Uwar sadiku complete - Chapter 21
Uwar sadiku complete Chapter 21: Uwar sadiku complete Chapter 21. Ranar asabar ce wadda gobe Lahadi jirgin Abban Sadik da Aisha zai tashi.
4,498 words
Ranar asabar ce wadda gobe Lahadi jirgin Abban Sadik da Aisha zai tashi.
Duk wani shiri da take bukata ta gama shi; abu dayane a ranta yanda zata tsara Abban Sadik ya yarda ta biyawa kanta kudin zuwa Dubai ta bishi. Tunda yayi maganar ta sa aka bincika mata aka gama yi mata lisaffi; kudin jirgi, hotel har zuwa kudin da take so ta kashe ta lissafa kuma taga cewa tana da su zata iya biyawa kanta.
Jirgin safe zasu tafi don haka zuwa goman dare sun gama komai sun kwanta. Yana kwance rigingine tana kwance a gefensa sai dai basu kashe fitila ba tukunna don basuyi bacci ba.
Mirginawa tayi ta koma jikinsa, ta dora kanta a kan hannunsa sannan ta dora tafin hannunta a tsakiyar kirjinsa, tace
‘Yallabai za a wuce da ni Dubai din?’
Ya dan dago kansa ya kalli fuskarta
‘A’a. Ai na gaya miki babu kudi amma kada ki damu kiyi ta addu’a business din ya kankama zamu je Dubai in Sha Allah.’
Sukayi shiru na dan lokaci, jimawa kadan ta muskuta tace
‘Don Allah to ni zan biyawa kaina, kaga dama adashin da nace maka na dauka last month 250k suna nan kuma inada wasu savings sai na kara.’
‘Um, kiyi abinda kika tsara zakiyi da kudinki in Sha Allah next time sai muje Dubai din.’
‘To kayi tunani dai kafin muje, kudin suna dollar account dina Kuma kaga visa din Dubai bata wahala. Kafin mu gama aikin Hajji kayi shawara. Kaga kafin ma mu dawo gida mun huta, ko kwana biyun ne ina laifi.’
‘Saboda muje kiyi min addu’a, ki tsara ni kiyi min wayo ko?’
Ta kyalkyale da dariya.
Suka karasa hirarrakinsu suka yi bacci.
Gari yana wayewa karfe tara na safe jirginsu ya daga sai Saudiyya. ___
Ranar litinin karfe shida na safe Uwar Sadiku suka kama hanyar garin Doguwa; a motar Amina suka tafi sai dai akwai Alele yaronta shine yake tukasu.
Nisan garin ya bawa Zahra mamaki matuka, don gani tayi kamar za a fita daga garin Kano. Ko da suka Isa Doguwa ma wucewa sukayi sai da suka kusa fita Kano sannan suka sauka daga kwalta suka fada wani daji, da ba don taga alamar motoci suna bi ba da zata ce babu wanda yake shiga wajen.
Hanyar tsakiyar daji take, babu koda gona a kusa.
Ta kalli Amina wadda suke zaune a bayan mota tare zuciyarta fal tsoro, Amina tayi murmushi tace
‘Kada ki damu, kina hawowa nan layin kin zama bakuwar Malam Jani, babu abinda zai cutar dake har ki fito ki kama hanya sosai.’
Ta dan gyara zama ta mayar da hankali ga kallon hanya duk da ba wani gani takeyi sosai ba.
Sun kai kamar minti goma sha biyar suna zura gudu a lokon nan kawai sai taga sun fado wani sarari mai fadin gaske; kamar wata karamar unguwa. A gaban wani babban gida sukayi parking wanda yake kewaye da wasu gidajen tsilli-tsilli sannan ga yara suna wucewa jefi-jefi. Yanayin wajen yanayi ne mai dadi, babu sanyi kuma babu zafi sannan ko ina a share yake tsaf.
A kofar babban gidan sukayi parking kusa da wasu motoci guda biyu wanda ga dukkan alamu masu kudine sosai kuma suma bakin wannan gidan ne.
Tun kafin su gama fitowa daga mota yaro ya fito daga cikin gidan yayi musu iso. Madadin su shiga ta kofar gidan sai yaron ya zagaya da su ta wata kofar da take bayan gidan.
Daki ne ya sha shimfidu na jajayen daddumai, har labulayen dakin duka jajaye ne. Ya nuna musu wata bakar dadduma yace su zauna, bayan sun zauna yace
‘Za ayi muku iso idan Malama ya gama, yana da wasu bakin.’
Kafin su amsa ya fice daga dakin.
Suna nan zaune tun wajen karfe tara na safe har sha biyu ta gota babu wanda ya sake lekosu, idan suka taba hira sai su koma suyi shiru.
Zahra ta dubi wayarta taga lokaci, ta dago ta dubi Amina tace
‘Amina anya ba a manta damu a gidan nan ba kuwa?’
‘Nace miki yana sane, tunda naga motocin nan na san yana da baki sai ya gama da su zai sauraremu.’
‘To ya ya za ayi muyi Sallah kin ga dai daya tayi.’
Ta dan zaro ido
‘Sallah! Ki rufa mana asiri, ai sai dai idan mukaje gida ma hade. Wa ya gaya miki ana kallon gabas a nan?’
Kallon da Amina take mata ya sa tayi shiru, suka cigaba da jira.
Jimawa kadan wajen daya da rabi yaron da ya rakosu dakin ya leko yace shu shigo. Ya wuce gaba suka bi bayansa. Kofar da suka shigo ba ita suka fito ba, wata kofar ce a dakin ya shiga suka bishi. Siririn corridor suka bi wanda ya sada su da wani daki mai kawanya.
Kusan komai na dakin ja ne sai fari tsilli-tsilli. Bangon da yake kallo kofar an bi shi kaf an rataye tarkace kala-kala, kayuwan dabbobin ita dai Zahra kamar har shekar tsuntsu ta hango.
Jar dadduma ce a shimfide a gaban bangon wadda kallo daya zaka yi mata ka san ta hadiye datti da yawa. Yana zaune ya tankwashe kafafu babu wata sutura a jikinsa sai gajeran wando da bai karasa gwiwarsa ba.
Tun da suka saka kafa a dakin Zahra ta damki hannun Amina ta rike gam saboda tsoro, ita kuwa Aminan da yake ta saba kai tsaye ta wuce gaban wannan bakin katon suka gurfana.
‘Ki gayawa bakuwarki ba a tsoro a nan Hajiya.’
Ya fadawa Amina da kakkausar muryarsa.
Nan da nan Zahra ta dan gyara zama tana kokarin ta dake.
‘Me kike so ayi da kishiyar taki da ta hanaki walwala?’
Sai da Amina ta zungureta sannan ta tuna ita akewa tambayar
‘Um ni so nake kawai a rabata da mijina, su rabu har abada kuma kada ya sake auren wata mace.’
Aka kyalkyale da dariya wadda har dakin saida ya amsa, sai dai ko da suka kalli fuskar malamin da suke gabansa babu alamar shi yake dariyar.
Ya mika hannunsa baya ya zaro wata babbar tasa wadda kusan za a iya cewa hannu daya ba zai iya dauka ba. Ya dire tasar wadda take dauke da ruwa a gabansu, ya dauki wata bakar kwalba a gabansa ya diga wani mai a cikin tasar sannan ya fara motsi da baki kamar mai wuridi. Lokaci kadan ya gama sambatun ya busa a tasar sannan ya dubi Zahra yace
‘Duba min nan.’
Amina ta dan dungureta suka matsa gaban tasar suka leka; Aisha ce sanye da abaya suna tafiya tare da Abban Sadik a wani wajen kamar farfajiyar masallacin Madina. Sai dai ita Aishan wani abu kamar glass ya yi mata kawanya shi kuma Abban yana gefenta babu abinda yayi masa kawanya.
‘Sune wadannan ko?’
Da mamaki take gyada kai tana
‘Eh, sune, sune.’
Aka sake bushewa da dariyar nan da basu san wanda yake yinta ba, sannan mutumin mai kakkausar murya ya nuna Aisha a cikin tasar yace
‘Kinga wannan, ba zata tabu ba. Ko me za ayi mata ba zai yi tasiri sosai ba domin ta fi ki shiri.’
Dariyar nan ta sake karade dakin, bayan ta lafa ya nuna Abba yace
‘Wannan za muyi miki aiki a kansa amma sai ya baro wajen nan da yake, idan ya dawo gida sai ki sanar damu.’ Cikin in ina tace
‘To ba zasu rabu ba kenan?’
Dariyar ta sake karade dakin, bayan anyi shiru yace
‘Aikin da zamu yi miki shine; zamu shafe masa ita daga tunaninsa. Zai manta da ita ya manta ya sake aure, ke duk wani wanda zai iya fada a ji ma a auren zamu mantar dashi labarin Aisha. Idan aka yi haka to tabbas ita da danginta zasu raba auren don bazasu iya tuna masa da ita ba, don auren ma ba shi zai saki ba sai dai suje kotu alkali ya saki. Daga ranar da mukayi aikin ba zai sake tunawa da ita ba.’
Dakin ya kuma cika da dariyar.
Ita kanta saida tayi murmushi saboda wannan tsarin nashi yayi mata,tabbas idan Abba ya manta da Aisha zuwa wani lokaci ne ‘yanuwanta zasu raba auren. Shikenan ta huta da wannan alakakan.
Kamar daga sama aka jefo wata karamar bakar tasa gabansu, mutumin yace
‘Ku juye duk abinda kuka zo da shi a nan.’
Nan da nan Zahra ta bude jakarta ta fito da kudin da ta zo da shi naira dubu dari biyu ta saka a tasar, a take tasar ta bace.
Mutumin yace
‘Idan ya dawo a zo a sanar da mu, zuwa lokacin dan matsuruto zai sanar da ku kudin aikin da zaku ajiye masa kafin aiki ya fara. Ku tafi, ku tafi.’
Nan da nan suka mike, yaron da ya shigo da su ne ya sake shigowa ya wuce musu gaba. Ya bi da su ta wata kofar da ban da ba ta nan suka shigo ba, sai a lokacin Zahra taga sun fito ta kofar gaban gidan daidai inda suka ajiye mota. Motocin da suka tarar da safe basa wajen sai dai wata bakar mota wadda da alama bayan sun shiga ne masu ita suka zo.
Ba tare da bata lokaci ba suka shiga mota suka kama hanya, nan dinma hanyar da suka bi ba ta ita suka fito ba.
Babu wanda yayi magana sai da suka fito daga daji suka hau kwalta. Amina ta dubi Alele da yake tuki tace
‘Alele duk mai abun da ka gani ka tsaya mu siya mu dan sa wani abun a bakinmu, na manta ban yiwo mana guzuri ba yunwa muke ji.’
‘To Hajiya, mun kusa zuwa wajen masu mangoron nan ai.’
Ta dubi Zahra tace
‘Kawata kin ga inda za a magance miki matsalarki ko? Yanda yayi miki alkawarin haka zai yi miki aiki zaki sha mamaki.’
‘Hmmmn! Ai na ga alama.’
Suka yi shiru kowacce tana kora ruwan robar da suka taho da shi.
Jimawa kadan Zahra tace
‘Kawata naji yana maganar kudin aiki bayan kudin da na ajiye masa.’
‘Eh, ai in dai kin shiga da jaka wannan dakin sai kin ajiye duk kudin da yake jakar a wannan tasar ko an yi aiki ko ba ayi ba. Kudin aiki kuma da ban za a sanar dake. Kawai idan zamu dawo ki sake ciko jaka.’
‘Hmm!’
Suka sake yin shiru na dan lokaci, jimawa kadan Zahra tace
‘Ni abu daya ne yake bani haushi, duk inda naje sai ace wai mutuniyarki bazata tabu ba. Na rasa waye malaminta a garin nan da bamu san shi ba.’
Amina tace
‘To tunda dai an sami makarinta ba shike nan ba, duk ma wanda yake mata aiki su karata. Idan ta rabu da mijinki duk ma yanda tayi ba shikenan ba.’
‘hakane kam, a sauka lafiya.’
Sai daga baya suka sami masu rogo sun fito daga wani kauye, suka saya sukayi ta ci har suka rage yunwa.
Saida aka idar da Sallar Magriba sannan suka ajiye Zahra a gida suka wuce, a kan idan alhazai sun dawo zasu koma a gama aiki.
UWAR SADDIKU
Written by Sakina Yazid (Innar su Amal)
30
Tunda suka dawo daga Doguwa kuma sai Zahra ta cigaba da harkokinta cikin walwala, musamman da yake yanzu gidan yana hannunta. Abu daya ne kawai bata sami yanda take so ba; ta riga ta tsara yanda zata yi yawon Sallah a motar Abban, sai dai kawai ranar da zasu tafi da motar ya fita ya kaita gidan Yaya Bello ya ajiye a can sanna Ali ya wuce da su airport.
Da ya sanar da ita wannan tsarin nasa da wuri da tabbas ta hanashi don da ya saba tafiya ya bar motarsa a gidan, amma dai wannan zuwa Doguwa ya wanke mata duk wata damuwa.
Nan da nan ta cigaba da shirin babbar Sallah da lissafin yanda zata kasafta naman san da ya bari a yanka. __
Tunda suka isa kasa mai tsarki Aisha ta dukufa addu’a; duk abinda take so saida ta roka kuma ta yiwa Abbanta addu’a sosai.
Tare da Abba suke a hotel don haka ma bata sake tayi wata kawa ba tunda yawancin ibada ma tare suke zuwa, don haka ko kasuwa ma bata tunanin zuwa.
Saura kwana biyu arfa suna zaune ita da Abban sun gama cin abinci suna hutawa a dakinsu na otel suna dan taba hira . Kamar wadda aka tunawa ta dubeshi tace
‘Uhm, Dubai din zamu wuce ko Yallabai don ka ga shi yasa ba zan yi tsaraba a nan ba sai na je can.’
Ya harareta yana jijjiga kai
‘Wannan mata bata da mantuwa.’
Ta dan zaro ido
‘Da mijin zan manta ko kuwa da kaina?’
‘To zamu wuce kin ji dadi?’
Zumbur ta mike tsaye
‘Allah, dadi kai! Ai bari ma kaga nayi Sallah na yiwa Allah godiya tukunna.’
Sai da ta gama murnar ta tambayeshi nawa zata turo a kudinta da tace zata biya, yace ta turo dubu dari biyu account dinsa ya isa shi sai ya cika sauran.
Sai bayan ya nuna mata visa dinta sanna taga kwana bakwai yayi musu booking, ta ji dadi sosai don haka ta fasa duk wata sayayya ta mayar da hankali wajen ibada da kuma addu’a. …………
Tunda suka tafi Saudiyya kusan kullum wayoyin Abban suna kashe, sai lokacin da ya zaba sai ya kunna suyi waya ta Whatsapp don ya ji lafiyar iyali. Tayi mita har ta gaji, don haka ya zama kawai sai dai ta bar masa sako a WhatsApp idan ya gani sai ya kirawota.
Tunda suka tafi ya ke shawarar tafiya da Aisha Dubai kuma yake tunanin yanda zai yiwa Zahra bayani ya rasa. Bayan Sallah da kwana hudu ya kama ranar zasu wuce Dubai kuma har ranar bai gayawa Zahra ba.
Kaf suka shirya kayansu ana yin sallar Magriba suka bi jirgi sai Dubai.
Sai da suka sauka a hotel suka huta sannan ya bude data.
Yana bude data kuwa kiran Zahra ya shigo kamar tana jiransa, a lokacin Aisha tana wanka. Ya amsa wayar ya fice daga dakin, ya dawo falon kasa wato reception na hotel din ya sami kujera ya zauna.
Bayan sun gaisa ya tambayi yaran, duka suna kusa da ita don haka ta bashi suka gaisa da kowa har Saddiku. Bayan ta karbi wayar suka dan taba hira, jimawa kadan yace
‘Yauwa ban gaya miki ba na wuce Dubai din fa, itama Aishan muna tare da ita a nan din tare zamu dawo.’
A dan razane tace
‘Um ban gane ba. Kace ita nan gida zata wuto?’
‘Eh. Na canza shawara daga baya tunda itama ta biyawa kanta kudin zuwa Dubai din kawai sai muka wuce.’
‘Um, Allah ya bada sa’a.’
‘Amin.’
Yanda yaji muryarta ta canza nan take ya san da sauran bayani, ya san idan ta fara mita abun zai daukesu lokaci don haka nan take yayi mata sallama ya kashe wayar. …………
Kwanki biyun farko da sukayi a Dubai shi kadai yake fita tare da wanda aka hadashi don ya raka shi kamfanin da zai yi sayayya. Yana fita Aisha take komawa bacci, domin dama ta tara bacci a Saudiyya. Haka ya kwana biyu yana yawo ita kuma tana hutawa, don ko abinci har dakin ake kawo mata.
Sun riga sun gama magana da Aisha a kan ya saya mata waya in ya so ita kuma sai tayi tsaraba da kudinta; don haka fitarsu ta farko ya sayo mata Samsung hadaddiya mai tsadar gaske.
Suna komawa daki ta kasa hakura, saida ta kunna wayar nan. Suka hadu sukayi launching sabuwar waya. Wayar ta hadu sosai kuma camera tana fitar da hoto don haka sai ya zama duk inda suka je haka zasuyi ta hotuna.
Sun hutu kuma sun ji dadi domin Aisha zata iya cewa bata taba jin dadin zama da shi ba kamar a wannan lokacin. Shi kansa yaji dadin tahowa da ita saboda yanda take jiyar da shi dadi kuma tana saka shi walwala, don haka ya saki kudi sukayi ta yawo suna sayayya. Hotuna kuwa Allah ne kawai ya san yawan wadanda Aisha ta dauka a sabuwar wayarta; wasu a dakin otel, wasu a wajen cin abinci, wasu a wajen sayayya wasu ma a kan hanya kawai. Ko wanne kuma sai ta makale a jikinsa take dauka ko ta sami masu wucewa tace a daukesu.
Ranar da suka kwana uku a Dubai rana suka je wani club na larabawa, wajen an yi masa tsari ne kamar a Sahara. Sanna ga rakuma da dawakai birjiki duk wanda kake so shi zaka hau, kuma abinci kala kala na larabawa. Wajen yayi matukar burge Aisha.
Tunda suka shiga wajen suke daukan hotuna.
Bayan sun gama hutawa rana ta fadi tace zata hau doki, suka karasa aka hada musu doki. Ita bata iya doki sosai ba don haka da ta hau wani balarabe ya ja linzamin dokin suka zagaya.
Daga baya Abba yace ta dawo su hau doki daya don su zagaya sosai.
Nan da nan ta sauka ta koma kan dokin Abba; ta zauna a gabansa ya rungumeta ta baya sannan ya ja doki suka kama hanya. Suna tafiya sunata hira da dariya.
Saida suka zagaye wajen tas.
Bayan sun dawo wani balarabe ya nuna musu hotunansu da yayi ta dauka a camera dinsa wanda idan suna so biyanshi zasuyi sai ya tura musu. Nan take ta mararaicewa Abba ya biya aka tura hotunan wayarta.
A gajiye likis suka koma dakin sai dai zuciyarsu fari tas saboda wunin ranar yayi musu dadi.
Washegari Aisha tana bude Whatsapp taci karo da sakon Zahida na murya wato voice note, nan da nan ta bude tana saurara:
‘Wai mutum yana Dubai amma ba zai tura mana hotuna ba, to wallahi ni ko kasuwar garinmu naje sai na ishi duniya da hoto balle na hau jirgi na keta hazo. Ko da yake ma Yusuf din zan tambaya nake bata lokaci.’
Saida ta gama dariya sannan ta zabi hotunansu wajen kala goma ta tura mata. Ta cigaba da dube-dubenta a waya. _
Duk da bacin ran da take ciki na tafiyar da yayi da Aisha Dubai bata fasa shirin tarbarsa ba kamar yanda ta saba; maganar Dubai ma ta riga ta bawa zuciyarta hakuri. Kawai dai ta yiwa kanta alkawarin ko da tsiya ko da tsiya-tsiya idan zai kuma fita kasar nan ko ina ne sai ya je da ita.
Hajja ta kawo mata kayan mata wadanda cikinsu harda na mallaka, duk ta fara amfani ma da su. Sai dai jiya da suka yi waya da Amina ta sanar da ita akwai wasu kaya da aka kawo mata daga Nijar, idan ta tashi daga office zata kawo mata su lallai ta gwada don ta bata tabbacin sai sun sa mata mutum sambatu.
Wadannan kayan kawai take jira tunda jibi zasu dawo.
……….
Ma’aikatar kudi ta jiha ne inda Amina take aiki. Su biyu ne a office dinta ita da abokiyar aikinta sai dai kowacce da teburinta. Daga gefe guda kuma akwai kafet karami wanda nan ne suke Sallah ko kuma su dan mike idan suna hutawa.
Yau ma a nan suke zaune, ita Amina tana rubuce-rubucenta yayinda Hadiza ke ta faman kalle-kalle a waya.
Sunayi suna hira jefi-jefi.
Hadiza ce ta budo wani status a wayarta tana kalla tana murmushi, can kuma a fili tace
‘To Amin, muma Allah ya kaimu wannan sharholiya.’
Amina tace
‘Keda wa?’
Ta dan matso tana nuna mata abinda ta gani a wayarta; mata da mije ne a kan doki yana rungume da matar suna ta dariya, ita kuma matar tana rike da kofi me straw tana zukar wani abu daga ciki. Yana wucewa wani ya fado suna tsaye ya rungumeta nan ma dariyar suke, shi yana sanye da kananan kaya ita kuma tana sanye da abaya. Bayan ya wuce wani ya fado yana kwance a kan yashin ita kuma ta tada Kai da bayansa tana ta dube-dube a wayarta. A kasan hoton karshe an rubuta “sharholiya made in Dubai. Allah ya maimaita mana.” Wani status din ya fara budowa Aminan tace
‘don Allah mayar dashi na kara gani; matar kika sani ko mijin?’
Tayi ‘yar dariya
‘Wallahi babu ko daya. Ina jin a group ma fa muka hadu da matar nan kuma fa ban san ko itace a hoton ba ko ‘yaruwarta ce don bamu taba haduwa ba sai dai a group. Kawai dai sun burgeni.’
‘Sunanta Aisha ko?’
‘Gaskiya a’a, sunanta Zahida M. K don haka take sawa a WhatsApp name dinta.’
‘To wannan ta hoton dai sunanta Aisha kuma kishiyar kawata ce don hotunan nan ma hada baki sukayi da mijin ya tafi da ita suka bar Uwar gidan a nan tana fama da yara.’
Ta zaro ido
‘Ke Amina?’
‘Wallahi kuwa, wannan tafiyar ta munafunci ce. Uwargidansa ya rainawa hankali don maganar da nake miki ma suna can sai jibi yace mata zasu dawo.’
‘Kai kawata maza ‘yan bura uba ne! Wato Uwargida jakar gida an barta a gida an tafi da amarya Dubai sharholiya. Kai Allah ya shiga tsakaninmu da irin wadannan kishiyoyin, ki gama wahala da miji a zo a nuna miki iyawa.’
A nan ta saka Hadizan ta tura mata hotunan wayarta tunda dama idan ta tashi daga office din gidan Uwar Sadikun zataje.
Tunda taga hotunan nan ta kasa zama a office din, sosai ranta ya baci don tana taya Amina jin zafin wannan tafiyar da aka yi babu ita. Taci sa'a ana yin sallar azahar ogansu ya fice daga office din don haka itama ta fice ta nufi gidan Zahra.
A falo ta sameta tana hutawa yayinda Jummai take aikace-aikacenta da goyon Sumayya. Kafin su gaisa ta jata falon sama, bayan sun zauna ta ajiye mata ruwan sanyi da lemo. Suna gama gaisawa Zahra tace
‘Wai ya na ganki kamar a fusace ne, ina dai fatan kin taho min da tsumin?’
‘Na taho miki da shi. Wani abun takaici na gani wallahi. Ni wai ba cewa kikayi kwana biyu Abban Sadik zai yi a Dubai bane?’
Ta tabe baki ta kawar da kai
‘Haka yace. Amma ai daga baya na gaya miki ya tafi da amaryarsa wai wani idan ya dawo naji bayani, don haka yanzu kwana bakwai zasuyi shine sai jibi zasu dawo. Ai duk wannan shirin da nake yi sai ya ji daga gareni don wallahi ina binsa bashin zuwa Dubai.’
‘Hmmmn! Sai ma kinga abinda na gani sannan zaki tabbatar kina binsa bashi. Yana can suna ta sharholiya shi da kanwarki baki gani ba kamar wasu saurayi da budurwa.’
Ta budo wayarta ta nuna mata hotunan da Hadiza ta tura mata; tana kalla tana jijjiga kai zuciyarta tana zafi saboda takaici.
‘Ni zai rainawa hankali! Sai yanzu ma na gane babu wani business da yaje yi wallahi kawai hutawa ya dauki amaryarsa ya tafi ya barni a nan da yaransa. Tunda mutumin nan ya tsara tafiya Hajjin da matar nan na san ya shirya raina min hankali wallahi. Kawai daga kara aure mutum ya zama wani karamin munafiki, komai zai yi sai boye-boye? Kin san ko Hajjin ma ban san yana shirin tafiya ba sai da ya zama saura sati daya su tafi ya sanar da ni.’
Ta dafa cinyarta
‘Kada ki damu kawata na karshe sukeyi, wannan hotunan ma gani nayi kamar kin yarda da zancensa shi yasa nace sai na nuna miki. Amma kada ki wani damu da sun dawo za ayi maganinsu.’
‘Hmmmn!’
Nan suka cigaba da hirarrakinsu, daga baya ta bata tsumin da ta kawo mata sukayi sallama ta tafi ta barta tana takaicin hotunan.
Hotonsu a kan dokin nan yayi matukar tsaya mata a rai don ita bata ma taba sanin Abban ya iya hawa doki ba. __
Jirgin safe suka biyo don haka wajen sha daya na safe suka sauka a gida Nigeria. Malam Ali yana jiransu a airport don haka nan da nan suka gama clearance suka dauki kayansu gaba daya aka zuba a mota suka kamo hanyar gida. Suna shiga unguwar Abba yace ya kai su gidan Aisha don haka can ya kaisu suka sauka ya sauke musu kayan gaba daya. Duk da gidan ya dan yi kura amma haka Abban ya tayata suka karkade dakinsa yayi wanka ya canza kaya sannan ya fito ya nufi wajen Mommy. ……….
Tunda Malam Ali ya shiga dasu gidan Aisha yara suka kai mata labarin Abba ya dawo yana gidan Anti; bata yi zaton haka ba don ta zata a gidanta zai sauke jakar tsarabarsa amma duk da haka sai ta daure. Ta tare yaran gaba daya ta hanasu fita don so take tayi kamar bata san ya dawo ba. Sai dai kafin ya gama wanka ya zo ranta har ya gama baci; kenan wani abun ya tsaya yi a wajen Aisha.
Tana zaune a falon sama tana ta faman cika tana batsewa ta jiyo yara suna ta murnanr dawowarsa bayan da ya shigo gidan. Sai da ya gama hirarsa da yara ya rarraba musu chocolate din da ya riko sannan ya hau saman ya sameta.
Da kyar ta daure ta amsa sallamarsa; ya fahimci damuwarta saboda dama tun lokacin da yace mata ga su a Dubai shi da Aisha ta daina kiransa a waya sai dai shi ya kirawo, Kuma da ya kirawo sai ta hadashi da yaran. Don haka ya shiryawa duk wata rigimarta.
Bayan sun gaisa ya tambayeta gida da yara ta tashi ta dauko kunun aya ta ajiye ta cika masa kofi, ta koma ta zauna a inda ta tashi kusa da shi. Sai da ya kwankwade kunun ayan ya ajiye kofin sannan ya dubi fuskarta.
Sai cika take tana batsewa tana ta faman harare-harare. Ya mike tsaye yana magana cikin halin ko in kula
‘To ni bari na koma dama akwai inda za mu dan……….’
A fusace ta mike tana harare-harare
‘Ban gane ka koma ba, ina kenan kuma? Shikenan mu…'
Ya kama hannunta wanda ya sha kunshi yayinda ta kara shan kuna, yayi taku daya ya matso gabanta sosai yace
‘To ai na ga kamar baki ji dadin dawowata bane shi yasa da zan dan koma na baki waje ko.’
Ta murgude bake zatayi magana, kafin ta bude baki ya sumbaci lebenta yayi dariya
‘Allah ya nuna min ranar da za a daina murgude min bakin nan na rashin kunya.’
Ta zumburo baki, ya sa hannu ya kara janyota jikinsa. Duk wata tsiwa da ta haddace zatayi ya goge mata haddarta, haushinsa take ji amma ta kasa ture shi. Yace
‘Na san dai kinyi kewata da yawa, to ba gani na dawo ba kuma shikenan sai a tare ni da murguda baki sai kace wani wanda bashi da galihu. Ai dole na koma tunda dama jakata a kulle take idan kika shirya sai na dawo.’
Shiru kawai tayi ta kwanta a kirjinsa ya rungumeta yana shafa bayanta. Tayi kewarsa kamar yanda shima yayi kewarta. Suna nan a tsaye suka ji motsin hawowa saman wanda kana ji ka san Ummi ne da Sumayya. Tayi gyaran murya ta dan ja baya don ta tabbatar shi ba sakinta zaiyi ba, tace
‘Yara fa suna nan.’
Ya ja baya ya koma ya zauna.
Nan ya zauna suka cigaba da hirarrakinsu shi da ita da Yara.
Jimawa kadan ya mike zai shiga daki, yace