Kenza eBookz

Uwar sadiku complete - Chapter 10

Uwar sadiku complete - Chapter 10

Uwar sadiku complete Chapter 10: Uwar sadiku complete Chapter 10. Rahma ta katse mata tunanin tana gaisheta, babu izgilanci ko alamar fushi a maganar…

4,500 words

Rahma ta katse mata tunanin tana gaisheta, babu izgilanci ko alamar fushi a maganar Rahman don haka itama ta dan saki jiki suka gaisa ba yabo ba fallasa.

Rahman tace

‘Yar taki ce tace ta fasa murfin tukunya kuma sai tazo da maganganu marasa dadi, shine nazo na ji wai me ya faru ne?’

Kamar ba zata yi magana ba, ta dan kauda kai tana murmushi sannan tace

‘Haba dai murfin tukunyar me? Abinda kaima a hannunka yana fashewa.’

Nan ta mayar mata da abinda ya faru da kuma sabulun da ta kama Yusran da shi, tace

‘Murfin tukunyar bai dameni ba kwata-kwata amma ace yarinya kamar Yusra ta san yanda zata bi ta cutar dani saboda ina auren babanta ai kinga dole na zata aikota aka yi.’

Mamaki ya cika Rahma, ta juya ta kalli Yusra. Yanda yarinyar tayi tsamo-tsamo ya tabbatar mata lallai ta aikata. Ta mayar da dubanta ga Aisha tace

‘Ikon Allah! To don Allah kiyi hakuri, wallahi abune na yarinta don na tabbatar babu yanda za ayi Mommy ta turota tayi wannan aika-aika. Kuma na tabbatar da taje bata gaya wa Mommy din abinda tayi ba, ta dai ce ta fasa miki murfin tukunya kinata fada. Zan yiwa Mommy din bayani in naje, yara ne sai hakuri in Sha Allah na san haka bazata sake faruwa ba.’

‘Hmmm! Babu komai ai ya wuce.’

Rahma ta mike tana fadin

‘Bari mu koma.’

Sukayi mata sallama suka fice.

Gaba daya yaran haushin Rahma suke ji saboda su zuwa sukayi ayiwa Aisha rashin mutunci amma ta zauna tana bada hakuri. Koda suka koma wajen Mommy din haka Rahma ta zauna tayi mata bayanin abinda Yusran ta aikata; sai dai daga yanda Mommy din take bata amsa ta san bata gamsu ba. Domin daga karshe ma cewa Rahman tayi sharri ne Aishan takewa Yusra, itama bata san sharrin Aishan bane shi yasa ta kama zancen.

Haka ta taso jiki babu kwari ta sauko daga falon saman tana jiyo hayaniyarsu. Tabbas daga wannan dan bayani da suka mayar ta gamsu ko da ba Mommy ce ta sa Yusra wannan aika-aika ba to da saninta aka aikata; haka ta zauna tana mamakin yaushe Zahra ta zama haka, ta watsar da tarbiyyar yaranta saboda kishi. ………

Ko da ma su Rahma basu zo ba dama Aisha bata yi niyyar gayawa Abban Sadik abinda ya faru ba, ba ayi abun a gabansa ba kuma zuwa yanzu ta fahimci Zahra mace ce da ta iya juya zance don haka ta barwa ranta abun. Amma idan suka gaya masa wani abu to tabbas da shi da su bazasu ji dadinta ba.

Sai dai itama Mommy din ta gane idan ta kai masa wannan maganar abun zai zama kamar ta kai karar kanta ne, don haka itama sai tayi shiru. Suma yaran ta gargadesu kada su gayawa Abbansu kuma kada su gayawa Rukayya wadda lokacin da akayi abun tana daki tana hadda. ……….

Wajen fiye da sati biyu kenan rabon da ya sha zobo a wajen Mommy, musamman da daddare. Don haka yanzu normal yake harkarsa, duk yanda yake so yana samu a wajen Aisha tunda ita Zahra tana jego. Baya son ya zargeta da zuba masa abun da zai taba lafiyarsa amma dai yana so ya tabbatar ko don ya gane abunda ya haifar masa da wannan matsalar.

Tun kafin ya karaso unguwar ya yiwo mata waya yace ta ajiye masa shayi in ya zo zai sha kafin ya wuce tunda kwanan Aisha ne.

Da murna ta tashi da kanta ta shiga kicin don dama tunda ta haihu ko zobon zata hada masa bata bari Rahma tayi kuma ko ya sha ko bai sha ba da kanta take zubar da sauran ba tare da mutan gidan sun sani ba.

Nan da nan ta dafa shayin ta juye a flask ta hada da kofuna biyu ta kai dakinta tunda yanzu mafi yawancin lokuta idan ya dawo tana dakinta.

A dakin kuwa ya sameta, tun kafin ma yace ina shayin ta zuba masa. Ya zauna a kan dadduma ya jingina da gadonta yayinda ita kuma take kan gadon. Yana shan shayin suna hira; a zuciyarsa yana fatan abinda yake zargi kada ya tabbata. Yana ji a jikinsa cewa Zahra ba zata iya cutar dashi ba ko da kuwa don kishi ne.

Sai wajen tara da rabi sannan yayi mata sallama ya tafi; yana ta mamakin yanda yau din take ta walwala fiye da ‘yan kwanakin baya, tana ta faman kakalo hira har ya shanye shayin.

A wannan daren duk yanda yake bukatar Aisha kasa yin komai yayi, sai jagwalgwala ta kawai da yayi. Sosai ta firgita saboda da ta fara murna cewa matsalarsu ta kare, don haka saida ya dauki lokaci yana kwantar mata da hankali yana bata tabbacin ya riga ya sami magani don haka daga wannan daren ba za a sake samun irin wannan matsalar ba.

Haka suka kwana tana fatan Allah ya sa da gaske yake ya sami maganin yayinda shi kuma yake matsanancin mamaki na yanda za ayi ace Zahra tana zuba masa wani abu a shayin don ya kasa kusantar Aisha.

Wayewar garin ranar ya kama kwananta ne ita Zahran, har dare yayi ya shiga wajen nata. Yayi niyyar ya tunkareta da maganar abinda take zuba masa a zobo amma kuma har suka kwanta bacci yana wasi-wasi.

Duk saukin kanta da halayenta masu kyau da yake so amma fa bata taba karbar laifinta; haka zata saka shi a gaba suyi ta musu a kan lallai sai ya fahimci ba itace mai laifi ba sai dai idan wani ne mai laifin. Don irin wannan ma ya san ba zata taba yarda tace ta saka masa abu a zobo ba, idan taga dama ma haka zata sa kuka ta juya zancen a kan cewa shine zai zargeta tayi ta rigima har sai ya bata hakuri.

Haka har gari ya waye sai dai kawai kallonta da yake yana mamaki; sau biyu tana tambayarta me yasa yake kallonta shi kuma sai yace mata babu komai.

Haka ya kare wannan kwana biyun ba tare da yace mata komai ba. Kuma duk cikin kwana biyun nan batayi zobo ko lemon tsamiya ba, shayi ma kuma da bai nema ba bata bashi ba. Sai na safe kawai wanda yace a daina saka komai a ciki a dinga bashi ruwa kawai zai hada shayinsa da kansa.

Ranar da zai koma kwanan Aisha ranar ne tayi zobo, lafiyayye sai kamshi ne yake tashi ga sanyi har gumi jug din yakeyi. Duk yanda yake son zobon nan haka ya hakura, har ta cika masa kofi ya dubeta yace

‘Kai ba zan sha zobon nan ba, bana jin dadin cikina sai dai ko wani lokacin.’

Suka cigaba da hirarsu a dining table, shi yana cin abinci ita kuma tana taya shi hira da yake lokacin wajen karfe biyar ne don haka ita ta riga taci abincinta na rana. Ya dubeta ya tura mata kofin zobon yace

‘To ai sai ki shanye wannan da kika zuba.’

Tayi ‘yar dariya tace

‘Ni kam na sha nawa, wannan ai naka ne. Sai dai idan baka sha ba na ajiye da daddare na sha.’

Ya cigaba da cin abincinsa; dama bai yi zaton zata sha ba tunda ta san ta saka wani abun a ciki don tabbas ya san da babu wani abun a ciki da tuni ta shanye zobon nan.

Ya kusa gama cin abincin Sadik ya shigo daga makaranta, ya riga ya shiga SS 2 don haka idan aka tashi daga makarantar yana tsayawa lesson sai biyar suke tashi. Bayan yayi musu sannu da gida ya dubi jug din zobon nan yana gumi yace

‘Abba in dauko kofi in sha zobonka, wallahi zafi nake ji yau an yi rana.’

‘Ai ba ma sai ka dauko kofi ba dauki wannan ka sha.’

Abban ya bashi amsa yana nuna wanda Mommy ta riga ta zuba masa a kofi.

Da sauri Sadik ya karaso da niyyar daukan kofin, kafin ya karasa ta balla masa harara tana kokarin buge masa hannu

‘Naka zobon ai yana kicin da abincinka ka shige ka dauka.’

‘Mommy wai na sha wannan din kafin na cire uniform.’

‘To ki barshi mana tunda ba sha zanyi ba.’

Abba ya fada yana kokarin daukar kofin ya mika masa, tayi wuf ta rigashi daukewa tana fadin

‘Allah ba zai sha ba sarkin rashin kunya, yaje ya sha nasa.’

Sadik ya jefa jakarsa kan kujerar falon ya shige kichin yana gunguni, ta mayar da kofin ta ajiye tana ta wani kumbura.

Sai da ya gama cin abincin tsaf ya dubeta yace

‘Zahra.’

‘Na’am.’

Ta amsa da alamun jikinta ya dan yi sanyi.

Ya kalleta suka hada ido, ta kau da nata idon saboda yanda yake kallonta kamar yana kokarin karanto wani abu a zuciyarta.

Yace

‘Ko dai akwai wani abu a zobo nan ne wanda ba Sadiku aka zubawa ba ni aka zubawa.’

Ta dan dirirce sai kuma tayi kokari ta waske

‘Ban gane ba? Kamar me kenan? Bayan ga irin zobon nan Sadiku ya debo daga kicin kuma ya sha.’

‘To me yasa ba zai sha wannan ba kema kuma ba zaki sha ba?’

Ta dan bata rai sannan tace

‘Gani nayi ai ba tarbiyya bace na zubawa ubansa abinci shi kuma ya dauka ya sha, a kofin ma da na zuba maka. Amma idan kana so lallai ya sha zaka iya kiransa ka bashi, ni dai ba zan sha ba tunda na gaya maka bana bukata. Me zan zuba maka a zobon? Shekaru goma sha kana shan zobona ban taba zuba maka komai ba sai yanzu? Saboda dai ni babu abinda zanyi na burgeka. Ai shikenan!’

Ta tura kujerar ta mike ta bar masa waje ta nufi dakinta, ya bi bayanta da kallo yana mamaki.

Dama ya san haka zatayi domin hakan ne dabi’arta a duk lokacin da bata da gaskiya, ya karasa cin abincinsa ya tashi ya shige dakinsa.

Ya saba bata hakuri idan sukayi irin haka sai dai yau ya ci alwashin ba zai bata hakuri ba don shima ta bashi haushi da mamaki. Bayan sallar isha’i ya gama shirinsa ya sameta a daki yayi mata sallama ya nufi wajen Aisha.

UWAR SADDIKU

Written by Sakina Yazid (Innar su Amal)

16

Tun daga lokacin da Aisha ta kama Yusra tana zuba mata sabulu a abinci sai kuma ta samu saukin fitnar Zahra, sai dai ita Aishan ta kasa sakewa da yaran gaba daya har Rukayya. Ko da Rukayyan ta zo tayata kwana sai tayi ta kula da ita tana kula da motsinta musamman a kitchen.

Tun wannan lokacin kuma sai fitnar Zahra tayiwa Aishan sauki, duk da bata fasa aniyar raba Aisha da Yusuf ba ta dai bari ne kawai tana jira ta tara kudin da zata iya bawa Malam Hatimu yayi mata aiki. Sannan kuma tunda Hajja ta bata maganin nan ta boye a bayan wardrobe ta sami natsuwa tunda duk abinda take so yayi mata yana yi, sannan kuma ko fada zai mata a kan wani abu da zarar ta bata rai sai ya fasa. -------

Kwanci tashi har shekara ta zagayo an fara lissafin azumi, tunda aka ce azumi saura sati hudu Abban Sadik ya fara maganar kayan Sallah.

Saida ya gama magana da Zahra tayi masa total gaba daya har na Aisha, ya tabbatar mata da anyi albashi zai saka mata kudin.

Yana zaune a falon Aisha ta tada kai da cinyarsa suna hira, ya mika hannu ya dauki wayarsa yace

‘Au, bari na turawa yayarki kudin kayan sallarku don na huta, sai kuma a shiga hidimar azumi.’

Ta dauke idonta daga kallon TV din da take kallo tace

‘Wai Mommy?’

‘Eh, kin san sallar ta matso.’

Ta tashi zaune ta sashi a gaba

‘Don Allah ni dai kada ka tura da nawa, ka turo min kudin zamu saya tare da su Zahida kaga waccan babbar sallar ma haka sukayi anko babu ni.’

Yayi ‘yar dariya

‘Yanzu ku kayan sallar ma sai kunyi anko? Mata masu gari. To gaya min lambar sai na tura miki naki ita sai na tura mata nata da yara.’

Tana gaya masa kuwa nan take ya tura mata dubu dari kudin kayan sallarta, sannan ya tura wa Mommy nata da na yaranta.

Bayan ya je gidan ne take tambayarsa taga kudi amma basu cika ba; yayi mata bayani cewa Aisha ta karbi nata zasu saya da ‘yan uwanta. Babu yanda ta iya haka ta hakura da shirin tsiyar da tayiwa Aisha domin duk mitar ta yace mata shi ya riga ya gama wannan maganar. ……..

Cikin azumi ya sanar da Mommy yana shirin zai je aikin Hajji kuma da ita zai je, a take ta fara murna. Tayi masa godiya sosai sannan tace

‘Amma wallahi da ma Umrar azumi ka biya min, ka ga zuwana Hajji biyu fa zan so zuwa Umra, musamman ta azumi. Kuma ka ga ma yanzu Sumayya bata isa yayeba.’

Ya danyi tunani yace

‘Hakane, to babu damuwa. Sai muje Hajin da Yaya Bello in ya so kafin karshen shekarar sai na biya miki Umrar ko ba zan je ba sai kuje da Sadiku. Ita kuma kanwarki badi sai muje Hajin da ita.’

Nan take ta sake cika da murna tunda taji yace zai biya mata suje ita da Sadik, tana ganin kamar ma idan ta saka shi a gaba da naci ya hada harda Yusra in ya so su tafi ita da yaranta. In ya so Hajin da yace zai je da Aisha kuma ta san yanda tayi a ka bar zancen don tana ji a jikinta kafin shekara war haka ma ta samu an yi mata aikin nan an kada mata Aishan. ……..

Saura kamar sati hudu tafiyar alhazai Aisha ta fara laulayi, amai da jiri babu sassauci. Suna zuwa asibiti aka tabbatar ciki ne da ita sati hudu, aka rubuta mata magunguna aka sallamesu.

Tun a hanya yake tsokanarta domin da ya fidda rai da yaga aurensu har ya haura shekara ko batan wata bata taba yi ba. Yana kaunar Aisha sosai don haka yake so ta haifa masa yara ko guda biyu ne, sannan ne zai tabbatar jininsa da tsokarsa ta gaurayu da ta Aisha.

Don haka suka dawo gida suka cigaba da rainon cikinsu; duk da bayan ta fara shan magungunan da aka bata laulayin yayi mata sauki tunda tana zuwa aiki kuma tana harkokinta sosai.

Sati biyu da zuwansu asibiti ya kama ranar da jirgin su Abba zai tashi.

Tsaf Abba ya gama shirinsa yayinda Malam Sule da Yaya Bello suke jiransa a mota, ya sa Rukayya a gaba ta hada kayanta, ya kaita gidan Aisha yace ta zauna a nan har sai ya dawo daga Saudiya sai ta koma wajen Mommy. Ya sanar da Mommy din kuma ta dinga duba masa Aisha don tana dauke da juna biyu. Yayi mata sallama ya fice suka kama hanya. Yana fita ta mike ta fara zarya a falon, wato don ma raini ita yake gayawa yayiwa amaryarsa ciki ta kular masa kafin ya dawo? Tayi kwafa, in sha Allah wannan cikin sai ya bare kafin ya dawo.

A take ta dauki wayarta, har ta lalubo lambar Hajja zata kirawo sai kuma ta fasa, ta kirawo Malam Hatimu mai almajirai.

Bayan ta sanar da shi cewa wancan aikin fa tana nan tana hada kudinsa sannan ta dora da bayani

‘Malam yanzu ciki ne da ita amma gaskiya ina so ne a lalata cikin, kwata-kwata bana so ta haihu na fi so yanda ta shigo ita kadai ta fita ita kadai kawai.’

Yayi ‘yar dariya

‘Wannan karamin aiki ne, yara ma zasu iya yinsa. Akwai laya da za ayi aiki a ciki a baki ki samu ta tsuguna a kan layar nan, idan dai ta tsuguna to kafin awa daya cikin ya rabu da jikinta.’

‘To Malam yanda za ayi ta tsuguna din shine matsalar don ka ga ma ba gidan mu daya ba.’

‘Kada ki damu, ko yara ki bawa su jefa mata a masai. Na san masanku na tangaran ne layar kuma mai sulbi ce ana jefawa ko ba a kora ba zata wuce, idan dai ta tsuguna a kan wannan masan cikin nan sai ya fita daga jikinta.’

Tayi murmushin farin ciki, yayi mata bayanin kudi Naira dubu goma sha biyar. Nan take tana ajiye waya ta tura masa kudin da alkawarin washegari zai taso yaro ya kawo mata har gida ita kuma zata sallami yaron.

Cikin walwala ta karasa wunin ranar domin dama babban abinda yake firgita ta shine Aisha ta tarawa Yusuf wasu yaran. Ta ci alwashin ko sau nawa yarinyar nan zatayi ciki sai ta barar da shi muddin Malam Hatimu yana raye. ---------

Tunda Abban ya kaimata Rukayya Rukayyan take ta magiya don Allah suyi cake tunda gobe da akwai makaranta kuma yanzu ta dawo na ta huta da dafa abincin makaranta.

Haka Aisha ta tashi ta hada kayan cake, da yake ta koyawa Rukayyan ma kusan duk ita tayi aikin da yake ba Mai yawa bane. Ta gama ta zuba cake din a oven tanayi tana wanke wanke, kafin magriba ta gama.

Ana idar da sallar magriba ta sa Rukayyan ta dafa musu indomie da kwai suka juye a tray suna ci suna hira. Sun kusan cinyewa aka buga kofa, Aisha ta tsame hannunta tana fadin

‘Cinye ragowar bari naje na duba kofa.’

Saida ta zo daf da gate din tace

‘Waye.’

Cikin isa aka amsa mata

‘Mune.’

Ko bata ga mai maganar ba ta san Yusra ce don haka ta bude kofar tana Lahaula a zuciyarta saboda sharrin yaran ya fara bata tsoro.

Tana budewa suka shigo ita da Sadik, ya dubeta shekeke yace

‘Ina Rukayya, Mommy tana kiranta.’

Ta juya tana fadin

‘Ku shigo tana ciki.’

Suka biyo bayanta.

Suna shigowa falon Rukayya ta mike tsaye da kwanon abincin nasu a hannunta zata kai kicin tana tande baki saboda indomie din da yaji. Suna karasawa ciki Sadik yace

‘Kizo in ji Mommy.’

Ta kalleshi da mamaki

‘Yanzu?’

Yusra ta balla mata harara tace

‘A’a gobe?’

Aisha ta karasa tana fadin

‘Ce miki akayi fa Mommy na kiranki kike tambaya Rukayya, kai kwanon kicin ki sha ruwa ki zo kuje in ya so kya dawo.’

Ta wuce kicin din ta ajiye kwanon ta fito, ta dauki hijabinta wanda tayi sallar magriba da shi a falon ta saka tace

‘Sai na dawo Anti.’

Suka tasa ta a gaba kamar wata mai laifi suka wuce.

Ta riga ta san wannan kiran ba na Allah bane don haka ta mayar da kofarta ta rufe don ta san ba za a bar Rukayya ta dawo ba.

Haka kuwa akayi, tana shiga gidan Mommy tace an gama kwanan ba zata sake taya wannan matar kwana ba. Tayi maganar kayanta aka ce yayyenta zasu kwaso mata gobe amma ita kam ma idan aka sake ganinta a kofar gidan sai an karya kafarta. Haka ta kwana tana matse kwalla saboda takaici; ga cake dinta a gidan wanda ta san bata isa tayi maganarsa ba don ko an karbo ba za a bari ta ci ba. ……….

Haka da gari ya waye Aisha ta tashi ta gama shirin zuwa aiki, a al’ada bakwai da kwata Malam Sule yake buga mata kofa su tafi, idan ya jiyeta sai ya wuce da yaran tunda makarantar da take koyarwa ta fi kusa. A shirye ta zauna a kan kujerar dining table tana jiransu, da taga da dan sauran lokaci ta kirawo Yaya Zainab a waya ta sanar da ita zata zo in an tashesu daga makaranta ta dauki Amira;’yar wajen Zainab din ce wadda shekarunta sun kai sha uku. Ta sanar da ita Abba ya tafi Hajji kuma Zahra ta hana ‘yar tayin kwanan tata, in ya so daga nan sai ta dinga kaita makaranta da safe suna dawowa tare tunda saura sati biyu a bayar da hutun Sallah kuma tana sa rai kafin a koma Abban ya dawo.

Suka gama waya ta ajiye ta cigaba da kallon agogo. Har karfe bakwai da rabi ta gota bata ji bugun Malam Sule ba, don haka ta kirawoshi a waya. Kafin ma tace wani abu ya fara magana cikin girmamawa

‘Afuwan Hajiya, wallahi Hajiya Babbace tace yara suna makara don haka na wuce na kaisu idan na ajiyesu na dawo na daukeki. Kin ganmu a hanya dana kaisu yanzu zan juyo in Sha Allah Hajiya ayi hakuri da ni.’

Tace

‘Babu komai Malam Sule, ba ma sai ka dawo ba yanzu zan wuce babu komai.’

Kafin yace wani abu ta ajiye wayar tana murmushin takaici; batayi mamakin hakan ba domin idan wannan munafukar matar ce mai fuska biyu abinda yafi haka ma zata iya yi tunda wanda take kunya baya nan. Haka ta mike ta fita ta hau motar haya ta kama hanyar makaranta. Tana tashi daga makarantar kuwa ta wuce gidan Yaya Zainab, can ta wuni sai bayan la’asar suka taho tare da Amira. ……….

Tun kafin sallar azahar dan aiken Malam Hatimu ya iso, babu kowa a gidan daga ita sai Jummai. Maigadi ne ya shiga ya sanar da su akwai yaro da yace an aiko shi wajen Hajiya.

Nan da nan ta sa aka shigo da shi bakin kofar falo, ko gaisawa basuyi ba ta karbi sakon wanda yake a nannade a bakar leda ta bashi naira dubu uku tace ya hau mota.

Yayi godiya ya tafi.

Tun lokacin take tunanin yanda za ayi ta aika Yusra ta jefa wannan abun a toilet. Tun lokacin da ta fasa mata murfin tukunya Yusran ta daina shiga gidan, gashi jiya batayi tunani ba ta aika suka taho da Rukayya. Da ta sani ma da ta bari in ya so yau din sai su yi amfani da wannan damar a jefa maganin kuma a taho da Rukayya. Rukayyan ta riga ta bawa Mommy tabbacin a dakin baki suke kwana don haka a nan ne take so a jefe layar tunda ta san shiga dakin Aishan zai yi wahala. Amma in dai tana kwana a dakin bakin to tabbas ko cikin dare sai ta shiga bandakin.

Suna zaune a falo suna kallon TV bayan magriba Rukayya ta dubi Mommy cikin sanyin murya tace

‘Mommy, kayana fa suna gidan Anti kuma harda books dina ina son naje na dauko don gobe da su zanje school.’

Bude baki tayi zata yi mata tsawa sai kuma ta tuna dama tana neman damar da zata yi aike gidan, ta dubeta tace

‘To, bari Yayarki ta rakaki ku dauko.’

Ta mike tana fadin

‘Ina zuwa.’

Sai da ta hau sama sannan ta kwalawa Yusra kira, tana zuwa ta jata daki.

Layar ta bata a hannunta tayi mata bayani yanda zata yi mata da ita, bayan ta gama bayanin tace

‘Ki kula fa kada wanda ya gani, idan ta wuce ko bakiyi flushing ba babu matsala amma idan kinga bata wuce ba to ki kora.’

Ta amsa

‘To.’

Har ta juyo zata fito ta juya tace

‘Mommy layar ta mecece?’

Ta harareta tace

‘Ina ruwanki? Kiyi abinda aka saka ki kawai.’

Ta juya ta fice ba tare da tace komai ba.

Falon kasa ta dawo ta zauna bayan ta nade layar a siket dinta, ta cigaba da harkarta kamar yanda Mommy din ta tsara mata. Jimawa kadan Mommy din ta sauko, tana zama ta dubesu tace

‘Kuje ku debo kayan Rukayyan, maza kada ku bata lokaci.’

Ta harari Rukayyan tace

‘Saura ki zauna wani shisshigin.’

Suka tashi suka fice. ……… Suna zaune ita da Amira a falo suka ji bugu, ta tashi ta bude kofar. Kamar yanda Yusra ta saba ko gaisheta bata yi ba ta sa kai cikin gidan, Rukayya ce ta gaisheta sannan a kunyace tace

‘Kayana Mommy tace mu debo.’

Ta dafa kafadarta tace

‘To muje ku diba, suna nan a inda kika barsu.’ Suna shiga falon Aishan ta zauna a kan kujera tace

‘Kuje ku debo.’

Suka nufi dakin baki inda nan ne kayan Rukayyan suke.

Suna shigewa Aisha ta dubi Amira tace

‘Bisu Amira, ki sa min ido musamman a kan Babbar.’

Nan take ta tashi ta wuce, Rukayya na tsaye a gaban wardrobe tana fito da kayanta wadanda dama ba yawa ne da su ba yayinda Amira take jingine a jikin mudubi wanda yake kusa da kofar bandaki. Amira tana shiga ta wuce ta zauna a gefen gado, ta kula da yanda Yusra take mata kallon raini don haka itama ta tsare gida.

Bayan ta gama fito da kayan daga wardrobe din ta dauki jakarta ta makaranta ta bude kamar tana neman wani abu. Ta dubi Yusra tace

‘Yaya Yusra dan zuba min kayan a ledar gata nan kusa dake, bari na tambayi Anti books din da nayi homework naga bata sa min a nan ba.’ Kafin Yusran ta amsa ta fice tana dauke da jakar. Tana fita Yusran taja tsaki

‘Ki kwashi kaya kawai sai kin bata mana lokaci.’

Ta dubi Amira tana kokarin bude bandaki tace

‘Bari nayi fitsari.’

Tayi wuf da shige bandakin ta turo kofar, tana shiga ta jefa layar a toilet tayi maza ta kora. Ta tsaya a gaban sink ta wanke hannunta ta danyi jinkiri sannan ta fito. A dai-dai lokacin Rukayyan ta shigo tana rufe jakarta wadda cake dinta ne taje ta juyo tana fatan Mommy ba zata gani ba in ya so gobe in taje makaranta sai su cinye ita da kawayenta.

Tana shigowa suka karasa hada kayan suka kwasa suka fice.

Suna fitowa falo Rukayyan ta yiwa Aisha sai da safe, har sun kusan fita daga falon Aisha tace

‘Rukayya idan kin je ki kunno min ruwa idan tankin ya cika zan bugo waya sai a kashe.’

Ta amsa suka fice.

Gida daya ne tsakanin gidan Zahra da na Aisha don haka bai sake hada ruwa ba a gidan Aisha. Sai dai kawai aka hada tankin gidan Aisha da injin jan ruwa a can gidan. Kafin ya tafi Hajji kullum da suba yake kunna ruwan tankunan su cika ya kashe daga can ko kuma da daddare idan ba a can ya kwana ba. Tun ana i gobe zai tafi ya manta bai kunna ba, ranar dazai tafi ma haka ya sake mantawa har ya tafi. Ya gayawa Sadik ya dinga kunnawa kullum, sai dai yana tafiya Sadik din ya murder wata waya ta yanda in ya kunna injin iya tankin gidansu kawai zai cika. Don haka ko da suka shiga gidan Rukayya ta kunna injin tankin gidansu ne kawai ya sake cika aka kashe.

-------

Sai wajen tara da rabi lokacin ma Amira ta fara gyangyadi a falon, suka wuce daki suka kwanta. Bayan sun shiga dakin saida ta duba ko ina ta daga katifa ta daga kafet don ta tabbatar Yusra bata binne mata wani abu ba sannan suka kwanta.

Can wajen Sha biyu da Rabi na dare fitsari ya matseta, tana tashi ta shiga bandakin da yake nan dakin tayi fitsarin ta dawo ta kwanta. Minti goma Sha biyar da kwanciyarta taji kamar ana karta wani abu a mararta, ta tashi zaune ta dafe mara ta takure a waje guda tana fitar da numfashi da kyar.

A firgice Amira ta farka, bata gani sosai saboda duhu haka ta lalubota ta tabata tana fadin

Readers Also Read

More by Bilyn Abdull