Uwa ko ukuba complete by m shakur - Chapter 24
Uwa ko ukuba complete by m shakur Chapter 24: Uwa ko ukuba complete by m shakur Chapter 24. By 9:30 yashigo maida kofan yayi ahankali ya maida yarufe yana…
4,083 words
By 9:30 yashigo maida kofan yayi ahankali ya maida yarufe yana kallonta yanda tarufe jikinta dan fuskanta ne kawai awaje tana bacci key ya murza a kofan saikawai yawuce gaban wardobe kaman bashiba kayan jikinsa yacire yarage dagashi sai singlet da boxer, boxer daya yacire yabar na cikin irin wanda ke kama gaba dinnan wlh gabansa kaman wani dankareren macijine awajen, zaro kayan dazai saka na bacci yayi yawuce bayi, baya taba iya bacci idan baiyi wanka ba he's too clean wanka yayi yafito shirye tsaf ya jefa kayan daya cire a basket yadauko bargo da bedsheet ya shimfida akasa pillow yasa hannu yadauka yana kallonta ya ijiye pillow akasa saiya zauna bakin gadon yayi shiruuu yana kallonta ya tsare lips dinta da idanu everything that happens dazu na dawomai, lowering gaze dinsa yayi tareda sakin wani cute full smile dimples dinsa suka lotsa sosai, kaman ba Hamad ba tashi yayi sai kawai yawuce ya kashe wutan dakin ya kwanta akasa ahankali yana rufa.
Wuraren 2 nadare cikin Asmeey yafara ciwo data kasa daurewa dukko uban baccin dake idanunta, tun kafin bacci takejin ciwon but yanzu duk nauyin baccinta saida tabude idanu ahankali takai hannu ta taba maranta tana wani irin kwanciya tai gaho tana kama cikin, most of the times tanayin ciwon mara every months but sometimes ciwon cikin baya tsanani haka but yanzu jitayi kaman ana barka mata mara da reza sabida azaba, gadon tashiga tabawa ahankali bataji kowa ba ga duhu gashi babu waya ko any haske close to her awani irin hankali ta mirgino zuwa bakin gadon rikeda cikinta murya chan kasa tace "Yayaaaa" wani irin nishi tasaki tashiga kokarin saukowa daga gadon kawai tafashe da kuka ahankali ta sauko da kyar tana dukewa zatai tafiya taji kaman ta taka mutum dasauri ta duka kawai saita fashe da kuka da kyau kaman yar yarinya ta shiga tabe tabe tace "Ya Hamadiiii" daidai hannunta sunyi landing akan fuskansa, bude idanu yayi cikin bacci yaji mutum akansa tana tattabasa tana kuka tace "Ya Hamadi" yunkurowa yayi da muryan da baya fita sosai yace "Baby!!" dawani irin sauri Asmeey tahau jikinsa ta manna fuskanta jikinsa tafashe da kuka tana daga yar rigan jikinta sama tana rike cikinta da hannu daya tace "Yaya cikina zan mutu" ahankali Hamad yadaura duka hannuwansa biyu abayanta yarungumota jikinsa sosai yace "wat happen to your ciki?" Kasa magana tayi sai wani kalan kuka datakemai kasa kasa tana matse cikin, rudewa Hamad yayi yazare hannunsa daya daga jikinta yashiga tattaba kasan yana neman wayansa luckily yaga wayan yadauka da sauri ya kunna flash ya ijiye wayan a gefensu ya kalleta dawani irin sauri Hamad ya kaudakai almost half of chest dinta is outside sannan takara daga rigan sama dan flat cikinta gabaki daya awaje ga yanayin zaman datayi he could see she stained a little from her short.
EPISODE 3️⃣7️⃣
Yakai almost 30secs sannan Hamad yasauke ijiyan zuciya kaman wanda yagama calculations da kyar yakalli fuskanta asanyaye yace "period?" Gyadamai kai Asmeey tayi da kyar, ko kadan besan mezai mata ba kukanta ma is not making him think clearly ga jikinta da mistakenly idan ya kalla sai lissafinsa ya birkice da kyar ya daidaita kansa yace "you need to shower wait stand up" yamike rikeda ita ajikinsa zai zaunar da ita akan gado taki zama kaman yara dinnan tashige jikinsa da sauri tana wani lalataccen kuka dake confusing focus din Hamad, ashagwabe tace "ciwo Yaya" Hamad kaman zai sume, wani dan banzan sha'awa jikinta ke sakashi ji sabida dan kayan jikinta da kyar yace "please ki zauna lemme put hot water for you" yayi maganan yashiga kwantar da ita da kyar Asmeey ta yarda ta kwanta mai tana bude idanu kadan ta kallesa tsabagen yanda bataso yayi leaving side dinta, bayi yawuce dasauri yabude hot water yana praying Allah sa ruwan da zafi sosai he's not sure idan nefa sun kawo wuta sabida akwai inverter agidan da kyar yasami ruwan zafin yatara yayi zafi sai yafito gani yayi tajuya takife tarike cikinta, yazo wajen yakamata cikeda tausayi yace "come" tasowa Asmeey tayi kaman zata fadi dasauri yariketa sai kawai ya dauketa bayin yawuce da ita ya ijiyeta murya chan kasa yace "wat should i bring for you? I don't know anything, mezan miki"? Wani melting zuciyanta maganan yayi dudda tana cikin ciwo, murya chan kasa tace "pad" "pad"? Hamad ya maimaita ahankali with hope zata kara gayamai menene abin but Asmeey tai shiru, ganin baisan mene ba but batada energy magana yasa ya gyadamata kai yace "okay" saiya juya yafita daga bayin tareda rufomata kofa zama yayi yadauki wayansa yafara browsing yaga komi toh yanzu ina zai sama mata pad this middle of the night cus yasan Mamie batada shi mema zatai dashi when she's above 50yrs, shiru yayi yasake browsing, it's 2 nadare da saiyaje supermarket yasayo, tissue ne yafadomai arai ahankali ya ijiye wayan yabude kofansu ahankali yafice ya sauka kasa store nasu ya shiga ya kwaso manya manyan tissues guda uku yadawo dasu dakin yasake kulle kofan ya ijiye agado sannan yabude wardrobe another short wando yakawo da vest again sune wanda yagani sai kawai yadauki pant nata guda daya duk yakawo gado yazauna yayi shiru yana tunani wat can he give her for the pain, browsing yakara yaga she can take hot tea bag, sai kuma asa hot water bottle a abdomen, tashi yayi da sauri yasauka kitchen heater kettle nasu yadauko da Lipton da cup da spoon duka yadawo samaa ya jona heater na ruwan zafi a socket yana ijiye komi daidai Asmeey daga bayi cikeda rashin kuzari tace "Yaya"wajen bayin yayi gently yasa hannu yabude kofan tsaye yaganta daure da towel white kanta ajingine da tiles na bango danji tayi kaman tsayuwa na neman ya gagareta, ganinta da towel kadai saida gabansa yafadi she looks damn sexy da kyar yadaure yashigo saiyazo kusada ita hannu yamika sai rigeta kawai saita taso da kyar ta shige jikinshi she just wants this morethan anything, she always have cramps but bata taba kalan wannan shagwaba ko shiga jikin wani haka ba, inama Mom tabata fuskan yin hakan saidai ta aiko Ramla tabata magani, mostly Ramla ma ke kula da ita but taga Ya Hamad especially yanda yake nan nan da ita saitaji kawai she just wants more and more and more of his attention, bataso wannan kula da itan dayake to ever stop cus it feels good, his care makes her feels har yanzu ita yarinya ce, she's still a small girl, ko duk period mood swings dinne oho, but she just wants tayi duk yanda taga dama while Ya Hamad na rudewa yana kula da ita, shiru Hamad yayi yana rikeda ita ahaka sai kawai yadan duka yakama kafafunta yadagata yafito da ita daga bayin yakawota gaban gadon yazauna ya zaunar da ita yanuna mata tissue murya chan kasa yace "I will buy pad in the morning" gyadamai kai Asmeey tayi da kyar hawaye na saukowa shaaa daga idanunta ya mike tsaye daga gadon yace "shirya"yajuya da sauri yawuce wajen kettle din ya tsaya, dan kallonsa Asmeey tayi yanda yajuya mata baya yana kallon kettle but kana ganinsa kasan his ears na kasa paying attention nashi to her even though baya kallonta, da hannu daya tadauki tissue ta bude ta yaga kafin tamike da kyar tana dukewa tadan kallosa ganin baya kallonta yasa ta shirya da sauri tasaka kayan daya ijiyemata saikuma ta duke nan kasan gado takama cikin tace "wayyoo Allah na"juyowa Hamad yayi dasauri yadauki kettle din ya hadamata Lipton baisa sugar ba yazo ya ijiye kan side drawer na gadon yasake dagata saiya zaunar da ita kan gadon, jikinsa Asmeey ta shige dasauri shima lura da kaman this is wat she wants the most sai kawai ya rungumeta yana patting bayanta without saying a word Asmeey tai lamo kaman mussa.
Lipton din yadauka yarikota yace "we will get drugs in the morning take hot tea" yakai bakinta kadan ta kurma saikuma ta kalli fuskanshi tsayawa yayi shiru yana kallonta shima, kwabemai fuska tayi ashagwabe kaman wata yarsa ahankali kaman mai whispering Hamad yace "ke raguwa ce ko?" Girgixamai kai tayi ashagwabe yace "toh sha" da kyar ta sha rabin cup ta girgiza kai, kwantar da ita yayi yawuce bayi yadauko bowl yafito da small towel dinsa yazo yazuba hot water yazo gaban gadon dan kallonta yayi amman saiya daure yakai hannunsa saman cikinta kulle idanunta Asmeey tayi da sauri hawaye na gangarowa, daga rigan Hamad yayi sama kadan yadan sauke ijiyan zuciya cikinta ya bayyana, kin kallon komi sama da cikin yayi saiya daga towel din ya matse yadaura kan maranta zafin towel din yasa ta sauke ijiyan zuciya taji wani dadi for the first time haka yacigaba da mata har around 5 bacci yayi awon gaba da ita.
Tashi yayi yasa hannu ya sauke rigan yarufe mata ciki batare daya bari idanunsa sun kallo boobs nata ba, bargo yasa ya rufamata yadauki tissues din yadaura kan drawer ruwan da komi yawuce yakai bathroom yadauro alwala yafito ya shimfida dadduma yana kallonta yayi rakatanil fajiri, mikewa yayi yadauki wayansa da key machine da jakansa yasake kallonta saikuma yadawo wajen gadon ya kalleta saiya juya wutan dakin yakashe mata yafice.
Wuraren 9 Mamie dake tareda Gwaggo da yau bata fita ba wayanta yahau ringing dauka tayi ganin Hamad ne saitadan tashi daga wajen takai wayan kunnenta anatse tace "Hamadi" dan shiru yayi cikeda bala'in jin nauyin Mamie tunda aka tashi daga salla duk inda zaije ba'a bude ba, ahankali tace "hello Hamadi" murya chan ciki yace "Mamie sh….she is not feeling fine" ya katse wayan, shiru Mamie tayi sai kawai tajuyo tawuce sama kai tsaye tai knocking kofan babu amsa but taji alamun kuka dasauri tabude kofan tashiga tundaga kettle heater su daga Lipton dinsu tissue Mamie ke kallo kafin ta kalli Asmeey dake zaune kan gadonsu but ta kifa ciki dasauri Mamie takamata tace "Asmeey meke miki ciwo?" Muryanta bamaya fita sosai tace "cikina" dasauri Mamie tace "Subhanallahi sannu sannu" before you know it Mamie tahada mata ruwan wanka, tana wanka Hamad yabude dakin da sallama ganin Mamie tsaye wajen bayi yasa da sauri ya sauke kai kasa Mamie tace "ka samo mata magani?" Gyadama Mamie kai yayi ya ijiye jakan sai kawai yajuya yafita Mamie tawuce ta dauki jakan tabude pad taciro guda biyar yakawo sai leda medic plus pharmacy magani ne aciki Mamie tafice takoma kasa takawo mata kunu da kosai tsaf Mamie ta tayata ta shirya tabata magungunan tasha tadan sha kunun da kosai sai kallon kofa take har ita Mamie saida ta lura tace "tunda kindanci bari naje zan dawo anjima na dubaki" gyadama Mamie kai tayi ahankali Mamie tafice, ko 1mins ba'ayi da fitan Mamie ba Hamad yabude kofan yashigo, hada ido yayi da Asmeey dake kwance kan gadon tana sanye da atampa ba dankwali akanta tayi wani irin kyau but idanunta sunyi jan kuka, tana ganinshi tai raurau da ido maida kofan yayi yarufe yazo bakin gadon ya zauna hannunsa yamika ahankali yakama nata yace "how are you feeling"? Gyadamai kai tayi awani irin hankali tace "zansha coke" abin yaso yabasa dariya yadanyi murmushi kadan yace "coke?" Gyadamai kai tayi tsareta yayi da idanu dasauri tasauke kanta kasa, sakin hannunta yayi yamike yafice tabisa da kallo saukowa kasa yayi yawuce kitchen fridge yabude yadauko coke mai sanyi yafito Gwaggo tace "kaga nima bani Lemun goran nan" "jeki dauka" Gwaggo ta ballamai harara, wucewa sama yayi yabude kofan dakinsu ya shiga kokarin tashi tahauyi da sauri yakaraso wajen gadon, ijiye coke din yayi yadagota ta zauna tareda jingina da bango ya zauna gefenta yadauki coke din yabude yabata karba tayi takai baki takafa tafara sha yanda ya tsareta da idanu yasa tasauke coke din dasauri daga bakinta ta boye fuskanta da hannu kunya taji, murmushi yayi yace "sweet tooth"murmushi tayi tacigaba da sha tass ta shanye tadanyi gyatsa ahankali zata koma ta kwanta kawai saiya rikemata hannu dasauri ta kallesa dan lumshe idanu yayi yabudesu sai kawai ya fizgota jikinsa and just hug her so tight, dan rawa jikinta yafara wani irin kunya nakamata, patting bayanta yashigayi yana sauke ijiyan zuciya ahankali, Ya Hamad hardly talks but action dinsa speaks with volume na so much care for her, suna ahaka taji jikinsa yasake bacci ya kwashesa a zaunen rikeda ita. EPISODE 3️⃣8️⃣
Dan dago kanta kadan Asmeey tayi daga kirjinsa takallesa wlh yayi bacci, in her entire life bata taba ganin mutum kwara daya that was as caring as Hamad is to her ba, Munir is very caring also yana sonta but dudda haka not like Ya Hamad, actions na Ya Hamad deeply screams I care for you and I will take care of you no matter what, ranan dayayi saving nata ta tuna yanda taga kofan ya karcesa har a hannu suna jini but baidamu ba he just wanna save her at that moment, bai damu da pain dinsa ba sai nata, if she's hurt because he cares yasan she's hurt, shi kadai yagane marinta akayi rannan, so many things dudda hardly yake magana but he knows better than kowa, yau kuma tun 2 yafarka sabida ita baikoma bacci ba, bai nuna yagaji da kukanta, koda yanda takemai shagwaba ko shigemai jiki ba, she don't really know exactly what she's feeling game da shi, idanma abinda takeji shine love din then she's very very happy she loves him, sosai take kallonsa he looks super calm even while sleeping gashi he's very fine, kawai bataso tafita daga jikinshi even for once second, shi kadai takeso taga tanama kuka yana kallonta dinnan even though bata tabajinsa ya furta sorry ba but the way yake lallashinta speaks sorry to her body, his looks are damn comforting sama da sorry or yakuri or even sannu, anytime yarike mata hannu she feels happy and calm is this love? Sannan bataso taga yafita wlh ko masallaci zaije saitaji wani iri batasan mesa ba kowa na gidan nan is her family ga Abba is Babanta ga Mamie gasauran su Yaya duk suna sonta but dukansu batajinsu kaman yanda takejin Ya Hamad, da kowa na gidan nan ya lallasheta gwara Ya Hamad ya lallasheta, idan kowa na nan Ya Hamadi bayanan she's not happy, ita kawai taita ganinshi agabanta. Sauke idanunta tayi kan lips dinshi dasauri ta kulle idanunta bataso ta tuna jiya kwata kwata dan yanzu zataji jikinta yafara ciwo, so take ya kwanta yanda yake zaune jikin gadon dauke da ita yana bacci looks exhausting to ya zatayi ta kwantar dashi? Daddagewa tayi ita adole mai karfi ta kulle hannuwanta abayansa zata kwantar dashi ko gezau baiyiba saima dan bude idanunshi dayayi kadan cikin bacci ya kalleta da sauri tai wani rauuuu da idanu tace "ka kwantar dani" ahankali cikin bacci kawai ya kwanto gadon tareda ita batare daya saketa yahau patting bayanta ahankali yana sauke ijiyan zuciya he loves sleep gaskiya most times idan yagama aikin dazaiyi a system bacci yake toh ba aiki garesa ba, sosai Asmeey ke kallonshi wlh dadi takeji yanda take jikinsa hannunsa abayanta yana shafawa kaman wata yar yarinya yana bacci murmushi tayi aranta tace "he's my husband" kirjinsa tabi da kallo da wuyansa dan gashi ta hango dasauri tacire idanunta takai kusan good 1hour kallon mijinta takeyi ta kalli nan ta kalli chan kafin bacci yayi nasaran kwasanta ta kankamesa ahaka itama.
Wuraren 1 yashiga bude idanunsa da kyar yakalleta yanda suke rungume da juna yayi shiru how did he ended up sleeping ma baisaniba dan kunya yaji kadan irin shine haka with a girl ajikinsa, gashinta yabi da kallo da kitsonta yana calculating kwanakin kitson tun ana gobe salla kitson na neman 10days yanzu, taji sauki he will take her to the saloon ayi wani, gently yatashi yana zare jikinsa batare daya tadataba yamike tsaye yawuce bayi kafin yayi wanka saida ya wanke kayayykinta na bacci tsaf ya shanyasu ajan bayin yayi wanka fitowa yayi ahankali daure da towel a waist yadan kalli gadon ganin tana bacci yawuce ya shirya cikin wani soft matron yard yasaka hula yabude kofa yafito yana kamshi sosai, Mamie bata falo baiji muryan Gwaggo ba yauta tafi gantali kenan Hameed na wajen aiki sai yamma Mamie ce kawai maybe itama tana daki sallan zuhur wucewa yayi yafice, salla yayi yafito daga mosque yana takowa anatse kansa akasa zuwa gidansu yaga wata faran benz gaban gidansu anyi parking karasawa yayi yadauke idanunsa daga kallon motan daidai yazo gaban kofan gidan aka bude mota aka fito yarinyar ranan nan ne dasuka hadu da ita randa ya siyo laptop kallo daya yamata ya dauke kai tana sanye da Atampa gown yamata kyau yabi jikinta sosai da dan karamin mayafi a shoulder ta zai shige gidansu kawai tashiga gabansa ta tsaya jikin kofan dasauri tace "Hamad it's Aneesah" oh daman itane Aneesah daketa damunsa da chat, kansa akasa cus he can't even look at her with the kind dressing dayake jikinta anatse yace "excuse me zan shiga gida" muryanta na breaking tace "I….i know…." Tayi shiru tana kallonsa kaman zata hadiyesa tace "I know is not proper nabiyoka har gida haka but narasa yanda zanyi kayi blocking dina a watsapp da calls, sometimes ko da bazakamin reply ba but naga ka bude message dina ka karanta shi kadai na kwantarmin da hankali wlh ina tsananin sonka tun rannan dana fara ganinka a hospital din Daddy"ahankali tace "wlh I love you" anatse Hamad yadan juya cus bama yason yanda take gabansa tace "inada mata she's enough for me kiyakuri" hawaye Aneesah taji sunzo mata tarikesu da kyar tace "idan na roki matar taka fa!" Wani kalan juyowa Hamad yayi for the first time yamata wani mugun kallo dayasa gabanta yafadi ta sauke kanta kasa da sauri yace "get your priorities straight! I have a wife Miss I belongs to her ita kadai I don't have any business with you, step aside" yafadi adan zafafe, matsawa Aneesah tayi Hamad yashiga gidan yarufo musu gate, Aneesah tabisa da kallo hawaye na gangarowa daga idanunta tawuce mota tabude tashiga wannan wani kalan jarabawa ne? She has so many suitors masu sonta but hakanan daga ganin wani tech guy yazo yima Dad installing software a hospital shikenan? Da yaya ma tasami number sa da kyar manager Dad ya nemo number yabata dayaya tai tracking gidansu? Rannan nan tabiyosu daga wajen system din nan that plaza tabisu har asibiti taga yafito kam machine tabisa taga gidansu.
Komawa cikin gida yayi Mamie yagani a dinning ta ijiye abinci da kula a tray tana ganinsa tace "zoka daukan muku abinci" karasowa yayi tace "this pepper soup na Asmeey ne zai rage mata ciwon cikin" gyadamata kai yayi yadauka yawuce sama kofa yabude yashiga Asmeey is still sleeping ijiye abincin yayi he's hungry jiya baici wani abincn kirki ba white rice da stew yadeba kadan yakoma desk dinsa yafara ci yana taba system wayansa yakalla saiyasa hannu ya dauka watsapp yashiga yaduba block yaga number yafito wajen calls yaduba shima yaga block saiya juyo ya kalli Asmeey saiyayi shiruuuu sai kawai yayi murmushi yamaida wayan ya ijiye yacigaba da cin abincinsa.
Wuraren 2:30 ta farka baccin yamata bala'in dadi yau dan motsi tayi hakan yasa Hamad yajuyo da kujeran ya kalleta saikuma yatashi yazo wajen gadon yadan kalleta suna hada idanu tasauke idanunta, mugun kunyanshi takeji tun jiya bata iya hada ido dashi dagota yayi tamike tsaye murya chan kasa yace "are you feeling better now"? Gyadamai kai tayi murya chan kasa na bacci tace "zansha coke Ya Hamad" dan dariya kadan yayi yace "I guess this is the period carvings dana karanta dazu" yayi maganan ahankali yana wucewa da ita bathroom nasu kayanta taga ya wanke akunyace ta sunnar da kanta ruwan zafi yatara mata a bucket sannan yafito drawer yaja yadauki ledan pad da pant yawuce nayin yasake knocking yabude ya ijiye mata komi yawuce yafita Asmeey tabisa da kallo he's so damn caring, he just knows everything.
Kusan 10min tabata abayin tafito tray tagani na abinci ya ijiyemata agado ga coke mai sanyi dasauri ta dauka coke din tana kokarin zamaya shigo hararanta yayi akunyace ta sauke kai magungunan ta ya dauka yabude su yazo gabanta ya tsaya ya mika mata karba tayi tasha da coke Ya Hamad kawai ya girgiza kai ganin she's in coke era yawuce ya zauna, pepper soup tasha taci rice itama kadan rannan haka suka wuni he was just taking care of her kaman kwai ko fita palor batayi ba all through rannan, Mamie ma saidai tazo ta gaidata daga kofa batare data shigo ba. ******
Bayan 4days
Yau day5 na MP! Kwata kwata batasan tanada son bacci hakaba sai agidan nan ashe ta iya bacci, babu abinda takeyi wlh tsinke bata dagawa, Ya Hamad yajuyo gyara daki ya wanke mata kaya yamata guga yakaita bayi yahada mata ruwan wanka yafito mata da kayan sawa yakawo mata abinci yabata magani iyakanta, tai wanka tashafa mai tasaka kaya sai kyau take kara yi Ya Hamad yasayo mata wani cream mai kyau na Olay da shower cream dinsa, fuskanta ya warke tsaf kaman ba'a taba marinta ba jikinta ma haka sai yan tabon da baza'a rasaba, kullum tana daki especially this days kuma Ya Hamad bai kara mata komiba dudda baida magana baida yawan surutu but idan yana kula da ita is as if he's communicating with her. Yau Saturday around 11:30AM ta farka Ya Hamad tagani gaban desk dinsa yakifa kai yana bacci murmushi tayi tashi tayi tabude wardrobe ahankali tadauki wani lace baby pink taciro yau kawai tanaso tayi gayu bayi tawuce dasu tai wanka ta shirya tsaf abayin tafito, cream ta shafa ta feffesa turare saita saka kwalli bata iya tasaka dan kunne da daura dankwali ba man baki tashafa taciro baby pink veil dinta tajuyo takalli abincin dake wajen bataso taci, indomie kawai takeso taci slippers ta zura tana gyara gyalen kanta tabude kofa tafice, ahankali take tafiya muryan su Abba taji a falo da yayinsu harda Gwaggo wani kunya taji kaman ta koma daki but tasan sun ganta hakan yasa tashiga saukowa kanta akasa, shi karan kansa Abba daya ganta saida yace "Masha Allah Asma'u, kin fito"? Gwaggo tace "yau kwanan ta nawa gidan nan jibi yanda yarinya tai kyau jama'a daman Asama nada kyau haka"? Hameed yace "ta ina zamu sani kullum muna ganinta da kumburaren kumatu da lips da jan idanu" Mamie ta hararesa yayi shiru, karasowa falon tayi akunyace tana lullube bakinta da gyale tana murmushi tace "Abba ina kwana" Gwaggo tace "toh mayafin zakisa abaki" murmushi Abba yayi yace "lafiya lau yarinyana ya karfin jiki ya hannu"? Ahankali tace "fine" Mamie tace "kinyi kari?" Girgixamai Mamie kai tayi ahankali tace "indomie zanje na dafa" Mamie tace "zaki iya dafa indomie da hannu daya konasa Lami ta tayaki dafawa ai tana kitchen"? Akunyace sabida yayinta tace "zan iya Mamie" takalli su Ya Mustapa tana rufe fuska tace "Yaya ina kwanan ku" duk murmushi sukayi Ya Mustapa yace "rannan Monday zakuzo asibiti za'a bude hannun ayi xray agani" gyadamai kai tayi, Ya Abdullah yace "Amarya anyi fresh" dariya Faisal da Hameed sukayi tawani lullube fuskanta cikeda iskanci Faisal yace "mijin naki fa?"Bata gane sarcasm dinsu ba hakan yasa da zuciya daya tace "bacci yake Yaya" Hameed yace "wayyoo Allah na aure, Abba ai gobe ne zuwan ku gidansu Zee ko"? Dakuwa Abba yamai yace "kaci mai garinku Hameed" Gwaggo tace "ahap na gayamaka idan baka aurar da takadirin nan ba saiya hanamu zaman lpy agidan nan" Mamie takalli Asmeey tace "jeki dafa indomie ki" gyadama Mamie kai tayi tamike tawuce kitchen har Gwaggo kallonta suke, Asmeey tayi kyau, tayi fresh sai sheki take, tawani kara kumari tayi haske ga fara'a a fuskanta. Gwaggo tace "wlh banyi nadaman wannan aure ba, aiko jiya Muhammadu Sani yakirani nake gayamai idan yaga yanda yarsa ta chanza zai rantse ba Asmeey bane toh babu mai dukanta kullum saidai naga Hamadi ya goyo wannan jakan katuwa ya sayawa matarsa kayan dadi yawuce sama baya sammin" duka yayyin saida suka wani harari Gwaggo, Faisal yace "kaga Gwaggo da magana ke matarsa ce dazai sammiki"? Gwaggo tace "yoh to ubanwa ya haifi ubansa? Baniba tunda dai shine mukeda shi agidan nan mai mata ai kamata yayi yakawo kayan dadin sai nima asammini nasa albarka" tashi Abba yayi yace "bari nadan kwanta yau natashi da ciwon kai" duka yaran harda Gwaggo sukace "Allah sawake Abba" wucewa yayi Mamie tabisa abaya yayyin suka cigaba da zama, ka'ida rannan asabar tareda iyayensu suke zuwa suyi breakfast idan ba sunada wani abinyi ba basa barın gidan sai wuraren azahar.