Kenza eBookz

Waye shi complete - Chapter 20

Waye shi complete - Chapter 20

Waye shi complete Chapter 20: Waye shi complete Chapter 20. Imran ya fad'a tsaye daga bayanta, suna tsaye daga wani balcony da ya fito ta cikin falon inda…

4,496 words

Imran ya fad'a tsaye daga bayanta, suna tsaye daga wani balcony da ya fito ta cikin falon inda akayi wani d'an karamin pool da aka jawo ruwansa daga cikin tekun sannan ga grass carpet mai taushi da kuma flowers da fitilu masu haske kala-kala a wajen, wajen yayi kyau it felt like a dream to her! Har yanzu gani take kamar ba da gaske itace a wajen ba, kamar zata iya bud'e ido a kowanne lokaci ace mafarki take yi.

Dazu taga k'ofar amma bata tab'a tunanin cewa wani wajen ne ba, tayi zaton toilet ne ko kuma d'an store kawai. Bata san sanda ta juyo da sauri ta kalle shi ba tace.

"Please Ulfat zamu zauna anan har abada?"

Ta fad'a tana kifkifta masa idonta alamun rok'o.

Yayi dariya mai zurfi yana kallonta.

"In kina so me zai hana, amma me zaki cewa su Inna?"

Inna. kiran sunan da yayi ya sata tuna cewa bata kira su ba.

"Ya salam! Ayunie ban kira su ba, ya kamata ace na kira su na fad'a musu inda muke tunda muka sauka."

Yayi saurin rik'ota sanda take kokarin komawa ciki.

"Kin san k'arfe nawa yanzu?"

Ta janyo d'aya hannunsa dake rik'e da wayarsa ta kalli agogon.

"K'arfe tara fa ai bata kwanta ba yanzu."

"Wannan setting d'in k'asar nan ne saboda na canja Sim amma k'arfe hud'u na asuba yanzu a Nigeria."

"Huh..?" Ta ware ido tana kallonsa.

"Ko so kike tayi tunanin wani abun?"

Ba tace komai ba ya sunkuyo da kansa daidai fuskarta.

"Zamu kira ta first thing zuwa gobe, yanzu kin gaji da yawa Sa'adha, kije kisa ruwan zafi a jikinki kizo mu kwanta."

Ya Allah, kunya ta kamata sanyin iskar wajen gabad'aya yasa ta manta da wani abu wai shi wanka. Ta d'aga kanta a hankali ba tare da ta kalle shi ba.

A minute alone would be perfect!

"Ko muje ne in taya ki?"

Bata san sanda ta kalle shi da sauri tana zare ido ba, ya sake yin dariya cikin husky voice d'insa, sannan yasa kansa cikin wuyanta, wani waje dake fitting d'insa perfectly.

Ya rad'a mata wani abu da muryarsa data koma can k'asa yadda taji kamar yana lasar fatar jikinta ne, taji k'afafunta sun daskare a wajen kamar k'ank'ara, tunaninta ya gwamutse a lokaci d'aya kuma kwakwalwarta ta kasa tab'uka wani tunanin.

A haka yaja hannunta suka koma ciki har bakin toilet d'in.

"I'm waiting for you." Yaja saman hancinta sannan ya juya ya koma ciki.

Tabi bayansa da kallo kafin ta tattaro dukkan k'arfinta taja numfashi cikin k'irjinta, sannan ta kalli kafad'arta don taga ko ta kama ne da wuta, don hakan wani abu ne da Imran bai tab'a mata ba, kullum tana jikinsa amma tun lokacin da ta tashi da wannan marks, ya daina mata irin wannan abubuwan. Taji a cikin ranta cewa wajen zai k'ara kusanci a tsakaninsu.

Babu wutar a kafad'arta, atleast babu a fili sai ta cikin fatarta da take jin wajen kamar an d'ora gaushi, ta lalubo jakar toiletries d'inta sannan ta koma toilet d'in, sai dai tana bud'ewa taga ta manta brush dinta, saboda haka ta shiga bud'e drawers din anan wani mamakin ya kamata, akwai komai da aka san d'an adam na iya buqata a harkar toilet, brands kala-kala masu kyau bama irin na Nigeria ba.

Saboda haka ta zuge jakarta ta ajiyeta a gefe, don ba ta yadda za'a had'a kyan kayan da nata, ta d'auko wani shampoo mai ainihin k'amshin extract d'in strawberry ta wanke gashinta tsaf sannan tayi wanka, shi kansa ruwan wani irin santsi ne dashi akan fata, bayan ta gama ta d'auko wani katon towel a cikin drawer ta nannade jikinta sannan tasa wani karami ta tsane ruwan kanta, ta jona hand dryer ta taje gashinta, yayi d'umi ya kwanta smoothly har gadon bayanta.

Sanda ta fito ta bud'e akwatinta, wani mamakin ya kamata, gabad'aya kayan da ta san ta jera da hannunta babu su, instead kayan da bata tab'a gani bane, k'ananan riguna da three-quarter skirts da wando, bayansu sai kayan bacci kala-kala masu mutuk'ar kyau.

Undies d'inta da kuma wasu dogwayen riguna uku na material sune kad'ai abinda ta sani nata. Ta fiffito da kayan, gabad'ayansu sababbi ne da tag d'insu, bata san yaushe ya siyo ba kuma bata san yaushe ya canja su da kayanta ba, ita kad'ai amma kunyar kayan ta kamata, ta tuno da abinda ya fad'a mata a gida.

"...bana jin ma duk wannan kayan zasu yi miki amfani sosai a can."

Da kyar ta iya zab'ar wata rigar mai gajeren hannu kalar Pitch da kad'an ta wuce gwiwa ta saka, Ta juya wajen mirrors d'in dake kan wani dogon counter a gefenta, ai kuwa tana kalla ta juya da sauri ta juyawa mudubin baya, gaskiya ba zata iya fita a haka ba, ita da ta saba kullum cikin dogwayen rigunan barcinta...ta koma cikin akwatin ta d'auko doguwar rigar material d'inta guda d'aya, toh ai kuma yanzu dare ne, ta yaya zata zumbula wannan rigar ta kwanta?

Numfashinta ya shiga fita kamar tayi gudu sannan hannunta ya fara rawa, sai kawai ta zauna akan sassayan tiles d'in d'akin ta cusa kanta a tsakanin k'afafunta, Zuciyarta ta shiga addu'ar kar ya gaji da jiranta yazo ya ganta, ta san in har ya ganta a haka shima hankalinsa zai tashi ne.

Zai yi tunanin she's freaking out saboda tsoronsa ne, ba zai yarda cewa she's freaking out saboda bata san ta yadda komai zai fara ba, ba zai yarda cewa shes freaking out saboda bata san ya k'addararta zata kasance ba lokacin da ta fita daga cikin d'akin nan.

Tana ji ne kamar zata fita cikin dubunnan jama'a wad'anda suke jiranta ba tare da ta san me zata fad'a ba.

Ta yaya ne mutane suke iya had'iye tsoro da kuma taraddadinsu su tunkari wani abun? ta yaya zata iya zuwa wajen Imran a yanzu?

Saboda kina son shi.

Zuciyarta ta amsa, Da ace ba imran bane ke jiranta, Da ace zuciyarta b ata riga ta amince dashi ba, da ace kowanne particles na jikinta basu san cewa yana sonta unconditionaly ba, ba zata tab'a iya daurewa zuciyarta ba, amma Ayuninta ne ke jira saboda haka ta rad'awa kanta cewar kar taji tsoro.

"Don't be a coward."

K'ofar d'akin ta bud'e a lokaci d'aya, lokacin da itama ta juyo daga kallon kanta da take a mudubi.

"Sulaiman ya kira ni yanzu, I don't know ke da inna wa yafi..."

Maganarsa ta katse lokacin da idonsa ya gano ta, kyawawan idanunsa suka sauka akan nata, sannan a hankali suka soma sulalewa zuwa jikinta, ya tako a hankali ya k'araso gabanta, sannan yasa hannayensa ya nannad'o ta cikin jikinsa. Tana kallon yadda mak'ogwaronsa ya motsa alamun ya had'iye wani abun.

"Kinyi kyau." Ya rad'a cikin kunnenta.

"Kinyi kyau sosai Mine!"

Ta k'ifta idonta hankali tace.

"Yaushe ka siyo kayan?"

Maimakon ya amsa mata sai ya d'ago hannunsa zuwa gashinta ya warware Bun d'in data k'ulle shi.

"I preffered your hair loose!" Ya fad'a cikin husky voice d'insa, muryarsa mai taushi dake d'auke hankalinta.

Zuciyarta ta buga da k'arfi sanda ya sunkuyo daidai fuskarsa yayi pressing lips d'insa a gefen bakinta.

Ya Allah!

Tunaninta ya d'auke gabad'aya, taji bakinta ya bushe sannan numfashinta ja fita da sauri, kamar zai janye gabad'aya ta suma, a cikin haka kwakwalwarta ta jiyo masa sanda ya fad'i wani abu, bata tabbatar ba amma taji kamar yace ne "Please" Sannan ya d'an tsaya kamar mai jiran wani abu, amma ta gaza yin komai, ta tsaya cak kawai hannayenta rik'e dashi ba tare da ta san me zata yi na, bayan wani d'an lokaci taji yana shirin d'aga kansa.

No! not so soon...!

Duk wani sauran tunaninta babu shi a lokacin, saboda haka tasa hannayenta dake rik'e da rigarsa ta janyo shi ya dawo...daga nan ta daina gane komai, magana d'aya kawai daya fad'a kwakwalwarta ta iya fahimta.

"If you feel something wrong...If I hurt you, ki gaya min at once."

Hasken ranar dake shigowa directly ta cikin windon shi ya tashe ta da safe. can safiya koma tsakar rana ne bata sani ba, Idonta ya bud'e tar tana ganin komai clearly, kuma ba sai tayi wani tunani ba ta san ina take, wannan farin d'akin mai k'aton farin gado, wajen tsit! k'ara d'aya ce kawai ke yawo, na kad'awar tekun dake waje.

Taji zata iya kwanciya a haka tsawon lokaci tana jin dadin yanayin, amma ba abinda ya dace kenan ba, a wani waje suke mai cike da d'imbin abubuwan da take d'okin gani, She'd to get up nd face all the wonders that awaits her!

Imran ya bud'e k'ofar d'akin ya shigo a daidai lokacin, sanye da wasu kayan bana jiya ba, annurin fuskarsa ya dawo mata da dukkan memories d'in da suka faru jiya, taji alamun kumaunta sunyi ja like she's blushing, and she wondered dalilin da ya kawo tsoronta da farko jiya, it seem silly a yanzu tama yi tunanin tsoro game dashi.

A lokaci d'aya ya k'araso kan gadon.

"Ka tashi lafiya" Ta fad'a a hankali tare da yin murmushi, maimakon ya amsa, sai ya kwanta a gefenta sannan ya jawo hannunsa yayi stroking a hankali.

Nanne ta kalli cikin idonsa, kalarsu ta canja daga bright zuwa wannan dark d'in alamun damuwa. Damuwa? me zai kawo masa damuwa a yanzu?

"Ayunie me ya faru?" Muryarta ta sake fitowa a hankali fiye da d'azu.

"Baki san me ya faru ba?" Sautin muryarsa was so deep sanda ya tambaya yana tracing hannunta kamar mai bin layin wani abun.

Ta k'ifta idonta a hankali tana kallonsa, sanda tunanin ko laifi ta masa yazo cikin kanta. kwalkwalwarta ta shiga lalube akan duk abinda ya faru jiya amma bata ga komai ba, ta shiga tace kowanne single memory da take iya tunawa amma ta kasa ganin wata tangard'a ko 'yar k'arama kuwa, to be honest komai ya tafi ne cikin sauqi ba kamar yadda ta zata ba, ita dashi sun dace ta hanyar data k'ara yardarwa kanta cewavana halicci kowannensu ne a matsayin abokin rayuwar d'aya, they fit together perfectly ta yadda har yanzu ta kasa gano abinda zai sa shi cikin wannan damuwar.

A hankali taji hannunsa yana tab'a tattarewar da fatarta tayi a tsakanin girarta..

"Tunanin me kike yi?"

"Tunanin abinda zai saka damuwa.."

"Wane irin ciwo kike ji a jikinki?" Yayi saurin katse ta.

"Ciwo...?" Fatar goshinta ta k'ara tattarewa lokacin da tayi focusing idonta akansa.

Jikinta k'alau yake in banda gajiya kad'an da take ji a wajen gab"ob'inta ba komai, sai ko damuwar da take yi a yanzu na yadda yake son b'ata safiyar da tafi kowacce a wajensu.

"Lafiyata k'alau Ulfat, ba abinda ya same ni I'm..."

"Shashshsh..." Ya katse ta tare da rufe idonsa.

"I'm sorry Noory, I made a mistake...Nayi laifin da nake jin na tsani kaina, dan Allah kiyi hakuri, I'm so sorry fiye da yadda zan iya fad'a miki."

A wannan lokacin tasa hannayenta duka biyu tayi cupping fuskarsa.

"Dan Allah ka gaya min me ya faru, me ka min? hak'urin me kake bani?"

Bai bud'e idonsa ba har a lokacin kamar baya son ganinta.

"Ayunie..."

Ta kira shi cikin wata irin murya kamar zata yi kuka. A hankali ya tattaro ta cikin hannunsa sannan ya mik'e tsaye, bai tsaya koina ba sai gaban mudubin nan ya dire ta cikin carpet d'in har a lokacin fuskarsa take kallo, a sannan shima ya bud'e idonsa da suka k'ara rinewa suka koma so dark sannan ya juya kafad'unta hankali tayi facing mudubin.

"Look at yourself Sa'adha."

Cikin umarnin idanunta suka tafi cikin mudubin sannan bugun zuciyarta ya tsaya a lokaci guda.

Marks, Bruises....bruises koina jikinta fal! ja jawur dasu kuma manya, gasu nan fal har wani na had'ewa da wani yadda ba wani sauran space da babu su.

Tayi burd'in-bird'in da ita!

●﹏●

WAYE SH?

AYSHA SHAFI'EE

51

So wannan itace longest chapter da na fara rubatawa a labarin man, hope you will enjoy it!😁

(☆_☆)

"Kayi shiru, I want to watch it quietly."

Nanne ta fad'a a hankali idanunta na kallon can gabansu, inda rana ke shirin fad'uwa, Tana kwance a jikinsa daga k'asan wata dogowar bishiyar kwakwa a bakin tekun dake ta ambaliya wani har yana tab'o kafafunsa dake mik'e.

A can gabansu rana ce ke shirin fad'uwa, wani abu ne da bata tab'a gajiya da gani tun zuwansu wajen, wani abu dake k'ara mata jin kamar ba'a cikin duniya take ba sannan wani dake k'ara k'arfin imani a zuciyarta...ranar tayi wani irin ja sannan brightness d'inta yayi reflecting a kowacce kusurwa ta yadda ya bada hasken rainbow, tana kuma yin k'asa a hankali kamar tana lumewa cikin makeken tekun dake gabansu.

A sannan satinsu biyu kenan da zuwa wajen, wani lokaci da Nanne tayi wa tambari a matsayi ranakun da suka fi kowanne farin ciki a rayuwarta, the most happiest days of her life!

Rayuwa ce ta kwanciyar hankali da nutsuwa, ba ruwan kowa dasu don wajen ba mutane sosai...saboda haka yadda zasu farantawa junansu rai shine kad'ai a gabansu.

Sun ziyarci wajaje da yawa har da wasu island d'in dake kusa da nasu cikin irin speedboat da suka zo, a yanzu Nanne ta riga ta kware a shiga jirgin don har rige-rigen wajen zama suke ita dashi wajen da a karshe dai su biyun ne zasu zauna, har cikin ruwan sun shiga amma ba can zurfi ba, gefe kawai inda 'yan k'ananan kifaye da kuma kunkurun ruwa suke amma sai da suka sa snokel tukunna, (Wani glass d'in ruwa dake rufe ido da hanci saboda shak'ar iska.)

Har da wani paddle na ruwa da ake tafiya a tsaye, abubuwa kala-kala yadda kullum suka fita sai rana ta fad'i suke komawa cikin cabin d'insu. Bayan fad'uwar rana kuma har fitowarta suke gani, Inran ya saka alarm a duk lokutan sallah saboda haka bayan sun idar da sallar asuba kullum zasu fito da overnight mat din da suka samu a cikin gidan su shimfidaa wannan balcony din na wajen pool, mat din na da laushi kamar katifa anan zasu kwanta suna facing fitowar ranar, yadda haskenta ke fitowa a hankali yana canja kalar duhun sama zuwa kamar royal blue da kuma shade d'in golden da kuma orange.

Sai dai a cikin kwanakin nan, Nanne ke fuskantar wani azababben barci da kusan kullum bata san lokaci da kuma inda yake d'aukarta ba, wani lokacin suna cikin cin abinci, wani lokacin suna zaune a falo, wani lokacin ma a cikin toilet kafin ta gama brush, sai dai ta farka da safe ta ganta a d'aki. Sau da yawa zaice mata ta huta kar su fita, amma tsananin d'okin ganin sababbin abubuwa shi zaisa tayi ta rok'onsa da magiya har sai sun shirya sun fita.

A yanzu bata da matsalar abinci don Menu guda suka kaiwa can wajen dake kawo musu abinci na irin simple-simple abubuwan da suka san zasu iya yi wanda su kuma zasu iya ci, don haka a kullum warmers d'insu cike suke da cima kala-kala, wani lokacin ma har sai an koma da wasu.

*******

Wajen k'arfe uku na rana, dawowarsu kenan daga waje, bayan sun bawa cleaning crew d'in wajen awa biyu na gyaran cikin cabin d'in nasu.

Nanne ta shiga wanka ta wanke fatarta tas! data k'ara wani sulb'i da haske a cikin kwanakin, bruises d'inta sunyi sauqi a lokacin sai dai basu tafi duka ba, har a lokacin akwai alamunsu a wani wajen, sunyi shade d'in pink kad'an.

Bayan ta fito ta saka wata 'yar k'aramar riga mai kyau dark pink da d'an short da bai kai gwiwa ba, a yanzu ta riga ta saba da duka kayan nan, kullum su take saw kala-kala har gani take da ta taho da dogwayen rigunanta ba lallai ta iya sasu kullum ba, tunda wanda Imran ya bar mata ma amfaninsu in zasu fita ne kawai, amna duk inda suka je tattare abinta take tasha iska da dogon wandon da take sawa a ciki tunda ba wasu mutane a wajen.

Tayi k'ok'arin b'oye murmushinta sanda idanun Imran suka zare bayan ta fito daga toilet d'in, amma cikin wucewar second d'aya yayi k'ok'arin controlling fuskarsa sannan yayi gyaran murya kad'an.

"You look beautiful Noory, kinyi kyau da yawa, kamar kullum!"

Ya fad'i abinda take shirin tambaya.

"Awwn..." Ta dunkule hannayenta a k'irji sannan ta d'an turo bakinta tana kifta ido.

"Thank you Ayunie." Ta fad'a sanda ta hau kan gadon da yake kwance yana karanta wata bussines magazine, ya mik'o hannunsa ya jawo ta jikinsa tayi hamma kad'an sannan ta d'ora kanta a kirjinsa.

"Yaushe zamu koma gida?"

"Har kin gaji? ke da kika ce mu zauna anan har abada."

Tana murza idonta da hannu d'aya tace.

"Wajen da dad'i Ulfat, amma ina missing su Inna."

"Kullum fa sai kunyi waya."

Ta turo bakinta kad'an. "Yau bamu yi ba."

Sai ya mik'a hannunsa gefe ya jawo wayarsa yana fad'in bari a kira su toh, ta rik'o hannun nasa da sauri.

"A'ah ba yanzu ba sai anjima, bacci nake ji."

"Bamu ci abinci bafa...I'm afraid bana feeding dinki sosai."

"You're trying, ka bari sai na tashi sai muci, na gaji yanzu."

Ya ajiye magazine d'in hannunsa ya sake kwantar da kanta a jikinsa.

"Ofcouse you're tired, Sleep, Love."

Muryarsa can k'asa ya fara mata humming wani lullaby a hankali yana shafa bayanta.

"Ban san me yasa nake yawan baccin nan ba Ayunie..." Ta fad'a a hankali idonta na shirin rufewa.

"...I hope hakan bashi da alaqa da kasancewarka ba mutum ba."

Yayi murmushi kad'an sannan ya cigaba da humming d'in.

"Tunda nake ban tab'a irin wannan baccin mai yawa ba, kuma akai-akai haka."

Ta sake fad'a muryarta so low. Humming d'in nasa ya tsaya a lokaci d'aya.

"Nima I was wondering, baccin naki yaso yayi yawa habibty, ba don minshirin da kike ba, har zato nake ko kin shiga Coma ne."

Da sauri idanunta suka bud'e, ta d'ago ta kalle shi.

"Wallahi bana minshari."

Ya d'age girarsa duka biyun.

"Har da rantsewa? ni da nake tare dake kullum? To ranar da muka zo nan da kika ji iska sosai, a firgice na farka na zata wasu ne suka tayar da inji."

Wani haushi ya cika mata wuya, bata san sanda ta wawuro pillon gefenta ba ta shiga maka masa, yana ta kyalkyaka dariya yana fad'in tayi hak'uri wasa yake yi!

****

BAYAN SATI BIYU.

"I'm sorry!" Jaamil ya sake fad'a karo na biyu yana kallon yadda tekun gabansu ke tambal-tambal cikin wani salo mai ban sha'awa.

Ganin Imran bashi da niyyar amsawa yasa ya juyo gefe ya kalle shi, suna zaune a wata kujera dake facing bakin tekun.

"Yarima." Ya kira sunan sa a hankali, maimakon ya amsa sai ya gyara zamansa ba tare da ya kalle shi ba yace.

"Ta yaya ka san muna nan?"

"Saboda na sanka, na san duk wani possibilities d'inka."

"Amma ka ture wannan sanin kake son biyewa plan d'in Naani? kake kokarin yin abinda ka san zai cuce ni?"

"Karo na uku kenan da nake maka bayanin cewa daga ni har Naani bamu yi wannan zancen don cutar da kai ba sai don kawai abinda muka tsara tun farko ya tafi daidai sannan a lokacin baka tsaya kaji ra'ayina ba yarima, ina fitowa ka shak'e ni da tambayoyinka."

Imran yayi ajiyar zuciya sannan yace.

"Naani ta sani?"

"I never told her, ta cigaba da tsarinta na yadda duk lokacin da ka kawo yarinyar zata raba ruhin da jikinta, a kwanakin baya ma ta kirani da saqon cewa in gaya maka zata nemeka nan gaba, saboda da farko ta gaya maka zata kira ka ne bayan sati d'aya."

"Ba zan taba kawo ta ba." Muryarsa ta fito kai tsaye.

"Na sani, amma ta yaya zaka iya karb'ar dutsen in lokaci yayi? tunda ka san b'arinka d'aya ba zai taba iyawa ba."

"I'm figuring a way out Jaamil, ban san wace hanya zan samo ba amma definetly zan samo hanyar da zan kare Sa'adha, I will, surely!"

Jaamil ya juyo ya kalle shi kamar mai karantar wani abun sannan ya koma da kallonsa kan tekun.

"Sooo..." yaja maganar yana kallon yatsunsa.

"Ta yarda dani." Imran ya fad'i amsar tambayar da bai furta da dogon kalamai ba.

"Na gaya mata komai kuma ta yarda dani jaamil, tace it doesnt matter ko ni meye, zuciyarta ta riga ta amince kuma zata zauna dani."

Jaamil ya d'aga kansa kafin yace.

"Kuma ka fad'a mata abinda Naani tace?"

"Ba zan iya fad'a mata wannan ba, ba zan iya karya zuciyarta bayan yardar data riga ta bani ba, saboda haka na gaya mata Naani bata dawo ba, kuma kota dawo zan san hanyar da zan kare ta."

"Insha Allah, zamu samo mafita yarima."

Sai a sannan Imran ya kalle shi cike da mamaki. shima ya juyo yayi focusing sosai yana kallonsa.

"Tun tasowarmu tare muke komai yarima, bamu tab'a banbanta wani abu namu ba, sannan tare muka fara wannan abin, tare Naani ta turo mu yin aikin nan, tare muka samo mafitar waccan matsalar, me yasa kake tunanin don wani abu ya faru yanzu hakan zai canja?"

Imran ya had'iye yawu kafin ya maida kallonsa kan tekun, a hankali muryarsa ta fito.

"Thank you."

Jaamil ya juyar da kansa shima sannan suka yi shiru. Zuwa can yace.

"And I like your wife, tana da kirki."

Imran yaji murmushin jin dad'i ya cika bakinsa, ya kasa daurewa har saida hakan ya fito.

Daga nan suka shiga tattaunawa akan yadda zasu b'ullowa lamarin ba tare da Naani ta sani ba, sun dad'e sosai kafin su fitar da wani kwakwaran plan wanda babu makawa shi zai zame musu mafita. Kafin su rabu hirarsu ta dawo daidai kamar ba abinda ya tab'a had'a su, dama haka yake kowannensu baya iya fushi da d'an'uwansa.

***

Mafarkin ya fara ne a wannan wajen, wannan filin mai tarin bishiyun da ta san cewa abinda tazo nema yana cikinsu, sai dai a wannan karon babu muryoyin su inna dake kiran sunanta daga can nesa.

Sannan kamar wancan lokacin Imran ya fito daga cikin bishiyun nan yana kallonta da lumsassun idanunsa, kamar koyaushe yayi wani irin kyau sanye da light kaya, fuskarsa ta haska, sannan kyakkyawan murmushinsa ya kwanta sosai a gefen fuskarsa, sai da ta shagala da kallonsa sannan ya d'ago yatsansa guda d'aya yayi mata alamun ta biyo shi sannan ya juya ya koma cikin bishiyun.

Taku daya kawai ya shigar da ita cikin duhun bishiyun, amma sai wajen ya zama sab'anin tunaninta kamar wancan karon, a maimakon duhu wajen mai haske ne da kuma kyau, korayen ciyayi da fulawowi sun baje a koina, ga wani dutse daga can gefe yana zub da ruwa.

Taji wani ya rungumeta ta baya, hannayensa sun zagaye k'ugunta sannan ya d'ora hab'arsa a daidai lungun wuyanta, ko bata juya ba ta san Imran ne kuma zuciyarta ta riga ta nutsu dashi, saboda haka ta cigaba da tsaiwa ba tare da ta juya ba tana jin d'umin jikinsa akan fatarta da kuma yadda numfashinsa ke busawa a k'asan kunnenta.

A lokacin ne abin ya faru, taji an caka mata wani abu mai tsini a wuyanta, abin ya huda tun daga farkon wuyanta ya fito ta d'aya gefen.

Numfashinta ya tsaya cak, sannan jini ya shiga gangarowa kan fatarta, tayi k'asa ta fad'i da baya sannan zafi ya shiga bin kowacce jijiya ta jikinta, taji ruhinta na barin jikinta a hankali sannan idonta na shirin rufewa.

Amma kafin komai ya d'auke mata, fuskar Imran ta shigo cikin ganinta, yana tsaye kamar lokacin baya akanta da wannan murmushin dake murkushe zuciyarta, sai dai wannan karon a gefensa akwai wani d'an karamin yaro fari tas! mai mutuk'ar kyau dake ta b'angala mata dariya, a hankali idonta ya dawo kan hannun Imran wanda ke ta faman d'igar da jini!

Ta mik'e da wani irin sauri lokacin data farka daga baccin. D'akin yayi duhu sakamakon yamma data yi sosai kuma an saki curtains d'in gabad'aya harda na jikin glass wall din an zuge shi, akwai sanyi air condition kad'an, amma taji gumi na gangarowa ta cikin gashinta.

Ta kai hannunta jikin bango ta kunna fitila, haske ya dallare koina, hasken daya nuna mata cewar Imran baya d'akin, a sannan ne kuma Idonta kan tarin takardun dake baje kusan koina a d'akin.

Kan drawars, gado, mudubi, da duk wani abu da yake da space a d'akin, ta mik'a hannu ta d'auko guda da'aya dake gefenta akan side-drawer.

I'm hoping ba zaki karanta takardar nan ba saboda ba dad'ewa zanyi ba, amma in har kina karantawa yanzu, wani abu ya rik'e ni kenan...but I 'll be back very soon, kiyi sallah kici abinci sannan ki koma baccinki kinjii...? Zaki ganni lokacin da kika sake tashi insha Allah. I love you...

...like crazy!

"I love you too."

Ta fad'a a hankali sannan ta maida ninkin paper ta rufe, ta mik'e ta tattaro dukkan sauran na d'akin da abu d'aya suke fad'a ta zuba su a handbag d'inta. Ta shiga toilet tayi alwala tayi sallar La'asar data nemi ta kub'uce mata sannan ta sake wanka, kamar wancan karon bata sa mafarkin nan a cikin kanta ba, abu d'aya ne kawai ya tsaya mata a rai...wannan kyakkyawan yaron dake tsaye a kusa da Imran yana b'angala mata dariya.

Bayan ta shirya ta fito don samun abinda zata ci kamar yadda Imran yace, ba wai yunwa take ji sosai ba amma tunda ya fad'a dole ne taci, tana tafe tana kunna duk switches d'in data san shi ya kashe da zai fita.

Ta k'ara jin gidan ya mata shiru fye da koyaushe sannan ta dinga ganin koina wani iri. Different somehow.

A kan stool d'in jikin counter ta zauna tana ta kallon abincin dake cikin warmers d'in, haka kurum take jin bakinta ba dad'i saboda haka tayi tagumi tana tunanin me zata ci. Da kyar ta tsaida zuciyarta ta janyo wani bowl dake cike da potato soup yasha yankan vegetables round kala-kala.

Yawu ya taru a bakinta tun kafin ma ta fara ci saboda haka ta ajiye cokalin data d'auko tasa hannunta ta fara, tana ci tana lashe hannu kamar wadda aka sanmata. Sai dai bata kai ga ko ci da yawa ba ta fara rage taunarta a hankali... Me ya same shi? wani irin k'amshi yake, ko dai ya fara lalacewa ne? Ta kai hancinta ta shinshina, ai kuwa wani irin k'amshi ne ko wari ya daki hancinta, bata san sanda tayi wulli dashi ba ta matsa da sauri jikin sink ta shiga kwara amai.

Sai da ta fito da duk wanda taci sannan ya tsaya ta d'auraye bakinta a hankali ta had'a har da fuskarta, tana d'agowa taji kuma kamar jiri ya kamaya, gidan ya fara juya mata saboda haka ta lalubi kujera ta dunk'ule akai, a can d'aya side din kujerar akwai wani blanket, amma kafin ta iya d'auko shi ta lullub'a wani sabon baccin yayi awon gaba da ita.

Sanda ta sake farkawa duhu yayi sosai, kuma Imran na zaune a gabanta, gaban kujerar da take kai.

"I'm sorry, ya fad'a yana shafa fuskarta a hankali.

"I'm sorry na barki ke kad'ai, wani uzurin ne..."

Readers Also Read

More by Bilyn Abdull