'yar sarki ce by uwar batoolerh - Chapter 21
'yar sarki ce by uwar batoolerh Chapter 21: 'yar sarki ce by uwar batoolerh Chapter 21. "Maha kiji storon Allah me kike yi a dinning cikin daren nan?"…
4,457 words
"Maha kiji storon Allah me kike yi a dinning cikin daren nan?" Mahreen ta faɗa da mamaki. Ga kuwa Abinda nake kin gani, abinci na gama ci yanzu zan dawo ɗakin. Yanxu duk jimawan da kika yi abinci kike ci? Cup na ruwa ta ɗauka ta sha ta miqe tsaye, tom na gama muje mu kwanta Addah am an gama waya da ya Abdoul ɗin ne? Gamawa tun yaushe Maha, kece ma da naga baki dawo ba na zaci ko ba lafiya ba ai. "To Kin ganni rass nake na ma fiki lafiya" ta faɗa yayin da suke shigewa ɗakin su. Tun da ta fita idon sa na kan qofan bai kau da ba. Me yarinyar nan ke nufi? Ina mata magana tayi banza ta wuce. "Mtswww" tsaki yaja. Dama ban qira ki ba ke kika kawo kanki shashasha kawai. System ɗin nasa ya buɗe yaci gaba da aikin sa in peace, amma dai qasan ran sa reaction na yarinyar na basa mamaki ko renin da ta masa har ya kai hana oho. Suna shiga ɗakin gado suka faɗa duka ko wacce addu'an bacci tayi suka ja blanket suka lulluɓu. Can ta leqa Mahreen gani tayi ita kam ta jima dayin bacci ma. Qaramin tsaki ta ja tace "Ɗan renin hankali kawai wai dan an damu baka da lafiya shine har da wulaqanci wani ai mai aiki ce ta kawo masa coffee, hmnn zan rama ne ba dai ka warke ba ina dede da mutum." Juyawa tayi ta rufe idon ta dan bacci ya ɗauke ta itama. Umma na shiga ɗakin murmushi Abban yayi mata! Ƴammata na sai yanzu aka biyo ni? "Yallaɓoi aimun aikin gafara" ta faɗa da murmushi itama. Matata bata laifi ko tayi ma an yafe mata. Gidiya nake yallaɓoi baban yara. Isowa wajan da yake tsaye yana rage kayan jikinsa tayi tana taya sa rage kayan, murmusawa yayi yace "Allah maki albarka" da Ameen ta amsa ta wuce bathroom ta wasta ruwa. Bayan ta fito shiryawa tayi cikin dogon rigan ta na bacci, zaunawa tayi bakin gadon gefen sa kallon ta yayi yace "Hajiya ta da alama dai bakinki da magana menene ya faru?" Yallaɓoi maganan yaron da su Ameerah suka yi jinyan sa ne, an turo mun layin nasa sai dai na qira ba'a ɗauka ba da alama ko wayan nasa baya tare da shi. Karki damu maman yara tunda gobe Litinin zamu Bauchin inyaso sai mu tafi tare daga nan sai kiga yaron naki. Maganan da yayi na "daga nan sai kiga yaron ki" ba qaramin tsaya mata a rai yayi ba hakan ya sanya tana qara jin wani iri game da yaron, wanda bata san ko menene ba? Cewa tayi "wai dama nufin ka yallaɓoi ku kaɗai zabkuje ni ba za'a je dani na gaida Mama ba?" A'a na isa Hajiya ta qafata qafar matata. Murmusawa tayi, Allah kaimu goben da rai da lafiya. "Ameen ya Rabbi Hajiya ta" Abba ya amsa mata. Bayan sun kammala abubuwan da ya kamata kwantawa suka yi sai muce safiyar alkhaery.
🅆🄰🅂🄷🄴 🄶🄰🅁🄸 Gari na gama haske Amjad ya gama kimstawa ya shirya, tuwon karin da aka kawo masa ma stakura yayi kaɗan. Gaba ɗaya yau jin sa yake cikin farin cikin nasaran samun maganin da yayi yake, gashi kuma yau zai kama hanya wanda da yardan Allah zuwa gobe zai ga Ummansa ta gansa ya faɗa mata irin kewanta da yayi, to sai dai agefe ɗaya kuma cike yake da fargaba da kuma tunani akan faɗuwan gaban dake damun sa wanda ya tabbata akwai abinda zai faru. Lumshe ido yayi yana faɗin "Ya Rabb ka sanya komi dake shirin faruwa dani yazo da sauqi Alfarman fiyayyen halitta SAW, tabbas stinkewan zuciya na ba alkhaeri kuma ko da akwai alkhaeryh to wani babban abu dai zai faru". Yau saura sati 1 da ƴan kai wa'adin da aka ɗibar mun su cika ya kamata ace ina gida iwar haka, Allah ka iya mun. Liman ya iso inda yake a tsaye a qofan ɗakin baqin, sallama liman yayi shiru Amjad bai amsa ba, qara Sallaman yayi shiru kuma du. Matsowa limamin yayi ya ɗan taɓa Amjad yace "bawan Allah mai kake tunani haka? Nayi sallama bakina uku shiru baka ko ji na ina fatan lafiya kam?". Qasa Amjad yayi da kai yana ajiyan zuciya sai yace "lafiya lau Alhamdulillahi Allah gafarta malam" A'a kaga yaro faɗa mun gaskiya wani abu ne ya faru kuma sai kace a'a lafiya. Can sai ya nisa yace "Allah gafarta malam gabana ke faɗuwa sosai-sosai kuma ni tun ina yaro haka nake indai wani mummunan abu zai faru to ko nayi mafarki ko kuma na tashi da faɗuwan gaba tom ina tunanin wani abun na shirin faruwa" Lima yace "subhanallahi! To yaro ko zaka iya haqura da tafiyan nan yau ne mu koma ciki Qasa Amjad yayi da kai cike da ladabi yace "Allah gafarta malam amun addu'a kawai amma zan tafi yau Inshà Allah yanzu ma haka munyi magana da wanda zai zo ɗauka na ya kusa isowa". Dogon numfashi malam liman yaja kamun ya jinjina kai yace "bawan Allah ba ina nufin hanaka tafiyan ka dan abinda kake tunanin faruwansa ba a'a ko ɗaya ina hanaka tafiyan ne dan samun nistuwan zuciyanka, ka riga da ka sanyawa ranka indai faɗuwan gaba ya sameka to mummunan abu ne zai faru to shiyasa nake son ka dakatar da tafiyan naka dan kasani cewa shi mumini a rayuwan sa akwai qaddara haɗe da jarabawar Ubangiji sannan duka abu biyu wanda kusan ma'anan su ɗaya ana son duk wani mumini wanda ya yarda da Allah da Manzon sa to yayi imani da su, wani lokacin alkairi zai kawo bugawan zuciyan ka wani lokacin kuma akasin alkairi sai dai duk acikin sun akwai abinda Allah ke nufi da hakan wa lau ya ɗaga matsayinka wa lau ya jarraba imaninka sannan..." sosai yai masa nasiha mai haɗe da tunatar wa. Ajiyan zuciya Amjad ya sauqe bayan malam liman ya ida nasihan sa, Allah ya saka da alkairi Malam in Allah ya yarda zan gyara amma ina mai bada haquri da maganan tafiyana yau, tabbas nasan komai sai Allah yaso kuma sai ya qaddara amma ina mai addu'an Allah yasa tafiyana yau ɗin ya zame mun alkairi, Bazan taɓa mance alkairinka gareni ba malam Allah ya saka da Aljanna Allah kuma ya qaddara saduwanmu. Amarya da hayra ne zaune a dinning area suna karyawa, shiru babu mai magana (table manners). Da sallama Abdoul ya shigo sashen kakar tasu, ganin suna dinning tsayawa yayi daga tsakiyan palourn yace "Amarya ta gud morning" Amarya tace "ubanka ke gudu da moni, ɗan jakar uba banson ɗiban albarka da tangaɗewa da sanyi safiya ka isheni da yaren ƴan wuta, yanzu inbanda sinqin sikitin layii da tangaɗi wai ƴan adam baza suyi yaren ƴan aljanna ba sai na ƴan wuta to haram ba dani ba ni Mairo". Tunda Abdoul yayi magana hayra ke dariya har amarya ta qare sababin ta dariya take har da kama ciki "ko shima ya Abdoul me ya kaisa oho" ta faɗa tana dariya qasa-qasa. Amarya Juyowa kanta tayi tace "matar ubanki hansatu ce ta kaisa, ba dai matar nan ta koya maki sinqin fistara ba to zan kwashe maki ƴar buhun uba kawai". Abdoul da ya gaji da tsayuwan jin surutun kakar tasu sai ta juya zai fice, amarya tace "yanzu Abdu renine har haka dan ni ba uwarka saratu ba ina faɗama gaskiya shine ka iza farantin goshinka a gaba zaka fice? To da mai ma ya kawo ka sashe na gulman me kazo yi? To in ban haifeka ba ai na haifi ubanka Muhammadu don haka ina zaka da sassafen nan ka faɗamun ko na kwashe maka sauran albarka". Qaramin tsaki Abdoul yaja jin fitinan stohuwar nan, ni na kawo kaina ai dole ki isheni da surutu. Kwantar da murya yayi yace "Amarya ta aike Umma ta sani bawan Allahn da mijin Ameera ya buge ne zanje mu haɗu dashi zai koma garinsu. Salati Amarya tayi tace "Abdu ɗan albarka zaka aikin lada shine dan tsabar sinqin baqin hali ba za ka ce na raka ka ba, to Allah shiryeka kuma ka tabbatar ka kawomun shi na sa masa albarka, kai ina tsaya dai na ɗauko mayafi mu tafi tare tunda motar da kuɗin yarona ka saya to sai na hau" ta qarisa faɗa tana miqewa ta nufi ɗaki. Abdoul na ganin ta shige ya fice a sashen da sauri, motorn sa ya shige yai mata key da gudu ya fice a gidan sanin halin kakar tasa. Hayra haɗa kwanuka tayi ta gyara dinning ɗin, duk abinda suke tana ganinsu dariya ne kawai take dannewa dan tasan tabbas yau akwai qaramin bori a gidan nan. Tana cikin tunanin haka Amarya ta fito a ɗaki sanye da hijab nata har da sanja kaya tayi tana faɗin "Angon kayi haquri na jima mu tafi yanzu.." bata qarisa ba ganin palour wayam ba Abdoul ba labarin sa da sauri tayi hanyan waje tana faɗin "ɗan albarka ai nace kayi haquri shine dan ka gaji da jira na sai kayi waje salon kaban wahala". Gama duba haraban gidan tayi amma ba Abdu ba motorn Abdu, Amarya ta cika tayi fam sai ta rasa me ma za tayi ɗaya? Sashen iyayen sa ta nufa gadan gadan ko sallama ba tayi ba ta tura qofa ta shiga tana bambami.. Amjad suna staye da malam liman sai qira ya shigo wayansa, ganin layin Abdoul ne sai ya ɗauka. Magana suka yi yayi masa kwatancen gidan malam liman kaman yanda limamin ya faɗa masa, da suka gama magana sai ya kashe wayan. Malam liman yace "yaro yanzu dai tafiyan zaka yi, to Allah ya tabbatar da alkhaeryh ya kuma kai ka gida lafiya ba na shiga gida ina fitowa kamun dai shi mai ɗaukan naka ya iso". Amjad yace "to Allah gafarta malam a fito lafiya".
Umma ce tsaye a tsakiyan palourn hannunta riqe da mayafi da kuma jakan ta waya a kare a kunnen ta tana cewa "wai kai Auta ba za ka fito bane sai mun tafi?" Daga ɗaya bangaren soja yace "Umma ina fitowa yanzu tashuwa na bacci ne shiyasa". Umma tace "ko ma baka tashi baccin bane ka fito yanzun nan inba haka ba zan saɓa maka" kitt ta kashe wayan. Ummeyh dake sauqo wa daga step's ce ke cewa "gaskiya ana takurawa yaro na tunda ba binmu zai yi ba abarsa ta huta mana". Umma tace "Gwaggon yara ki qyale wannan yaron naki ko kaɗan baya ji wallahi ni na rasa ma ya zan yi dashi wai dai ace yaro ka fito ka gaida iyayen ka ko ba za ka bisu ba ai ka musu addu'an a dawo lafiya amma kwata-kwata habeeb ba ya ji". Ki sa masa albarka kawai Umman yara. Hmmn! kawai Umma tace tayi shiru. Dai-dai Abba ma ya fito iso palourn shima Soja ya iso, kallonsa Umma tayi ta kau da kai tace "wai ina su doter ne suma ko ba za su mana a dawo lafiyan bane?" Tana gama rufe baki Maha da Mahreen suka shigo palourn su ma. Maha ce ta fara stugunnawa ta gaida iyayen nasu kamun Mahreen ma ya gaishe su, Umma qara kallon soja tayi ganin bai gaishe su ba kuma shi ya fara zuwa palourn, qawafa tayi. Soja gaisar da Abba da Ummeyh yayi kamun ya gaida Umma ko kallon sa ba tayi ba bare yasa ran zata amsa. Ummeyh tace "ataimaka dan Allah da Manzon sa a amsa mana" kamun ta amsa gaisuwan sama-sama. Maha tace "yanzu Abba tafiya za kuyi ku barmu mu kaɗai a gida?" Murmushi Abba yayi yace "doter may be yau ɗin nan zamu dawo in bai samu ba kuma zuwa gobe Inshà Allah ku dai ku kula sosai kunji" Mahreen tace "Inshà Allah Abba Allah ya kaiku lafiya ya dawo daku lafiya" duk aka amsa da Ameen. Waje suka nufa duka har parking space suka raka su, Umma da Ummeyh suka shiga baya soja ya shiga mazaunin driver Abba ya zauna a kujeran gefen sa, Soja yaja motor suka fice a gidan. Kaduna state airport suka nufa, ko da suka je Private jet da yake kusan mallakin Abba wanda wajan aiki aka miqa masa dan tafiye-tafiyen sa, shi suka shige jirgin nasu ya ɗaga sai Bauchi shi kuma Soja ya ja Motorn ya juyo gida. Abdoul ya ɗan sha tafiya dan anguwan da ya masa kwatancen musan qarshen gari, ko da ya isa sanda ya qara qiransa ya haɗa sa da malam liman ya masa kwatancen da kansa da qyar har da tambaya kamun ya samu ya gane gidan, yana isa parking yayi a qofan gidan ya ɗau waya ya qira Amjad. Qiran Abdoul ya shigo wayan sa ɗagawa yayi yace "ka iso ba? Dan naji qaran motor". Abdoul yace masa "eh ina qofan gida" Malam liman qira ya kwaɗawa ecleemah. Da tazo yace "ta ɗau jakan Amjad ta kai waje" Amjad yace "Allah gafarta malam tayi hutawan ta zan ɗauka, Qanwata ki koma ciki abunki zan ɗauka". Ecleemah bata saurare sa ba tabi umurnin mahaifin ta jakan ta ɗauka tayi hanyan waje malam liman da Amjad suka rufa mata baya. Qofan back seat Abdoul ya buɗe mata ta saka jakan da ta ɗauko kamun ta juya idonta cike da qwalla tace "yayana Allah tsare hanya ya kaika lafiya" tana gama faɗa ta shige gida bata tsaya ko jin me Amjad zai ce ba. Bin bayanta yayi da kallo har ta shige sau kawai yaji wani irin, maganan malam liman ne ya sanya shi Juyowa da barin kallon qofan shiga gidan. Malam liman yace "yaro kaga kalman da ake cewa baqo raɓa ko gashi a jiya zuwa yau har za muyi kewanka kaman kar ka tafi amma kuwa ba dama sai dai mu bika da addu'an Allah kaika lafiya Allah kuma yasa andace kenan" Da Ameen Amjad ya amsa sai yayi qasa da kansa kawai. Malam liman suka gaisa da Abdoul cikin girmamawa sai yace wa Amjad "bawan Allah ka shiga ku tafi tafiyanka ba na ɓata lokaci ba" ya buɗe baki zai yi magana sai malam liman ya ɗaga hannu yace "karka damu da komi kai dai ka shiga kuje" juyawa yayi ya shiga mazaunin gefen driver Abdoul ya zagaya ya shiga mazaunin driver suka wa malam liman sallama Abdoul yaja motor, malam liman yana ɗaga masu hannu har Motorn nasu ya ɓace a layin nasu gaba ɗaya. Juyawa malam liman yayi ya shige gida cike da kewan baqon nasa na kwana ɗaya wanda kuma yana tunanin qara haɗuwan su wataqil sai kuma a qiyama. gaisawa Abdoul da Amjad suka yi wanda tun da Amjad ya shiga Motorn yake jin gabansa ya tsananta faɗuwa, Abdoul kallon sa yayi sai yace "bros ina muka nufa?" Amjad yace "airport zaka kaini" Abdoul ya kuma kallon da ya kalli hanya yace "haba dai airport ba zaka je gida ka gaida Amarya ba? Am Amaryan ina nufin kakata gaskiya ya kamata kaje ka gaida ta inba dai kayi booking Flight na safe ba". Amjad yace "nop banyi booking Flight ba yanzu dai in munje zanyi sai na jira, Amarya kuma inka koma kace wani jikanta na gaida ta sai wani lokacin zanzo". Murmushi Abdoul yayi ai tunda ba kayi booking jirgi ba gaskiya daganan sai gida ba wani airport da zamu ai in bankaika gida ba yau ba mai kwata na a hannun masifaffiyar stohuwar nan, kwashe yacce suka yi da Amarya yayi ya faɗa wa Amjad yana dariya. Amjad sai da ya Murmusa jin rigiman stohuwar sai dai kuma har yanzun faɗuwan gaban sa na yawaita, da Abdoul ya dage ba yacce zai yi qarshe yarda yayi ba dan yaso ba amma bai qudiri aniyan kwana ba yana zuwa ya gaida mutanen gidan su Abdoul ɗin zai kawo sa airport ya samu ya shirya komi na tafiyan sa yau ɗin nan. Abdoul ne jin yayi shiru yace "bros ya kayi shiru? Maganan tafiya yau fa kabar sa dan anan kam ba lallai ka samu Flight direct to Qatar ba sai dai ko in zaka hau na Abuja daga can to sai ka samu na Qatar kaga kuma duka long process ne gashi yanzu rana ya fara ka bari kawai anjuma kayi booking anan sannan mijin Ameera ya maka na Qatar ɗin in yaso d sassafe ka tafi ko in ansamu na dare sai kabi na Abuja da yamma da dare kuma ka hau na Qatar ɗin" Amjad ba yacce ya iya haka ya aminta suka nufi GRA. Amarya sashen baba qarami ta shiga tana bambami, kai jama'a Allah raba ɗan mutum da wahala yo in ba wahala da tangaɗi ba ace wai jikanka ya mai da kai birin wasa ai wannan ba ko kaffara uwar sa ke kista masa hmm! Shi uban kuma da yake maloho tangaɗaɗɗe baya iya stawatar wa an mallakesa ni Mairo na shiga uku an raba ni da yara na. Baba qarami da ke zaune a palourn mama hafsatu yana aiki a system nasa kasancewar yau yayan sa na hanya shiyasa bai fita aiki ba, muryan mahaifiyarsu da ya jiyo ne ya sanya shi rufe system ɗin ya miqe ya nufa hanyan babban palourn da yasan bazai wuce tana can ba. Tarar da ita yayi tsaye tana share hawayen da babu shi da gefen hijab nata, baba qarami na isowa har qasa ya durqusa yace "Gwaggo ina kwana antashi lafiya?" Wani kallo Amarya ta masa sai kuma ta fece hanci tace "yanzu ba dan ubanka mijina bane kuma ya rasu bawan na kwance cikin rahamar Ubangiji yo da sai nace dan jakar ubanka, amadu ban kwana ba kuma in mutuwa nake na rashin lafiya ba to ba ruwanka,kullum faɗi nake ka riqe azkar da salatin Annabi za ka fi qarfin duk wanni stubbace-stubbace amma dan tsabar lalacewa da tangaɗewa yaron nan ba kayi, amadu baka neman albarka" baba qarami dake stungune a qasa ba abinda yake cewa sai "Gwaggo ayi haquri a yafeni". Mama hafsatu da ke qarasowa palourn ne tace "Alhaji ai ba haquri zaka bada ba tambayan me kayi zaka yi" Amarya kallonta tayi sai tayi qwafa za tayi magana sai baba qarami ya riga ta "ke Hafsa banson rashin hankali". Amarya tace "a'a karka sona amadu ba laifinta bane ai komai tace kai ka nuna masu ba dai baka neman albarka ba?" Mama saratu ta qaraso palourn itama tace "Gwaggo Barka da shigowa ki zauna mana". Kallonta itama Amarya tayi sai kawai ta sa kuka "yanzu amadu fistaran da kuke shuka mun kai da matanka har ya kai haka? Wai ni da gidan Yaro na sai ance na zauna da uban wani ya gina masa gidan to banson shishishigi shigilitu, amadu kai dai Allah staremun kai amma mata sun mallake mun kai ai daɗi na da Haruna kenan bawan Allah gashi dai mace ɗaya gare sa kaman mahaifin sa amma yafi qarfin gidan sa yanzu dan stabar ba mai ganin girmana a gidan nan ace yaranku ma kun hure masu kunne sun fistare qafafunsu sun ɗauko baqin halin ku" baba qarami jin haka to yasan tabbas wani abun Abdoul ya mata dan in hayra ce ba mai jin tsakanin su suyi faɗan su su shirya acan ba mai ji amma in ta shigo tana faɗa tom indai yara ne Abdoul ne ya mata abu ko kuma Autan ta Jamila. Ajiyan zuciya baba qarami ya sauqe yace Gwaggo kiyi haquri Insha Allah zan ɗau mataki kiyi haquri ki zauna, Amarya kujera ta samu ta zauna har da ɗaura miqe qafa tace "tunda kana neman albarka har da haɗa ni da Allah tom na zauna Allah maka albarka amadu na Allah yasa ka gama da duniya lafiya yanzu dai amadu kaji storon Allah kaji storon haɗuwa da shi wai ace ba za ka yiwa yaranka faɗa ba ka nuna masu nice uwarka nice na haifeka sai sun kyautata mun nasa maka albarka kamun suma zasu samu kasa musu albarka su gama da duniya lafiya" ayi haquri Gwaggo Insha Allahu za'a gyara. Ai nasan zaka gyara amadu wai ni zancewa Abdu ya jira ni na ɗauko lufaya muje aikin ladan tare amma wannan yaro da farantin goshinsa kaman na uwar sa tunda shina dai kaman hariran matar ubansu tana hure masu kunne tunda ita bata haifa ba ita ta mallake ku duka da kai da uwarsu da su ɗin dan kar kuyi albarka, yaron nan ya ja akwalan motar sa ya tafi ya barni tsaye riqe da lufaya kaman mata mai takaba yo Allah na tuba tun ba'a auri uwarsa ba na gama takaba na ja'irin yaro zai dawo ya same ni, du Allah miqo mun ruwa na jiqa maqoshi na duk yaro ya sani surutu maqoshi na kaman zai tsage bani ruwa na yayyafa masa". Mama hafsatu da ke kusa da fridge miqewa tayi ai Amarya da sauri tace "haramun ni Mairo ban aike ki ɗibamun ruwa ba Saratu ƴar albarka tashi kiban" Mama Saratu tashuwa tayi ta ɗauko ruwan ta bawa baba qarami yasa a cup ya miqawa Amarya ita kuma ta amsa ta kai baki da mugun sauri ta tufar da ruwa ta ɗaura hannu a kai tace "amma dai Saratu Allah shiryaki shi kawai zance maki kashe ni za kiyi wannan sanyin ruwan ai kurɓa ɗaya sai lahira, kinga Hansatu ɗiyata ƴar albarka bani ruwa nasha" mama Hafsatu ta miqo mata ta amsa tasha tayi hamdala. Kallon baba qarami tayi tace "Amadu kai da matanka ni Mairo ba abinda zance muku sai Allah ya maku albarka Allah yasa kuma yaranku su kula da ku su muku biyayya Allah sa ku gama da duniya lafiya, amma ke Hansatu ki dena mun fistara in ba haka ba kwashe maki albarka zan yi ba naje na jira ja'irin yaron naku da kuka hure wa kunne yau sai ya faɗa mun sadakin uwar sa tunda ni zai ɗauka birin wasan sa ya tafi ya barni kaman stinkakken silifas" qarisa maganan tayi tana miqewa, baba qarami haquri ya qara bata Mama Hafsatu da Mama Saratu duka suma haqurin suka bata, tayi gaba suka bi bayanta suka nufi hanyan waje dukansu. Amjad bayan zuciyansa dake stinke wa yanzu kuma da yaga sun shiga anguwan sai yana jin wani irin zafin wuta na bugun sa kaman yana tunkaran wajan da aka hura gunguman wuta haka yake ji, ga faɗuwan gaba ga kuma wannan zafin da yake ji yana tunkara. Abdoul ne ya juya ganin yanayin sa sai yace "brother lafiya kuwa?" Lafiya lau amma Please in bamu kusa iso gidan ba mu juya. Kallonsa Abdoul ya kuma yi mu juya kuma? Ga gidan nan fa banda waɗan can gate ɗin da kake gani wancan na gaban shine gidan. Amjad suna qara tunkaran gidan tururin wutan da yake ji na qara daɗuwa suna iso qofan gidan kuma kaman an kama masa maqoshi sannan ji yake kaman tsakaninshi da wutan da zafin sa ke damun sa bai wuce taku ɗaya ba. Qofan fitan baba qarami ya buɗe ma Amarya ta fito shima ya fito mama Saratu ne ta fito itama Mama Hafsatu kuwa da ke staye a bakin qofan haka kawai sai taki kaman ana juya mata gidan jiri lokaci ɗaya ya kamata ha wani kukan jarirai da take ji ya cika mata kunne, dafa qofan sashen nasu tayi ta jefo qafan ta waje. Amarya da ke zuba surutu har yanzu kaman zata ari baki sun iso tsakiyan haraban gidan kenan mai gadi ya wangale gate sakamakon horn na motorn Abdoul da yaji. Suna shiga cikin gidan tun bai qarisa parking ba Amjad da ya sanya hannunsa a wuyan sa sanadin jin shaqan da aka masa yayi yawa kuma kaman an jefa sa acikin wutan wani wawan qara ya saka wanda ya kusa da Abdoul sakin staring motorn, yana sakin qaran hannun sa a wuyan sa sai ya faɗo jikin Abdoul a matacce ba numfashi Ba shiri Abdoul yayi parking. Wannan qaran ya razana duk wani halitta dake cikin gidan, Amarya da Mama Saratu san da suka kusa sakin fistari a staye duk suka rikice, baba qarami nufan Motorn yayi sai kuma suka kuma jin wani qaran a bayan su da kuma sautin faɗuwan mutun, waye za kuma su gani? Mama Hafsatu ce yashe a qasa. Amarya zama tayi dirsham a qasa gaba ɗaya ta rikice Mama Saratu kuwa ba'a magana, baba qarami qara juyawa yayi sai ya kuma jin.... Jirgin su Abba yayi landing a tafawa ɓalewa airport dake garin Bauchi, Abba waya ya ɗaga yayi qira shiru ba'a ɗauka ba, ganin haka sai ya tare taxi ya juya dan mawa su Ummey magana suzo su shiga sai kawai yaga Umma ta yanke jiki ta faɗi..... TIRQASHI TASHIN HANKALIN DA BA'A SAKA MASA RANA KENAN! CAKWAKIYA, SARQAQIYA GAMI DA ƊAUREWAR KAI. WAI ME KUKE TUNANI? ME KE FARUWA? DUK ME YA JAWO WANNAN TASHIN HANKALIN? ME YAKE FARUWA DA AMJAD? MENENE YA SAMU MAMA HAFSATU LOKACI ƊAYA? ME KUMA KE FARUWA DA UMMA? DUK MENENE HAƊIN WANNAN TASHIN HANKALI DA YA SAME SU LOKACI ƊAYA? INA LABARIN UMMAN AMJAD? INA LABARIN GIMBIYA DA MAGANAN AUREN SU DA AMJAD? ANYA WANNAN NE DALILIN FAƊUWAN GABAN DA KE DAMUN AMJAD? IN BA WANNAN BA ME ZAI FARU GABA KENAN DALILIN FAƊUWAN GABAN SA? ANYA MA KUWA AMJAD NA DA RAI? TAMBAYOYI BARKATAI DAI SANNAN ANAN NA KAWO QARSHEN FREE PAGE'S DOMIN SAMUN AMSOSHIN WANNAN TAMBAYOYI DA SUKE RANMU DA KUMA KUNCEWAR WAƊANNAN RIKITATTUN AL'AMARIN KUYI HANZARI KU BIYA NAIRA ₦300 KACAL DAN ACI GABA DA LABARI DA KU. NORMAL PAYMENT GA WAƊANDA KE GROUP ALREADY ₦300 GA WAƊANDA BASA GROUP ₦400 GA MASU BUQATAN COMPLETE PAGE'S ₦500 V.I.P COMPLETE DOCUMENT ₦500 ONLY TA WANNAN ACCOUNT 👇 2220553988 HARIRA SALIHU ISAH UBA BANK 🏦 KO KATIN WAYA TA WANNAN LAYIN 09161720046 MTN 07015870735 AIRTEL SANNAN ZAKU TURO SHEDAR BIYA TA WANNAN LAYI A WHATSAPP 09161720046
Ina mai qara baku haquri waɗanda tun farkon littafi suka biya sannan ina da babban garaɓasa gareku a next book namu da kuma baku zaɓi akan labarin da kuke so mu fara. Ƴan uwa abokan arziqi masu daraja gaisuwa gare ku Ako da yaushe kuma ako ina kuke a faɗin duniyan nan daga taku har kullum mai nishaɗantar daku HARIRA SALIHU ISAH (UWAR BATOORL) MARUBUCIYAR 🥀 𝐌𝐀𝐅𝐀𝐑𝐊𝐈 𝐍𝐀𝐇 🥀
YANZU KUMA 👑 𝐘𝐀𝐑 𝐒𝐀𝐑𝐊𝐈 𝐂𝐄 👑 Sannan da labarai daɗaɗa da na tanadar domin ku da nishaɗin ku.
Kar ku manta sunan labarin da muke ciki 👑ƳAR SARKI CE 👑 DAGA DAUSAYIN ALQALAMIN UWAR BATOORL 🔥
💋💋 امى بتولة💋
𝘿𝙤𝙢𝙞𝙣 𝙩𝙖𝙡𝙡𝙖𝙩𝙖 𝙝𝙖𝙟𝙖𝙧𝙠𝙪, 𝙠𝙪 𝙩𝙪𝙣𝙩𝙪𝙗𝙚𝙣𝙞 𝙖 𝙬𝙖𝙣𝙣𝙖𝙣 𝙡𝙖𝙮uka:- 09161720046 𝘾𝙝𝙖𝙩 𝙤𝙣𝙡𝙮. 07015870735 𝙔𝙤𝙪 𝙘𝙖𝙣 𝙘𝙖𝙡𝙡 𝙙𝙞𝙨 𝙤𝙣𝙚, 𝙭𝙖𝙢𝙪 𝙢𝙖𝙠𝙪 𝙩𝙖𝙡𝙡𝙖𝙣𝙠𝙪 𝙖 𝙧𝙖𝙝𝙪𝙨𝙖 𝙢𝙖𝙞 𝙨𝙖𝙪𝙦𝙞, wai hausawa sukace sai an gwada akan san na qwarai. Ni Hareeyh ina maraba da ku masoya, har da alakoron talla inayi😁
NOTED : karku nemeni a wannan layi 08146292652 domin yanzu baya aiki both whatsapp and call.