Kenza eBookz

Wata kishiya complete by sa'adat - Chapter 44

Wata kishiya complete by sa'adat - Chapter 44

Wata kishiya complete by sa'adat Chapter 44: Wata kishiya complete by sa'adat Chapter 44. Har wuraren 10:am Duk yadda ta kaiga san tayi bacci sam kasawa…

2,683 words

Har wuraren 10:am Duk yadda ta kaiga san tayi bacci sam kasawa tayi, ta daura hannunta a kan cikinta taji sam yadena harbawa ya koma gefe daya ya dunkule, ta tashi zaune a hankali hadi da dafe gurin da babyn ya koma ya zauna, tayi addu'ur'i ta tofa a gurin saboda dr Mus'ab ya gaya mata in har baby ya dena motsi akwai matsala, nan take hankalinta ya tashi abin ya zamar mata goma da ashirin, ta kai 30mnt zaune tana addu'ur'i tana tofawa cikin nata kana taji ya fara motsa mata ta sauke ajiyar zuciyar nutsuwa kadan, ta koma ta kwanta, ta rintse ido Hadi da addu'ur'i ba jimawa bacci me nauyi yayi awan gaba da ita... Ko awa daya batayi dayin baccin ba tashiga wasu mugayen mafarke-mafarke a baccin nata, saude take gani tana binta zata kasheta, har tazo zata caka mata wuka kenan a ciki, ta farka a matukar gigice kadan ya rage ta fado daga bed din datake kai, wata murya nata ce mata ki gudu a gidan! A mafarkin..... Data tashi zumbur ta mike zaune,ta jike sharkar da zufa, nishi kawai takeyi da addu'ur'i, hankalinta ya kuma tashi kan tashin hankalin datake ciki, sound din muryar mece mata ki gudu!shike yawo a cikin brain dinta,. A zabure ta mike ta dakko rigarta doguwa tasaka hankalinta a makutar tashe, tasaka takalmin slifas ta fito compound din gidan sanye take da hijjani Army green, a matukar gigice ko karfi babu a jikinta, ta nufa bakin get,.. Securities suka zubo mata ido, tana isowa inda suke duka hau miko mata gaisuwa, sbda tashin hankali ko kallansu batayi ba, ji takeyi kmr ana zuba mata wuta a jikinta, Allah-Allah kawai takeyi ta fice a gidan dukda batasan ina zataje ba. Securities na kallanta ta fice a get na daya ba halin su hanata, sede suka bita da ido, ta fice a get na biyu ma babu wanda ya hanata sede suka bita da gaisuwa, get na ukuma ta fice a cikinsa babu wanda ya iya dktr da ita ba sam, saboda basu da damar hakan,.... Tafiya tashigayi a kan line din tana tunanin ina zataje, haka kawai seta tsinci kanta da raguwa a tsananin damuwar datake ciki data fito a gidan.. Tafiya tashigayi da kafafuwanta cikin sauri kai bakace akwai tsohon ciki a jikintaba, har ta fito kan ti-ti, taga motoci na wucewa a kan babban titin unguwar sarki wanda ze kaika kawo. Kawai ta miki hanya dukda batasan ina zataje ba, ta hau tafiya a ti-ti manya manyan motocin masu kudi nata tsayawa suna mata magana sun ga jar fata, sam ko cikin jikinta basu gani, ko saurarensu Almuqri'ah batayi ba se zuba sauri takeyi sam ma ta mance da ciki a jikinta, kmr wasa ta isa kawo pack,, tana isowa cikin pack din ta samu guri ta zauna nan kasa tanata nishin uban wahalar datasha na tafiya, mararta ta kulle gu daya, se nishi takeyi, ko miyaun bakinta da kyar take hadiyeshi, tinda ta taho bata huta ba seda ta iso pack din batasan ma ina take ba. Nan yan union sukayi mata caaa da tambayar "ina zakije yarinya! Kano ne ko Zariya ce, ko adamawa yola, yar fara matar manya..." Almuqri'ah ta dago tana me bin ko wannensu da ido. "Ai wannan dagani garin fulani zataje, domin kuwa bafullatana ce sak wannan ma tafi fulani kyau..." Cewar daya daga yan union din dasuka rufeta a kallah sun kai mutum goma. "Kwarai kuwa..." Sauran yan union din suka hada bakin fadar hakan,. "Taso ga motar garinku nan zata tashi daman harta cika, mutum daya ya rage...." Dayan dan union din ya fadi hakan kai kace yasan inda zataje, ba musu Almuqri'ah ta tashi da kyar tabi dan union din dayace mata ga motar garinsu can,. da kyar ma take tafiya cikin jikinta yayi lakur ko motsin kirki ya denayi sede kadan-kadan, kafafuwanta sun kukkumbura sosai duk ta fice a hayyacinta. Dan union din ta mata jagora ta shiga mota ta zauna daman mutum daya ya rage motar ta tashi, wadda take ta yamma ce domin tini ta safe ta tashi yanzu ana neman 4:30pm ne. Almuqri'ah na zama me Mota yace miko kudin motarki..." Almuqri'ah ta rasa yazatayi ita de bata da kudi, ta zubawa me motan ido, ta fiddo hannayenta biyu tana kallansu ta rasama yazatayi. "Ki kawo kudi akace so mukeyi mu tashi mu samu mu fita a kaduna dawuri saboda a nan garin matsalar hanyoyi take da barayi da masu garkuwa da mutane..." Cewar dreva din dayake gajere kmr a kife. "Banda kudi ..." Ta fadi da bebanci, nan take kaf mutanen dake cikin motar suka jiyo suka kalleta, maza sunyi yawa a motar mace daya ce tal wadda Almuqri'ah ta zauna kusa da ita a kalla zata kai 36yrs. Haka kawai dreva din yaji tausanta ya rufesa saboda ganinta nakasashiya, amma beda yadda zeyi saboda motar shima ba tashi bace. "Ba a tafiya ba kudi malama,sakko to bakima shiryawa tafiyarba ashe..." Cewar daya daga dan union din, Almuqri'ah ta sakko dreva din se kallanta yakeyi da yan motar, ta zubawa motar ido matar dake cikin motar ta zubo mata ido, tin sadda ta ganta dazata shigo motar taji tausan yarinyar ya kamata domin dagani tana cikin tashin hankali, again ga ciki a jikinta. Bude jakarta tayi ta kirgo kudade yan dubu dubu ta mikawa dreva din motar tace, dreva ya kalleta yace "Kudinnan na menene?'' Matar tace "Na biyawa yarinyarnan kudin motar tashigo muyita tafiya Allah ya kaimu lafiya, d'a na kowa ne Ai..." Matar tayi maganar zuciyarta na kara cika da tausan Almuqri'ah. Dreva yace "Haka ne kam..." Ya kalli Almuqri'ah yace "Shigo yarinya wannan baiwar Allahn ta biya miki kudin motar,..." Almuqri'ah ta kalli motar dame motar ya nuna mata, ta masa godiya da bebanci, matar tace "Bakomai yarinya D'a na kowa ne,..." Almuqri'ah tashiga motar matar ta matsa mata sosai hadi dacewa "Zauna a hankali saboda larurar jikinki......." Almuqri'ah tace toh hadi da gyara zamanta. Dreva ya shiga mazauninsa ya tada motar suka fice a pack din, Almuqri'ah nata kallan bakin window ita kadai tasan me takeji a zuciyarta, Abdoljalal ne ya fado mata rai ta lumshe idanuwanta, tana mejin bugun zuciyarta na yawaita, tasan har abadan bazata kara ganinsaba a rayuwarta. "Ina zanje?'' Ta tambayi kanta a zuciyarta, motarma data shiga batasan ina zata kaisu ba, ita de kawai tashiga mota, kuma tanajin sassauci a zuciyarta data shiga motar, tasan barinta gidan shine mafi alkhairi kwara ko ina ma zataje taje kawai inhar zata tsira da d'an dake cikinta,,,,zuciyarta ta cunkushe da dumbin damuwa,. Ammah dinta kawai takeso tagani ita kadai zata gayawa dmwarta , tasanma ko ganinta tayi zuciyarta zata nutsu,, ita da knta tasan tana kan jarabawar ubangiji,,, ''Alhamdulillahi ya ilahil alameen..." ta fadi idanuwanta na cikowa da kwallar dasuka wanke fuskarta shaaaaaaa.

Paid book ne.

36 jimmalo ta dan samu bacci kadan amma sam mara nutsuwa, se azahar ta tashi tayi wanka tayi sallah tunaninta na kan Almuqri'ah da halin da take ciki,, tana idar da sallarh ta fito ta nufo dakin Almuqri'ah, tana shigowa dakin taganshi a bude, tasa kai hadi da kiran sunan Almuqri'ah cikin sanyin murya. Amma taji shiru tashigo dakin taga bata nan , kuma taga toilet a bude, jimmalo ta leka taga bata nan, ta fito waje hadin da kwalo mata kira taji shiru, ta duba duk inda zata ganta bata ganta ba, a nan nefa hankalin jimmalo ya matukar tashi gashi tayima kande kiran duniyarnan amma waya bata shiga tini d'an kande ya dauki wayar ya siyar yaje yayi shaye-shayensa shida Abokanayensa da kudaden. Bakin get jimmalo ta isa ta tambayi securities ko sunga inda yarinyar tayi? Nan suka tabbatar mata data fita tin dazu, fuskokinsu cike da nadamar barintan dasukayi ta fitan ,sbda sunga ta jima taki dawowa. Hankalin jimmalo ya matukar tashi hantar cikinta ta kad'a nan take zazzabi ya rufeta. A matukae gigice ta tambayesu ko tagaya musu inda taje. Alnustapha Yace "bata gaya mana ba..." "Innalillahi wa'inna ilaihirraju'un!'' Jimmalo ta fadi yayinda kanta ya buga,, ta fice a gets din gidan cikin hanzari take tafiya ko zata ganta. "Allah yasa ba guduwa tayi ba..."jimmalo ta fadi hankalinta a tsananin tashe, tinda Almuqri'ah tazo gidan tanada tabbacin bata taba fita ba se yau, to tabbas yau din data fito tasan da wuya in ba guduwa tayi a gidan ba. "To ina taje? Gunwa zataje da tsohon cikin jikinta na megida?'' Jimmalo ke fadi a bayyane kmr zararriya, tazama kamar mahaukaciya, tunanin Abdoljalal kawai ya fado mata rai. Har wuraren 6:pm jimmalo nata yawo a gari a kafa, tafi gabas, ta dawo tabi yamma, tabi kudu, tabi arewa Amma sam bataga Almuqri'ah ba ko me kama da ita ma bata gani ba..se bayan isha'i jimmalo ta dawo gidan securities suka bita da ido. Direct jimmalo dakin Almuqri'ah ta nufa dan ganin kota dawo amma taga bata dawo ba. Cikin tashin hnklim dabaze misaltuba jimmalo takoma dakinta taci gaba da kiran kande amma shiru waya bata shiga. Jimmalo ta fashe da kuka me kunar da zuciya, yau ko ruwa batasa a cikintaba , batajin zata iyashan ko ruwan ne a cikinta,. Ranar sam kasa bacci jimmalo tayi, ta rasa waxata kira ta gayawa damuwarta, lmbr kande bata har zuwa yanzu, ta kirata yafi 1m amma shiru.

*A asibiti* Kwana doctors sukayi da wuni a kan hajiya saude amma sam taki dawowa hayyacinsa,, likitoci ma sun fara cire rai dazata dawo hayyacin nata, Abdoljalal ya shiga tashin hankalin dabe taba shigarsa ba,babban tashin hankalinsa besan a wani hali Almuqri'ah take ciki ba, taci ko tasha, besani ba, shifa dmwar ciwon saude kadan ne a ransa, yanaso yabar asibitin yaje yaga Almuqri'ah dinsa da babyn cikinta dayayi kewarsu amma ba hali saboda baze yu ya bar asibitin ba dole se an tabbatar daya sauden ta kasance, ko tunanin shan ruwa Abdoljalal bayayi dukda yanajin kishi amma sam be damu da hakan ba, gashi ko waya bezo da ita ba balle ya kira yarinyar yaji dadih,. tin a daren ranar dasukaxo asibitin yayi wankan tsarki a toilet din dr umar Abokinsa ne tare sukayi scul, sanadin kawo saude asibitin yaga dr umar din, Ahamad ya dakko masa jallabiya blue a motar Abdoljalal din ya cansa, dmn baya rasa kayayyaki a motarsa.

Abdoljalal ya gaji da kewar Almuqri'ah ya amshi wayar ahamad ya kirata amma bata daga ba, seda ya mata kira goma amma bata dauka ba, nan hankalinsa ya kara karkata zuwa gida, amma dole ya jure aga abinda hali zeyi a kan Saude, kaf 2days din da Abdoljalal da yayi a asibitin ko ruwa besha wa cikinsa ba yana tafiya iska na neman daukarsa, ahamad yayi-yayi yasha ko ruwan ne amma sam Abdoljalal besha ba, dmwarsa dayace Almuqri'ah, zuciyarsa na yawan bugawa a kanta,ji yakeyi santa na karuwa a zuciyarsa, yayi kewarta tmkar yayi 10yrs begantaba. Da kyar doctors suka samu kan hajiya saude bayan sunyi 3days a kanta, se cikin dare 2:am suka samu tadawo hayyacinta, suka mata Allurori aka bata daki, tare dasa mata drib. Da Asubahi Abdoljalal nayin sallar asubahi yayi lazimi a daddafe 6;am ya nufo gidansa ya bar Ahamad nan asibitin. se Allah-Allah Abdoljalal yakeyi ya isa gidansa domin ya ga Almuqri'ah d'an cikinsa, zuciyarsa na yawan bugu a kanta. Yana isa gidan yayi packing a tsakiyar gidan ko packing space bayajin ze iya isa saboda ya kagara yaganta. Ya fito ma'aikatan gidan se miko masa gaisuwa sukeyi ko amsasu beyi ba hankali da duk tunaninsa yana kan Almuqri'ah da bebynsa. Direct ya nufa dakin Almuqri'ah, securities dasuke kallanshi ko wannensu seda hankalinsa ya kara tashi, saboda sun san yau zasuci bura ubarsu daman tin tini suke cikin fargaba mara misaltuwa, su basusha cewa Almuqri'ah bazata dawo ba sunsha zataje ta dawo ne, shiyasa suka barta ta fita ba musu,suna tsoron dktr da ita sbda suna bata girma,, gabako daya de a lokacin basusan meya shiga kansu Ba suka barta ta fita.

Da sallama ya shiga dakin. , idanuwansa suka sauka a kan gadonsu, yaganshi kace kace ba gyara,, nan take yaji jikinsa ya masa wani iri,zuciyarta tayi ba ddh, dayaga bata dakin seyasha tana toilet ne dan haka ya nufa toilet din ya Ganshi a rufe yashiga toilet din hadi da kwalo mata kira amma shiru, se yasha ko tana farfajiyarsa tashan iska, dan haka ya nufa can , yana kwalo mata kira, securities na kallansa duk suka sha jinin jikinsu dacewar yau zasuci durin uwarsu, tin tini basu shiga damuwa ba se yanzu. Jikin Abdoljalal har yana rawa ya isa farfajiyarsa tashan iska be gantaba. "To ko tana dakin wannan yarinyar .." Wato jimmalo yake nufi. dan haka ya juyo ya nufa part din ma'aikatan mata. da larai yaci karo, be taba zuwa part din masu aiki ba se yau,. sam larai batayi mamakin ganinsa a part dinsu ba, domin zuwa yanzu kaf ma'aikatan gidan mata sun san Almuqri'ah ta gudu a gidan,sun san komi dake gudana a gidan, amma suna nuna kmr basu sani ba, larai dake kawo musu labari ita ke daurasu a darasin su nuna kmr basu san meke faruwa ba a gidan,kaf komi sun sani, harda sanadin kai saude asibiti sun sani sude fatansu kada saude tadawo gidan domin inta dawo seta ci bura ubar kowa na gidan.. Da larai tasamu labarin Almuqri'ah ta gudu a gidan a gurin salisu tantiri taji, seda ta rabgada gudar farin ciki daman ita ta tsani yarinyar saboda san da saraki kemata da kuma daukakar da Allah yama yarinyar daga zuwanta gidan a gun saraki tinda gata da cikinsa ai tasamu daukaka. Tsugunnawa larai tayi ta gaida Abdoljalal hadi da tambayarsa ya jikin hajiya saude... Ba tareda Abdoljalal ya amsataba yace "kiramin wannan yarinyar, yasunanta ne wadda kuke aiki tare, me jikinnan..." Larai tace "Jimmalo..." "Kiramin ita yi sauri, in Almuqri'ah na dakin ki kirawomin ita seki bar ita waccan yarinyar..." Cewar jalalu. Larai tace toh hadi da mikewa ta nufi dakin jimmalo se murmushi larai takeyi a zuciya da zahiri. "Insha Allahu kaida ganin wannan me sunan larabawar har abadan, tanacan kilama ta afka gidan yankan kai..."larai tayi maganar a zuciyarta. A kofar dakin Jimmalo larai taga jimmalon ta kalleta taga idanuwainta sunyi luhu luhu tayi kuka tagaji. Larai ta tabe baki tace "ohh aiki yasamu gwari...aise ki tashi kije oga na kira.." Jimmalo taji gabanta ya yanke ya fadi jin abinda larai tace a karshe, ta mike tsaye hadi da gyara zaninta wanda ke kokarin kubce mata, tashin hankalin datake ciki baze misaltuba, ko sadda ubanta ya mutu bata shiga tashin hankalin datake ciki ba a halin yanzu, tin tana ganin yarinyar zata dawo yanzu ta cire raima da yarinyar zata dawo gidan yau kimanin 2days kenan bata gidan, jimmalo kullum kwana da wuni takeyi tana kuka, tunaninta daya ne ina yarinyar taje?'' Ta tabbatar in Abdoljalal yaji bata gidan tsawon 2days seya fi jimmalo damuwa "wane itama...." A jere jimmalo da larai suka iso inda Abdoljalal yake, jalalu yabisu da ido yaga bega Almuqri'ah ba sede jimmalon, kallo daya ya mata yagane bata cikin hayya cinta kmr yadda shima baya cikin hayyacin nasa lips dinsa duk yabi ya bushe rakayau se faman jikashi yakeyi da yawon bakinsa.. "Ina Almuqri'ah na?'' Abdoljalal yayi tmbyr idanuwansa na kan jimmalo, larai taji kmr ta kashe knta dayace Almuqri'ah na. Jimmalo kam gabantane ya yanke ya fadi, ta daburce ta rasama mezatace masa, kawai se yaga hawaye sharr a idanuwan ta..hakan ya bala'in jefa Abdoljalal a tsananin tashin hankali mara misaltuwa , ya tabbar da akwai babbar matsala.."nace ina Almuqri'ah da d'an cikina? Ina take? Ina d'an cikina? Kiyimin magana, ina cikina danayi mata? Ina cikina dake jikinta?!!!'' Abdoljalal yayi mata tambayoyinnan cikin tsawar data kada hantar cikin jimmalo ta kalleshi tayi kasa da kanta, duk yabi ya haukace, a hakama dan beji komi ba kenan. "Ina take nace?!!!! Ina cikina?!!!!" Abdoljalal ya kara tmbya cikin tsananin tsawar da har securities seda sukaji, dukkaninsu suka hada baki gun cewa "Anxo wajen..." Kaf jikinsu ya dauki rawa, suka kira masu gadin get din tsakiya dana farko duk suka dawo cikin gida sukayi tsuru tsuru, tini wasunsu sun fara zawo.

Readers Also Read