Turken gida book1 by janafty - Chapter 26
Turken gida book1 by janafty Chapter 26: Turken gida book1 by janafty Chapter 26. "Ke kam Zaituna me zai hana ki tsayawa a gida ki yi abinci? Shi ya sa…
3,343 words
"Ke kam Zaituna me zai hana ki tsayawa a gida ki yi abinci? Shi ya sa Yaya Abubakar da ya shigo ɗazu ya ce a zuba masa abinci ashe da yunwa kike barin shi."
Yaya Balki ta faɗa tana kallon ta kafin ta samu zarafin mgana Yaya Aina ta karɓe da cewa" To ta ina ma mace na da miji da ƴaya za ta fita ba ta yi girki ba? Ai ko fitar sassafe ce ka yi dai ko fara ba mai ne kafin ka fita." Ina gyara zama na ce" Ta saba ne. Ita fa Zaituna ba ta son komai ba sai shigen yawo da shige shige. Ko mu nan da kika ganmu sai mun yi abinci muke fitowa daga gidajenmu ballatana ke."
Na faɗa ina kallonta sai tafara kame kamen wai ita ina ta ke zuwa karaf ko Yaya Murja ta ce" A a Zaituna. Kina da shigen yawo kullum ba ki iya zaman gidan ki. Na rasa gidan wa kike zuwa da ya fi gidan mijin ki?
Har ta na rantsuwan wai ita ba in da ta ke zuwa ko da yaushe tana gida ba domin rashin lafiya Alhaji ai ta fi sati ba ta fita ba, Ma'u na dariya ta ce" Ko ana gobe rashin lafiya Alhaji kin biyo gidana kika ce daga anguwa kike hanya ta biyo da ke? Ko ba a yi haka ba?
Ta faɗa tana kallonta ganin an ƙure ta sai ta wayance da cewa ta tuna sun je gaisuwa can ɓarayin su Ma'u shi ya sa ta biya ta gidanta.
Ganin ta na neman sauya hirar ya sa na kalleta ina mai kiran sunanta. "Zaituna kenan. Ki daina ma karya kowa ya san halin ki nan kwanaki na ji an ce kin cinye kuɗin adashen mutane har da yan sanda suka dauko miki, to ni dai ba zan ce ki bari ba amman in kika ɗauko rigimarki ki riƙa tsayar da ita a kan ki ko akan dangin ki, ki bar ɗan uwana ya huta duk kin tsufar da shi kin saka shi a uku, kar ki kashe mini ɗan'uwa gwara ma ki daina abin da kike yi."
Sai ta kasa mgana Yaya Balki ta ce gaskiya ne Yaya Abubakar duk ya fara tsufa saboda wahala da rashin kwanciyar hankali. Yaya Murja sai ta taɓe baki kafin ta ce" Ai Allah ya bashi wasu kudaɗen sai na ce ya kara aure ita kuma ta je can ta ƙarata, ka rasa abin da take siya da kuɗin da ta ke rigima komai dai dai gwargwado ya na yi miki zaituna me kika nema kika rasa? Ganin mun yi mata taron dangi ya sa ta fara kuka tana murza idanuwana.
Yaya Balki ke faɗin" Me ye na kuka? Domin fa muna sonki ne ya sa muke gaya miki gaskiya da wasu dangin ne wallahi sai dai ki ji wata maganar, to ki ɗauka mu muna sonki ne shi ya sa muke faɗa miki gaskiya domin ki gyara." Yaya Aina ta karɓe da faɗin" Kwarai da gaske in wasu dangin mijin ne ita kanta ta san ba za su ɗauka ba. Faɗan ke so kan ki muke yi miki ki gyara saboda ke ba yarinya ba ce kin san abu mai kyau da mara kyau, in kika bari ya yi zuciya ya ɗau wani mataki akan ki ba za mu saka baki ba to kafin akai ga haka ki sauya rayuwar nan da kike yi, ki zauna a gidanki ki fita daga shiga rigima tunda ba abin da mijin ki ya rage ki da shi'
Kowa na ta tofa albarkacin bakin shi, Yaya Murja dai ta ƙare mganar da cewa" Ke ko koyi ba za ki yi da su khaleesat da Laila ba? Dube su kowacce tsaf ita da ƴaƴanta, kuma suna rawan jiki akam mazajensu suna tattalin su amman ke ba wannan a gabanki sai shirme, to ki fara gyara kanki da gidanki in kuma ba haka wata rana za ki yi nadama."
Ma'u ta saka baki tana faɗin" Ki rika kwalliya Zaituna. Haba kamar ba mace ba, ba ki gyara balle ki gyara ƴayan ki? Namiji fa na son gyara kuma in kika gyara wallahi sai ya ji daɗi" Nima na yi mata nasihan ta daina zama kaca kaca ta zauna a gidan ta gyara kanta tana kuka tana mana godiya tare da alƙwarin ta daina muna mata fatan haka daga nan sai muka saki maganar muka shiga wata hira ana mganar Baba Sani zai tafi gobe su Yaya Hamza sun bar kuɗi a ba su Yaya Aina ta ce in muna da wani abu mu haɗa masa ko in akwai mai sabulai da omo mu kawo ni dai na ce ina da sabulai zan aiko da safe Ma'u ta ce za ta ga abin da za ta aiko, har da kaya ma Yaya Balki ta ce tunda wancan zuwan da suka yi Matar Baba Sani ta mata zencen kayan yara haka suna so.
Yau dai zaman gwanin daɗi ba faɗa ba bakar magana kowa ya binne abin da ke ran shi, Yaya Aina ce ta kalli Ma'u lokaci ɗaya tana faɗin" Ke ko Ma'u dangin babanki na neman ki yanzu? Sai ta yi shuru kafin ta ce" E. Muna waya da wasu daga ciki can kwanaki ma wata wacce da mamanta da babana uwar su ɗaya uba ɗaya ta zo wajena har ta yi kwanaki. Ni dai na daɗe ban je ba amman Alhaji ya ce in ya samu lokaci za mu je mu gan su." Yaya Murja ta yi karaf ta ce" Ba dole su neme ta ba. Sun ji labarin ba ta wulakanta ba. Ta na da abin duniya."
Yaya Balki ke faɗin" To daman ai sai an san kana da amfani ake nemnka. Lokacin da suka san su za su wahala da ita ai ba su damu ba. Sai yanzu da suka san za su more ta. Ba komai abin da ta ke dashi ta yi musu ba shike nan ba." Ni ko ina gefe na ce shiken nan kuwa. In kana da shi ka yi in baka dashi ne in baka yin ba matsala. Ita dai sai gyaɗa kai ta yi tana faɗin in sha Allahu.
Sallar la'asar ya tashe mu a wajen, bayan mun idar da sallah na shiga ɗakin Gwaggo na gaida Baaba ta amsa kamar yadda ta saba amsa mini. Daga nan ɗakin Mama na yi shigewata ina duba wayata su Firdausi ne a tsakar gida suna shara wasu na wanke wanke su Yaya Murja na baro su ɗakin Gwaggo. Tun da su sun rigani zuwa karfe biyar Yaya Aina ta yi sallama ta wuce gida bayanta Yaya Balki tare suka fita da Zaituna ni ma sai na yi shirin tafiya har Ma'u na fadin ta ɗauka sai dare zan tafi, da haka na so amman sai na tuna zan yi ma su Jidda kitso ba zan zauna jiran Yallabai ba.
"Tafiya zan yi. Na yi ma su jidda tsifa zan kama musu kai gobe makaranta." Yaya Murja na gefe ta ce" Da kin zo da su Firdausi ta yi musu." Sai na ce mata ban yi tunanin Firdausin za ta zo ba ne, ina shirin tafiya Munirra ta kirani a waya ta na tambayan muna asibitin ne ko gida? Sai na ce mata muna gida sai ta ce mini gata nan zuwa ita ta tsayar da ni na jirata har sai da ta zo na rakata falon Alhaji ta gaishe shi.
"Matar ƙanin Yallabai ne Alhaji"
"Allah ya yi mata albarka. Na gode.".
Har da kankana ta kawo masa Gwaggo na ta godiya, mun dawo ɗakin Mama sai ga su inna Mariya sun zo duba Alhaji ta ce Amina ce ta faɗa mata jiya shi ne ta ce bari ta zo ta duba shi, dalilin haka yasa na daɗe a gidan tun da sai bayan sun tafi tare ta ke da matan su Kawu Tasi'u, sannan ita Munnira ta ce min ba daɗewa za ta yi ba na fito rakata har bakin gida bayan ta yi sallama da su Gwaggo ta ke ce min.
"Ke na taɓa ki da alheri matar Yallaɓai. Kin ji Yaya Usman zai kara aure? Ban samu zarafin mgana ba ta cigaba da faɗin" To yanzu ma mganar da ake yi Anty Zabba na gidan su. " Cikin nuna mamakin na ce"Wai har yanzu ba ta koma ba? Munnira ta ce" Ina fa ta koma, a bakin Nasir na ji wannan satin mai shiga Yaya Usman ɗin zai zo, na so kiran Anty Zabba sai na fasa kar ta ce ina da son jin gulma" Ina mata dariya na ce" Wallahi haka za ta ce."
Munnira ta kama haɓa kafin ta ce" Shi ya sa ban kira ba. " Na ce gwara hakan itama Munira ta na faɗin ba ta ji daɗi ba, koma mene da ta yi hakura ta zauna tunda matar na shi ba akanta za ta zauna ba.
"Uhm ke dai Munira Allah dai ya kyauta ya dai dai ta su." Ta amsa min da Amin Amin daga nan muka yi sallama na koma cikin gida sai na ga Aneesa da wayata wai ana ta kirana ina dubawa sai na ga Yallaɓai ne da sauri na ɗaga kiran.
"Yallaɓai ka taho ne?
Cikin wani irin murya ya ce min" Sadiya ta congratulation." Ina yar dariya na ce" Yallaɓai ka biya mini makka ne? Shima dariyan ya yi kafin ya ce" In sha Allahu ina saka ran haka, amman dai yanzu ina so na faɗa miki ne an biya ni half payment na aikin nan namu na Rano." Cikin murna na ce" Don Allah fa Yallaɓai" "Allah Sadiya ta. Yanzu kuɗin suka shigo sun kuma kirani sun faɗa mini."
Ɗakin Mama na faɗa ina faɗin" Alhamdulillah mun yi kuɗi" Ya na yar dariya ya ce" In an yi mangariba zan fito sai na zo mu dawo tare" Da haka muka yi sallama, muna gama wayar na yi hamdala ina jin daɗi Allah ma ji roƙon bayin shi.
Na ƙosa mangariba ta yi ma saboda murna, ina idar da sallar mangariba na shirya lokacin har Yaya Murja ta tara yayanta sun tafi gida ni da Ma'u kawai ne a gidan ita kuma tana tare da Baaba. Yallaɓai sai bayan isha'i ya zo, ya ƙara duba Alhaji sannan na yi musu sallama muka tafi gida. Muna hanya ya kalle ni kafin ya ce" Yanzu da me zamu fara Hajiya ta? Ina dariya na ce" Mu je gida mana Alhajina."
Sai muka kalli juna kafin mu kwashe da dariya, ni ko har ina dukan kafaɗansa kafin na ce" Ranka ya daɗe mai girma Tafida." Shi dai ya na ta dariya ni kuma ina masa kirari "Angon Sadiya Ɗan gatan Nene, uban Jidda da Maimuna. Allah ya ƙara ja zamanin Tafida mai girma Injiniyan gine gine, mai muƙamin zane zane takawar ka lafiya"
Ya na dariya ya ce" Me kike so Sadiya? Ina masa dariya na ce" Me kuwa na ke so? Yallaɓaina kaɗai na ke so." Gira ya ɗaga min kafin ya ce" Kin yi kyakyawan zaɓi kuwa." Muna tafe muna hira, har muka isa gida. Baby har ta yi barci, dole na tashe ta tana kuka tana komai na yi mata kitso, Yallaɓai na ta faɗan wai ban iya kitso ba ne na saka yarinya tana kuka.
Baki sake na kalle shi kafin na ce" Au ban iya ba ko? Ya na kallona ya ce" To ni dai ban san lokacin da kika koyi kitso ki ka iya ba" Sai kawai na yi banza da shi Jidda dai lafiyan lau muka yi kitson mu, sai bayan na gama mu su ne na ce su yi shirin kwanciya Baby daman Babanta ya lallasheta har ta yi barci. Wanka na sake yi na yi shirin kwanciya Tea na haɗa mana muka sha sannan muka zauna kassafa kuɗi, abu na farko kayan abinci na yi masa mgana sai kuma na ce ya ijiye kuɗin makaranta yara tun da sun kusa fara jarabaawa.
"A'a ki bari sai zuwa lokacin ai da sauran lokaci." Kamar zan yi mgana sai kuma na fasa saboda na san wataƙila zuwa lokacin ya zo babu, mun yi mgana ya cire wasu kuɗi saboda Gidan bulo da office sai na yi masa mganar Halima ta haihu ba a yi mata komai ba sai ya ce zai turamin 20k ya ce a siyi abin da ya kamata ina so na ce ya rage min ko kaɗan a cikin kuɗina amman ban yi ba kamar ya san me na ke tunani sai ya ce
"Zan ba ki 50k ki rike a hannunki. Kuɗin ki kuma in gwammati ta biya mu sai na baki duka in sha Allahu."
Ina yar shagwaɓa na ce" Yallaɓai buɗe saloon ɗin fa? Da sauri ya ce" Wannan ni na ce zan buɗe miki, kuɗin ki kuma haƙƙn ki ne zan biya ki in sha Allahu." Sai ya ga na yi shuru sai ya shafa kumatuna kafin ya ce" Kar ki damu. In sha Allahu duk za a yi."
Sai na gyaɗa masa kaina. Mun cigaba da lissafi ya ce 30k na kayan maggi da kayan tea, sai na ce ai ya haɗa gabaɗaya cikin na kayan abinci tunda tare muke siya a kasuwa a wani babban shago yana da lambar wayarsa list ɗin kawai zan rubuta ya tura masa da ƙudin har gida za a kawo mana kayan abinci. Har da sabule da omo, ni kuma sai ya ce zai ƙara mini 30k saboda siyayyarmu ni da yara su Unders da sauran kayan kwalliyan mata. Kuɗin asibiti kuma ya ce zai ware mini 50k saboda bamu san nawa za a nema ba sai dai goben in mun je mun gani. Sauran kuma ya ce zai yi amfani zai sallami sauran ma'aikata da shi ko da rabi rabi ne, ni na san har da kyatttuka sai ya yi in dai Yallaɓai ya samu kudi kamar suna masa kwaiƙwayi ni na yi masa mganar Nene, daman in za mu yi siyayya kayan abinci har da ita da kayan tea sai sabulan wanka sai ya ce na rubuta list ɗin gabaɗaya sai ya tura babban shago za a kawo kayan zuwa gobe in sha Allahu.
Sai na ce to a daran na rubuta abin da na manta na ce zuwa da safe zan tuna. Saboda zuwana asibiti tun asuba na tashi na yi ma yara shirin makaranta Yallaɓai jiya ya siyo indomie da kwai , sai buredi sai na soya musu buredin da tea ɗin suka tafi da shi makaranta, ni kuma muka shirya daman tun safe na tura ma Dr Fatima saƙo sai ta dawo min da amsar za ta ƙara kiran Dr Aisha ɗin amman na je asibitin na siya kati za a kai ni gynea unit ɗin in ce dai Dr. Aisha na zo gani a shigar mata da Fayel ɗina za ta duba ni in sha Allahu.
Tare muka fita da su Jidda muka kai su makaranta daga nan muka wuce Aminu kano. Da taimakon Yallaɓai nan da nan muka siya kati har aka yi mana hanya zuwa Gyea Unit da taimako irin masu zirga zirga rarraba katina Yallaɓai ya yi ma ihsani, ya faɗa mai mun zo ganin wata Dr Aisha bukar ne. Wajen ta zai kai mini Fayel ɗina sai ya ce ba matsala ba ta ƙariso ba amman tana hanya.
Sai wajen tara da wani abu likitocin suka fara zuwa. Muna zaune da Yallaɓai bangaren yan jira aka shigar da Fayel ɗin mu, Saboda ihsanin da Yallaɓai ya yi mishi sai ya shiga ciki ya yi ma Dr Aishan bayani sai ta ce eh ta na sane fayel ɗina daman a sama ya saka min ni ce ta farkon da aka fara kira na shiga ganin Dr Aisha Bukar kamar yadda ke rubuce jikin Office ɗinta.
*Janafty* *TURKEN GIDA.*
*Wattpad:Jamilaumar315* *Arewabooks:Jamilaumarjanafty*
*SADAUKARWA GA BARRISTER SALAMATU DOMA(MOMMY)*
https://chat.whatsapp.com/GKzdnJ5Gb62IjjqT6AYpcC
No 1 online shopping kenan inda zaku sami duk wani kaya da ku ke buƙata, tun daga kan kayan kicin, laceses, atamfofi, shaddoji kayan yara maza da mata ,da uwa uba magungunan supliments wadanda ba su da illa na manyan mata inda zaki fito ki yi das da ke ki zama abin sha'awa, ga kuma Arabian sabaya powder wacce baki taba cin karo da irin ta ba, ke dai maza shigo ki kwashi romon arziki a gidan mutunci da karamci a kai Miki kaya har inda ki ke babu fargaba.
Eaman ScholarSphere. Where ideas Take Shape.
WHAT WE DO. ASSIGNMENT PRESENTATIONS. ARTICLES PROJECTS. BOOK
AND MANY MORE.
CANTACT US THROUGH. 02347067793152
MOTTO: "Pathways of Knowlodge Academy, Nurturing minds, illuminating Futures"
*🅿️15*
Aminu kano Teaching Hospital. Gynecologist Unit.
Ina zaune a kan kujeran da ke fuskarta wajen zaman likita. Idanuwana kir a kan Dr Aisha Bukar ina ƙare mata kallo. Ta fi Dr Fatima shekaru ita babbar mace ce gaskiya a kallah in ba ta haura 40 ba za ta tsaya a hakan ta na da kaurin jiki, ga tsawo ga kiba sannan ba ta da wani haske sosai.
Tana zaune tana duba fayel ɗin gabanta gefe ɗaya kuma hankalinta na kan system ɗin dake gabanta da alama dai akwai abin da ta ke dubawa a ciki. Fuskarta da gilashi siriri sannan sanye take da rigan likitoci kanta kuma ta sanya ƙaramin breziya Hijab fari.
"Sadiya Sulaiman Yashe"
"Maa."
Ba ta kalle ni ba hankalinta na kan system ɗin gabanta ta ce" Ke ce wacce Dr Fatima ta yi transfer ɗin ki daga ABU KO?
Sai na gyaɗa mata kai lokaci ɗaya da cewa" Yes" Saboda da turanci ta yi maganar.
Tsayin mintina goma sannan ta ce" Ga Report ɗin ki da ta tura mini ina kan dubawa."
Da hausa ta yi mganar wannan karon kafin ta dawo da hankalinta kaina.
"Sunana Dr Aisha Bukar. Zan cigaba da jagorantar matsalarki har zuwa lokacin da za ki samu waraka in sha Allahu."
Ba ta jira jin ta bakina ba kawai ta cigaba ta faɗin.
" A yadda na ga ɗan brief na matslar ki, kafin mu je kan matakan da muke ɗauka ga masu irin laluran ki, kin san abin da ke damun ki? Ko dalilin da ya sa ba ki sake haihuwa ba?
Na ɗaga mata kai zan yi mgana kawai cikin zaƙin muryanta ta ce.
"SECONDARY INFERTILITY"
Kai tsaye kuma ta cigaba da bayanin ta.
"Kuma shi Secondary infertility ( rashin samun ciki bayan mace ta haihu ko hayayyafa) yana faruwa ne lokacin da mace ta haihu sai kuma haihuwa ta zo ta ɗauke kwata kwata ayi ta nemanta ruwa a jallo amma bata samuwa wani lokacin har sai an dangana da asibiti. Mace a haihuwar farko ta san lafiyarta lau saboda ta samu ciki ba tare da neman taimakon likita ko shan magani ba, amma kuma daga nan sai haihuwar tayi ɓatan dabo."
Nan ma sai ta ɗan dakata kafin ta cigaba da faɗin.
"Yawancin abubuwan da ke haifar da secondary infertility sun haɗa da low egg quality(wato kwan haihuwar mace ya kasance baida karfin haihuwar) matsalar mahaifa, matsalar rashin karfin maniyyi, yanayin abinci da wasu abubuwan wanda suka danganci rayuwar mace kama daga yanayin cututtuka da uwa uba Family Planning"
Ta ɗan ɗago ta kalleni ganin ina kallonta sannan hankalina na kanta ya sa ta ɗan gyara zama gilashin ta sannan ta sake cigaba da faɗin.
"Babban abunda ke kawo secondary infertility musamman a kasar hausa shine family planning wato tsarin iyali. Yawancin mata idan sunyi tsarin iyali yana haifar masu da matsaloli wanda cikin matsalolin nan babbansu shine sanadin family planning. Family planning na haifar da jinkirin rashin samu ciki da wuri saboda karfinshi da kuma aikin da yake a productive system na mace Kama daga hormones har zuwa Reproductive organs
"Kuma kowani abu ya na da Siide effect, kuma shi planning yana ninka adadin shekarunsa sau ɗaya ma'ana zai iya haurawa da kashi ɗaya, wani lokacin har biyu, kamar ke ɗin nan kin yi na shekaru biyar amman ya haura ki har shekara tara ba ki haihu ba, sannan kafin ki samu ciki side effect ya taɓa ki kin ta samun matsaloli ko? Ba ta damu da na amsa ba ta cigaba da faɗin.