Uwa ko ukuba complete by m shakur - Chapter 27
Uwa ko ukuba complete by m shakur Chapter 27: Uwa ko ukuba complete by m shakur Chapter 27. Ahankali take bude idanunta da kyar kanta yayi mata nauyi,…
4,387 words
Ahankali take bude idanunta da kyar kanta yayi mata nauyi, jikinta tabi da kallo an lullubeta da bargo, komi daya faru jiya nadawo mata dasauri tabi dakin da kallo especially wurin desktop din Ya Hamad datasan anan Mamie tafadi saitaga an maida komi daidai, dawani kalan sauri tamike ta tashi zaune tana dafa goshinta dataji yana mata ciwo tace "Mamie" dudda babu karfi ajikinta saukowa tayi daga gadon tana tafiya ahankali, Mamie kawai takeso taje tagani, bude kofan dakinsu tayi ahankali baiyi making sound ba tafito, tundaga wajen take jiyo muryan Gwaggo adakin Mamie na zubawa Mom ashar, cigaba da tafiya tayi daidai gaban dakin zatasa hannu tabude kofa kenan taji muryan Hameed yace "haba dan Allah just look at bakin cikin da Hamadi ya kwana dashi! This is what I said lokacin nan, what is the point na auro yar matan nan da lafiya ta da tunanina? This is the same reason yasa su Ya Musty basu taba kwadayin auren su Aya da Aysha ba, waye ita? What gives her the right ta taba mahaifiyar mu? Wlh wlh I said it jiya, Hamadi ma yafadi if anything happens to Mamie mu that woman will pay for it na rantse da Allah!"Faisal yace "kawai dai dan laifin wani baya shafan wani ne but mata irin Salima baka fatan wani abu nasu ma yashigo hannunka I am so angry God!" Ya Abdullahi yace "jikina har tsuma yake da ace damuka ganta awaje munsan ta taba Mamie da wlh sai na mata jina jini, saina fasa munafukin gilashin idanun nan nata, very stupid useless woman" Gwaggo dake kuka tace "wlh, wlh dan kawai Asama jikata ce babu yanda zanyi amman da wata ce da sainayi nadaman aurota da Hamadi yayi" anatse Ya Mustapa yace "duk ku yakuri Mamie is fine bagashi nan tana bacci ba" Ya Mustapa yace "Hamadi stand up kaje dakinku Mamie is fine" ahankali Asmeey taji Ya Hamad yace "I want to stay with Mamie Yaya!" Wani iri zuciyan Asmeey yayi sai kawai tashiga komawa baya zuciyanta na radadi tajuya da dauri takoma dakinta maida kofa tayi ta rufe ta jingina da kofan tana wani irin kuka feeling extremely bad because of ita Mom tayi hurting mahaifiyarsu, Mom tayi hurting Mamie all of them are angry with her, tip na hancinta da bakinta har wani rawa rawa yake tsabaragen yanda zuciyanta ke radadi, dago idanunta tayi ta kalli wardrobe nata tai shiru saikuma ta kalli karyayyen hannunta, "What is special about rayuwanta? Is all because of her zuciyan kowa ke lalacewa tundaga kan Mom, Baba, yayyinta Ya Aysha tace Mom bata magana da Ya Aya all sabida ita, Munir kullum jin haushin Mom yake all sabida ita, itama Mom haushin Munir takeji all because of her, Baba yasaki Mom all because of her, Mom tayi hurting Mamie all because of her, kowa is angry, ran kowa ya lalace even Gwaggo, tasan har Abba, Ya Hamadi too mai hakuri he's angry sabida Mom ta taba mahaifiyarshi, yau ta farka ita kadai all alone ana cemai yazo wajenta yaki, kowa is angry with her anajin haushinta, as long as she's here Mom will keep on coming and she will hurt Mamie sabida kowa na fita aiki agidan nan aiki, as long as tace zata koma Bauchi Baba bazai bari ta zauna ba he will be angry, how many more rayuwa da zukata zasu lalace sabida ita? Because of ita kadai ba'a zaman lpy a danginsu gabaki daya menene amfanin rayuwanta? She is the only one in best position na to end all this drama, all this headache, She's tired! Kisan kai haramun ne but Allah can have mercy on her ya iya yafe mata duba da yanayin kalubalen rayuwanta ko? Ta tambayi kanta, already ita tsinanniya ce, duka bakin da Mom tamata sun kamata, Mom tariga tace she will never be happy gashinan tagani she's not, gidan nan da kowa ke sonta kowa ke ji da ita yau kowa ya tsaneta, kowa na jin haushinta sabida abinda Mom tayi har Ya Hamadi! Har Gwaggo, nobody is here with her and she's sick! She's all alone! Kanta is banging but she's alone, batada kowa, kawai sai Munir yafado mata arai.
Tashi tayi tadauki wayanta dake gaban madubi tabude tana addu'a Allah sa tanada kati dialing number shi tayi ringing daya yadaga yace "Ya Asmeey naaaaa wlh I miss u awajen Baba na karbi number nan saisa nakeda shi, yau nake shirin kiranki dama" hannu ta daura akan bakinta tana taushe kukan datakeji da danne kukan kafin ta cire hannunta ta daure karya gane wani abu tace "duk duniyan nan kai kadai zuciyata tace inkira not even Ya Aya ko Ya Aysha, Munir you are my best best best brother wlh ina sonka Mun…..ir…"Muryanta yafara rawa dasauri ta daura hannunta saman baki Munir kaman yaso yagane saikuma yace "menene wai kewana kikeyi ne kike gayamin kina wani sona" Gyadamai kai tayi kaman yana gabanta tace "I just called to tell you ina sonka Munir you are my best best best brother the best, bye" yana kokarin magana ta katse wayan ta mike dagudu tayi wajen wardobe tabude tashiga fito da kayanta tana jefarwa kaman mahaukaciya tadauki ledan maganin ta bude taciro maganin bera, ta tsaya ta kalla an rubuta RAT POISON ajiki, sai kawai tashiga budewa da hakori kanta na banging taci nasaran bude maganin kawai tadaga maganin tabude baki zata zazzaga aciki aka bude kofan Hamad na shigowa, idanunshi sundan kumbura sunyi ja fuskanshi da wuyansa ma haka ya kalleta, tsayawa Asmeey tayi tana kallonsa ahaka, shima yana kallonta yana kallon ledan Rat poison daya gani a hannun, kawai Asmeey ta daga zata juye abakinta taku daya Hamad yayi kaman wani zaki yawani daki hannunta ledan maganin ya kufce mata ya zube akasa, yawani yi ihu da saida gidan ya amsa yace "are you mad or are u sick upstairs? Did you know abinda kike kokarin sha"?Kallonshi Asmeey ta tsaya tanayi hawaye na fita daga idanunta zuciyanta namata zafi sai kawai ta tsugunna batare data cemai uppan ba yaga takai hannu tana tattare maganan na kasa ta kwasa da hannu tabude baki zata zuba kawai yadagata yaja kama hannunta ya kakkabar ya jinjiagata tareda daka mata tsawa. "Husnah!". EPISODE 4️⃣5️⃣
Hamad yace "kidawo hayyacinki do you know what this is?" Kin kallonshi tayi a idanu cikin wani irin murya na wacce is deeply hurt tace "is rat poison I want to take it na mutu kowa ma yahuta!" "Kinaso ki mutu!"? Hamad yafada azafafe, Asmeey tayi wani ihu da zakin muryanta yadauki gidan tace "yessss, ni kabarni na mutu me ruwanka dani!" Daidai su Ya Mustapa na fitowa cus Hamad yabar kofan abude they could here them, Abba biyedashi da Gwaggo da gudu jin hayaniyansu da sauran yayyinsu dasauri Abba yashiga tsakiyansu yana kallon yanda Hamad kewani irin huci yana kallon Asmeey itakuma kanta akasa tana kuka sosai tana goge fuskanta da bayan hannu yace "menene Hamad? What happened"?Dukawa Ya Mustapa yayi yadauki ledan maganin yace "munada rat poison agidan nan ne? Hamad ka sayo rat posion ne akwai bera adakinku ne?" A mahaukacin zuciya Ya Hamad yace "ask her Yaya?" Ya Musty yakalli Asmeey zaiyi magana Abba yariga sa yace "an ina kika samo maganin bera mezaki dashi?" Kanta akasa ta daure ta danne kukan datakeji tace "ci zanyi Abba" "ci Asmeey? Ci zakiyi"? Gyadama Abba kai tayi tace "Abba so nake naci sainai bacci kawai namutu a baccin kowa ya huta at…..atl……" tafashe dawani irin kuka tace "Abba at least kaga na mutu Mom bazata dinga zuwa gidan nan tana hurting Mamie ba kowa saiya huta, you all don't have to be angry with me abarni ni kadai, basaikun tsaneni ba" dudda maganan Asmeey harda yarinta amman saida Abba yayi mutuwan tsaye haka sauran ma! Hamad da kirjinshi ke zafi yace "you think tsanan ki akayi? Wayake da time na tsanan ki acikin mu"? Ahankali tace "amman ai kun tsani Mom so tsananta ya shafeni, I get it I know Mom hurt Mamie that was very wrong but Mamie tafara pushing Mom, I was telling Mamie tabarmu da Mom karta shiga but she was not listening to me, but kowa hates my Mom and kun tsaneni nima" cikin tsananin fushi Hameed yace "ke kindaisan apart from being Matar Hamad ke kanwarmu ce ko idan kikamana shirme anan i will come and beat nonsense comot from your body tunda maybe bugamiki kai da muguwar matan nan tayi jiya yataba miki brain" cikin wani irin kuka tace "everybody is beating me! I am nothing! Ni ba kowa bace, kowa treat me like Asmeey is just bag of dirt, banda daraja na yar adam, i told you banga amfanin rayuwana ba I just want to die and rest, na tabbata mutuwa yafi rayuwana sauki" Gwaggo tace "ba shakka maganan Hameed asama kin haukace wallahi, uwarki takawo miki maganin bera dai tace kici shine kike fakemana da bama sonki yooohh dan ubanki inbanda ke jakace Mamie ta ture mahaifiyarki sabida ubanwa tayi? Ba sabida taga ana kokarin kasheki bane?" Juyawa Asmeey tayi zuwa wajen wardrobe kawai tace "tunda kun hanani kashe kaina I'm living Kano zan koma gidanmu, bansan dalili na Mamie takara jin ciwo or got hurt kutaru ku tsaneni abar ni kadai adaki ba, I'm living this house" dasauri Abba yayi wajenta cus all he sees is small little yarinya with no exposure in pains and feeling guilty and insecure hannunta yakama cikeda lallashi yace "My poor child Asmeey babu inda zaki" cikin kuka tace "Abba bazan iya auren nan ba! Bazan iyaba Abba zuciyana ba dadi I can't do this Abba barin gidan nan zanyi" "fine!" Hamad yafadi cikeda zuciya kaman kuturu, Asmeey takalleshi tana kuka ahankali, jikinshi ya shiga tattabawa yaji babu kudi saiya juya yawuce wajen bagpack dinshi yabude ya kwaso duka cash din dayake dasu cikin sunkai kusan 30k yataho zuciye kowa na kallonsa yawani kalan jefa kudin akan gado yace "pack your things kitafi ga kudin mota!" Yajuya zai tafi atare duka yayinsa da Abba ganin Hamad ya zuciya sosai sukace Hamad! Asmeey ma takalleshi sosai idanunta sunyi jajur zuciyanta kaman zai fito takara harkuza, amman Hamad ko juyowa baiyiba yayi kofa zai fita Hameed da Faisal suka tare kofan ya tsaya chak yana musu wani kallo yace "kutashi daga kofa na fice"Abba yace "Hamad badakai nake magana ba" juyowa yayi idanunshi sunyi jaa yace "Abba tace she wants to go tagaji she's not doing again nabata kudin mota ta tafi what else? She thinks she's the only one hurting anan? She wants to commit suicide ko? Tayi parking things nata ta tafi Bauchi taje tayi achan? She's blaming Mamie na that stood for her how dare she! She thinks all of us bama sonta? She feels we are angry with her? Tace anbarta ita kadai did she know who my mother is to me?Comparing wani abu kike ko measuring something?" Cikin kuka Asmeey tace "bazan taba comparing komiba, I love Mamie sama da yanda kuke sonta ma, ina tashi ita nafara tunawa I went straight naduba ta naji maganganun da akeyi har ana cemai yazo wajena yaki!" "Why will I come? Mezanzo namiki? Are you that insensitive Asma'u dazaki bude ido and conclude anajin haushinki you think everyone is like your mother Salima!"? Kallon Hamad Asmeey tayi maganan sa sunmata zafi sosai shima kallonta yake maganganunta sunmai zafi, kan kowa na dakin yadauki chaji, bayan hannu Asmeey takai tashiga share fuskanta tana kara yarda yes bakin Mom ya bita especially maganganun da Hamad ya gayamata yau, saita kalli Abba dayama rasa tacewa tace "Abba I know not everyone is like my mother but she's still my mother ba yanda zanyi! I can't stay da mijin da baya girmama uwata ba! Koba komi yauna fahimci dalili guda da Mom batason auren nan Ya Hamad ya tsani mahaifiyata sosai and kowama ya tsaneta kaga ai aure bazai yu ba nahakura!" Azuciye Hamad yace "nima nahakura! Go and marry your Mom" Kai! Kowa saida yakalli Hamad yawuce kofa ganin yanda ya zuciya zai iya barar da Hameed da Faisal yasa suka matsamai yabude kofa yafice fiuuuuu. Gwaggo tace "lallai Asama yau kin gwadamin ke diyar mahaifiyarki ce Salima indai zaki bude baki ki gayama mijinki maganganun nan, yaron da duka azaban yajin da uwarki tasamiki saida kika gogamai ajiki kin manta ko? Anan ya kwana zaune dake bai runtsa ba, sabida ke Hameed saida ya hakura da aurensa mun zauna za'a fara magana kenan yakiramu kan mahaifiyarki tazo Hameed yabar aikinsa na baki duk sabida muzo mu ceceki kice mana bamu sonki haushinki mukeji, Mamie na kwance gado allura na uku kenan Docta ke mata amman ki bude baki kice laifinta ne mesa ta shigan miki itace ta fara tura Uwarki, da asuban nan kafin muje dakin Mamie dukan mu muna nan muka dubaki doctor yaduba ki kafin muwuce dakin Mamie, na mance dudda jiya Mamie na layi saida tabi Hamad bayi ita tamiki wanka ta wanke miki yajin jikinki da ruwan gishi da kankara amman Asmeey godiyan dazaki mana kenan! Kin nuna mana taki kalan kitafi Allah yakiyaye hanya"dasauri duka yayyin Hamad suka kalli Gwaggo harda Abba suka mata wani mugun kallo, tace "Allah sa hakane mafi alkhairi kije idan darabon zamu sami jana'izar ki bayan uwar ki ta halakaki zamu samu, kije" Gwaggo tajuya tafice Hameed yafice Faisal yafice Ya Abdullahi yafice dakin yarage daga Abba sai Ya Mustapa ciki.
Asmeey tajuya azuciye zata cigaba da ciro kayanta na sip saikuma taji takasa sai kawai takifa kanta a kofan wardrobe din tana wani irin kuka mai bala'in sosai zuciya tabama Abba da Ya Mustapa tausayi Abba yariketa yakamata saiya zaunar da ita akasa yakalli Mustapa yace "bani goran ruwanchan kagani" dasauri Ya Mustapa yakawo bottle water dake kan desk yabude yabama Abba ya karba tofa addu'a yayi ciki na sanyaya duciya yadafa kan Asmeey yace "sha ruwan nan" da kyar Asmeey ta iyashan kadan Abba yacire ruwan daga bakinta yashafa kanta yana kallon yanda take wani irin kuka ta taba zuciyanta tace "Abba na shiga uku na lalace wlh na bani Abba, Abba zuciyana yanamin kaman yafi komi na duniyan nan nauyi, Abba mutuwa baifimini ba da irin yanda zuciyana keyi? Eh"? Abba yace "kowani dan Adam da tasa kalan jarabawa aduniya kuma kashe kanka da kanka haramun ne wuta zaki shiga direct sannan kinyi wahalan banza, kingama wahala na duniya kisha wahala dan Allah baya karban ran wayanda suka kashe kansu ta sauki, kikagama wahala ki mutu kije kabari ki wahala kije lahira ki wahala toh ina dalili? Asmeey ina tauhidin ki? Ina tawakkul dinki? Ina Imani da kaddara dinki mai kyau da mara kyau? Ina yarda cewa komi daga Allah ne? Eh Asmeey?" Tana wani kalan kallon Baba face "Abba yaya zanyi kasan yanda zuciyana kemin sabida abinda Mom tama Mamie? Abba abin yamin ciwo sama da kowa, Abba kaga sabida ni Baba yasaki mahaifiyata! Sabida ni Mom bata magana da Ya Aya, bata shiri da Munir! Munir haushin Mom yakeji sabida ni! Sabida ni Mom ta tsaneku gabaki daya! Abba everything is happening because of me, this beautiful house, this beautiful family da kowa ke murmushi kullum baku fada bakujin haushin kowa yau because of me sabida kun shigo dani gidan nan komi ya chanza!"Abba I think ni kambun baka ce duk inda na taka ko na shiga fitina na bini banda good luck, bantaba jin ance Mamie batada lafiya ba but sabida ni Mamie na gado ba lafiya everything's na faruwa because of me me me me meeeeee, Abba Abba ku barni natafi I don't want to be reason dazaisa wani abu yasami Mamie koya sami gidanku koya sameku, Abba ni yar Mom ce kome tamin is okay wlh nasaba but is not okay ya shafeku nacigaba da zama anan more and more abubuwa will happen tayaya zan kalleku? How can I look at you all bayan nasan I am the reason for everything"? Ya Mustapa yakusan kuka forget some maganganun Asmeey akwai shirme da yarinta but now datakema Abba addressing abun he understood where the girl is coming from she's feeling extremely guilty because of Mamie, bama ta kanta da ciwonta takeba ta Mamie take and she feels barinta nan will make everything okay koba komi tanada certainty cewa Mom bazata kara zuwa ba so kowa will be safe. Kanta Baba yashafa yace "stop blaming kanki for mistake na mahaifiyarki! Abinda yasami Mamie Allah yariga ya kaddara hakan zai faru and it's okay komi yawuce, koda wasa kada ki kara kuskuren fadin cewa mun tsaneki ko wasu maganganu makamantan haka koda ace baki auren Hamadi ke diyata sannan kuma kannin su Faisal I know yarana they will never hate you saima suyi protecting naki kinji" gyadama Abba kai yayi yace "magana ta wuce banson kara jinta karki kara tunanin kashe kanki wannan rayuwan Allah ne ya baki shiya halittoki shi kadai keda ikon karbanta ki gujema azaban Allah sannan kiyi istigifari da abinda kika aikata na kusan kashe kanki just now"
Sosai wani tsoron Allah ya shigeta tace "Astagafurullah!" Abba yace "konmayi salla?" Girgixamai kai tayi anatse yace "tashi kije kiyi salla kiyi wanka zansa mai girki takawo miki abinci" gyadama Abba kai tayi Abba ya yunkura zai miki ahankali tarikeshi Abba yajuyo ya kalleta yunkurowa tayi sai kawai tayi kneeling agabansa tahade hannuwanta biyu tafashe da kuka tace "Abba I am sorry kayafemin, Ya Mustapa kuyakuri dan Allah bazan karaba, I am very sorry" murmushi Abba yayi sosai anatse yace "nahakura Doctor kaima kahakura?" Gyadamata kai yayi yace "tashi kije kiyi wanka komi yawuce"tashi tayi ahankali su Abba suka wuce suka fita suka kullo mata kofa tsayawa tayi takalli kudin da Ya Hamad ya watsamata akan gado sai taji kukan dayafi na dazu yazo mata sosai, Abba duk suka juyo kukan Abba zai koma Ya Doctor yarike Abba tareda girgizamata kai yace "she's crying sabida mijinta ne yanzu, kabarsu Abba zasu shirya, kuma mubar Hamad yayi fushi karkamai maganan ya shirya da ita, Asmeey na bukatan tasan daraja da kima da mutunci dakuma matsayin mijinta arayuwanta, bakaga da kanta takasa cigaba da fito da kayan ba? Ai bamu cemata karta tafi ba shima kuma yabarta ta tafi, she needs to know mahinmacin mijinta Abba next time bazata kara irin kuskuren nan ba, sun sami rashin fahimta su biyu dudda Hamad bai fahimceta da manufanta kaman yanda mu yanzu muka fahimceta ba, but abinda yamata was very good Abba! Shine mijinta and yes shine mijinta! Comparison na uwa da mata is a no no dudda itama yarinta yasa tai maganan she didn't mean it, but gwara daya mata haka next time suka sami wani matsala bazata sake kalan kuskuren nan ba" ijiyan zuciya Abba ya sauke he respect thought na Dr sosai a yaransa sabida yanada hankali da hikima sosai yace "amman kana gani auren nan zaiyi lasting wannan mayyar mata tazo kano"? Murmushi Dr yayi yace "Abba babu abinda zai sami aurensu sabida yarannan sunason junansu sama da yanda su kansu suka sani and type of love nasu is not something that is easy to break, Asmeey da kanta tace daza tafi da kanta kuma takasa cigaba da ciro kaya, dakuma kanta da zauna tana kuka, dakuma kanta tabamu hakuri, Abba she's gradually developing love for Hamadi that is getting stronger than tsoron datakema mahaifiyarta, da ace dane da tuni ta tafi but kalla dudda uwarta na fushi she stays here dudda babu wanda ya riketa mijin yama bata kudin mota but she couldn't go, Let them be, auren nan Allah kadai zai iya rabasa" ijiyan zuciya Abba ya sauke yace "bari naje wajen Mamie je wajen kanninka" Gyadamai Kai yayi Ya Mustapa yawuce dakin Hameed.
WAYE KEDA LAIFI A FADAN NAN?
HAMAD WENT TOO FAR RIGHT?
SHI YA NUNA TASA UWAR NADA DARAJA YANUNAMA ASMEEY TATA UWAR BATADA DARAJA??
SHIN HAMAD YA KYAUTA?
ASMEEY TA KYAUTA DATAI BLAMING MAMIE?
COMPETITION ASMEEY KEYI DA MAMIE??
SO TAKE HAMAD YAFI SONTA KAN MAMIE??
WAT EXACTLY ASMEEY KESO??
Let's discuss 💃 EPISODE 4️⃣6️⃣
Hamad yagani zaune kan gadonsa yajingina da bango yana kallon window gasu Faisal da alamu sunmai magana sun gaji yaki kulasu, karasawa yayi yazauna gefen Hamad din yakallesa sai kawai yayi patting hannunsa yace "Hameed nasan kaine sarkin update, is this the second lovers fight ko first?" Atare Faisal da Hameed har suna hada baki sukace "second ne Ya Doctor" dan murmushi yayi yakai hannu yashafa kan Hamad yace "ba'a handling mata da zuciya haka Hamad! Kacika zuciya, aka ganka sai adauka bawan Allah ne kai ba'asan kaine fitinannen yaron gidan nan ba mai dan banzan zuciya, why will you give matarka kudi and tell her to go"? Baimason maganan yunkurawa yayi zai tashi daga gadon zai wuce Ya Mustapa yarikeshi kawai saiga hawaye shaar! Yasauke kansa kasa hawayen na diddiga, Yayinsa duk suka taso, murya chan kasa Hamad yace "leave me alone Yaya" Ya Mustapa yace "anki dawo ka zauna anan" yakamasa badan yaso ba ya zaunar dashi, ahankali Ya Mustapa yace "ba inda zata, Asmeey is not going anywhere" murya chan kasa yace "ina ruwana" yawani juyar da kanshi su Faisal sukace. "awwwwnnnnnn" cus He looks so cute wlh dayace ina ruwanshi, Ya Mustapa yace "kadauka you can live without Asmeey ta tafi? Haka zaka dinga mana kuka kullum" bayan hannunsa yasa dasauri ya goge fuskansa yace "ni I am not crying because of her ta tafi mana! I am just sad ne because of Mamie" Faisal yace "wlh karyane munafuki! Ta tafi wazaka dinga matsawa agado"? Dawani kalan sauri Hamad yamike Ya Mustapa yakamosa yana ma Faisal dakuwa yace "wat is wrong with u?"Ya Abdallah yace "Ya Doctor gaskiya ne fa mace wasa ce? Idan ta tafi baida wajen biyan bukat….." tashi Hamad yayi yace "niku saken" ya fizge hannunshi yawuce yafita daga dakin Ya Mustapa bai damu ba he will talk to him later dan yan iskan yaran nan will not let him speak to him, sai suma yahau magana dasu kan Asmeey yana musu bayanin situation na yarinyar.
Wanka tayi tafito wani gown tasaka da hijab tai salla saitai shiru kan dadduma tana kallon kayan data ciro saikuma ahankali tace mesa ban tafiba? Fuskan Ya Hamad tagani ahankali kaman wata marainiya ta kwanta kan dadduma tana kuka saikuma ta lallaba ta tashi tacire hijabin tawuce tashiga kwashe kayan nata tana maidawa wardrobe wlh hakanan taji bazata iya tafiya ba bazata iyaba and for the first time in her life saitaji damuwan fushin Ya Hamad over shadow tunanin Mom da rashin kashe kanta da batayiba, tsaf ta maida komi tasa hannu ta tattara kudin tawuce ta ijiye akan desk dinshi, tsintsiya tawuce tadauka tazo zata fara shara danta kwashe maganin beran kawai she now realize bata taba share dakin nan da kanta ba tunda tazo fidan nan kullum Ya Hamad keyi kuka taji yazo mata mai kyau tazauna tayi ta koshi sannan tashiga shara ta share komi ta kwashe ta zuba akwandon shara tazo ta gyara gadon da hannu daya takara zama akasa ahankali tai shiru tana kallon kofa knocking, akayi dasauri ta dago kanta ana bude kofan Hameed tagani rikeda plate na abinci dasauri ta sauke kanta kasa tanajin wani kunyansa, maida kofan yayi yarufe yana kallon yanda ta gyara ko'ina aransa yace "ohh my bro don charm this girl finish Asmeey you are a goner, kitafi mana mugani bayan Hamad yagama siye zuciyanki" zama yayi ahankali akasa kan carpet din ya ijiye abincin agabanta yace "even though nace zan zazzaneki that does not mean zan barki da yunwa, now eat" abincin ta kalla ahankali saikuma ta kalleshi suka hada ido ita yake kallo duk tausayi ma take bashi, hawaye ne suka zubo daga idanunta ahankali tace "I am sorry Ya Hameed I am sorryyyyyy" murmushi yamata yace "kintaba ganin yaya yayi fushi da kanwa I was never angry with u dazu ma u piss me off yasa nace zan zaneki but I will never do that so kike Hamad ya shakeni ke kinsan karfin mijin nan naki kuwa"? Yazaro idanu yace "yafi Antony Joshua wannan wrestler din karfi fa, na tabamai mata ai sunan Hameed sorry, Oya it's okay eat" bude kofan akayi Faisal yace "is there water here ko no water" Ya Abdullahi biye dashi yace "I come bearing drinkssssss" coke da Fanta a hannunsa making wani funny gesture dayasa tayi murmushi hawaye na gangaro mata feeling so bad akan abinda tace akansu wai sun tsaneta sai kawai ta fashe da kuka duk sai sukazo suka zauna suka zagayeta Ya Abdullahi yace "it's okay Asmeey" Faisal yace "ya isa kinji Asaman Gwaggo" one thing she understand is men are so easy going da matane su probably da basu yafemata ba but look at them, ahankali tace "Yaya dan Allah karku gayama Mamie abinda nayi dan Allah" atare dukansu sukasa hannu a lips sukace. "Pinky promise" Coke Ya Abdullahi yabude mata yace "gashi take" amsa tayi ahankali yace "but don't ever ever ever think of suicide kinji ke musulmace idan kika kara kalan tunanin lokacin ne zamuyi fushi dake sosai right boys" tare sukace right! Ya Abdullahi yace "Hameed karo abincin duk muci tare naga nata duk ya biyamin rai" tashi Hameed yayi yace "shikenan nadawo in charge of kitchen yanzu" yafice chan sai gashi da katon plate na abinci da spoons kawai duk suka zauna wajen sunaci tare tareda ita suna surutu she felt better suka gama suka fice da plates tashi tayi ahankali tayi kofa budewa tayi tafito tana kalle kalle.
Dakin Mamie tabude ahankali ta shiga zaune taga Mamie da farkawanta kenan babu kowa adakin tana ganin Asmeey tace "zo Asmeey naga goshinki Subhanallahi dünya kumbura" wani iri Asmeey taji how could she even blame this woman meya sameta dazu kawai dawani gudu tayi wajen Mamie kawai ta rungume Mamie tahau kuka tace "I am sorry Mamie I am sorry" Dagota Mamie tayi tace "common I am fine ya isa dena kukan haka jibi udanunki tuntuni kike kuka ko? Bagani lafiya ta kalau ba komi yawuce ya isa" Mamie ta sharemata idanu tana murmushi, Abba ne yashigo yace "ahh kin tashi akwai abinda ke miki ciwo"? Girgizamai kai Mamie tace "babu abinda ke damuna Alhamdulillah" tashi Asmeey tayi tafice danta basu waje takoma dakinta saita kwanta agado tai shiru tana kallon kujera da desk din Ya Hamad tarasa yanda zatayi taji dadi she miss him badly. EPISODE 4️⃣7️⃣