Kenza eBookz

Uwar sadiku complete - Chapter 34

Uwar sadiku complete - Chapter 34

Uwar sadiku complete Chapter 34: Uwar sadiku complete Chapter 34. Kafin ta gama fadin abinda tayi niyya Rukayya ta dage iya karfinta ta tunkudata. Ta tafi…

4,483 words

Kafin ta gama fadin abinda tayi niyya Rukayya ta dage iya karfinta ta tunkudata. Ta tafi taga-taga, saura kadan ta kai kasa ta dafe kofar dakin ta tsaya tana kallon Rukayyan da mamaki. Cikin kunan rai tace

‘Kan bala'i, wato saboda matar nan ta gama dake ni kike turewa saboda baki da kunya kuma kinga babu idon Mommy ko?’

A fusace ta nufo ta yayinda ita kuma Rukayya take tsaye ta nade hannuwanta a kirjinta tana fadin

'Babu ruwanki da ni Yusra, fita a harkata! Zan je na tambayi Abban idan yace kada naje sai na fasa amma ke baki is…’

Kafin ta rufe bakinta Yusran ta dauke ta da mari. A take ta dafe kumatunta tana huci, kafin tayi wani tunani ta zare hannu itama ta gaurawa Yusran mari.

Da gudu Ummi ta fice tana kuka ta haye sama don ta kirawo Abba. Yusran ta cakumo wuyan hijabin Rukayya, cikin zafin nama Rukayyan ta fisge ta tunkede Yusran wadda ta fadi kasa, ba tare da bata lokaci ba Rukayyan ta bita kasa ta haye kan ruwan cikinta tana ta kai mata duka ko ta ina; duk wani bacin rai da Yusran ta dade tana cuzguna mata da shi tun kafin rasuwar Mommy ya dinga dawo mata don haka ta rufe ido tana ta faman kai mata duka. Ganin abun yayi yawa yasa Yusran ta fara ihu tana kokarin ture Rukayyan daga kan cikinta wanda ya gagara, kamar ma karawa Rukayyan karfi takeyi. A dai-dai nan Abba ya banko kofar ya shigo Ummi da Sumayya suna biye da shi. Da karfi ya fincike Rukayya daga kan Yusra wadda idonta ya rufe, ta fizge daga rikon da Abban yayi mata tana huci. Ba tare da bata lokaci ba ya gaura mata mari wanda ya dawo da ita hayyacinta ta dafe kumatun tana kallonsu shi da Yusran tana fitar da hawaye masu zafi.

Da gudu Sumayya ta fice ta nufi bayan gida inda Jummai da Nana suke wanki don ta kirawosu.

Abban ya tsuguna a kan Yusran ya kamata ta mike tsaye yana nuna Rukayya yana fadin

‘Wannan wane irin rashin hankali ne Rukayya, yayarki kikewa wannan dukan kamar kin sami wata jaka?’

Ta sunkuyar da kai hawayenta yana diga yayinda Abban ya tallafi kafadar Yusran yana kokarin zaunar da ita a kan gado yana duba fuskarta inda bakinta ya fashe yake fitar da jini.

'Baki da hankali Rukayya? Kalli yanda kika ji mata ciwo. Fice kije dakina ki jirani kuma ki daina wannan kukan don sai jikinki ya gaya miki.’

Ya zaunar da Yusran a gefen gado yana share mata hawaye yayinda Rukayya ta ja kafa ta fito daga dakin. Tana fitowa taci karo da Saddiku yana shirin shiga dakin wanda shigowarsa gidan kenan yana dauke da jakar computer dinsa. Ya sha gabanta ya dafa kafadarta da mamaki a fuskarsa yana tambaya

'Rukayya me ya sameki?’

A nan Jummai ta shigo da gudu Nana da Sumayya suna biye da da ita, suka tsaya a inda suka ga Saddikun yana tambaya. Sumayya ce ta bashi amsa tace

'Fada sukeyi ita da Yaya Yusra shine Yaya Rukayyan ta zane Yaya Yusran.’

A nan Rukayya ta fada jikin Saddikun ta fashe da kuka, ya dafa bayanta yana bata hakuri.

Jummai ta wuce shi ta shige dakin, ta tsuguna a gaban Abban tana fadin

'Subhanallahi. Muna can ni da Nana muna wankin uniform ashe fada suke yi haka. Yaya me kika gayawa kanwarki ya fusata ta haka? bari na samo ruwa a wanke bakin.’

Abban yace

'Yauwa wanke mata, ina zuwa.’

Yana fitowa yaci karo da Saddiku yana bawa Rukayya hakuri, ya dubesu yace

'Ba ce miki nayi kije dakina ki jirani ba, mara kunya fitsararriya?!

Ya maida dubansa ga Saddikun yace

'Ka kyaleni da ita ka shiga kaga yanda ta kama ‘yar uwarta da duka sai kace mara hankali.’

Cikin damuwa Saddikun yace

'Abba Yusra ce fa bata da gaskiya.’

Abban ya harareshi yace

'Gafara ka bani waje Malam, ka ga abinda ya faru ne zaka ce Yusra ce bata da gaskiya. Ka shiga ka ga yanda ta yiwa Yusran duka. Wuce kije ki jirani a saman.’

Ta ja kafa ta wuce saman tana shesshekar kuka, shi kuma Saddiku ya wuce dakinsa.

A hankali Abban ya ja kafa ya karasa kan dining a table din kasan ya zauna ya dafe kai, wannan wacce irin musiba ce? Yaran da basu taba yin wani fada irin wannan ba? Me yasa Aisha tayi masa haka? Da tana gidan nan ai da hakan ba zata faru ba. Jummai ta fito daga dakin ta sameshi a zaune, ta rage tsawo tace

'An wanke fuskar Alhaji, ciwon ma ai baiyi tsananin ba. Yarinta ce take damunsu, gashi Yaya ta iya tsokana. A yi hakuri a yiwa Rukayyan a hankali.’

Kai kawai ya daga mata ta tashi ta wuce kicin tana rike da hannun Sumayya. Jimawa kadan shima ya tashi ya haye saman zuciyarsa a jagule. UWAR SADDIKU

Written by Sakina Yazid (Innar su Amal)

43

Ba a jima da idar da sallar Magriba ba ta tsaya a bakin gate din gidan, ta matsa horn don ta san Abdallah yana nan. Kafin ta danna na biyun ya leko, yana ganinta ya koma da murna ya bude gate din. Ba tare da bata lokaci ba ta tura motar cikin farfajiyar gida, ta sami guri a cikin garejin gidan ta ajiye motar ta yanda duk wanda ya kalla ya san motar a nan zata kwana.

Tana fitowa daga motar ta mikawa Abdallah mukullin motar ta nuna masa akwati a bayan motar tace shi kadai zai dauko ya bar sauran kayan sai daga baya.

Kamar mara gaskiya ta shiga gidan da sallama, Hajiya, Anti Uwani da Farha suna zaune a falon. Da gudu Farha ta mike daga kusa da Anti Uwani ta rungume Mamanta tana mata sannu da zuwa. Kafin ta gama amsawa Abdallah ya shigo da akwatin ya nufi dakin Anti Uwani da shi. Itama Farha ta dubi Aishan tana murmushi tace

'Mama kwana zakiyi na kai miki jakar dakinmu ko?’

Ta daga mata kai a take ta bi bayan Abdallah.

Ta karasa cikin falon ta zauna a kan kafet daga gefen Hajiya wadda take zaune kafafunta a mike. Ta gaida Hajiya sannan ta juya ta gaida Anti Uwani. Hajiya ta dubeta fuskarta da alamar tambaya tace

'Lafiya dai da magribar nan kuma naga ana kwana zaki yi kina daga kai?’

Ta danyi murmushin yake ta kawar da kai saboda yanda kallon da su biyun suke binta da shi yake saka ta jin kamar wata mai laifi. Tace

'Kwana zan yi Hajiya, sai gobe zan tafi.’

Cike da mamaki Anti Uwani tace

'Ikon Allah! To wa kika barowa gidan da yaran?’

'Suna can Anti, ai akwai mutane a gidan.’

Ta mike da hanzari tana fadin

'Bari naje nayi sallah, ko magriba ban yi ba ga shi nan har an fara kiran isha'i.’

Ba tare da ta saurari abinda zasu fada ba ta bar wajen da sauri ta shige dakin da yaran suka shiga da kayanta.

Hajiya ta dubi Anti Uwani tace

'Kin ga yarinya don Allah, guduwa fa ta yi. Tabbas wannan zuwan nata akwai dalili.’

Anti Uwani tace

'Barni da ita, bari ta idar da sallar na ji abinda ya kawota.’

Har aka ci abinci akayi sallar isha'i tana daki, babu wanda ya nemeta. Sai dai Anti Uwani ta zuba abinci ta bawa Farha ta kai mata daki. Da yake tana tattare da yunwa ta dan taba tuwo, ta mayar ta rufe kwanukan ta wanke hannunta a bandakin da yake cikin dakin sannan ta dawo ta kashingide a gafen gadon Anti Uwani.

Bata dade da zama ba Anti Uwani ta turo kofa ta shigo dakin, bayan Aishan ta amsa sallamarta ta wuce ta zauna a gefen gadon yayinda Aishan ta gyara zama ta janye kafafunta. Bayan Anti Uwanin ta zauna ta dubi Aishan, suna hada ido ta sunkuyar da kanta yayinda Anti Uwani tayi murmushi. Tace

‘Kya ji kunya mana Shatu! To ya aka yi? Don dai wannan zuwan na san ba na lafiya bane.’

Sukayi shiru na dan lokaci, Anti Uwani tana sauraronta ita kuma tana kallon hannunta tana tunanin ta inda zata fara. Jimawa kadan ta gaji da yanda Anti Uwanin ke kallo da sauraronta ta bude baki da kyar tace

'Cewa yayi idan na zauna a gidan zaman kaina nakeyi, shine na taho.’

Mamakin Anti Uwani ya karu, ta gyara zama tace

'Ban fahimceki ba fa, Yusufan ne yace zaman kan ki kikeyi ko kuwa? Kiyi min bayani yanda zan gane.’

Ta dan muskuta ta fara yiwa Anti bayanin abinda ya faru a kan umarnin da ya bata ta koma gidan yaransa har zuwa inda yace idan bata koma ba zaman kanta takeyi ba zamansa ba. Ta kara da

'Shine na taho.’

Mamakin Anti Uwani ya sake karuwa, domin duk wannan bayanin da Aishan ta dauki lokaci tana yi kara kulle mata kai kawai tayi; ta kasa gane dalilin da ya sa ita Aishan ba zata koma wajen yaran nasa ba. Tace

‘A’a! To ai dole yace zaman kanki kikeyi Aisha, matar nan ta mutu fa me ya sa ba zaki bi umarninsa ki koma gidan ki kular masa da yaran ba? Wannan ai kowa ma ya san haka ce zata kasance.’

Nan ta fayyacewa Anti Uwani dalilan da suka saka ba zata rike masa Yusra da Nana ba, ta bata misalan wasu daga cikin abubuwan da Yusran ta yi mata.

Suka yi shiru na dan lokaci, Anti Uwani tace 'Kina da gaskiya Aisha, to amma fa gaskiya bana jin akwai wanda zai saurareki. Kowa cewa zai yi yarinya ce in an tsawatar mata zata daina; amma ni na fahimceki sosai. Rayuwa ce mutum zai yi ta yi rigima daga wannan sai wannan, kuma tsakaninki da miji kullum sai fitna.’

'To ai shine. Kuma ni Allah bai dora min zama da yaransa ba, ya kai su dangi uwarsu ko kuma ya auro wata ta rike masa su amma ba ni ba. Kinga ni uwarsu musamman take koya musu tsanata don haka zai yi wahala a sami wanda zai saukesu daga kan koyarwar uwarsu, amma kinga idan wata ya aura watakila su bata dama ta zauna da su.’

‘Hakane Shatu. Amma fa gaskiya duk bayanin nan naki babu wanda zai fahimceki fa don ina jin ko Hajiya ba zata saurareki ba. Ina ga gara kiyi hakuri ki koma in ya so a zauna da Yusufan ya tsawatarwa yarinyar watakila ki ga abun ya zo da sauki.’

Ta share kwalla sannan tace

'Wallahi Anti Uwani ba zai tsawatar mata ba, kuma ko ya tsawatar mata babu abinda zata fasa tunda yaran sun saba ba sa jin magabarsa. Ba zan iya rayuwa da wannan yarinyar ba wallahi don idan ta kasheni nawa marayun yaran ta cuta shi ubanta wata zai auro su cigaba da rayuwarsu. Idan kuma bata kasheni ba to in ta kureni nace zan dauki mataki a kanta wallahi kowa ba zai ji dadi ba tunda ai duk muguntarsu nima na iya Allah ne yake katangeni.’

Sukayi shiru na dan lokaci. Abun ya sha kan Anti Uwani sai dai ta san babu wanda zai fahimcesu. Ita ta san irin wadannan yaran don ta zauna da su, don daya har bayan an yi mata aure ma haka ta dinga zuwa cikin gidan tana haddasa fitna a karshe sai da ubanta ya saki Anti Uwani a kan laifin da ba nata ba. Ta muskuta tace

'Hmm! To yanzu ya za ayi Aisha?’

'Su Baffa suyi masa magana, idan ya dauke Yusra da Nana bani da matsala da sauran yaransa, ko dan shege ya bani kuma zan rike masa da amana. Amma idan dai aka ce sai na zauna da Yusra to gaskiya na hakura da aurensa.’

'A'a abun ma ba zai kai haka ba in sha Allah. Amma dai ina kokonton yiwuwar abinda kike so domin su fa maza gani suke kamar tunda suka aureki to ko me suka rakito dole ki zauna da shi. Iyayenku ma kuma goya masa baya zasuyi. Kuma daga baya idan ta kashe miki auren a cigaba da zaginki.’

'Duk ma abinda zasuyi sai dai suyi don wallahi Anti Uwani idan aka ce sai na zauna da yarinyar nan zaku nemeni ku rasa ba zaku sake gani na ba.’

Ta bata rai tana harara Aishan tace

'Bana son rashin hankali, kada na sake jin wannan zancen kin ji na gaya miki. Ki ci gaba da addu'a in sha Allah za a sami maslaha.'

Sukayi shiru na dan lokaci kowa da abinda yake tunani, jimawa kadan Anti Uwani ta tashi ta fice ta koma dakin Hajiya; inda ta tarar Farha har tayi bacci yayinda Hajiyan take zaune a kan dadduma inda ta idar da shafa'i da witri.

Nan ta zauna ta bawa Hajiya labarin abinda Aishan ta gaya mata. Cike ta mamaki da takaici Hajiya tace

'Kin ji ko Uwani, na gaya miki yarinyar nan fa bata da hankali har yanzu. Ya za ayi kina matsayin matar mutum kuma kice yaransa marayu sai kin zabi wadanda zaki rike masa?’

'To Yaya ai tayi mutunci ma tunda ita nata marayun ko daya bai zaba ba balle ya taya ta rikonsu.’

Ta harareta

'Kinga Uwani ki daina tunzura yarinyar nan fa. Ke da baki taba haihuwar nan ba ba kin zauna da ‘yayan kishiyoyin ba kala-kala, me ya kasheki? Duk sharrinsu ba haka suka hakura suka barki ba?’

Ta kawar da kai

'Na hakura na barsu dai Yaya bayan sun sa ubansu ya kore ni. Kuma zama da su din ai rayuwa ce wadda na cikin gidan yari ya fi ka ‘yanci kuma ko makiyi na bana yiwa fatan irin wannan rayuwar Yaya.'

Suka yi shiru na dan lokaci. Hajiya bata so ta tunawa Anti Uwani tata rayuwar ba don ta san tabbasa ta sha wahala a hannun yaran kishiyoyi domin ita din Allah bai taba bata haihuwa ba. Kuma haka Allah ya hada ta da mijin da ya dinga auren mata suna haifa masa yara yana sakinsu, kusan duka yaran ita ta rikesu. Duk wata fitnarsu haka zai muttsike ido yace itace bata san ciwon yara ba don bata haifa ba, haka tayi wannan rayuwar kuma daga karshe ya saketa a kan laifin da ba nata ba. Sai daga baya kafin rasuwarsa ya dinga kokarin mayar da aurenta ita kuma a lokacin ko sauraronsa bata yi ba.

Anti Uwani tace

'Idan gari ya waye zan gayawa Abubakar ya sanar da Baffansu; ai tayi mutunci ma tunda ba duka yaran tace ba zata rike ba. Tunda na bude ido nake zuwa islamiyya har yau ban daina zuwa ba kuma ban taba ji a cikin karatu an karanta aya ko hadisin da yace dole idan kina auren mutum ki rike masa yaran da baki haifa ba, hasali ma har aka gama bayanin masu riko babu matar uba a ciki to na me za ace sai ta yi? Idan yana so ta rike masa su kuma ai matarsa ce sai yayi amfani da dabara ya lallabata ba wai ya nuna mata isa ba. Kuma idan sun sabauta Aishan ai yaranta suka cuta da mu da muka haifeta, tunda shi ubansu aure zai kara ya cigaba da rayuwarsa.’

Cikin sanyin jiki Hajiya ta dafa hannun Anti Uwani tace

'Hakane. Bari dai gari ya waye Baffa yazo, idan aka bi abun a hankali za a sami mafita in sha Allah.'

Jimawa kadan Anti Uwani tayi mata sai da safe ta tashi ta koma daki; dukansu zuciyoyinsu babu dadi. Ita Hajiya ba da son ranta ta tunawa Anti Uwani tata rayuwar auren ba wadda take cike da jarrabawa kala-kala ga rashin haihuwa, ita kuma Anti Uwani abubuwan da suka faru da ita suna dawo mata tana tunani babu yanda za ayi ta bari Aisha ta shiga irin rayuwar da ita tayi.

Haka suka kwanta bacci kowa da abinda yake ransa.

Rayuwar auren Anti Uwani ce gaba daya ta dinga dawo mata; abubuwan da tace ba zata sake tunawa da su ba balle su sa mata damuwa amma yau sun hanata bacci. Shekaru kusan talatin tayi a gidan miji amma iya shekarar farko ne kawai zata ce tayi a nutse. Tunda ta shekara bata haihu ba dangin miji suka fara takura mata, tun baya biye musu har shima ya fara damuwa. Kuma babu wanda ya taba cewa taje asibiti sai dai ayi ta bata tsimi tana shanyewa, haka tayi ta shan rubutu da tsimi wani daga gidansu wani kuma daga wajen dangin mijin. Ga kuruciya a tare da ita don bata fi shekaru Sha biyar ba a lokacin. Shekara uku a gidansa ya kara aure; yarinyar kuwa tana tarewa ta sami ciki. Haka aka mayar da Anti Uwani kamar mai aiki a gidan; kwashe amai, wanki, girki duk itace idan kuma dare yayi maigidan yace wajen amarya zai kwana kada wani abu ya sameta. A haka cikin damuwa da hantara suka cigaba da zama da matar nan har ta haifa masa yara biyar duka mata, daga baya ya saketa ya kwace yaransa tunda dama ko da uwarsu tana nan ma duk wata hidimarsu da ta gida Anti Uwani ce take yi. Bayan ita ya auro wata wadda ita kuma tana shigowacta haifa masa yara biyu maza. Haka Anti Uwani ta cigaba da bauta mata saboda da zarar ta ki yin wani abu sai maigidan yace tana bakin ciki don Allah bai bata haihuwa ba. Daga karshe tana zaune a tsakar gidan tana hura wuta zata dora abinci yayinda amaryar gidan take janyowa maigidan ruwan wanka a rijiyar tsakar gidan karamin yaron gidan mai shekaru kamar bakwai yayiwo tsokana ya shigo gidan da gudu basuyi aune ba sai ji sukayi ya fada rijiyar nan. Nan take uwarsa tace Uwani tana kallonsa ya fada rijiyar bata rikeshi ba. Shi kuma maigidan yace idan dai yaron ya mutu to ya saki Uwani saki uku. Da kyar aka dauko gawar yaron daga rijiyar inda a nan take maigidan ya kora Uwani gida. Bayan wanna kuma ta auri wani mutum wanda shi kuma lafiya suka zauna don shi bai hadata da iyalansa ba ma suna gari da ban da ban, shekara tara da aurensu Allah ya karbi rayuwarsa. A nan wancan ya dawo cikin zawarawa ita kuma tace gaba daya ma ta gama aure a duniya tunda ko babu komai a lokacin ta tsufa.

Da kyar bacci ya kwasheta tana tuna rayuwarta ta baya kamar mai kallon fim.

—----

Bai san tsawon lokacin da ya dauka a zaune a kan dining table din ba, gajiya kawai yayi da zaman ya tashi jikinsa babu kwari ya hau saman. Kai tsaye dakinsa ya wuce, yana shiga ya zauna a gefen gadon ya dafe kansa da hannuwansa. Motsin da ya jiyo daga daya gefen gadan shine ya janyo hankalinsa, ya sauke hannuwansa ya kalli bangaren da ya jiyo motsin. Rukayya ce a takure a kasa daga gefen gadon ta hada kai da gwiwa; sai a lokacin ya tuna shi ya ce tazo ta jirashi a daki.

'Rukayya.' Ya kirawo sunanta.

Ba tare da ta dago kai ta dubeshi ba ta amsa a gajarce

'Um.'

'Taso ki zo nan.’

Ta taso tana goge fuskarta wadda tayi ja gaba daya saboda kuka; duk da zuwa yanzu babu hawaye a fuskarta. Ta zagayo ta dawo gabansa ta tsuguna tana kallon kasa. Ya kare mata kallo na dan lokaci cikin damuwa, ya mika hannuwansa ya kamo nata hannuwan wadanda suke ajiye a kan gwiwarta ya rike tafukan hannunta a cikin nasa ya sake kiran sunanta. Ta amsa a gajarce tare da daga Ido ta kalleshi ta mayar da idonta kasa. Yace

‘Me ya hadaki da Yayarki kuke fada haka?’

Kafin ta amsa ya cigaba

'Kin san bana son karya don haka gaskiya zaki gaya min.’

Cikin sanyin murya tana kokarin danne hawayen da yake shirin kwace mata tace

'Cewa tayi bana son Mommy.'

'Ba kya son Mommy? Yusran ce tace haka?’

Kai kawai ta daga masa alamar eh.

'To me ya sa zata ce ba kya son Mommy?’

'Saboda zamu je gidan Anti Aisha ni da Ummi?’

Ya saki hannuwan nata yana jijjiga kai yace

'Ban gane ba Rukayya, kiyi min bayani sosai. Me ya hadaku fada? Me yasa don zaki je gidan Anti Aisha za a ce ba kya son Mommynki?’

Sukayi shiru na dan lokaci, shi yana sauraronta yayinda ita kuma take tunanin yanda zata yi masa bayani ba tare da ta fadi laifin Mommy ba. Shirun ya dan tsawaita kuma ta san ita yake jira tace wani abu, ta share kwalla daga idonta sannan ta fara yi masa bayanin abinda ya faru har ya sa suka fara fadan. Bayan ya gama sauraronta yace

'To zuwa gidan Antin ne ya zama yiwa Mommy rashin biyayya ko kuwa wa yace mata zaki sake uwa ne?’

Bata son yanda yake turata kan bayanan da zasu shigo da Mommy cikin maganar amma ta san dole ta bashi amsa. Ta kosa da tsugunon sannan kuma bata son maganar, haka ta sake share kwalla ta cigaba da bayani.

Tayi masa bayanin yanda Mommy ta hanata zuwa gidan tunda ya auro Aishan sannan tace

'Kuma yanzun ma ba zama zanyi ba, zuwa zanyi na gani ko akwai kayan da zan tayata kwasowa tunda ka ce mana zata dawo shine ita kuma ta fara gaya min maganganu.’

Yayi shiru na dan lokaci yana so ya hada zantukan gaba daya ya basu ma'ana, sai dai kansa gaba daya ya cushe sai sara masa yake. Da kyar ya daga kwayar idonsa ya kalli Rukayyan saboda yanda duk wani motsi na kwayar idon nasa yake kara masa ciwon kai. Yace

'To kiyi hakuri, idan kin je gidan Aisha ba yana nufin zaki sake uwa bane don babu wanda yake iya sake uwa, sai dai Aishan itama uwarku ce gaba daya tunda kinga yanzu nan zata dawo ta dinga kula da ku. Amma bana son ki sake yiwa wani irin dukan da kika yiwa yayarki, rashin hankali ne zaki iya jiwa mutum ciwo.’

'To Abba.'

'Tashi kije, kada ki sake kulata kuyi wani fadan idan ta yi miki wani abu ki zo ki gaya min ko ki gayawa yayanku.’

'To.'

Har ta kama hannun kofar zata bude ya sake kiran sunanta, don haka ta dawo ta tsuguna daga gefe. Yace

‘Akwai wani abu da Anti Aishan takeyi ne wanda yasa Mommy din bata son kuje wajenta?’

'Wallahi Abba babu wani abu, haka kawai ne sai Mommy din taga kamar Antin zata cutar damu kuma wallahi ba haka bane. Ita kuma Yaya Yusra sai ta dinga zugata ba zata bata hakuri ba.’

Ya jijjiga kai ya sallami Rukayya wadda ta fito daga dakin ta rufe masa kofa.

Gaba daya kansa ya kulle; tabbas ya san Zahra bata son Aisha kuma ya san akwai lokutan da take hana Rukayya zuwa gidan amma bai san abun ya kai haka ba. To ko shi yasa Aishan tace ba zata zauna da Yusra ba? Watakila wani abune na kiyayya da Yusran take bayyanawa Aishan yasa take jin ba zata iya zama da ita ba. To amma ai babu inda zai kai Yusra don haka dole Aishan tayi hakuri ta zauna da yaran gaba daya. Zai yi magana da Yusran zuwa da safe kuma zai sakata a gaba suje ta bawa Aishan hakuri in yaso ma sai ta tayata kwaso kayanta kafin su Rukayyan su dawo makaranta ta dawo gidan.

Sarawar da kansa yakeyi tayi yawa don haka ya mike ya matsa gaban karamin fridge din da yake dakin ya bude ya dauki ruwa sannan ya koma gaban mudubi ya dauki Panadol ya hadiya. Ya shiga bandaki ya yiwo alwala da nufin yayi sallar Magriba wadda bai yi ba ya tsaya rabon fada gashi har ana kiran isha'i; sai dai yanda yaji da ya fito ya tabbatar ba zai iya yin sallar a lokacin ba. Don haka ya kwanta a gefen gadon ya dafe kai tare da rufe idanuwansa.

……. Washegari da wuri ya tashi duk da kasancewar ranar asabar ce. Karfe bakwai na safe ya sauko daga saman, yaran gaba daya suna kan dining table suna cin abinci domin akwai tahafiz wadda karfe takwas saura kwata ake shiga. Yusra ce kawai wadda bata tashi daga bacci ba bata wajen amma har Saddiku ma yana zaune. Bayan ya amsa gaisuwar su ya tambayesu Yusra inda suka tabbatar masa bata tashi daga bacci ba. Surutunsu ya sa Jummai ta fito daga kicin inda take aiki, ta tsuguna ta gaisheshi. Bayan ya amsa ya koma ya haye saman inda Rukayya ta bi bayansa da abincin safen sa ta ajiye masa a table din saman ta sauko.

Ya shige dakinsa ya kashingide a kan gado ya fada tunani; tabbas yana bukatar mace a gidan don da ace da mace a gidan wadda ba ‘yar aikin gidan ba da ya san yanzu yana bacci amma dole ta sa kullum sai ya tashi ya tabbatar yaran sun shirya sannan idan sun tafi makaranta shima ya shirya ya fita nasa aikin. Ya san Aisha karfe takwas take tafiya islamiyya don haka bari zai yi sai bayan azahar lokacin ta dawo yaje suyita ta kare. Domin shi yau din nan yake son ta dawo gidan.

Har bayan azahar yana gidan yana sauraro ko zai ji shigowar Aisha amma bai ji motsinta ba. Don haka wajen karfe uku bayan yara sun tafi islamiyya ya shirya ya nufi gidan Aishan da shirin zai je yaji abinda ya hanata dawowa, da shirinsa na wucewa gidan Yaya Bello bayan ya gama da Aishan.

Har ya isa gidan yana mamakin wannan taurin kan na Aisha.

Da mukullinsa ya bude gate din ya shiga, yana zuwa kofar shiga falon yaganta a garkame da kwado. Mamaki ya rufe shi; tunda yake da Aisha bata taba fita ba tare da ta tambayeshi ba. To daga islamiyya ne bata dawo ba ko Kuma wani wajen ta wuce bata gaya masa ba?

Har ya saka mukulli zai bude kofar sai yaga idan ya shiga ma babu abinda zai yi don haka ya juya ya fice daga gidan ya nufi gidan Yaya Bello yana san ra duk ma inda taje kafin ya dawo ta dawo in ya so sai yaji.

A farfajiyar gidan ya sami Yaya Bellon yana zaune yana shan fura da ‘yar autarsa Minal wadda zazzabi ya hanata zuwa islamiyya. Bayan Minal ta gaisheshi ta shiga gidan ta karbo masa kofi don ya sha furar, tana ajiyewa ta koma cikin gidan.

Bayan Abban sun gaisa da Yaya Bello suka cigaba da hirarrakinsu. Yaya Bello ya dubeshi yace

'Ya yaran? Aishan ta koma wajen nasu?’

Cikin yanayi na damuwa yace

'Wallahi Yaya bata koma ba, sai wasu dokoki da ta kafa na shirme. Ni gaba daya ma na kasa fahimtar ta. Wai ita bazata rike yaran duka ba sai dai dole na cire Yusra da Nana su bazata iya zama da su ba.’

'Ah, kamar Yaya? Wannan ai zancen banza ne ma. To su Yusran da Nana gidan marayu zaka kai su kenan ko ya take so kayi dasu?’

'Wallahi Yaya nima dai na kasa fahimta.’

'To kuma bata baka wani dalili ba?’

Readers Also Read

More by Bilyn Abdull