Kenza eBookz

Turken gida book 2 cmplete by janafty - Chapter 36

Turken gida book 2 cmplete by janafty - Chapter 36

Turken gida book 2 cmplete by janafty Chapter 36: Turken gida book 2 cmplete by janafty Chapter 36. "To ina ruwan ki da Sha'anina! Ko uwarki gata nan zaune…

3,356 words

"To ina ruwan ki da Sha'anina! Ko uwarki gata nan zaune ba ta isa ta hana ni abin da na yi niyya ba. Sai dai ta ba ni shawara ballatana ke karan kaɗa miya? Kuma kina duniya zan auri ɗiyar yayar Sadiya sai dai ki mutu saboda baƙin ciki"

"Kawu ni.."

"Ba na son ji wata magana. Ke daman ina da labarinki kin cika saka ido. Ke wa ya je gidan mijin ki ya takura miki? Ok to ke da kike zaune lafiya ke ma asirin kike yi kenan ko?

Kawu Abba ya ƙarishe faɗa a fusace, da ga ganin yadda ya ke mgana ran shi a ɓace ya ke. Tafida dai ƙala bai ce ba daga shi har Nene da Hajiyar Tafida.

Sai Anty Bahijja ta fara kuka. Kawu Abba ya ce ta rufe ma mutane baki, kuma fa bai girmeta ba amma matsayin shi na Kawunta sannan kuma daman shi ba shi da wasa.

"Kin takura mata ita da mijinta amma ke kina can kina zaune lafiya a gidan auran ki? Wanzami daman ai ba ya son jarfa ke ko an faɗa miki wata mgana ya kamata ki zo ki saki maganar kai tsaye? Shekaran Sadiya nawa tare da ku duk ba ki san haka ba sai yanzu?

"Ni kaina sai da na ce ta bar mganar da ta faɗa min amma ba ta ji magana ta ba "

Nene ta faɗa cikin bayyana ɓacin ranta.

"Ni fa ba laifin kowa na ke gani ba sai na wannan yar'uwan Sadiyan duk ita ta ɓata komai. Ya kamata itama ta na wajen nan" Hajiyar Tafida ta faɗa itama.

"Ba ruwammu da ita. Can tsakaninsu ne da Sadiya amma tabbas alaqar tun da ba ta alheri ba ce rabuwar shi ya fi." Kawu Sa'adu ya ce haka sai Anty Maimuna ta fara faɗin ai Ma'u ta na auran yaron yayar mijin Anty Bahijja ne.

"To sai me? Za mu raba alaqar ko da ta fi karfin haka ballantana ba ta yi wani karfi ba."

"Sosai. Tunda daga ita Bahijjan har ita dayan ba alheri a zukatan su."

In ji Mimisco da daman ita yar gaskiya da gaskiya ce. Duk kuma mganar da aka faɗa sai Anty Bahijja ta karyata Allah ya sa ga shaidu suka maida yadda na faɗa daki daki.

Gimbiya ta sha kunya domin kai tsaye Kawu ya kalleta ya na faɗin" Ke Saudatu ke ma kin ƙara hura fitina ke da kika zauna gidan Sadiya ta dafa abinci ta ba ki kina kwance sai ki saka mata da sharri? Kuma ke fa kika aure mata miji ita ba ta biki da sharri ba sai ke? Sai ta fara kuka tana faɗin a yi haƙuri kuskure ne ba za ta ƙara ba.

"Ba tarbiyan da na yi ma Saudatu ba kenan ni kaina ta ba ni kunya."

In ji Hajiyar Tafida. Ita kuma Nene sai ta ce koma me ya faru Anty Bahijja ce ta ja shi. Sai ta ƙara saka kuka ta na faɗin shike nan duk an maida laifi a kanta ba a duba nima cin mutumcin da na yi mata ba.

"Ke kika fara ci mata mutumci. Kuma ta yi min dai-dai da ta rama kwatankwacin yadda kika yi mata."

Tafida ya faɗa cikin fusata Kawu Abba ya taya shi da cewa" Kuma daman in babba bai ji kunyar hawa jaki ba. To shima jaki ba zai ci kunyar ka da shi ba. Ke kika zubar da girman ki, ban ga laifin duk wanda ya taka ki ba. Me ya sa ita Zuwaira ba a yi mata ba? Saboda ta kama kanta ba ta kuma zama ji da jiyarwan da kika zama ba." Sai ta ƙara fashewa da kuka ta kasa mgana ita da Gimbiya sai kunya.

"Ba kuka za ki yi ba haƙuri zaki juya ki ba ta ki kuma janye kalaman da kika yi a kanta. In ba haka ba zan bar Tafida ya ɗau matakin da ya dace." Kawu Sa'adu ya faɗi haka Anty Bahijja da ta san akwai ranar da za ta zo ta ba ni haƙuri da ba ta aikata ba abin da aikata ba. Kowa kuma ita ya ba ma rashin gaskiya har su Maman farko dole ta juya ta ba ni haƙuri na ƙi mgana.

"Sadiya ki yi hakuri kin ji ko? In sha Allahu ba za ta ƙara ba."

In ji Nene sai na ga girmama maganar Nene shi ya sa na ce na yafe mata amma sai dai na ce"kin ci darajan Yusuf da Nene shi ya sa na yafe miki." Gimbiya ma aka ce ta ba ni haƙuri ta ba ni haƙuri Hajiyar Tafida ma ta ba ni haƙuri na yi shuru ban yi magana ba itama.

"Ki yi hakuri kin ji ko?

Yallaɓai ya faɗa a hankali ya na kallona.

"Zan haƙura amma sai na cire mata kokwanto." Kafin ma ya yi mgana na zazzage jakata na fito da mgungunan a tsakiyar falon.

"Ga mganin da ta ce Inna ta ta kawo min mganin sanyi na wanke mahaifa ne na ga ta karɓo ma yarta yana yi shi ne na ba da kuɗi ta kawo min. Wallahi tallahi ban taɓa karɓan wani abu da sunan na asiri domin na cutar da mijina ko makusantansa ba."

Na karishe faɗa ciki son na yi kuka.

"Ba ki yarda da ni ba ne? Yallaɓai ya katse ni, jin na ce zan Kira Inna Mariya ta yi mgana anan wajen.

"Ba sai kin kirata ba Na yarda da ke duniya da lahira Sadiya."

"Ba kai ba. Kowa ma saboda ya cire tantama a kaina."

Kawu Sa'adu ya ce a bari na kira hakan da na kyau. Nan ta ke na kirata na saka ta a handfree bayan mun gaisa sai na ce. "Inna Mariya wai mganin da kika karɓo min mganin me ya ke yi wata ke tambaya ta?

"Ya na wanke mara sannan ya na mganin sanyi sannan ya na wanke mahaifa ko mace ta daɗe ba ta haihu ba in dai ta yi amfani dashi ana dacewa. Ya na da kyau sosai kin fara amfani da shi ne?

"Ban fara ba amma zan fara."

"Ki fara Sadiya in sha Allahu za ki da ce"

"Na amsa mata da Amin sannan muka yi sallama kai tsaye na kalli Gimbiya kafin na ce" Ina so ki sani ko ban taɓa haihuwa ba, ba zan yi shirka ba saboda ni na fito gidan tarbiya. Ballatana na haihu Saudatu ƴaƴana biyu ko a haka ubangiji ya bar ni ya gama min komai saboda haka ki sani ko duniya za ki tara abin da za ki haifa ba zai taɓa tsole min ido ba. Sannan duk da ban yi dogon zama da ke ba, ba zan yanke miki hukunci ba, zan yi miki kyakyawan shaida da uziri ina fatan ko anan gaba ki rika yi ma mutanen zaton alheri ba na sharri ba. Na yafe miki Allah ya kyauta na gaba."

Na faɗa ina mai kauda kai, sai ga shi kunya ya gama lulluɓeta. Kawu Sa'adu ya ce" Gaskiya ne ya kamata mu riƙa kyautatama junan mu zato."

Nima ya saka ni na ba ma Anty Bahijja haƙuri, na ba ta ba domin ina ji a raina na yi mata wani abun ba sai domin yi masa kara tun da shi babba ne kuma bai kamata na watsa masa ƙasa a ido ba.

Sannan ya sha ta layi tsakanin Bahijja da Ma'u ya ce kar ta ƙara zuwa gidan nan bai hana su haɗu can dangin mijinta ba amma in aka sake jin wata mgana ta bullo ba za su hana ni na ɗau matakin da ya kamata ba.

"Nima Kawu ka faɗa mata kar ta ƙara shiga harkan gidana da matana. Ba Saudatu ba Sadiya ba. Ta kama girmanta a matsayinta na yayata su kuma su girmamata a matsayinta na yayar mijinsu."

In ji Yallaɓai.

"Fakat"

Kawu Abba ya faɗa, Kawu Sa'adu ya ce gaskiya kar ya ji kar ya ƙara gani. Har Anty Maimuna itama an ce kowacce ta ji da kanta ba ruwansu da matan ƙannensu. Mazan su ne dolen su su tsaya a kansu. Itama Gimbiya Yallaɓai ya ce ya yi mata tsakani da Anty Bahijja bai ce ya raba su ba amma ta sani su yi zumumcin su kawai in har wani munafunci ya sake fitowa sai ta raina kanta da sauri ta ce ba za a ƙara ba. Kafin a tashi Kaawu Abba ya gyara zama ya na faɗin"

"Na so sai mun gama daidaitawa da Marwa kafin na kawo mganar amma tunda maganar ta yo kutse, shi kenan ni na ga ɗiyar Yayar Sadiya ina so ga Tafidan nan shi ya rakani gidansu na nemi izini ko Sadiyan ba ta sani ba, ina so kowa da ke nan ya shaida nan da lokaci kaɗan zan tura maganata domin a yi maganar aure. Wanda bai so abin ba ya yi shurun sa kar ma ya saka albarka tunda da saka albarkarshi da rashin sakawan duk ɗaya ne ni a wajena."

Kawu Sa'adu ya ce duk lamarin bai kai haka ba. Abu dai ya riga ya faru a yi haƙuri a tari gaba tun da sun ba da haƙuri sun ce ba za su ƙara ba. To a yi musu afuwa. Da haka taron ya tashi, ban ko tsayawa ba na ce zan koma gida Yallaɓai ya ba ni kuɗin adai-daita muka fita tare da su Hauwa suna ta cewa Anty Bahijja ta sha kunya, da ga ita har Gimbiyar ni dai ban ce komai ba. Duk da na ɗan ji sanyi da Yallaɓai ya tsaya min amma ba a biyani ba tunda ba a bar ni na kai hukuma ba.

Gidana na koma amma na kira Ya Aina na faɗa mata, na ce an yi muui mgana sun nemi gafara Amma sun shiga tsakanina da su gabaɗaya.

"Hakan ma ya yi. Hamza ya ce min ya na hanya ma."

Na ce Allah ya kawo shi lafiya. Tuɓewa na yi na fara gyaran gidana da ya yi datti. Bayan na gama ɗora girki, taliya na yi da miya, kayan miyan ma sai da na kira Yallaɓai ya aiko min da cefanen kayan miya shi na ya yi bilandin na yi miya da kifi.

Da su Jidda suka dawo makaranta suka ganni suna ta murna na sha labari wajen Baby. Jidda na faɗin suna ta tambayana Abba ya ce wai na yi tafiya ne ni kaina na ji daɗi da na gansu ashe na yi kewarsu ban sani ba. Da su na yini a gidana suka ɗebe min kewa sai bayan isha'i Yallaɓai ya shigo da kayan marmari da yawa a leda.

*Janafty* *TKG019019*

Da yake na san Yallaɓai ba ya son cin taliya a cewarsa wai ba ta ƙosar dashi. Shi ya sa sai na dafa masa shinkafa mai karas da kabeji. Mu kuma sai muka ci sauran taliyan da ta rage ni da yara. Kayan marmarin da ya kawo rabi na ɗibar mana na wanke muka ci, rabi kuma na saka a cikin frizer.

Sai da Yallaɓai ya yi wanka ya sauya kaya zuwa wasu sauƙaƙku na zaman gida sannan ya ci abinci ya na cin abincin ina gefen shi amma da ka ganni za ka fahimci sai a hankali saboda na zama wata shuru shuru kamar wata mara lafiya. Duk da na saka kaya masu kyau amma ban yi kwalliya ba fuskata kawai in ka kalla za ka fahimci damuwa ƙara ƙara tun da har damuwar ta bayyana.

Ya na gama cin abinci bayan na tattara komai na mai da kitchen yara kuma na ce su shiga ciki su kwanta. Nan na bar Yallaɓai a falo ya kunna kallo ni kuma sai na shiga ciki tiolet na fara shiga na kama ruwa sannan na fito na yi shirin kwanciya. Har na ma kwanta na rufe ƙafafuna zuwa saman cikina da bargo na kuma rage hasken ɗakin sannan can na ji shigowar Yallaɓai shima kayan jikinsa ya cire ya saka na barci sannan ya biyo ni kan gadon. A bayana ya kwanto ya na mai riƙo hannuwana da na harɗe ƙirjina da su, ya fara ɗan shafawa kaɗan kaɗan lokaci ɗaya ya na kiran sunana.

"Sadiya ta."

"Uhm"

Na amsa a cikin maƙoshina, sai da ya ɗan yi jim kafin ya cigaba da faɗin" Ki yi haƙuri kin ji ko? Sai na gyaɗa masa kai ba tare da na yi magana ba. Haƙurin kam tabbas zan yi amma ba na jin zan iya mantawa da abin da suka yi min har gaban abada kuwa.

"Ki yafe musu. Musamman ma Daughter ta yi nadama sosai kuma ta faɗa zugan Anty Bahijja ne sai sheɗan ya yi tasiri a kanta."

Ita ce sheɗaniyar kanta na faɗa a cikin raina a fili ko numfashi kawai na fesar ba tare da na sake yin wata mgana ba.

"Ki yi haƙuri ki manta komai don Allah" Nan ma shuru na yi sai ya leƙo fuskata lokaci ɗaya ya na faɗin" Kin ji ko? Sai na kaɗa kaina kafin na ce" Na ji. Ya wuce."

"Ba irin wannan wucewan ba. Ina so ki yafe musu sannan ki manta da komai kar ki ce za ki riƙe su a cikin ranki. Sannan kar ki ce za ki daina zumunci da su. Sun zama dole a garemu Sadiya. Daugther matata ce Anty Bahijja kuma yayata ce ita ta saki nono na kama. Kin ga ke ma sun zama dolen ki, ina so ki cire abin a ranki in kun haɗu ki mu'amalance su kamar yadda kika saba."

Kawai sai na yi shuru ina sauraran Yallaɓai. Haba ai maciji sau ɗaya ya ke saran mumini ya yi hankali. Shi a tunanin shi zan ƙara sakar musu ne! Har abada ai sun yi min hankali sannan na yi karatun duniya na ƙara shiga taitayina.

"Ba ki ce komai ba?

Ya sake tambayata sai na gyara kwanciyata kaɗan duk da har lokacin bai bar jikina ba sannan bai sake ni ba.

"Ban yi maka alƙwarin zan cigaba da mu'amala da su kamar baya ba. Sai dai na yi maka alƙwarin zan manta komai a hankali ba da gaggawa ba."

"Me ya sa?

Sai da na ɗago na kalle shi ta hasken da ya ke shigowa ta window ɗin bedroom ɗin mu. Sannan na koma na kwantar da kaina a saman filo ina faɗin .

"Saboda sun yi min hankali. A kan su na ƙara sanin karatun duniya. Ka yi haƙuri amma ba zan iya sake sakin jiki da su ba."

Ya buɗe baki zai yi magana na yi saurin tare shi.

"Kar ka matsa min Yallaɓai. Wataƙila a hankali in na manta na iya kallon su a matsayin kallon da na ke yi musu a baya. Shi ya sa na ce kar ka matsa min don Allah."

Sai ya yi shuru bai ƙara magana ba. Sai dai ya karkato ni ina fuskantar shi, sumbatar goshina ya fara har ya gangaro saman bakina ya fara sumbatata. Duk da ba na cikin mood ɗin amma ban ture tayin shi ba. Sai nima na tallafe shi muka samar ma junanmu natsuwa ba mu wani daɗe kamar yadda muka saba ba daga shi har ni ɗin ba mu da wani karsashi da baƙatuwa shi ya sa lamarin bai yi mana armashi kamar yadda muka saba ba. A daran muka tsarkake jikin mu, shi ya rigani barci ni kam na daɗe ban yi barci ba sai wajajen biyu saura na dare na samu barci ya kwashe ni.

Washegari kuma daman Asabar ne. Ina idar da sallar asuba na fara azkar kenan barci ya ɗauke ni a nan saman darduma Yallaɓai ne ma ya tashe ni ina layi na haye gado. Ba ni ta shi ba sai da wayar Ya Hamza ta tashe ni. Sai bayan mun gama wayar ne na duba agogon wayata na ga har sha ɗaya saura na safe ai sai na diro daga kan gado na fita can falo yara na iske ba su nan sun tafi hadda. Sai Yallaɓai kaɗai ne a gidan ya na aiki a system ɗin shi.

"Ina kwana."

Na faɗa lokacin da na shiga falon shi na gan shi zaune ya na aiki.

"Kin tashi lafiya?

Ya faɗa ya na mai ɗagowa ya na kallona.

Sai na jinjina masa kai. Ban tambaye shi yara ba saboda na san sun tafi hadda ne. Na juya zan bar falon na ji shi ya na ce min." Tea suka sha sai ƙwai da Jidda ta soya musu suka ci suka tafi makaranta." Sai na gyaɗa kaina daga nan kitchen ɗin na shiga wato aikin na manya ne an yi kaca kaca da kitchen ɗin da jiya na gama wahalan gyarawa. Haushi duk ya kamani mu ma tea ɗin na sake dafa mana sai na fere mana doya muka sha dashi. Na so na ɗan gasa mana buredi sai kuma na fasa ganin rana ta yi, muna cikin karyawa na ce ma Yallaɓai ina son zan je Ɗorayi.

"Ki shirya in zan fita sai na sauke ki kafin na wuce office"

Yadda bai tambayeni me zan je ba, nima ban faɗa masa ba saboda na san ya san ba zai wuce maaganar Ma'u ba. Muna gamawa Yallaɓai ya fara yin wanka ni kuma sai na ɗan tsaya na gyara kitchen ga himilin wanke wanke. Saude ba ta nan fa ta tafi garin su ni kaina ban san ta tafi ba sai daga baya. Na yi ta faɗa da cewa ana tsakar makaranta ai ba a tafiya, ita kuma Balaraba sai ta ce wai auren ɗiyar ƙanin babansu ake yi Sauden ta matsa sai ta je. Ni dai fata na kar su je can su yi mata aure tun da can ƙauye sokoto ne garin baban na su.

Wanke wanke kawai na yi sauran ayyukan na ce in Jidda sun dawo ta ɗan gyara gidan. Yallaɓai na son tafiya tun da ana ta kiran shi ya yi baƙi. Mun bar gida wajen sha ɗaya da rabi na rana ya kai ni ɗorayi bai ko shiga ba ya wuce.

Na je na iske Ya Hamza da Gwaggo a falon Alhajinmu ne suna hira nima sai na bi ayarin su. Bayan mun gaisa da Alhaji da Gwaggo ne na juya ina gaida Ya Hamza ina tambayan shi ya wajen su Khaleesat?

"Duk suna nan lafiya. Sun ce a gaishe ku."

Mun ɗan yi hira sama sama a kan sanyin da ake yi a can zaria. Sai ya kalleni kafin ya ce" Jiya an yi zama a can gidan Baban su Jiddan? Sai na gyaɗa masa kai kafin na fara bashi labarin abin da ya faru. Gwaggo na gefe ta na ji ita da Alhajinmu.

"Ka ji ko Alhaji.? Ma'u sheɗaniya ce. Ta haɗa husuma ta na neman wargaza zaman lafiya a gidan auran Sadiya."

Ya Hamza ya faɗa cikin ɓacin rai ganin haka ya sa na kalli Alhajinmu shi da Gwaggo da suka yi shuru sun kasa mgana na ce" To ita da ta ce ma Anty Bahijja a yi hankali da ni. Ina shige shigen malamai zan iya yin komai domin na ga bayan cikin Amaryan Yallaɓai." Gwaggo ta saka salati tana tafa hannu. "Kai Ma'u ta yi asara. Ta kuma ba ni mamaki. Wallahi tun da na ji abin da ya faru na kasa suƙuni kawai mamaki na ke yi me kika yi ma Asma'u da zafi haka da ta nemi tozarki haka Sadiya?

"Me kuwa na yi mata Gwaggo? Na faɗa muku tun a baya kan fasa auranta da Ya Hamza ne daman ta ce na jira zan gani. Kuma ta daɗe ta na yi min shige da fice yanzu dai burinta ya cika akaina ta yi min sharri ta kuma yi sa'a na tozarta."

"Za ta ko ci ubanta. Har Baaba sai an kira ta zo domin a kawo ƙarshen makircinta."

Ya Hamza ya faɗa cikin jin haushi Gwaggo ta ce haka ya kamata a matseta sai ta faɗi dalilinta na aikata abin da ta aikata. Alhajinmu na zaune amma ƙala bai ce ba sai kaɗa kai kawai ya ke yi lamarin ya gama ba shi mamaki. Muna cikin magana da Ya Hamza Alhajinmu ya kira sunana na amsa ina mai kallon shi.

"Ki faɗa min tun farko yadda lamarin ya faru."

Readers Also Read