Kenza eBookz

Yarima suhail complete novel - Chapter 47

Yarima suhail complete novel - Chapter 47

Yarima suhail complete novel Chapter 47: Yarima suhail complete novel Chapter 47. au nima ce Aunty? Eh man tun kan inji safkar bulala,,,dariya sukasaka…

3,361 words

au nima ce Aunty? Eh man tun kan inji safkar bulala,,,dariya sukasaka gabad'ayansu nan yad'age mata riga yana kallon cikinta da yake motsawa, d'ago kai yayi yakalleta, murmushi tasakar masa tare da lumshe idanunta, shafa cikin yashiga yi yace kinga babyna shima ya k'agara yafito yaga daddynsa.

Uhm nima ai na k'agara yafito inhuta da wahalar nan, har ma rasa rigimar wa zanji da ita nake tsakanin babyn ko daddynsa.

Ido yazuba mata yace au nima rigimar nake? Fari tayi masa da ido sannan tace wata ran ma k'ara na babyn dan taka rigimar har rasa yadda zanyi nake.

Haka kika ce? Eh, Tallabo fuskarta yayi tare da kallon cikin idanunta yayi ahankali kamar me rad'a yak'ara cewa haka kikace? Gira tad'aga masa alamun eh, bata ankaraba sai jin bakinsa tayi cikin nata nan tabiye masa suka shiga nuna ma juna salon so, gabad'aya suka fita hayyacinsu a nan parlour suka baje, saida taga yana shirin wuce tunaninta sannan tasamu tazame jikinta tamik'e dak'yar tanufi bedroom dan gabad'aya ya kashe mata jiki.

Nan yarima yai pillow da hannunsa tare da maida idanuwansa yalumshe, ahankali yayi k'ayataccen murmushinsa cike da k'asaita.

Bayan kwana d'aya sultana bilkisu da sultana sadiya visarsu tafito nan suma suka kama hanyar garin Abuja sosai sukaji dad'i da sukaga memartaba dan a yanzu har 'yar magana yana d'anyi.

Yarima ko tun ranar da yayi masa aiki rabon da yak'ara sakasa a idonsa, saidai yatura wasu doctors domin sugano masa lafiyarsa ammah duk da haka duk wani abu da za'ayi masa shi yake bada umurni ahaka har memartaba yacika sati guda yawarke garas kamar bashiba dan har takawa yakeyi dakansa batare da anrik'esaba, dressing ko kusan kullum akeyi masa dan a yanzu d'inkin ma ya had'e har an warwaresa.

A ranar da yacika sati guda saida yarima yatabbatar da ba abinda yake damunsa sannan yasallami doctors d'in da suka taimaka masa wajen kula da memartaba dan burinsa ya cika nan shi kuma yafito yanufi gida.

A ranar bayan wani doctor yashigo yai masa injection nan dr muhammad bashir da Dr mu'az suka shigo, bayan sun gaisa da su memartaba, Dr muhammad Bashir kallon memartaba yayi yana murmushi yace ranka yadad'e ya kake jin jikin naka?

Shima memartaba murmushin yayi yace Alhmdllh discharge kawai nake jira dan najini daidai nake, ance min ma har yanzu baku fad'i kud'in da za'a biyaba ai yakamata ace zuwa yanzu kun fad'a anbiyaku.

Murmushi sukayi tare da kallon juna sannan Dr mu'az yace kar kudamu ai angama komai ranka yadad'e.

Memartaba kallon sultan ahmad yayi yace karubuta musu cheque kabasu tunda bazasu fad'i kud'inba hakama mungode da karamcin da akayi mana Allah yabiya.

Dada ce tace ai naso inga wannan d'an albarkan da yayi aikin inmasa godia ammah har yau doctor baku gwada mana shi ba.

Dr muhammad Bashir yaga samu yaga rashi haka aka basu cheque d'in ammah yak'i kar6a.

Sultan abbas ne yace kukar6a mana ai duk abinda zamuyi muku bamu biyakuba saidai addu'a,,, girgiza kai Dr mu'az yayi yace ai doctor d'in da yayi theater d'in ya riga yabiya komai babu abinda baiyiba dan ya ma ce kar a kar6i komai naku.

Gabad'ayansu da mamaki suke binsa da kallo,,,sultan ahmad ne yayi k'arfin halin cewa ya biya komai fa kace? Saboda me zai biya?

Dr muhammad Bashir murmushi yayi yace wannan kad'anne daga cikin halin Dr S, mutum ne mai kyauta da karamci.

Girgiza kai sultan ahmad yayi yace duk da haka baidace yataimaki irin mu ba, taimakon da yayi mana na theater ma kawai ya isa mungode dan bamuda abinda zamu biyasa, yanzu kukar6i wannan kukaimasa.

Memartaba ne yace wai wanene wannan Dr S d'in? Miye full name d'insa? Dan Allah kuyi masa magana yazo mugaisa insaka masa da abinda yayi mani.

Shuru Dr mu'az yayi dan shi ya ma rasa abinda zaice musu,,,muryar Dr muhammad Bashir ce yajiyo yana cewa Dr suhail shine full name d'insa.

Gabad'ayansu saida gabansu yafad'i kusan a tare suka maimaita Dr suhail? Ummi da dada fashewa sukayi da kuka dan antuna musu da suhail d'insu.

Memartaba ne yace dan Allah wanene wannan Dr suhail d'in? daman d'an nan garin ne ko zuwa yayi? Kutaimaka kukaini ingansa ko jikanane.

Shuru sukayi sukarasa amsar da zasu bashi sai chan Dr muhammad yakalli Dr mu'az Girgiza masa kai Dr mu'az yayi alamun kar yafad'a.

Memartaba mik'ewa yayi ya isa inda suke yace dan Allah Kutaimaka min ingansa inaji a raina suhail d'ina ne da nake nema kusan wata ukku kenan yatafi yabarni.

Sultan abbas ne yazo yarik'osa yace ranka yadad'e anya suhail d'inmu ne? Kayi hak'uri kaga bakada lafiya, bana tunanin shine me zaizo yi a garin abuja alhali baida kowa a nan, kuma taya zai ganmu batare da yayi mana magana ba.

Girgiza kai memartaba yayi yace bazan ta6a gamsuwa da maganarkaba har sai nagane ma idona, nidai kukaini ingansa dan Allah.

Dr mu'az cike da jin tausayinsu yace tabbas suhail d'inku ne ranka yadad'e.

Arazane gabad'ayansu suke kallonsa ummi dasauri tamatso inda yake tsaye dada da sultana sadiya suka take mata baya, memartaba ko rik'o masa hannu yayi yace k'ara maimaita min abinda kace kamar kunnena bai jiye min daidaiba kasan inba sunan yarima ba babu abinda yake son ji.

Murmushi Dr mu'az yayi yace tabbas ranka yadad'e abinda kaji gaskiya ne, yarima ne yai maka komai shi yabuk'aci da kar abayyana muku kansa.

Alhmdllh, sultan abbas da sultan ahmad sukashiga furtawa.

Hawayene suka shiga zuba daga idanun memartaba yace dan Allah kataimaika kakaini inga suhail d'ina.

sultana bilkisu ma cikin kuka tace na rok'ek'a kataimaika kakaini inga d'ana.

Dada ma cikin kuka tace kakaini inga jikana ko nasamu sanyi a raina.

cike da tausayin family d'in Dr mu"az yace na amince zan kaiku kugansa a duk lokacin da kuka shirya.

Sultan abbas ne yayi karaf yace yanzu mukeso kataimaka kakaimu.

jinjina kai Dr mu'az yayi yace toh shikenan ranka yadad'e zamu iya tafiya.

Yarima yana komawa gida a bedroom yatarar da zarah tsaye tana shiryawa da alamu wanka tafito, kallonta yayi yace yisauri kishirya yanzu zamubar gidannan.

da mamaki zarah take kallonsa tace barin gida? Ina kuma zamuje daga nan? Wata uwar harara yarima yawurga mata yace ba shawara nake nemaba umurni nabaki,,,,yana fad'in haka yawuce yaje yabud'e wardrobe yafara tsintar musu kayansu.

Zarah kasa ida sanya kayan tayi nan tai tsaye tana kallonsa cike da mamakin dalilin da zaisa subar gidan alhali mutanen suna da kirki, chan kuma sai tace ko dai gida zamu koma, har yagama shirya kayan tana tsaye ,,,juyowar da zaiyi ganinta tsaye yasa cikin fad'a yace bazakisa kayanba?

Nan cikin sauri Zarah tacigaba da saka kayan dan gabad'aya ya koma mata yarima suhail sak.

_Comment_ *Nd* _Share_

_Sis Nerja'art✍🏻_[5/1, 7:01 PM] Sis Naj Atu: 👑👑👑

_*YARIMA SUHAIL*_

👑👑👑

_*Written By~Sis Nerja'art*_

_*DEDICATED TO MY DAUGHTER ZARAH*_

https://m.facebook.com/Intelligent-Writes-ASSO-294634797868361/

*INTELLIGENT WRITER'S ASSOCIATION ®* *[onward together]* *{ we give the readers of ours the best out of the bests,,our inks are melodious and dropping a kinda lights to readers }* THE PEN OF LOVE 😘 HEART TORCHING ❤ TEARS OF SORROWS 😭 CURDLES 🙂 GIGGLES 😁 AND MARRIEGE THINK💑 *JUST GIVE US FOLLOW....*✔

*PAGE* 6⃣8⃣

Tana gama sa kayan bayan yarima tabi suka fito, kallon part d'in jamila tayi taga a kulle yake kasancewar jamila taje anguwa, har cikin ranta bataji dad'iba dabasu samu sunyi sallama da jamila ba.

Suna janye da trolly d'insu sukafito zasu nufi wajen motar yarima, daidai lokacin aka hangame gate motoci hud'u a jere suka shigo, tsaye sukayi suka zuba ma motocin ido cike da mamaki dan basusan ko suwanene ba a ciki.

Tun kan a ida yin parking ummi tabud'e murfin mota tafito dagudu tanufi wajen yarima.

Mutuwar tsaye su yarima sukayi tana zuwa tafad'a jikinsa tarungumesa tare da fashewa da kuka tana cewa kaine my son, daman zan k'ara ganinka?

Tsaye yarima yayi yakasa ta6uka komai, d'ago kai tayi takallesa tare da shafa fuskarsa tace suhail d'ina kaine a gabana ko mafarkin da nasaba ne?

Muryar yarima tana rawa yace ummi na. Rungumeta yayi sosai a jikinsa yace ba mafarki kikeba nine dai a zahiri ummina nayi missing d'inki.

K'ara shigewa tayi a jikinsa tace shine kuma katafi kabarni baka nemeniba? Meyasa? Meyasa kaimin haka suhail.

Ahankali yabud'e baki zaiyi magana hango su memartaba da yayi sun zuba masa ido yasa maganar ta lak'afe a bakinsa.

Takowa memartaba yayi yanufo inda suke,,,ganin haka yasa yarima yajanye ummi daga jikinsa tare da d'an ja baya kad'an.

Memartaba yana isowa wanka ma yarima mari yayi, gabad'aya wajen ido aka zuba masa cike da mamaki ganin yadda yake d'okin ganin suhail ammah daga had'uwa sai mari, zarah ko jikin sultana bilkisu tafad'a tana kuka,,

Duk'ar da kansa yarima yayi ammah ko kad'an bai gezaba,,,muryar memartaba tana rawa yace sake guduwa kake shirin yi a karo na biyu saboda kar muzo gareka? ka kyauta suhail yanzu har kayi tsawon wata ukku batare da kazo ka nemeniba? Hakan da kayi daidai ne?

Cike da mamaki yarima yad'ago yakallesa,,,,memartaba yacigaba da cewa eh suhail koda ni nakoreka ammah ai cikin fushine kaduba kaga yadda nakoma duk akan rashinka, ni kaina nasan na aikata babban kuskure da na iya korarka daga cikin danginka, suhail taya kake tunani zan iya yafema kaina bayan daga baya nagane kaine akan gaskiya, wlh sumayya ta cuci rayuwata, ya zanyi a yanzu inwanke wannan laifin da na aikata kaicona ina ma ace duk cikin mafarkine.

Girgiza kai suhail yashiga yi cikin sauri yafad'a jikin memartaba yace ranka yadad'e kayi hak'uri bahaka bane, ni ban rik'ekaba ko kad'an kawai dai umurninka nacika, kayi hakuri da bijire ma maganarka da nayi wlh nima bahakanan na rabu da ku ba kawai dan gudun abinda za'a aikata daga baya azo ana da nasani ne domin zarah kwata-kwata batada laifi acikin maganar, ina tsoron in cuceta domin na tabbata sai Allah ya bi mata hak'inta, tunda tana k'ok'arin kyautata min taya zan saketa batare da tayi min komai ba, kayi hak'uri ranka yadad'e,

Shafa bayansa memartaba yayi yace hakan da kayi shine daidai suhail nidai burina kabiyoni mukoma gida.

Janye jikinsa yayi daga na memartaba tare da yin murmushi ahankali yace zarah,,,sai a lokacin memartaba yakalli zarah da take a jikin ummi, murmushi yayi yace d'iyata zo mugaisa mana,

Ummi janye zarah tayi daga jikinta, nan zarah taduk'a cikin sauri tagaishe da memartaba.

Amsa mata yayi cikin sakin fuska sannan yace kiyi hak'uri da abinda yafaru zarah.

Girgiza kai zarah tayi cikin kuka tace bakuyi mana komai ba ranka yadad'e duk abinda kukayi akanmu daidaine tunda kune sama da mu, mune yafi dacewa mubaku hak'uri tunda mu mukayi laifi.

Jinjina kai memartaba yayi cike da jin dad'in lafazin zarah, yace Allah yai muku albarka.

Sultan abbas isowa yayi yarungume yarima, yace yarimana naji dad'in ganinka dafatan zaka yafe mana abinda yafaru.

Murmushi yarima yayi yace abbana akodayaushe bakwa laifi nine dai nayi muku laifi. Yarima ma baya laifi hakan da yayi shine daidai,,,cewar sultan abbas.

K'ara shigewa jikinsa yarima yayi yace nagode sosai abbana.

Yarima janye jikinsa yayi daga na abbah yaje yarungume dadynsa cikin jin dad'i yace daddyna kayi hak'uri kayafe min nasan nayi muku laifi.

Shafa kansa yayi yace kar kadamu my son tuni laifinka yagogu daga garemu bare ma suhail d'ina baya laifi, Allah yaimuku albarka

Dariya Yarima yayi yace nagode sosai daddyna, ina alfahari da ku,,,kallonsa yakai ga su dada dasuke gefe d'aya tsaye ita da sultana sadiya, murmushi yayi sannan yawuce yanufi inda suke tsaye ganinsa yasa dada tahad'e hannunta biyu waje guda cikin kuka tace suhail,,,rungumeta yarima yayi cikin sanyin murya yace meyasa matata zatayi kuka bayan ga mijinta a tare da ita? Cikin kukan tayi dariya tare da rungume yarima tace suhail ina farin cikin ganinka, kayi hak'uri da abinda yafaru kayafemin wlh duk abinda nakeyi maka sumayya ce take kawomin zuga.

Murmushi yayi tare da d'ago kai yakalleta yace kakata duk abinda kikayi daidaine kuma kin cancanci kiyi fiye da haka saboda kin isa da jikanki.

Itama d'agowa tayi tace dagaske, d'aga mata gira yayi yace toh ya kikace.

Jan kumatunsa tayi tace suhail bakada dama ammah nagode da naganka.

Murmushi yayi yace nima haka matata,,, daganan yamatsa kusa da sultana sadiya da taduk'ar da kanta tana hawaye, gyaran murya yayi, kamar daman jira take cikin sauri tafad'a jikinsa tare da fashewa da kuka tace suhail kayafemin na cuceka na k'untata ma rayuwarka tun kana k'arami na d'aura maka karan tsana, dan Allah kayafemin akan abubuwan da nayi maka wlh nayi nadama insha Allahu yanzu zan gyara rayuwata.

Janyeta yayi daga jikinsa yace ummah kidaina tunawa da abinda yariga yawuce na yafe miki tun tuni.

Cikin kuka tace nagode sosai suhail Allah yabiyaka.

Ameen ummana.

Nan sultana sadiya da dada sukaje cikin jin kunya sukaba zarah hak'uri akan abinda sukayi mata.

Girgiza kai zarah tayi cikin kuka tace wlh bakuyi min komai ba inma kunyi toh na yafe.

Dr mu'az da yake tsaye chan baya yana kallonsu takowa yayi ya iso inda suke nan yaimusu jagora suka shiga cikin gida Sultana bilkisu tana manne da yarima haka suka shiga kamar wani ya ce zai k'wace mata shi

A main parlour suka yada zango nan zarah taje tad'auko musu ruwa da lemu, memartaba yai gyaran murya yace Alhmdllh gaskiya naji dad'i sosai da naga yarima a yanzu ji nake duk wani ciwo da yake tare da ni ya warke, dan haka gida kawai zamu koma gabad'ayanmu gobe.

Girgiza kai yarima yayi yace kagafarceni ranka yadad'e a yanzu banaji zan iya komawa gida kubarni nan kawai inyaso zan dawo daga baya.

Gabad'ayansu ido suka zuba masa, memartaba ne yai k'arfin halin cewa saboda me suhail, me zaka zauna nan kayi? Kodai baka huceba?

Cike da girmamawa yace ba haka bane ranka yadad'e ina nufin zamu tafo daga baya.

Ina wlh bazaka k'ara kubce manaba k'afarka k'afarmu kayi hak'uri kawai mukoma gida,,,,cewar dada.

Sultana bilkisu ma rik'o hannunsa tayi tace suhail kar kace haka ka amince kawai mutafi 'yan uwanka suna chan suma suna burin ganinka.

Eh suhail ka amince kawai,,,,cewar sultan abbas.

Shuru yarima yayi nad'an lokaci sannan yakalli mu'az da yazuba masa ido, nan mu'az yad'aga masa kai alamun eh, murmushi yarima yayi sannan yace shikenan na amince zan biku.

Gabad'aya nan sukayi murna, haka sukayi ma mu'az godia sosai akan kulawar da yaba su yarima, murmushi mu'az yayi yace duk abinda nayima yarima ban biyasaba domin shi yamin fiye da haka addu'a ce kawai zanyi masa inbiyasa.

Nan memartaba yasa aka kira waya yace ayankar musu ticket.

Jamila ma koda tadawo nan tatarar da su memartaba cike da girmamawa tagaishesu nan mu'az yagabatar da ita.

Sai gab da magrib sannan memartaba yace sutashi sukoma masaukinsu dan su shirya, yaso su yarima subisu masaukinsu ammah yarima yace a'a sai dai goben zasu shigo, ummi rik'esa tayi dan gani take kamar zai k'ara kubce mata.

Murmushi yarima yayi yace kar kidamu ummina babu inda zanje ina tare da ke, kuje kawai gobe zan shigo dasafe.

Kwallah ce tacika mata ido tace kayi alk'awali?

Murmushi yayi a karo na biyu sannan yace eh ummi.

ajiyar zuciya tasafke nan sukayi musu rakiya har wajen motocinsu, saida sukaga tafiyarsu sannan suka dawo, mu'az zama yayi saman kujera tare da dafe kansa.

Ganin haka yasa yarima yazo gefensa yazauna tare da cewa abokina ya dai?

'Dago kansa yayi Cike da damuwa yace prince yanzu tafiya zakayi kabarni? Ya zamuyi idan kuka tafi wlh mun saba da ku bamuso kutafi.

murmushi yarima yayi yace mu'az wa yace maka zamu iya rabuwa? Ai ko muntafi zamu dinga kawo muku ziyara inma takama dakaina zan neman maka transfer kakoma hospital d'ina kacigaba da aiki tunda dama bakada kowa a garinnan aikine yakawoka.

Murmushin jin dad'i Dr mu'az yayi yace prince wlh da ka gama min komai, dan Allah idan kakoma kayi min wannan taimakon. Murmushi yarima yayi yace kar kadamu kafi k'arfin haka wajena insha Allahu zanyi iya k'ok'arina. Nagode sosai prince Allah yasaka da alkhairi.

Koda su yarima suka koma part d'insu kallon zarah yayi da takasa kulle baki saboda murna yace kina murna zaki tafi gida ko?

Eh man sosai ma, kaima kana murna?. Shuru yarima yayi yakyaleta,,,matsowa tayi kusa da shi tare da tallabo fuskarsa saida takalli cikin idanunsa sannan tace kaima nasan zakaso mukoma garinmu dan zamanmu cikin family d'inka shine kwanciyar hankalinmu.

jan hancinta yayi yace kedai tunda kina murna shikenan ammah ni nafison zamanmu a nan.

Marairaicewa tayi tace saboda me kace haka,

Murmushi yayi har saida beauty point d'insa suka lotsa sannan yace saboda a nan babu mai takura mana, a chan ko baza a barni inhuta da matataba.

Murmushi itama zarah tayi tace kar kadamu hearty babu abinda zai hanamu kasancewa da juna dan a yanzu mun riga munzama d'aya.

Ajiyar zuciya yasafke yace hakane dear, ammah zanso kihaihu nan.

Langwa6e kai tayi tace kayi hak'uri mukoma chan garinmu tunda kaga haihuwar da sauran lokaci kuma zatafi dad'i muna cikin danginmu,,,kaga fa kungama magana da su memartaba cewa gobe tare zamu tafi

Shikenan dear tunda kinfi son mutafi toh nima na amince.

Rungumesa tayi a jikinsa tace Nagode sosai my heartbeat.

Su sultan abbas sunkira su waziri a waya sunce gobe zasu dawo nan cikin jin dad'i sukayi musu addu'a akan Allah yamaidosu lafiya.

Memartaba fadar sarkin garin yasa suka wuce suka gaisa tare da yi masa godia akan karamcin da yayi musu a nan suke shaida masa gobe sukeso suwuce garinsu.

baiji dad'iba da yaji sun ambaci tafiya nan yashiga rok'onsu akan suk'ara kwaana biyu. ammah memartaba yace a'a nan suka shaida masa har ticket sun sa a yankar musu.

ba yadda ya iya kan dole yahak'ura a nan sukayi sallar magrib sannan suka wuce masaukinsu, tare da yi musu alk'awali gobe dashi za a je rakiyarsu.

Koda suka koma had'a kayansu suka shigayi cike da farin ciki biyu ga lafiyar da memartaba yasamu ga ta bayyanar yarima.

Daga chan 6angaren su yarima ma haka zarah tak'ara shirya musu kayansu, duk yadda yarima yaso tazo sukwanta k'iyawa tayi saida tagama shirya duk abinda tasan suna so sannan taje takwanta.

Washe gari tun k'arfe goma wayar da ummi tayo masane ta tashesu daga baccin da suke, bayan sun gaisa nan take shaida ma yarima flight d'in k'arfe biyu zasubi dan haka sugama komai dawuri kafin biyu.

Wajen k'arfe sha biyu suka gama shirinsu gwanin kyau, a parlour suka tarar da su Dr mu'az suna jiransu nan suka gaisa sannan suka wuce sukayi breakfast daga nan sukahau yin hira saboda gabad'ayansu basuson rabuwa da juna,

yarima key d'in motarsa yad'auko yadamk'a ma Dr mu'az yace gatanan ka k'ara, zaro ido Dr mu'az yayi yace ranka yadad'e kodai a ajiye maka ko inje dakaina inkai maka har gida? Girgiza kai yarima yayi yace kod'aya na mallaka maka ita halak malak yanzu tazama taka.

Dr mu'az da matarsa godia sukayi ma yarima sosai cikin jin dad'i har da duk'awa k'asa saida sukaga ran yarima ya fara 6aci sannan suka daina godiar

Memartaba ne yadamesa da kira dan haka suka tashi gabad'aya suka nufi chan masaukinsu har da su Dr mu'az,

Rungume yarima Memartaba yayi cikin jin dad'i, sultana sadiya ko jan zarah tayi kusa da ita, duk yadda zarah take nok'ewa ammah duk motsi kad'an da zatayi sai sultana sadiya tayi mata sannu.

Bayan sunyi sallah sarkin garin dakansa yasa aka shirya motoci nan yazo dakansa masaukinsu, lunch ma daga masarautarsa yasa aka kawo musu, bayan sungaisa nan Memartaba yagabatar mashi da yarima da matarsa.

Sosai sarkin garin yanuna farin cikinsa akan ganin yarima da akayi.

Bayan sungama kimtsawa gabad'ayansu suka nufi airport nan suka zauna har saida flight d'in ya iso sannan sukayi bankwana da juna cikin rashin jin dad'in rabuwa da za'ayi.

Dr mu'az, matarsa da zarah har da 'yar kwallarsu yarima ma ne maik'arfin halin basu baki.

Basu sukabar wajenba har saida flight d'in yatashi sannan.

A cikin flight d'inma Memartaba yana tare da jikansa, inda zarah take gefen dada kad'an kad'an da tad'aga ido sai taga yarima idanunsa suna a kanta gabad'aya sai taji kunya saboda su Memartaba da su daddy dan hakama sai tadaina kallonsa.

A chan airport d'in garin gazban tun kan su iso ya cika da jama'a kowa yana farin cikin son ganin memartaba dan basusan tare suke da yarima ba.

Readers Also Read

More by Bilyn Abdull