Kenza eBookz

Turken gida book 3 cmplete - Chapter 49

Turken gida book 3 cmplete - Chapter 49

Turken gida book 3 cmplete Chapter 49: Turken gida book 3 cmplete Chapter 49. "To ni yanzu me ye nawa a cikin wannan mganar?

3,336 words

"To ni yanzu me ye nawa a cikin wannan mganar?

Na tambaye shi ganin kamar ni ya fi jin haushi.

"Naki shi ne ba ki yi hukuncin kan gaskiya ba, kin goyi bayan Gimbiya tun da kuna tare, sannan ni ba ki kirani kin gaya mini ba? Kin kyauta kenan? Girman kenan?

Na buɗe baki haa ina kallon Yallaɓai Gimbiya ta saki sheewa ta tafa hannu ni ko na ma kasa mgana tsabar mamaki.

"Ni fa Abba abu ɗaya ya yi mini zafi, wai Maman Jidda ta ce ina yi musu rashin kunya! Kuma ni wallahi ba wacce cikinsu na ke yi ma rashin kunya Maman Khalifa ce yau daga zuwa na yi mata mgana ta fara zagina"

Ta karishe faɗa har tana shessheƙan kuka, kawai sai Yallaɓai ya juya wajenta yana faɗin" Ki yi shurun ki ai na san halin kowa a cikin ku, tun tuni ba ki yi rashin kunya ba ne sai yanzu? Da man ita Saudatu fitinnaniya ce, na san za ta aikata ita kuma Sadiya ban san ta da bangarenci ba sai yau, amma duk zan yi mganin abin yanzu nan."

Ya faɗa yana nuna mu da yatsa, a kausashe, Gimbiya ta sake sakin shewa kafin ta ce" Za ka sake mu ne? Shi ne karshen mganin mu da ka ce za ka yi ko?

Ta faɗa tana tsare shi da ido, shi kuma sai ya taso mata tana faɗa yana faɗa, har yana ce mata hakuri kawai yake yi da ita darajan iyayansu. na gaji da hayaniyar sai na saka baki.

"Don Allah ku yi hakuri wannan fa ba girman ku ba ne."

Daga ba da hakuri kawai nima Yallaɓai ya dawo kaina yana yi mini masifa.

"Ai duk laifinki ne, haɗa kai kuka yi za ki kashe mini mata ko? Don kun gan ta yarinya ko?

Ban san na mike ba sai da na ganni tsaye kan kafafuwana.

"Dakata."!

Na faɗa da karfi ina ɗaga ma Yallabai hannu idanuwana har rufewa suke yi saboda bacin rai da bakin ciki wallahi tun da bai san ina yi masa kara ba yau sai na yi ma yallaɓai wankin babban bargo.

"Ka dakata Yusuf.."

Na sake faɗi cikin ɗaga murya, saboda raina ya baci zuciyata ma tafasa take yi a lokacin. Ba shi ba, har matan na shi tsayawa suka yi suna kallona saboda mamakin tsawar da na daka masa.

"Ni kike yi ma ihu Sadiya??

"An yi maka Ihu, an yi maka ihun Yusuf ka yi abin da za ka yi don Allah Haba."

Na faɗa ina yarfa hannu, bayan na nuna shi da hannu, sai na ga kawai ya tsaya yana kallona cikin mamaki.

"Maman Jidda yau ba Yallaɓan?

Gimbiya ta faɗa cikin mamaki.

"Na bi yallabai da gudu, haba ka isheni a cikin gidan nan da fitinarka, na yi maka shuru na yi maka shuru amma na fahimci ba ka san kara ba, kuma ba ka san ina yi maka kawaici ba, to wallahi na gaji, na gaji da jidalinka da na matanka na gaji Yusuf" Na ƙarishe faɗa ina ƙara daga murya saboda a lokacin ji na yi zuciyata ta yi duhu ko gani ma bana yi saboda bacin rai.

Sai falon ya yi shuru ganin na harzuƙa.

"To yi hakuri zauna mu yi mgana."

Yallaɓai ya faɗa cikin sigan lallashi ganin yadda na taso masa ya san halina in na fusata ba ni da kyau.

"Ba zan zauna ba, lokacin da na ke zaune ba ka so a yi mganar cikin laluma ba, yanzu sai dai kai ka koma ka zauna ka saurareni domin ni ce zan yi mgana."

Ban jira cewarsa ba na cigaba da faɗin" Yusuf auren soyayya ne a tsakanina da kai, a shekarun mu har zuwa matakin yau ba ka taɓa fahimtar cewa ina yi maka kara ba ne? Ba ka taɓa jin cewa a ranka kana yi mini wasu abubuwan da suka yi kama da cin fuska ina kyaleka ba! Mene ne ba ka yi mini ba, mene ne ba ka faɗa mini akan auran ka da Gimbiya ba? Wani baƙincikin matanka ne ban ƙunsa ba? Wani takaicin yan'uwanka ne ban ƙunsa a cikin zuciyata ba? Mun yi aure tun ba ka da komai muka yi gwagwamaryan arziki tare, daga baya da me ka saka mini? Ka yi mini gorin haihuwa na yi haƙuri, ka yi mini na gida na yi hakuri, ka yi ta mini alƙawaruka amma ba ka cika ba, na yi maka mgana? Ka nuna mini bambamci a kan matanka na taɓa yi maka mgana? Ka goyi bayan yan uwanka a kaina na yi maka mgana? Gimbiya ta yi mini abubuwa ta ci kasuwa a kaina kala kala amma duk ban ɗaga kaina ba, saboda kai Yusuf. Saboda karan da na ke yi maka, shi ya sa duk kake yi mini wasu abubuwa ba na ɗaga kaina, ba wai don bana jin zafi ba ne, sai domin ina kauda kai saboda kai, saboda ina daraja zaman mu da kai, ina daraja auran mu da soyayyarmu, ina kambama tarbiyan da iyayena suka ba ni, sabo da ina girmama bautar ubangijina, ka danne mini haƙƙi, ka yi mini wulaƙanci akan matanka, ka tozartani a kan su na taɓa yi maka mgana? Ka taɓa zama ka yi tunanin abubuwan da kake yi mini rashin kyautawa ka ware rana ɗaya ka ba ni haƙuri? Don ina matarka uwargidanka sai na zama bolarka, don ina haƙuri da kai sai na zama mazubin sharan da kai da matan kuke zuba duk dattin ku a kaina? Ɗauka ka ke yi alfarma ce ka ke yi mini da na ke zaune da kai? Wallahi tallahi na rantse da wanda raina ke hannun shi Darajan aure ne, bautar ubangiji ne ya sa na ke raga maka, amma ba domin haka ba wallahi tallahi ba ka isa na zauna kana cin kasuwa a kaina ba. Ba ka isa ba Yusuf ba ka isa ba wallahi, daga kai har waɗanan matan da ka ajiye a cikin gidan ba ku isa ba."

Na karishe fada ina nuna shi da yatsa manuniya, bayan shi suma na nuna su ɗaya bayan ɗaya cikin baƙin ciki, domin gabaɗaya na rasa control a kan ɓacin raina ji na ke yi auran na Yusuf kwata kwata ya fita kaina da gidan shi da matan na shi duk na yi nisa da su ko zan samu salama da kwanciyar hankali.

Na sake buɗe baki in yi mgana na kasa Kuka ne ya taso mini da ya sa na kasa ƙarisawa, su ko gabaɗaya sun yi shuru sun kasa mgana dukkansu sun nemi waje sun zauna saboda mamakin maganganuna. Ina da tabbacin ko shi da muka kwashi shekaru tare, bai taɓa ganina na yi masa hauka ba, sai yau balle su da suke baƙin ganin ɓacin raina.

Ina kuka na cigaba da faɗin.

" Sha'anin matanka da komai na su ka sanyani shiga ciki, na shiga saboda ina yi maka kara, lokacin da za ka auro Rabi'atu ka yi abubuwa ba domin na kauda kai ba da ba za mu kawo yanzu ba, ka aurota ka ce na ja ta a jikina na bi umarninka, in ba domin kai ba ita ta isa ne? Ba ta isa ba amma saboda ina yi maka kara bana daga kai akan komai da kake yi mini a cikin gidan nan, ita kanta ta sani bana kishi da ita kamar Jidda na ke kallonta amma ita ka tambayeta ni kamar uwar jidda take kallona?? Ka bata dama tana cin kasuwa a kaina, duk bai isheka ba sai kaima ka zo ka ci kasuwar ka a saman kaina? Komai ya taso na matanka sai ka danganta shi da ni? Ina ruwana a ciki? Na san an yi? Ba sai da suka yi faɗansu sannan salima ta zo ta faɗa mini ba? Ka ce na yi son kai na shigar ma Gimbiya saboda muna tare, ka ce mun taru za mu kashe maka mata, Yusuf kai kake faɗin haka? Da bakin ka? Yau ko ba auran ka a kan Gimbiya ya dace Rabi'atu ta yi faɗa da ita? Sa'arta ce? Balle tana gaba da ita a shekaru, tana gaba da ita a wajenka da gidan nan, in har ina da mutumci da daraja a wajenka ya dace a gaban matanka ka kirani kana yi mini ihun cewa ban yi adalci a kan matanka ba? Ya dace? Me kake nuna musu? Ban da daraja kuma cewar da kake yi ni ce wakiliyarka duk karya ce tun da kalamanka na yanzu sun bayyana yadda ka ɗaukeni."

Na dakata ina sauke numfashi, saboda ina mgana ne zuciyata na zafi saboda bacin rai murya ta har ta dishe saboda kuka.

"Sadiya ki bar mganar nan ki yi hakuri kin ji ko?

Yallaɓai ya faɗa cikin lallashi har yana tasowa zai rikeni na matsa baya ina mai ɗaga masa hannu lokaci ɗaya ina faɗin.

" Ba mganar hakuri ba ne, hakuri ai na yi shi da ban yi ba, da ba ka ganni zaune a gidanka ba. Da a ce ina riƙe da irin cin kashin da kake yi mini na rantse da Ubangijina da tuni wata rana ka wayi gari ka ga bana cikin gidan ka. Kawai ina so ka san cewa kawaici na ke yi maka, kuma shi ne kuskure na, yau da ban nuna maka zan ɗauka ba, da duk wannan cin mutumcin bai biyo baya ba."

"Don Allah ki yi haƙuri."

Ya faɗa cikin lallashi kamar zai yi kuka, ashe karyan iskanci ne abin na shi.

"Ki yi hakuri Maman Jidda."

Gimbiya ta faɗa jiki a sanyayye.

"Ki yi hakuri."

In ji Rabi'atu ita kanta jikinta ya yi sanyi.

"Ba komai ni ce na yi sakacin da komai ma ya faru. Ni na sabama Yallabai da hakan shi ya sa ba ya jin shakkar yi mini ihu akan matan shi, amma ina so ku sani daga yau sai yau, ba ruwana da abin da ya shafe ku, kai ma kar ka kara sakani cikin sha'anin matanka, mganar ni ce wakilayarka ba ta, gida na ka ne dukkanmu muna karkashinka ne, kar ka sake kirana akan su ko ka ce za ka yi mini ihu ko ka faɗa mini mgana nima ba zan sake shiga hurumin su ba, duk kawaicin da na ke yi maka na daina domin na fahimci baka daraja haka."

Ina gama faɗin haka na juya da gudu na bar falon ina jin sa ya biyo ni yana kiran sunana ban jiyo ba sai da na fita haraba na saita kaina har na kai bangarena duhu duhu na ke gani saboda bakinciki, ina shiga na kulle kaina a bedroom ina ta kuka, ya zo ya yi bugu yana yi mini magiyan na buɗe ban buɗe ba, har Gimbiya ta so itama da magiyan na yi hakuri na buɗe itama na yi mata banza Baby ta zo tana kirana da Umma ki yi hakuri ki bude itama na yi mata banza, har Jidda dake makaranta ina jin Ubanta ne ya kirata ta yi ta kirana a waya ban ɗauka ba, kukana na sha, har na koshi sannan na lallashi kaina da alƙawarin Yallaɓai ya gama cin kasuwa kaina in dai akan matan shi ne.

Sai da safe na buɗe kofa na fito fuska a kumbure, Yumna da Baby suna rige rigen gaisheni fuska ba yabo ba fallasa na amsa, ba su zauna ba suka shirya direba ya kwashe su zuwa Tahfez tun da jiya ba su samu zuwa ba.

Tea kawai na sha, na koma falo na kwanta, da na kuma san Yallabai zai shigo mini da ɗaki zan koma amma sai ya ritsani, Yallaɓai duƙa mini yayi har ƙasa akan gwiyoyinsa yana bani hakuri faɗi yake yi

"Ki yi hakuri Sadiyata. Wallahi na san ina yi miki wasu abubuwan na kure hakurin ki amma baki taɓa mgana ba. Na sani kina yi miki kara da kawaici ban kyauta ba don girman Allah ki yafe mini."

"Ai da ba yafiya Yusuf da ban sake kallonka ba, da ban sake ba ka wata dama ba kawai ka kiyaye kar ka ƙure ni na yi abin da ban saba ba."

"Ba zan kure ki ba in sha Allahu. Ki yafe mini Sadiyata"

Duk yadda ya so bai ga dariyata ba, da gaske na ke yi na daina yi masa alfarma kuma ya san haka shi ya sa ya ruɗe, bayan fitan shi sai ga Gimbiya itama hakurin ta yi ta bani.

"Ba komai fa, abin da ya wuce, wani abun ai da ba a hakuri da ba a kawo wannan matakin ba maman khalipa"

Itama Rabi'atu ta zo tana bani hakuri itama na ce mata ni ba komai, domin in da ban yi hakuri ba da ba ta zo ta iske ni ba, tun daga ranar na tsame kaina daga sha'anin Yallaɓai da matan shi, kuma daga lokacin na samu sauki daga shi har matan na shi suka fara shakkata domin gabaɗaya na dauke musu wuta, ashe da gangan ne Yallabai ke yi mini wulakanci sai da na buɗe bakina na yi mgana na fahimci yana sane da abin da yake yi, tun daga ranar na shata masa layi sai na zauna lafiya ya kiyayeni suma suka kiyayeni, kuma abu in dai ya shafeni yana rawan jiki, suma haka matan na shi, saboda yadda na fidda kaina daga duk abin da ya shafe su na gyara kuskuren da na yi sakaci tun farko.

Aka ce mai hali ba ya fasa halin shi, ya riga ya saba da kwaso mini ko wata mgana amma yanzu da ya zo ya fara, kallo kawai in na yi masa zai shiga taitayinsa, in ma ban kalleshi ba, banza na ke yi da shi har ya gama ɓaɓatun shi kanzil bana cewa, in ya gaji sai ya ce Sadiya ta ba ki ce komai ba! In ma na ɗago na yi masa wani sakaran shi da kan shi ya ke kama kanshi ya tashi yana kame kame, wallahi aure bauta ne ba domin bautar ubangiji ba da Yusuf bai isheni kallo ba wallahi. Shima ganin yanzu ya fita zuciyata shi ya sa duk wani abu na kyautatawa ba wanda ba ya yi mini. Ni ce wai Yallaɓai ke yi ma tsaraba in ya fita bini bini Sadiya ta ko kina son wani abu? Kafin na yi mgana ya yi mini alheri jikinsa na rawa da zuciyarsa a kaina ni ko bai san na riga na gama sanin shi ba ba kuma wani yaudaran da zai zo da shi ya sake ruɗata. Ni dai tun da sun kiyayeni daga shi har matan shi shike nan na samu salama da zaman lafiya.

*****

*BAYAN SHEKARA ƊAYA DA RABI.* NOVEMBER. 2025.

Alhamdulillah Rayuwa ta miƙa Ubangiji ya ara mana dama. Ya ba mu rai da lafiya sannan ya azurtamu. Ba abin da za mu ce sai godiya ga Ubangijin mu. Yau da jiya da gobe ba su bar komai ba tun muna kirga kwanaki mun koma na wattani ga shi muna kirga shekaru ashirin da huɗu cikin na biyar da auren na da Yallaɓai. Rayuwa ta zama sai godiya kawai mun faro gwagwamarya kuma ba za ta kare ba har mu koma ga Allah amma dai muna fatan ko da yaushe mu yi kokuwa da matsalar mu mu ga bayan ta ba wai ace ita ce za ta ga bayan mu ba.

A halin yanzu shekaruna na haihuwa arba'in da biyar Yallabai kuma girma ya zo an gangangara gidan hamsin da biyu har da ɗoriya. Rayuwa ba za ta koma jiya ba sai ta yi ta gaba kana karuwa a fuskantar yarintarta ka. shekarun mu sun mika amma kuma mun samu wadatar rayuwa sai godiya. A shekara ɗaya da rabin da suka gabata abubuwa na alheri da aka sin sa duk sun faru amma na alherin da farincikin sun fi yawa.

Gimbiya ta haihu ta samu yarta mace ta ji sunan Hajiyar Tafida. Ahalin yanzu ma Rabi'atu ta na da ciki kimannin wattani biyar. Tuni har ta yaye yan biyu tun da suna cikin shekaru na biyu ne. A gidan Yallabai tsakanin Gimbiya da Rabi'atu ne ake gasan haihuwa da kishi ni kam na koma gefe na zama Umma, sai dai na ba da shawara ko na raba in na ga abin da bai kamata ba. Na yarda na amince ina da wani hali da ba zan iya barin shi ba, duk yadda na kai ga kauda kaina ga sha'anin Yallaɓai da matan shi in na ga abin da bai kamata ba, ba na iya shuru sai na tanka, na ɗauki hakan a matsayin hallita ce ta Ubangiji, ba ni da riƙo sannan kyakyawan zuciyata ba ta barina na daɗe ina jin haushi wani a cikin zuciyata.

Yallaɓai har gobe bai dai na faɗin bai cire rai ba bai kuma haƙura ba yana fatan bayan Yumna na sake haihuwa ni kuma na kan ce masa na gama. Ga su Gimbiya nan dai su yi ta cika mana gida da yara Alhmdulillah. A tsawon zamana da Yallaɓai ya yi mini tarin alhern da suka goge sharrinsa a wajena amma babban abin da ya yi mini da ya ƙara samun daraja a cikin zuciyata shine ya biya mini kujeran makka a wannan shekaran na je na sauke farali sannan ina dawowa na yi cukun_cukun buɗe shagon Saloon ɗin da na ke buri, domin na fahimci Yallaɓai ba zai iya cika mini alƙawari ba, Musbahu na saka a jagoranci sai dai Yallaɓai ya ji labarin an kama shago a wajen ƙaninsa domin ni ban faɗa masa ba, sai ga shi ya zo yana borin kunya shi da man yana da niyyar da na dawowa daga Saudiya ya buɗe mini shago shi ne target ɗin shi, har yana faɗan me ya sa na yi masa haka? Ni ko na ce kar ya damu ba komai ai na san abubuwa ne suka yi masa yawa, ba na ce ban gode masa ba ne na gode tun da ya yi sanadin da na je ɗakin Allah, amma mganar buɗe shago bana son tunawa saboda tsabar renin wayau da renin hankali Yallaɓai ya yi mini shi, tun yaushe? Mgana ce tun auran mu, yana da shi ba wai ba shi da shi ba ne, kawai bai yi ra'ayin cika alƙawari ba ne shi ya sa na kuɗiri niyyar sai dai ya ga ana yi, da jarin hijabaina da kudaɗen hannuna na haɗa na kama shago na yi siyayyan wasu kayan shi kuma Gogan sai ya ji kunya ya dunkule 800k ya bani da na ce ma ba zan karɓa ba wajen Alhajinmu ya kai ni kara shi ya tursasani na karɓa sannan a ɓoye ya saka aka yo mini oder ɗin kujeru da sauran kayan injinan shagon sai dai na ga an kawo sannan ya shiga ya fita sai da aka gyara shagon nan ya ga komai ya kamallah, har yana yi mini mganar ko zai kama mini wani babba ne! Ya ga kamar wannan ya yi ƙarami na ce na gode ƙaramin ma ya ishe ni. Gabaɗaya dai kunya ta hana shi suƙuni ni kuma ko a fuska ban nuna masa ba, shi ne dai ya san bai kyauta ba yana ta kame kame na yi banza da shi. To ni Yallaɓai ai ya daina damuna, na tattarashi da sha'aninsa na watsar tun a baya.

Da shago na ya kamallah mai suna S.S YASHE BEAUTY SALOON. Na yi Farinciki da ban san iyaka ba da man ina cikin farimcikin ne na je na ga ɗakin Allah A shekaran tare muka je da Alhajinmu Hajji da Ya Hamza da Ya Auwal suka haɗa kudi suka kai shi sai Ya Usman da Anty Zabba Allah ya taimaka a masauƙi ɗaya muka sauka. Yallabai ya girmama ni tun da ya ce ni ce uwargidan shi ni zan fara zuwa amma daga baya ɗaya bayan ɗaya zai kai su Gimbiya. Suma ɗin ba su nuna damuwar su ba sun yi fatan Allah ya sa suna da rabon zuwa ita Gimbiya ma ta taɓa zuwa Umra tsohon mijinta ya taɓa kai ta, Yallaɓai ma a shekarslan da ya biya mini ya je Umra ya dawo.

Readers Also Read

More by Bilyn Abdull