sani, ta ce kowa ya barta ta sarara, sai cikin ya fito duniya zasu ga menene a ciki, haka suka hakura suka rabu da ita.
Ba yadda gwaggo bata yi da Lion ba a kan ya zo ya ga yaran Aseef, amma ya murje idanuwansa ya ce shi wlh ba zai je ba, kuma kada a kawo mashi su ɗaki baya so, ita kam gwaggo yanzu al'amarin Lion a kan tsanar yara ya fara bata tsoro, ga Maryam matar Sir Safwan har tana da ɗan kara min ciki, amma shi Lion shiru, hakan yasa gwaggon ta fara zarginsa a kan anya ba wani abin yake bawa Rimsha yasa bata ɗaukan ciki ba?.
(Nima Princess Teema na yi wannan tunani🤔 gwaggo ki binciko mana gaskiya, ina dalili? Mu muna son muga little Lion)
Kowa yasan da cewa Lion ya fi Kaunar Aseef sama da kowa a cikin ƴan uwansa, amma kuma duk wannan uban kauna da take a tsakaninsu Lion ɗin yaki yarda ko da ido ya kalli ƴaƴan Aseef ɗin, da yake Aseef ɗin yasan tun farko Lion baya son yara, sai bai yi gigin kai mashi labarin Akila ta haihu ba, sai ya rabu da shi kawai ya rungumi ƴaƴansa abinsa, sai murna yake yi ya sami TRIPLETS tashi ɗaya.
Ita kuma Rimsha Allah ya gani tana son yara, kullum sai ta yi zancen cikin Akila da Jehan ɗin, amma da zarar ta fara yi wa Lion ɗin zancen haihuwar zai canza masu topic na hira, shi zancen yaran ne sam baya so, amma kuma duk da haka yana tsananin bawa Jehan kulawa na wuce misali, a yanzu haka tana a part nasu da zama, saboda yana ganinta tamkar Areef, dan maganarsa ta karshe da Areef ɗin ma kenan a kan Jehan ɗin ne da abin da yake a cikinta, amana ɗan uwan nasa ya bashi na Jehan ɗin, dole ya kula da wannan amanar ta ɗan uwan nasa, saboda bashi da tabbacin Areef ɗin zai dawo a raye ko kuma zai mutu?.
Hakan yasa yake kula da Jehan ɗin over, bedroom ɗin da take ma sai da ya saka mata camera, duk da a cikin part ɗaya suke, yana iya jiyo motsinta, amma bai wadacesa ba hakan, sai ya kara mata da camera dan ya rinƙa kallon duk wani abin da take yi.
Haka shi ma sir Safwan, ya fi kula da Jehan ɗin sama da yanda yake kula da matarsa Maryam, wani lokaci abin har yana neman ya zamar masu faɗa a tsakaninsa da Maryam ɗin, sai ta rinƙa cewa meyasa ya fi bawa cikin dake jikin Jehan kulawa sama da nata cikin? Ita da cikinta ma karami ne, ita ya kamata ya bawa kula sosai, dan kada a samu matsala, amma sai ya fi kula da cikin Jehan ɗin, kullum yana part ɗin Lion wajenta, da ta yi motsi kaɗan zai tambayeta tana lafiya kuwa? Abin ya fara bawa Maryam ɗin haushi, kun san mata da kishi, kada kuga laifinta, haka muke........😂
Duk yadda gwaggo ta kai ga son Jehan a wannan karon sai da ta hakura ta barwa Lion da sir Safwan kula da Jehan ɗin, domin kuwa suna ɗaukar Jehan ɗin ne a matsayin Areef ɗinsu, cikon QUADRUPLE nasu, kuma kowa yasan sir Safwan da Areef ɗin sun fi shakuwa sosai, dole kunga ya mayar da hankali wajen kulawa da ɗan uwan nasa kayansa fiye da komai.
Wasa wasa har cikin Jehan ya shiga watannin haihuwa, su Areef shiru basu babu labarinsu, Lion yasa an tura wasu runduna na sojoji ma, amma still shiru, suma rundunar sun tafi basu dawo ba, ba wani labari.
Kullum cikin kuka a ɓoye Jehan take yi, duk da Lion ya ce mata Areef sun je ƙasar China ne yin wani aiki, zasu dawo bada jimawa ba, amma ta kasa samun nutsuwa, tana jin kamar ma Areef ɗin baya raye a duniya ne, ga rashin iyayeta na tsawon watanni da dama, abin sai ya haɗu ya yi mata yawa, ga uban ciki haihuwa yanzu ko anjuma, duk ta rame, ta yi wani irin duhu sosai. Amma Lion yana iya ka bakin ƙoƙarinsa wajen ganin ya kwantar masu da hankali ita da Rimsha da kuma gwaggo, abin ne yana neman ya fi karfinsu.
Ƴanƴan Akila sun fara wayo, ta tare a part ɗin gwaggo abinta, kullum na Allah Aseef yana manne da baban ɗan nan nasa wanda ya fi kama da shi, ba'ayi shagalin suna ba, sun ce sai Jehan da Anaya sun haihu za'a haɗa dukka ayi party, daga nan a shirya zuwa Nigeria, sai dai an sanyawa yaran suna kamar yadda addinin musulunci ta tanada, Aseef ya yi wa Abban Akila takwara, ya kuma yi wa Dr William sai kuma sunan Lion ya sakawa autar cikinsu, baya taɓa yarda wani ya ɗauka yaran nan idan ba gwaggo ba, ko su Anaya ya hanasu, sai dai ka kalli yaran da ido suna kwance a saman bed nasu, gasu gwanin ban sha'awa, ƴan ɓul ɓul da su, amma baka isa ka ɗauka ba, ubansu ya ce kar a karya mashi su, a barsu a kwance a rinƙa kallonsu.
Yau ni PRINCESS TEEMA ina ganin ikon god a wajen Aseef, wai kada ayi a karya mashi su, Kai jama'a, yara masu daɗi, Allah mai iko, Allah ka bamu masu albarka
Shi kuma fa zai ɗauki yaransa son ransa, kuma koda yaushe idan ya zo ɗauka bai iya ba sai gwaggo ta ɗauka ta miƙa mashi su, amma a haka yake cewa kada wasu su karya mashi yara basu iya ɗaukarsu ba, Aseef duniya.
Yau ta kama Monday, tun karfe 7 Lion ya hau shiri. A tunanin Rimsha office zai tafi, sai kuma taga akasin haka, dan ba shirin zuwa office yake yi ba, abin ya yi mugun bata mamaki.
Yana gaban mirror yana gyara dark black curly hairnsa ta fito daga cikin toilet ɗaure da towel a kirjinta ta same shi.
Karisowa wajensa ta yi tana faɗin. "Noorish ina zaka je da irin wannan shiga haka? Yau kuma me ya haɗaka da Army's shirt?".
Yana aiki sauri sauri ya bata amsa a takaice da cewa. "Wajen su Areef".
Da yake bata san ina su Areef ɗin suke ba, bata san ina suka tafi ba, sai ta ce. "Amma Noorish tafiya zaka yi ne da irin wannan shiga haka? Kuma naga kamar harda gun ka ɗauka, to dai nima zan bika".
Shiru ya yi bai bata amsa ba, domin harshensa ma wani irin azababben nauyi take yi mashi, yau ba zai iya hakuri ba sai ya bi bayansu Areef, sai dai duk abin da zai faru ya faru, tun da ya tashi barci yau da asuba, zuciyarsa take tsananin buga mashi da karfi karfi, kuma already kunsan zuciyar QUADRUPLE tana irin wannan bugawar ne idan wani abin ya sami ɗayansu, so yana kyautata zaton akwai abin da ya sami Areef, hakan yasa ya ji ba zai iya zama ba, duk bala'i yau da izinin Allah sai ya kai in da ɗan uwansa yake!!. To fa babbar magana.
FATEEMA ZAHRA MUSA A-K-A PRINCESS TEEMA CE.....✍️🔥
❤️🔥❤️🔥❤️🔥❤️🔥❤️🔥❤️🔥🔥❤️🔥❤️🔥❤️🔥❤️🔥❤️🔥❤️🔥❤️🔥❤️❤️🔥
*KINDADE KINA NEMAN ABUN DA ZAI SANYAKI QIBA,QIBA MEKYAU KIYI DIMIMI DUK INDA KIKA SHIGA BABU RAINI KINYI TA SIYA KINA ASARAR KUDINKI🤔 ALBISHIRINKI NAZO MIKI DA ABUN DA ZAKISHA BA TARE DA KINYI ASARAR KIDINKI BA 💃 Yana da matiƙar kyau sosai ko'ina naki zai chiko ki xama abar sha'awa duk mai buƙata ta nemeni ta wannan number 09067614054, kada ki bari ayi babu ke, kayanmu tested and trusted ne, guarantee ne*.
*KINDADE KINA NEMAN ABUNDA ZAI SANYA KISAMU XAMAN LFY TARE DA KWANCHIYAR HANKALI? TO BABYN HABIBI KIXO UMMU AFFAN TAXO MIKI DA SHAHARARRUN KUMA INGANTATTUN MAGUNGUNAN MATA, KAMA TUNDAGA KAN HUMRA, TURAREN WUTA, INFECTION KILLER, COLACCA, SAI KAYAN GYARA PAGE. KACA KACA. YALLAGWADA. JIGIDA. RUWA RUWA. BANI BANI. WOMEN JELL BATA BATA. DAFIN KAXA. TANTABARA. XABUWA. CICCIƁI. AND EXCLUSIVE, XUMA TASTED AND TRUSTED INA FARIN CHIKIN SANAR DA KU MUN FARA RAMADAN PROMO GAME BUQATA XA A IYA TUNTUBA NA TA WANNAN NUMBER 09067614054 JIGAWA STATE MUNA AIKAWA KO'INA CIKIN AMINCI DA YARDAR ALLAH, BABYN HABIBI KARKIMANTA DA KAYANMU FIRST CLASS NE, DAGA KANSA AN RUFE KOFA, YANA DA INGANCI NA WUCE TUNANINKI*.
❤️🔥❤️🔥❤️🔥❤️🔥❤️🔥❤️🔥❤️🔥❤️🔥❤️🔥❤️🔥❤️🔥❤️🔥❤️🔥❤️🔥❤️🔥
https://whatsapp.com/channel/0029VaMOfZZI7BeKXPU9gK2S
❤️🔥❤️🔥❤️🔥❤️🔥❤️🔥❤️🔥❤️🔥❤️🔥❤️🔥❤️🔥❤️🔥❤️🔥❤️🔥❤️🔥❤️🔥
TSARAWA DA RUBUTAWA......✍️
❤️FATEEMA ZAHRA MUSA (💫PRINCESS TEEMA💋)
*Domin samun damar karanta littafin nan daga farko har karshe zaki iya nemana ta wannan number 08161390581*
E51
"Noorish baka ce komai ba, na ce fa zan bika". Ta yi maganar kamar zata yi mashi kuka.
Ta cikin mirror ya zuba mata idanu yana kallonta, ta rame sosai, ga wasu kasusuwa da suka bayyanar mata a wuyarta, tamkar ba Meesharsa ƴar dumur mur da ita ba, yanzu ta dawo sai a slow, sai dara daran fararen Sleeping eyes ɗin nan zaka gani, hakan yana nuni da cewa kullum a cikin damuwa take.
Sai ƙoƙarin latsa wayarta take yi tana son kiran number Anaya a kan ta zo su haɗu a part na gwaggo, sam bata lura da yana kare mata kallo ta cikin mirror ba, ga shi daga ita sai ɗan ƙaramin a kirjinta, wanda kuma tsawonsa sam bai gama rufe mata rabin santala santalan cinyoyinta ba.
Tun ranar da aka sace daddyta, tun ranar Lion ɗin bai sake kusantarta ba, saboda suna cikin wani hali, sam baya ma jin wata sha'awa face damuwa, daddynta ya zamar mashi wani ɓangare ne na rayuwarsa, hakan tasa baya jin sha'awar komai face tunanin daddyn nata.
"Meesha". Ya ambaci sunanta in a cool voice.
Ɗago da idanuwa kawai ta yi ba tare da ta ɗago da kanta ba.
Juyowa ya yi gareta da kyau tare da buɗe mata hannayensa a kan ta zo gare shi.
Cool murmushi ta sakar mashi da ramammiyar kumatun nan nata, da sauri ta taho ta faɗa saman Lion chest nasa.
Ajiyar zuciya ya sauke kafin ya sa hannu ya rungumota da kyau da kyau.
Ƙanƙame shi ita ma ta yi, kamar nace zan kwace mata shi......😒
"Meesha kin rame sosai". Ya faɗa can kasan maƙoshi.
"Kai ma ai ka rame sosai Noorish". Ta bashi amsa tana ɗan ɗago da kanta.
Zai sake yin magana Tvn dake manne a bangon ɗakin nasu wanda yake haɗe da camerar ɗakin Jehan ya fara fitar da sauti mai kama da sautin numfashi.
A hanzarce ya ɗago da blue eyes nasa tare da kai kallonsa saman screen ɗin Tvn.
Ai bai san lokacin da ya saketa a dubu ɗari ba ganin abin da yake faruwa. Ita kanta bata san lokacin da ta waro idanuwanta waje tana kallon Jehan ɗin ta cikin screen ɗin ba.
Kafin ta yi mashi wani magana tuni ya fice daga ɗakin cikin sauri. A hanzarce ta bi bayansa ko mayafi bata ɗauka ba, daga ita sai wannan towel ɗin.
Yana saka kafarsa a cikin bedroom ɗin da Jehan ɗin take ciki, baby na faɗowa, ashe tun ɗazun naƙuda take yi, kun san halinta da dakiya tare da juriya, duk azabar nan da take ji ta daure ta kuma jure, sam bata nuna alama ba, sai da abin ya fi karfinta ne haihuwar ta zo gadan gadan, shi ne ta rasa ya zata yi, kuma karfinta duk ya kare, ta rasa mada fa, hakan yasa ta zamo ta sauko kasa daga saman bed ɗin nata, a nan ta cigaba da murkusoso tana fafutuka har sautin numfashinta ya fara fita da karfi karfi, ta so ta lallaɓa ta tafi wajen gwaggo a lokacin da ta sauko kasan gadon, amma ina karfinta duk ya kare, ta jigata sosai, hakan yasa ta kasa iya tafiya koda da ja a kasa ne, ta kasa, shi ne kawai ta hakura ta zauna a kasan tana ta fama ta kuma zubawa sarautar Allah iso.
Duk tsananin kin yara da Lion yake yi yau da hannunsa ya ɗauki babyn Jehan a cikin jini, saboda babyn ta haife shi da riga, abin da ake nufi da babyn da aka haifa da riga shi ne, wanda ake haifarsa yana zuwa da wani abu mai kamar yana da yake rufe mashi fuska, wanda idan ba'ayi saurin cirewa ba yana kashe yaro nan take, dan yana tare mashi numfashi ya hanasa yi, hakan ce tasa Lion ɗin ya ɗauke shi cikin jinin ya yi saurin yage abin ya cire.
Da gudun gaske Rimsha ta shigo cikin ɗakin, kan Jehan ɗin ta ƙariso tana ambatar sunanta da karfi.
"Get out Meesha". Shi ne abin da Lion ɗin ya ce da ita yana ƙoƙarin janyo duv dake saman bed ɗin dan ya kwantar da babyn dake hannunsa.
Kasa fita waje ta yi, sai ma kara matsowa da ta yi tana ƙoƙarin riko Jehan ɗin.
Wani irin nishi Jehan ɗin ta sake yi tare da riƙo wuyar rigar Lion ɗin, dan ya fi kusa da ita a kan Rimshar, Rimsha tana ta gefenta ne, shi kuma yana tsungunne ne a ta gabanta in da ya ɗauki baby, hakan yasa da azaba ta yi azaba bata san lokacin da ta damko wuyar rigarsa tana sakin wani irin numfashi mai matuƙar razanarwa ba, tamkar mutuwa zata yi, baiwar Allah.
Cikin zafin nama Lion ɗin ya janyon duv ɗin a dubu ya kwnatar da babyn tare da kai hannunsa dukka biyu ya riƙo shoulders ɗin Jehan ɗin yana mai dakawa Rimsha tsawa a kan ta fita a ɗakin kamar yadda ya faɗa mata tun farko.
Wannan tsawa da ya daka mata ya yi dai'dai da faɗowar baby a karo na biyu, ita kuma Rimshar tsabar tsorata da tsawar, sam bata san lokacin da ta kwasa a guje ta bar room ɗin ba, daga ita sai towel a kirji.
Yau dai Lion da baya kaunar yara a rayuwarsa, saboda kaunar Areef da yake yi tasa ya karɓi haihuwar Jehan da kansa, shi da ya ce ko kallon yaran baya son yi, sai ga shi da Allah ya tashi kamasa a hannunsa aka haifo yaran Areef, daga karshe ma gabaɗaya jikinsa ta yi dama dama ta yi wanka da jini, dan kuwa ba ƙaramar damka Jehan ta rinƙa yi mashi ba, saboda azaba, babynta na uku dana huɗu kam ma kusan a jikin Lion ɗin ta haifosu, duk ta fita daga cikin hayyacinta, hasalima bata san waye ne a wajen ba, Allah ya bata haihuwar QUADRUPLE a saukake, dan kuwa a saukake za'a ce, duk wannan azaban da ta sha wlh ya zo mata da sauki, saboda ba kowace mace ba ce zata iya haihuwa ƴan uku da kanta ba ma bare QUADRUPLE, wannan sai ikon Allah da ya bawa gwaggo da Jehan ɗin damar yin hakan, idan baku manta ba, ita ma gwaggon hakan ce, Jehan ƴar ɗakinta ta yi gado sosai sosai, a komai ta gaji gwaggon, bata rage komai ba abinta.
Duk taurin zuciya irin ta Lion wlh sai da idanunsa suka ciko da kwallah, ya yi matuƙar tausaya mata, dan daga karshe ma sai da ya bata iskar bakinsa ta iya cigaba da numfashi, a haihuwar na karshe ta kasa samun numfashin da zai riketa ta iya haifar baby, sai da Lion ɗin ya tallafa mata, ga shi su gwaggo basu kusa, dan gwaggo ma tana can sama hawa ta karshe ita da Josephine suna tsara yadda tafiyarsu Nigeria and Dubai zai kasance, sam bata kawo cewa haihu zai zowa Jehan ɗin a satin nan ba, a nata kissafin sai cikin next week, shi ne yasa suka ɗan matsa kusa da ita.
A lokacin da Rimsha ta fita daga bedroom ɗin, kai tsaye bedroom na gwaggon ta nufa, sai dai ko da ta je bata sami kowa ba, abin ku da yarinta, a maimaƙon ta fita ta nemi gwaggon a cikin gidan, dan ta gaya mata halin da ake ciki, sai kawai ta haye gado tana kuka tare da addu'ar Allah yasa kada Jehan ta mutu, Allah yasa ba mutuwa zata yi ba.