Kenza eBookz

'yar sarki ce by uwar batoolerh - Chapter 9

'yar sarki ce by uwar batoolerh - Chapter 9

'yar sarki ce by uwar batoolerh Chapter 9: 'yar sarki ce by uwar batoolerh Chapter 9. Da sallama mai martaba ya shiga palourn baqin nasa, amsa masa suka yi…

4,449 words

Da sallama mai martaba ya shiga palourn baqin nasa, amsa masa suka yi ya qarasa ya samu kujera ya zauna. Duk yunqurin sauqa qasa suka yi dan gaida sa mai martaba yayi saurin dakatar dasu "haba ku kuwa kuyi haquri mana ku zauna, bákomi wallahi" sarki ya faɗa da murmushi. Gaggaisawa suka yi duka, mai martaba ya qara gode masu da masu ban gajiya. Gabatar da kansu suka fara yi ga Sarkin. Mutumin farko dake sanye da qananun kaya yace "sunana Peter James, wannan corporal abeed ibn Zayd, wannan major Ibrahim khadeer sai kuma marshal Abubakar Idris. Murmusawa mai martaba yayi, gaskiya muna godiya sosai naji daɗin zuwanku kunga yanzu sanadi yasa ansan juna, sai dai bansan daga ina kuke ba. Wannan mai qananun kayan shi ya kuma magana, yace "Ni daga Dubai nake nine shugaban sojojin Dubai, abeed ibn Zayd daga Bahrain yake, Ibrahim khadeer daga Nigeria sai kuma Abubakar Idris da ke nan qasan Qatar a yankin Doha." Mai martaba da murmushi yace " a'a wai Abubakar dai wanda na sani? Ya aka yi tom ban ganeka ba?" Abubakar wanda ke sanye da jallabiya da hirami a kansa murmusawa yayi yai washe baki yace "Allah ja kwanan mai martaba aimana afuwa, ayyukan ne sai a hankali tun bayan appointment ɗin ban zauna ba sai this time, to Yanzu ma wani shungullan ake yi naji labarin wannan taro nace Tom insha Allahu zamu halarci wannan taro". Mai martaba yace "Allah yayi jagora bákomi marshal Allah temaka sannun ku da qoqari gaskiya ina godiya" Marshal Abubakar ne ya nisa yace "ranka shidaɗe mai martaba dama dai wani kyauta ne daga garemu kuma haɗe da roqo fatan za'a duba roqon namu". A'a Abubakar mai zai hana mu amsan kyautan naku tunda dai duka gida muke, karka damu muna godiya, menene roqon naku? Faɗin mai martaba. Allah qarama tsawon rai dama akan wannan bikin da za'a yi ne, kyautan mu shine Captain Peter yace yanaso yayi magana da wannan yaron da yaci gasan akan zai ɗauki nauyin komi da Yakamata yaron yayi zai masa shine kyautan sa, abeed ibn Zayd kuma ya basa kyautan motor, sai Ibrahim khadeer da yake roqon in ba mastala yanaso su ɗauki yaron aikin soja a can Nigeria, Tom maganan Ibrahim kam Ni da kaina nace a'a dan gida bata qoshi ba baza'a bawa waje ba muma in da dama muna buqata. Numfasawa mai martaba yayi, yace "shukran shukran gaskiya ina godiya sosai, Allah saka da alheri abu yayi kyau sosai an gode. Maganan aikin soja kuma ni bazan ce komi ba amma dai da Nigeria da Doha duk gidane insha Allahu, sai dai kuma in munji daga bakin sa, muma nan shine yariman mu na gobe in Allah ya yarda. Zantawa suka ci gaba dayi tsakaninsu cikin fara'a kaman waɗan da suka jima da sanin juna! Mai martaba ya qira waziri akan a maida su masauqin su ganin dare yayi lokaci ya ja sun ce zasu koma da wuri gobe, sunyi sallama da mai martaba suka bi wanda zai masu jagora har masauqin nasu. Mai martaba ko da ya tashi ɗakin sa ya wuce, babban rigan jikin sa ya cire ya rage kayan jikin sa ya shiga banɗaki ya wasta ruwa. Shiryawa yayi cikin kaya mara nauyi ya ɗau alkyabban sa ya sanya, fitowa yayi ya nufi sashen matar tasa...

Umma da Abba sun nemi taxi ya kaisu har gida, da sallama suka shiga gidan nasu shiru ba'a amsa ba, qaran ruwan da suka jiyo a banɗaki shi ya tabbatar masu Amjad ya dawo. Taburma Umma ta ɗauko ta shimfiɗa, ta wuce madafin su ta dauko kulolin abincin nasu ta jera, bayan ta gama ta shige ɗaki wajan Abba. Samun Abba tayi yana rage kayan jikin sa, sanda ta taya sa kamun ta fito a ɗakin dai-dai Amjad ya fito banɗakin. Ayoyo Umma ya sannu da dawowa, sannun ka jarumin Ummansa je ka shirya kazo ba baka abinci nasan ka gaji ga kuma yunwa, amsawa yayi "Tom Ummata" ya wuce ɗakin sa. Umma ruwan wanka ta kaiwa Abba banɗakin, ta dawo ɗakin nata, Abban jarumin Umma nakai ruwan wankan aje a wasta . Fitowa a ɗakin Abba yayi yana zolayan Umma "bazaki zo ki mawa mijin ki wanka ya gaji". Murmusawa Umma tayi tace "umm Abban yarona kai da ka girma nan da kwanaki zaka ji anfara ce maka kaka" Abba murmushi yayi yace "wai dai yanzu kice kishi kike tun da an kusa haifamun Amarya sabuwa gal. Umma murmushi tayi batace komai ba, Abba ya shiga wanka ya wasta ruwan ya fito ya shirya, Amjad ma ya fito a shirye, tabarman da Umma ta shimfiɗa masu Abba da Amjad suka zauna suna fira Abba na zoyalan sa. Umma wasta ruwa tayi ta shirya cikin kaya marassa nauyi, zuwa tayi ta zauna a tabarman gefen ɗan nata. Abinci ta zuba masu duka, kallon Abba tayi tace bismillahi Abban Yarona. Da hanun ta take ɗibo abinci tana bawa yaron nata a baki, Abba zuba masu ido yayi yace "wato dai a gidan nan kullum sai an nuna banbanci, yanzu mutumin da nan da shekara zai haifoman jika shine ake bawa abinci a baki" Amjad murmushi yayi! Abba yanxu dai jinjiri dani kake wannan magana? Umma ce tasa masu baki a maganan nasu, ba kyau surutu in ana cin abinci. Shiru suka yi Abba yaci gaba da cin abincin sa, Umma ta ciyar da ɗan ta sanda ya qoshi kamun ta sawa cikin ta. Bayan sun gama cin abincin tattare kwanukan Umma tayi ta ajiye gefe suka kama hira, sallahn magrib da aka qira shi ya tada su duka suka yi alwala Amjad suka yi masallaci dan yin Sallah Umma kuma ta tada nata a gida.

Da sallama mai martaba ya shiga ɗakin matar tasa, akwance ya same ta kaman yadda ya tsammani, Gimbiya ta rungume ta tana baccin itama a gefen ta . Kallon su yayi sai ƴar tasa ta basa tausayi, shi ciwon rashin uwa bai da daɗi! Ita kuma nata qaddaran ga uwan amma bata da lafiyan da ma zatayi hira da ita bare ta bata shawara ko ta mata faɗa, Allah baki lafiya Meerah. Hawaye ne ya cika idon mai martaba wanda ke nuni da cewa abu ya tuna, banɗakin ɗakin ya wuce yayi alwala yazo ya tada sallah, nafilfulu yayi ya ɗaga hanun sa sama yana addu'a hawaye na bin fuskan sa. Ya ɗau stawon lokaci yana addu'an kamun ya miqe ya naɗe darduman, ganin ƴar tasa na kwance gefen mahaifiyar ta bai yi gigin tashin ta ba, addu'a ya masu ya shafa masu ya ja masu qofan ɗakin ya fita ya nufi sashen sa. Rage kayan jikin sa yayi ya kashe wutan dakin ya kwanta, amma bacci ya kasa ɗaukan mai martaba sai juyi yake, daga qarshe alwalan ya qara ɗauro wa yazo ya tada sallah kuma.

Bayan dawowan su masallaci suna zaune duka Amjad, Abba da Umma sai aka masu sallama a qofan gida, da mamaki Umma ta kalli qofan sai Abba ya yunqura zai tashi, Amjad yace "Abba ka zauna zanje na duba waye ne" ya tashi ya nufi qofan gidan. Amsa Sallaman yayi ganin dogari ne daga fada sai ya masa iso cikin gidan amma sai dogarin yace "a'a ranka ya daɗe nanma yayi, saqon qira ne daga mai martaba, yana buqatan ganin ka gobe da sassafe bayan sallahn asuba" Amjad yace "tom shikkenan Insha Allahu zanzo da safen" godiya Amjad ya masa suka yi sallama dogarin ga juya ya shiga motor ya kama hanyan komawa fada. Ko da ɗan aiken ya tafi kulle qofan gidan Amjad yayi ya dawo ya zauna gefen Umman sa, Abba ne yace "waye ne yayi sallaman? Amjad ya ce "dogari ne ya zo wai mai martaba ya turo sa, nan ya kwashe duk yacce suka yi da dogarin ya faɗawa wa iyayen nasa". Umma ce ta nisa tace "Allah gwada mana goben da rai da lafiya, Allah shige lamarin ka Allah maka albarka ya dafa maka Jarumin Ummansa. Da Ameen suka amsa shi da Abban nasa. Umma ce tayi gyaran murya tace "Jarumin Umma mai yasa ɗazu ka maida hanun kyauta baya ? Meyasa kayi jayayya da maganan babba? Sunkuyar da kansa Amjad yayi ya buɗi baki yace "Umma ta kiyi haquri ki yafemun, kece kika haifeni na kuma kika mun tarbiyya na tabbata kinfi kowa sanin waye ni, in wasu zasu gane ma da su tambayen dalilin qin amsan wannan dukiya ke ya kamata su tambaya dan kece mahaifiya ta, ko mai nayi cikin tarbiyan ki ne. Umma ba jayayya nayi da mai martaba ba face nema wa kaina da iyayena dama ita kanta Gimbiyar mutunci a idon duniya, sannan maganan kyauta kuma Umma yacce muke rayuwanmu haka yafi burgeni, nasan tunda mai martaba yasan daga gidan da nake kuma ya yarje na shiga jerin masu hasa hakan ya tabbatar ya aminta ƴar sa tayi irin rayuwan da muke saboda baiga qazanta a ciki ba, Umma ina mai neman afuwanku ku yafemun na yanke hukunci ba tare da yin shawara daku ba, juyawa yayi wajan Abba , Abba ku gafarce Ni in nayi ba daidai ba. Murmushi Abba yayi ya sauqe hannun ɗan nasa da ya haɗa alaman roqon afuwan su yace "Allah maka albarka baba na Allah dafa maka a rayuwanka gabanka da bayanka hukunci da ka yanke da dalilin hukuncin duka sunyi sai dai muyi fatan Allah ara mana stawon rai muga bikin nan har da ƴan jikokin mu. Umma ma da murmushi tace "Ameen Angon Amare masu zuwa, Jarumin Umma Allah maka albarka, akoda yaushe ina kasancewa cikin Godiyan Allah da ya bani kai a matsayin ɗa na tabbas akace ɗaya mai albarka yafi dubu taron yuyuyu, Allah maka albarka Allah tabbatar maka da dukkan alkhaeran rayuwanka". Hira suka ɗan taɓa akan abin da ya gudana yau a cikin garin nasu,. Bayan wasu a wanni tashuwa suka yi duka, raka Amjad ɗakin sa suka yi, Umma ta masa addu'a suka ja masa qofan ɗaki suka nufi nasu ɗakin.

_________

Ameera da Daddyn Little mutan Abuja jirgin su yayi landing lafiya, taxi ne ya kwashesu sai gidan su dake anguwan Asoo road a cikin garin Abuja. Sun yi isan yamma wanda hakan ya sanya bata yi girki ba bayan sun huta suka tafi eatery suka ci abinci suka dawo, da wuri suka kwanta dan gobe Daddyn Little na da morning meeting a wajan aiki kuma ya kwana biyu bayanan. Yana aiki a 𝘾𝘽𝙉 (𝙘𝙚𝙣𝙩𝙧𝙖𝙡 𝙗𝙖𝙣𝙠 𝙤𝙛 𝙣𝙞𝙜𝙚𝙧𝙞𝙖).

𝙒𝘼𝙎𝙃𝙀 𝙂𝘼𝙍𝙄.....

Amjad bayan sunyi Sallahn asuba sallama ya wa Abban sa, daga masallacin bai koma gida ba hanyan gidan Sarki ya kama dan amsa qiran mai martaba, tafiya ne mai ratan gaske tsakanin su da gidan sarautan, dan gari ne guda Masarautan nasu. Masarautan qubaish cikin jihar Al-khawr a qasan Qatar.

Gimbiya ba itace ta farka ba sai qiran farko na asuba, janye jikinta a na mahaifiyar ta tayi taje ta ɗauro alwala ta tada sallah. Mai martaba ne ya shigo ɗakin da zummar tada su Gimbiya suyi Sallah, bakin sa ɗauke da sallama ya shigo tarar da Gimbiya yayi akan sallaya tana nafila, ganin haka sai ya juya da niyan fita a ɗakin, mai ya tuna sai kuma ya dawo zama yayi bakin gadon ya jira ƴar tasa ta idar da raka'atainil fijir. Ko da ta idar durqusawa tayi ta gaida sa, sabahul khair papa, mai martaba yace "sabahul Noor ibnateey, khaifa antee khaifa Amma ki? Nahnu bi Khair papa, khaifal umur? Ibnateey umur sai shukran Lillah... Bayan sun gama gaisawa mai martaba yace "inkin idar da sallah anjuma inason ganinki kamun gari ya gama waye wa" ya faɗa yana miqewa dan fita zuwa masallaci. Tom Papa Allah kaimu adawo lafiya Allah amshi ibadunmu, da Ameen mai martaba ya amsa ya fice a ɗakin. Gimbiya carbi ta jawo ta fara lazumin ta kamun a shiga sallah.

Amjad ya iso gidan sarautan lokacin gari yayi haske, yana isowa qofan fada dogarayen dake wajan suka miqe suna gaida sa, fuska a sake ya ɗaga hannu ya amsa. Wani a cikin dogarayen ne ya masa jaroga har zuwa qofan shiga palourn baqi na mai martaba, suna zuwa qofan dogarin yace "ranka ya daɗe za'a maka iso ni iya nan ne mastaya ta, afito lafiya" yana gama faɗa ya juya ya bar Amjad tsaye a wajan. Yana tsaye wani dogari yazo ya masa iso har cikin palourn baqin, palourn mai girma ne yana ɗauke da set na kujeru 2 sai TV dake maqale a bangon palourn sai fridge babba a gefe, akwai toilet guda biyu a palourn da dai sauran su, palourn ko a Saudi albarka kenan. Wani qofa dogarin ya nuna masa, yace "ranka ya daɗe wannan qofan zaka shiga mai martaba na ciki, afito lafiya ya masa" ya juya ya fita a wannan palourn. Kallon ɗayan qofan yayi ya tunkare sa, sallama yayi a bakin qofan sanda aka amsa masa kamun ya tura qofan ya shiga palourn. Mai martaba ne a kishingiɗe sai wasu mutane guda huɗu a palourn, girman wannan palourn ya ninka wanda ya wuce domin kuwa wannan set na kujeru uku 3 ne aciki, sannan ga kumbo a jere a qasa set huɗu 4. Mai martaba na kishingiɗe a shumfiɗeɗɗen carpet da aka jera kumbon akai riqe da carbin sa, sauran mutane huɗun suna zaune a qasa da alama tattauna wa suke. Zaunawa yayi a qasa shima ya sunkuyar da kai ya gaida mai martaba cikin girmamawa mai martaba da murmushi a fuskan sa ya amsa yana "ka saki jikin ka yarona Muhammadu" qara yin qasa da kai Amjad yayi ya kuma gaida waɗannan mutane suna cikin girmamawa, duk suka amsa da fara'a. Mai martaba ne yayi gyaran murya kamun ya fara magana "Yarona Muhammadu waɗan nan da kake gani baqi ne da suka samu halartan wannan gasa da kuka yi jiya, sunji daɗin irin salonka kuma sun yaba da kwarjinin ka da jarumtar ka, wanda hakan har ya kwaɗaita masu neman wata alfarma a wajanka da kuma qarin kyauta na yabawa bajintan ka, nan mai martaba ya kwashe yacce suka yi da mutanen, abubuwan da suka faɗa da kuma daga inda suke duka ya faɗawa Amjad en, sannan ya faɗa masa amsan da ya basu, yanzu sun buqaci ganin ka dan amsa a bakin mai shi yafi daɗi, yanzu dai muna sauraran ka Muhammadu, mai martaba ya faɗa yana mai da kallon sa kan Amjad wanda kansa ke sunkuye. Shirun da Amjad yayi shi ya qara burge Mai martaba dan ko ba komi tunanin babba da yaro ba ɗaya ba, yasan tabbas abun da ke ran Amjad bai wuce son shawartan iyayen sa ba. Mai martaba ya nisa yace "ya kayi shiru Muhammadu ? Amjad Ya buɗe baki zai yi magana corp. Abeed ibn Zayd ya tari numfashin sa yace "ina ganin a barsa yayi shawara na, mu zamu tafi inyaso ko mai ya yanke daga baya a sanar damu mai martaba amma maganan kyautan goben nan Insha Allahu komi zai iso sa, hidiman biki kuma Allah nuna mana lokaci duk abin buqata za'a yi. Mai martaba yace "shikkenan hakan za'a yi Allah mai daku lafiya, muna godiya sosai sosai". Amjad sai lokacin ya ɗago kan sa, godiya ya musu sosai da addu'oee. Bayan sun kammala maganan Sallaman mai martaba suka yi duka suka miqe dan su samu su wuce akan lokaci, qara godiya Amjad yayi ya bisu da addu'an Allah stare hanya.

Bayan fitan su mai martaba yayi qiran wani dogari, da dogarin ya shigo ce masa yayi "a qiramun Gimbiya ta iso" amsawa dogarin yayi ya bi ɗayan qofan ya fice. Ko da ya fita ya samu Gimbiya a main palourn sashen mai martaba a zaune don dama already mai martaba ya qira ta a waya jira take a mata izin isa ciki. Dogarin durqusawa yayi, yace "Allah ja kwanan Gimbiya Allah baki tsawon rai mai martaba na maki iso" gyaɗa kai kawai tayi ta miqe ta nufi palourn ko da ta isa bakin qofan janye abun da ta rufe fuskanta tayi ta kama handle en qofan ta murɗa ta shiga. "Assalamualaikum" ta furta yayin da take shiga palourn, jin muryanta ya sanya shi ɗagowa, kallo ɗaya ya mata ya kau da kai. Amsa Sallaman suka yi shi da mai martaba, ganin sa a palourn ya sanya ta jin haushi buɗe fuskan ta da tayi, ba yacce ta iya haka ta qaraso ta zauna a wasa kusa da mahaifin nata, bata ko kalli inda Amjad yake ba tawa mahaifin nata Barka da hutawa ya amsa. Mai martaba kallon su yayi duka biyun ya ga kowannen su gefe yake kallo kuma ba mai alaman yiwa ɗan uwan sa magana, girgiza kai yayi faɗi yake a ransa "duk zaku yi ku bari zaku dedeta kanku ba wanda ya sani".

Gyaran murya mai martaba yayi sannan ya fara magana kaman haka "inban manta ba dama nayi daku akwai sharaɗi na biyu dukanku ga duk wanda yaci wannan gasa, wanda wannan sharaɗin nace ba dole bane shi babban damuwan shine gasan, fatan kana tune da wannan magana Yarona"? Gyaɗa kai Amjad yayi yace "eh ranka shidaɗe ina tune da maganan ɗayan sharaɗin" to Allah maka albarka, maganan ɗayan sharaɗin zaku yisa da ita Gimbiya amma kamun nan inason sanin dalilinka na qin Karɓan dukiya da nace zan bawa wanda yaci gasan. Cikin girmamawa Amjad ya fara magana "Ina mai neman afuwanka mai martaba akan wannan abu da na yanke ba tare da wani dalili ba. Jinjina kai mai martaba yayi yace "shikkenan Yarona Muhammadu Allah maku albarka duka, da Ameen ya amsa, Gimbiya kuwa tana sauraran su batace qala ba. Mai martaba ne ya kalleta yace "Gimbiya maganan ɗayan sharadinki zaku yi tsakaninku, ni kuma na gama nawa maganan Aure nan da wata huɗu 4 in Allah ya yarda, sannan zai cigaba da zuwa wajan ki daganan har lokacin da al'ada ta ɗibar bazai ganki ba in anfara hidima. Kai kuma yaro na zaka iya zuwa cikin gidan nan a duk lokaci da kaga dama ba tare da sai anmaka iso ba ko jagora kaima ɗan gida ne nan gidanku ne. Godiya Amjad yayi wa mai martaba dake qoqarin miqewa, tashuwa mai martaba yayi yace tom "zan tafi fada Gimbiya zata kawo maka abun karyawa banyarda ka fita a gidan nan ba tare da ka karya ba, gyaɗa kai Amjad yayi Tom ranka shidaɗe, ke kuma Gimbiya ki sa a kawo masa abun karyawa ki tabbatar ya karya kamun ya tafi" mai martaba na gama magana ya buɗe qofan ya fice a palourn. Mai martaba na fita ta tashi ta koma kan kujera ta zauna ta maida abun fuskanta ta rufe. Murmushin gefen baki Amjad yayi ganin yacce take wani cika tana batsewa, kau da kai yayi kaman baison yin magana yace "Malama Gimbiya ki cire abunda kika sa a fuskan naki sai muyi magana ko" A gadarance tace malami baza'a cire ba in ya dameka zaka iya zuwa ka cire bazan cire ba, kamun ta rufe baki taga mutun a gefenta( hhhh!!! aiki da cikawa) Saurin matsawa tayi ta yaye abun fuskan nata ta harari gefe tana tura baki, cewa yayi "na zaci zaki tsaya na cire ne kinsan qaramin aiki nane acikin abubuwan da zan iya" suna cikin haka jakadiya tayi sallama ta shigo ɗauke da qaton tire da aka cika da kayan abinci kala-kala da kuma kayan marmari da abubuwan sha, ganin Amjad kusa da Gimbiya sai tayi qasa da kanta. Tashuwa Amjad yayi ya koma ɗayan kujeran ya zauna ya dake kaman ba shi ba, qarasowa tayi ta ajiye tiren abincin a gaban Amjad, ta tashi ta juya zata fita Gimbiya tace "wa zai zuba masa abincin in kin tafi? Kallon Gimbiya Amjad yayi ya kalli jakadiya dake shirin dawowa dan zuba Abincin yace "karki damu baiwar Allah zaki iya tafiya" godiya jakadiyan tayi ta juya ta fice a Palourn. Kauda kai Gimbiya tayi tace "da ka bari ta tafi kai zaka zubawa kanka abinci ko waye? Ya kalleta yace "Ke zaki zuba mun ba wata ba, sannan ina fatan kin iya feeding. Saurin kallonshi tayi ta buɗe qaramin bakinta ta murmusa! Subhanallahi Murmushin da ya kusa ɗauke wa Amjad numfashin sa da sauran jarumtar da yake da, tace "you most be joking indai MEHWISH ce kake nufin zata yi serving naka and kana magana akan feeding, girgiza kai tayi tace funny you". Duk maganan da yake kaman an sashi dole yayi haka yake maganan, dogon magana in ba da Ummansa ba bayayi bai saba ba magana wahala yake basa wani bin har yayi ciwon kai in ya yawaita magana. Ba tare da ya kalleta ba yace "can you come and serve me or I should come over there and make you serve me"? hararan gefen da yake zaune tayi taqi tasowa, kallon hararan yayi ta gefen ido ya ɗan yi Murmushi irin na nafiki iskancin nan, aransa kuwa cewa yake "zaki setu ne yarinya bari ki shiga hannu duk stiwan naki zan magance sa staff" a zahirin kuwa da ya murmusa baice qala ba, illa miqa hanu da yayi ya ɗau apple yana ci.

Ganin yana cin apple cewa tayi "better da ka taimaki kanka ka nemi abinci if not ba randa zan yi serving naka ni Mehwish" ta faɗa tana karkaɗa qafan da tayi Cross-leg tana danna wayan da ke hanun ta qirar iPhone 14 pro. Kallon ta yayi, baice komi ba yaci gaba da taunan apple nasa kaman yana storon taunawa. Jin bece komi ba takuma cewa "Yes gwanda kayi shiru dan ni ɗin ƳAR SARKI CE ko aurena kayi sai dai nasa amaka ba dai na maka ba, inkuma ka hana sai kayi da kanka faqat". Ba tare da ya kalle ta ba yace "ke kikasan ke ƴar Sarki ce, for me I don't know this, all i know is that ke mata tace I will soon own you and make you deed whatever I want, so you should be minding your words dan karki bari nasa harda wanke bayi a ayyukan da xakiyi a gidana nan da wata huɗu. Saurin kallonsa tayi tace "Au ashe har;na zama matarka, and kana lissafin zanyi ayyuka, murmushi kawai tayi tana kallonsa. Lumshe ido yayi, bai ce komai ba, gaba ɗaya kallonta da irin kallon da take masa da wannan killer smile natan na haddasa masa shiga yanayin da bai son kusantan sa bare ya shiga, stiririn tsaki yaja kaman a kasalance yace "can you please stop looking at me with dis ur tiny eye's" haɗe fuska tayi alaman taji haushin abinda yace, cewa tayi "Ko makaho ya ganni ya san idanuna ba qanana bane bare mai ido. taci gaba da cewa "am abu na gaba da yake sharaɗin qarshe wanda zai tabbatar mun zaka iya aurena ko ba zaka iyaba shine, mahaifiyata bata da lafiya kuma a sharaɗina dole wanda zan aura sai ya nema mata magani, mai martaba yace maka wannan sharaɗin bai zama dole ba amma ina so na sanar maka wannan ne babban sharaɗi na. Yana jinta har ta gama magana bai ce ko qala ba, ko ci kanki baice ba. Tashuwa tayi tace" inka gama zaka iya biyo ni muje ka ganta" tana gama faɗan haka ba tare da ta staya ba tayi gaba abunta. Tashuwa yayi ya bi bayanta, ba ta ainafin cikin gidan suka bi ba ta cikin sashen mai martaba suka bi hanyan da zai sada su da shashen Sarauniyar. duk inda suka wuce bayin wajan gaida su suke har qasa da shi da ita duka. Sun iso qofan ɗakin ta buɗe qofan t masa iso, da sallama dukansu abakinsu suka shiga ɗakin, a kwance Amman nata take sai dai da alama mai martaba ya goge mata jiki ya sauya mata kaya (dama ko shi ko Gimbiya suke wannan aikin). Tace masa "ga Ammaa na, a take kuma sai kwallah ya cika idonta, tun da ya ɗaura idon sa akan matar yaji tausayin ta da na iyalanta duka ya rasta jikin sa, sai ya raya da ace ke wannan ciwo ya zaiji, a take ya ji mugun tausayin Gimbiya ya shigesa lokaci ɗaya. Zuwa kusa da Ammaan nata yayi ya durqusa a gefen gadon, addu'oee masu yawan gaske yayi mata na karya sihiri da kuma kariya da neman sauqi, ya kuwa minti talatin a durqushe, da ya idar da addu'an ya kama kanta ya tofa ya shafa mata. Miqewa yayi ya masta kusa da ita yace "karki sa damuwa a ranki Insha Allahu Ammaa zata samu lafiya bada jimawa ba kuma Ni Muhammad Amjad na maki alqawarin sai randa na samowa mahaifiyar ki magani tukunna za'a yi aure na dake, inafatan hakan ya maki? Ba tare da ta kalle sa ba ta share hawayen ta ta ɗaga kai.

Daga haka ya miqe zai fice bayan sa tabi har suka fita a sashen mahaifiyar tata, ba wanda yace da ɗan uwansa qala kowa da abinda yake tunani a ransa, rakasa tayi ta juyo ɗakin ta ta wuce direct, tana cike da alhinin Maganan ciwon Ammaa nata, ga shi maganan da yayi harda alqawari ya baya mamaki dan tasan mai martaba bazai taɓa fasa maganan auren nan da wata huɗu ba. Sai dai har a ranta ta yarda da shi tana ji a jikinta Insha Allahu za'a dace.

Maganan da basu qarasa ba kenan shima ya fito, dogari ne yazo da motor ya staya gefen sa ƴallaɓoi ka shigo mai martaba yace a kaika gida, ba musu ya buɗe murfin baya ya shiga dogarin yaja motor suka nufi gidan su Amjad..

Dogarin har qofan gida ya kawo sa, sauqa yayi ya masa sallama ya tura qofan gidan nasu ya shige. Abban sa ya tafi kasuwa Umma ce kawai a gida ya sameta. Ummansa na kallonsa ta yi guɗa tana murmushi tace "Kaga Angon Gimbiya Jarumin Umma ɗan gidan Abba" Amjad murmushi kawai yayi wa Umman tasa amma bai ce komi ba. Ganin yanayin sa sai jikin Umman sa yayi sanyi, amma batayi yunqurin tambayan sa me yake faruwa ba. Ruwan wanka ta kai masa yaje yayi wanka. Bayan ya fito Umma tace masa "jarumin Umma zo ka karya" Umma ta a qoshe nake na karya a can. Ko ba komi taji daɗin da har ya karya a can ɗin hakan na nufin Insha Allahu komai lafiya, sai ta ci gaba da ayyukan ta, shi kuma ya shirya ya fito ya ma Umman tasa sallama ya bi Abban sa kasuwa.

Ko da ya isa kasuwan Abban sa yayi farincikin ganin sa, ya so tambayan sa ya suka yi a gidan Sarkin amma ganin suna kasuwa sai ya bari sai sun koma gida zai tambayesa. nan suka zauna suna kasuwan su tare sannan Amjad ya kan yiwa Abban sa tambayoyi akan wasu ciwuka Abban sa na qara masa bayani, duk da dai shi irin sana'ar nan baiwa ce kawai ta Ubangiji...

Readers Also Read