Waye shi complete - Chapter 2
Waye shi complete Chapter 2: Waye shi complete Chapter 2. Abin ma yaso bawa nanne dariya, wai a cikin gidansu ake mata tayin abinci kamar taje wani bak'on…
4,496 words
Abin ma yaso bawa nanne dariya, wai a cikin gidansu ake mata tayin abinci kamar taje wani bak'on waje, abincin da a yanzu in ta tuburewa inna bashi take so ba, dole ta fad'awa mama azumi a canja in yaso wanda ba zai ci ba, ya nemi wani abin.
Ta girgiza kanta.
"A'ah mama taci abinta wallahi, a k'oshe nake."
Tana fadin haka ta juya ta bar dakin, sai dai kafin ta gama zura takalmanta taji sanda maryam ta furzar da wani abu sannan cikin muryar fushi tace.
"Meye wannan?"
Da murmushinta ta nufi falon aunty amarya, inda ta tarar gabad'aya yaranta na nan banda 'yan biyu da suka tafi wajen fitar da auduga, safiya da surrayya sun baje suna kallon wani film d'in larabawa, ta tab'e baki ganin yadda hankalinsu ya tafi gabadaya akai, ita abinda baya gabanta kenan kallo, don tvnsu ta dakin inna sai tayi kusan sati biyu bata kunna ba, tunda itama inna ba kallon take ba, sadiq dake can kan dining ya d'ago daga cin abincin da yake yi bayan su safiya sun amsa sallamarta.
"Kayan kika kawo a ledar? don wallahi na tabbata suna hanya yanzu."
"Sadiq na gaya maka ka fita harkata, don wallahi daga kai har kayan gabadaya sai in had'a in zage ku."
Ya kyalkyale da dariya harda buga table din gabansa.
"Na zata ai zaki ce harda mai kayan, tunda baki ji waccan shawarar dana baki ba bari in sake miki wata, kije ki canja kaya kisa masu nauyi-nauyi da zasu kare miki duka ba wannan fale-falen ba, don jawur zaki koma yanzun nan."
Taja tsaki kafin ta juya wajen surayya 'yar autarsu da bata fi shekara tara ba tace.
"Ina Aunty?"
"wanka take yi."
Kamar ta jira ta fito kuma ta tuna sadiq yace yanzun nan su suraj zasu dawo, kuma ba lallai ma ta samu wata tarbar arziki daga wajen Auntyn ba don haka tace.
"In ta fito kice nazo gaishe ta."
Har ta juya safiya mai bin sadiq ta tsaida ita.
"Yaya Aisha tace zata samu a gad'ar da cousins dinta zasu yi ranar kamu, in kina so ki fada mata kema ta saki."
Kamar tace mata eh kuma ta tuna rawa ce, daya daga cikin abubuwan da bata iya ba, saboda haka tace.
"Gaskiya bana jin inna zata barni."
Safiya ta gyada kanta sannan ta maida hankalinta kan tv. Dad'in nanne dasu kenan ita da surrayya basa taba mata rashin kunya ko wani abu, duk ko da cewar mahaifiyarsu bata sonta. Shi yasa itama take jin dadinsu musammam ganin sune kadai wad'anda ta girma a gidan.
Tana isa falon hajiya Babba ta tarar kanwarta mai suna Aunty hadiza da wata mata da bata sani ba sunzo ana lissafin adadin labulayen da za'a siya na gidan Aisha kasancewar sunje sun gano gidan.
Ta gaishe su suka amsa mata ba yabo ba fallasa sannan ta tambayi inda Aishan take, hajiya babba ta shaida mata tana dakinta, tayi zaton zata kirata ne don haka ta cigaba da zama a wajen, sai dai ga mamakinta kai tsaye hajiyan tace ta tashi ta shiga dakin.
Tun daga kofa take k'arewa dukiyar da aka narka a dakin kallo, tana iya tunawa shigarta ta karshe komai na dakin lemon green ne amma yanzu an canja zuwa milk and ash, gaskiyane da inna ke cewa ita kanta hajiya babba mai kudin kanta ce, su mama rabi kawai haukansu suke a gefe.
"A'ah daga nan, karaso mana."
Aisha dake kwance a gado tana waya tace da nanne.
"...zaka d'an ara min miti biyu?" ta tambaya cikin wayar, wanda suke wayar da ba tantama nanne ta fahimci wanda zata aura ne ya fadi abinda ya sata murmushi kafin ta katse kiran ta mike zaune.
"kina lafiya? Kwana da yawa?"
"Lafiya kalau." Nanne ta amsa da murmushi, a ranta tace 'ya'yan hajiya babba kenan, ko basa sonka baza su taba nunawa ba shi yasa a duk sanda ta gansu gaisuwar mutunci ke hada ta dasu, duk ko da kafin ta gansu din aiki ne, don ko ita Aisha da take mace sai tafi sati bata ganta ba don kusan kullum a makaranta take yini, balle kuma mazan dake aiki, kuma yawanci ma sunfi shiga dangin mamansu.
Daga nan bata ko kalli hanyar d'akin mama rabi ba wanda ke cike da mutane tayi kasa ta nufi kicin. Anan ta tarar gabadaya ma'aikatan gidan harda wanda ba b'angaren girki suke ba anata hada hadar abinci kala-kala da kuma snacks fal duk cikin umarnin mama rabi.
Ta wuce can karshe inda mama azumi dasu lami ke packaging wasu snacks d'in a foil paper.
"Farar mace alkyabbar mata, balle kuma in tasa jan kaya, haba wa!."
"Kai mama azumi, kema ai jan kayan ne a jikinki."
"Yo ke kya had'a fatar budurwa data tsohowa irina."
Tayi murmushi sannan ta mik'a mata ledar.
"Gashi inji inna."
"Me muka samu....kinga kanwa mai kyau wallahi, a ina ta same ta haka?"
"Wa ya sani...." ta fada tana d'anewa kan durowar data zagaye k'aton kicin d'in, bata ko kalli su lami ba dake ta faman d'auke kai suna maganganu don su nuna kamar basu ganta ba.
"...Naji kamar tana kawo mata akayi. Mama azumi a d'an zubo min kad'an yunwa nake ji."
"Kai uwata, na san fa tare kuka ci tuwon nan da inna, ina yunwa ta isa ta kamaki?"
"Toh dan Allah a d'an bani ladan k'anshin da naji."
"Haka dai zaki ce, kuma wannan ai ko baki fad'a ba."
Ta yago foil paper dake hannunta ta shiga zubo mata su samosa da meatpie wadanda ke cike taf! da nama bisa umarnin mama rabi. Tana ci suna hirarsu da tare, don dad'i sai shilla k'afafunta take yi tana zuba santi wanda kesa mama azumin dad'a tsokanarta.
"Toh ga fa 'yan gona nan sun dawo."
Mama azumi ta fada tana duban windon dake bayanta, nanne na juyawa ta ci karo da samarin gidansu kaf! Su tara, har kuwa da yaya Ahmad da yaya ibrahim masu aure, sun sako baffa a tsakiya kowanne cikin shadda mai kyalli da hula kalar kayansa, baffan sai murmushi yake yana yiwa ya Ahmad magana, idonta ya kai kan 'yan biyu da suka yi ankon shudiyar shadda daga gefen yaya umar, kamar kodayaushe suraj ya had'e girar sama data k'asa kamar me shirin lailayo zagi, ta inda ake gane su da salim kenan don shi ba laifi yana da d'an sakin fuska.
Cikinta ya bada k'ara lokacin da tayi saurin juyowa don kar su ganta, mama Azumi kuwa sai fadi take.
"Masha Allah, masha Allah...Allah ya bawa kowannen ku zuri'a irin haka kuma."
Ta had'iye abinda ke bakinta kafin tace.
"Haba dai in kowannensu ya sami 'ya'ya irin haka, ai ina jin sai mu shiga tarihi a matsayin zuri'ar da suka fi kowacce yawan haihuwa."
"Yo ai ba abin gudu bane uwata, 'ya'ya fa suna d'aya daga cikin rahamomin duniya."
Daga nan ta juya tana bawa su lami odar a shiryawa 'yan mazan abinci don ta san yanzu kowannensu zai fice ganin mata sun fara cika gidan.
Nanne ta dad'e a kicin d'in tana ta ganin hada-hadarsu kafin Rahma tazo ta tarad da ita.
Rahma ita kadai ce k'awar da take da ita bayan kawarta ta makarantar boko Amina, jikar d'aya daga cikin tsofaffin ma'aikata gidan ce wadda ake kira da hajiya, a yanzun haka ita hajiyan ta rasu sai babar rahman ce ta maye gurbinta kasancewarsu masu k'aramin hali, wanda a yanzu shekara biyar kenan tun rahman na 'yar karama take zuwa da ita har ta fara wayon da take d'an kama mata wasu abubuwan, dalilin da yasa ma kenan ya zama kullum tare suke zuwa, don gidansu ba nisa daga nan.
K'awancen nasu ya fara ne tun suna k'anana lokacin da kowannensu bai san ciwon kansa ba, in sunzo za'a had'u dasu zainab da nannen ayi ta wasa wani lokacin ma har da sadiq da yazama sune sa'anninsa. Sai dai tsakanin nannen da rahma ne kawai abotar ta d'ore saboda ita rahman tana da tsananin hakuri, tana jure duk wani rashin mutunci da abubuwan da nannen ke saka ta har zuwa yanzu da don kanta take ragwanta mata ganin irin hak'urin da take yi da ita.
"Wai tun d'azu dama kinzo ina nan inata jiranki?"
"Kiyi hakuri yau aikin gidan ne da yawa, kin ganni ko hijabi ban cire ba wallahi tun zuwanmu."
"Toh ya zancen zuwan? Zamu je fa."
"Ki bari dai zuwa d'an anjima in anci karfin aikin, yanzu in na tafi mama zata iya yin magana."
"Saboda ke sai a kasa yin wani abin, kin san fa anjima 'yan kawo lefe ne zasu zo, gidan k'ara cika zaiyi."
"Toh bari in gaya mata inji."
"Ki dai wanke hannunki bari inje in d'auko mayafina."
Ta mik'a mata ragowar meatpie da samosan hannunta kafin ta diro k'asa.
"Nagode." Ta k'arb'a da murmushi.
Nanne na d'age labulan kofar d'akinsu tayi turus! Ganin 'yan mazan gabadaya sun baje a cikin falon, inna na daga tsakiyarsu tana ta washe baki, kowannensu kuwa ya d'ago ya kalli kofar d'akin harda yaya sulaiman dake maitar danna waya.
Ta had'iye yawu lokacin da yaya Ahmad ke fad'in.
"Ke dama kina nan?"
Duk da da gabanta dake fad'uwa a ranta saida tace.
"Ina zani nida gidan ubana."
Tayi kamar ta juya ta koma amma muryar hadiza ta katse ta daga baya.
"Zamu wuce."
Ta juya ta gansu kusan su biyar d'auke da manyan-manyan tire shak'e da kayan abinci.
Ba musu tayi cikin d'akin, sannan ta dan durkusa ta gaishe su lokacin da ake ta faman dire musu abincin.
"ke zo nan!"
Tar! muryar suraj ta kirata a cikin hayaniyar da aka fara ta zuba abincin, ba damar tace bata ji ba don saboda wani tsautsayi yana magana ta kalle shi.
"An shanya min kaya a baranda jiya kuma daga nan ba'a gansu ba."
Ya fada kamar mai bata labari bayan ta isa gabansa, zuciyarta cike da tsoro ta daure tace.
"Toh ni meye had'ina da kayanka?"
A cikin hayaniyar nan suka tsinci muryar innan na fad'in.
"Surajo me tayi maka ne?"
Bai ko bi ta kanta ba yace.
"Kije ki d'ebo min su yanzu kafin in mik'e in fasa kanki." ya fad'i kalmar fasawar kamar zata fashe da bakinsa.
"Ban gane ba, kana nufin ni na d'auka? Toh ni ba barauniya bace, kuma ko zanyi sata ma sai in k'are a kayanka..."
Kafin ta rufe bakinta kuwa taji saukar wani azababben mari a fuskarta wanda ya taho tare da salatin inna.
"Kai meye haka?"
Yaya Nasir da yaya umar suka had'a baki wajen fad'a, nanne ta rusa wani irin kuka da rabinsa na k'arya ne.
"Me tayi maka?" ya muhammad ya tambaya, kafin ya amsa kuwa inna ta karbe.
"Me ko zata yi masa banda tsananin azaba irin tasa."
"Nace me tayi maka?" ya muhammad ya sake tambaya.
A dak'ile ya amsa.
"Yaya kayana na shanya a courtyard ta d'ebe."
Kafin a tambayeta nanne ta k'ara rushewa da kuka tana fadin wallahi tallahi k'arya yake ita ba abinda ta dauka.
"Kai dama tana d'aukan kayan ka ne?" yaya Ahmad ya shigo zancen.
"Ba wai tana d'auka bane, na san ita ta d'auka don ita kadai ce a wajen lokacin da aka shanya."
"Toh ai hakan baya nufin ita ta dauka...ke kuma kar in sake ji kince k'arya yake, tashi ki tafi."
Dama abinda take jira kenan, saboda haka yana fad'a ta mike tayi ciki.
"Guda nawa ne kayan?" Taji yana tambayar suraj bayan ta shiga d'aki.
Ta wanke fuskarta sannan ta yafa d'an karamin mayafi lightbrown akan doguwar rigar, ta nufi wajen kayan wankinsu ta janyo kayan suraj d'in dake can k'asa ta cusa su a bak'ar leda tana fadin..
"Kai da kayan nan har abada wallahi."
Ta fito har a lokacin suna hayaniyarsu ana ta dariya, kanta a mik'e ta fita, Allah yaso idon inna bai hango ta ba lokacin ta juya tana ganin adadin abincin da yaya ibrahim ke zuba mata.
Tana sauka k'asa ta tarar Rahma na jiranta a bak'in k'afar bene.
"Me tace?"
"Tace dai kar mu dad'e, don wai an tafi markad'en Alala zamu yi k'ulli."
"Ai dama ba dad'ewa zamu yi ba, abinda ya kaimu kawai zamu yi."
Ko dai abinda ya kai ki. Rahma ta fad'a a zuciyarta.
Don inda zasu je d'in gidan wata 'yar islamiyarsu ce Hafsa, a sati biyun da nanne bata je makaranta bane hafsan ta tada ballin cewa nanne na neman kwace mata saurayinta, wanda kullum aka tashi zai zo ya raka ta gida. Ta dinga masifar cewa wai duk sanda aka tashi sai ta dinga binsa da kallo wani lokacin ma harda murmushi.
Abin ya zama topic d'in ajin nasu kullum sai an tada zancen da za'a zazzage ta, ganin ma taki dawowa yasa suka rubata takarda aka gaya mata bak'ak'en maganganu sannan aka bawa safiya ta kawo mata shekaranjiya da yamma, jiya kuma ta titsiye rahma sai da ta gaya mata dukkan abinda yake faruwa da bata nan.
"Zamu biya ta shagon khalid kafin muje."
"Wane khalid?"
"Mai shagon bakin titi mana."
Khalid irin 'yan karyar samarin layin nan ne da ba abinda suka sani sai d'aukan wanka, iyayensa masu rufin asiri ne daidai nasu, amma shi inda yake kai kansa yafi haka, shagon da yake dashi ma na soft drinks da recharge card wani Alhajin layinsu ne ya bud'e masa. Dalilin haduwarsu da nanne kenan wajen siyan lemo.
Suna isa kuwa ya tsuke bakinsa yana murmushi, kafin ya fito ya fara shafa sumar kansa irin ta fulani.
"Kin b'uya fa, kwana wajen shida kenan ban ganki ba."
"Shida?"... Ta zare ido tana kallonsa.
"Har wani kirgawa kake?"
"Sosai ma, ke d'in ai ta daban ce."
Ta tab'e baki kafin ta mika masa ledar hannunta.
"Kaga rik'e, kaya ne na kawo maka ban sani ba ko zasu yi maka?"
"waww! Ai ko nagode sosai zasu yi ma insha Allah..."
Ya d'ago ya kalleta, idonsa d'aya a kanne.
"Thank you, har na hango ni a ciki."
"Wai me yasa kika damu da Khalid d'in nan ne."
Rahma ta tambaya bayan sunyi gaba.
"Saboda bashi da matsala, kuma yana yin duk abinda nace."
Ta amsa kanta tsaye wanda kuma hakan ne, in dai mutum zai jure halinta ya kuma dinga yi mata biyayya toh fa zasu yi shiri dashi.
Rahma bata kara cewa komai ba, tunda ita ta san abinda khalid ke tunani daban ne, don har ya fara yad'awa a unguwa cewa nanne sonsa take yi, zaiyi auren jari.
●﹏●
WAYE SHI?
AYSHA SHAFI'EE
04
(☆_☆)
An kawo lefe kamar yadda kowa ya zata, akwati goma sha shida da kuma bayanin cewa bayan auren a can nijar jamilan zata zauna, anci an sha a gidan kamar gidan biki sannan kuma an tarbi mutanen nijar cikin girmamawa kafin su tattara su tafi wani guest inn dake bakin titin unguwarsu inda baffa ya kama musu d'akunan kwana. Su mama rabi an samu abinda ake so, wato lefen 'yarta yafi na kowa, don na Aisha guda goma sha biyu ne, nasu maryam da nafisa kuma takwas-takwas. Saboda haka sai washe baki take yi anata hidima.
Duk wannan abin ya faru ne bayan an gama tashin hankali da bala'i a gidansu hafsa, inda nanne ta rufe idonta ta zage ta tas! a gaban 'yan gidansu, ba don rahma bama da abin ya kaisu harda kokawa don sun tarar maman su hafsar da kishiyarta basa nan sai 'yan matan gidan kawai, amma duk da yawansu ba wanda nanne ta kyale a cikinsu, sai da rahma taga abin zai koma kokawa sannan ta jata da kyar suka bar gidan.
Suna zaune bayan sallar isha a barandar dake kofar kicin itada Rahman dake b'arar maggi, ta sake yin kwafa tace.
"Na rantse da Allah rahma don dai ba zan iya kula wannan jagwal din yaron bane, amma wallahi da sai yarinyar nan ta zama 'yar kallo tsakanina dashi sai na mayar mata da tunaninta ya koma gaske."
"Dan Allah ki bar maganar nan, tunda dai kinje kin ja mata kunne ai komai ya wuce."
"Ba abinda ya wuce, in dai bala'i ne yanzu aka fara, saboda da sai wani satin nake tunanin komawa makarantar, amma wallahi ranar asabar d'in nan zanje muyi ta da sauran 'yan iskan k'awayen nata da suke biye mata, sai naci mutuncinsu d'aya bayan d'aya."
"Kin san fa malam murtala ya dawo, wallahi aka kai masa ku kuna fad'a ba zai muku da sauki ba, don ranar litinin d'in nan kusan bulala talatin yayi wa su Anisa."
"Ko d'ari zaiyi min wallahi sai nayi musu kacakaca a ajin nan..."
Ganin bata da niyyar sauka yasa ta karkato da farantin kan cinyarta tace.
"Allah ya kaimu asabar d'in toh....yanzu dai d'an taya ni b'arar maggin nan."
Suna cikin yi, rahma ta sako mata zancen saurayinta daya nace akan zai turo iyayensa, ita kuma ta dage sai ta gama makaranta tukunna tunda dama ss3 zata shiga yanzu, tare dasu nannen.
"Toh wai meye? Tunda dai mamanki ta yarda dashi ki bari ya turo mana."
Rahma ta kalleta da murmushi.
"Kalli wadda take cewa ba wani abu bane, ke da har yanzu ba wanda kika taba saurara...kuma kin san in dai za'ayi auren zainab baffa dake zai hada tunda ba dole sai kun fara jami'a ba, gashi ita tana da wani."
Nanne ta tabe baki.
"Nifa na gaya miki harkar samarin nan duk wahala ce, ni in zanyi auren ma cewa baffa zanyi kawai ya zabo min babban mutum mai hankali, don duk samarin nan 'yan duniya ne."
"Haka dai kike gani don baki taba tsayawa kin saurari wani ba, ga masu son miki magana da yawa."
Da jin haka, idonta ya hango mata fuskarsa, wani mutum guda daya da ta kasa cire shi daga tunaninta, tun ranar data fara ganinsa har yanzu da baya nan, yanzu da take jin kamar tana kewarsa, kewar yadda take ganinsa tsaye a kofar gidansu duk sanda ta dawo daga islamiyya, a saman mota yana danna waya ko tare da abokansa.
Yawanci iya haduwarsu kenan, sai ko da safe wani lokacin in zasu makaranta ta hango shi ya dawo daga morning training, ita ko sanin gabadaya 'yan gidansu ma bata yi ba don bata taba shiga ba, duk da cewa yanzu zasu yi kusan wata hudu da dawowa, kuma wata k'anwarsa ma sun saba da safiya don ta shiga islamiyarsu.
"Wai tunanin me kike?" Rahma ta katse ta.
"Ba komai, me kike cewa?"
"Wannan purple jakar ta lefen aunty jamila tayi kyau sosai, kinga d'an flat takalminta kuwa?"
Daga nan ta shiga santin abubuwan ciki, wanda a lokacin da ake d'agawa ita nanne hankalinta ya tafi wajen zirawa Aunty nanah (k'anwar mama rabi) fara cikin rigarta, don sun kusa yin karo da ita a hanyar bene ta zageta har tana fad'in tayo halin rashin mutunci irin na Nuratu mahaifiyarta.
Ai kuwa ba'a gama ganin kayan ba, ta hau make-make a jikinta, kafin ta tashi da gudu tayi d'aki.
***** *****
Sati d'aya bayan haka rayuwar gidan ta cigaba da tafiya tare kuma shirye-shiryen biki daga kowanne b'angare, don kuwa kowa ya dage wajen ganin bajintarsa tafi ta sauran saboda wata guda ne kawai ya rage ayi bikin, baffa ya saiwa kowacce amarya dank'ara-dank'aran gadaje guda biyu da kuma furniture saitin kujeru suma guda biyu, sai manyan-manyan tvn plasma da sauran kayan saitinsu.
Sauran abubuwa irin na kitchen da kuma k'arin wasu abu na ado wannan duk na iyayensu mata ne, sannan ya bawa kowacce a cikin matan nasa dubu d'ari tasa gudunmawar don yaga take-takensu na cewar bayan events d'in daya had'a za'a yi gabad'aya, kowacce na shirin kama waje tayi wani bikin da 'yan uwanta. Hatta Aunty amarya saida ya bata dubu hamsin yace tayi d'inki itama da 'ya'yanta. Don haka a kowacce rana gidan cike yake da mutane na 'yan uwa dake zuwa anata faman hada-hada tsakanin gidan da kasuwa.
A lokacin an koma makarantar boko daga dogon hutun da akayi na sabon zango, wanda su nanne suka shiga aji shida itada sadiq da zainab, safiya kuma na aji uku, surrayya ce kad'ai a ajin na k'arshe a primary. 'yan biyu kuma sun sami abinda suke so sunyi candy, sai aikin baccin safe kamar baza su tashi ba, da yamma kuma su tafi ball ko yawon eatery da abokai.
Da safe nanne na zaune a falo ta hard'e k'afa d'aya kan daya tana shan tea, uniform d'in makarantarsu ne a jikinta na farar riga da bak'in wando, ba d'ankwali a kanta sai jelar manyan kalbar da rahma tayi mata sun zubo har k'asan kafad'arta.
Inna ta juyo ta kalleta daga kan sallayarta data gama lazumi.
"Yanzu nanne baza ki dubi girman Allah da magiyar da nake miki ki tsefe kalbar nan ba? Tafi sati biyu fa akanki."
Ta yamutsa fuska.
"Inna na fad'a miki sai na wanke kan ne kafin in sake kitson kuma wankin wahala yake bani, so nake in samu lokaci inje saloon tukunna."
"Ai shikenan. sai kiyi ki gama kafin su fara jelan kiranki."
Tana rufe baki kuwa safiya ta shigo falon, ta durkusa har k'asa ta gaishe da innan sannan tace.
"Nanne tun d'azu fa muke jiranki, kowa ya fito kuma yaya umar ne zai kaimu yau."
"Yaya umar?...ina idris d'in?"
"Wai ya aiko bashi da lafiya."
"Toh maza tashi, don kin san halinsa." inna ta fad'a da sauri.
Ta zura hijabi sannan ta dauki jakarta tare da safa da dankwali tabi bayan safiya, tun daga waje sadiq dake zaune a gaban sienna da ake kaisu ya langwab'e kai yana mata murmushi, hakan ya tabbatar mata sun dad'e suna jiranta kenan.
Suna isa safiya ta shige baya sannan ta zauna a kujerar gefen surrayya ta rufe kofar motar, umar ya ajiye tab d'in da yake dannawa a gefe sannan yayi magana ba tare daya juyo ba.
"Ke kina jina?"
"Eh." Ta fada kanta tsaye.
"Idan kin dawo kije wajen mama Azumi ki karbi key din d'akina, ki gyara shi tas! Ki wanke band'akin, sannan kuma for the whole week ni zan dinga kaiku makaranta, idan kin ga dama ki bari kullum in dinga riga ki shigowa motar nan."
Yana gama fad'in haka yaja motar suka yi gate, ta had'a ido da sadiq ta cikin mudubi ya sake sakar mata murmushi motsin fatar bakinsa na fad'in 'yan mata! Ta gallara masa harara kafin ta sunkuya saka safarta.
Suna isa makarantar ta tarar har malami na farko ya shiga, wata malamar biology mai tsanani rashin son surutu ta juya kan allo tana rubutu, bata bari ta ganta ba ta shigo a hankali ta wuce bencinsu ita da Amina, dukkan 'yan ajin na kallonta ba wanda yayi magana, don duk da cewa ba tsoronta suke ji ba kowa yana d'an shakkar surutun ta, irin dai karar da akewa mutum mai baki.
Tana zama Amina tasa hannu ta cusa mata jelar gashinta da ta fito ta gefe. In da akwai abinda ya banbanta halin nanne da Amina to rashin kunya ce, saboda ita magana ce kawai da ita amma bata da rashin kunya irinta nanne.
"Ya akayi yau kika zo da wuri?" ta tambayeta a hankali.
"Azababben yaya umar ne ya kawo mu wallahi."
"Ina idris d'in?"
"Wai bashi da lafiya."
"Kice kin daina missing first period."
Taja guntun tsaki.
"Wai a tunaninsa ma fa haka na makara ban fito ba."
Amina ta d'anyi dariya kafin tace.
"Zaki saka mai wani sabon tunanin ne."
"Ke bari a fita break, akwai maganar ma daza muyi."
"Haba? Ko munyi first catch ne?"
Ta juyo daga kokarin d'auko littafin da take, ta gallara mata harara.
"Ke dai 'yar iska ce, baza a taba wani abu a duniya ba sai saurayi."
A daidai nan malamar ta juyo ta kalle su.
"Surutun me kuke yi?" Ta tambaya da turanci.
Kai tsaye Amina ta d'ago tace.
"Malama rasuwa aka mata ne shine nake mata gaisuwa."
"Ajin nawa ne gidan gaisuwa?"
Ta sake gyara murya tace.
"Ma, ai yadda mutuwa take zuwa ko'ina haka gaisuwarta ma ana iya yi a koina."
Ta kalle ta da mamaki kafin ta nuna musu hanyar kofa.
"Toh ku fita waje kuyi zaman makokin."
Inda sabo dama hakan yasha jawo musu fitowar bakin aji, don Amina irin mutanen nan ne da basa taba rasa amsar fad'a, ko waye mai tambayar kuwa.
Har sun kai k'ofa ta tsaida su da tambayar waye ya rasu, Nanne tayi rau! da ido kafin ta amsa da kazar da take kiwo ce, abinda ya jawo dariyar gabadaya ajin kenan wanda ya jawo musu kneel-down a gaban aji, next period ma english ba suka shiga aji ba, tunda malaman k'awaye ne haka suka zauna har aka fita break.
Da break d'in ma basu samu damar maganar ba saboda haduwa suka yi da 'yan click dinsu akayi ta hira kala-kala, wata maryam tayo musu dan malele ana sha ana cafta. Bayan an kada kuma suka tafi wanko farantan da suka aro a kicin din makarantar, suna dawowa kuma aka tafi physics lab, suka ci uban note sannan aka fara practical, last period ya kasance geography ne, wani malami mai azabar dictation shima.
Sai da aka tashi sannan suka tsaya daga k'asan wata bishiya a harabar parking lot din inda ake d'aukarsu. Nanne ta kalli Amina sosai tace.
"Ta yaya aljanu suke shiga jikin mutum?"
Amina ta d'an had'e girarta.
"Ban gane ba, nifa ba malama bace."
"Dalla ina nufin kamar yanzu ni in inaso aljanu su shiga jikina me zanyi?"
"Sa'adha aljanu? Me zaki yi dasu?"
"Wani malami nake so na waskawa mari a islamiyarmu."
"Me yayi miki?"
"wai kawai daga cacar baki ta had'a mu da wasu mahaukatan yara a aji, ya kama ya mana bulala ashirin-ashirin."
"Toh kiyi na k'arya mana, me zai sa ki jawo wa kanki bala'i?"
"Malamin ne mugun d'an izala ne, yanzu sai ya iya ganewa."
"Wallahi ba ta yadda za'ayi ya gane tunda aljanu dai ba ganinsu ake ba, kuma a yadda na sanki zaki iya, kawai abu d'aya ne kar ki tab'a bari ya dake ki da sunan ruk'iya tunda kin san ke za'a jibga."
Ta d'anyi shiru tana tunani.
"Kuma fa hakane, ba dai ihu ake ba da zare ido?"
"Sannan ki cire d'ankwalinki ki tsaida idonki tar! ko waye yazo kar ki nuna kin sanshi ma balle wani tsoronsa, ki zagi duk wanda kike so kuma."
Nanne ta tsaida idonta waje d'aya, tunaninta na hasko mata ita a hoton da Amina ke zanawa.
**** ****
BAYAN SATI BIYU.
Da maghriba ta dawo daga bayan layinsu gidan wata hajiya talatu, ta karbowa inna tarin adduwa a cikin bakar leda wai ta gaji da cin goro. Tana tafe tana cilla ledar a hannunta, layin ko'ina da haske saboda wuta da aka kawo a lokacin kuma babu mutane da yawa, daga tsillin masu wucewa sai masu gadin gidaje da suka fito waje da 'yar rediyonsu.
Cilla ledar da zata sake yi sama sai kawai ta yage a daidai sanda ta karyo kwanar layinsu, gabadaya adduwar ta tarwatse wasu ma suka shiga gangarawa cikin kwalbatin dake gefenta, taja karamin tsaki.
"Ai wallahi dama na san sai ledar nan ta yage, matar nan tana tab'a bada wani abin arziki ne?"