Kenza eBookz

Uwar sadiku complete - Chapter 38

Uwar sadiku complete - Chapter 38

Uwar sadiku complete Chapter 38: Uwar sadiku complete Chapter 38. Tabbas Yusra ta shaki haushi amma tana kan bakanta na Aisha bata isa ta bata hakuri ba.…

473 words

Tabbas Yusra ta shaki haushi amma tana kan bakanta na Aisha bata isa ta bata hakuri ba. Shi ma Abban nata haushinsa take ji saboda tana tunanin ya zabi Aisha a kanta. Da ba don Yaya Bello ne yazo daukansu ba da wallahi babu wanda ya isa ya fitar da ita daga gidan; to amma Yaya Bello yana mata kwarjini ba kadan ba, kuma ta san shi baya daukan taurin kai kamar Abbansu. Yanzun nan zai bata kashi ko ya gaya mata maganganu masu ciwo. Don haka ta wuce suka shiga bayan motar ita da Yaya yayin da Hanan ta dane gaban motar.

__

Haka rayuwar gidan Abba ta cigaba. Gaba daya yaran Aisha ta hada tana kula da su, su kuwa su Farha sai dai idan su zo wuni. Ita kuma Yusra ta ki ta bawa Aishan hakuri shi kuma Yaya Bello yace kada wanda ma ya sake yi mata maganar gidan nasu, gara a bar masa ita a nan don yana ganin kamar idan ta koma can ma lalacewa zata yi. Shi kuwa Abbanta gaisuwa ce kawai take hadata da shi don ta sawa ranta ya daina sonta don ya fi son Aisha. Sai dai kawai idan ta tuna da Mommy tayi ta kuka tana fadin Mommy itace uwarta itace ubanta don a yanzu ita bata da Uba. Wajen su Yaya Murja kawai take zuwa taji sanyi a ranta, tunda suma suna jin haushi yanda a zatonsu Aisha ta sa Abba ya rabu da ita. Ga kuma labarai na karya da gaskiya da take yawan kai musu, tunda in ta ga dama ko daga makaranta sai ta hau motar haya ta wuce gidan Suwaiba ko Murjan.

Shima Abban rashin dawowar Yusra gidan yana ci masa tuwo a kwarya sai dai babu yanda zai yi. Bai ga alamar Aisha zata saurareshi a kan maganar Yusra ba kuma baya son rabuwa da ita musamman ma da yake yana jin dadin kulawar da take bawa yaran, sannan kuma gashi Yaya Bello ya ma ce ba zai bashi Yusran ba shi zai yi mata aure. Don haka ya tattara ya hakura.

Baya son ya tuna Zahra saboda yanda tunaninta yake bata masa rai, gashi in ya tunata ma sai ya kasa nema mata gafarar Allah sai dai kawai cutarwarta a gareshi da yake tunawa.

Idan ya kalli Aisha da cikin da yake jikinta sai ya kara jin haushi Zahran; domin yanzu ya tabbatar itace ta san kulle-kullen da tayi ta hana Aishan haihuwa.

Idan ya kalli Yusra kuma sai ya kara jin haushin Zahran saboda yanda yake ganin ita ce ta turawa Yusran wasu akidu masu muni wadanda suka sa ya rasa yanda zai yi da Yusran.

………

Babbar Sallah ta wuce da wata hudu Aisha ta haifi yaronta lafiyayye, aka saka masa suna Muhammad Bello. Yayyensa suka yi masa lakani da Baba karami.

KARSHE.

Readers Also Read

More by Bilyn Abdull