Waye shi complete - Chapter 16
Waye shi complete Chapter 16: Waye shi complete Chapter 16. Muryarta mai dad'i ta fad'a tana nunawa Imran hannunta. Jaamil yaji wani abu mai kama da…
4,483 words
Muryarta mai dad'i ta fad'a tana nunawa Imran hannunta. Jaamil yaji wani abu mai kama da tausayinta a cikin zuciyarsa, tana cikin wani sirad'i mai had'ari amma bata sani ba. Her voice was innocent!
Imran ya murza 'yan yatsun nata yana fad'a mata wani abu da bai maida hankali yaji ba, sannan yayi kissing saman goshinta, ta ture shi a hankali tana murmushi.
"Naji dadin ganinka Jaamil, ka taimake shi don har na fara tunanin ko bashi da freinds ko d'aya."
Jaamil ya juya ya kalli Imran, da ido yayi masa alamun zaiyi masa bayani daga baya, saboda haka ya kalleta yace.
"Nine da laifi amarya, kamata yayi inzo har gida in gaishe ki amma na d'anyi tafiya ne."
"Tafiya?" Ta juya ta kalli Imran.
"Bai fad'a ba kuma."
Kafin Imran d'in yayi magana wata Nurse ta k'araso tace da Sa'adha likitan da zai fad'a musu result d'in tests d'in na jiranta, tare da Imran suka tafi bayan ta rok'i jaamil akan kar ya tafi. Ba yadda ya iya haka ya zauna har suka fito, daga nan suka koma gida.
Inda sa'adha ta rik'e shi da hira da d'awainiyarta har sai bayan sallar maghriba sannan ya samu ya tafi, Imran na tayi masa dariyar yadda a dole yau yaci abincin da Sa'adha ta tarkata masa kala-kala, tun yana iya ci har sai da ya fito k'iri-k'iri ya gaya mata ya k'oshi sannan ta daina kawo layin cimar da bai tab'a ci ba kala-kala.
Imran ya gaya masa cewa ta tambaye shi su waye freinds d'insa ne shi kuma ya rasa sanda bakinsa ya furta mata sunansa, amma ya tabbatar masa bayan hakan babu wani abu nasa data sani.
Bayan jaamil ya tafi, ya taya ta suka yi tarin wanke-wanken data tara, zuciyarsa cike da farin cikin irin karb'ar da ta yiwa jaamil, yaji dama yana da wasu 'yan uwan da zasu taya shi ganin kyautatawar matarsa, saboda itama tana masa tambayoyin da suka shafi 'yan uwansa amma bata cika matsawa sosai ba.
Zuciyarta a kullum tana danganta shine da abubuwa masu kyau kawai, alhalin shi d'in akasin hakan ne a wajenta.
Ya tuno bayanin likitan nan da yake gaya musu cewar komai a jikinta lafiya k'alau yake, kawai bugun zuciyarta ne ya ragu kuma shima 'yan dalilan dake sashi ba masu k'arfi bane. Hankalinsa ya kwanta a lokacin amma tunanin abinda zai faru nan gaba kuma yazo ya rugurza komai.
Don kamar yadda jaamil ya fad'a masa ne kafin ya tafi, rashin jin komai da suka yi daga wajen Naani ba lafiya bane, dole akwai wani dalilin da har haskenta ya shigo gidan amma bai iya tab'a Sa'adha ba, don haka dole suyi tsammanin jiran koma meye a yanzu.
"What's with d'ankwalin kanki yau?"
Ya tambayeta da daddare lokacin da suke zaune a falo, ya d'auko system d'insa yana k'arasa wani kwantan aikinsa dake ciki, ita kuma tana gefensa tana b'are tulin maggin da take tarawa a cikin wata jar, idonta na kan tv tana kallon wani tsohon indian film da wata channel ke nunawa.
Ta kai hannu ta tab'a d'ankwalin kamar tana so ta tabbatar in yana nan d'in.
"Aunty maryamah tace in daina zama ba d'ankwali."
Ya juyo ya kalleta. "Saboda me."
Tayi shiru kamar ba zata fad'a ba sannan ta kalle shi tace.
"Wai saboda aljanu zasu iya shiga jikina."
Yadda tayi maganar ya bashi dariya kamar itama bata yarda da abinda ta fad'a ba, yayi murmushi a k'asan numfashinsa sannan ya jawota jikinsa.
"Aljanu kike tsoro?"
Ta girgiza kanta.
"Su suke fad'a dai, bana fad'a maka wasu malamai sunce har bak'ak'en aljanu ne wai suke son shiga jikina ba."
Har yanzu da murmushin a fuskarsa yace.
"Duk ki rabu da wannan zancen Noory, in dai har kina tare dani ba aljanin daya isa ya shiga jikinki... babu shi a duniyar nan!"
Ta d'ora idanunta sosai a kansa.
"Ta yaya ka san hakan?"
Ya kai hannunsa a hankali ya cire d'ankwalin sannan ya cusa yatsunsa ya warware bun d'in da tayi da gashinta.
"Saboda su kansu Aljanun suna tsoron irin jinsi na Sa'adha."
Kanta ya d'aure da mamaki.
"Wane irin jinsi ne kai d'in?"
Ya tura kansa gefen wuyanta yana shak'ar dadd'an k'amshin shampoo d'inta kafin ya amsa.
"Jinsina na masu yawan addu'a mana."
Tana jin hakan mamakin fuskarta ya kwance, sannan murmushi ya maye gurbinsa.
*******
K'ARFE BIYU DA RABI.
K'arfe biyu da rabi na daren wannan ranar abinda Imran ke tsammanin jira ya faru!
●﹏●
WAYE SHI?
AYSHA SHAFI"EE
42
Wannan chapter ta k'unshi zallar bayani na abubuwa da yawa da muke son kwancewa daga farkon labarin nan.
(☆_☆)
MUZAFFAR!
Ta tsirawa taswirar fuskarta ido ta cikin garai-garai d'in ruwan dake wucewa a gabanta. Watakila ta shafe awanni biyar zaune a wajen koma fiye da hakan, ba zata iya tantancewa ba, don dad'ewarta a wajen ba damuwarta bane, fatanta kawai abinda take zaman jira ya k'araso, ya k'araso gareta ta sashi a idonta ko ta samu nauyin dake zuciyarta ya kauce, wani nauyi daya taru tun tsawon shekara guda data wuce.
Tana zaune ne a bakin wani rafi, ta d'age rigarta kad'an ta zira k'afafunta ciki, sunkuyawar da tayi ta zura hannuta yasa dogon gashinta ya bita cikin ruwan, yana motsawa a hankali tare da gudunsa, sannan daga kowanne gefe na lambun tarin hadimanta ne ke tsaye suna gadinta.
Duwarta ta fara ne tun lokacin da YARIMA ya bar cikin duniyarta da niyyar yiwa Naani wani aiki da har yau bata san mene ne ba, bayani d'aya kawai ta sani wanda ya fad'a mata kafin tafiyarsa na cewar sai tayi hak'urin jure rashinsa don ba zata iya ko jin muryarsa ba daga can inda ya tafi d'in, a lokacin komai zai kasance ne cikin watanni hud'u kawai, amma a yanzu, shekara d'aya itace k'irgen da kowa keyi na tsawon tafiyarsa.
Tayi hak'urin har ya k'are ta sake lalubo wani ta d'ora ya cigaba cinyeta, cinye siffar da take mutuk'ar so a rayuwarta. Idonta ya sake kaiwa kan ruwan, watak'ila da ita bil'adama ce da in ta samu biyan buk'atunta nan gaba kad'an hankalinta ya kwanta da sai jikin ya koma yadda yake, amma abu ne da ta san ba zai tab'a faruwa ba wanda ya tafi ya riga ya tafi kenan!
A tsawon rayuwarta ba abinda take mutuk'ar k'auna irin siffar bil'adama da kuma son shiga cikinsu, amma sai ya zama kamar abubuwa da yawa a rayuwar tata, Naani tayi mata katanga dashi akan dalilin da ta san ba zai rasa nasaba da d'aya tilo da idonta kad'ai ke gani ba. Gata d'aya da tayi mata shine mayar da jikinta da tayi ya koma irin na bil'adaman, wani abu da ita kad'ai ke dashi a duk fad'in nahiyarsu.
Amma duk da haka ta k'udirce a zuciyarta cewa sai ta fanshe duk wata wahala data sha a wajen dukkaninsu, duk wanda keda hannu a cikin bak'in cikin data tashi dashi.
Mussaman shi yariman, wani halitta data tsana fiye da kowa a rayuwarta, ta tsane shi tun lokacin da hankalinta ya iya banbance tarin k'aunar da Naani ke masa akanta, Bata tab'a ganin Uwar dake fifita d'an wani sama da nata ba irin tata uwar, ita kad'aice 'yarta a duniyar nan, amma hankalinta da tunaninta baya tab'a zama akanta, ita d'in koyaushe tana zuwa ta uku ne a jerin al'amuranta.
YARIMA DA JAAMIL sune sunayen data tsana fiye da komai a rayuwarta, kuma sunayen data yi alkawarin sai ta kawar dasu a duniyar nan, sai ta zama ajalinsu, ta yadda dukkan wani abu da Naani ke shirin mallaka musu zai dawo gareta, ya zama dukkan tanadin da take shirya musu ya k'are akanta, yadda bayan taga hakan itama daga baya ta kashe ta.
Ta dad'e da tsara wannan shirin a cikin kanta, abu d'aya ne ta tsaida faruwarsa har yanzu, shine tafiyar yarima, domin komai zai fara ne bayan ya aureta. Shi yasa a yanzu take zaman jiran wannan nauyin zuciyar tata ya kauce!
"Ranki ya dad'e sak'on ya iso...yarima ya shigo cikin masarauta yanzu."
Wata hadima daya shigo lambun a daidai wannan lokacin ta fad'a kanta a k'asa.
A hankali wani murmushi ya sauka a gefen kumatun SAREEFA, wani murmushin da tayi tanadinsa tsawon shekara guda!
Lokacin data k'arasa cikin masarauta, komai ya canja...a jiya ne kad'ai Naani ta sanar da zuwansa amma a jiya kad'ai aka canja fasalin komai gabad'aya.
K'erarren ginin masarautar yana tsaye kyam! cikin wata irin k'awa da ado na alfarma, an canja launin kalarsa zuwa kalar rawaya da fari, yanayin lokacin yamma ne mai cike da lumshi da kuma iska mai dad'i, amma duk da haka tsuntsaye ne birjik! tun daga hanya sunyi rumfa da fuka-fukansu cikin wani tsari mai ban sha'awa, sannan ga tarin halittu nan taf! jinsi kala-kala suna durfafin isowarsa, ko'ina ka juya fuskoki ne cikin farin ciki, ga kuma tashin wani kid'a mai dad'i dake tashi a ko'ina.
Zuciyar Sareefa ta matse ganin irin tarin k'aunar dake fuskokinsu, a dawowarta na k'arshe masarautar, bata samu koda rabin wannan tarbar daga wajen kowa ba, hatta daga Naani kuwa saboda ta tabbata k'awata masarautar ma anyi ne bisa umarninta.
A ranta ta ayyana cewa saura lokacin kad'an duk wannan ikon ya dawo mallakinta, ta tsaida hadimanta daga bin bayanta sannan tabi iskar wajen ta baiyana a cikin masarautar!
*******
Imran na tafe cikin siffar da al'ummar nahiyarsa suka sanshi a matsayin YARIMA, a gefensa jaamil ne shima cikin ainihin tasa siffar suna ratsawa ta cikin tarin halittun da suka yi durfafin ganinsa, kowannensu cike da farin cikin ganinsa bayan wani tsawon lokaci.
Nan d'in shine k'asarsa, mahaifarsa inda jinsinsa da duk wani gatansa yake, kuma ya saba da rayuwa a cikinsa tun zamanin k'uruciyarsa, ya saba da wannan matsayin da ake bashi sannan ya saba da wannan yanayin da jikinsa ke ciki, amma a yanzu ji yake komai ya dawo masa sabo, kamar ansa wani abu an goge wani waje a kwakwalwarsa da yayi saving duk memories d'insa na baya.
Gani yake kamar shi d'in a yanzu baqo ne, komai ya canja masa, komai d'in da baya tunanin d'imbun halittun dake gabansa sun fahimta, koma jaamil dake gefensa, don watakila canjin da yake ji yafi nasaba ne da cikin zuciyarsa, wadda bata tare dasu a lokacin, tunaninsa ya koma can nahiyar da ya baro kusan awanni uku baya, k'irgawa yake cewa Sa'adha ta kusa tashi a yanzu, tunda ya saka mata Alarm a sabuwar wayar daya kawo mata wanda zai tashe ta sallar Asuba.
Yafi sau d'ari a cikin zuciyarsa yana hasko yadda yanayinta zai kasance in ta farka bata ganshi ba, kowanne reaction na duniyar nan ya d'ora akan fuskarta amma ba wanda ya gamsar dashi cewa hakan zata yi.
Sweatheart,
Wani uzuri ne ya taso min urgently kina bacci, i'll be back soon! don't panic dan Allah, zanyi miki bayanin komai in na dawo kinji? I love you...
...like crazy!
Ya tuno d'an k'aramin note d'in da yayi scrambling a papers wajen hamsin ya ajiye a kusan koina na gidan daya san idonta zai kai. kusa da pillow, kofar toilet, kan slippers d'inta, kan fanfon sink, kan kujera, kan dining table, kan drawers d'in kitchen, kan gas, kan sink, da duk wani waje daya san zata yi amfani dashi, he wanted to make sure hankalinta bai tashi ba ta fahimci uzurinsa.
"Da alama al'amarin ba zai kasance yadda muke tunani ba, tunda da tayi fushi sosai, ba zata sanar da al'ummah ba har ayi wannan taron."
Jaamil ya fad'a lokacin da suke takawa cikin hanyar da zata kaisu ga fadar Naani.
"Na san koma meye ta riga ta samu hanyar da za'a magance shi yanzu, saboda haka ka yiwa Allah yarima ka karb'i dukkan wani abu da zai faru a yanzu da hannu biyu."
Kamar yadda tun lokacin da yazo masa da saqon neman da Naani ke musu wajen k'arfe biyu da rabi na dare baice komai ba, haka ma yanzu baiyi magana ba har suka kai ga cikin tamfatsetsiyar fadar, da bata da wani fasali da kwakwalwar mutum zata iya fahimta.
Suna isa ciki, jaamil ya nufi wajen mahaifiyarsa 'Bwama' da ya hango a gefe, a sannan ne kuma idanun Imran suka hango masa Sareefa tsaye daga gaban karagar Naani cikin siffarta ta bil'adama, bai tab'a d'aukan yanayinta da daraja ba irin yanzu, a da baya ko damuwa yaga banbancin siffarta da tasu don a tunaninsa son da takewa bil'adama shirme ne, matsayin da Allah ya basu ya isa rayuwarsu ba sai sun kwatanta dana bil'adama ba.
Amma a yanzu, gani yake sareefa ta yiwa dukkan al'ummar daya had'u dasu zarra a idanunsa, kamar tana tuna masa cewa zai koma wajen Sa'adha ne nan da k'ank'anin lokaci. Kafin ya k'arasa tunaninsa ta baiyana a gabansa sannan cikin sauri ta rungume shi.
"Maraba da sauka yarima, maraba, maraba...nayi kewarka fiye da tunanin duk wata halittar Allah."
Muryarta ta fad'a a cikin jikinsa. Imran yaji jikinta yayi k'arfi a cikin hannayensa, ya saba da irin wannan rungumar tata a baya sau da yawa, amma yanzu daya saba da jikin Sa'adha na mutane, sai yaji kamar yana rik'e da dutse ne.
"Da kinyi kewata da yawa, da na dinga samun sak'on ki akai-akai wajen jaamil."
Ya fad'a sanda ya matsar da ita daga jikin nasa, idonta ya nuna rashin gaskiya kafin tace.
"Kullum ya dawo zai koma wajenka, sai na tare shi da saqona, watakila shine baya fad'a maka."
Rashin gaskiyarta ya fito k'arara har a muryarta, sai kawai yayi murmushi yana kallonta.
"Ka canja yarima, ka canja sosai ka k'ara kyau fiye da baya, watakila duk inda kake ba a cikin wahala kake ba."
"Babu wahala ko kad'an, na saba da komai kuma ina ji ma kamar..."
Bai k'arasa ba ta katse shi, muryarta cike da mamaki.
"Me ya sami ruhinka? me ya sami b'arin ruhinka?"
Yaso ya manta ne sareefa tana da baiwar ganin duk wani abu dake jikin wata halitta ta duniya, bama iya jinsinsu kad'ai ba.
"Akwai matsala tare da jikinka, ta yaya kake iya rayuwa da b'ari d'aya kad'ai? kuma d'aya b'arin baya kusa da kai?"
Ya lumshe idanunsa a hankali.
Yana kusa dani sareefa! Sa'adha tana kusa dani!
*******
"Me ake ciki game da aikin da ya kaika..."
Muryar ta fito cikin kaushi kamar kodayaushe tare da amo mai girgizarwa, a yanzu da ya dad'e bai jita ba, sai yake jin kamar sautin ta yana tab'owa ne har k'asan zuciyarsa. don yana iya jin yadda zuciyar tasa ke amsawa.
Imran ya d'ago da idonsa ya kalli hallitar dake zaune a gabansa, wata halitta data zama gata da tallafin rayuwarsa, a kullum ya d'aga ido ya kalleta sai yaji girma da matsayinta ya k'aru a idonsa, ya gyara murya a hankali sannan yace.
"Komai ya kammala Naani, a yanzu haka muna jiran wani taro ne da za'ayi na cikar kamfanin shekaru Ashirin. Na tabbatar a wannan lokacin buqatarmu zata biya, tunda a yanzu haka ya riga ya amince dani yadda ba wani abu da ake zartawa a kamfanin ba tare da umarni na ba.
Shi yasa a lokacin da jaamil ya fad'a min lokacin fitowarki, nayi tunanin zamu kammala komai kafin nan."
"Komai yana nufin har da matsalar data k'aru bayan bana nan?"
Muryar tasa tsigar jikinsa mik'ewa, bata danganta abin da laifinsa ba saboda haka ya samu kwarin gwiwar bada amsa.
"Matsalar data faru Naani wani tsautsayi ne da yafi k'arfin mu, shi yasa muka yi amfani da hanyar da iya tunaninmu ya bamu kawai wajen neman mafita, amma koda mun samu buqatar data kaini cikin bil'adama, zamu jira ne har ki dawo, don ba wanda zai iya raba ruhin da jikinta."
"Na samu labarin komai tun ina can, kuma na shaidawa jaamil cewa abinda kuka yi garaje ne, akwai hanyoyi da yawa da za'a sami mafita bayan cewa ka aureta, saboda a kowacce halitta aure ba k'aramin zance bane, tunda yanzu in har zaka rabu da ita, sai a nemi wata hanyar da zamu shafe batunka daga tunanin duk wani bil'adaman daya shaida aurenku, wanda hakan ba k'aramin aiki bane.
Sannan nayi k'okarin b'oye wannan zancen daga wajen sareefa, don na sani baza ta tab'a jin dad'i ba, taji kayi aure acan koda na wucin gadi ne, bayan tsawon jiran da take yi maka anan."
Imran ya had'iye yawu jin hakan, zancen aurensa da sareefa ba sabon abu bane, amma a yanzu da yaji shi sai yake tunanin wane irin tunani ne dashi a da? ta yaya ya yarda da auren sareefa alhali bai tab'a sonta ba? da baije cikin mutane ya had'u da Sa'adha ba haka zai rayu kenan bai taba sanin mene ne so ba?
"Aiki ya riga ya zama guda biyu a yanzu, zan raba yarinyar da ruhinka sannan a fara k'ok'arin hanyar da zaka rabu da ita, abinda na gayawa jaamil kenan, kuma a jiya na duba yarinyar a cikin haskena, sai dai abinda na gani Yarima ya wuce tunaninku."
Sai a sannan ya d'ago da idonsa ya kalleta, kwarjinin siffarta ya cika kowacce gab'a ta jikinsa.
"Ruhinka ya riga ya had'u da jikinta sosai, ba zan iya raba shi tun daga nan ba, dole ne ka kawo yarinyar nan!"
Gabansa ta fad'i a lokaci guda, zancen ya masa girma.
"Ta yaya hakan zai yiwu Naani? ta yaya zan iya kawo ta cikinmu? har yanzu bata san ni WAYE ba."
Shiru ya biyo baya kafin ta amsa.
"Ba abu ne mai wuya ba, zamu iya komai mu gama har ka maida ita cikin abinda baifi awa biyar ba, sai dai kawai zata fita daga haiyacinta ne."
Sa'adha ta fita daga haiyacinta? Shine zaisa ta fita daga haiyacinta? Ta yaya zai iya hakan?
"Da bakinka ka shaida min cewa ba son yarinyar kake ba, kuma jaamil ma ya tabbatar mun da kyar ka yarda ka aureta, toh me ya kawo tunani yanzu fuskarka?"
Ya had'iye yawu a hankali, abu na k'arshe da zaiso a yanzu shine Naani ta fahimci wata matsalar daga wajensa, ita d'in wata halitta ce da duk duniyar nan bashi da kamar ta, kuma baya jin zai tab'a sab'a mata a rayuwarsa.
"Ina tunanin yadda hakan zai kasance ne."
"Zuwa nan da sati d'aya, zan sanar da kai lokacin da zaka kawota, kafin nan ka cigaba da dukkan harkokinka, komai ya kusa zuwa k'arshe ka dawo cikin rayuwarka, ina baka hak'urin dukkan wahalhalun daka sha."
Daga haka ya san maganarta ta k'are kenan ta sallame shi. A yanzu zai iya komawa wajen Sa'adha, can nahiyar da rabin ruhinsa yake, don ji yake kamar a takure yake yanzu, ta yaya ne wai ya iya rayuwa shekara da shekaru a wannan wajen?
Ya tattara dukkan zancen da suka yi a yanzu ya tura can k'arshen zuciyarsa, ba zai bi ta kansa a yanzu ba, sai ya koma inda hankalinsa zai kwanta tukunna, inda zaiyi tunanin wata mafitar ba wannan ba, don ba zai tab'a iya cutar da Sa'adha da hannunsa ba.
Bayan ya fita jaamil ya shiga kamar yadda Naani ta umarta, sai dai k'afafunsa suka kasa barin wajen, yaji ba zai iya motsawa zuwa koina ba in dai har ba barin wajen zaiyi gabad'aya ba saboda haka ya tsaya anan yana jiran fitowar jaamil, don ba zai iya komawa cikin tarin al'ummar dake jiran fitowarsa avwaje shi kad'ai ba. A lokacin ne kuma kunnensa ya jiyo masa muryar Naani daga ciki.
"Ka tabbatar Yarima ya bar wajen?"
"Na tabbatar ranki ya dad'e." jaamil ya amsa.
"Zan fad'a maka wani abu ne dana kasa gayawa masa, don yau shine rana ta farko a rayuwarsa da ya fara min k'arya, shi yasa nima ya zama rana ta farko dana fara b'oye masa gaskiyar lamari na. Saboda haka ina so kai ka bani had'in kai mu k'arashe abinda kuka fara, wanda shine dalilin dawowata da wuri."
Imran yaji mamaki ya sark'e kafafunsa dake rik'e dashi a wajen, abinda yake ji wani abu ne da bai tab'a zatonsa daga wajen Naani ba, Muryar ta cigaba da shiga kunnensa.
"Abinda kuka yi babbar matsala ce da zata iya jawo tab'arb'arewar komai a cikin rayuwarmu gabad'aya, amma nayi shiru ban fad'a muku bane saboda ina tunanin duka zan samu had'in kanku mu shawo kan matsalar, don haka ko ban sami amincewar yarima ba, kai ka saurareni da kyau kaji abinda zan fad'a maka.
Dalilin da yasa ban iya raba ruhinsa da jikin yarinyar a jiya ba shine ruhin ya riga ya kusa had'ewa da nata, ba zai tab'a yiwuwa a raba su ba kuma a sami dukkaninsu, dole sai an rasa d'aya.
Ko dai in an raba su a sami na yarinyar a rasa na yarima, ko kuma a rasa yarinyar a sami nasa, kuma daga yadda na karance shi, ya riga ya gina wata alaqa da yarinyar da ba zai so ya rasa ta ba, kuma ka san cewa idan har babu cikakken ruhinsa a tare dashi burinmu ba zai tab'a cika ba.
Saboda haka na yanke shawarar zamu cire ruhin nasa koda kuwa yarinyar zata mutu.
Nayi masa bayani akasin naka, kuma zan gaya masa ranar da zai kawo ta nan, idan har mun gama komai sauran abubuwan zasu zo da sauqi tunda in har ta mutu, danginta ma zasu karbi hakan ba tare da wata matsala ba!"
●﹏●
Akwai lauje da yawa a cikin nad'i game da chapter nan.
Da farko munji irin tunanin Sareefa akan Imran...na irin kishin da take yi akan yadda Naani ke fifita shi akanta.
Ga ainihin gaskiyar dalilin da yasa take son aurensa ka kuma son kasancewarta bil'adama, me kuke tunani zai faru in har ta san Imran cikin mutane yaje?
Kuna tunanin cewa da gaske Naani tana son Imran ne kamar yadda kowa da kuma shi kansa yake gani?
Me zai faru a yanzu da ya san ainihin abinda zai faru ga Sa'adha?
****
WAYE SHI?
AYSHA SHAFI'EE
43
(☆_☆)
"Munyi waya dasu Inna, kowa yace a gaishe ka."
Nanne ta fad'a tsaye a gaban Imran wanda yake zaune a hannun kujerar falo, kusan awarsa guda kenan da dawowa gidan amma banda waya ba abinda yake yi, zata iya k'irgawa yayi waya da kusan mutane sun kai goma kuma duk daga kamfaninsu, umarni yake ta bayarwa na yadda zasu k'arashe ayyuka kala-kala sannan a lokaci guda kuma kamar yana neman izinin wani abu daga wajen wasu manyansa.
Bata san meya faru ba ko kuma me yake faruwa ba tun jiya da ya dawo a gigice, lokacin da yake tambayarta me ya sami zuciyarta da kuma sanda ya kaita asibiti, ita ta san ba abinda ya same ta amma daga yadda taga ya damu, sai zuciyar tata ta fara kokwanton ko dai akwai abinda ya same ta ne, tunda sau da yawa a gida ma inna ce ke fara gane rashin lafiyarta kafin ita ta fahimta, musamman in zata yi zazzab'i.
Amma tunda likitan nan ya tabbatar musu da cewa a yadda suka aunata bugun zuciyarta ne kawai ya sauka k'asa kad'an mamaki ya kamata...ta yaya Imran ya iya gane hakan? ta yaya mutum zai iya gane abinda ya sami zuciyar wani ba tare da an gwada ba? tayi tunanin zaiyi mata wani bayani bayan sun dawo amma taga ya d'auko aiki a computer ya fara, kuma daga yanayin fuskarsa tunda yamman ta fahimci baya buqatar yawan magana saboda haka tayi shiru da tunanin zasu yi maganar washegari.
Sai gashi ta tashi baya nan sai tulin takardunsa a ko'ina, notes d'in da basu nuna mata ainihin lokacin daya bar gidan ba, tunda wajen k'arfe biyu na dare ma ta farka ta ganshi a kusa da ita.
Yanzu kuma k'arfe tara na safe ya dawo da alamun gajiya fal! a tattare dashi amma tun shigowarsa daya zauna a hannun kujera bai tashi ba, danne-danne kawai yake yi a waya yana lalubo numbobin mutane. Duk abinda tazo ta gaya masa sai yace mata yana zuwa, sai dai har ta gama dukkan harkokinta bashi da alamun tashi daga wajen.
Saboda haka tazo ta tsaya a gabansa da sak'on dake cin zuciyarta tun tashinta a yau da suka yi waya da dasu Inna, Sadiq ta fara kira kasancewar number Innan a kashe take, suka gaisa dasu Surrayya abin mamaki harda Aunty Amarya da kuma Salim, amma banda Suraj uban 'yan cusguna, wanda ta tabbatar kuma yana tare dasu a lokacin, a hanyar kaiwa Inna wayar ya had'u da Mama Azumi itama suka gaisa, a cikin d'akin Inna kuma Mama halime taje gaisheta itama ta karb'i wayar, daga k'arshe tana jin muryar Inna hawaye ne suka fara zubo mata, masu d'umi da bata san tayi tanadinsu ba sai a lokacin.
Imran ya kamo hannunta a hankali yana cigaba da aika message d'in da yake a waya, sai da ya tura sannan ya d'ago da kansa daga kan screen d'in ya kalle ta.
Nanne taji numfashi ya zarce cikin makogwaronta, ta gagara janye idanunta daga cikin nasa, wanda dogwayen gashin jikinsu yayi musu rumfa, hakan yasa a kullum suke da wani irin yanayi dake tsaida tunaninta, yanzu kuma da yake cikin damuwa sai suka juye zuwa kamar na mai jin bacci, ko kuma wanda ake cewa drunken eyes d'innan, D'an tafiyar da yayi kawai tsakanin tashinta da yanzu taji tayi kewarsa fiye da zatonta. Mata nawa ne wai a duniya suke yin sa'a irin tata?
"Ina amsawa sosai Noory, yau kika kirasu?"
Muryarsa a hankali ta fita, kamar wani mai jinya, dole akwai wani abu daya same shi wanda ya kamata ta sani.
"Eh, d'azu muka gaisa dasu harda su mama halime, kowa na gaishe ka."
"Nima ina gaishe su, duk da ina jin gobe ma zamu je muyi musu sallama."
Mamaki ya fito a fuskarta sosai.
"Sallama? wani wajen zamu je?"
Ya murza 'yan yatsunta a hankali.
"Wani wajen nake tunanin zamu je, but I'm not yet sure Sa'adha, na kasa tsaida tunani na waje d'aya...abubuwa da yawa sun had'e min a cikin kaina, and It's like I'm scared of all of them!"
Tayi shiru tana juya zancen nasa, kamar lokuta da yawa a baya, bata cika fahimtar duka maganganunsa ba.
"Me yake faruwa toh? na zata zaka min bayani tun jiya da muka dawo shi yasa ban tambayeka ba, gashi kaima kuma ka canja tun jiyan, kamar baka da lafiya, me ya faru?"
Taga giftawar wani abu a cikin idonsa kafin ya sunkuyar da kansa kan hannunta ya murza shi a hankali, Sau da yawa tasha tunanin ko Imran jinin sarauta ne, yadda yake abubuwa cike da isa, magana misali...kamar ka'ida ne yin shirunsa kafin ya amsa.
A cikin tunaninta taji ya janyo kafad'unta k'asa, ya durk'usar da gwiwoyinta a gabansa, sannan ya kalle ta sosai, kamar yana shirin fad'a mata wani babban Secret na rayuwarsa.
"Na tab'a fad'a miki cewa hannunki na da laushi?"
"Me yasa kake son canja zancen? ka gaya mun da Allah inda zamu je.."
Ta fad'a da murmushi tana kwace hannayen nata.
"Ni wa? Sa'adha ban tab'a ji fa kin kira suna na ba, ko sunan nawa bashi da dad'i ne?"
Ta kalle shi sosai.
"So kake in dinga fad'ar sunanka?"
"A'ah..." Ya sake kamo hannun nata.