Kenza eBookz

Waye shi complete - Chapter 22

Waye shi complete - Chapter 22

Waye shi complete Chapter 22: Waye shi complete Chapter 22. "Tana ganin cewa zai yiwu ne?"

4,439 words

"Tana ganin cewa zai yiwu ne?"

"Ba zata tabbatar in zai yiwu ba sai ta gama ganinta yanzu, amma ta fad'a min ne k'aunar uwa ga d'anta wani abu ne da babu irinsa a fad'in duniya, tace kowacce uwa tana son jininta komai irin munin halayya da siffarsa, so inaga ta fahimci abinda Sa'adhan take ji ne a yanzu, shi yasa ta matsa min a lokaci d'aya cewa sai mun taho don taga irin halin da take ciki."

Imran ya had'e tafukan hannayensa sannan ya d'ora su akan lebb'ensa, kwakwalwarsa ta tuno masa hirarsa da ita jiya da yamma.

"Ina ji a jikina ulfat Babyn nan alkhairi ne a garemu, ba zai tab'a zama irin tunanin da kake ba...ina son shi sosai Allah, kuma kaima na gaya maka zaka zo ka so shi fiye da tunaninka insha Allah."

A lokacin suna zaune yana bata yoghurt a baki, abinda a yanzu suka gano cewa shi kad'ai cikinta ke d'auka ba tare da ta amayar daga baya ba.

"So habibty Babyn namiji ne?" Ya tambaya yana goge mata smudge na yoghurt d'in a gefen bakinta.

A lokacin d'aya kumatunta suka yi blushing zuwa pink... wata kala mai kyau, mai kyau sosai da yaji kamar an caka masa wuk'a a cikinsa, wata wuk'a mai tsini da kuma tsatsa saboda zuciyarsa ta kasa tantance wace irin k'auna Sa'adha ke masa, he'd hurt her in so many ways amma har tana iya wannan farin cikin around him.

"Yau ce rana ta farko daka fad'i wani abu good akan Babyn nan Ayunie..."

Kafin yayi magana ta cigaba.

"...ban sani ba ko mace ne ko namiji , amma ni a mafarkina namiji nake gani."

"Har mafarki kike yi da Babyn?"

A lokacin da ya fad'i haka zai iya rantsewa yaga giftawar wani abu cikin idanunta, kamar akwai wani sauran bayanin tattare da mafarkin nata da take k'ok'arin b'oye masa amma sai ta sake yin murmushi tace.

"Zanso in iya nuna maka shi a mafarkin, yana da kyau sosai saboda da kai yake kama!"

Kafin fuskarsa ta iya rik'e wani reaction d'in ta rik'e hannunsa dake shirin kai mata wani spoon d'in baki tace.

"Kaci abinci?"

Ya langwab'ar da kansa kad'an irin abin tausayin nan yace.

"Noory ba abinda naci."

"Awwn...I'm soory na barka da yunwa, kaine kuma kak'i bari na in tashi."

Ta fad'a tana cupping fuskarsa a cikin hannunta, a lokaci d'aya kuma ta tashi ta nufi kitchen, bai b'ata lokaci ba shima ya rufe robar yoghurt d'in yabi bayanta. A gaban deep freezer ya same ta ta bud'e tana kallon kayan ciki, ya matsa a hankali ya juyo da ita, hannunsa d'aya zagaye da waist d'inta, d'aya kuma ya karb'e bowl d'in markadadd'en kayan miyan data d'auko.

"Me zaki yi?" ya tambaya fuskarsa dab da nata.

"Abinci zan dafa maka."

"Yaushe nace ina jin yunwa."

Ta d'age girarta d'aya.

"Kace baka ci komai ba."

"Amma bance ina jin yunwa ba." Ya fad'a yana kallon bakinta da idanunsa masu d'auke da emotions kala-kala da take hango su ta cikin maik'on idon.

"Toh ai zaka nemi abinci anjima kuma sai mu zauna ba'ayi girki ba don ni ba zan..."

Kafin ta k'arasa kawai ya had'e lips d'inta da nasa and just like that...ta manta k'arshen zancenta, kwakwalwarta ta tafi cloud 9 ta nutse can cikin duniyarsa.

Ya k'ara manna ta a jikinsa yana jin kamar ya cusa ta cikin zuciyarsa ta gano yadda yake mutuqar k'aunarta, ita kuma ta rik'o wuyansa kamar tana tsoron zata fad'i.

"Kasha tea Ayunie, bakinka na k'amshin madara." Ta fad'a breathlessly sanda ta d'an ja baya kad'an.

Yayi murmushi so soft idanunsa kusan a rufe, kafin ta k'ara magana ya sake sunkuyowa yana k'ara kissing d'inta, wannan karon itama ta taya shi, k'arar heartbeat d'insu ya had'e waje d'aya.

"I want to tell you something, abinda zan gaya maka yana mutuk'ar muhimmanci."

Muryar jaamil ta jawo shi daga tunanin da yayi tafi, ya juyo a hankali ya kalle shi.

"Mene ne?"

Kamar bai ji ba, sai da yayi shiru kafin yace.

"Ban san ta ina zan fara maka bayani bama."

Ya sake fad'a ba tare da ya juyo ba, Imran ya d'an tsuke gira yana kallonsa.

"How about the begining?...ka fara ta farko."

Maimakon ya amsa, sai ya d'ora hab'arsa akan hannayensa duka biyu sannan yace.

"Yaushe ne lokacin da Naani take jira?"

"Jiya na koma company, sunyi fixing date nan da kwana goma sha shida, atleast dai sati biyu, so i was thinking zamu iya samun mafita kafin nan."

Jaamil ya girgiza kansa har a lokacin bai juyo ba.

"Babu wata mafita da zamu nema yarima, Allah ya riga ya kawo mana sauk'i."

"Ka samo wata hanyar kenan?"

"Ban samo ba, kuma ba abinda zan samo, hasalima ba zaka je karb'ar award d'in ba, wannan dutsen ba zai tab'a shigowa hannunka ba."

"Ban gane ba..." Da tsananin mamaki Imran ya furta reaction d'in dake kan fuskarsa.

"Me kake nufi jaamil? ka san wannan dutsen shine dalilin duk abubuwan dake faruwa yanzu, shine dalilin shigowarmu cikin bil'adama kusan shekara guda kenan..ta yaya sai yanzu da komai ya kammala, Dr. turaki ya gama amincewa dani a matsayi wanda za'a bawa award d'in sannan zaka ce ba zan karb'a?

Idan har matsalar b'arin ruhina dake jikin Sa'adha ne na san zamu iya samo wata mafitar kafin sati biyun, amma ba zamu tab'a k'in cikawa Naani alk'awarin da muka d'auka ba..she has sacrificed alot don a kawo wannan lokacin saboda haka zamu k'arasa komai ba tare da saninta ba, na san in dai har na iya karb'ar dutsen na kai mata, ba zata takurani akan matsalar Sa'adha ba tunda ta samu abinda take so...sai dai kuma in nemi yadda zanyi da sareefa don Allah jaamil a yanzu ba zan iya rabuwa da Sa'adha ba."

Har ya kai k'arshen zancen jaamil bai katse shi ba, sai da yayi shiru sannan yace.

"Ban san ta yaya zan fara maka bayani ba yarima, amma abinda kake shirin ji yanzu zai karya zuciyarka."

Imran yayi focusing idonsa sosai yana kallonsa kwakwalwarsa na son tsinto yanayin da fuskarsa ke nunawa, yasha ganinsa cikin fushi, cikin b'acin rai, tashin hankali, mamaki, rud'ani da kuma ciwo...

Amma yanayin fuskar tasa a yanzu wani abu ne daya girmewa tashin hankali ko rud'ani, a cikin idanun bil'adamansa yana iya hango ainihin kwayar idonsa da tayi jawur duk da cewar baya kallonsa, ya tsirawa wata 'yar k'aramar flowerpot d'in dake gabansu ido ne kamar an cinna masa wuta, duk zagayen tunanin Imran ya kasa gano dalilin da zaisa jaamil cikin wannan yanayin.

"Naani ta yaudare mu yarima... bata turo mu samo dutsen nan don kariyar nahiyarmu ba kamar yadda ta fad'a."

Imran ya k'ifta ido jin hakan, kwakwalwarsa ta maimaita zancen ta k'ara maimatawa amma ya kasa gane me suke nufi.

"Kamar yadda kaji zancenmu da Naani, haka nima naji zancensu da Sareefa jiya bayan ta kira ni da saqon cewa in gaya maka ka kai Sa'adha wajenta gobe.

"Gobe? Ta gama dukkan shirin da tace zata yi kenan na cire ruhin daga jikinta?"

"Ba wannan ne mai muhimmanci ba." Jaamil ya fad'a yana ciro wani dunk'ulen abu daga aljihunsa, Imran ya riga ya san mene ne...HABLER, wani abu da suke recording murya dashi.

Ya bud'e shi a cikin tafin hannunsa, take wasu abubuwa kamar fuka-fiki biyu suka fito ta kowanne b'angare suka shiga kad'awa, a lokacin muryar dake ciki ta shiga fitowa.

Wannan muryar mai cike da kaushi da kuma k'arfin amo mai girgizarwa, kamar koyaushe Imran yaji sautin ta yana tab'owa har k'asan zuciyarsa. don yana iya jin yadda zuciyar tasa ke amsawa.

"Na fahimce cewa zuciyarki ta fara karkata akaina sareefa, kina ganin kamar bana sonki, kamar ina fifita su yarima fiye dake...a yau zan shaida miki wani abu da babu mahalukin daya sani...ina amfani da yarima da jaamil ne kawai don cimma manufar da zata gyara rayuwarmu ni dake, shi yasa na d'auke su na nunawa al'umma su na fifita su duk don zuciyarsu ta amince dani suji zasu iya sadaukar da rayuwarsu don yi min komai...!

Kamar yadda tun tasowarki kike ganin suna yi min aiki kala-kala, haka a yanzu ma na tura su yin aikin da shine dalilin d'auko yarima da nayi daga kwararo na gyara rayuwarsa na bashi dukkan wata kulawa daya rasa a baya.

Na taba gaya miki a baya cewa ina neman dutsen Nil, wani dutse da zai bani k'arfin da zaisa zuri'ata ta d'ore wajen mulkar nahiyar nan...toh daga baya mun samo dutsen a cikin bil'adama, wad'anda basu san amfaninsa ba sai kawai kyau da yayi musu suke ado dashi a matsayin kyauta, a lokacin yana wajen wani mutumi dake shugabantar wani kamfani saboda haka nayi niyyar d'aukowa amma sai farme ya shaida min cewa kona d'auka dutsen ba zai tab'a min amfani ba, k'arfinsa yana aiki ne kawai ga duk wanda ya same shi ta hanya mai kyau, ma'ana sai in har mai shi ya bani da yardarsa inba haka ba ba zai tab'a min amfani ba.

Tun a lokacin nayi niyyar tura dalak (Babban bawanta) a matsayin bil'adama yaje kamfanin mutumin har yayi aikin da zasu yarda dashi a bashi dutsen amma sai muka sake ganowa cewa ba kowa ne zai iya rik'e shi ba, sai irin d'aid'akun halittun cikinmu masu k'arfin ruhi, saboda haka nasa farme ya shiga nemo min irinsa.

A sannan ne ya gano wani bawa dake can nahiyar Sabeel, saboda haka mu karkata zuciyar mai shi ya taho muzaffar da niyyar saida bayinsa ya samu kud'i, bana so ko kad'an matashin bawan ya san inada hannu a cikin lamarinsa don haka muka shirya komai ya tafi a tsare, Farme ya kashe ubangidansa a daren da suka shigo Muzaffar sannan ya taimaka wajen kwance sark'arsa ya gudo. Sai bayan sati d'aya da shigowarsa cikin muzaffar sannan na shirya had'uwa dashi, shine a ranar da muka fita cikin kasuwa har dake ya taimaka wajen cetona daga fad'awa rami da Farme ya shirya komai, ni kuma nayi amfani da wannan damar na 'yanta shi na kawo shi cikin masarauta.

Ban tsara komai da jaamil ba saboda bana son cutar dashi a matsayinsa na d'an 'yar uwata, amma daga baya na fahimci alaqarsu tayi karfin da ba zan iya raba su ba saboda haka na barshi a matsayi mai taimakonsa nake tura su yin abubuwa kala-kala duk don su saba da hakan, sai da na fahimci zuciyar kowannensu ta yarda dani sannan na bijiro musu da buqatar samo min dutsen Nil, kuma ba wanda yayi musu a cikinsu duk da cewa basu tab'a wani abu makamancinsa va wato canja siffarsu su shiga cikin bil'adama.

Na tsara komai ba tare dana gaya musu ainihin manufata ba, sannan na tura su da dukkan wani abu da zasu nema yadda komai zai tafi daidai su samo dutsen kuma su danqa minshi da yardarsu! sai dai gabad'ayansu sun sab'awa umarnina a yanzu sunyi wani abu da babu shi a cikin tsarinmu...wani abu da zan d'auki mataki akansa duk ranar da suka gama abinda na tura su.

Saboda haka ki kore dukkan wani tunanin dake cikin kanki game da ina fifita su yarima akanki, K'arshensu ya kusa zuwa kwanan nan , daga lokacin da suka kawo min dutsen Nil, daga lokacin zan shafe tarihinsu daga tunanin al'ummar nahiyar nan gabad'aya, don hatta aurenki dashi na yarda da baikon ne wai don in k'ara samun yardarsa game damu ba wai don hakan zai kasance ba.

Ke kad'ai ce d'iyata Sareefa, ke kad'ai ce zan iya sadaukar da komai akanki...kuma saboda ke kad'i nake duk wannan tanadin!"

â—īšâ—

So i can recall wata ta tab'a cewa Anya Naani son da take wa Imran na gaske ne ba wai don yana da wani abu ba?....so whoever you are nayi saluting d'inki! u guess right!...😀

My humble readers, what do you think of this chapter ...?

And me kuke tunani Bwama zata ce game da cikin Nanne?

******

WAYE SHI?

AYSHA SHAFI'EE

54

(☆_☆)

"Toh kin gansu nan, kala biyu ne...wannan da nono zaki samu ki dama shi wannan kuma da ruwa kawai in kinga dama ma ki watsa shi a bakinki haka, cikin cokali d'aya ya isa."

Nanne ta d'age hanci da gira tana kallon k'ullin magungunan da inna ke nunawa a gabanta, ita tunda aka bud'e k'ullin wani yellow taji cikinta ya juya, yoghurt d'in data sha na safe na shirin fitowa.

"Wai daga ina ma aka samo su?"

"Tun zuwan da nayi Niger na taho dasu a wajen malam na vonni."

Mamaki ya kamata, ta saki baki kawai tana kallon inna, ta kasa yarda cewa tun sanda suka je Niger da zancen aurenta inna ta karb'o mata maganin ciki.

"In zaki sha tea da safe ma kawai ki saka shi a ciki tunda na san baki fiye son nono ba."

"Inna nifa bana jin zan iya shan wannann abubuwan, ba komai ma nake iya ci ba."

"Haka kuwa zaki sha, ko kina sha zasu dawo baza a rasa mai amfanin da zai tsaya ba, wad'annan d'in da kike rainawa sune masu amfani amma ku kunfi ganewa kwayoyin turawa da zaku yi ta sha ana haifar 'ya'ya da cututtuka."

Ta fad'a tana janyo manyan ledojin da aka shigo dasu na tsarabar kayayyaki masu kyau da Nannen tazo dasu, komai a rabe yake don kowa a gidan saida ta d'auko wani abu da sunansa, hatta 'yan aikin gidan su lami sai da ta d'auko musu mayafai irin na mutanen can, inna ta shiga warewa tana fad'in kuma ya biye miki kuka yita kwaso kaya haka, amma can k'asan ranta farin ciki ne fal! na ganin tarin alkhairin da kowannensu baisa rai dashi ba, ta riga ta sani tun da Nanne bata da rowa ko kad'an, abin hannunta bai dame ta ba don bata k'i tayi kyauta da komai nata ba har kuwa ga wanda ba shiri suke ba, rashin kunyarta iya ta baki ce kawai.

"Ki d'auki fa magungunan kisa a jakarki."

Ba yadda ta iya haka ta d'auka tasa a handbag d'inta ba da niyyar sha ba, don tun zuwanta a yau da inna fahimci cikin dake jikinta tayi ta tambayarta game da zancen sunje asibiti da kuma yadda take jin jikinta, ba sai an fad'a ba ta san murna ce tsantsa a can k'asan ranta don tana iya hango kyallin hakan daga cikin idanunta sanda take gayawa Mama Azumi data shigo.

Zuciyarta ta karye da tunanin yaya zasu ji a lokacin da suka san irin sirrin da take b'oyewa, kafin zuwan Imran cikin rayuwarta bata taba tunani akwai wanda zuciyarta zata amince har tayi sharing sirrinta dashi bayan Inna ba, sai gashi a yau innan take b'oyewa sirrinta, sirrin wani abu da take ganin ya zama jigon rayuwarta...take kareshi da karya kala-kala a wajen innar tata.

Don ko awa d'aya bata rufa da zuwa gidan ba ta fara tambayarta game da zancen 'yan uwan Imran, ba yadda ta iya haka ta bud'i baki ta fad'i k'aryar cewa ai daga dawowarsu can bauchi suka fara sauka, sai da suka suka kwana biyu aka zagaya da ita cikin danginsa sannan suka taho. Jin haka yasa hankalin innan ya kwanta ita kuma nata ya karkasu waje da yawa.

A cikin wajajen harda wani waje mai kama da damuwa ganin cewar dukkansu basu san irin cikin dake jikinta ba kuma basu kawo zaton komai a ransu ba, mama halime ce kawai data shigo tace mata in ta koma asibiti tayi complain akan idanunta don k'asansu yayi rami kad'an, basu san cewa ko sau d'aya bata bi hanyar asibiti ba, kuma bata jin har lokacin haihuwarta zata nemi asibitin.

Bwama ta riga ta gama yi mata duk wani therapy da take buqata kuma ta gaya mata abinda a kwanakin baya take jin zata iya saida ranta don ta ji shi, Abinda ya zama dukkan wani fata da burinta a lokacin da Imran ya dasa ayar tambaya game da cikin nata.

Allah ya sani a lokacin da yake gaya mata b'arin ruhinsa yana tare da ita, taji tsoro kad'an don bata son sake experiencing abinda taji a baya, har wani part na zuciyarta yayi fatan dawowar Naani don a cire shi, amma daga sanda bwama ta dubata, ta ganocewar wannan b'arin ruhin shike rik'e da cikin nata, ta mik'a godiyarta ga Allah da har a lokacin ya kasance a jikinta, don tace ba don shi ba, babu ta yadda za'ayi cikin Imran ma ya iya zama a jikinta kona 'yan mituna...jikinta is too weak d'in da zai iya rik'e shi!

Amma a yanzu tana fatan cewa k'arfin zai iya rik'e shi har zuwa watannin da abinda ke cikinta zai fito, watannin da bwama ta tabbatar mata ba zai zamo d'aya dana mutane ba, don they grow so fast ba irin halittar d'an adam ba.

Ta tuno yanayin Imran sanda ya shigo gidan bayan tafiyar Bwama, ga mamakinta emotion d'in fuskarsa was weak! zata iya fassara yanayinsa da kamar na d'an karamin yaron a lokacin da yaga mamansa bayan ya b'ata na kwana biyu.

"Come here."

Ya fad'a a hankali yana bud'e hannayensa ba tare da ya bar tahowa wajenta ba, ai kuwa yana rufe baki ta ajiye sassak'en itacen da Bwaman ta bata ta tafi da sauri ta had'e distance d'in dake tsakaninsu, yadda ta cusa kanta cikin jikinsa ya tabbatar masa da kuka take shirin yi.

"Wani abu ya faru ne sweetheart?"

Ya tambaya daga saman kanta. Muryarsa kad'ai a lokacin ta tabbatar mata da dole akwai wani abu daya same shi a lokacin, akwai wani abu da suka tattauna jaamil bayan fitarsa, bata san ko meye ba amma taji zuciyarta ta sake tsinkewa, hawayenta ya k'aru har yana gangarowa kan kuncinta.

Ya jijjiga ta a hankali yana share hawayen da d'aya hannunsa.

"Me ya saki kuka?" Ya tambaya yana d'auke hawayen da yatsunsa masu taushi, amma raunin muryarsa da take ji yasa suka kasa daina fitowa.

"I'm so happy Ayunie, murna nake yi..."

Ta amsa muryarta a karye.

"...Bwama tace we can keep it!"

Ya fad'i abinda ya san zai zama next words d'inta, daga can saman kafad'arsa ta d'aga kai sannan ta k'ara rungume shi.

"Alhmdlilah."

His voice was low again, saboda haka ta d'ago ta kalle shi, a lokacin ne zuciyarta ta girgiza sosai don ganin wani abu da bata tab'a zata ba, wani abu da tunaninta bai kawo mata ba.

TEARS!

*********

HAWAYE.

Wani abu ne da Imran bai san ya d'uminsu yake akan fata ba, wani abu da bai tab'a using ba tun shigowarsa cikin mutane.

Amma a lokacin da yake rungume da Sa'adha bayan tafiyar Bwama, a lokacin yayi experiencing yadda mutane keji sanda suke fitar da kwallar farin ciki da godiya ga Allah kan wata baiwa da yayi musu...

Ya k'ara yarda cewa itace shi a yanzu, itace dukkan wani hope da zaisa ya cigaba da rayuwa mai kyau a gaba, Sa'adha k'addararsa ce da Allah ya shigo da ita don ta tallafe shi a lokacin daya rasa kowanne gata...kamar yadda jaamil ya fad'a ne zuciyarsa ta karye gutsi-gutsi ta dagargaje bayan muryar Naani da ya gama ji, muryar data fallasa dukkan wani zargi da zuciyarsa ta fara d'arsa masa tun lokacin da Naani ta d'auko shi a matsayin wanda ta 'yanta kamar d'anta, amma sai tarin alkhairinta suka ture masa komai a lokacin.

Sai a yanzu yake hasko dukkan abinda ya faru a baya tar! a idanunsa, kamar a da yana cikin wani d'aki ne mai duhu a yanzu kuma aka kunna fitila mai haske yake ganin komai a gabansa.

Ya godewa Allah da yasa komai ya baiyana a yanzu, a yanzun da abubuwa basu zame daga hannunsa ba, a yanzun da yake da Sa'adha... wata mace guda d'aya da ta san dukkan wani secrets d'insa but she still stood beside him, a woman who love and trust him da dukkan zuciyarta, wadda ta bashi hope d'inta 100% ba tare da ta tab'a zarginsa ba, macen data bashi wata irin kulawa da bai tab'a experiencing irinta a wajen wani mahaluki ba, a woman who had every reason d'in da zata guje shi amma bata yi ba, ta baro iyayenta da kowa tayi sacrificing rayuwarta da zata iya gyarawa a gaba and choose to stand by him!

Ya rantse da ubangijinsa zai so Sa'adha ya kula da ita, ya kare ta da dukkan wani iyawarsa a duniyar nan, saboda ya fahimci cewa iya abinda zai iya yi mata kawai kenan!

***

A cikin mota lokacin da yaje d'aukarta bayan ya shiga gidan ya karb'o godiya kala-kala a wajen kowa, Nanne tayi ajiyar zuciya mai nauyi, ya mik'o hannunsa da baya kan sitiyari yayi squeezing nata a hankali.

"Me ya faru? how did it went?"

"Ba abinda ya faru Ulfat, Inna ta fahimta tun kafin ma in bata slightest hint...kuma kowa da yaji yayi farin ciki komai ya tafi daidai."

Ya gyad'a kansa ba tare da ya kalleta ba idonsa na kan titi.

"Komai zai tafi daidai insha Allah Noory."

"Insha Allah." Itama ta amsa.

Ta san cewa ya fahimci akwai 'yar damuwa a tare da ita amma bai tambaya ba, and she was glad that ya barta tayi keeping abun a cikin zuciyarta, in ba haka ba bata san ta yaya zata gaya masa cewa zuciyarta a tsinke take na ganin irin farin cikin da inna ke ciki game da Babynta ba alhalin ita tana b'oye mata wani babban abu da ya kamata ace ta sani, ta yaya zata gaya masa cewa zuciyarta ta dagargaje kamar irin yadda tasa tayi ranar da aka d'aura musu aure, ranar da yaga irin tarin al'ummar daya d'ora akan fake labarinsa.

Maimakon ya kaita gida a lokacin sai ya canja hanya zuwa wani k'aton mall dake d'auke da wajaje da yawa a cikinsa, watakila ya fahimci damuwar da take ciki ne a lokacin, ya fahimci yanayinta ya canja kamar yadda itama take gane komai nasa da duk wani slightest bit na motsinsa, cikin sa'a kuma sai frozen vanilla yoghurt din da suka siya ya taimaka wajen lifting spirit d'inta, taji sanyinsa har yana barin wani danshi a can k'asan zuciyarta.

Kusan minti talatin suna zaune a d'aya daga cikin kujerun park d'in wajen ba tare da sunyi magana ba, shiru da sanyin bishiyun wajen ya saukar da wani peace of mind a zuciyar kowannensu.

Sai da Nanne ta d'aga robar yoghurt d'inta taji ya k'are tas! sannan ta yar da ita a gefe, ta juya ta kalle shi sannan tace.

"Ayunie we need to talk... akwai abinda kuka tattauna da jaamil lokacin da Bwama tazo, You need to tell me, ina son inji me ya faru."

Imran yayi squeezing robar chocolate ice-cream d'in da ya gama sha shima, he'd seen this coming...ya riga ya san Sa'adha ta fahimci damuwar da yake ciki tun wancan lokacin kuma ya dad'e yana jiran zuwan tambayarta dama, tambayar da ya riga ya shirya amsarta daki bayan daki.

Sai dai kafin yayi magana, idonsa ya hango masa text d'in da ya turawa jaamil a d'azu.

Komai zai cigaba da tafiya kamar yadda muka tsara jaamil, ba abinda zai canja ko ya tsaya, zanje in karbo dutsen Nil....zan kare Sa'adha dashi kuma zan d'auki fansa akan Naani dashi!

â—īšâ—

Revenge guys!

What do you think?

****

WAYE SHI?

AYSHA SHAFI'EE

55

This page is yours! My amarya freind..It's your day SHAMSIYYA ADO MA'AJI...Happy Birthday dear! 😍

Chill Out Mrs. Abdullahi...we love you!

(☆_☆)

"Naani ce ta dawo kuma ta san da dukkan abinda ya faru amma bata san da zancen cikinki ba...so mun tattauna yadda zamu b'oye mata sanin hakan ne har zuwa lokacin da zaki haihu, saboda in har ta sani ba zata yarda ba Sa'adha, ba zata yarda muyi abinda baya cikin tsarinta ba."

Imran ya fad'i k'aryar da zata lullub'e ainihin gaskiyar da yayi niyyar gaya mata a da, ainihin gaskiyar da zata sa ya daina barinta a duhu game da al'amarin Naani, don a yanzu yana ganin ta cancanci ta san ko wane gutsiren al'amari game dashi, he can't hide anything fom her! amma sai kalaman da Bwama ta fad'a masa suka hana shi furta mata ainhin gaskiyar...

"Kar ka tab'a bari ranta ya b'aci har ta shiga damuwa yarima, dole ne ka dinga b'oye duk wani abu da kasan zai takura zuciyarta...oum veri nah kour menku rajern! (stress will only make her more ill.) irtou nah kalabg daer waqatu harvil jourda gnawyer bayadda ferl...(Zuciyarta da duk wani k'arfin jikinta sun ta'allak'a ne yanzu akan abu guda, she can't be distracted.) hazar fumerbe ferl don sartu nah, gzarde ser tah ngam! (You have to he composed, you can't make it harder for her.)

Wad'annan kalaman su suka hana shi fad'a mata ainihin yadda zuciyarsa ta dagargaje da kuma irin ciwon da take yi bayan yaji kalaman Naani daga cikin Habler nan, Amma kwakwalwar Sa'adha was so sharp than tunaninsa.

Ta tsuke idanunta kad'an sannan tace.

"Ayunie ka tabbata ba wani abu da Naanin take shiryawa da zai cutar dani ko kai?"

A lokacin data fad'i hakan wani abu a k'irjinsa ya tarwatse sannnan harshensa ya k'ulle... ta ya zai fara gaya mata cewa he just found out cewa Naani bata tab'a nufinsa da alkhairi ba, ta d'auko shine kawai don ta gyara rayuwarta daga k'arshe shi kuma ta tsaida tasa...

Daga yanayin fuskarsa Nanne ta fahimci cewa ba zai bata amsa ba, saboda haka ta kwantar da kanta a kafad'arsa sannan ta zuro hannunta ta cikin nasa.

"Koma meye Ulfat, na san I'm safe with you!"

Matsalar kenan! gabad'aya tunaninta akansa were all backwards... bata tab'a gane hatsarin da rayuwarta ke shiga akansa, a koyaushe tana bashi wata yarda ne da shi bai cancanta ya samu daga gare ta ba, maimakon guduwa tana k'ara cusa kanta ne wajen da yake da hatsari...watakila kuma laifinsa ne da tun farko bai nuna mata hakan ba.

Amma ta yaya zai kare ta daga kansa alhalin dukkan zuciyoyinsu basa son hakan?

Sai ya jingina kansa shima a saman nata a hankali, idanunsu na kallon k'ayatattun lilukan park d'in dake can gabansu!

****

BAYAN WATA UKU.

"Kina da popo pos?" Hidaya ta tambaya zaune daga kujerar island na kitchen d'in.

Nanne ta k'ara d'auraye bakinta daga d'an guntun aman da tayi a sink sannan ta juyo ta kalleta da murmushi, wani murmushi da ya fad'a can cikin ramin kumatunta kamar yadda idanunta da suka d'ashe suka yi zurfi a can cikin lungunsu.

A cikin watanni uku kawai wanda ya san Nanne a baya zai yi mutuqar wuya ya gane siffarta a yanzu, wata siffa da a kullum innarta ke kira da kwarangwal... don d'an karamin jikinta ya yamushe sosai cikin abinda za'a iya kira fata da k'ashi kawai, fuskarta ta sirance sosai ta yadda k'ashin gefen hab'arta ya fito k'arara yana haska idanunta da suka d'ashe tas!

Readers Also Read

More by Bilyn Abdull