Kenza eBookz

Uwa ko ukuba complete by m shakur - Chapter 52

Uwa ko ukuba complete by m shakur - Chapter 52

Uwa ko ukuba complete by m shakur Chapter 52: Uwa ko ukuba complete by m shakur Chapter 52. Washe gari asibiti taje da ragowan kudin aka duba kafanta Dr…

3,958 words

Washe gari asibiti taje da ragowan kudin aka duba kafanta Dr yace aiki za'ayi a yanke naman wajen gabaki daya asamata another nama kafin poison din yashiga kashinta, aiki da nama da za'a saya 500k. Gida Mom tadawo taje takira dillaliya ta saida set na kujerun falo da carpet da dinning da dankararen tv su komi kuma na falon na Baba ne, kayan da normal normal ko tv falo yafi 1m da kyar Mom tahada 1m abanza dillaliyan tasaya washe gari takoma asibiti tabiya akai admitting nata gobe za'ayi surgery tayi undergoing other investigations su xray da sauransu akace takira azauna da ita but batada wanda zata kira she just realized Fawaz yasa tayi feeling nobody is important in her life kawai she just followed him like a fool, washe gari aka shiga aikin aka kwashe naman anan akaga dafi ya shiga kashi fa dole ayanke but bazasu iyaba dole Mom saita farka tabada consent haka aka lullube kafan ba'asa nama ba aka fito da ita, bayan like 5hours allura yasaketa Dr yamata bayani Mom tai shiru tana kallon Doctor is this even real? Ita za'a yankema kafa, bata tabajin tsoro yakamata irin na rannan ba da gaske alhaki nabin mutum dama, no gaskiya zataje wani hospital bazata yarda ayanke mata kafaba ai rayuwanta yakare kennan tace "Dr asamin fatan dana biya nidai bawata yanke kafa zanje Dubai adubani" Dr yace "gwara ayanke miki yanzu aka saka miki fata kafan ya warke rubewa kafarki zata fara taciki" Mom tace "I reject rubewa pls finish wat I paid for"? Dr yayi yayi Mom taki haka yabarta aka komar da ita aiki aka mata just 1hour yadaukesu aka fito da Mom, kwananta uku a hospital aka sallameta ta tafi gida tasake kirawo dillaliya tv sama da kujeru tasaida da curtains da kujerun flat nasu Abba da Kawu duka kaya dayawa tahada miliyan uku taje tanemi second hand toyota tasaya da kyar hankalinta ya kwanta tazo gida. Kwananta uku agida kafanta yafara wani irin ciwo dako tafiya da kanta yasoma gagaranta wani hospital taje private nan fa suma suka faracin kudi ana test daban daban before aceme ana neman kusan 1.5 Mom tasake kiran dillaliya funityres na dakin Baba tafitae dana dakin şu Asmeey dana dakin Ammi kaman nata duka ta saida tahada 2M, takoma hospital sai hope suke bata bazasu yanke kafa ba aka bata magunguna masu kyau da allurai tadenajin zafi jikinta yayi kyau tadawo gida again, bayan 4 days saitaga ruwa nafitowa daga aikin takara komawa private hospital din sukace zasu mata aiki su chanza fatar 5m aiki daganan tagama wahala Mom takoma gidan duka wani funityres daya rage na sauran flats din dana dakintama kawai katifa ta ijiyema kanta akasa ta saida tahada 5m takoma akai admitting nata akai aiki bayan 3days tadawo gida tana recovering ba bacci just 2days wani ruwan yauki me wari yafara fitowa daga aikin takoma asibitin sukace ita ke wanka tana bari ruwa yashiga sai an sake chanza skin din 5m again zata kara biya this time komi daya rage na gidan ta sauda harda kayayyakin kitchen da katifan data barma kanta da motan data saya kap tahada 5m da kyar takoma aka sake aiki sunfaga kashin yarube but sunki fada mata sai patch patch suke mata kawai Mom tasake dawowa gida praying wannan ne karshe cus bata da anything left again, rannan takira number Aya wayan ya shiga Aya bata dagaba, ana biyu bata dagaba ana uku Aya tadaga kafin Mom tai magana Aya tace "duk wani relationship dake tsakanin mu da ke mun yanke Mom! Ke kika fara nuna you hate us! You killed our sister and her baby all sabida dadironki Fawaz, u make your choice muma we make ours shine mun barki dashi! Har abada Mom nagama jin tsoronki ko shakkan ki cus kinriga kinyi loosing every respect we have for you! Wlh I wish and wish and wish da bakene mahaifiyata ba! I wish inama Mamie ko Ammi ce mahaifiyata, you don't deserve to be called my mother! The only reason nake daukan wayanki is because someone has to say it to you, Ayasha da Munir sun fini zafi ko fuskanki basuso su gani dan haka na barki lafiya!" Ya Aya takatse wayan Mom tai wani mutuwan zaune rayuwa kenan! Wato ko duk wanda bai yarda Allah shine above everything and everyone ba yaci baya, is this not Aya da idan tai tsawa saitahau kuka tarude? Yau Aya ce ke gasamata magana haka? Sauran yaran sunmayi blocking nata? Duk tsoron nan da shakka da fargabanta babu shi ko daya aransu ita Mom dake tunkaho tana alfahari da yanda yaranta ke tsoro ta yau yaranta sun nunamata she's a nobody! Zuciyanta yayi wani iri Asmeey na fado mata arai the only person datasan da ace tana raye zata tausayamata is Asmeey and takashe ta, Asmeey ce kadai yarta dake mata wani kalan mugun so! Ita tasan da ace Asmeey nada rai taganta in this condition she will hugged her cry and tell her Mom I love you! You are the most beautiful Mom….. Mom tawani rushe da kuka wani nadaman abubuwan datama Asmeey na zuwan mata cus Asmeey tafi duka sauran yaranta sonta! Asmey tafisu tausayi! Tafisu soft heart! Tafisu shakuwa da mahaifiyarta! Why did she do all of those things to Asmeey because of a man dagashi nan yau yajuya mata baya? Ita the almighty boss lady Mom ce haka yau? Where is the barristerness? Where's the connection and her elite contacts yan presidency? She learnt all this elite people datama case sukaci are only using her, idan bakada amfani u are no one to them babu Wanda ya tai maketa and most of them knows she's sick ta aikama abokan aikinta hotunan kafanta but nobody gave her one kobo not all called sef, she knows Allah is punishing her, tashi daya yasa Fawaz yarabu da ita, yaranta haka, mijinta haka, is time ta nemi gafara, dudda batasan inda Baba yakoma ba ai tasan shagunan sa gobe zataje Allah sa tagansa, zataje gidan Yayanta ta nemi gafaransa shima, zata hada kudi taje Bauchi ta nemi gafaransu, ta nemi yanda zata sami Hamad ta nemi gafaransa takashemai dan ciki da mata.

EPISODE 1️⃣3️⃣9️⃣

Washe gari haka ta shirya hijab tasaka tashiga keke sai rufe hanci yake taje plazan Baba but security suka hanata shiga mutanen da da idan tazo Hajiya Hajiya ake mata ana mata fadanci ana gaidata akace Alhaji yace kar akara bari tashiga da kyar ma ta iya samin Information kan yabar Bauchi yakoma kano one in a while yake zuwa duba shago jikin Mom yayi sanyi daganan ta tafi gidan Yayanta Alhaji Mahmoud, kasa shiga gidan tayi bataso yamata rashin mutunci agaban yaransa haka ta zauna awaje kudaje sai binta suke, around 4 yadawo a babban motansa tundaga nesa yake kallon Mom akofar gida kome sister shi tazama bazai taba iya kasa ganeta ba Salima ta lalace tayi baki, tayi duhu ga kuda sai binta suke, dan farin glasses dinta ya tsufa duk ya koke kaman wata makauniya, budemai gate akayi ya shiga da sauri Mom tashiga tashi tsaye tashiga gidan kashe mota yayi yafito saida yaji wari yakalleta saikuma ya watsar zai wuce ciki da sauri tasha gabansa taduka tahade hannaye looking pathetic tace "Yaya kamin rai! Yarana sun gujeni, mijina haka, duniya ta juyamin baya, kafana tun cizon karya ba lafiya, kamin rai Yaya!" Kafin takara magana yanunata da hannu cikin kakkausan murya yace "nabaki second biyar kitashi kibar gidana! Salima baki isa ki nunamin ni ban isa namiki fada kona gayamiki gaskiya ba sai yanzu da komi ya kwabe miki, Allah ya gwada miki iyakarki zaki nemeni kizo wajen, Wallahi wallahi bazan taimaka miki ba!" Alhaji Mahmoud yafadi azafafe yana kallon Mom yace "babu lallashin duniya daban miki ba ina gayamiki gaskiya amman kin gwammace ki rasa kowa sabida wani dan iskan yaro dakike bi? Harda kashe diyar ki da abin cikinta kaico! Ke bakiga komiba stand up and leave this house, stand up! Yau ina yaran dakike tunkaho kina fafa kina daga kafada cewa sai yanda kikai dasu? When I was telling you a day like this can come da yaran nan dakike gani kin gama dasu zasu juyamiki baya bagashi rannan tazo sooner than I even expected ba? Wacece ke! Ke din banza da wofi! Ke ba komi ba sai girman kai kina feeling kinfi mijinki da kowa nasa ilimi yau ina ilimin? Ina sanayyan manyan mutanen eh hajiyar kotu? Ina kudaden yanzu? Tashi kibarmin gida nace!" Yayi kan Mom kaman zaki takoma baya da gudu, Alhaji Mahmoud yakalli gateman yace "take this smelling woman out of my sight! I do not care kome zai sameki wallahi wallahi I don't! Bakiga komiba duk wanda baiji bariba zaiji hoho! Go and pay for ur sins alone wallahi ko ajikina! Nayi nawa nayi iyakan kokari na kika maidani jahili baki tubababa Salima, dan da komi zai dawo miki ba chanza wa zakiyi ba, women like u can never change, get out of my sight! Ni ba dam Uwanki bane! Kuma baki bani tausayiba! Abinda kikayi ke binki, ga cin gado ga kisan kai" Mom ta tsorata bata taba sanin her very own blood brother can abandon her in this condition ba well daman ance yara maza basuda tausayi, agaban Yayanta mai gadi yajata yafitar yana jefar bawai beji ciwo aransa bane yaji wlh but yasan Allah ke kamata kuma daman yasa dole a day like this will come, zunubin kisan kai fa? Ga alhakin yarinya hmmm, Mom tayi kuka ahaka daga gidan kawai tawuce tasha around 4something tashiga motan kano sai wari take but tasha ne hakanan aka dauketa wajajen 6 mota tacika sai Kano……

TOM MOM ZATAJE KANO!

ASMEEY NA KANO!

MEZAI FARU?

KUNA GANIN ASMEEY ZATA YAFE MATA TAGA COMDITION NA MOM? CUS ASMEEY NA SON MOM SOSAI?

WAYYOO MOM TABANİ TAUSAYI😭 EPISODE 1️⃣4️⃣0️⃣

Today marks the 3rd week tun dawowansu Kano. Rannan dasuka sauka washe gari aka fara gyara Asmeey dan wata mai gyaran jiki daga Chad Mamie tabiya tun tana Washington ta iso, ciki da waje ake gyara Asmeey while tana shan su rubutu daga sauransu, kullum rannan duniya suna waya da Ya Hamadi sau biyu ko sau uku, she's sorrounded cikin yan uwanta su Ramla duk sun gudo wajen Mamie, like gidan Mamie yanzu akwai yara dan gidan Baba is just bayan layinsu, Ya Aysha tazo week dasuka dawo Nigeria, this week ma tazo tareda Ya Aya zasuyi just Saturday Sunday su koma, Asmeey is very happy matsalanta yanzu kadai a rayuwa shine wani jarababben kewan sex datakeyi, ko zama tayi ita kadai sai kawai tafara tuna moments nata da Ya Hamadi, sai kawai taji tajike, she wants to do it again, she wants to kiss him, hug him and do the sex dashi sosai, abinda ba wasa abin har tsoro yake bata ko magungunan datakesha ne oho but feelings takeji sosai.

Yau sunday dukansu suna kitchen din Mamie Ya Aya, Ya Aysha, Ya Ramla, da Asmeey suna aikin, fatan Asmeey sai sheki take tana glowing tayi kiba jikinta yasoma dawowa tana jefa kosai a wuta suna hira while su Mamie da Abba na falo tareda Gwaggo suna hira tareda Ya Mustapa, Ya Abdullahi da Ya Faisal, Hameed ne kawai baizoba, fitowa da kunu Ya Aya tayi Gwaggo tace "ai ina shirin zuwa kitchen din kunu kaman kuna sarrafasa daga farko sabida hira" Abba yace "kyalemin yarana suyi hira abinsu, zo zubamin nawa Aya" murmushi tayi tama Gwaggo gwalo tazo tadauki cup na Abba tasamai saiga Asmeey tafito da kosai a flask mai kyau Mamie tabita da kallo yanda Asmeey ke kara kyau ka kalleta saika kara tafi koda yaushe kyau and she's very happy ijiye kulan tayi tadauki kosai daya a hannunta tazo kusada Mamie cikeda so takai bakin Mamie tace "Mamie dandana kiji yayi dadi ninayi" Ya Aya tace "kikayi mene?" Turo baki Asmeey tayi takalli Ya Aya Gwaggo ta kwashe da dariya tace "gaskiya tafadi kike tura mata baki" Mamie tabude baki ta gutsura tace "ni nasan y'ata ce tai kosan nan share Aya da Gwaggo kinji uhmmm yayi dadi" dariya Asmeey tayi takai ragowan bakinta ta tashi tawuce kitchen Mamie na binta da kallo hips dinta sun fito sosai magungunan nasa kiba ne koko ciki gareta? But last cikinta raman da ita yayi this one kiba zai sata? This is just sati na uku, ciki zai iya nunawa a 3weeks but she's really suspecting pregnancy aran Mamie tace "Hamadi ba dama ka kama yarinya saika mata ciki ikon Allah! Yarona is very fertile" tai murmushin manya. ***

Around 1 nadare suka iso kano dan motarsu ta lalace a hanya, sama da kasa Mom ta kalla this middle of night gwara ta kwana atasha wani bench tasamu ta zauna tabuga tagumi tana tunanin rayuwanta duk wanda yazo zai zauna awajen saiya tashi sabida yanda take wari, tayi shiru kawai tana kallon kafan da tagaji bashine agabanta ba haka gari yawaye still tana zaune, fargaban zuwa gidan nan take, tana zaune ahaka har wajajen 8 tamike tanemi ruwa tasami gefe tai salla sannan tashiga tafiya gabaki daya tai butu butu keke ta tare yace zai kaita drop dubu uku ta kalli kudin hannunta sukenan gareta tabasa tashiga har unguwan gabanta sai faduwa yake gabaki daya sun chanza gidan anyi renovating anguwan ma sunsa titi which she's sure sune sukasa gate din tayi ga security guda biyu awajen takarasa zata wucesu suka tareta. "Yes who are you?" Yadan koma baya sabida warin datake, ahankali Mom tace "masu gidan nake nema" kai tsaya yace "kidawo Friday rannan ake bada taimako not today" shiru M Mom tayi tana kallonsa araunane tace "dan girman Allah kagaya musu Alhaji Abubakar nake nema ko Gwaggo! Sun sanni" kallonta yayi from head to toe saiya daga waya yana komawa baya Ya Mustapa na zaune a falo wayansa yayi ringing yakalla ganin security ne yasa yadaga kai tsaye yace "a woman is here she wants to see Gwaggo ko Alhaji! She looks like a begger wat do I do?" Dan shiruuu Ya Mustapa yayi normally normally bazai fitoba but ambato sunan Gwaggo yasa saiyace "I am coming" mikewa yayi Mamie tace "ina zaka baka cinye abinci ba"? Anatse yace "yanzu zan dawo Mamie wata tazo neman taimako lemme give her something" yayi maganan yana ficewa yataba aljihunsa yanada yan 1k yaciro duka yarike a hannu yataho wajen gate din yasa hannu yabude kofa ahankali yakalli security batare dayama lurada Mom dake daga gefe sanye da dogon hijab ba yace "where is sh…." "Mustapaaa!"

EPISODE 1️⃣4️⃣1️⃣

Mom takira sunansa asanyaye dayasa Ya Mustapa yajuyo yakalli Mom to be honest saida yayi kusan 15secs yana kallon Mom kadın yaganeta cus this is not the Salima he use to know, tundaga kasa zuwa sama yabita da kallo yana maida kudaden hannunsa aljihu sannan yajuya zai koma ciki Mom tace "Mustapa kamin rai! Yafiya nazo rokonka, dan girman Allah kuyafemin dan Allah!" Juyowa yayi yama Mom wani kallo sannan kawai yakalli securities yace "don't let her in" yawuce yakoma ciki ransa abace bude kofa yayi duk aka bisa da kallo cus yanayin fuskansa ya chanza Baba yace "lafiya Mustapa" murmushi ya kakalo yace "fine Baba" saiya kalli Asmeey dake dinning tanashan kunu tana hira da Ramla smiling looking happy yadan kwana biyu bai ganta ba cus yaje China finalizing production na company su sai jiya yadawo yaganta kallo daya yamata yagane the girl is pregnant again, koda wasa he will not want Asmeey taga matan nan cus she will remember everything which can cause harm to her little pregnancy dako a month baikaiba cus Mom tariga tabata traumatic experience, duk suna zaune awajen sukaji anyi mummunan buga gate nasu at d same time wayan Mustapa na ringing Abba yamike tareda Baba dasu Ya Abdullahi sukace wai lafiya wake buga gate haka Ya Faisal yabude kofa yafita da sauri suna jiyo ihu sosai wlh wlh saina shiga Ya Abdullahi yabiyota Baba haka Abba haka sai Ya Mustapa yabiyosu yama Mamie alamu da idanu datakai Asmeey sama, kawai jikin Mamie yabata Salima.

Takalli Asmeey da Ramla tace "tashi kuje dakina ku gyaramin" tashi sukayi Asmeey tace "Mamie wake buga gate haka" Mamie tace "ba mamaki yan sadaka ne ga yayyinki sunje sorting out, kuje sama kumin gyara" wucewa sama sukayi Aya takalli Mamie dasauri Ayasha ma haka Mamie bata cemusu komi ba tawuce tabude kofa tafice sai kawai suka biyota. Faisal ne yafara bude gate yafita yaga Securities nakama Mom dake ihu sosai tana buga gate ga mutane har an fara taruwa kafin yayi magana su Baba duk sun fito kowa ya tsaya chak ganin Mom ga kudaje dake binta tana wani wari kaman tai kashi ajiki Baba ya kalleta yasake kallonta daidai Mamie dasu Aya ba lullubi ajikinsu suka leko Mom karaf ta gansu saita taho tana wani irin kuka zatabi gefen şu Baba tashiga gidan Ya Faisal da Ya Abdullahi suka wani sha gabanta strictly Faisal yace "kinada wani alaka da yan gidan nan ne dazaki shiga"? Mom takasa magana sai Aya datake kallo da Aysha dasuke kallonta cikeda tsana at dsame time kuma zakatansu yayi wani iri ganin mahaifiyarsu in a condition da basu taba tsammanin zasu ganta ba ko amafarki juyawa Ya Aysha tayi takoma ciki kaman ba mahaifiyarta tagani ba Mom tace "Ayshaaa!" Juyawa Aya itama tayi takoma ciki abinta Mom ta daura hannayenta akan bakinta tana wani irin kuka tace "dan girman Allah kuyafemin" juyawa Baba yayi kaman baisan wacace itaba yace "Yaya mukoma ciki mu karasa kari, Faisal ku kira yan sanda suzo suga wannan Matar da bamu santa ba tana kokarin shiga gidanmu" Baba yaja hannun Abba yayi ciki dashi Mustapa yajuya yabarsu Faisal yaciro wayansa ba wasa yashiga kiran yan sanda Mamie ta tako tafito tasa hannu ta karbe wayansa ta katse tace "kumu wuce ciki securities send her away" Faisal da Ya Abdullahi basuyi musu ba suka juya suka shiga gida Mamie ma tajuya zata wuce Mom takama kasan riganta Mamie yajuyo takalleta kneeling Mom tayi tana wani irin kuka tace "Hamidaaaaa!" Cikin wani irin murya mai sanyi Mom tace "Hamidah ki taimaken! Ki tausayamin! Nazama abin tausayi look at me meya rage? Nasan ban chanchanci yafita gareku ba amman abinda nazo nema kenan ko zanji rahaman ubangiji arayuwana, Mamie dubeni yanda Allah ya maidani? Look at me nothing is left nazama kaskantacciya, wlh nai nadama nayi dana sani Hamidahhh kiji tausayina" Mom tafashe dawani irin kuka mai sosa zuciyan muminai. EPISODE 1️⃣4️⃣2️⃣

Allah yasani Mom tabata tausayi sosai, Mamie tajuyo takalleta yanda Mom ke kuka tana hade hannayenta da yanda kudaje ke binta Mamie zuciyanta yamata wani kala batasan sanda cikin kuka tace "how could you Salima? Look at you today jibi abinda kikama kanki da kanki ina amfani? Babu wanda yafi karfin Allah duk girmanka daji da kanka da ganin kai wane wane ne Allah yaga sama zai iya karbe komi cikin sakannni da ba wayanki ko hikimanki ko basiranki bace ta maida ke abinda kike ba, yau ina Salima me takama datazo har gidana tacimin mutunci kika zage yarona kina cewa mun aurama yarki jobless guy? Munsa yarki a dakin kurkuku anama bata abinci, is she eating balance diet da salad, menenen menene Salima kin dauka anama Allah isgilanci? Baka raina samin mutum, da masu kudi da talakawa, da farin fata da bakın fata duk daya muke wajen Allah, wanda yafi wani awajen Allah shine wanda yafimu tsoron Allah, Salima gori, cin mutunci da kallonmu ba akomi ba bawanda bakiyi ba yau jibi yanda Allah ya maidaki just look at you!" Ahankali Mom tace "nayi kuskure sherin shedan n….." "Kece shedaniyar kanki!" Mamie tafadi azafafe, Mom takara fashewa da kuka, Mamie tai shiru zuciyanta na breaking she hates Salima takashe mata jika but she's not wicked! Banda haka she's a Muslim! Islam promotes tausayi, da jin kai, da yafiya, duk wanda yarufama wani asiri Allah zai rufa masa rannan gobe kiyama, babu kuma wanda yafi karfin jarabawa arayuwan nan, tayafe mata and she will try her best yaranta da kowa su yafemata to mema aduniyan gabaki daya kowa in this family hates her idan ita bata tausaya mata ba ina zatasa kanta, Mom nawani irin kuka idanunta akulle taji an kama hannunta ahankali dasauri tabude idanu Mamie tagani bata kyamaceta ba tace "tashi mushiga ciki!" Allahu Akbar! Mom saitaji takasa motsi tana kallon Mamie abubuwan data mata na dawowa fresh aranta, this is matan data zaga, taciwa mutunci, tama habaici, tazo har gidanta tacimata mutunci ta sumar da ita, tunda kalubalen nan yasameta Mamie this same Mamie data sumar is the first person that offers a helping hand to her not even her own blood brother saitawani fashe da kuka tace "Mamie namiki abubuwa dayawa, nazageki namiki tijara, na dakeki but kene zaki taimakeni har kina rikeni dudda ina wari eh Hamidah!?" Idanun Mamie sunyi ja sosai tace "tashi nace yawuce" daga Mom tayi tana kuka sosai Mamie takamota tashigo da ita compound din da babu kowa cikinsa, Baba dake kallon Mamie ta window yahau masifa. "Akan me zata shigo da matarnan cikin gidan nan saita fita" zaiyi waje Abba yakamasa ahankali yace "kayakuri Muhammadu Sani" Gwaggo tace "hakurin uwarmene Abubuakari dalla ka kyalesa sabida Allah ya maidata haka zata dawo garemu taje bataga komiba badai kisan kai ba wlh karma ku kawota nan bazan kalleta ba kuma bazata shigo falon nan ba"

Bq gidan Mamie ta kaita tabude mata bayi tace "shiga kiyi wanka zan aiko yar aikina takawo miki wasu kaya ki chanza sai nazo na kaiki ciki kuyi magana" gyadamata kai Mom tayi tana kuka tafito tadawo flat tashigo kowa na hararan Mamie bata cemusu komiba tawuce sama dakinta hira taga Asmeey nayi da Ramla suna ganinta sukai shiru Mamie tace "gyaran sakin kenan ko" wardrobe tabude tadauki wasu kaya tafito falo taba yar aikinta takai sannan tazo falon tazauna kusada Gwaggo dake hararanta da kowa ma harda su Aya Mamie takalli kowa tace "nasan Salima tamana laifi, takashe mana jika, which is not only mine nakune duka adakin nan, Asmeey almost lost her life…." Mamie tadanyi shiru bataso tama lissafo laifukan Mom sabida haushinta za'a cigaba da ji ahankali tace "you all should take a look at her, idan mu nan bamu yafe mata ba how do we even make Asmeey and beg yarinyar ta yafema mahaifiyarta, Abba, Baba, Gwaggo, Doctor, Abdullahi, Faisal, Aya, Aysha" Takira sunan dukansu a falo tace "kowa da kalan jarabawansa da kalan kaddaransa arayuwa! Dukanmu nan musulmai ne! I'm not asking any one of you to have wani relationship da Salima no that is your choice but yafiyan datazo nema mu yafemata bakomi rayuwa ce munama Allah laifi ya yafemana, look at her please ku yafemata" takalli Aya da Ayasha da idanunsu sukai jaaa Mamie tace "uwa uwa ce kodako bokace ita! Ba yanda zakuyi, tanada hakki akanku, koba komi she trained you girls to be responsible girls" cikeda zuciya Aysha tace "torture dai! Every single day cikin tsoro nake nabata mata rai! Fear fear fear! Tunda nake bantaba jin peace da farin ciki kaman wanda naji this period ba sabida nayi eliminating nata in my life, I don't want her, Mamie I don't want that woman wallahi, Mom dinmu is evil, she's wicked she's a bad moth……" takasa karasa maganan kuka yaci karfinta sosai Aya tai biting lips nata takalli Mamie tace "I looked at her dazu all I was feeling is finally Allah yafara hukuntata this is exactly abinda tai deserving for her sins amman tabani tausayi I wish ita ba mahaifiyata bane sabida nai dariya nace mata Allah ya kara, but how can this woman be my mother mata kalan Salima UKUBA CE BA UWA BA!" Aya tai shiru yaran sunbama kowa tausayi a falon Gwaggo ma jikinta yayi sanyi harshi Baba. EPISODE 1️⃣4️⃣3️⃣

Readers Also Read