Turken gida book 3 cmplete - Chapter 43
Turken gida book 3 cmplete Chapter 43: Turken gida book 3 cmplete Chapter 43. "Me ya faru?
3,359 words
"Me ya faru?
"In kin zo za ki ji "
Ya faɗa sannan ya kwashe wayar ina jin haka na san ba lafiya, ina jin haka ban tsaya ba na yi musu sallama tare muka fita da su Ya Aina na ajiye su a juction na wuto gida. Abin da ya ba ni mamaki Yallaɓai na haraba yana jirana shi da Gimbiya kamar yaƙi.
Ina gama parking ɗin motana na fito Gimbiya ta taroni da cewa" Maman Jidda baki faɗa ma Baban su Khalipa mun sauya tsarin kwanaki kwana ba ne? "Ban faɗa masa ba me ya faru? Na faɗa ina kallonta saboda mamakin abin da ke faruwa.
Yallabai na kalla kawai sai na ga ya juya zai shiga shashen Rabiatu Gimbiya ta bishi tana faɗin"Ai ka ji sai ka dawo bangarena sai gobe ne za ka koma mata."
"Ba zan koma ba. Wannan tsarin ku ne ba nawa ba, nawa wanda na sani jiya na shiga ɗakin ki, yau da daddare na fita zan kwana a bangaren Rabi'atu."
"Wallahi ba ka isa ba"
Gimbiya ta faɗa cikin ɗaga murya ta juya zai shiga ta sha gaban shi har tana riƙe masa riga. Ni dai sai na yi tsaye kawai ina ganin ikon Allah.
"Ba ni hanya in wuce."
"Ba fa za ka koma shashenta ba sai gobe wallahi "
"To ni kuma yau a nan zan kwana in kin isa ki hana ni "
"Ni kuma wallahi in har ka kwana a ɗakin yarinyar nan Da haƙƙin kwana na Allah ya isa ban yafe ba"
Gimbiya ta faɗa har tana shan wallahi. Shi kuma Yallaɓai ya fizge rigar shi ya tureta gefe ya shiga yana faɗin" Da sauki tun da ba tsine mini za ki yi ba " Ta kwashi kururuwa za ta bi shi ciki, shi ko yana shiga ya rufo ƙofar ta ciki sai ta fara bugu tana kiran sunan shi.
"Yusuf ni za ka wulaƙanta? Wallahi in har dai ka kwana a ɗakin nan ban yafe maka ba tun da dai haƙkina ne yau "
Kawai sai ta fashe da kuka ni wallabi ban saba ganin haka ba yasa sai jikina ya yi sanyin da na kasa motsi. Ganin maigadi na gefe yana kallon komai ita kuma tana ta kuka tana buga ƙofa tana Allah ya isa ba ta yafe ba. Yau ba Baban Khalipa Yusuf ne kai tsaye. Ƙarisawa na yi ina mai saɓe da yumna da ta fara barci a mota na ƙarisa wajen Gimbiya ina kiran sunanta amma ba ta ji na.
"Haba don Allah wannan ba girman ki ba ne. Ki zo mu tafi bangaren ki."
Amna bata saurareni ba, ganin kamar ba ta cikin hayyacinta yasa na saka hannu ɗaya na rike ta ina fadin" Megadi na ji fa kar ki jawo mana mutane don Allah."
"Gwara ya ji. kowa ya ji cewa ba ya adalci. Maman Jidda yau fa yana dawowa shashen yarinyar nan ya tare na shiga na yi masa mgana a bangarena yake ya fara masifa shi bai san da haka ba. Ita kanta ta ce masa kin faɗa mata amma bai yarda ba ya kira ɗin ma ya tabbatar daga bakin ki amma ki duba fa a gabanki ya shige ciki saboda zalunci har yana rufe mini ƙofa saboda tozarci?
Ta faɗa tana kuka, abin da Yallaɓai ya yi bai kyauta ba amma ita ta ja ma kanta, da ƙyar na lallasheta na ja ta bangarenta. In da Allah ya taimaka yara suna bangarena tare da Baby. Haka na zauna ina ba ma Gimbiya haƙuri amma tana ta kara shan wallahi in dai ya kwana a bangaren Rabi'atu ba ta yafe masa ba
"Ki yi hakuri mana. Ki yi masa uziri tun da bai sani ba."
"Da bai sani ba amma ai yanzu ya sani."
Ta faɗa tana jan majina.
"Ki yi haƙuri zuwa da safe sai mu yi magana gabaɗaya "
"In yana so na saurare shi to ya fiti daga ɗakin yarinyar nan in kuma ya kwana wallahi ba zan saurari kowa ba "
Jin haka yasa na ɗaga waya na kira Yallaɓai sai da ta katse na sake kira ya ɗaga ko mgana bai yi ba daga gani ranshi na ɓace ne.
"Yallaɓai don Allah ka fito mu yi magana."
"Ba zan fito ba. Ke ma ina mai ba ki shawara karki dame ni in ba haka ranki ya ɓaci."
Ya faɗa a fusace.
"Ka yi haƙuri ka fito don Allah."
"Ta ce Allah ya isa to zan kwana Allah ya bi mata haƙƙin ta kamar yadda ta ce."
"Ba za a yi haka ba. Ka dai yi haƙuri "
Da ƙyar na samu ya anince zai fito mu yi magana da ya fiton ma cewa ya yi ba zai shiga bangaren Gimbiya ba jan shi na yi zuwa bangarena mu ka yi magana, ina ba ma Yallaɓai haƙuri yana yi mini tsawa.
"Ina ruwan ki? Ki ƙyaleni kar ki dane ni "
"Kar ka yi haka. Ka je ka kwana ba gobe ba ne shike nan!
"Ba zan kwana ba "
Ya katse ni, sannan ya cigaba da faɗin" Kina faɗa mini wai ta fada za a dawo kwana biyu ni kun faɗa mini ne? Kuma ma haka za ta zo tana mgana da ni gaban Rabi'atu tana yi mini rashin kunya?
"Ka yi haƙuri ai ta fada mini laifina ne da ban faɗa maka ba"
"To kema ki fita idanuwana. Ke ce ke aurana da za ki riƙa yanke hukunci a gidana ba tare da sanina ba?
Ai ina jin haka sai na yi shuru, ya riƙa masifa har da rantsuwan zai gyara bangaren shi da yanzu sai dai bishi can in ya ga dama ya kori kowa ya kwanta shi kaɗai.
"Ka yi haƙuri '
Nawa kenan ban haƙuri, dakyar na samu ya amince zai kwana a ɗakin Gimbiya.
"Ka yafe mata Allah ya isa da ta yi sheɗan ne "
"Ke ina ruwanki da abin da zan yi mata? Sadiya kina mini abin ba na so wai nan gidan gidan ki ne ko gidana?
Ina dariya na ce"Gidanmu dai Ranka ya daɗe " Sai da na saka shi dariya. Na samu dai ya shige ban san yadda suka ƙare ba, yara ma a bangarena suka kwana da safiyar Allah Gimbiya ta bugo mini waya tana sharban majina wai da na sani na ƙyale Yallaɓai ya yi kwanciyarsa a in da yake so.
"Tun da ya shigo ya ke faɗa sai abin da ya manta bai faɗa mini ba. A falo ya kwana a kan kujera da asuba da na gaishe shi wai in na ma sake gaishe shi zai yi mini Allah ya isa."
Ni gabaɗaya ma sun sakani a tsakiya. Yallabai tun bakwai na safe ya fita na kira shi a waya Yace kar na dame shi kamar ya san maganar Gimbiya ne ya taka mini burki.
"Sadiya in dai ba ke kika auro mini Saudatu ba to ki fita a mganata da ita. Tsakanimmu ne ba ruwanki."
"To ta zo tana mini ƙorafin kai ma kace in ta sake gaisheka Allah ya isa."
Kawai sai ya yi tsaki kafin ya ce" in ta sake zuwa ki kore ta. Ki faɗa mata ni na ce ba ruwanki"
Zan yi magana ya tare ni da cewa"Wallahi kema zan yi miki Allah ya isa in baki ƙyaleni ba haba." Ai ina jin haka na kama kaina daga ƙarshe ya ce in na sake yi masa magana wallahi zai yi mana yaji kuma in ya tafi ba zai dawo ba sai ya ga dama."
"Abin har ya kai haka? To Allah ya huci zuciyarka "
Ya ce Amin a fusace ya kashe wayarsa tun da na ji haka na cire kaina a ciki. Da Gimbiya ta dawo tana faɗa mini wai ita Baban su Khalifa zai wulakanta saboda wata zaunar da ita na yi na faɗa mata gaskiya da cewa ta yi haƙuri ta kauda kanta a kan Yallabai da Rabi'atu in ba haka ba wata rana komai zai iya faruwa. Ta koma gefe ta zama yar kallo amma ba ta ji ba. A cikin kwanakin ma sun sake wata rigima wai in ya shiga ɗakin Rabi'atu da daddaee zai yi mata sallama yana ɓata lokaci, rigima suka yi sosai Gimbiya ta sake masa Allah ya isa a kan haƙkinta shi kuma ya ce ya gaji ya ɗaga waya ya kira Nene ya faɗa mata. Sai da Nenen ta zo gidan sulhu ne na ji labari gabaɗaya ta taramu ta yi mana faɗa shi dai ta jadadda masa ya yi adalci ne.
"Nene ina iya bakin ƙoƙarina. Saudatu ta cika ƙorafi sannan ba ta da hakuri tun da na yi auren nan ba ta bar mu mun zauna lafiya bq"
Ita kuma tace me ya sa yake mata rashin adalci in yana da gaskiya ai ba za ta riƙa mgana ba. Rabi'atu dai shuru bata mgana, Yallaɓai ya rantse ya ƙara rantsewa in Gimbiya ta sake masa Allah ya isa zai dauƙi mummunan mataki a kanta Nene ta yi mata faɗa ta kuma sakata ta bashi haƙuri nima ta yi mini faɗa da nariƙa nuna ma Gimbiya wani kuskureta in ta yi wani abun
"Ko ta nuna mata wannan zata ji ta ne? Wallahi Nene Sadiya ba ta taba ɗaga mini hankali da zan auero Saudatu ba a wannan auren ma bata ɗaga mini ba. Amma kin ga wannan y'ar taki? Haƙuri na ne ya ƙare amma ta yi mini diɓar albarka ba adadi ina shanyewa."
Nene dai ba ta bar gidan ba sai da ta yi musu sulhu. Kwana biyu kamar an samu canji. Rabi'atun ma na nuna mata ta riƙa bin Gimbiyae har ɗaki tana gaisheta. To na ga tana shiga, amma fa kishi Gimbiya take yi da ita kamar hauka kishin da take yi da ni ne ya koma kan Rabi'atu tun da ta ga Yallabai a gaban mu ma yana nuna mata rawan jiki. Rigima ta lafa sama da wata ɗaya kawai a wani dare muna kwance da Yallaɓai yake faɗa mini ya siya ma Rabi'atu mota saboda zirga-zirgan makaranta cikin satin nan za a kawo motar. Kamar zan yi masa mgana na ce ya manta da Gimbiya! Domin ko kwanaki ta yi masa mganar ya sauya mata mota ko ciko ne ya yi mata ta saida tata ta siya wata ya ce sai zuwa gaba. Kar yace ina baƙin ciki ya sa ban ce komai ba. Mun yi maagana da kwana biyu mota ta iso, Musbahu ya tuƙo ta ya kawo ta gidan Corolla ce Gimbiya ta ɗauka motarta ce har ta fara murna sai gogan ya ce na Rabi'atu ne. Gimbiya ta cika ta yi fam Rabi'atu ta yi ta santin mota tana murna nima dai na fito na gani na taya murna lafiya lau muka kwanta da mota amma ko da garin Allah ya waye gabaɗaya an yi ma gilashen motar nan rugu rugu.
*TKGB3020A*
Follow this link to join my WhatsApp group: https://chat.whatsapp.com/LgZezgwmkmy8ZCuNsHiNxX
Assalamu Alaikum Fanmily, mun fara saro muku kayan Kitchen ko wani nau'i, duk abin da kuke bukata na gyaran Kitchen ɗin Amarya da uwargida duk za ku same su a JANAFTY KITCHEN ITEMS, kayan mu masu kyau ne da inganci sannan za ku same su akan rahusa, muna aikawa da kayanmu ko'ina a falin Nigerian nan. Domin karin bayani ku tuntuɓe mu ta waɗannan lambobin kamar haka. 09069067488. +234 706 234 9732
Muna maraba da masu siya ɗaya ko sari🥰
Ni dai har ga Allah bayan fitan Yallaɓai masallaci na ji kamar ƙaran fashewar abu amma sai ban mayar da kai ba tunani kunnuwa ba su jiyo mini sautin daidai ba. Ashe ko acikin gidan ne tun da Yallaɓai ya ce har ya fita sallar asuba motar na nan lafiya ba abin da ya same ta. Kenan bayan fitan shi ne koma me ya faru ya faru ɗin.
"Innalillahi ko jifa aka yi ne daga waje Yallabai?
Na faɗa ina riƙe baki saboda duk mun fito haraba har da su Baby gabaɗaya ana ta jimami amma Gimbiya ba ta ko buɗe ƙofar shashenta ba.
"Wani jifa? Wannan aikin da gangan ne, da kuma niyya aka yi shi an fasa gilashin gaba an fasa gilashin window just imaging fa Sadiya"
Ya faɗa yana zagaye motar yana dubawa, Rabi'atu ta yi tsaye da hijabi ta kasa magana wannan shi ne ta ga samu ta kuma ga rashi.
"To waye ya yi wannan aikin?
"Ko waye ma za mu sani yanzu." . Yallaɓai ya nufi wajen Megadi Yumna ce ke zillo daga hannuna ya ce kar na sauke ta saboda gilasan da ke watse a wajen.
Mu dai muna tsaye da ni da Rabi'atu da Baby ina riƙe da Yumna muna jajantawa Baby faɗi take yi" Za a iya gyara motar Anty Rabi'atu kar ki damu." Nima ganin ta damu ina ta ce mata kar ta damu za a ce a saka wasu gilasan ba damuwa ba ce ni fa har tunani na yi ko tsawa ce sai na tuba ba damuna muke ba, amma ban taba kawo ma kaina Gimbiya ce ta aikata wannan ɗanyen hukuncin ba.
Muna nan tsaye sai gani kawai muka yi Yallaɓai ya dawo daga wajen megadi a fusace kamar zaki ya zo ya wuce mu ina ts kiran shi amma bai saurareni ba. Kofar shashen Gimbiya ya fara bugawa kamar mahaukaci yana kiran sunanta da tsawa abin da ban taɓa ji ba, ina jin ko ita Rabi'atu ba ta taɓa jin muryan sa cikin fushi haka ba.
"Saudatu!. Saudatu! Saudatu!"
Haka yake kiranta lokaci ɗaya yana buga ƙofa kamar zai balla na ruɗe na biyo shi ina faɗin" Subhanallah lafiya Yallaɓai? Ko kallo na bai yi ba sai ma ya matsa baya kaɗan ya fara tokarin ƙofar da ƙafarsa. "Haba Yallaɓai wai miye haka ne?
Na faɗa ina ƙoƙarin rike shi ya fizge jikinshi yana ce mini na matsa baya.
"Ɓalla ƙofar kuma za ka yi?
"E ina ruwan ki? In ma na ɓalla ma ba gidana ba ne?
Hake ya ce mini a tsawa ce sai na yi shuru kawai na kasa mgana ina kallon shi.
"Ki koma baya in ba za ki yi zama yar kallo ki koma bangaren ki "
Na sake yunƙurin mgana ya kira sunana a tsawace kafin ya ce" Kar ki sake yi mini mgana." Tsawa ya yi mini sai da na yi baya Yunma ta tsorata ta fashe da kuka ai sai na yi gefe ina maimaita innalilllahi a ƙasan raina ina tunanin meke faruwa ne? Ganin ni kaina an yi mini tsawa ya sa Rabi'atu ma ba ta matso kusa ba, balle Baby da ta maƙale a bayanta jikinta na rawa.
Duk wannan bugun da hayaniyar Gimbiya na ji ba ta buɗe ba, har ta window ya je yana kiran sunanta sai da ta ga dama sannan ta buɗe bayan har handle ɗin kofar sai da Yallaɓai ya kar ya shi wajen jan shi, ta fito daga ita sai rigar barci doguwa a cikinta da hula mai raga raga ta fa gan mu duk tsaye ga uban gayya na huci kamar zaki amma duk ba ta sha jinin jikinta ba.
"Topha! Lafiya na ga an taru a ƙofar bangarena?
Ta fada tana mai kallon mu ɗaya bayan ɗaya. Mamaki ya hana ni magana shi kuma Yallaɓai ban san dalilin ba ina tunanin shima dai mamakin ne sai cije baki yake yi alamun yana ƙoƙarin sarrafa ɓacin ran shi ganin haka yasa na yi saurin tare ta da cewa. "Ke yanzu duk ba ki ji abin da ke faruwa ba? "Ban ji ba me ya faru? Ta faɗa cikin halin ko in kula.
Motar na nuna mata ina faɗin" Motar Rabi'atu ne muka wayi gari an yi mata haka' Sai ta wani kama baki kamar na mamaki da firgici kafin ta ce" Subhanallah garin ya ya haka ya faru? "Shi ne ake son sani yanzu" Na bata amsa sai na ga ta wata dariya ta ce" Ikon Allah! To ko aljanu ne suka yi haka?
"Aljanu ko ke da kanki?
Yallabai ya katse mata mgana a fusace, sai na kalle shi jin abin da yace ita ko sai ta ware ido kafin ta ce" Ni kuma? "E ke" Ya faɗa yana takawa kusa da ita ƙokarin kare rabin jikinta take yi da ƙofar ya saka ƙafa ya tokari ƙofar ta buɗe sai ta yi baya da sauri tana faɗin" Ban gane ba daga ganin abu sai kawai ka ce ni ce na yi? Ina ruwana? Ta faɗa cikin rashin kunyar da ta saba da shi a kwana biyun nan.
"Saboda ke ɗin ce mai muguwar zuciya a gidan na."
Ya faɗa yana mai kallonta kamar ya jawota ya fara dukanta a yanayin shi.
"Oho dai kai ne mai mugun zuciya wallahi. Ban da rashin adalci tun yaushe na ke bin ka da ka saiya mini mota amma kaƙi shi ne ko kunya za ka siyo ma matarka mota ni ba ka siya mini ba! Hakan da ka yi adalci ne? Wallahi kai ne ba ka da zuciya mai kyau kuma duk cutata da ka yi saboda wannan yarinya Allah na sama."
"Bum!!"
Ya saka hannu ya buge mata baki kafin ta karisa magana sai da na ji tsoro ganin abin da ban taɓa gani ba. Yallaɓai na kai hannun shi jikin mace.
"Tun kafin Megadi ya tabbatar mini da ke ce da man naa ji a zuciya ke ce kika yi haka? Ni za ki yi ma asara saboda shegen kishin ki na banza da wofi?
"Wallshi da man na ce sai dai kowa ya rasa"
Ta sake faɗa har tana rantsuwa sai a lokacin na gama fahimtar komai wato dai Gimbiya ce ta yi wannan ta'asan.
"Ba ka yi adalci ba sai ka siyo biyu in kana so a zauna lafiya ko ka fara siya mini bayan an kwana biyu sai ka siya mata amma ko kunya ba ka ji ba ka je ita ka siya mata ni kuma ko oho? Wallahi ba ka isa ba in dai ina gani ba wanda ya isa ya yi mini rashin adalci ban yi magana ba."
"An yi miki rashin adalci ki yi duk abin da za ki yi"
Ya faɗa a fusace kafin ya ce" Kuma wallshi ki sani ba ni kika yi ma asara ma kanki kika yi mawa. Sai kin biya duk abin da kika bannatar kin ji ma na rantse."
"Wallahi ba zan biya ba. Rashin adalcin ka ya jawo maka asara " . Ta faɗa har tana rikr kugu ina so na shiga na yi magana amma ina tsoron kar ya haɗa da ni amma hayaniyarsu ta fara yawa ga su Khalipa har sun fito suna tsaye sannan ita bakin ta yaƙi yin shuru shima haka tana fada yana faɗa. Ganin haka yasa na ce ma Baby ta tattara yaran su koma shashena. Rabiatu ma da na duk ta tsorata na ce su shige ciki sai da na samu sun shige ciki sannan na koma wajen su Gimbiya abin har ta kai ga tana kiran shi Azzalumi kuma sai Allah ya kama shi.
"Alhamdulillah na ji ni azzalumi kuma kin ga ba za ki cigaba da zama da mai zalunci ba. Zo ki fice mini daga gidana Saudatu wallahi nima na gaji da zama dake."
Jin haka yasa na yi zaraf na shige tsakaninsu ina faɗin" Haba Yallaɓai." "Ta zo ta fice mini dags gida na ce ko! Ya sake maimaitawa, ita kuma jin haka sai jikinta ya yi sanyi ta fashe da kuka.
"Ni yau kake kora a gidan ka Yusuf?
"Na kore ki gidan ki ne ko gidana? Wallahi na gaji dake da halin ki, da man tun tuni ya da ce na kore ki, kin fara yi mini asaran dukiya wata rana rai za ki kai ma hari."
"Duk abin da ya faru kai ne sila. Domin da ka yi adalci da haka ba ta faru ba maimakon ka yi nadama amma sai ka kore ni? Ni za ka tozarta a kan wancan yarinyar?
"Ba sunanta yarinya ba. Sunan ta Rabi'atu ce matatace kamar yadda kike matata. "
Gimbiya ta sake sakin kuka kafin ta ce" Saboda ita yau kake kora ta? "E saboda ita ne domin ita ba mahaukaciya ba ce kamar ke"