Waye shi complete - Chapter 11
Waye shi complete Chapter 11: Waye shi complete Chapter 11. "Tun ranar dana fara ganinki a k'ofar gidanku rayuwata ta canja, duk wani tsari da nake dashi…
4,475 words
"Tun ranar dana fara ganinki a k'ofar gidanku rayuwata ta canja, duk wani tsari da nake dashi ya ruguje, na zama ba abinda nake iya yi ba tare da tunaninki ba, tun ban fahimta ba har nazo na gane cewa sonki nake yi, irin son da zuciyata bata taba yiwa kowa ba.
Zan so in iya fad'a miki kuma ki fahimci irin son da nake miki sa'adha, duk sanda na rufe idanuna ke nake gani, in na bude su kuma sai inji ke d'in kawai nake son gani, duk da bana iya samun ganinki kullum amma i always feel your presence around me.
Every second, every moment, every hour, my eyes search for you only, call this love, craziness or the beat of my heart... it is all same for me.
I love you very very much Sa'adha and i don't want to lose you, ever!
Shi yasa a ranar dana ce miki zanzo naje na sami yayanki sulaiman na gaya masa damuwata, shi yace inje wajen baffa sa'adha, shi yace kar in neme ki na tsawon lokacin nan sai na samu yardar baffa tukunna. a duk tsawon lokacin ba mantawa nayi dake ba, ina ta fad'i tashin neman amincewar baffa ne har na samu ya saurare ni, don da farko yace min yayi maganar ki da wani d'an abokinsa ne.
Da Sulaiman da umar su suka yi ta min kokari a wajen baffa har na samu ya saurare ni, daga nan kuma yace zan iya turo magabata na, ko a lokacin na so zuwa in sanar dake komai amma sulaiman yace in bari inji me zasu tattauna tukunna.
Kamar yadda aka fad'a miki nima haka naji zancen sa'adha, bayan tattaunawarsu, sun yanke mana rana zuwa nan da wata guda kuma wallahi duk da bani na tambaya ba i'm more than happy.
Shi yasa jiya dana kira ki na kasa cewa komai...nace miki laifina da yawa sai nazo zan fad'a miki duka reasons d'ina, kuma nazo kika ce min bakya nan."
Ya k'arashe zancen muryarsa can k'asa kamar k'aramin yaro.
Nanne taji duk wata jijiya a jikinta tayi sanyi, gabad'aya fushin da take ji game dashi yabi iska, maganganunsa kamar sun sa hannu ne sun yaye rabin duhun da take ji game dashi, bakinta ya k'ulle ta rasa me zata ce. sai ta jingina kawai da jikin gado ta dunk'ule jikinta waje d'aya.
Shiru ya biyo baya ba tare da yayi magana ba.
"I'm sorry Sa'adha, i'm reeeeallly sorrry, dan Allah kiyi hak'uri if i've hurt you in anyway."
Yadda muryarsa ta fita a hankali da kuma zurfi, yasa taji kamar zata narke gabad'ayanta.
I'm so sorry nima da na kasa fahimtarka a baya, i'm sorry da duk wahalar da kasha akaina, i'm so sorry dana kore ka d'azu.
Ta ayyana hakan duk a zuciyarta, sannan ta sake k'ank'ame wayar a hannunta ba tare da tace komai ba.
"Sa'adha..."
Sai da zuciyarta ta buga da k'arfi jin yadda muryarsa ta nannad'o sunan kamar tun asali shi ya bada shawarar a rad'a mata.
"Na yarda kiyi punishing d'ina duk yadda kike so amma dan Allah kar kice kin fasa."
"Na fasa me?"
"Aure na."
Kalmar tayi mata nauyi sosai, don duk sauran dauriyarta ta tattare ne wajen yadda muryarsa ke shiga kowanne lungu da sak'o na jikinta.
"Na san ba zaki fad'a ba koh?"
A hankali ta daure tace.
"Baffa ya riga yayi magana ai ba zan iya masa musu ba."
"Saboda Baffa ne ba saboda kema kina sona ba?"
Ta damk'e k'arshen hijabinta da k'arfi sanda sallamar sallar inna ta shiga kunnenta. jin tayi shiru yasa yayi murmushi sannan yace.
"Karki damu, zan koya miki yadda zaki so ni, for now wanda nake miki ma ya ishemu mu biyu."
Taji maganganun suna shirin yi mata yawa a rana d'aya kawai da komai ya kwance mata saboda haka tace.
"Sai da safe."
"Zaki kore ni? dan Allah sa'adha kar ki d'auki fushin nan da nisa, so nake mu sake komai afresh, in sanki sosai kema ki san ni."
Tayi shiru tana cije lebb'enta na k'asa.
"Kinjiii....?"
Da sauri tace.
"Naji, sai da safe."
"Ya na iya...sai da safe, Allah ya tashe mu lafiya."
"Ameen."
Tana shirin d'auke wayar daga kunnenta taji abinda ya d'auke numfashinta gabad'aya.
"I love you!"
●﹏●
Next chapter zamu ji yadda akayi imran ya iya tsara duk wad'annan abubuwan.
Sannan zamu ji yadda zata bashi damar da zai gaya mata WAYE SHI.
Kuna tunanin zai gaya mata gaskiya?
Ko rabin gaskiyar?
****
WAYE SHI?
AYSHA SHAFI'EE
30
Assalamu Alaikum...i can't beleieve we are up to chapter 30 already! ya Allah kamar jiya ne fa kawai naci na qoshi na rasa me zanyi na jawo wayata na fara typing...gashi har mun fi rabi na cikin labarin nan.
Kuma Allah ba don ku ba, da tuni na jefa shi a dustbin d'in da nake tara irinsu, cox i have lots of uncompleated stories kamar meh?
Nagode da dukkan support d'inku...dix shapta is dedicated to o laf yuuu!...(lol😁) I mean all of you!
Enjoy!😘
(☆_☆)
"Nanne...?" muryar Rahma ta kira ta.
"Mhmmm." ta amsa halfway cikin barci ba tare da tunanin komai ba.
"Yau baccin me kike yi haka, sha d'aya fa ta wuce."
Jin haka yasa ta bud'e idanunta da sauri ta kalleta.
"Da gaske kike sha d'aya?"
"Na gaya miki ma fa ta wuce, inna har ta fita asibiti nima shigowata kenan."
Ta mirgina a hankali ta juya kan bayanta.
"Ni kaina ban sani ba, na dad'e banyi bacci irin haka ba."
"An kawo miki sak'o yanzu wani yaro ne ya kawo daga waje, shi yasa ma na tashe ki."
Nanne ta had'e girarta waje d'aya.
"Sak'o? meye a ciki?"
"Sak'o fa nace miki, ta yaya zan bud'e."
Ta matsa jikin dressing mirrow ta d'auko wata brown leda k'atuwa mai logo d'in hannaye biyu.
"Kamar wani kwali ne a ciki."
Nanne ta mik'e sosai akan gadon ta karb'i ledar, tana bud'ewa taci karo da wani pink box medium size a jikinsa akwai large prints d'in flowers purple.
Ba tare da tunanin komai ba ta bud'e cikinsa, idanunta suka ci karo da ledoji na different kinds of chocolate, tun daga kan wanda ta sani harda wanda bata tab'a gani ba, gasu nan fal! a ciki.
"Lallai kayan dad'i ne ashe, daga ina haka?"
Rahma ta fad'a tana zama akan gadon, ita dai tayi turus! da murfin a hannu tana kallon su, daga can gefe idonta ya hango mata wata takarda ta janyo ta a hankali ta bud'e.
Sa'adha....!
Yau ina tashi da safe naji a News wai sugar yana kwantar da anger dake jikin mutum, zaki taimaka kisha wannan ko zamu samu fushin da kike dani ya ragu?
Bata san lokacin da wani d'an guntun murmushi ya sub'uce daga fuskarta ba.
Bayan ta fito daga wanka ta zauna a gefen gado tana shafa mai tana kallon fuskarta ta cikin mudubi, akan mudubin wannan box d'in alawar yana facing d'inta.
Wayar da tayi da imran a jiya kawai ta wanke abubuwa da yawa a cikim kanta, idan ta tuno cewa duk tsawon lokacin nan ba share ta yayi ba yana ta neman hanyar da zai same ta ne sai taji wani dad'i ya wanke zuciyarta, sannan idan ta tuno kalaman daya gaya mata cewa shima yana sonta sai taji kamar tana daya daga cikin wadanda suka fi kowa sa'a a duniya, don Imran daban yake daga irin mutanen data sani kuma take gani.
Ance mutum baya taba zama cikakke, amma ita gani take shi komai nasa perfect ne! komai da ta sani a yanzu, kamar ice cream mai dad'i ayi topping d'insa da m&m's...
Ta ina za'a sami matsala a cikinsa?
Ta kalli box d'in ta tuno da d'an short text d'in nan, wani dad'i ya ratsa ta, kamar an saka k'ank'ara a cikin zuciyarta.
Da gaske Imran yana sonta.
Da gaske ne ba mafarki take ba.
Yace yana so suyi starting komai afresh, kenan zai gaya mata waye shi da duk sauran details d'in rayuwarsa, kamar yadda ya fad'awa baffa har ya yarda ya bashi aurenta, in ma bata san duka a yanzu ba, ta tabbata zata sani nan gaba.
Tunda k'addararsu ta riga ta zama d'aya.
A lokacin ne taji wani abu a gefenta yace zut! tana juyawa taga ashe tana zaune ne kusan akan rabin wayar inna, aikuwa idonta ya gane mata number da taje tana kira, number Imran ce da yake itace ta farko akan call log d'in.
Da sauri tasa hannu ta katse kafin ya kai ga shiga, me zai kaita kiransa a yanzu? tace masa me?
Ta mik'e ta nufi sa kaya, sai dai kafin ta zak'ulo kayan da zata saka k'arar shigowar message ya shigo.
A wayar inna dai ta san banda layin gidan waya babu masu turo da text, sai ko wani lokacin wrong number, amma kawai sai ta samu kanta da matsawa ta d'auko wayar.
Da gaske text d'in ne kuwa, kuma ba daga layin waya ba balle wrong number ba. Daga number Imran.
Missing me already?...ki min afuwa zan kira ki anjima yanzu zamu shiga meeting ne. nima nayi missing d'inki Habibty...
...like crazy!
Hannayenta suka shiga rawa, dama kiran ya shiga kenan? ya salam! yanzu me zaiyi tunani akanta? zaice har ta fara kiransa kenan? ta ya zata ce masa bata san ta kira ba?
Ta ajiye wayar ta koma wajen wardrobe ta jawo kayan da hannunta ya fara kaiwa kansu, ta saka rigar amma kafin ta zuge zip ta koma ta d'auko wayar ta sake karanta text d'in.
Habibty. Ta fad'a a hankali.
He just call her habibty!
*******
"Toh ina jinka...sai kuma kayi me bayan nan?"
Jameel ya tambaya yana kallon Imran dake zaune a study room d'insa yana signing wasu papers. shi kuma yana zaune ne akan wata couch dake jikin glass wall na d'akin. D'akin triangular ne mai bango uku, bangon k'arshe shine aka yishi da glass gabad'aya inda daga ciki kana hango d'an k'aramin garden d'in gidan mai d'auke da flowers.
"Na kira ta a waya, na bata hak'uri kuma nace mata nima ina sonta kamar yadda itama take sona, sannan nace mata zanyi mata bayanin ko ni waye saboda ni da ita mu fahimci juna."
"Yarima...."
"Na sani jamil..." yayi saurin katse shi.
"...Ba sai ka tuna min ba, na san bamu tsara haka ba, na san na dawo yanzu ne saboda ciwonta yana shirin dawowa sannan na san bamu yi da kai zan kulata ba har lokacin da za'ayi auren.
Amma idan har muna tsarinmu dole ne mu dinga duba yanayin rayuwarsu suma. ba zai yiwu don iyayenta sun yarda da auren ba kawai ace babu wata alak'a da zata shiga tsakaninmu a yanzu, a tsarinsu dole ne a samu fahimtar juna tsakanina da ita wanda in babu hakan, ba yarinyar kad'ai ba har iyayenta zasu fara suspecting wani abu, kuma babban abinda zai fara rusa mana shiri, shine in har wani ya fahimci cewa akwai wata manufar da yasa nake son aurenta.
Saboda haka dole ne jaamil sai nayi acting cewa da gaske ina son ta ne. kamar yadda ka fada a baya ka gama naka aikin saura nawa, don haka ba sai anyi auren zan fara zan fara part d'ina ba, zai fara ne tun daga yanzu."
Jaamil ya d'anyi shiru yatsunsa akan lebb'ensa yana nazari, daga can kuma yace.
"In dai zaka tafi da hakan akan tsarinmu ba matsala bane yarima, I'm just afraid kar ka zama so close da ita nan gaba...."
"Na gaya maka bana sonta jaamil, abinda ya faru tun farko ya riga ya wuce, har yaushe zaka yarda dani ne wai?
Sannan ni kaina ina da hankalin da zan san cewa Sa'adha ba abokiyar rayuwata bace, halitta ta da tata daban ce, ko banzo cikin mutanen da wannan manufar ba, ba zan tab'a fad'awa wannan kasadar ba.
Rayuwata daban ce da irin tasu kuma na san a kowacce halitta aure shine cikar rayuwa, to ta yaya zan k'arashe rayuwar da ban fara anan ba?"
Jaamil yayi shiru baice komai, hakan ya bawa imran tabbacin cewa ya d'aure shi ne da jijiyoyinsa.
***
K'arfe sha biyu saura na rana, Imran na cikin office d'insa yana harhad'a takardun da ya gama signing, sha biyu daidai zasu shiga meeting da wani sabon company da suke son fara bussiness dasu.
Wayarsa tayi haske, wani d'an mitsitsin haske da ba don idonsa na kusa ba zai gani ba. ya mik'a hannu ya jawo ta gabansa, mamaki ya kamashi ganin number Sa'adha, ya sake kallon agogo, yau friday...bata je makaranta ba kenan?
Ya tuno da fuskarta a jiyan nan, sanda ta lek'o tana kallonshi daga cikin gate din gidansu. a lokacin yaji kamar ya shekara ne bai ganta ba, duk da cewa bata canja ba, amma wad'annan fararen idanun nata cike suke da damuwa wanda ya tabbatar masa da cewa abinda ya karanta da ita a sanda yaje don kwantar da ciwonta gaskiyane kenan.
Zuciyarta tana cikin damuwa, damuwa mai yawa kuma rabi akansa ne, ya fahimci cewa in har zasu tafi akan tsarin da suka yi da jaamil kawai to dole zasu fuskanci matsala nan gaba, don ba zata k'i aurensa ba amma zuciyarta baza ta yarda dashi ba wanda hakan dole zai jawo matsala nan gaba.
A daren ya lura kamar kuka take, daga baya kuma ya fahimci mafarki take yi kuma kamar wani abu ya same ta ne a cikin mafarkin, ya san zata iya farkawa a kowanne lokaci saboda haka yayi sauri ya d'ora hannunsa akan goshinta sannan ya shiga kwantar da d'aya b'arin ruhinsa dake tare da ita.
Sai dai kafin alamun cewa hakan yayi, ya fito, ta bud'e idonta da sauri tare da yin ajiyar zuciya, a sannan ya tabbatar da cewa mafarki tayi wanda ya tsorata, yana cikin d'akin har sanda tayi alwala ta fito sannan ta tsaya gaban mudubi, ya matso dab da bayanta ya tsaya don yaga abinda take gani a cikin wayar data d'auka.
Number daya kira yace mata zaizo ce, ita take ta kallo kamar tana so ta tantance ko shima kiran da yace mata zaizo a mafarkinta ya faru, ya lura ta haddace number saboda haka dole ya nemo layin duk inda ya shiga, don bayan ya kirata ba zai iya tuna inda yasa shi ba.
Ta d'ago ta kalli mudubin, a lokacin ne alamun cewa ciwon ya kwanta ya faru, wani hayak'i ya fito daga rabin fuskarta ya tarwatse a iska, kamar yadda yake yi kullum.
Tun daga yadda yaga ta tsorata a lokacin, ya san sai ya kwantar mata da hankali in ba haka ba abubuwa ne zasu k'ara cakud'ewa a cikin kanta.
Shi yasa bayan yazo ta hana shi ganinta, ya san sai yayi amfani da dabararsa don ya saita tunaninta, saboda haka ya kirata bayan sallar magriba.
Amma kamar yadda ya sani ne, bai yarda da kansa in yana tare da ita ba, bai yarda da zuciyarsa akanta ba. Saboda haka tun lokacin data amsa sallamarsa bai k'ara bi ta kan tsarinsu ba, yayi amfani ne da hanyar daya san zata kwantar da hankalinta kawai.
Bayan nan kuma ya tafawa kansa da shirmen da yayi, shirmen da ya fara tun ba'aje koina ba, shirmen da yayi k'ok'arin lullub'ewa jaamil d'azu cewar ba wani abu bane da zai b'ata tsarinsu, shirmen da yayi d'azu na aika mata da sweets d'in nan, sannan shirmen da yake shirin sake irinsa yanzu.
Ya bud'e cikin wayar ya shiga typing mata message.
Missing me already?...ki min afuwa zan kira ki anjima yanzu zamu shiga meeting ne. nima nayi missing d'inki Habibty...
Ya tsaya ya kalli abinda ya rubutu, sannan a hankali ya k'ara da..
...like crazy!
●﹏●
WAYE SHI?
AYSHA SHAFI'EE
31
(☆_☆)
"Kin min shiru Sa'adha don Allah kiyi magana, ko har yanzu fushin ne?"
Nanne ta sake tankwashe k'afarta akan gadon tana nannad'e bakin rigar filon dake kan cinyarta, a hankali tace.
"Kana lafiya?"
"Ina lafiya kuma yanzu da kika tambaya sai na k'ara jin lafiyar ta kama ni."
Tayi murmushi mai fad'i.
"Ina jinki ki fad'a min sau nawa kika tuna ni bayan lokacin da kika ce min sai da safe?"
Bata ce komai ba kamar yadda ya zata.
"Ko sau d'aya ne kawai sanda kika yi min flashing?"
Da sauri tace.
"Ni ba flashing nayi ba ban sani bane kawai kiran ya shiga na zauna a kusa da wayar."
"Irin wannan bayani haka kamar laifi kika yi?...yanzu toh ba wannan ba, baki tambayeni sauran bayanin jiya ba."
Ta d'an hade girarta kad'an.
"Wane bayanin?"
"Bayanin koni WAYE mana, ko ba kya sonp kiji abinda nace wa baffa ya bani aurenki? ko kuma ki san wane irin miji zaki aura?"
"Na san zaka fad'a min ai."
"Ta yaya kika sani? saboda kin san ina sonki?"
Kamar baza ta amsa ba sai kuma tace.
"Mhmmm.."
"Toh mhmm kema kina sona?"
Ta sake yin shiru.
"Ya Allah! Sa'adha kin mayar dani d'an jarida sai tambaya nake tayi akai-akai."
"Toh ina jinka, ka fad'a min."
"Shikenan mu ajiye wannan a gefe zamu dawo kansa daga baya, bari in fara baki tarihin mijinki tukunna.
Sunana Imran kamar yadda kika sani, amma full name d'in Imran Siddiq, ni d'an garin bauchi ne iyayena sun mutu tun ina yaro saboda haka a hannun k'annin mahaifina na tashi, A bauchi nayi duk karatuna da komai, sai daga baya na samu aiki anan garinku.
Aiki a company ORZ dake kula da harkokin talla na media platforms, shi yasa nake zaune ni kad'ai ba tare da kowa ba, don dukkan 'yan uwana suna can."
This is it! just simple kamar yadda suka tsara a farko zuwansa, haka normal rayuwar matashi irinsa ya kamata ta kasance.
Jin tayi shiru yasa ya cigaba da cewa.
"Tun daga bauchi 'yan uwana suka zo nema min aurenki kwanansu biyu a garin nan, kuma a duk kwanakin suna ta yabawa da irin tarbiyyar gidanku, sunce baffa mutumin kirki ne zanyi sa'ar auren 'yarsa."
Ta cigaba da nannad'e rigar filon a hannunta.
"Tun da suka koma kuma ake ta min waya daga gida, masu son ganinki na da yawa Sa'adha, basu san cewa ni kaina an hana ni zuwa ba."
Ya k'arashe zancen a hankali yana jin nauyin kalamansa na baya, tun farkon sanda ya fara wannan rayuwar, yana tafiya ne akan wannan tsarin, wannan k'aryar...amma tunda yake bai tab'a jin komai ba sai a yanzu da yake gayawa Sa'adha.
Saboda daga yanayin bugun zuciyarta da yake ji ta cikin wayar, ya san ta yarda dashi ne, ta yarda da duk abinda ya fito daga bakinsa.
Amma duk da haka yaji yana son sanin me take tunani a yanzu, meke faruwa a cikin kanta, ya rufe idonsa da k'arfi amma ya kasa jin komai, zuciyarta tayi masa nisan da ba zai iya reaching ba.
Saboda haka yayi shiru shima yana sauraren fitar numfashinta a hankali da kuma bugun zuciyarta. kusan minti biyu kafin ya kira sunanta, ga mamakinsa sai yaji ta amsa nan take.
"Zan iya ganinki gobe?"
"Me za'a yi?"
Kamar a lokutan baya, tana iya jiyo sautin murmushinsa daga d'aya b'angaren kafin yace.
"So nake inzo inyi hira da iyalina."
Kalmar tayi mata nauyi da kuma dad'i a lokaci daya, taji son da take yi masa ya k'aru a cikin zuciyarta, kamar a d'ebo yayi ne a k'ara akan wutar dake ci.
A hankali ta fad'i abinda take fad'a a kodayaushe.
"May be da yamma?"
"Baki tabbatar ba?"
Ta rufe idonta sannan tace.
"Na tabbatar Allah ya kaimu."
"Ameen Noory!"
Jin wani sabon sunan yasa ta bud'e idanunta kad'an sannan ta lumshe su.
Noory yau kuma?
Sunan ya mata dad'i sosai.
******
Har k'arfe hud'u na yamma Imran na jin kuzari a jikinsa da wani irin annashuwa daya manta lokaci na k'arshe da yaji haka.
Wayar da yayi da sa'adha d'azu k'arya ce, haka ma duk maganganun daya gaya mata, amma the fact that ta yarda dashi kuma a cikin duniyarta babu tunanin cewa k'aryar ne shi yake masa dad'i, yana son ya ture gaskiyar shima ya tafi da tunaninsa a hakan, ba don komai sai saboda yana jin dad'in abinda yake yi, yana jin dad'in duk wani moment d'in da yake tare da ita.
Duk cewa da yana tsoron kar biyewa son zuciyarsa ya jawo musu wata matsalar kamar yadda a baya ya jawo wadda suke cikinta a yanzu. Amma wannan tunanin baya tab'a zuwa duk sanda yake tare da ita.
"Uhmm....Siddiq are you with us?"
Muryar Ibrahim ta shigo cikin tunaninsa, ya d'ago da sauri ya kalle su, sai yanzu ya tuna suna zaune a cikin office d'insa su biyar suna tattaunawa akan advert d'in sabon company da suka yi meeting dasu d'azu, wanda har sunyi signing contract da komai yanzu zasu fara shirya yadda za'a baiyana wa al'umma kayaiyakinsu ne, wato irin tallan da za'a yiwa jama'a.
"I'm sorry dan Allah, wani abu ne ya d'an shiga kaina."
Ya karb'i file d'in da yake mik'o masa ya shiga karantawa, sai da ya gama tsaf! sannan ya d'ago ya kalle su yace.
"I don't think i like this idea, can't you come up with anything that will leave an immediate and strong impression?"
Wani usman ya d'an duba paper gabansa sannan yace.
"We just thought since the products are fibres, a simple advert will do."
Imran ya girgiza kansa.
"You should'nt have thought that, advert komai k'ank'artarsa komai rashin amfanin kayan ga al'umma, hakk'in mune mu tallata shi in a way da zamu iya karkata tunanin mutane daga kan neccesssities d'insu zuwa shi.
Saboda haka zuwa gobe, just keep thinking about something any idea that wiil catch the mind of viewers, prepare something more spectacular please.
Usman after that, I think you can work with Director Phillps to come up with a way to convey it. Ibrahim you will be in charge of the copy writing, and Maryam...
Ya juya ya kalleta, tana zaune a gefensa cikin shigarta ta matsatstsun kaya kamar kullum d'an karamin mayafinta na reto a kafad'a. Ba abinda ya sashi tsayawa da maganar kenan ba, hannayenta, hannayenta da suka sha wani had'add'en kunshi daya zauna d'as akan farar fatarta. Bai san ya akayi tun farko ya bari ta fahimci cewa yana son k'unshi ba, shi yasa duk sanda ta san zasu had'u take zuwa tayi don ta san ko ba komai zata samu alfarmar ya saurareta. Ya had'iye wani abu a mak'ogwaronsa kafin ya cigaba.
"...make a list of all the client that we will work with for the next quarter by tomorrow."
Ya juya ya kalli wata dattijuwar mata da kowa a companyn ke kira da Aunty Fati, mace ce mai tsananin kirki da sanin hakk'in al'umma, shi kansa yana ganin girmanta sosai saboda yadda ta maidashi kamar d'anta, don babban d'anta ma Abdullahi ya girme shi kuma ya sanshi duk sanda suka had'u suna gaisawa sosai.
"Aunty can you make me an appointment with Dr Turaki? I need to see him tomorrow."
Tayi murmushi kafin tace.
"Insha Allah Imran."
"Okay, we can call it a day."
Da haka kowa ya d'auki takardunsa suka mik'e, sai dai kafin Aunty fati ta kai ga fita, Imran ya tuna da abinda jaamil ya gaya masa jiya.
"Abu biyu ne da suka rage mana yanzu, wai akwai kaya da ake kaiwa gidansu yarinyar sunansa lefe, ni ban san ta yaya zamu had'a su ba.
Da kuma zancen gida, dole ne sai ka tashi daga gidan nan, saboda yayi kusa daga gidansu kuma ance min suna kawo kayan gida daga wajensu suma. Saboda haka inda zaka nema bana tunanin sai ka sayi komai.
Tuno hakan yasa yayi saurin tsaida ita, ta dawo ta zauna a kujerar dake gefensa.
"Aunty Faty wani abu ne ya taso min wallahi, kin san families d'ina ba'a nan kusa suke ba kamar yadda na fada muku..."
Ya d'an yi shiru yana juya abinda zai fad'a, amma murmushin fuskarta ya sashi cigaba da magana.
"...Toh aure na ne ya tashi, kuma bana son har sai na tafi can kafin a had'a lefe, shine nake so in tambaye ki ko zaki taimaka..."
"Kar ka kuskura ka k'arasa Imran, in har kace taimako kenan baka yin uwar dani kamar yadda ni na d'auke ka, Alhmdlilahi, wallahi naji dad'in wannan zancen sosai, dama na dad'e ina maka sha'awar aure a wannan lokacin, don shine cikar mutuncin kowanne mutumin arziki.
Zancen lefe kuma kar ka sami damuwa, insha Allahu za'a had'a ba da wata matsala ba, dana koma gida zan samu 'yan uwana, mu zauna muyi lissafin yadda muka had'a na Abdullahi, zaka ji duk wani bayani daga baya. Nayi murna sosai wallahi, Allah ya tabbatar mana ya sanya alkhairinsa a cikin lamarin.
Allah yasa kuma ta zama alkhairi a gare ka da kuma 'ya'yan da zaku samu a gaba."
*******
A cikin sati uku, kusan komai ya koma daidai a rayuwar Nanne, sunyi jarabawar first term sun k'are har an bada hutu na wata d'aya.
Hutun data san ita ta gama zuwa makaranta kenan, don baza ta koma second term ba sai lokacin Waec da Neco kawai kamar yadda baffa yace. Shirye-shirye ya kankama sosai daga kowanne b'angare, don hatta iyayen Imran maza sun kawo lefe akwati goma sha uku, Sannan ya had'a ta da'yan uwansa a waya sun gaisa.
Daga b'angaren inna kusan ba abinda bata tanada ba na harkar kayan d'akinta, ko baffa abinda ya bayar kad'an ne inna tace ta yafe masa tunda bai dad'e da bikin mata hud'u ba.
A cikin wannan lokacin ma Nuratu tazo da nata gudunmawar ita da 'yan uwanta, a sannan ne kuma Nanne take jin cewa shima Nuran da tayi mata zancensa an kusa bikinsa a lokacin itace bata sani ba a lokacin.
Ranta yayi fari kal! da tunanin shawararta Nanne ta karb'a ta yarda da aure a yanzu, musamman kafin su tafi da Imran yazo suka gaisa, sai farin cikinta ya k'aru, tana ganin ba k'aramar sa'a Nanne tayi na samun miji irinsa ba.
A kullum kuma alak'ar dake tsakanin Nanne da Imran k'aruwa take, a yanzu ta saba dashi sosai don har tana sakewa tayi masa hira a waya ko kuma in yazo. Duk da cewar wayar tasu tafi yawa, don a k'aida ne kullum zai kirata sau uku, da safe in ta tashi, da rana in yana office, da kuma da daddare in zasu kwanta.
Da gaske ne ya dad'a koya mata yadda zata so shi, don ko kad'an yanzu ba alamun wannan damuwar data shiga kwanaki sanda baffa yace aure zai mata, ta daina tunanin duk wasu abubuwa da zasu faru nan gaba, burinta kawai a kullum Imran ya kirata ya kara tuna mata cewa ta kusa zama tasa, duniyar gaba da take hangowa mai tsananin kyau ce tunda tana tare dashi.
Don hatta karatun da take tunanin zata cigaba a yanzu ji take yi meye ma amfaninsa in dai Imran yana cikin duniyarta.
Kusan komai ya gama kammala a satin da aka tsayar na auren. Imran ya bada muk'ullin gida a can wata unguwa dake nesa dasu.