Kenza eBookz

Yarima suhail complete novel - Chapter 31

Yarima suhail complete novel - Chapter 31

Yarima suhail complete novel Chapter 31: Yarima suhail complete novel Chapter 31. Yarima jin kukan nata yake har cikin ransa dan duk ta kashe masa jiki,…

3,356 words

Yarima jin kukan nata yake har cikin ransa dan duk ta kashe masa jiki, ahankali kamar mai jin bacci yace toh shikenan zan tafo miki da shi, kukan ya isa.

Zarah tsagaitawa tayi daga kukan da take tace toh nagode please kahad'o min da shawarma, sai kadawo.

Yarima tsinke wayar yayi tare da dafe kansa yana tunanin ta yadda zai fara tsayawa wajen me nama siyan nama, tsaki yaja nan yajanyo wayarsa yakira d'aya daga cikin yaransa yace yaje yasiyo mai balango mai dad'i da shawarma.

Yana gama wayan yamik'e yad'auki key d'in motansa yafito yanufi gida.

Zarah bayan sungama wayar dariya tayi sannan tatashi tashiga wanka.

Bayan ta fito simple makeup tayi nan tashirya cikin gown d'inta maikyau. Saida tayi sallah sannan tajanyo wayarta takira su mama dan sugaisa, hira sukayi sosai nan mama take shaida mata jibi za'ayi baikon Aysha da malam bello, Zarah murna tayi sosai dan har cikin ranta taji dad'in hakan dan tasan malam bello zai kular mata da k'anwarta, nan tace insha Allahu zata shigo ranar, bayan sun gama waya da mama takira Aysha sukasha waya tana tsokanarta daga nan kuma tasa taba yaya rauda wayar nan ma sukaita hirarsu sun dad'e suna hira sannan sukayi sallama.

Mik'ewa Zarah tayi tad'auko veil d'in gown d'in, a gaban dreesing mirrow tatsaya tatufke kanta tayi kamar gambo sannan tayi rolling d'in k'aramin veil d'in nata nan tayi gwanin kyau, tafito tanufi part d'in yarima dan tasan indai ba ita tajeba toh mawuyacine yakawo mata dakansa.

A parlour tasamesa zaune yana waya, gefensa sumayya ce sai wannan cika take tana batsewa, ganin zarah yasa tawurga mata harara tace malama lafiya zaki shigo ma mutane? Murmushi zarah tayi tace malama ba fa wajenki nazoba.

Yarima da yake waya juyowa yayi yazuba mata ido, itama Zarah kallonsa tayi tasakar mai murmushi, muryar sumayya taji ta ce kedai wlh ban san wace irin natatta bace ke kullum kina manne da mutum, ta6e baki zarah tayi tace kanki akeji.

Yarima kashe wayar yayi batare da ya kallesuba yace kudai bakuda aiki sai fad'a.

Sumayya kwantar da kanta tayi a kafad'ansa tace dear itace tawani shigo ma mutane dan neman fad'a...tak'arashe maganar tare da wurga ma zarah harara.

Zarah murmushin mugunta tayi mata sannan ta ida isa gefen Yarima tazauna 6ata fuska tayi kamar zatayi kuka tace baby nifa zuwa kawai nayi inkar6i abinda nace kasiyo min wlh yunwa nakeji babynku yana wahalar da ni yau, janyo hannunsa tayi tad'aura saman cikinta tace baby kaji motsi yakemin....tak'arashe maganar tare da kashe mai ido d'aya.

Yarima janye idonsa yayi daga kallonta tare da safke ajiyar zuciya ahankali yace bari inkirasa.

Sumayya cikin 6acin rai tace babbar bura'uba ke wa zakiyi nuna ma duniyanci? Wlh baki isaba kanki farau cikine?

Zarah murmushi tayi tace sorry Auntyna wlh ba kaina farauba kawai dai ina buk'atar ci ne,

Yarima mik'ewa yayi tare da yin dialing d'in number d'in yaron nasa yana shirin kira, knocking d'in k'ofa da akayine yasa yabada izini ashigo.

'Daya daga cikin guards d'insane yashigo d'auke da leda d'an rissinawa yayi yace ranka yadad'e sak'one aka kawo maka.

Kar6a Yarima yayi batare da yayi magana ba, nan guard d'in yajuya yafita.

Yarima juyowa yayi ya kallesu duk sunci face, yanayin yadda sukayi ya so yabashi dariya, tsaye yayi da ledar sai chan yabud'e yaduba ganin kashi biyu ne yasa yad'auki kashi d'aya yamik'a ma sumayya yace ga naki.

Yamitsa fuska sumayya tayi tace duk naman da yake gidannan sai ansiyo na waje, ni gaskiya bazan iya ciba. Ta d'auka yarima zai lallasheta kawai sai gani tayi ya mik'a ma zarah duka ledar yace gashinan.

Kar6a zarah tayi tare da yin murmushi tace nagode sosai baby, nan tamik'e tare da kallon sumayya da tacika tayi fam tace Aunty sumy kiyi hak'uri idan na 6ata miki sai anjima, tana fad'in haka tajuya tafita tabar d'akin.

Yarima komawa yayi yazauna tare da d'auko remote yana canza channel, sumayya kallonsa tayi tace yarima kana ganin abinda yarinyarnan take min ammah baka iya yi mata magana.

Wani irin kallo yawurga mata kamar ba zaiyi maganaba sai kuma chan yace sumayya akan me zanyi magana bayan a da tana baki girmanki kece dai kikak'i kirik'e girman naki kinga kenan laifin nakine dan haka in zaki gyara toh kigyara.

Sumayya haushine yakamata gani take kamar ya goyi bayan zarah, yamutsa fuska tayi tace ya dai kamata kadinga adalci a tsakaninmu dan mu dukanmu matankane kuma ita d'in da kake ma rawan kai ai.......wata irin harara da yawurga matane yasa tayi shuru batare da ta k'arashe maganartaba,

Cigaba yayi da kallonsa inda Sumayya tamik'e cike da jin haushi taficce tabar d'akin.

Cikin rashin damuwa yarima yayi kwanciyarsa saman kujerar, dan shi yanzu halayyar Sumayya har ta daina bashi mamaki.

A chan 6angaren sultana sadiya koda jakadiya tadawo mata da kular tambayarta tayi zarah ta ci kwad'on? Jakadiya saida taduk'ar da kanta k'asa cike da girmamawa sannan tace eh ranki yadad'e dan dukansa tacinye ta ce tana godia sosai.

Murmushin jin dad'i sultana tayi sannan tace kai haba toh menene abun godia a ciki? Ai taimakon kai ne, yanzu zaki iya tafiya.

K'ara duk'awa jakadiya tayi tace toh ranki yadad'e atashi lafiya, tana fad'in haka ta tashi cikin sauri tabar d'akin.

Bayan ta fita sultana k'yalk'yalewa tayi da wata irin dariya tace yarinya bakisan wacece ni ba wayace miki koda da second d'aya zan iya sonki? Kallon agogon da take manne ga bangon d'akin tayi sannan tace nan da minti talatin cikinki zai tashi aiki, tana fad'in haka tayi murmushin mugunta sannan tajanyo wayarta takira sumayya nan tafad'a mata komai.

Sumayya murna tayi sosai har da 'yar taka rawarta nan tanemi 6acin ranta tarasa.

Yau ko da taje d'akin yarima da dare shi kansa saida yayi mamakin ganinta cikin farin ciki bai dai tambayetaba yashareta yai kwanciyarsa haka tazo bayansa takwanta yanajinta tarungumesa nan yamaida idanuwansa yalumshe ahaka bacci yai awon gaba da su.

Da safe sumayya sa wata kuyangarta tayi takular mata da duk wani motsin zarah dan ta yi tunanin za'a fito da ita aje asibiti ammah da mamakinta har wajen 10am ammah shuru dan haka tashirya da kanta tanufi part d'in zarah dan tagane ma idonta abinda yake faruwa, cikin ranta tace ina ma insameta kwance tana fama da ciwo, murmushine yakubce mata tace Allah yasa haka, daidai lokacin tad'aga labulen d'akin zarah tashiga, curus taja bakin k'ofa tatsaya ganin zarah da tayi zaune saman lallausan carpet d'in da yake shimfid'e a tsakiyan parlourn hannunta rik'e da waya tana dannawa da ka ganta kasan tana cikin k'oshin lafiya.

'Dago kai zarah tayi takalleta tare da sakar mata murmushi sannan tace sannu da zuwa Aunty sumy, kishigo man.

Ta6e baki sumayya tayi cike da mamaki tace bashi yakawoni ba.

Zarah ma kallonta takeyi tace toh me yakawoki?

Cikin nuna isa sumayya tace wannan ba matsalarki bace malama saidai inaso ink'ara tunatar miki akan mijina babu abinda ban iyayi, dan haka a kowane lokaci kisaurareni, tana fad'in haka tajuya tafita tabar d'akin.

Zarah binta tayi da kallo har tafita sannan tayi murmushi tace Allah yashiryaki sumayya, A kullum ba zan ta6a yin k'asa da gwiwaba wajen addu'a Allah yakareni daga dukkan sharrinku.

Sumayya tana fita bata zarce ko'inaba sai part d'inta a parlour tayada zango tashiga zagaye d'akin cike da tashin hankali nan takira wayan ummanta.

Ummah tana d'aga wayan sumayya tace ummah na shiga ukku wlh waccan matsiyaciyar tana nan lafiya lau babu abinda yasameta anya kuwa ummah kin zuba mata?

A firgice sultana sadiya tace sumayya me kikace? Tana nan lafiya lau fa kikace kai ba zan ta6a yaddaba.

Gimbiya sumayya kamar tafashe da kuka tace wlh ummah tana nan babu abinda yasameta ummah gaskiya cutarki akayi ba maganin zubar da ciki bane aka baki.

Cike da jin haushi ummah tace ke gidanku sumayya da me zanji da rashin zubewar cikin ko da banzar maganarki marar amfani, ni babu wanda yacuceni wannan maganin na sanshi kuma nasan nazubar da cikine dan da anyi amfani da shi ba'ayin rabin awa sai ciki ya fita , toh inhakane ya akayi cikin nata bai zubeba? Shuru ummah tayi tana nazari sai chan tace kenan hakan yana nufin zarah bataci k'wad'onba? Tabbas bataciba.

Sumayya cike da mamaki tace ummah kina nufin bata ciba? Toh ko tasan k'ullalliyar da kikayi matane?

Ummah girgiza kai tayi kamar tana a gaban sumayya, tace batasan komai ba akan haka saidai idan wani dalili yahanata ci.

Toh fa ummah yanzu ya za'ayi wlh banason cikinnan nata kokad'an...sumayya tak'arashe maganarta cikin kuka.

Ajiyar zuciya sultana sadiya tayi tace kidaina kuka sumayya kikwantar da hankalinki yau zansa ashirya mata wani kwad'on ni zanje da kaina inkai mata taci.

Sumayya fashewa tayi da dariya kamar ba ita bace take kuka cike da jin dad'i tace ummah hakan kawai za'ayi gaskiya da kin gama min komai dan ni yanzu wlh cikinta ya fi aurenta da yarima d'agamin hankali.

Hmm duka dai da matsala sumayya ammah dasannu zamu magance komai.

Sumayya cikin jin dad'i tace Allah yabar min ke ummana.

Dariya sultana sadiya tayi tace Ameen shalelena yanzu dai bari inje inyi abinda yadace.

Toh ummana sai najiki, nan sukayi sallama kowa yakashe wayarsa.

Sultana sadiya k'wala ma d'aya daga cikin kuyanginta kira tayi, cikin sauri tashigo jikinta yana rawa taduk'a cikin girmamawa tace ranki yadad'e na amsa kiranki.

Yamitsa fuska sultana sadiya tayi sannan tace kije kisami baiwata sabura kice nace yanzu tahad'amin kwad'on zogale yaji kayan had'i sai takawo min nan ina jiranta.

Kuyangar tace toh ranki yadad'e angama, cikin sauri tamik'e tafita tabar d'akin.

Sultana sadiya maida kanta tayi ta jingine ga kujerar da take tana murmushin mugunta.

_Comment_ *nd* _Share_

_Sis Nerja'art✍🏻_ 👑👑👑

_*YARIMA SUHAIL*_

👑👑👑

_*Written By~Sis Nerja'art*_

_*DEDICATED TO MY DAUGHTER ZARAH*_

https://m.facebook.com/Intelligent-Writes-ASSO-294634797868361/

*INTELLIGENT WRITER'S ASSOCIATION ®* *[onward together]* *{ we give the readers of ours the best out of the bests,,our inks are melodious and dropping a kinda lights to readers }* THE PEN OF LOVE 😘 HEART TORCHING ❤ TEARS OF SORROWS 😭 CURDLES 🙂 GIGGLES 😁 AND MARRIEGE THINK💑 *JUST GIVE US FOLLOW....*✔

_Masha Allah my friendy *Sadiya Sidi S* Ina tayaki murnar fara sabon novel d'inki mai taken *RAYUWAR MATA* yadda kika fara lafiya Allah yasa kigama lafiya, Allah yabamu ikon d'aukan darasin da yake cikinsa, kurakuren da suke ciki Allah yayafe miki, I hrt u over dear😘_

*PAGE* 5⃣0⃣

Sultana sadiya tana nan zaune tana sak'e-sak'e a ranta a k'allah ta ci kusan minti goma sha biyar a haka, zuwan da baiwarta tayine yasa tabata izini tashigo.

Baiwar shigowa tayi d'auke da wata kula a hannunta cikin sauri tazube k'asa tana kwasar gaisuwa wajen sultana sadiya.

Sultana yatsine fuska tayi sannan ta amsa ciki-ciki, baiwar k'ara duk'ar da kanta tayi sannan tace ranki yadad'e na cika umurninki.

Sultana kallon kular tayi sannan tace bud'e mugani, Cikin sauri tabud'e mata, tana addu'a cikin ranta Allah yasa kar sultana tace baiyiba dan tana tsoron wulak'ancinta.

Ta6e baki sultana tayi tace tashi kitafi.

Cike da jin dad'i baiwar tace toh ranki yadad'e nabarki lafiya, tana fad'in haka tamik'e cikin sauri tafita tabar d'akin.

Mik'ewa sultana sadiya tayi taje tad'auko maganin tazuba tamotse sannan tayi murmushi tace yau dai dole kicisa zarah, k'ulle maganin tayi tamaida ma'ajinsa sannan tadawo tasaka alkyabbarta tasa wata kuyangarta tad'aukar mata kular suka fito suka nufi 6angaren su zarah.

Zarah lokacin kwance take saman 3 seater tana ta juyi saboda wata irin yunwa da takeji gashi ta kasa cin komai, wayarta tad'auko takira yarima har tatsinke baiyi picking ba.

Haushine yakamata ta aje awar tana ta jan tsaki kad'an kad'an, bayan minti biyu sai ga kiransa ya shigo.

Zuba ma wayar ido tayi har tatsinke batare da tayi picking ba.

Daga chan 6angaren yarima da yafito wanka mamakine yakamasa ganin batayi picking ba kuma tsakanin kiran da tayi mai zuwa lokacin baifi 2 minutes ba, har zai k'ara kiranta a karo nabiyu sai chan 6angare d'aya na zuciyansa yace ba ajinka bane kak'ara kiranta, tsaki yaja ya aje wayan yacigaba da shirinsa ammah kuma duk da haka a cikin ransa yana jin ba dad'i dannewa kawai yakeyi dan shi abun har mamaki yake bashi ganin yadda yake ma zarah ko sumayya bata samun haka.

Lokacin da sultana sadiya ta iso part d'in zarah har a lokacin zarah tana kwance, ganin sultana sadiya yasa gabatanta yayi wani irin mummunan fad'uwa cikin ranta tsarin ubangiji take nema, koda sultana sadiya yau ma kamar jiya fuskarta a sake take.

Zarah cikin sauri tamik'e tsaye, murmushi tayi tare da d'an rissinawa tace ummah sannu da zuwa.

Sultana sadiya ma maida mata martanin murmushin tayi saida tazauna sannan tace yauwa zarah.

A k'asa zarah tazauna cikin girmamawa tagaisheta.

Amsa mata sultana sadiya tayi tace ya k'arfin jikin naki?

Zarah duk'ar da kanta tayi tace Alhmdllh ummah.

Kuyangar da sukazo tare da sultana sadiya duk'awa tayi tagaishe da zarah.

Cikin sakin fuska zarah ta amsa mata, nan sultana ta amshi kular tace tafita tajirata a waje, ahankali tace anganma ranki yadad'e sannan tamik'e cikin sauri tafita tabar d'akin.

Sultana sadiya kallonta tamaida ga zarah da take wasa da yatsun hannunta tace yau ma dai ga kwad'on na kawo miki dan nasan masu ciki akwaisu da kwad'ayi bare ma irin wad'annan kwad'on ganyukan...tak'arashe maganar tana 'yar dariya.

Murmushi zarah tayi tace toh ummah nagode sosai.

Sultana sadiya tace haba zarah ai bakomai ke da sumayya duk d'aya nad'aukeku.

Zarah ahankali tace hakane ummah Allah yasaka da alkhairi.

Ameen, kibud'e kigani man,,,cewar sultana sadiya.

Zarah bata musaba tajanyo kular tabud'e saida tahad'iyi yawu saboda kwad'on ya burgeta kamar taitaci dan ganinsa yasa yunwar da takeji ta tashi, maidawa tayi tarufe takalli sultana sadiya da tatsareta da ido tace ummah ya yi min sosai kuma nagode Allah yasaka da alkhairi.

Murmushi sultana sadiya tayi tace kar kidamu zarah, kici kawai naga kamar yunwa kikeji.

Gaban zarah saida yafad'i jin sultana ta ce taci cikin ranta tace Allah yaimin tsari da abinda kuke shiryawa akaina, itama murmushin tayi tace ummah zanci sai zuwa anjima yanzu bana jin cin komai.

Fara'ar da take fuskar sultana sadiya raguwa tayi tace haba zarah yau fa dakaina nayi kwad'on kuma nayo tattaki nakawo miki ai bai dace kik'i ciba.

Zarah marairaicewa tayi tace ummah zan ci ai inason kwad'on kawai dai nafiso sai zuwa anjima.

Sultana sadiya cikin ranta tace wannan d'iyan akwai d'an banzan wayau anya batagane abinda nayimataba? murmushi sultana sadiya tayi tace hakane ammah ko kad'anne kid'anci kiji.

Zarah kallon sultana sadiya tayi, gyad'a mata kai sultana tayi alamun taci.

Zarah ido tazuba ma kwad'on tarasa yadda zatayi tana tsoron taci asamu matsala, d'ago kai tayi takalli sultana.

Sultana sadiya tasakar mata murmushi tace kici man.

Zarah har ta kai hannu zata d'iba sai ga yarima ya shigo da sallamarsa da mamaki yake kallon sultana sadiya itama ido tazuba masa tana kallonsu dan kwata-kwata bataji dad'in zuwansaba.

Zarah hamdala tayi tare da janye hannunta daga cikin kular.

Sultana sadiya murmushi tasakar mai tace ranka yadad'e ashe kana nan ai ban saniba da na aiko ankiraka mun gaisa.

Yarima batare da ya ce mata komai ba yasamu waje yazauna, kallon Zarah yayi da take zaune gaban kula sannan yamaida kallonsa ga sultana sadiya, ahankali kamar wanda baya son magana yace ummah barka da rana?

Sultana sadiya washe baki tayi tace yauwa yarima dafatan na sameku lafiya? Ai na ji labarine wajen dada ashe amaryarmu batada lafiya shine nazo ind'an dubata.

Jinjina kai kawai yarima yayi batare da yayi maganaba,

Haushine yakama sultana sadiya cikin ranta tace ka ji dai da abunka munafuki, chan sai tace ya jikin nata?

Murmushi yarima yayi yace Alhmdllh

Kallon zarah yayi da tatsaresa da ido har ya bud'e baki zaiyi magana sai kuma yafasa janye idonsa yayi yamaida ga kallon dramar da ake a TV d'inta.

Wajen shuru yayi ba wanda yak'ara magana, ammah gabad'aya yarima hankalinsa yana ga zarah dan ransa ya bashi dakyar inba wani abu sultana sadiya take son shiryawaba.

Sultana sadiya ko ta cika ta yi fam takaicinta shigowar da yarima yayi batare da tasamu zarah ta ci kokad'an bane, ji take kamar tarufe yarima da duka, ganin baida niyar basu waje yasa takalli zarah tasakar mata murmushi tace dota bari intashi intafi Allah yak'ara lafiya.

Itama zarah murmushin tayi sannan tace nagode ummah, sultana sadiya kallon yarima tayi tawurga ma k'eyarsa harara sannan tace ni na wuce.

Yarima batare da ya juyo ya kalletaba yace toh ummah mungode.

Wucewa sultana sadiya tayi zata fita cikin sauri zarah tamik'e tabi bayanta koda suka fito sultana sadiya kallon zarah tayi fuskarta d'auke da murmushi tace zarah kikoma kar kibar mijinki shi kad'ai.

Zarah duk'ar da kanta tayi cike da jin kunya tace toh ummah mungode sosai Allah yabada lada,

Sultana sadiya tace Ameen.

har zarah ta juya zata tafi sai jin sultana sadiya tayi ta kira sunanta, tsayawa zarah tayi tare da juyowa. Murmushi sultana tasakar mata sannan tace dan Allah kitabbata kinci kwad'on nan ko kin d'an samu k'arfin jikinki dan daga ganin yanayinki yunwa kikeji, na san zai taimaka miki sosai idan kikaci kinga badad'i ace kina zama da yunwa.

Zarah murmushi itama tayi sannan tace toh ummah insha Allahu zan ci.

Cike da nuna kulawa sultana tace kin tabbata?

Zarah d'agamata kai tayi alamun eh.

Murmushin jin dad'i sultana sadiya tayi tace yauwa Allah yaimuku albarka.

Zarah tace Ameen ummah, nan suka k'ara bankwana sannan zarah tajuyo tadawo part d'inta, yarima har a lokacin yana zaune inda tabarsa, ahankali tace sannu da zuwa?

Yarima batare da ya kalletaba ya amsa

Wucewa tayi tad'auki kwad'on sai a lokacin yarima yajuyo yakalleta yace ina kika sami wannan abun?

Zarah kallon kular kwad'on tayi sannan tace ummah ce takawomin.

Ta6e baki yarima yayi sannan yace kinci? Girgiza mai kai kawai tayi alamun a'a.

Janye idonsa yayi daga kallonta sannan yace ban amince kiciba.

Zarah fuskarta d'auke da mamaki tace saboda mi?

Yarima juyowa yayi yawurga mata harara sannan yace saboda hakan nayi ra'ayi.

Shuru zarah tayi batace komai ba, cikin zuciyanta tace daman ai ba ci zanyiba, chan kuma tace anya yarima baisan wani abuba game da matarnan?

Muryar yarima taji ya ce meyasa da nakira wayanki bakiyi picking ba?

Zarah cikin zucinta tace kujini da mutum saikace ba ni nakirasa bai d'aukaba, kallonsa tayi taga idonsa yana a kan tv, ahankali tace bana kusa da wayanne.

mik'ewa yarima yayi yana kallonta yace akwai abinda kike buk'atane?

Zarah kallonsa tayi tace inason cin faten tsaki.

Toh ai zaki iya sa ma'aikatanki suyi miki ko?

Zarah gyad'amai kai tayi alamun eh.

Wucewa yarima yayi zaifita cak yaja yatsaya batare da ya juyoba yace wannan abun kije kizubar a shara sannan ko nan gaba ban amince a aiko miki wani abu kiciba, duk abinda kike buk'ata kisa ma'aikatanki suyi miki indai bakya iya yi dakanki.

Zarah cike da mamakin maganarsa tace Toh.

Wucewa yarima yayi yai tafiyarsa yabar zarah nan tsaye rik'e da kula.

Bayan ya fita Wucewa tayi tashek'a ma zogalen ruwa saida tawankesa tass sannan tak'ulle a leda takira wata kuyangarta tace taje tazubar a bola ammah kar tabari kowa yaganta.

Kuyangar duk'awa tayi tace Toh ranki yadad'e sannan tamik'e tafita.

Zarah komawa tayi tazauna tare da dafe kanta tana mamakin yarima tace anya baisan wani abuba game da halin su sultana? Chan kuma tatuna da maganar jakadiya da tafad'a mata cewa yarima ko iyayensa bai cika bari suna sanin ta cikinsaba saboda yana da zurfin ciki sosai, jinjina kai tayi sannan tamik'e taje tahad'o coffee dan ji tayi fatenma duk ya fita ranta.

Ahankali tasamu tasha coffeeen ba laifi sannan tajanyo remote tacanza channel tacigaba da kallonta, ahaka har aka kira magri tamik'e taje tad'auro alwallah.

Bayan sallar isha'i saida tayi karatun alk'ur'ani sannan tamik'e taje tashiga wanka, bayan ta fito shafe jikinta tayi da lotions masu k'amshi, powder da lipstick kawai tashafa sannan tad'auko night gown d'inta iya cinya tasaka, gyara gashin kanta tayi tafeshe jikinta da perfumes alkyabbarta tad'auko tad'aura saman kayan jikinta saida takashe gloves d'd'in d'akin sannan tafita tasallami kuyanginta tawuce tanufi part d'in yarima.

Ko da tashiga parlournsa bakowa dan haka tawuce tanufi bedroom d'insa ahankali tabud'e k'ofar kwance tahangosa tsakan makeken gadonsa ya yi pillow da hannuwansa kansa yana kallon ceiling kamar mai tunani.

Readers Also Read

More by Bilyn Abdull