Kenza eBookz

Uwa ko ukuba complete by m shakur - Chapter 47

Uwa ko ukuba complete by m shakur - Chapter 47

Uwa ko ukuba complete by m shakur Chapter 47: Uwa ko ukuba complete by m shakur Chapter 47. Zama yayi bakın gadon bama ya iya kallon jikin Asmeey banda…

4,152 words

Zama yayi bakın gadon bama ya iya kallon jikin Asmeey banda fuskanta Mamie sai kallonsa take tanajin nauyin tamai maganan da Mustapa yamata kan suje gida zai kwana da matarsa shima kuma Hamad yanajin nauyin musu maganan koba komi Aya na wajen akwai that kunya and regard he has for yayar matarsa wlh har 10 yakasa maganan itama haka Mamie hakan yatashi yace "saida safe Mamie" Aya tace "Mamie saida safe mezan dafa nakawo miki?" Mamie tace "shinkafa da wake mai da yaji wlh nagaji da abincikansu" Aya tai dariya Hamad yawuce yafita Ya Aya tabisa abaya. Mamie tayo alwala tazo ta shimfida dadduma tai salloli har wajajen 2 tanakan dadduma saita taso ta linke dadduman instead of taje kujeran dakin dake komawa gado sai tazo wajen gadon tana kallon Asmeey dataga idanunta abude suna kallon sama yawanci tana bacci tana rufe idanun abakin gadon Mamie ta zauna tana kallonta tace "yarinyana kin tashi?" Saitai shiru tunda take kwana da ita idan Asmeey tarufe idanu ariund 8 nadare sai 8 nasafe ko 7 take bude idanu, Mamie takalli drip na abincinta tace "ko yunwa kikeji?" Takai hannu ta taba cikinta, tace "ko sanyi kikeji Asmeey na?" Ta gyara mata bargo takai tsumma ta goge mata baki Mamie tai shiru tana kallonta tace "Allah yabaki lpy Asma'u!" Shiru Mamie tayi tana kallonta kafin ahankali Mamie takai hannunta tadaura kan gefen fuskanta tai shiru murya chan kasa Mamie tace "Asmeey nasan how painful life has been to you! I know you feel gwara this state dakike ciki yanzu daki dawo daidai kicigaba da rayuwa cus wat exactly are you living for? Mahaifiyarki ta tsaneki and the only beautiful little gift da Allah ya baki tarabaki dashi your little baby" Mamie tadanyi shiru tace "to wat are you living for?" Mamie tayi shiruuuuu tana kallonta, ahankali Mamie ta shafa kumatunta tace "Asmeey don't live for me! Don't live for Abba, ko Baba, ko su Aya, ko kowa ma, I want you to live for one person!" Mamie ta nuna yatsanta guda daya tace "this one person I think he deserves to live with you Asma'u! Sabida halaccin sa! Dakuma kaunar dayake miki" Mamie tai shiru hawaye na cika idanunta ahankali Mamie tace "Asmeey inasonki sosai wallahi tallahi" tadan fuzar da iska Mamie takasa daurewa kawai tafashe da kuka sosai tace "Asmeey inason Hamadi! Ina matukar son yaro na! And I'm gradually loosing him! Karkima d'ana haka Asma'u ki barsa zai haukace! Yarona na sonki Asmeey yana sonki da duka rayuwansa knowing u are alive shine ke basa karfin rayuwa ma, Asmeey come back for my son dan girman Allah kar wani abu yasamesa karya haukace, Hamadi tun yana yaro ba kaman sauran yara bane, alot of people call him mara lafiya, mai tabin hankali da sauransu sabida yanayinsa, wlh yarasaki zai haukace, I don't want to loose my son Asmeey" Mamie tafashe da kuka sosai tace "bayacin abinci baya bacci baida natsuwa ga damuwa Asmeey kin dandana menene kaunar d'a ina matukar kaunar Hamadi ya isa haka come back for him kuyi rayuwanku tare komi yayi farko zaiyi karshe no one will hurt you again, Asmeey Hamadi zai haukace sabida ke! For the sake of soyayyan dakuke ma juna come back for him kinji"Mamie tafashe da kuka sosai ta duka ta rungume Asmeey tarasa yanda zatayi ita karan kanta damuwa yamata yawa, machines din da aka jona Asmeey dasu taji sun shiga kara dawani irin sauri Mamie tadago da kanta takalli Asmeey rawa taga jikinta yafara da kafafunta da hannayenta harda bakinta dasauri Mamie tayi ihu. "Docto……" dakin taga Doctors kusan uku sun shigo da nurses, nurse daya tacema Mamie come with me Ma'am. Mamie arude tana kallon Asmeey dake rawa tace "wat happened to my daughter? Tell me" nurse din takama Mamie dake kuka tace "calm down, allow Doctors to see her first he will communicate with u come with me" takama Mamie data dauki waya tafito da ita wajen dakin Mamie ta zauna jikinta na rawa tarasa mezatayi sai kawai tai dialing number Hamadi Hamad na zaune kan dadduma wayan dake hannunsa yanzu tahau kara faduwa gabansa yayi sosai yakai hannu ya dauka ganin dayan number sa ce ta wajen su Mamie da gudu ya dauka yana mikewa tsaye kafin Mamie tai magana yace "Mamie! Meya faru?" Daurewa Mamie tayi tace "Asm……kazo Hamad?" Katse wayan kawai yayi gabansa na faduwa sosai yazarı kaya ya chanza yasaka coat yafito yayi wajen dakin Ya Aya yana knocking ta taso itama tana kan dadduma tabude kofan yama kasa magana kawai yajuya taklami kawai ta zura kan dadduma tabisa suka sauka kasa baida license na tuki but yaja motan nan cikin 10min sukakai hospital tsabagen gudu. EPISODE 1️⃣1️⃣7️⃣

Yana parking yafito da gudu ya shiga hospital din gabansa na faduwa sosai yahau gudu sosai zuwa ward nasu Mamie yagani gaban dakin tsaye tana goge hawaye da bayan hannu yazo wajenta da sauri yace "Mamie meya sami matana?" Hannunsa takama tace "she was shaking machine na kara doctors na ciki yanzu" gyadama Mamie kai yayi yarike hannun Mamie jikinsa na rawa Ya Aya na isowa wajen suna kallon dakin gaban Hamad na faduwa sosai. Sunkai kusan 10mins ahaka sannan Doctors suka bude kofan suka fito dadan murmushi kan fuskansa yamika ma Ya Hamad hannu yace "congratulations Mrs Hamad! This is good news! Your wife is awake….." rawa bakin Hamad yashigayi yace "aw……awa…..ke?" Dr yayi yar dariya yace "I mean she's conscious! Cus she has been awake all this while but not conscious but now your wife is fully conscious! But we still have to run some investigation in the morning! Congratulations once again she did it! Your wife is back!" Chak Hamad ya tsaya hawaye sun cika idanunsa saiyakai hannunsa daya yadaura kan fuskansa guys! He's exceptionally happy! Baimasan how he can express his happiness ba, doctors sukai dariya yadan buga kafadansa yace "common champion! You've waited for this moment for months! Now is the time! Go in and see your wife! She's waiting!" Doctors suka wuce, Mamie da Ya Aya duk suka tsaya babu wanda yayi gigin shiga dakin cus Hamad deserve to see her first much more than them! He deserve to see matarsa first, tabasa Mamie tayi hakan yasa yasauke hannunsa kasa idanunsa sunyi jajir na kuka, yadan fuzar da iska yakalli Mamie cikin wani irin murya yace "Mamie nayi kyau?" Dan dariya Mamie tayi daya bulbulo da hawaye daga idanunta hakama Ya Aya, takai bakin lullubinta kan fuskansa tace "kayi kyau idanun nan ne sukai ja sosai dai" sharemai tayi hawaye na kara zubowa yace "Mamie Asmeey ta farka da gaske?" Mamie tace "shiga and confirm for us" gyadamata kai yayi kai jama'a Hamad is very emotional, ahankali yajuya yataka ya tsaya jikin kofan yakara kai bayan hannunsa ya goge hawayen dasuka sake zubomai yadan fuzar da iska he's anxious, he's scared, kafin ahankali yabude kofan ya shiga dakin yamaida kofan yarufe yadago kansa yakalli gadon, cikin wasu kalan gajiyayyun idanu Asmeey ke kallonsa an samata oxygen a hanci cus data farka she couldn't breathe properly! Tsare Hamad tayi da idanunta na mara lafiya sosai tana kallonsa taga wani haske mafi kyawu tareda shi, tunda ta farka tabude idanu this is the first haske datake gani dat warm her eyes and bodyup! She missed this face! She missed this man! All she wants right now is yazo wajen nan so that she will have a chance to just hug him tight and never ever let him leave! Sosai Hamad ke kallon Asmeey dake kallonsa da gajiyayyun idanu! Matarsa da yaganta asankare looking like wacce akaima wankan powder acikin pool of dried maroon blood a tiles! Matarsa da he watched aka fito da ita from hospital akai confirming nata death aka sa a motar ambulance, matarsa da he watched as women suka mata wankan gawa, aka lullubeta da likafani, auduga in her ears, nose her eyes completely shut! Matarsa that literally became an imbecile ba uhn or uhum'uhm sai yawu that is drooling nonstop da karkataccen baki and fixated eyes, bata moving or making any gestures, matarsa ce Allah yadawo masa da ita alife yanzu laying on this bed looking directly at him, fuzar da iska yayi, like idan duka dukiyar daya mallaka yadauka ya ciyar da marayu ya gina masallatai still baijin ya nunama Allah kalan godiyan and thankfulness dayake feeling right now towards Allahu Subhanahu Wata'ala ba! Is not enough! He's super duper and over grateful to Allah! Hawaye yaji yazo mai yakai bayan hannu yashare yafara tafiya ahankali yana goge idanunsa da bayan hannu haryakai gaban gadon yana wani irin kallon Asmeey kafin awani irin hankali ya zube akasa yayi kneeling kansa na leveling da gadon dakuma kan Asmeey hannunshi na rawa sosai yakai yakamo duka hannayen Asmeey guda biyu yana kallonta yayi wani huci yakai hannayen bakinsa yayi kissing saikuma awani irin hankali yadaura hannayen nata saman fuskansa yayi placing yana kama hannun yana kallonta yafashe dawani calm yet serene emotional cry that says a whole lot to Asmeey har wani huci yake kaman maciji ya kankame hannunta sosai Hamad is crying while Asmeey na kallonsa wasu hawaye masu zafi nabin gefen idanunta suka saukowa dropping a pillow, she wants to just move her body even if it's just a little bit ta matso ta rungume mijinta ta lallashesa amman takasa but dudda haka da all the energy datake dashi yawani yunkuro dasauri Hamad yataso kafinma yayi wani abu with the last ounce of energy nata tasa hannayenta takwanto da kansa kirjinta dawani Irin gudu Hamad yayi placing kansa a kirjinta Asmeey takai hannayen nata da bata iya motsi dasu da kyau bayan wuyansa ta kankamesa feeling yanda heart nasa ke beating same with hers, Hamad yayi kuka ajikin Asmeey kukan that says alot i thought I've lost you! I thought bazaki taba dawowa ba! I've missed you Asmeey! I love you so very much Asmeey! That's just the cry dayake mata itama she's just crying she wished tanada karfin lallashinsa but jikinta na mata kaman batasan yanda ake moto movement bama, yakai 10min akirjinta ahaka sannan yadago kansa yakawo fuskansa dab da nata, idanunsa har sun kankance sabida kuka, cikin wata yar kankanuwan murya dake nuna tsantsagwaran so yace "are you okay?" Tsayawa Asmeey tayi kallonsa tunda ta taso Hamad has always been the only person asking her this particular question na are you okay, tana gidansu! Sanda Fawaz yaso raping nata! On so many occasions! And today also is the first kalman daya fito daga bakinsa! Lumshemai idanu tayi tabudesu alamun eh, dayake oxygen pipe aka samata na nose trill kadai ba irin mai rufe baki da hanci ba tsayawa yayi yana kallonta yanason Asmeey! Soyayyanta har wani fizgansa yake, murya chan kasa yanadan kallon lips nata yace "can I kiss you?" Shiru Asmeey tayi tana kallonsa ayanda yake kallonta yadawo kaman maraya kaman yama fita jinya ya rame yasa talumshe idanunta tabudesu alamun eh, awani irin hankali Hamad yasauke bakinsa kan na Asmeey, he doesn't care it's been months batai brush ba, ko she has been drooling din yawu daga bakin, koko tanada wani infection abakin, koma menene he doesn't care! Yakamasa cutan, Awani irin hankali yashiga kissing nata yana wasu kalan ijiyan zuciya mai ban tausayi yataso da kyau yahayo gadon yawani irin kankameta ajikinsa he's kissing her idanunshi a lumshe while Asmeey idanunta abude tana kallonsa hawaye na gangarowa daga idanunta, ya bala'in bata tausayi kaman taita yimai kuka, kaman zai hadiye mata baki he's kissing her kaman zai cinyeta, kiss na mugun shaukin so da kewa da bege, sau biyu ana knocking baijiba itakuma bata iya moving jikinta takasa gayamai ana knocking, bude kofan Mamie tayi tareda Ya Aya dawani irin sauri Hamadi yasaki bakin Asmeeey yatashi da sauri daga saman gadon jikin Asmeey, gabaki daya ya mance su Mamie na waje Mamie ma bakaramin kunya yakamta ba ko kadan bata kawo zatazo ta tarar da Hamadi harya haye yarinya mara lafiya yana sumbata kaman zayi shanye mata baki haka ba wlh kaman takoma tafice da gudu amman tadaure tai kaman bata gani ba itama Ya Aya tayi kaman bata gansu ba ganin ashe Ya Hamadi maye ne yooo daga farkawan yarinya harka hau gado kana shan baki! Asmeey tamaida idanunta ta lumshe cikeda kunya Hamad yajuya yana kallon bango yana sosa kai kaman ya shige kasa wlh, Mamie ta waske tace "bacci takeyi ne Hamadi?" Dan juyowa Hamad yayi yakalli Asmeey saiya wuce yaje ya zauna kan Couch yakasa magana jikinsa sai rawa yake. EPISODE 1️⃣1️⃣8️⃣

Wucewa wajen gadon sukayi Mamie tashafa fuskan Asmeey hakan yasa Asmeey tabude fuskanta kadan takalli Mamie kunya yakamata, hawaye Mamie tashiga sharewa tace "yarinyana kin tashi? Kinajin yunwa me zakici?" Tsayawa Asmeey tayi tana kallon Mamie cikeda so hawaye na cika idanunta, bakinta namata wahalan buduwa dan motsi lips nata sukayi hakan yasa Mamie takai kanta wajen bakinta tace "fada naji" dasauri Hamad ya kallesu murya chan kasa da baya fita kwata kwata dan bata iya moving muscles nata da kyau tace "kosai, kunu" dasauri Mamie tadago takalli fuskanta tana murmushi tace "aiko zan miki lafiyayyen kosai da kunu yau ga Aya" Mamie ta matsa gefe Ya Aya ta taho awani irin hankali akuma taushashe take kallon Asmeey takasa magana but her gaze says alot lumshe mata idanu Asmeey tayi tabude hakan yasa ahankali Ya Aya taduko she just hugged her little sister very tight tama kasa magana hawaye na fita daga idanunta ahankali she promise cewa this second chance da Allah yabasu da kanwarsu they will not take it for granted, she will show Asmeey wat a big sis means, bawai Asmeey bata sonsu bane no tana sonsu but da yanzu Asmeey zata shiga trouble data kira su gwara takira Munir cus Munir has always been the one standing for her, she will change it, she will be Asmeey biggest support system she will be her mother, she will make sure Asmeey ta aminta dasu and show her cewa she can come to them for anything sunkai kusan 10minutes ahaka sannan tadago takai hannunta tashare fuskan Asmeey, Mamie takara kallon Asmeey cike da farin ciki takalli Hamad dake kallon Asmeey tace "kaga kira gida fara kiran Baba Hamadi! Ni bari nakira Abban ku oh Alhamdulillah Alhamdulilah, Aya kira Aysha kai kai jama'a yau ina cikin farin ciki" wayansa Hamad yaciro yana kallon Asmeey data sake lumshe idanu she's not strong at all, he wants to be there but Mamie da Aya duk sun tare wajen, wayan Baba yakira kafin yamayi ringing na farko Baba yadaga cikeda natsuwa yace "Hamadi ya wajenku? Yakuma mai jiki"? Dan murmushi Hamad yayi ahankali yace "Baba ta tashi just now" "Allahu Akbar! Allahu Akbar! Allahu Akbar! Alhamdulillah! Alhamdulillah! Alhamdulillah! Hamdan Kaseeran Dayyiban Mubarakan Fee!" Baba yafadi cikeda farin ciki yace "y'ata Asma'u na ta farka Hamadi?" Gyadamai kai yayi yace "eh Baba" Baba yace "zata iya magana?" Girgiza kai yayi yace "ah'ah bazata iyaba Baba" Baba yace "Allahu Akbar na fahimta tayi watanni kwance ba magana ba harsu tafiya da sauransu wahala zasu dinga mata, Alhamdulillah dukanmu nan kap dinmun munyi visa dama jira muke ta farka muzo, in sha Allah yanzu zan kira Faisal asama mana next available flight zanzo na dubaku, yaushe za'a sallameku?" Ahankali yace "bansani ba but sai tayi physiotherapy adan gasamata kasusuwanta dasukai sanyi tafara moving jikinta just like before" Baba yace "ba shakka, to Allah muku albarka Allah bata lafiya ka gaidamin ita da Mamie da Aya" Hamadi yace "tom Baba" Ya Mustapa yakira ya sanar dashi saikuma yakira number Munir na Egypt danhar Baba yagama komi yaron na Egypt kullum saiya kira Hamad ya tambaya jikin sister sa ringing daya Munir yadauka yace "Ya Hamadi ina yini" batare daya amsa ba yace "Asmeey ta tashi" ihu Munir yayi da saida Hamad yacire wayan daga kunnensa saikuma yahau kuka cikin tsananin so yace "Yaya zakamin booking jirgi nazo even if it's just a day naga Asmeey na koma?" Shiru Hamad yayi chan yace "wat about ur studies"? Dasauri yace "Yaya 2days trip won't affect my studies I need to see my sister" Asmeey Hamad ya kalla da kaman bacci ya kwasheta he knows the way she loves Munir seeing him will brighten her mood more, seeing all her family too can help her overcome any atom of sadness left hakan yasa yace "okay I will book flight for you na gobe get ready" ihu Munir yayi yace "Ya Hamadi wlh I love you! You are the best cousin and best brother in law, thank you Ya Hamadiii" Hamad ya katse wayan, Mamie ta kallesa tace "muje namata kosai da koko" kallon Asmeey yayi saiya tashi suka wuce kaman karyaje gidan.

Around 6 Asmeey ta farka Ya Aya takira Doctors sukazo suka dubata ta tambayesu ko zata iya mata wanka aka bata dama suka tayata sa Asmeey awani wheelchair na wanka aka kaita bayi.

Yarinyar can't really move her body cire kunya Ya Aya tayi gashinta tafara wanke mata da shampoo da conditioner sannan tamata brush kafin tamata wanka soso da sabulu da ruwa mai zafi sosai har tiriri fatanta yake sannan ta gasa mata jiki tafito da ita an ijiye musu new uniform na wando dogo da riga, Aya ta shafe mata jiki da man habbatu Sauda da duk Hamad ne yakawo tasa mata kayan sannan ta gyara mata gashin tai combing tashafa mai sannan tamata all back guda biyu yamata bala'in kyau tasamata safa sannan tadan fesa mata body spray sama sama Asmeey tai wani irin kyau sai kallon dakin take Ya Hamadi take nema kaman Aya ta lura da hakan tace "suna hanyan dawowa, zokihau gado" kamata tayi tahau da ita gadon taja bargo tarufa mata takoma taja wheelchair ta matsa daidai ana bude kofa dawani irin sauri Asmeey tabude idanunta Mamie ce sai Ya Hamad dake rike dawani basket mai bala'in kyau ya kallota ijiyan zuciya Asmeey tasauke ahankali tadan jaye idanunta daga kallonsa…. EPISODE 1️⃣1️⃣9️⃣

Mamie tace "yarinyana tayi kyau sosai wanka kukayi Aya?" Ya Aya tace "eh Mamie sunce zata iya wanka shine na wanke mata kan na mata kitso biyu" Mamie tace "yayi kyau sosai, Hamad bani basket lemme feed her" kawo basket din Hamad yayi yana kallonta, itama dan kallonshi tayi tamai wani raurau da idanu da sauri ya matso gefen gadon zai zauna Mamie tarigasa zama batare data lurada shi ba rike da bowl of Pap data deboma Asmeey dan dakatawa Hamad yayi saikuma yajuya ahankali yawuce couch ya zauna Asmeey tadan saci kallonsa ta sunnar dakai.

Mamie feed her, tasha kunu sosai but kosan was somehow hard for her to chew da kyar ta iyacin guda daya, but tasha kamu sosai, suna ahaka saiga nurses biyu sun shigo dawani wheelchair tace "Asma'u it's time for physiotherapy" Mamie ta tashi daga gadon, Hamad yadan kalli Asmeey ba hula akanta Aya ya kalla suka hada ido dan dauke kai yayi yace "asamata hula" murmushi Ya Aya tayi tabude jakansu taciro hula tasama Asmeey sannan suka sata akujera suka fice da ita Hamad yabisu ba'a barsa yashiga dakin physio dinba but daga nan waje yana kallonsu cus transparent glass ne, kafin ma adagata kafafunta aka makala jikin wani machine da hannuwanta ma machine din yafara daga kafafunta sama da hannuwanta sama ahankali Asmeey nadan yatsine fuska abin kaman yana mata wahala kuşan 30min ahaka sannan aka kamata aka tsayar with so many people around her akace data gwada daga kafan suka matsa kokarin yi tayi but tai baya zata fadi dagudu Hamad yazo wajen but harsun riketa, jikinta na mata kaman batasan yanda ake komiba, kusan 3hrs tayi adakin sannan suka fito da ita aka komar daki Hamad yabisu akaso aka mata 2 injection aka kuma bata magani abaki bata wani bata lokaci ba sai bacci an gayamusu karsu damu zatai long sleep.

She slept all through d day har zuwa next day sanda ta tashi Hamad yatafi airport dan kusan su Baba da Munir sun sauka at dsame time. Mamie kuma ya sauketa agida dan zatai girki gida zai wuce dasu suyi freshen up kafin hospital.

Yana tsaye a airport yana magana da Ya Mustapa awaya ya hangosu, at first only Abba, Baba, and Ya Mustapa yasan zasuzo daga Nigeria saiyaga Hameed, Faisal da Ya Abdullahi, ga Munir tareda su cus sun hadu, dukansu kallon Hamad suke daya rame sosai ga security sa tareda shi da driver motarsa ma ai bazata iya daukansu ba, yakalli driver sa yamai magana yasamo cab ko yakira uber yajuyo duk kunya yakeji, Hameed na zuwa yace "Ango Ango Ango Amarya ta farfado" yawani rungume Hamad daya tureshi yana dan turo baki kunya yacika sa cus hakanan wani extra special kunyan Baba yake, da gangan Hameed yace "Baba surukinka na kunyan ka fa" Baba yayi dan dariya yace "zan ci gidanku Hameed bazaka kyalemin yaro ba taho nan Hamadi" adan kunyace Hamad ya sunnar dakai yace "ina yini Baba, ina yini Abba" kansa Abba yashafa yace "kanacin abinci kuwa?" Gyadamai kai yayi yajuyo yadan kalli Ya Mustapa akunyace sai yadan duka yasa hannu ya karbi jakan hannunsa murya chan kasa yace "welcome Yaya" murmushi kawai Ya Mustapa yayi anatse batare dawani yajisu ba yace "kuka yakare ko? Wife is awake" murmushi yayi mai bala'in kyau cikeda kunya yawuce wajen Faisal da Ya Abdullahi wani kallon iskanci da Faisal yamai yasa yajuya dasauri zai wuce Faisal yarikesa cikin whispering yace "duk ka rame sabida rashin coitus" zokaga dariya mutane dasuke airport ana kallonsu, Ya Abdullahi yace "yana resuming yanzu jikin zai dawo" zokaga dariya barinma Hameed, Abba yace "a airport zamu kwana wai" wucewa Hamad yayi abinsa yabude motarsa Abba da Baba suka shiga, sai wata bus mai kyau ta uber da security sa yasamo su suka shiga harda Ya Mustapa Hamad ma yashigo bayan an gama sa kayan a booth zama kusada Ya Mustapa yayi kansa akasa driver yaja motan sai wasa yake da hannunsa su Ya Abdullahi na surutu abinsu. Ahankali yace "ina Gwaggo"? Ya Mustapa yace "tana sabon gidan da Baba ya saya anan kano tareda Ammi da yara" gyadamai kai yayi yace "Kawu fa ya maida Mama?" Girgizamai kai yayi yace "not yet" shiru Hamad yayi Ya Mustapa yace "wat are the doctors saying about Asmeey?" Ahankali yace "everything is fine kawai physiotherapy ne sabida tafiya and body movement in general" gyadamai kai Ya Mustapa yayi mota na tafiya chan yace "zaka iya daurewa har agama mata physio?" Dawani irin sauri Hamad yakalli Ya Mustapa hada ido sukayi shima kallonsa yake dasauri yamaida kansa kasa Ya Mustapa ya tsaresa kur da idanu, gabaki daya Hamad ya rame ya lalace kana ganinsa kasan harda sha'awa ke neman hallaka sa yakasa magana sai wasa yake da yatsu, anatse Ya Mustapa yace "after tayi physio na today ask them to discharge her and hire wayanda zasu dinga zuwa gida everyday suna mata, ana home service sosai, sannan every week saika dinga kaita hospital din for checkup, take your wife home tayi full recovery adakinta" dan murmushi kadan Hamad yayi wlh yanason Ya Mustapa, Ya Mustapa yakallesa sosai ganin murmushi yake yasa yadauke kai yace "and be gentle na sanka" kifa kansa Hamad yayi a cinyansa dasauri Faisal dake kallonsu tuntuni yace "Ya Doctor wai me kake gayama yaron nan ne yaketa blushing haka yana wani kifa kai a legs" dasauri Hamad yadago kansa, shikuma Ya Mustapa yama Faisal mugun kallo dayasa yace "okay tai tsami zamuji ai" har gidansa sukaje akai parking Ya Mustapa yace "a hotel zamu zauna munyi reservation namu" ahankali Hamad yace "Mamie tamuku girki da daddare sai kuje hotel din" sama suka wuce sai kallon gidan da Hamad yake suke skyscraper apartment suka shiga Hameed yayi wajen Mamie da gudu yace "Mamie na" hakama sauran yaran su Faisal, Faisal yace "Mamie wlh nayi kewanki nazo gidan nan har kunci nakeji banga Mamana ba, tunda na sanki baki taba tafiya kin barmu ba kin dade haka ba" dariya sosai Mamie tayi tace "bagashi ka biyoni ba ga nama" yabude baki tasamai ciki Hameed ma haka Ya Abdullahi ma haka duk girma Ya Mustapa shima yabude baki tasamai takalli Hamad dake falon tace "zonan" tahowa yayi tasamai shima Abba yace "wai yaran nan kunsan ni mijin mahaifiyar ku na nan"

Baba yace "wlh Yaya kagansu fa manyan yara dasu harda likiti duk sun zagaye mahaifiyarsu a kitchen kaman sunyi shekara basu ganta ba" murmushi Mamie tayi tace "ina zuwa barkanku da zuwa" duka yaran tayata daukan kuloli sukayi da plates duk aka kawo falo Mamie ta zauna kusada Abba aka gaisa akaci abinci akai nak sannan akai salla aka fara shirin zuwa asibiti, akwai bathroom a falo akaia ana dakin su Mamie duk wanda Hamad yacema yashiga na dakinsa saiyaki sundai duba dakin an shiga ko'ina an kalla cus yayi kyau but basuyi using bathroom na dakinsa suka shirya tsaf da Hameed da Faisal suka gyara ko'ina harda wanke wanke basu bar any aiki ba sannan suka tafi hospital din. EPISODE 1️⃣2️⃣0️⃣

Readers Also Read